taje ta kunna wuta gabanta na faɗuwa ganin kaman zai faɗo daga kan gadon ta ƙarasa wurinshi da gudu tana jijjiga shi Muryarta na shaking take ƙiran sunanshi
"Ya...ya Saraki! Ya Saraki...!
Ka buɗe ido.. Ka tashi ya Saraki mafarki ne... Don Allah ka bude ido...innalillahi!"
Duk ta rikice ta ruɗe sai dai kaman bai san tana yi ba har lokacin idanunshi a rufe suke yana jan numfashi da kyar, kuka ta saki tana janyo wayanshi ta shiga neman Layin likitarshi jikinta na tsuma saboda tashin hankali, kiranta tayi Allah ya taimaka ya kusa yankewa ta ɗaga
"Dr. Yaya Saraki ne... Ban san me zan mishi ba ya ƙi tashi sai juye juye yake kaman zai mutu ki taimakeni..!"
Likitan da take sensing tashin hankali a Muryar Afeefah tausayinsu duk ya rufeta ta ce
"Ki natsu Afeefah natsu! Faɗa min me yake yi?"
Kaman za ta taya shi kokawa da numfashi ta shiga cewa
"juye juye yake yi, ya jiƙe sharkar da zufa, he's just gasping for air kaman baya iya isar da numfashi inda ya kamata jikinshi rawa yake.."
"Ki ji Afeefah Rayyan na gab da shiga cikin mummunan yanayin matsalar kwakwalwa idan baki taimakemu ba, ki taimaka ki san yadda zaki yi ki saka shi yayi kuka ya zub da hawaye in ba haka ba akwai matsala..."
Wasu tips ta bata tare da yanke wayan akan dole gobe da safe su tafi asibiti he cannot continue like that.
Jefar da wayan tayi a kan gadon ta tattare ƙarfinta gabaɗaya ta ɗago shi ta jijjigashi da karfin gaske tana ambatar sunanshi sai ya ja numfashi mai tsawo yana buɗe idanu amma sai idanun su tafi luuu kaman za su rufu idan ta sake ƙira sai su buɗu sun yi wani irin ja da sauri ta kafa gwiwowinta akan gadon ta zare hijabinta ta jefar tare da ma kanshi ta mishi kyakyawar masauki a kan kirjinta ta rungumeshi Tsam tana kuka sossai, yadda ta yi hugging nashi, yadda take shafa kanshi da duk hannayenta biyu zuwa wuyanshi yadda take kara matse shi, sautin fitan muryarta cikin kuka ya sa bai san sadda ya mayar da hannayenshi jikinta ba ya rungumeta ƙamƙam... Cikin sautin kuka take furta
"Ya Saraki ka sassautawa zuciyarka don Allah, wannan wahalar yayi maka yawa don Allah ka daure ka zub da hawaye ko kaɗan ne... Zan zama kurma daga jin sautin Muryar fitar damuwarka! Zan zama makauniya daga kallon ruwan hawayenka! Kwakwalwana zai shiga ɗimuwa har lokacin nan ya zama tamkar mafarki ko dilusion a gareni just cry ka ji? Ka yi kuka ba zan ji muryarka ba i promise...Muna mu...na son lafiyarka we will always be there for you... Ka yi kuka just let your worries our this will be our Lil secret ka ji?"
Har lokacin bata daina shafa suman kanshi ba cikin wani irin kulawa, sake ƙamƙameta yayi kaman zai ɓallata jikinshi na sake ɗaukar rawa zuciyarshi na wani irin tsitsinkewa Dukda irin yadda take ji da zafi dake ratsa ta haka ta sake hugging nashi, she hugged him until his soul melts into tears sai ji tayi yana sauke wani irin numfashi mai tafe da zafafan hawaye masu rikitarwa.
Lips ɗinta ta datse tana runtse ido a sadda sautin shi ke shiga cikin kunnuwanta a hankali yana samun masauki a cikin zuciyarta, bata daina shafa shi ba shi kuma bai daina sake kankanmeta ba ya fi mintuna talatin cikin wannan yanayi kan a hankali ya fara sassauta riƙon, gefe gefe tayi ta kwanta yayinda ya bita har lokacin kanshi na kan chest ɗinta dake beating so so fast tana shafa shi da hannunta tana jin jikinshi na sauyawa daga zufa zuwa zafi dake shiga har cikin jikinta, sai da suka kai kwance ta iya jin ruwan hawayen shi na sauka a kan silk maroon rigan baccinta Yana taɓa fatarta ta runtse ido kawai. Basu san iya adadin lokutan da suka ɗauka a hakan ba har bacci ya ɗauke shi itama baccin tayi.
Ƙarfe biyu da wani abu ya sake farkawa, shiru yayi yana shakar fitinannen kamshinta yana jin hannayenta a jikinshi, ɗaya a cikin tattausan gashin kansa ɗaya a bayan wuyanshi, a hankali ya zame ya miƙe zaune wutan ɗakin a kunne har lokacin amma ba tarrr ba mai ɗan duhun yana iya kallon fuskarta a haka, idanu ya zuba mata yana aikin kallo her caramel skin, dogin lashes ɗinta pointed nose ɗinta zuwa thin beautiful lips ɗinta he just felt lost a kallon nata moments ɗinsu na ɗazu na dawo mishi kaman yanzu, he can't believe that it happened.
It really happened! he cried in this little Girl's arms, the way she caresses him, pet him like a Lil boy ya tsaya mishi sossai a rai. Sauƙa yayi daga gadon ya ja duvet ɗin ya rufeta zuwa kirji sai ta ɗan gyara kwanciya kaman dama a takure take ya shiga toilet yana jin wannan nauyin na cikin zuciyarshi ya ragu, ruwa ya kunnawa kanshi ya jima a ciki har lokacin kuma duk motsinshi kallon kanshi yake akan chest ɗinta tana bashi utmost kulawa, wanka yayi ya fita ya zo ya nemi jallabiya ya saka ya fara nafilfili har sai da ya ji zazzabi na neman fin karfinshi ya miƙe ya zare jallabiyar ya saura daga shi sai guntun wando da karamar vest da ya bayyana duk wani kakkarfar sura mai cike da zati da Allah ya mishi gadon ya hau ya ja bargon shima ya ɗan rufa tare da juyawa ya zubawa face ɗinta idanu tana baccinta peacefully har bacci ya sake sace shi a haka.
Ita ta fara farkawa da asuba ta sauke idanunta akan kyakyawar fuskarshi, ta ɗan jima tana kallonshi kwakwalwarta na tuna mata abin da ya faru a daren, nauyi da kunyarshi suka lallaɓo suka rufeta amma ta kasa ɗauke idanu daga kallonshi he's just handsome so so handsome da bata san ya zata kwatanta shi ba, yana baccin kaman ba shi bane Saraki mai zuciya a kusa, wannan masifaffen marar fara'a da son Magana murmushi ta tsinci kanta da yi Alhamdulillah atleast ta samu riba a kanshi wani abin dole ta san ya ragu mishi hakan kaɗai ya faranta mata, sauƙa tayi daga gadon tare da ɗaukan hijabinta ta saka ta shiga toilet don yin alwala tana jin ko me ta mishi bata ragu ta kowani fanni ba saboda he's her life savior ba don shi ɗin ba da yanzu tana cikin matattu matattun ma cikin sahun masu gingimemen laifi wa ubangijinta.
Tana rufe kofan bayin ya buɗe idanu sai dai bai motsa ba don zazzabi ne sossai a jikinshi har numfashin da yake fesarwa na fitar da zafin hucin zazzabin, bayan tayi alwala ta taho gadon ta taɓa goshinshi sai taji shi rau a hankali ta shiga kiran sunanshi
"Ya Saraki..! Ya Saraki...!!"
Ya rasa wani irin effect sunan ke dashi a zuciyarshi don wani irin tsalle zuciyar tashi tayi a sadda ta ƙira sunan cikin tsiririyar muryarta
Idanu ya buɗe ya kalleta
"Sannu! Na ji jikinka zafi sossai za ka iya tashi ka yi sallah? Ko in idar in kawo maka ruwan nan?"
Idanunta kawai yake kallo hakan ya sa ta kawar da idanun yace a hankali
"Zan iya"
Daga haka ta koma baya ta tada sallah kar ya ga kaman ta cika zaƙewa, shi kuwa ya ɗan jima a haka kan ya yunkura ya miƙe zaune yana dafe kanshi, a hankali yake tafiya har ya isa bayi yayi alwala ya dawo sai ya kasa Sallar a tsaye duk kafin halinshi a zaune ya gabatar bayan ya idar ya miƙe ya koma gadon tare da lullubuwa, bayan ta idar ta miƙe ta ninke sallayar tana shirin fita wayanshi ya ɗauki ƙara sai ta koma taje ta ɗauka ganin Likitarshi yasa ta ɗaga suka gaisa take tambayarta ya ya kwana nan ta mata bayanin zazzabi ne a jikinshi sossai Dukda ya samu ya zub da hawayen.
Hamdala tayi da farko kan tace za ta turo yanzu collegue ɗinta zai zo ya saka mishi drip da wasu allurai in shaa Allahu zuwa yamma zai samu lafiya don Allah ta kula dashi ta amsa tare da godiya ta sauƙe wayan, ficewa tayi zuwa kitchen ta ga abinda suka fara a lokacin gari ma ya fara haske taje ta watsa ruwa don duk yadda ta motsa kamshinshi kaman tayi wanka da turarenshi kamshin na sakata jin kaman har lokacin yana kwance ne a jikinta rungume da ita Dukda ba don soyayya ko wani romance suka yi ba taimako ne ta mishi amma hakan ya mugun tsaya mata,bayan ta fito ta shirya cikin atampharta riga da siket da ya zauna mata chass ta ɗaura dankwali sai ta nemi gyale mai girma da kauri ta yafa ta fita parlor tana shirin shiga side dinshi aka yi mata sallama.
"Mery ya dai?"
"Wai wani likita ne ya zo duba Oga Rayyan"
"oaky ki ce ya shigo"
Tana nan tsaye har ya shigo suka gaisa kan ta mishi jagora har ciki, har lokacin yana kwance ba bacci kuma yake ba don zafin zazzabin bai barshi ba, tana daga chan gefe har likitan ya haɗa drip ya mishi allura ciki ya saka mishi canular yayi wani a canular kan ya ɗaura ruwan sai ɓata fuska take kaman ita ake ɓula wa.
"Toh madam za ki iya samun ruwa masu ɗan dumi kaɗan da towel ƙarami a shafa mishi a kan nan da Goshi zafin jikin zai ragu Dukda na mishi allurai amma hakan ma na da kyau don temperature ɗin shi is very very high"
"in shaa Allahu mun gode kwarai Dr"
"Mention not"
Daga haka ya fice, bayi ta tafi ta haɗa ruwan ta samo ƙaramin towel ta dawo bakin gadon ta zauna ganganshi ta cire gyalen ta ajiye tare da matsa ruwan ta ɗora mishi a Goshi ya buɗe ido ya kalleta saboda sanyin da ya ratsa shi yana sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi, wani iri take ji da kallon nashi amma ta dake ta cigaba da shafa mishi da kanshi ya gaji ya mayar da idanun ya rufe sai ta sauke numfashin da ta riƙe tuntuni, idan ta zo daidai kwantaccen sajenshi sai ta tsinci kanta da zame towel ta bar fatar hannunta na shafa lallausan gashin wurin a hankali.
Jin abin nata na so ya fi karfinshi ya ɗaga hannu ya ture hannunta, ta ɗan tura baki ta miƙe ta nufi bayi tana mita
'Mutum bama shi da lafiya amma hali ba zai chanza ba!' Sarai ya ji ta a maimakon ya ji haushi Sai ɗan murmushi da yayi a cikin zuciyarshi wanda ko alama bai fito fili ba, bata ma fito ba bacci ya ɗauke shi don akwai allurar bacci ciki daga nan ta ɗauki gyalenta ta yafa ta nufi cikin gidan, ɗakin su Abeeha ta shiga inda ta samu suna zaune sun yiyyi wanka Mommy da mama da suna nan tun rasuwar basu tafi ba suma suna ɗakin da alamu sun zo duba kwanansu ne.
Har ƙasa ta duƙa ta gaishe su suka amsa cikin kulawa kan ta dubi jannah ta gaisheta tare da mata sannu da jiki suka gaisa da Abeeha a karshe, wata cousin ɗinsu Aaliyah ce tace
"Na ga likita yana shiga wurin ku da safen nan Allah dai ya sa ba wani abu bane?"
Kanta ƙasa tace
"Wlh Ya Saraki ne ya kwana da zazzabi amma Alhamdulillah an saka mishi drip yanzu haka bacci yake"
Cike da jimami suke mishi Allah ya kara sauƙi ta ɗan jima anan har aka gama fito da kayan kari ta karya anan suna hira kaman dama chan ita ma she's part of the family don basu ware ta ba sam.
Sashensu ta koma ta leƙa ta samu har lokacin bacci yake ta koma parlor tana kallon time, a chan kuwa fitan ta ba jimawa sai ga su mommy sun shigo babban parlor aka dawo da gaisuwar makota dai kan shigo a yi gaisuwa da su Ƙawayen su Afeefah har ma da dangin mijin jannah ita dai Samha sai baza ido take ta ga ta inda Afeefah za ta ɓullo amma bata ganta ba.
Ko da Saleem ya shigo suka gaisa Abeeha ya tambaya Rayyan fa don ya ta kiran wayanshi ba'a picking nan ta faɗa mishi ai bashi da lafiya an ma saka mishi drip kila bai tashi ba har lokacin, bai shiga ba don ya san akwai bambancin da da yanzu ba zai yiwu ya je har ɗakin ba sai fita yayi akan yana parlorn waje.
Sai karfe sha ɗaya da rabi da Afeefah ta leƙa ta samu baya kan gadon alamar ya shiga wanka, gadon ta gyara tsaf kaman ba'a kwanta ba ta fice chan sai gata rike da tray mai dauke da dafaffen dankali sai wani curry chicken soup da ta mishi da kifi gasashe a gefe sanin yana so sai tea da ta haɗa mishi, ya gama shiryawa cikin riga da wando masu taushi don ba jeans bane wandon cotton ne mai ɗan faɗi Brown, shirt ɗin burnt orange ya karɓe shi sossai ya sake zama pale kana kallonshi zaka san yana ciwo.
A kan table na gaban couches na ɗakin ta ajiye ta kalleshi shima ita ya kalla sai suka haɗa idanu ta ɗan rausayar da nata tace
"Ina kwana Ya Saraki? Ya jikin?"
Bata zaci zai wani amsa ba sai kuma taji ya ce
"Alhamdulillah da sauƙi"
Dukda a hankali yayi magana amma ta ji ta ɗan murmusa
"ka karya sai ka sha magani"
Ya nufo inda take sai da ya ɗan wuce taji ya ce
"Thank you!"
Zama yayi ya ja abincin ya shiga ci hakan ya faranta ranta sossai ta juya ta fice, a parlor ta zauna tana kallo kusan mintuna talatin sai gashi ya fito ya fita waje.
Sai lokacin hankalinta ya kwanta ta miƙe itama ta nufi wurin su Jannah tana shiga babban parlorn da sallama suka hada idanu da Mommy...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*41*
"Sannunku"
Ta faɗa tana ɗauke kanta daga cikin idanun mommyn da ta kusa daskarewa a wurin a zaune.
Bata ƙara firgita ba sai da taji matar uncle sanusi na cewa
"Sannu Afeefah, jigilar nan ba zai haifar miki da ciwon jiki ba? Kece nan ke ce chan ya kamata kina hutawa fa"
Matar uncle Mansur tace
"Gaskiya kam ya kamata ki dinga ji da mijinki kawai su jannah duk ba ga mu nan ba, shima ba don baudadden halinshi ba ai da duk sai mu kula da ku don kema na tabbatar raunin tafiyar Mammi na nan ɗanye a zuciyarki."
Murmushi ta ɗan saki tana zama za tayi magana Sameera ta miƙe tsaye don tun dazu duk su huɗun kaman an kafa su ne idanunsu ƙurrr a kanta.
Nuna ta take hannunta na rawa
"Afee...fah?"
"Ita ce ko Ya Sameera? Ita ce ba gizo na gani jiya ba ashe!"
Samha tayi saurin faɗa kaman jira take wani ya fara magana cikinsu.
Mommy ta kasa ma magana tsabar yadda taji da ganin Afeefar ƙare mata kallo take yadda ta wani sauya tayi mugun kyau ko atamphar jikinta ka gani ka san bata cikin wahala sai hawaye suka fara zuba mata ta tuna ranar auren Saleem inda take ce mishi a lokacin Afeefah na chan tana raba wa maza kanta tana samun na cin abinci idan zai mantata gyara ya mantata.
"Kun santa ne?"
Mama tayi tambayar da mamakin irin shock da ta gani a tare da su ga mommy ta fashe da kuka.
Jannah ce da daman ta kasa sakewa dasu saboda har lokacin bakinsu take gani akan abinda suka yi wa Afeefah tace
"Sun santa Mama, mommy kin ga ta sauya ko? Kun ga yadda Allah ke ikonshi ko? Ku kun ƙi ta mu mun so ta mun karɓeta hannu bibbiyu, kun muzguna mata hakan bai hana ta muku taimako mafi girma ba a rayuwarku... Ita ce ta taimaka da ayoyi da ruwan tofi ba ji ba gani har saida ta tabbatar asirin da aka yiwa Ya Saleem ya karye, gata nan yanzu haka ana dawowa makaranta exams na karshe zasu rubuta tana kan karatu. Nasara mafi girma da daraja shine tayi aure ta auri namijin nunawa sa'a wanda ko cikin maza sai an tara dubu a samu tamkarsa ɗaya. Afeefar da kuka sani ce dai ita ce matar Ya Rayyan ta sunna a yanzu haka"
Afeefah ta mayar da kanta ƙasa hawaye na taruwa a idanunta sam bata san sun zo gangarta ba sai jin mommy tayi ta riƙe hannunta tana sake ƙara fashewa da kuka mai tsuma rai, Abeeha ma bata yi shiru ba ta kara da labarin irin yadda ta taimakesu akan Saleem.
"Don Allah ki yafe mana Afeefah, haƙiƙa ba mu da bakin neman yafiyarki saboda mun aikata miki ba daidai ba, mun kasa duba kasantuwarki mace mun kasa yarda cewa Allah ke komai a sadda ya so na bi dare na raba ki da Saleem karfi da yafi na aura mishi wacce nake ganin ta fi cancanta ashe ban sani ba ƙabari na haƙa mana... Haƙiƙa na so na ganki ba tare da aure ba nayi adu'ar Allah ya bayyana mini ke ko ta wani hali in nemi yafiyarki in kuma gyara kuskurena ashe ke kam Allah ya dubeki ya Musanya miki da alkhairinki... Don Allah ki yafe mana ki yafe mana Afeefah!"
Sossai duk suke kuka suna neman yafiyarta sai ta nemi rudewa Dukda tayi mamaki amma ta sani duniya aka ce makaranta.
"Mommy ku daina neman yafiyata wlh tun kafin na bar gidan duk na yafe muku Yaya Saleem ya wuce yadda kuke zato a wuri na. Ban riƙe ku a zuciyata ba ku daina wannan kukan don Allah".
Samha ta fi kowa bata haƙuri sai Mommy, duk ta nuna ita komai ya wuce a wurinta suka koma gefe suna ta kallonta ko motsi tayi burgesu take, basu taɓa sanin haka take ba sai a yanzu yinin da suka yi a ranar suka kara sanin wacece ita kunyar duniya duk ya rufesu na tunanin duk irin wulakancin da suka yi mata, lallai da gaske ne da aka ce mai haƙuri shi yake dafa dutse har ma ya sha romonta.
Mommy ta tabbatar Saleem bai san da wannan labarin ba, gab za su tafi ta kira shi a waya akan ya zo ciki duk jama'ar sun watse a babban parlorn sai Afeefah dake zaune tana duba abu a waya mommyn ta fito daga ɗaki ganinta yasa tace
"Yauwa ashe kina nan dama ke zan je dubawa kitchen. Yanzu Saleem zai shigo ku gaisa..."
Gabanta ne ya faɗi rabon da su hadu kusan watanni bakwai zuwa takwas kenan, ya rabu da ita cikin kuna da zafin zuciya tare da hawaye a yanzu zai haɗu da ita matsayin matar aure, matar ma ta abokinshi me zata ce mishi? Ta san akwai laifin mahaifiyarshi a rabuwarsu amma ta san dole zai ji zafin samun wannan labari, anya ma zai yi farin ciki da ganinta? Bata gama tunanin ba ta ji sallamarshi gabanta ya sake faɗuwa ta miƙe tsaye sai suka haɗa idanu a lokacin da take amsawa da iyaka lips ɗinta.
"A...Afeefah? Ke..ke ce nake gani? Afeefah ba gizo idanuna suke min ba kece tsaye a gabana?Ta yaya kika zo gidan nan? Ina kika shiga Afeefah? Ina kika shiga...?"
A ruɗe yake maganan idanunshi na cika da kwallah kaman yadda nata ya cika fal da hawayen ganinshi.
"Ya Saleem...!"
Ta faɗa a sanyaye sai ta kama hawaye.
Sake matsowa yayi kaman zai taɓa ta tayi saurin matsawa baya sossai tana girgiza mishi kai.
"Ka gafarceni Ya Saleem yanzu da baya ba ɗaya bane..."
"Afeefah na san akan mahaifiyata ne wlh yanzu duk sun yi nadamar abin da suka aikata miki, na tabbatar za kuma su nemi yafiyarki don Kullum adu'arsu shine mu ganki mu nemi yafiyarki...ko babu komai a yanzu za mu cika burinmu za mu cika alkawarinmu na mallakar juna..."
Daidai lokacin Rayyan ya sanyo kai parlorn he just stood there fuskarshi kadaran-hadaran yana kallonsu.
Hawaye take yi sossai
"Lokaci ya riga ya ƙure ya Saleem, kayi hakuri Allah bai nufa na zama rabonka ba. Ni din yanzu matar aure ce."
Jikinshi yayi wani irin sanyi wani tashin hankali da damuwa na lallaɓo wa ya rufe shi murya na shaking yake furta
"A..a..aure Afeefah? Aure kika yi? Da waye? Me..me yasa?"
Idanunta ne suka shiga cikin na Rayyan da sauri ta kawar heartbreat ɗinta na kara gudu ganin kallon da yake mata.
"Ka sa a ranka ƙaddara ce ta zo haka, amma ni matar aure ce don Allah ka ajiye zancen alaƙar da ta riga ta wuce Ya Saleem"
Daga haka tayi saurin wucewa sashensu ta barshi kanshi a matukar kulle, idan bai ce ya matuƙar kaɗuwa da wannan zance ba yayi ƙarya zuciyarshi raɗaɗi ya shiga mishi, saboda rauninshi tuni hawaye suka shiga zubo mishi haƙiƙa ya so Afeefah kaman ranshi har gobe yana ƙaunarta amma gashi ƙaddarar su ya zaɓar musu rabuwa aure tayi a sadda yana chan ya rasa hankalinshi, me yasa bata yi haƙuri ba? Meyasa bata jira ba? Me yasa yayi jinkiri? Tun da ya dawo hayyacinshi a neman ta yake ko Allah zai sa ya ganta ashe ita kam tana chan tare da mijinta tana rayuwa mai kyau don ko skin ɗinta ya bayyana hakan.
Mommy ce ta fito ganin yanayin da yake ciki ta kalli Rayyan dake tsaye har lokacin a bakin kofa hannunshi harde a kirjinshi wanda da alama Saleem ɗin bai kula da wanzuwar shi ba tayi saurin kama Saleem ɗin ta zaunar taje ta kawo mishi ruwa bai karɓa ba sai ma maganganu da ya fara
"Mommy ta ya kika ga Afeefah? Me ya kawo ta gidan nan? Mommy wai da gaske Afeefah aure tayi? Aure tayi? A yanzu haka Afeefah ta haramta mini?"
Mommy ta kalli Rayyan ta mayar da idanunta kan Saleem.
"Saleem Afeefah ta yi aure laifina ne duka, laifina ne ta subuce maka ka yafemin ciwon da nake sakawa zuciyarka ka ɗauki dangana da haƙuri. A gidan nan muka samu Afeefah tana kuma auren abokinka ne Rayyan..."
Da ƙarfin gaske ya miƙe har yana Buge ruwan hannunta ya faɗi ƙasa
"Rayyan?? Mommy all this while Rayyan na tare da Afeefah? Har ma ya aureta? Rayyan dai Rayyan Moh'd Khamis??"
Gabaɗaya wani duhu ne ya taso ya rufe mishi gani tsabar wani irin bacin rai da ya zo mishi juyawa yayi zai fita yaje ya samu Rayyan ɗin sai suka haɗa idanu nan ya nufe shi ya tsaya a gabanshi.
"Rayyan da gaske Afeefah ka aura?"
Shi karan kanshi ya san yayi mugun ƙoƙari a sadda ya buɗi baki ya furta
"Saleem Afeefah matata ce idan har ka san darajar aure da kuma martabarsa za ka kiyaye irin kalmanka a kan matata... Ƙaddara ta riga ta raba ku ta bani ita a lokacin da ban yi zato ko tsammani ba don haka don't Look at me with those eyes dake nuna kaman I betrayed you or something like that, you should questioned yourself nd your family not me..."
Yana kai nan ya wuce don har ga Allah bai san dalilin da yasa yake ji kaman zai kama da wuta ba, mommy ya kalla har kaman zai wuce ya tsayar da idanunshi kanta ba zai iya yi mata magana kai tsaye ba ba kuma don komai ba sai don uwa ce ya juyo ya kalli Saleem dake kallonshi rai a tsananin ɓace yace in a respectful manner.
"Rasuwa aka yi mana ko ba rasuwa ba muna da darajar da ba za'a tako har nan a ci mana mutunci ba Saleem, idan ba zaka taya mu baƙin ciki da jajen rasa wani sashe na bangonmu ba za ka iya zama da kai da familyn ka a gida. Mun gode"
Daga haka ya nufi sashensu ya bar su nan tsaye calmly kaman ranshi ba suya yake ba.
Wani irin duka Saleem ya kaiwa bangon wurin yana yin baya tare da zuba yatsun shi cikin gashin kanshi kaman zai fashe haka yake ji, su Samha ne duk suka fito a tare da Abeeha jin salatin mommy.
Ganin yanayin da suke ciki suka shiga tambayar me ya faru? Menene?
Mommy tana zubar da hawaye tace
"Na sake wani kuskuren, da na san hakan zai kasance Saleem da ban nemi ku gaisa da Afeefah ba! Na zaci zaka yi farin cikin ganinta idan ka ji kuma tana da aure zaka taya ta murna da Adu'a
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 40