Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a gareta da ma shi baki ɗaya. Ɗan uban sun Men lace ne fari kal mai shegen tsada ƴar ciki da babban riga ya wani zauna mishi sak kaman don shi aka halicci yadin, hula da takalminshi bakake ne haka agogo tsadadde dake ɗaure tsintsiyar hannunshi zuwa azurfa mai baƙin dutse da ke ƴar yatsar shi, fasalta irin fita a angon da yayi ma ɓata lokaci ne sai kamshi kam kaman an yi barin turare, fuskar Mammi ya zubawa ido kawai don bai taɓa ganinta cikin nishadin da ya ganta a ranar ba sai ya ji wani abu mai sanyi na sauƙa cikin zuciyarshi, matsowa tayi ta kama hannunshi tana murmushi tace "Za ka tafi a saurayi ka dawo matsayin magidanci Saraki, ba zan ce komai ba illah Allah ubangiji ya tsare muku hanya daga zuwanku har dawowanku" Yayi murmushi ya juya zai fita tace "Saraki...!" Ya waigo ta ɗauko turarenta ta sake fesa mishi ya fita ranshi fess Dukda wani abu da yake ta ji na tsungulinshi akan auren. Ga dumbin mamakin shi yana fita ya tarar da motoci sun fi sha biyar dauke da tarin ma'aikatan asibiti da ma 'yan uwanshi sojoji, a hankali ya juya ya kalli Sulaiman da ke mishi murmushi sai yaji wani abu na mishi yawo a jiki, bai taba zaton za'a mishi irin wannan karan ba duba da gaisuwa ce kawai ke hada shi da kowa, wani iri yake ji a sadda ya shiga gaban motan Sulaiman suka fara barin unguwar babu saleem, ya nemi saleem a waya har ya gaji baya samunshi ko da ya dawo gidan ya je mai gadi ya tambaya ya tabbatar mishi sun yi tafiya da madam, ya tambayi su mommy yace basa nan suma. Ko jiya sai da ya koma amma bai same shi ba akan basu dawo ba bai ji daaɗi ba sam da hakan ta kasance. Bai gama shan mamaki ba sai da ya kalli tarin dangin Mammi, iyalai da jikokin uncle ɗinta motoci kusan nawa har da abokanan arziki don a matsayin auren jikan Uncle ɗin za'a yi, kan su tafi Mammi ta roƙi uncle Musa akan duk runtsi a dawo da sadakin Afeefah wanda Saraki zai bayar in ya so ko wani abu ne a bashi daban amma sadaki na Afeefah ne. Mutanen Dutsen-wai suna zaune kawai suka fara ganin lafiyayyu kuma tsararrun motoci suna shigowa one after the other, babban masallacin garin da bashi da wani girma sai haraba suka yi wa tsinke tuni dama Uncle Mansur ya aiko da masu canopies an kafa dayawa a harabar don masallacin ba zai ɗauki mutanen ba, an shimfida carpets-carpets anan suka yi masauki, Kawu an nemo na ƙasan akwati don maƙon shi ma bai barshi yayi sabon ɗinki cikin dubu hamsin din chan ba bai tashi jin kunya ba sai da ya ga mutanen alfarmar da suka taru a wurin, kowa mamaki yake yara sai leke suke wasu matan ma na maƙale saman katangu ana kallon ikon Allah, kowa Allah Allah yake a ce wannan shine mijin Afeefah Annoba su kare mishi kallo... Fara haramar ɗaurin aure ake, a hankali Rayyan ya kalli Sulaiman "Nawa ake bayarwa?" Sulaiman ya ɗan juya hannu alamar mene kenan? "Sadakin?" "Duk abinda kake dashi hawa hawa ne amma last da na duba a masallaci ƙarancin sadaki yana dubu ɗari da tamanin da uku ne" A lokacin aka fara ambatan sunayensu a hankali ya karkata ya zaro bandir ɗin dubu-dubu guda biyar ya miƙawa Uncle Sanusi aka miƙawa liman an ɗaura auren Afeefah Kamal da Rayyan Moh'd Khamis akan sadaki naira Dubu ɗari biyar lakadan ba ajalan ba, wani irin yanayi ne yake ratsa shi da ya kasa fahimta, idanunshi da suka sauya ya runtse yana ji ana ta rabon goro da dabino da sweets. Sai hannu ake bashi ana mishi murna da kyar yake iya kawo murmushi fuskarshi don yanayin da yake ji baya misaltuwa mishi, kawu sai kallonshi yake baki galala yana ayyana lallai wannan zai iya zama maye tunda gashinan irin mazan da yake kallone idan yara suna kallon India, a fina-finan ma wannan ko ya aka yi kuɗinshi daban ne, limami ne yake rike da kuɗin sadakin kawu yaje ya fara kokarin karɓa sai uncle Musa yayi interrupting ɗinsu "Kun dai san sadaki hakkin mallakar matar ce ko?" Limamin ya gyaɗa kai "Toh zan tafi da wannan tunda ita yarinyar na gabana zan bata" Yana kai nan ya nuna Mansur shi kuwa ya karɓi kudin gabaɗaya wani irin kullutun bakin ciki ne ya tasowa kawun har wuya, uncle Musa ya murmusa ya fiddo dubu hamsin ya ba kawun Dukda haka bai huce ba sai kumburi yake, anan aka yi reception 'yan kauyen sun ga abinci da kaji iya gani, yana ta mamakin ya aka yi Mammi ta shirya waennan abubuwan with her condition, duk kauyen babu gidan da ba'a ci shinkafa da kajin auren Afeefah ba don enough aka yi shi. Karfe goma sha ɗaya suka fara barin garin, kawu ya tafi zai shiga mota Uncle Musa ya janyo shi "Malam Labaran na ga kana kokarin shiga mota?" "Eh wai dama in je ne in kalli inda 'yar tawa za ta zauna" "Ah ai ba'a yi haka ba, ba yanzu ba zaka bari sai ta kwana biyu da kaina zan zo in kai ka yanzu ka ga mutanen da ka tara dole ka tsaya ka ga sun tafi cikin salama" Yana maganan ne yana tuna zancen Mammi da tace duk rintsi kar su dawo da kowa, tana so ta dasa musu wani bakin ciki ne a rai gashi dai wacce suka kora sun haɗa ta da ƙaddarar ta rabonta shine ya kawo ta har cikin Kaduna, sannan gashi sun gani kuma sun shaida a yanzu ta shallake wa tunanin su kuma babu yadda za su yi babu abin da suka iya. Kwalelen biri da hantar kura. Shi dai bai gamsu ba amma haka uncle Mansur yayi ta mishi zaƙin baki har motocin suka watse illa Sulaiman da Rayyan wanda yake jingine jikin mota ya harde hannayenshi a kirji yana mamakin ikon Allah wai yau shi ne da aure. Ko sha'awar kallon kawun baya yi don ko da kawun ya zo yana washe mishi baki tattare girarshi yayi ya haɗe fuskarshi ta koma ainihin shi mai tarin kwarjini dole kawun ya kyale shi. Su ne karshen barin garin sai masu canopies, sai cece kuce ake to Annobar ya saki Afeefah ne ko an mata maganin mayun ne? Kap kauyen babu yarinyar da aka ɗaura mata aure kwatankwacin na Afeefah, sadakinta kaɗai yayi sadakin mata ashirin a kauyen kaf... Inna Larai na zaune da suntumemen kafa da kullum kara hauhawa yake tana jin komai tana hawayen bakin ciki, inna Asabe ma sai uhmm uhmm take tayi abin duniya ya taru ya masu yawa barin ma da aka aiko kulolin abinci wai na gidan kawun, ko da Afeefah ke mata abincin sayarwa wannan yayi jarinsu sau goma don daga ganin shinkafar ka san ba na yara bane ga kaji baja baja. Suna gani Afeefah ta haye? Garin yaya duk basu sani ba. Ni kam na ce Allah take dashi. Ko da suka iso Kaduna shi kadai ya nufi babban parlorn akwai mutane ciki sossai don yan uwa Mammi duk suna nan ga su Umma duk sun zo yara ana ta ciye ciye ana wasa, kai tsaye karamin parlorn Mammi ya leƙa sai ya ga wata cousin ɗinta tace mishi "Tana sashen ka Rayyan" Bai amsa ba don duk ana ta ango ango kanshi kasa da kyar yake dan murmusawa don kanshi sara mishi yake. A parlorn shi kuwa ya samu Mammin da wasu, tsayuwa yayi kawai yana kallonta ta ci wanka cikin leshi blue doguwar riga ta ɗora gyalen da ya shiga da leshin a kanta da aka yi wa dauri mai kyau, daga wuyanta kunnenta zuwa hannayenta da yan yatsunta gwalagwalai ne da suka kawata adonta ta mishi kyau ainun har bai san ya fadada murmushin shi ba ya shigo ciki. Ta tako a hankali ta kama hannunshi sai hawaye suka shiga zubo mata "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana, Allah na gode kwarai da ka ba ni lafiyar kasancewa da ɗana a rana mafi muhimmanci cikin rayuwarshi, Allah ka dube su ka basu zaman lafiya Allah ka sanya musu tausayi, jin kai, bege da kaunar junansu ka bashi ikon bata kariya da sauƙe duk wani hakki nashi na aure... Rayyan..." Sai ta kasa magana sai hawaye, kaman zai yi kukan shima yana jin adu'o'in nata har a cikin zuciyarshi ya sa hannu yana dauke mata hawaye, jan shi tayi suka zauna ta zaro wayanta ta kira Abeeha "Ku zo da ita" Daga haka ta kashe. A gefen Mammin ya zauna yana gyara mata gyalenta nan masu hoto suka shiga aikinsu, sossai suke yin kyau don shine yake ba ta kulawa bayan ya gama gyara mata gyalen ya sake share mata fuska kan ya kalleta yana murmushi duk ana ɗaukar su, suka kalli cameran suka murmusa a tare ba karamin kyau suka yi ba, zai yi magana suka yi sallama suka shigo ganin murmushin Mammi yayi yawa ya sa ya kai idanunshi inda take kallo. Afeefah ce ke tahowa a hankali kaman wacce ke tafiya a kan ƙaya, tayi masifar kyau cikin wani exlusive luxery lace da aka yi wa ɗinki na amare, ko ina na jikinta a rufe ne ruf banda hannu da fuskarta makeup da aka mata ya matuƙar amsarta ko don shine karo na farko a rayuwarta ne bata sani ba, amma kam tayi kyau Tabarakallah. Mammi ta miƙe ta tarbota "Masha Allah, Tabarakallah ɗiyata you made a beautiful bride" Shi kam kallon seconds biyu yayi mata ya janye idanun har suka zo suka zauna Mammi tana tsakiya Afeefah na gefenta na hagu yana zaune a gefenta na dama, idanunshi ya ɗan tsayar akan yatsun Afeefar da suka yi kyau ainun har yanzu mamaki yake, Mammi ce ta kama hannun shi ta kamo na Afeefah ta haɗe a tare suka ɗago sai zuruf idanunsu suka faɗa cikin na juna, idanunta da suka sake haske suka yi mai saboda kwallin da aka saka mata ya tsayar da kwayar nashi a kai, ba zata iya jurar kallon ba sai ta duƙar da kanta daidai Mammi ta ɗora nata hannun a kan nasu camera man yayi musu magana suka kalleshi aka shiga ɗaukar hotuna. Ko da za'a musu su biyu Mammi bata tafi ba don ta san in ta bar wurin shima sai ya bari, ta miƙe ta mishi umarnin komawa mazauninta ya koma ɗin amma har lokacin da space tsakanin shi da Afeefah mai hoton ya kalleta yace "Amarya ki ɗan matsa kadan sai ki sa kan ki akan kafadarshi" Irin bugawar da zuciyarta ke yi tunani take kila saura kiris ya fashe ta mutu, kamshinshi presence dinshi a kusa kusa da ita haka sai ya nemi ruda ta, yana so ya tashi don ya gaji hakan ya sa ya ɗan matsa kaɗan Jannah da duk tsoronta ta zo ta kama hannun su ta haɗe sai suka kalli juna don duk sadda jikinsu ya haɗu su suka san abinda suke ji, kallon ya ba da wani ma'ana na daban nan aka shiga daukar hotuna. Sossai yake a takure na tsaye aka ce shine last Mammi dai bata yi magana ba amma idanunta ne ya hana shi barin wurin wallahi. Bayanta ya koma, ya matso sossai har tana jin kirjinshi na taɓa bayan nata babu zato ta ji hannunayenshi duk biyu ya zagaye cikinta, a ɗan razane ta ɗora nata biyu a kan nashi "Kin natsu ko sai na karyaki biyu? Baki san mutum ya gaji bane??" Da ɗan faɗa yayi maganan a kausashe amma wanda suke tare za su dauka wani abin arzikin yake rada mata aka daddauka ya zame ya bar wurin su ma suka fice. An yi yini an ci an sha an yi hidima har la'asar kan aka sake wanka aka fito harabar gidan walima, amarya na sanye da wani tsadaddiyar Abaya da yanayinshi kaɗai ya bayyana tsadar shi canopies da kujeru aka shirya sossai aka yi walima aka ci aka sha kan mutane suka fara watsewa don bayan isha aunties ɗin su Jannah za su kaita part dinshi dake cikin gidan, Mammi bata mishi maganan wani gida ba saboda ta sani ne ba zai taɓa tafiya ya kyaleta a gidan ba, kuma parts dake gidan kenan don a tsare aka yi ginin Allah ma ya sa dakuna biyu ne a nashi part ɗin da kitchen da store sai parlor da dining section kaman flat ne mai zaman kanshi. Aiko kan bayan isha mutane kadan ne a gidan masu aiki sai aikin tattare gidan suke, Afeefah tayi sallah aka shirya ta again cikin atampha aka ɗora mata lafaya aka miƙa ta wurin Mammi, sossai ta yi mata nasiha tana hawaye itama kuka take don bata da bakin godiya ga Mammi, ta yi mata abubuwan da godiya sun yi kadan ta cika mata burinta na ganin ta auru, ta rungumeta ta zame mata uwa da uba ta bata duk wani gata da take tunanin ta rasa to da me zata saka mata in ba da zama lafiya da kuma zuciya ɗaya jal da ɗan ta mafi soyuwa a gareta ba? Sossai take kuka tana tuna mamanta da Aunty zee ina ma Aunty zee na nan ta ga wai Afeefah ce a ɗakin miji? A haka aka kaita ɗakinta da Adu'a a Bakinta. Mammi waya ta ɗaga ta kira shi, ba'a yi mintuna biyu ba ya shigo sanye da kananun kaya ash har da hoodie don zazzabi yake ji tsabar hayaniyar da yake ji ya mishi yawa ya saukar mishi da ciwon kai sossai. "RAYYAN...." 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh ADABI WRITERS ASSOCIATION *FREE BOOK* *33* "Rayyan a yau Allah ya nufa ka sake samun wani nauyi a kanka bayan nawa da na ƙannenka, na san ba wai ka ganta bane ka ji kana so har aka yi muku aure Allah SWT ka ba zaɓi shi kuma ya zaɓa maka abinda ya fi dacewa da kai da kuma rayuwarka, idan har ka ci amanar ta ko ka ha'inceta ba ita ka yi wa ba Allahn da ya baka shi ka yi wa, kar ka kalleta domin ni, kar ka so ta domin ni, kar ka yi mata wani abu na alfarma domin ni duk abin da zaka yi mata ka yi saboda Allah, idan ka so ta ka so ta saboda Allah don Allah ba don ni ba ka ba marar ɗa kunya. Ka zame mata gatan da ta rasa, ka zama uwa, uba kuma jigo a rayuwarta, ka zama majingina a gareta ka tallafi rayuwarta daga cikin duhuwa zuwa haske madawwami" A hankali ya ɗan ɗora kanshi a gefen kafaɗarta sai ta ji hucin zafin jikinshi na sauƙa Mata, hannunta ya kama "Mammi in shaa Allahu zan yi amfani da duk abin da kika ce" Daga haka bai sake magana ba, ta san a takure yake ta kuma san akwai abinda ke cinshi a rai a yanzu haka wanda bata tantama shi ya haddasa mishi zazzabi kuma muddin ya cigaba a haka ba zai yi bacci ba amma sam ba zata tambaya ba, ba za ta matsa mishi ba. "Ka tashi ka sha magani Saraki" Ta faɗa, da kyar ya buɗe lumsassun idanunshi da suka rine ainun ya miƙe zaune, karbar pills ɗin yayi ya sha wanda ta haɗa da panadol a hankali ya kalli time karfe tara ne da wani abin, Miƙewa yayi yana mayar da hannayenshi cikin aljihun hoodien jikinshi cike da dauriya yace "Sai da safe" "Allah ya baka lafiya" Ya amsa da Amin kan ta mishi sai da safe ya fice da kallo ta bishi ta san sai a hankali zai saba da wannan sabuwar rayuwar kuma, ta san sai Afeefah tayi haƙuri ta kara juriya kafin ta samu yadda take so da shi matsalar kawai ya kasance ta shiga ranshi murmushi ta ɗan saki kan ta sha nata maganin itama ta shiga don kwanciya saboda kowa ya tafi baƙi kam duk babu kowa. Wani iri yake ji a haka ya kutsa kanshi cikin parlorn bakinshi ɗauke da sallamar da iya shi kaɗai ya san yayi kayanshi, taku biyar yayi ya samu kujera ya zauna yana dafe kanshi da kaman zai rabe gida biyu, numfashi ne yake mishi wahalar fita kuma ya san yanayinshi ne da tunanin da ya saka a ranshi, wani irin zafi yake ji kaman ana ɗora mishi wuta a kan zuciyarshi ina ma da zai iya da kuka zai yi da ihu zai yi ta yi sai ya samu salamar abin da yake ji a ranshi, zamewa yayi ƙasa kan carpet ya ɗora kanshi a kujeran yana rike zuciyarshi ya jima sossai cikin wannan yanayi sai da ya ɗan samu relief ya miƙe ya nufi ɗakinshi kai tsaye, ruwa ya sha har gora uku kan ya shiga zame kayan jikinshi daga wurin yana nufan bayi, ruwan sanyi ya sakarwa kanshi yana yamutsa gashin kan nashi a lokaci ɗaya yana dan buga glass ɗin wurin wankan da hannunshi. Sai da yaji zai iya faɗuwa idan bai bar wurin ba ya fito ɗaure da towel ya hau gadon ya kwanta ko ruwan jikinshi bai tsaya tsantsanewa ba ya ja bargon ya rufe har kanshi ba wai don zai yi baccin ba don ko ya rufe ido abin da ya tsana yake kallo. Ita kam Afeefah dama ta san ba zuwa zai yi ba, bayan kowa ya tafi ta miƙe tana kallon ɗakin har lokacin zuciyarta ke maimaita mata wai ita ce fa matar aure, yanzu ita ta tashi daga buduruwa matar auren ma wai matar Rayyan, Allah buwayi gagara misali Allah mai yadda ya so a lokacin da ya so, a hankali take bin ɗakin da kallo ya ji kaya iya kaya yayi kyau fiye da misali gashi wadatacce don za ta iya komai free ciki yana da girma, akwatunan da aka jera mata ta bi da kallo guda goma sha biyu wai akwatunan aurenta ne, ita dake da kayan da basu wuci biyar ba ita dake fama da allura da zare a kullum tana facin kaya ita dai Afeefah Annoba kuma Mayya, sai hawaye suka fara sintiri a idanunta tana jin karin imani tana jin wani irin yarda da ubangijinta. A haka ta shiga bayin shima ta ƙare mishi kallo komai na 'yan gayu, bata yi wanka ba don sai da tayi wanka ta saka kaya aka kawo ta karamin akwatin da Abeeha tace mata kayan bacci ne ciki ta buɗe ta duba silk riga da wando cream Color yana da adon Black lace daga kirji da kuma ƙasan kafafun wandon ta saka, kamshinta da kamshin ɗakin har ya so yayi mata yawa ga sanyin Acn dake busawa kashe wutan tayi ta hau gado ta kwanta tana sake jin salama a ranta sam bata wani sa damuwar rashin ganin Sarakin ba don ta riga ta sakawa kanta haƙuri da juriya har Allah ya kawo karshen komai Dukda bata san yaushe ba bata san ko karshen zai zo ba amma she have her trust in Allah zai mata komai ba sai ta damu kanta ba Adu'a ne babba kuma zata cigaba. Washegari da safe bayan tayi sallah ta ɗan koma bacci, ƙarfe tara ta farka ta sauƙa daga gadon da kaman kar ta tashi tsabar daadinshi da take ji ta wuce bayi ta yi wanka ta fito ta fara neman kaya cikin sababbin dinkunan da telan Jannah ya chanchada mata, wani atampha doguwar riga A shape ta fitar ta shirya ciki tayi kyau sossai ta feshe jikinta da turarukanta sababbin waenda kamshin suka yi mata ta kafa ɗauri, bata sa kwalli ba sai ta saka lipstick kawai accesories da tayi anfani na silver sai suka ƙara haskata tayi kyau ainun gidan ba baƙonta bane amma sai ta fara tunanin ta saka gyale ne ko kar ta saka? Tsoro take kar ta fita su haɗu don yanzu ba kaman da bane da ba lallai ma su hadu ba in ba wurin Mammi ba, a hankali dai ta sa hannu ta buɗe kofan ɗakin ta sanyo kai cikin parlorn, ko taku biyu bata yi ba idanunta suka sauƙa kanshi a farko ta tsorata sai kuma ta fahimci kaman bashi da lafiya ne don ga matar da take matsayin likitarshi zaune a kujeran dake fuskantar shi, yayi relaxing sanye da wasu blue pjamas riga da wando complete, kafafunshi babu takalmi suna lume cikin tattausan carpet ɗin dake shimfide parlorn, fuskarshi yayi ja sossai haka gashin kanshi a hautsine. Wani iri taji a ranta sai taji tausayin shi na bin jikinta kaman ruwa, ta riga ta san dalilin da ka iya kawo mishi ciwon a hankali ta shigo cikin parlorn Likitar na kallonta ta saki murmushi itama ta mayar mata a hankali ta ɗan duƙa ta gaisheta ta amsa da kulawa tana tambayarta Ya Rayyan da jiki? Ita dai ta amsa da da sauƙi amma bata ma san bashi da lafiyan ba sai yanzu. A hankali ta kalleshi idanunshi na a lumshe har lokacin, matar ta miƙe "Allah ya baka lafiya zan zo gobe da safe, please make sure ka ci abinci ka sha waennan pills ɗin" Ta karashe tana ajiye mishi wasu pink pills a roba. Sai a lokacin ya ɗan buɗe ido "Thank you" Tayi murmushi ta yiwa Afeefah sallama ta fice. Sai aka bar su su biyu a parlorn, yatsina fuska yake don kamshinta har kanshi yake ji ba tun yanzu ya fara ji ba tun ranar da suka same shi a dining da Abeeha ya iya bambance nata kamshin da na Abeeha, yanzu ma gashi ta zo ta tsaya mishi sai hawa kanshi yake tsaki ya ɗan ja ya buɗe ido sai karap suka hada idanu don kallonshi dama take tana tunanin ta inda zata fara gaishe shi ganin ya kalleta sai tayi saurin cewa "Ina..kwana!" Ya yunkura ya miƙe zaune da kyau, bata yi zaton zai amsa ba sai jin deep and calm voice ɗin shi da bai yi matcing da situation da yake ciki ba ya ce "Good Morning!" Daga haka ya miƙe ya wuce ta ya shige ɗakinshi, ta sauke numfashin tsoro tana nufan kofa saboda knocking da ake, masu aiki ne rike da baskets na abinci kai tsaye suka jere mata su a dining suna gaisawa don sun saba da juna dama, plates, cups da spoons taje ta ɗauko ta zo ta ƙarasa haɗa dining ɗin amma bata sani ba ta kirashi ne ko ta kyale shi, ta san ba zai so shisshigi ba in ta dameshi ya iya karyata don ya sha ambata kalan ya zo ya faru ta shiga uku, abincinta ta zuba ta ci har ta gama karyawa bai fito ba don haka tayi sashen Mammi don ta duba ta. A zaune ta sameta ta gama karyawa tana shan magani tana ganinta fuskarta ya washe da fara'a "Ɗiyata ni da nace yau za ki huta sossai sai ga ki da sassafe? Sannu da zuwa" Yadda take mata sai ya saka kunya kamata kaman wacce ta fito daga wani unguwar, a ƙasa ta duƙa ta gaisheta tana mata ya jiki. "Alhamdulillah dawo nan gefena Afeefah, ina shi Sarakin?" Wani kunyar ne ya sake lullubeta ta kasa magana Mammi tayi dariya kawai ta janyo wayanta ta kirashi "Jiya ya tafi anan ban gamsu da yanayinshi ba, kun gaisa da safen nan?" Kai ta gyaɗa "Eh na fito na same su da likitan shi suna magana" "kin ga ko, sai in rasa Meyasa yake ajiye damuwar da baya bayyanawa yanzu baya so in sani ne ya ƙi zuwa nan tun sassafe na kira ban same shi ba je ki ce ya zo" Gabanta ne ya faɗi rassss, ta ya zata fara kiranshi? A hankali ta miƙe ta fice zuciyarta na racing har ta shiga parlorn inda Allah ya taimaketa ma ta samu yana parlor a zaune kan dining yana karyawa wayanshi na a speaker alamu waya yake, a gefenshi ta ja ta tsaya sai ta ji Muryar dake tashi kaman ta san Muryar kuka me Muryar take har tana shidewa a hankali take cewa "Ya Rayyan bakin cikin Ya Saleem zai kashe mana Mommy, duk abubuwan da ya dinga yi a baya mai sauƙi ne yanzu ya kore mu ya saka surakanshi a gidan, bai damu da mun

Chapter 20 of 40