da na san inda muka nufa ba, na taɓa zuwa mambila sau ɗaya don haka inda muka nufa bai min kama da hanyar ba, idan nayi bacci na gaji na farka na tambayi Ammie har yanzu bamu isa ba sai ta mayar da ni jikinta ta rungume tace har yanzu da saura ban sani ba ashe nesanta ni take da asalina, nesanta ni take da inda na fi wayo da kuma farin cikina duk ku biyu, yamma ne sossai muka isa inda ban sani ba hatta yaren su kaɗan kaɗan nake ji shima saboda akwai wasu kuyangai dake yi anan ina sha'awar iya yaruka na saka su a gaba ina koyo, ko da ta saka driver tsayawa kuka take yi ta bani ƙullin kayan marmari da abinci waenda basa lalacewa da wuri cikin guzurinmu tace in riƙe, muka sauka muka bar driver da Kuyangarta Kande a mota mun yi tafiya sossai har muka kawo gefen wani juji da babu hada hadar mutane sossai ta kalleni.
"Ka yi haƙuri ɗana ina sonka amma dole ta sa zan rabu da kai babu yadda na iya!"
A karye na ce mata
"Ammie Meyasa tunda muka fito kike kuka? Meyasa za mu rabu? Me muke yi anan?"
Ta ja numfashi tana share hawayen dake kara gangara tace mini
"Nan shine inda na ji ya kwanta min ka cigaba da rayuwa, ka yi aiki kaman na jaruman maza ka nema da kanka ka samu har ka tsaya da kafafunka, idan da rabon mu gana watarana za mu gana amma a yanzu ka cire cewa kai ɗan sarki ne jikan sarki, ka jingine ka taɓa sanina ko mahaifinka, ka manta ka taɓa ko da amsa suna Ciroma Sameer ka samu sabuwar rayuwa zan maka sdu'a ba zan gaji ba amma daga yau ka gama zaman masarauta..."
Hankalina ya tashi da kalaman ta na rikice ina tambayarta
"Meyasa Ammie? Me yasa zan manta ku? Meyasa zan manta Abeey?"
"Saboda Dole ne Sameer!"
Ta daka min tsawar da bata taba min irinshi ba Dukda na razana kuma kuka ba ya daga cikin al'amarina ban san na fashe da kuka ba na riƙo hannayenta ina roƙonta kar ta bar ni anan ban san kowa ba, kar ta bar ni anan ba zan iya rayuwa ba Ammie ta zame hannunta ta tureni har na faɗi na rarrafa ba tare da na damu ba na rike kafarta ina kuka sossai da roƙonta ta tafi da ni amma ce min tayi
"Ko a mafarki ka biyo baya na ba zan taɓa yafe maka ba Sameer!"
Baya baya nayi na zube a ƙasa a zaune ina kallonta har ta ɓace min, na ji na tsani duniyar na ji na tsani kowa da komai kuma a lokacin zuciyata ta kafe Abeey na ji ba zan iya sake yi mata kuka ba tunda bata so na ta tsaneni, babu abin da yafi kona min rai irin bolar dake gangana nan uwata tace min in ci gaba da rayuwa, nan fa ta zaɓa min. A inda ta barni anan na zauna har dare ban motsa ba dare da naga karnuka na zuwa wurin cin abinci na bar musu duk abinda ta bani don ba zan iya amfani dasu ba na koma wani gini da ba'a ƙarasa ba na zauna daga ranar na rasa bacci na Abeeyy daga na rufe idanu kalaman ta su ke farautar numfashina....A ranar Ammie ba rabuwa da ni kawai tayi ba ta kashe ruhi da zuciyata kisa mafi muni na yi kwana biyu ban iya cin komai ba sai ruwa kan wani almajiri ya ja ni muka fara sana'ar wanke gilasan mota Dukda ban taɓa mishi magana ba amma shi yana min surutu sossai, kayan aikin nashi ne idan ya gaji zai bani in yi ko kwanaki goma ba'a yi ba garin wanke gilasai mota ta kaɗe shi ya rasu, kayan aikin nashi na cigaba da amfani da su har Allah ya haɗa ni da Mammi.."
Nan ya cigaba da bashi labarin komai da komai mai martaba banda hawaye babu abinda yake, a lokacin da ya zo rasuwar Mammi sai da hawaye ya ziraro mishi ya sa hannu ya ɗauke jijiyoyin kanshi duk sun tashi raɗa raɗa idanunshi sun yi ja sossai da sossai.
Shiruuu ne ya ratsa parlorn fiye da mintuna biyar Abeey a hankali ya ce
"Mahaifiyarka ta cuce ni ta ci amanata Sameer! Ban san me zan yi na huce wannan zafi da raɗaɗin da nake ji ba... Bata da uzurin bani na wannan laifi da ta aikata. Hakika na so Mammin ka tana raye in ganta ido da ido in yi mata tarin godiya marar adadi akan kaunar da ta nuna maka sai dai kash! Allah bai taɓa barin wani don wani yaji daaɗi ba idan ajali ya zo babu mai ƙara ko da second guda ne sai an tafi, a yanzu ma bata ɓaci ba za mu tabbatar mun yi tarin abubuwan alkhairi masu yawa da sunanta don ladar ya je mata a makwancinta. Allah ya musu rahama ita da mai gidanta ya sada su da annabin rahama"
Ya amsa da ameen
"Ɗauki ipad ɗin chan ka kira min Mahaifinta video call za mu yi magana"
Ipad ɗin ya dauka ya saka numbern uncle Musa ya kira aka taki sa'a yana online ya ɗaga zaune yake da Uncle sanusi da Uncle Mansur suna tattaunawa ganin fuskar Rayyan ya sa suka yalwatu da fara'a ya shiga gaishe su yadda ya saba suka amsa kan ya mayar da fuskar kan fuskar Abeey ba tare da ya ce komai ba.
"Assalamu Alaikum warahmatullah..."
Amsawa suka yi suna ta kallonshi kan Uncle Mansur ya zare idanu
"Laamiɗon Fombina mai girma Muhammadu Modibbo Aliyu.."
Duk sai lokacin suka ɗago suka shiga gaishe shi da girmamawa don shima ba ƙarami bane idan bai girmi uncle Musa ba za su yi sa'anni. Sannan ko babu girman shekaru akwai na mulki da sarauta mai girma.
"Na yi muku laifi ina Fatan za ku yi haƙuri ku yafe min kuma ku dubi uzurina, kaman yadda kuka sani sunana Muhammadu Modibbo Laamiɗon daular kudu maso arewacin Kasar nan, a cikin tarihina ina da ɗa namiji tilo da ya ɓace da kananun shekaru inda an yi neman duniya an rasa shi sai satuttuka da suka wuce Allah ya bayyana min shi. Wannan yaro ba kowa bane face ɗan ƴar wurin ku mai rasuwa wato Rayyan a chan anan kuma Muhammadu Sameer"
"Allahu Akbar kabiran! Allah mai girma! Allah mai yadda ya so iko sai Allah ashe dama Rayyan ɗanka ne? Kai Alhamdulillah wannan abu na farin ciki ne Alhamdulillah ina ma Mamanshi na raye ta ga wannan rana..."
Uncle Musa ke fada cikin tsananin farin ciki suka shiga taya su murnar saduwa da juna. Bayan gama barka da jaje Mai martaba ya ɗora
"Laifin da na muku shine na sanar da ku a waya, shi Ciroman ya so ya je ne don martabarku ya shallake haka a gareshi amma ban ba da goyon bayan hakan a yanzu ba, zai iya zuwa ziyara ko wasu kananun al'amura da bai kamallah ba amma sai ya gama blending da dangi ina fata hakan bai ɓata muku ba, in shaa Allah zan yi tattaki na zo da kaina na kawo ku kuga inda yake"
Uncle Musa ya ji daaɗin martaba da ƙimar da aka basu yace
"Ba sai ka zo ba ranka ya dade da kanmu za mu zo har nan mu taya ku murna in shaa Allahu"
"Sai abu na ƙarshe ban san ko za'a yi min wannan alfarma ma"
"Alfarmar ka ya wuce ka roƙa mai martaba sai dai umurni"
Uncle sanusi ya faɗa don basu taba zaton sarkin haka yake da saukin kai da iya mu'amala ba Dukda tarin dukiya da irin rigar mulkin da yake ciki hakan bai hana shi yi musu magana cikin girmamawa da fahimta ba.
"Idan za ku taho ɗin ba matarshi kawai za ku taho da ita ba, za ku taho min da 'ya'yana Jannah Da Abeeha ita jannah za ta koma ne kawai saboda auren dake kanta Abeeha kuwa ta zama tawa aure ne zai fitar da ita daga wannan gida bi'izinillahi"
Sun gamsu suka yi godiya don martabarsu ne Dukda suna da dukiyar da zasu iya rike Abeeha amma Mammi Rayyan ta barwa shi kuma duk inda Rayyan yake dole ta zauna dashi...
Bayan sun ajiye kan sadarwan Mai martaba Laamiɗo ya dubi Ciroma
"Alhamdulillah! Yanzu ka je kayi shirin juma'a idan an sauƙo akwai media team da suke son ganawa da rundunarku da kuka ceto su Aissatou to amma su sun tafi bayan na sallamesu don komawa ga iyalan su bayan sun bar nan shugabanku ya kira ni akan ba za su iya zama har Washegari ba dole na wakilta Galadima ya je ya min godiya ya kuma sallamesu kai za ka gabatar da shirin madadin ku gabaɗaya"
Bai so ba amma ya ya iya dole ya amsa ya yi godiya ya miƙe ya fice.
Yau suka yi finals jiya garin gigin baccinta an dauke musu wuta kuma ba'a yi rana ba don ruwa suka samu basu samu chargy a solar ba kan a kunna gen ta tafi fitsari ta jefar da wayanta a ruwa, ta ji haushi saboda bata da wayan kallonshi tunda ba ya kira yanzu, sossai take jin kewanshi kaman sun wani saba sukuku ta shigo parlorn abin da ya kamata tana murnar kamallah secondary da aka yi da kyar amma damuwar da zuciyarta ke ciki ya hana ta.
A babban parlor ta samu Abeeha na kai da komo wa tamkar ruwan cikin kwano ta kasa zaune ta kasa tsaye ganin Afeefah yasa ta daka tsalle ta riƙo hannayenta
"Afeefah mun warke... Innalillahi wainna ilaihi rajiun khaihhh farin ciki zai kashe ni...! Afeefah Albishirrinki.."
Cike da zumuɗi take maganan har jikinta na rawa
"Goro.."
Ta faɗa cike da mamakin me ya saka Abeehar farin ciki haka
"Afeefah kin zama Gimbiya matar yarima ko in ce Sarauniyar gobe matar Saraki... Ashe Saraki da Mammi ke kiran Ya Rayyan ba'a banza ba? Afeefah mijinki ashe ɗan babban sarki ne mai tarin daraja da tushe me kyakyawar asali? Ashe ya Rayyan jinin sarauta ne ke yawo cikin jikinshi? Kaii amma Allah ya isa wa mahaifin yarinyar nan da ya kalleshi yace kila ba tsatso mai kyau aka samo shi ba ya ci mutuncin sarauta.."
Afeefah dai ta kafe a tsaye tana ta kallon Abeeha na zuba chan tace
"Anya Adda Abeeha lafiyarka kuwa? Wani irin magana kike tayi ba kan gado...? Wani yaya Sarakin?"
*Wayyo Hannun mar'atussaliha😩
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*47*
"Yaya Rayyan mijinki nake magana a kai girlll wlh da gaske nake miki yanzun nan Baba Musa ya ƙira ni yake cewa za mu shirya tafiya Fombina gobe sun sayi tickets already, ya ce mu shirya kaya kuma mu kintsa komai don za mu iya ɗan jimawa bamu zo kd ba."
Bata san me ta ji ba a lokacin mamaki ko tsananin farin ciki, tayi matukar taya shi murnar reconsiling da iyayenshi don dole su ɗin su ne dolenshi ko ba jima ko ba dade, ashe yana da alaƙa da sarauta? Fuskarta cike da murmushi tace
"Alhamdulillah Allah mun gode maka"
Wani sashe na zuciyarta kuma tsoron tafiyar take don bata san me kuma zata tarar ba, hakika ta fi jin natsuwa da kwanciyar hankali a gidan na Mammi, sai ta fara tunanin idan basu karɓeta ba fa? Dama gashi ba sonta yake ba kila suna ce mishi ya rabu da ita zai rabu da ita a yadda ta san tsarin gidan sarauta.
Abeeha ta wuce ta shige sashensu zuwa ɗakinta ta samu bakin gado ta zauna
"Allah mai girma annabi mai dumbin daraja! Yanzu ni ce Afeefah ke da matsayin matar ɗan sarki mai daraja a wannan ƙasar? Anya? This is too good to be true... Hankali ba zai kama ba ni Afeefah dai ta Dutsen-wai annoba Mayya ajalin duk wanda ya raɓe ki!"
Bata san adadin lokutan da ta dauka zaune a wurin ba har lokacin sanye da uniform don ba sallah take ba bare tayi tunanin azahar da aka idar a wasu masallatan, tana nan zaune sai ga Abeeha ta shigo da sauri bayanta jannah tana cewa
"Zo ki ga wani abu Khaihh Ya Rayyan duniya ne! Sarakin Maammi ne a gasken gaske an tashi kaina!"
****
Yana fita daga sashen Laamiɗo Saleem ya ƙira yana tafiya a hankali suna magana sun jima sossai suna wayan Saleem ya san komai a kanshi ya kuma taya shi murna kwarai shima kuma yana cikin masu tahowa gobe ɗin, idanun Rayyan ne suka sauƙa akan Fulani Adama dake tahowa hanyar sashen mai martaban, bai wuce ba sai ya tsaya yana cigaba da wayan idanunshi na a kanta yadda take tafiya cike da izza da takama bayi da kuyangi na zube mata ko kallo basu isheta ba ɗauke ido yayi ya cewa Saleem
"Zan saka maka wani abu ka sallami duk ma'aikatan gidan ka kuma ba su haƙuri na barin aikin ba tare da an sanar da su da wuri ba, za'a basu abin da zai ishe su jarin wata sana'ar in shaa Allah. Please a rufe komai yadda ya kamata don zan dawo ba na zo kenan ba!"
Kalamanshi na karshen karab a kunnenta, idanu ta zuba masa Dukda kaɗuwar da tayi na namijin da ta gani a gabanta ta wani sashen ta ɗan ji sanyin kalaman nashi har hakan bai ɓuya a kan fuskarta ba sai da tayi murmushi ya sake kawar da idanu a kanta yace
"Na gode Saleem za mu yi magana please ka sanarws Sulaiman kafin na ƙira shi, Sai na ganku a gobe ɗin..."
Yana sauƙe wayan ya kalleta
"Barka da wannan lokaci Mama..!"
Ya faɗa da ɗan murmushi mai dauke da dumbin ma'anoni.
"Ashe rai kan ga rai Sameer? Ko da shi ke na zaci ka manta da mu gabaɗaya ai shiyasa ban ga ka kawo gaisuwa ba..."
Har lokacin yana dan murmushi yace
"Wani abin ake mantawa amma wani ya fi ƙarfin mantuwa Mama, zan zo in shaa Allahu ban gama warware gajiyar aiki bane. Na bar ki lafiya"
Yana kai nan ya wuce ta Gaabɗo ya bishi da sauri.
Da kallo ta bi bayanshi sama da mintuna biyu kan ta juya ta nufi sashen na mai martaba.
****
Saleem na sauke waya ya kalli Mommy dake zaune cikin kujera a sabon gidansu da suka dawo komai na ciki sabo ne kuma a tsare gwanin kyau da ɗaukar ido yace
"Mommy kin ji ikon Allah ko?"
Duk su Sameera idanu suka mayar kanshi mommy tace
"Me ya faru?"
"Mommy ashe Rayyan jinin sarauta ne, mahaifinshi shine Laamiɗon Fombina."
"Da gaske kake ko wasa?"
Cike da dumbin mamaki mommyn ta jefa mishi tambayar
"Wallahi da gaske mommy yanzu haka yana masarautar su ashe ƙanwar shi ce aka yi kidnapping suka je suka samu sa'ar tseratar dasu, gobe duk su Afeefah za su tafi chan nima yanzu zan sayi ticket"
"ikon Allah ikon gaske, wato a wannan duniya ka kalli mutum ne kawai baka san waye shi ba, No wonder yake da ɗabi'ar sarautar... Ikon Allah wannan abin mamaki dayawa yake"
Sadiqa tace
"Oh wa zai tuna Afeefah za ta iya sa'ar zama matar irin wannan mutumi? Yanzu mu fa ko kallonshi sai da hanya...waye bai san irin tarin dukiyarsu, karfin mulkinsu da izzarsu ba!"
Samha tace
"Gaskiya tayi dace kam tsuntsu daga sama... Mun mata murna Allah ya cigaba da basu zaman lafiya haɗe da zuri'a dayyaba"
Duk suka amsa da Ameen amma mamaki da tsoron Allah na sake rufe su rufff.
Saleem ya miƙe ya fice daga gidan.
****
Kitchen ya shiga kai tsaye bayan shigarshi sashen ya dafa indomie don babu abinda babu na girki cikin babban kitchen ɗin komai na zamani komai kuma fess kaman ka lashe don walwali, a plate ya juyo ya dawo parlor hannunshi ɗaya rike da ruwa yana gama ci ya mayar da kwanonin ya wuce ɗaki bai samu ya Kira Abeeha da ya ga missed call nata ba saboda lokacin masallaci dake kokarin ƙurewa ya sauya kaya zuwa wasu Fararen jumpha hadadden ɗinki 'yar ciki da babbar riga ya fita yayi kyau ainun daga ka ganshi zaka san yaro da kuɗi ne abokin tafiyar manyan, ga sarautar amma ya tafi da tsantsar wayewa, ilimi da sanin kan tsarin shiga.
Hula da takalmin da ya saka duka farare fatarshi sai shining yake Dukda ma ya ɗan yi duhu kaɗan saboda zaman da suka yi daji amma fess yake ba ma zaka gane ba idan ba ka san shi ba, turare ya feshe jikinshi da su kala daban daban kan ya zari wayanshi ya fito tuni duk suka miƙe dogaran suka fara zabga mishi kirari ya ɗaga musu hannu don bai cika so ba yayi gaba suka rufa mishi baya har mota, Dukda masallacin ma a cikin masarautar yake sai dai akwai 'yar nisa don haka dole mota ya shiga suka yi har motoci uku da dogaran suka nufi masallaci.
Mai martaba na shiga shima ya iso ya shiga nan aka fara huduba bayan an gama tsaf aka gabatar da sallah kaman yadda addini ya tanada aka yi adu'o'i kan aka shiga watsewa a hankali, daga nan fada suka nufa don sarki na son ganinshi yana isa gaban manya jagoran addini da al'ada na fulani wato Laamiɗo ya gabatar dashi a matsayin Ciroman Fombina kuma Yarima Fuunange na ƙasar Fombina (Yariman Matasa) a take aka mishi rawani fari ƙal mai kamshi wow ya fita kaman ka sace shi ciki, kasancewar wurin akwai yan jarida kala kala tuni ya fara zagaya duniya.
Turaki ne ya karɓi abin magana ya gabatar da kanshi kan ya ce
"Ciroma alhakina ne da in sanar maka aikin matsayinka, na san ka riga ka san Ciroma shine wanda aka ɗauka matsayin ɗan gado ko mai jiran gado. Yarima Fuunange wato Yariman Matasa kuwa mun bar maka goben matasan mu ne a hannunka, kai ne shugabansu wurin ganin sun cimma al'adar mu na fulani bisa kan daidai wato:
• Koyon Pulaaku (hakuri, ladabi, kunya, jarumta).
• Koyon sana'a ko aikin iyaye (kiwo, noma, ko fatauci).
• Haskawa a cikin al'umma ta hanyar waka, rawa, da wasan al'adu da gargajiya.
Muna yi maka Fatan alkhairi da Fatan Allah ya baka ikon sauke wannan nauyi da aka ɗora maka"
Tuni sarkin busa ya fara busa algaita mai daaɗin sauraro dogarai suka shiga jefo kirari daban daban, ya miƙe tsaye ya isa gaban mahaifinshi yayi godiya ya juya aka yi mishi rakiya da wannan busa da sarewa
"Taaakawarka lafiya ɗan sarki jikan sarki kuma uban sarkin gobe, kaaaareka Ciroman duk duniya Yariman Matasa gaba saalaamun baya salaaamun, maƙiyanka fadawarka ɗaawisu sarkin ado... Kyaun ɗa shi ne ya gaji mahaifi kaareka Ciroma"
Abin da ake ta nanatawa kenan busa da sarewa na tashi har parlorn baƙin shi na sashenshi inda anan zai gana da 'yan jaridar da suke jiran shi kan aikinsu.
Zama yayi ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya yana dan lumshe ido ya buɗe saboda gajiyar da yayi ga chan ƙasan ranshi wani abu na mintsininshi na kewar abin da zuciyarshi ke mararin ko da sauraron muryarta ne bai samu dama ba.
"Ranka ya daɗe Dukda abin da ya ajiye mu anan daban sai dai za mu fara ne da taya ka murnan shigowa cikin ahalinka lafiya, shin me za ka iya cewa akan farin cikin da kake ciki a yanzu? Menene kuma ya zama babban mukamin bayyanarka a wannan lokaci?"
Murya ya ɗan gyara bayan yayi sallama da Fatan alkhairi kan ya furta
"Komai lokaci ne na yarda da wannan, sannan bafulatani yace Munyal deefan hayre, ko va'i fu jippan"(mai haƙuri kan dafa dutse kuma duk nisan jifa ƙasa zai dawo)"
Amsar kenan da ya bayar, dan jaridar ya zaci zai kara wani abu amma sai ya ji shiru sai yace
"Masha Allah, Toh bari mu koma abin da ya ajiye mu anan shin menene ya faru? Ta ya aka yi taron al'umma suna jiran ganin waennan miyagu sun kasance Fulani kaman yadda aka jima ana yi wa Fulani kuɗin goro sai kuma aka haihu a ragaya?"
"Dama chan kulba ta jima tana ɓarna ana cewa jaɓa ce, bana manta ina da wani shugaba a baya da sanadiyar kudin goro da ya mana ban taɓa furta mishi ni bafulatani bane amma ya kafa min karar zuka ban ci mishi ba ban sha mishi ba, hakika wannan irin zato na duk bafulatani ɗan ta'adda ne ya jima yana ciwa dayawa tuwo a ƙwarya.
Ba a tuna baya in ji masu iya magana wai gyartai ya ci sarauta, a lokacin da duniya ke kwance kabilu mabanbanta kan shiga rugagen Fulani ayi wasa tare, a ci abinci tare a sha kindirmo a dalilin haka har zumunci ya ƙullu sai auratayya ta shiga tsakani. Da tafiya tayi tafiya a sannu sannu aka fara kwacewa Fulani shanu da matayensu a rugage kafin komai ya ta'azzara da abin ya fara zuwa gidan gona da kauyuka sai aka yi musu kuɗin goro aka far musu da kisa na kan me uwa da wabi wanda kan iya ɗarsa ɗaukar fansa, dayawa daga cikin Fulanin da suke rayuwa a daji babu ilimin addini ba na zamani, malamai babu ruwansu da kai da'awa, gomanti babu ruwan ta da samar da ingantacciyar ruwa ko makarantun zamani, aka kwace sandunansu na kiwo aka damƙa musu makamai saboda wani ƙudiri kawai na samun duniya a ji daaɗin cin ta da tsinken sakace.
A hankali ringingimu suka fara yawa ta yadda zaman lafiya yayi mana ƙaura hakan ya shafi har waenda basu ji ba basu gani ba, shi fa ɗan ta'adda bashi da ƙabila, yare, addini ko jinsi in dai mutum bai da imani ko wanene shi bahaushe, Fulani, kanuri, yoruba ko igbo zai iya kasancewa ɗan ta'adda hasali ma ku sani ba Fulani bane suka aikata mana wannan ta'asar idan ma su ne suka aikata wa wasu daga cikin mu a wannan karon ba su bane don ma turanci ne tsantsa a bakin waennan, makamai da abincin da suke ci be yi yanayi da na bafulatanin ruga ba sai na wayayyen mutum ɗan zamani amma kuma idan zasu yi hausa su kan yi da sigar harshen Fulani Lallai an jima ana ruwa ƙasa na shanyewa."
Ɗan jaridar cike da gamsuwa yace
"Barka da Yariman Matasa Ciroman Fombina, hakika gwalagwalan kalamanka sun fi yanayi da na hikima Allah ya sa mu gane. Toh wace hanya kake gani za'a bi wurin dakile wannan al'amari da ya ta'azzari al'umma yake kuma lalata musu Matasa?"
"Hanyoyin masu sauƙi ne ga al'umma amma masu wuya ga gomnati don zai kawo musu cikas amma idan al'umma suka tashi suka yi aiki a tare za'a iya maganceta cikin sauƙi, hanyoyin za su iya haɗa wa da
• Karfafa tsaro da sa ido a kan dazuka da
hanyoyi.
• Ƙara horo da kayan aiki ga jami'an tsaro.
• Bincike da hukunta masu laifi cikin hanzari.
• Ƙarfafa al'umma da aikin yi ga matasa.
• Ƙarfafa haɗin kai tsakanin al'umma da hukumomi - wato tsaro na gari.
• Ƙin biyan kudin fansa - domin rage ribar garkuwa"
Yana maganan ne yana ƙirgasu da yatsun shi cikin aji da iya magana.
Kanshi duk ya ishe shi da ciwo da kyar ya gama sallama da mutane yayi la'asar ya shiga ya kwanta yana lumshe idanunshi da suke mishi nauyi ainun duk yadda ya washi baccin yamma bai san ya ɗauke shi ba don ya sha magani ga gajiya da ya tarar mishi.
***
Idanu kawai Afeefah ke Binshi dashi tun sanar da dawowanshi hasko shi da aka yi ana mishi sarautar Yariman Matasa da ma hirar da aka yin don live ne a manyan jaridu har international, Fatan alkhairi da ake Binshi da shi da yabon da yake sha duk suna kallo a ipad ɗin Abeehar, ita dai ta rasa me ke damunta ma hawaye kawai ta fara tsabar feelings ɗin sun zo mata daban daban, ya mata kyau ba ƙarami ba yadda kuma ya mata ta san yayiwa yanmata dayawa, kishi na taso mata sai kuma ta shiga damuwar anya ma a mace ya dauƙeta? Don ko ta wani ɓangare tana ganin ita ɗin ba tsararshi ba ce, tun daga tsatso, asali, ilimi, dukiya da kuma mulki ba ta inda tayi matching da shi kenan 'yan uwanshi za su iya ware ta yadda take jin labarin gidan sarauta?
Meyasa be neme ta ba? Sukuku haka su Abeeha suka taya ta haɗa kayanta akwati biyu suna ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 40