Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
jin alfahari zuciyarta fal godiyar Allah tace "Lets start with the shopping" Kai tsaye shopping din ya kaita a tare suke tafiya hannunshi rike da nata ɗayan yana tura chart na shopping din ita kuma tana duba abinda zata ɗauka. Tsaye yake sai dai bayanshi a jingine da stall ɗin kayayyaki inda suke babu wasu yawaitar mutane, ita ke sayayya shi ya zuba mata idanu yana aikin kallo, sanye yake da full Black Jean nd top ya saka facing cap da ya zauna mishi sossai saboda mutane kar su gane shi, takalman kafafunshi ma bakake ne, hannayenshi duka a zube a aljihu... Don tun dazu suke tsaye wurin choculates ɗin tana ta rawan ido. Ta ɗauko wani choculates tana dubawa sai kuma ta ɗan ɗago karab suka haɗa idanu kusan karo na biyar kenan a take ta Shagwaɓe fuska tana kallonshi ya ɗan saki smile yana ɗage mata gira guda "ya dai? Na miki ne?" Ya ƙarshe da wani kayataccen murmushi... "Ni ya kamata in ce haka ai tun da ni ake ƙarewa kallo.. Ni Allah watarana har muni na sai ka binciko" Ta faɗa cikin yanayin da ya saka shi faɗaɗa murmushin shi, choculates na hannunta ta ɗaga sama "Ina son picking wa su suhail wannan yayi ko? Ko me kake tunani?" Very naughty yana ɗan lashe lip ɗin shi na ƙasa ya furta "I am thinking of kissing you..." Hannu ta saka ta rufe baki tana zazzaro ido ya saki dariya mai sauti kan ya yunkura ya nufe ta, kalle kalle ta fara kan ta yunkura kuwa da gaske yayi pecking lips ɗin nata hannunshi na ɗan manna ta da jikinshi. "Ya Saraki waje fa muke" "Ina ruwana" Ganin yana ta kallon fuskarta ta san zai iya aikata abinda ma ya fi haka don haka ta janye ta saka choculates ɗin tace su tafi ita kam ta gama, sai murmushi yake mata don ta bashi dariya yadda take zare ido kaman yayi komai ne gaban mutanen, shi ya biya kuɗin suka fice. Sossai suka zazzaga ya kashe ta da tarin soyayya wai murnar kamallah exams sai dare suka koma masarautan, a sayayyanta har su Ammie ta yiwa don haka tana idar da isha ta fito hadimarta tayi saurin karbar manyan ledojin hannunta suka nufi sashen Ammin don shi bai shigo ba tukuna, ta shiga sashen Ammin da sallama sai idanunta suka sauƙa kan zarah dake tsugune ƙasa sanye da hijabi tana kuka sossai. Gefe ta samu ta zauna bata ce komai ba har zarahn ta gaji da kukan ta fara roƙon su yafiya duk ta rame tayi duhu. Ammi ta sauke numfashi tace "Zarah ki daina kukan nan haka ni kam na yafe miki, wlh ban taɓa bambanta ki da Aisha ba Dukda na ji mamakin ƙudirinki a kaina amma tunda kin gane kuskuren ki Allah ubangiji ya yafe mana gabaɗaya" Aisha ma tace ai ya wuce. Ta kalli Afeefah zata yi magana Afeefah tace "Ni dai baki min komai ba wlh zarah. Allah ubangiji ya cigaba da ɗora mu duka bisa turban gaskiya" Suka amsa da Ameen kan ta miƙe ta fice suka bi ta da kallo. Afeefah ta gaishe da Ammie ta amsa cike da kulawa tana tambayarta exams "Alhamdulillah Ammie mun gama lafiya" "Allah ya ba da sakamako na alkhairi, yanzu sai shirye shiryen tafiya Kaduna ko?" Kai ta gyaɗa Ammie tace "Masha Allah, Allah ya nuna mana. Akwai saƙo zuwa da safe za'a kawo miki sai ki duba ki ga idan akwai abinda kike son ƙari ko chanji duk sai a yi" Godiya tayi sossai kan ta miƙawa Ammie ledar hannunta daidai Rayyan ya shigo kenan tana cewa "Ammi mun je shopping ne sai na ɗauka muku da Abeey" Ta miƙawa Aisha nasu. Ammie ta buɗe ledar Dukda duk wani kyauta da za'a yi mata tana da halin yin fiye dashi amma kyautatawa abu ne mai daaɗi kwarai kuma ta ji daaɗi har ƙasan ranta Leshi ne mai tsadar gaske sai turare shima designer na Abeey, Abeeha da Zarah dogayen riguna ne egypt Abaya sai yan abun ciye ciye tarin choculates. Shi karan kanshi Rayyan fuskanshi ya nuna jin daaɗi ainun Dukda tare suka Saya amma ko kusa bai san har da su Ammie ta yi wa sayayyar ba sai darajar ta ya ƙaru a idanunshi barin ma da ya ji adu'o'in da Ammie ke yi mata anan ya fahimci duk kudin iyaye kyautata musu na saka su farin ciki kuma hakan Allah ne kadai ya san irin ladar da zai baka bisa wannan murmushi da ka sanya su aiko ya ƙudiri aniyar cigaba da ganin wannan murmushi na Ammie, Sai kusan goma suka bar sashen. Bayan kwana biyu da gama exams ɗinta suka fito a shirye tsaff cikin shiga na alfarma, tafiyar har da Abeeha da Aisha don duk sun gama exams motoci shida ne ya kaisu Airport yana riƙe da hannunta cike da kulawa da so da kauna har suka sauƙa a filin tashi da saukar jirgi na Abuja, anan ma motocin alfarma bakaken prado sai sheki suke da securities ne suka zo ɗaukar su ya san aikin mai martaba ne don haka babu wani dogon nazari suka shiga zuwa gida, sun samu gidan a cike su Saleem da sisters ɗin shi ga Sulaiman da matarshi da Twins su fauza ga jidda an shirya musu abinciccika iri daban daban kasancewar tafiyar mintuna 40 ne ba wani gajiya suka yi ba nan Sulaiman da Saleem da kuma Rayyan suka zauna sitting room yayinda 'yan matan suke ta hira a parlor babu wani nuna bakunta ko rashin sanayya kaman 'yan uwa. Sai wuraren isha duk bakin suka tafi Aisha ta sauƙa ɗakin Afeefah na ɓangaren Mammi yayinda su Afeefah suka sauƙa sashensu. Washegari da safe suka fito a shirye tsaff suka shiga wannan motocin nan a jere suka Lula sai Anchau Shigowar su Layin su Aunty zee suka jera gabaɗaya securities ɗin suka fiffito aka buɗe musu kofa za ta sauƙa ya riƙe hannunta yana kallon gidan da ya fara ganinta ciki a sadda ta sallamar da Rayuwa, ita kanta tana tuna ranar da aka yi yunkurin kashe ta a wannan gida, tana tuna rayuwarsu da Aunty zee tana iya tuna ranar da ya fara tare ta a cikin jikinshi lokacin da ta yanke yin mai Dungurun gum da rayuwarta Wai HAIHUWA DA HANJI a sadda ta sallamar cewa barin ta duniyar shine maslaharta idan har ta tafi ai shikenan babu mai kallonta bare yayi mata sharrin maita ko zama annoba. Idanunta cike da hawaye ta kalleshi ya lumshe nashi cikin su fuskarshi babu walwala yace "Kin ga dalilin da ya sa bana so ki zo ko?" Ta mayar da kanta ƙasa ta san kuka kam sai ta yi shi kuma abinda baya so kenan sam. "Ki min alkawari ba za ki yi kuka ba" Tayi shiru bata ce komai ba, ya zame hannunshi yana sauke numfashi sai ta juya ta sauƙa ta nufi kofar kyauren gidan da ya tsufa mata ainun kaman ba gidan Aunty zee ba da yake fes fes, jama'ar unguwa dayawa sun fita suna kallon wanda ya zo don jiniyar masu take musu baya ya ja hankalinsu sossai. Sanye take da wani dakakken purple lace mai shegen tsada an yi mata dinkin Borno style straight skirt da bubu da yayi mugun kyau ta zuba accesories gold ne daga wuyanta zuwa hannunta mayafinta ya zauna mata sossai hannunta rike da wani sabon designer bag da ta dauka cikin kayan aurenta da har lokacin suke gidansu na Kaduna don bata tattare ba, sai takalmin ta mai ɗan tudu wannan vibe ɗin na manyan mata kuma hajiyoyi yan gatan mazajensu shi take bayarwa har ta tura kofan gidan ta sanya kai da sallama. Wasu yara biyu ta gani suna wasa sanye da wasu kaya da suka fi yanayi da tsumma sun yi dukun dukun macen gashinta kaman wanda yayi shekara bai ga ruwa ba, kafafunsu babu takalmi, ganin ta yasa suka tsaya suna kallonta kamannin fuskokin su yasa taji tayi bursting to tears, gabanta na tsananin faɗuwa ta ce "Suhail...! Suhailaah???". Abeeha ce ta dafa ta ganin tana ƙoƙarin faɗuwa saboda jirin da ta ji ya ɗauketa a lokacin da suka amsa, waennan su ne yaran Aunty zee? Su Suhail ne haka? Innalillahi wainna ilaihi rajiun "Ina Babanku?" Cikin maganansu suka ce "Yana ɗaki kwance ba shi da lafiya" Da sauri ta nufi ɗakin da yake kwancen babu komai cikin ɗakin sai tantagaryan siminti, me ya faru? Ta fara tambayar kanta kan ta isa inda yake kwance kan taburma idanunshi a buɗe yana kallonta ta duka gangarshi "Uncle Usman!!" Hawaye na zubo mata babu kakkautawa a hankali yace "Afeefah?? Ke ce??" Hannayenta ta sa ta toshe Bakinta tana sakin kuka da gaske su ɗin ne cikin wannan hali? "Uncle me ya faru? Ina Hamdiyya? Me ya samu aikinka baka da lafiya ne?" Duk ta rasa ma me zata tambaya shima yana kuka yace "Ki yafe min Afeefah don Allah ki yafe min na cutar da ke, na kasa rike amanar da zainabu ta tafi ta bar mini ki gafarceni AFEEFAH" "Baka yi min komai ba uncle wlh baka yi min komai ba hasali ma ka rike ni da amana tsawon shekara da nayi a gidan nan baka taɓa hantara ta ba, wlh baka min komai ba ni ban ga laifinka ba ko da ka zarge ni saboda ina da tambarin tun farko manne a goshina" "Na kasa amincewa da cewa Allah ne me kashewa kuma mai raya wa, hankali na ya tashi ainun don bayan mun binne zainab kin dawo mun kore ki sai muka muka je asibiti da su Suhail za'a yi musu riga kafi a kuma ba mu madarar da ya kamata su cigaba da sha anan ne likitan ya ji maganan da muke yi da Hamdiyya da maiyya ce ta kashe zainabu yayi saurin taka mana birki ya kuma shiga yi mana bayanin abinda ya faru da zainabu wanda bamu sani ba, ya ce mata dayawa suna samun wannan matsala na Postpertum ko a samu taɓuwar mu'amala ko irin ciwon cikin wasu kam ma har a zaci sun haukace ne, ciwon cikin nata bamu farga da wuri ba sai da ya mata illah kwarai muka koma a sannan babu abinda za su iya ta rasu. Hamdiyya kuma dama ta jima tana yi mata hassada tana jin haushin yadda ta samu ciki ita tana zaune hakika ta yi yunkurin illa ta cikin tun kan su zo duniya Allah na kare su har ta haihu tana ganin kaman za ku haɗu ku kwashe dan abinda na mallaka da ke da zainabu ga yarana da farin cikin samuwar su bai ɓoya mini kuma dama ta jima tana sanyawa ranta ba sonta nake ba na aureta ne kawai don in haihuwa a yanzu da bata haihu ba matata ta haihu ta gama amfani kenan zan iya sakarta kowani lokaci hakan yasa ta ƙarfafa hassadarta a kanku musamman ke tana amfani da baƙanta miki tana kuntatawa Zainabu. A ƙarshe tayi sanadin da kika bar gidan nan anan ta fara rainon azaba ga yarana ba tare da na sani ba, duka zagi tun basu san kansu ba, ta bar su da yunwa ta bar su cikin ruwan wanka duka don ba ita ta haife su ba Allah ne ke kare su ban sani ba, a ranan da na san duk abinda take kullawa na shiga masifar tashin hankali marar misaltuwa musamman in na tuna abinda na yi miki daga nan jinina ya hau na samu matsalar shanyewan jiki, a takaice Hamdiyya ta tattara komai ta sayar akan ba zata iya zama da ni ba ga jinya, ga rainon ƴaƴan da ba nata ba kuma bata da damar haihuwa, ko sati ba'a yi ba na samu labarin mota ta kaɗe ta ta rasa kafafunta ta kuma rasa rabin fuskarta duk kudin yana tafiya a jinyar da har yau bata warke ba. Kuɗin da Zainabu tayi ta ajiye miki a asusu da su na tsira sai waenda abokan arziki kan kawo da shi nake aika yaran nan su sayi abinci su ci ko makota su basu, bana iya yi musu komai ko wanka sai dai su je su watsa" Sossai Afeefah ke kuka, Allah sarki rayuwa amma Hamdiyya ta cika azzalumar matar uba kuma ko a yanzu ta ga ishara, Rayyan Aisha ta kira don Afeefah ta kasa daina kuka hankalinta ba karamin tashi yayi ba shi ya kira aka dauki uncle Usman yace a koma cikin Kaduna dashi a kaishi asibiti zai kira Sulaiman kan su juyo. Su Suhail na rungume da Afeefah suka fito zuwa mota yan unguwar na zuwa su gaisheta suna ta mamaki har wasu na tambayar ko Afeefahn Aunty zee ce ta gyaɗa musu kai, Rayyan ya zubar da dukiya don duk wanda ya nuna ya gane ta aka gaisa sai ya mishi kyauta daga nan suka nufi Dutsen-wai. "Afeefah!" Ta kalleshi ya riƙe hannunta ya sa hannu yana share mata fuska yace "kuka sam bai kamace ki ba, ko don zafin da nake ji a nan ya kamata ki sassauta" Ya ƙarasa yana nuna zuciyarshi. Ta gyaɗa kai ya ce "Na san burinki shi ne ki yi kuɗi, ba kuma don wani abu ba sai don ki tallafawa al'umma musamman na ƙauye irin cikin kauyen ku da ake rayuwa kara zube babu neman ilimi, babu sana'a ana rayuwa irin rayuwar dabobbi ko zamanin da chan baya, ina so in sanar miki cewa na ba da wannan gudumawa na buɗe miki Center na farko ina fata ya zama farkon buduwar tarin alkhairanki... Ina adu'a Allah ya sanyawa gidauniyarki daga na farko har na karshe albarka ya dafa miki ya kuma isar miki da ladan... Akwai Center da aka gama buɗewa a Dutsen-wai da Sunanki a yau za'a yi taron kaddamarwa a cikin wannan plaza akwai kayan aiki da malamai na Musamman da zasu ke koyawa mata sana'o'in dogaro da kai kaman su ɗinki da sauransu akwai kuma makaranta islamiyya da malaman da muka yi hiring na musulunci da za su tsaya tsayin daka wurin ganin sun koyawa matan wannan kauye da ma mazan addini akwai kuma babban masallacin juma'a a kusa da wannan plaza shi kam na Mammi ne ina Fatan duk Sallar da za'a yi ciki ladar ya isa gareta. Ba ni da alaka da kula da wurin daga yau duk naki ne ga takardun da ma komai da komai na plaza ɗin kyauta ne na musamman zuwa gareki" Jikinshi kawai ta faɗa don ta gigice ta rasa ma wani irin abu zata yi, kuka kawai ta saka mishi yana ta aikin rarrashi za tayi godiya ya manne Bakinta da nashi yana kissing passionatly sai da ya tabbatar ta daina hawayen kan ya saki yayi pecking goshinta "Anything for you my baby girl ki sani wannan ɗin mafarin nasararki kenan a rayuwa, duk wanda ya baƙanta miki a da a yanzu yana a karkashin kafafunki, na ji daaɗi da kika nufi saka musu da alkhairi bayan sun bi ki da sharri amma ki sani wannan yunkuri naki na basu ilimi makami ne mai girman gaske a duniyarsu ladar ki sai a wurin ubangiji" Daidai nan suka isa cikin Dutsen-wai ita ke kwatanta musu har kofan Gidan Kawu Labaran. 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh ADABI WRITERS ASSOCIATION *FREE BOOK* "Last Page na zuwa anjima in shaa Allah. Wlh jiya na yi gajiyar da ban san adadi ba ina buɗe ido da niyyar typing idon na rufuwa ganin ba zan iya ba yasa nayi bacci and yau ma same thing zan lallaɓa in ba ku shafin karshe in shaa Allah. Na gode da haƙuri da ni* *59* A gaban gidan ta tsaya ta ƙura mishi idanu kaman yanzu ne komai ke faruwa da ita, tana tuna baƙar wuyar da ta ci daki-daki cikin wannan gida, hawaye ne suka cika mata idanu shaidan na raya mata ta juya ta koma kawai don basu chanchacanci duk wata alfarma daga gareta ba, da kyar ta hadiye wani abu da ya tsaya mata a wuya tana tuna ni'imomin Allah a gareta sai ta furta Alhamdulillah don ko daga fasalin gidan zaka san cewa rayuwa ya ƙara taɓarɓare musu wane wane don daga inda take tana kallon har kofofin dakunan gidan saboda rushewar ginin ƙasan dake zagaye da gidan, yunkura wa tayi zata shiga sai ta ga Fitowar wani dattijo a yanayin shiga da fuskarshi ya nuna kamilalle ne wanda kai tsaye bata kawo ko kusa Kawu Labaran bane sai da suka haɗa idanu, Chakk ya tsaya yana ƙare mata kallo kaman yadda ita ma take ƙare mishi kallo. Sanye yake da jallabiya baƙa har da hula taɓani ka ji hadisi da chasbi riƙe a hannunshi sai wani littafi da ya nuna mata na addini ne, ya rame kam gabaɗaya ya lalace, shi karan kanshi bai gane ta ba sai da yaga kallon da take mishi da hawayen dake zuba mata don kaman an yi mata wankin inji ne, kaman bata taɓa sanin menene wahala ba a rayuwarta, muryarta na rawa tace "Ka..kawu" Tana tuna ranar da ta zo da Saleem yayi mata kora irin ta miyagun aljannu da kayan tsubbu da komai. "Af...Afee..fah??? Ke ce Afeefah? Da gaske ke c..e?" Cikin wani irin karyayyen murya yake maganan, ta ɗaga kai sai gani tayi ya iso gabanta ya zube gwiwowinshi ƙasa da sauri itama ta durkusa yadda yayi suka saki kuka a tare, nata dai bata san me take ji ba don abubuwa ne suka haɗe mata shaidan na tuno mata duk wani minti da tayi a gidan cikin azabtarwa yana tuna mata irin muggan kalaman kawu a kanta da rayuwarta yana nuna mata basu chanchanci komai na alkhairi daga gareta ba ta wani ɓangaren tana jin babu daaɗin yadda ta zo ta ga inda suke rayuwa da kuma lalacewar da kawun yayi kaman kuɗin guzuri. Shi kuwa nadama ce, nadama da kunyar kasa riƙe amana da zumuncin ɗan uwanshi yake yi wa kuka, kunya mai tsanani da ba zai iya cewa ya taɓa jin irin shi ba yake ji na ɗiyar cikinshi. "Afeefah idan na ce ki yafe min na so kaina dayawa, na san na yi miki abubuwa masu yawa na zalunce ki, na ci amanar zumunci, na cutar da rayuwarki fiye da ƙima, na wargaza natsuwarki har ya kai na kore ki da kaina daga kusa na bisa tarin jahilci da baƙar zuciyata... Ina kallo matana kowacce take abinda ta so da rayuwarki ana gara ki kaman kwallo, na dauke ki da kaina na jefawa hukuma ke don kawai ina ganin kin zame min Ƙashin kifi, an zo neman aurenki har nan na lalata komai saboda kawai wani zargi wanda babu wanda ya tabbatar, saboda son zuciya irin tamu... A ƙarshe na aurar dake ba tare da na ko yi binciken wanene za ki aura ba, mecece sana'ar shi, su waye danginshi don kawai sun cika ni da kuɗi sun kuma nemi auren kawai suke so, tun bayan aurenki da kaddara ta faɗa min bisa neman zuwa wurin ki da nayi na ci arziki na faɗa hannun 'yan shan jini a ranar na san cewa ke ba Mayya ba ce yadda muke faɗa, a ranar na tabbatar harkar shan jini da maita ya fi karfin kwakwalwarki nadama mai yawa ya rufe ni a kullum Adu'a ta shi ne yadda zan ganki kafin ƙasa ya rufe min idanu Afeefah...." Sossai yake kuka ta mayar da kanta ƙasa tana cigaba da hawaye, hatta Aisha da Abeeha hawaye suke shi kuwa Rayyan kanshi ya kawar yana jin zuciyarshi na jagulewa. "Ashe za ki zo inda muke Afeefah? Ashe za ki neme mu?" Zuwa lokacin makota duk ana maƙale ana kallon me ke wakana Larai da Asabe da ma wasu yaransu dake gida duk sun fito sai dai ita bata kai hankalinta kansu ba yayinda duk suke kuka. Hannun kawu ta riƙe tana jin yadda zuciyarta ke kakkaryewa tace "Dole na nemeku kawu dole duk inda zan shiga ku ne nawa, ko me za ku yi min ku ne dole na duk duniya ba ni da waenda suka fi ku. Tsoro nake ji... Tsoro nake ji kar ku ƙi karɓa ta.." "Ko a ya kika zo Afeefah wallahi ba zan ki karbarki ba a yanzu, na tuba na yi nadama mai tarin yawa, na roki Allah a salloli dayawa akan ya waiwayo mana dake ya sa ki tuna da mu. Don Allah, Don darajar Allah ki dubi girman shi ki yafe min Afeefah ki yafe min don Allah" Kai take gyaɗa wa ta kai hannu ta share mishi fuska "Na yafe maka kawu wlh duk na yafe muku Allah ya yafe mana gabaɗaya" Inna Asabe ta rarrafo "Afeefah don Allah ki yafe mana don Allah" Ta kallesu sai ta ga inna Larai na ja da duwawu kafa ɗaya kam babu gabaɗaya kuma ba sanda bare wheelchair zubewa tayi tana neman yafiyarta duk ta yafe musu, Rayyan da ya gaji da kukan ya taho ya ɗaga ta tsaye yana kallon cikin idanunta ya fidda hanky fari tas mai cike da kamshi ya fara ɗauke mata hawayen fuskarshi babu ɗigon walwala. "Am sorry" Ta faɗa a hankali. Iso aka yi musu sai dai duk gidan an rasa ma taburma mai haske da za'a iya shimfida musu su zauna, Rayyan take kallo ta juya ta kalli kawu ta sake kallon Rayyan. "Ko za ka tafi mota ka zauna Ya Saraki?" Ya harareta ya samu wani dutse ya zauna a kai ta mayar da kanta ƙasa ko wannan kaɗai ya isa ta yafe musu, wa zai ce Rayyan zai iya zama a irin wurin nan saboda ita? Saboda kawai tana wurin idan ba don haka ba me haɗin kifi da kaska? Rayuwar mutanen gidan sossai ya chanza mata ko da ta ji irin neman ilimin da kawu ke yi tun daga sanadiyar yan shan jini da suka kama shi Allah ya nufe shi da shiriya ta tabbatar da gidan sun rabauta don ilimi shi ne ginshikin rayuwa, yaranshi duk sun dawo kan hanya sai talauci da yayi musu matuƙar yawa don Allah ya jarabcesu da babu tun bayan tuban shi abinda za'a ci ma wahala yake sai dai basu daina neman ilimi ba kuma dayake tuban gaskiya suka yi yana iya yinshi ya ga an ci wani abu ko da sau ɗaya ne a yini, tayi kuka har sai da Rayyan ya fara yi mata faɗa ganin da gaske ranshi ya ɓaci ya sa ta daina, ta basu labarin duk abinda ya faru da ita har kawo yau "Allahu Akbar... Allahu Akbar kabiran lallai shi mahakurci mawadaci ne kuma mai haƙuri shi yake dafa dutse... Yanzu Afeefah har 'ya'yan sarki mai tarin daraja biyu ne a gidana ta sanadiyar ki? Ashe ke ce kike gina wannan tamfatsatsen gini da masallacin juma'ar da babu irinshi a wannan gari? Allah mai girma Allah mai yadda ya so" Kawu ke magana cikin hawaye da tabbatar da girman zatin ubangiji. Kallon Inna Larai tayi tace "Kawu me ya sameta?" "Maciji ne ya sare ta mun yi gargajiya har mun gaji kafan ya rube dole muka nemi taimako dai da kyar muka hada kudi aka yanke kafar sai dai babu kudin ko sanda ne bare kujeran guragu a dole take yawo a haka da ja da duwawu" Lokaci Ryan ya kalla ya mata umurnin su tafi ana jiran su wurin taron da suka gayyata, kawu da iyalan shi duk suka tafi dasu wurin taron kusan duka jama'ar garin suna ɗakin taron barin ma fankoki dake kaɗa su ya sa sai nishadi suke. Mai gari ne ya fara yin bayani da kuma godiya ga wacce ta dubi garin ta zaɓi inganta rayuwarsu ta hanyar ba su ilimi wanda ta wannan hanyar ta riga ta gama musu komai, da ya zo wurin kiran suna sai ya ce "Wannan ɗin ba kowa ba ce illa mata ga Ciroma Sameer, Ciroma mai jiran gado kuma Yariman Matasa na ƙasar Fombina Afeefa..h Afeefah kamal??" Sai yayi saurin kallon matar da ake cewa ita ce Afeefahn, duk yan garin ido suka zuba mata suna mamaki da ikon Allah, wasu kunya na rufe su a yayinda tayi murmushi ta miƙe ta haura podium ɗin ta karɓi mic "Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai ɓatar da shi, wanda kuma ya ɓatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu

Chapter 38 of 40