gaba har gidan, kawu suka fara nema ko da ya fito da kallon tsana ya shiga bin ta.
"Yau kuma magana kika janyo min ko? Kayan uban wa kika sata ko uban wa kika kashe??"
Dattijo ɗaya daga ciki yace
"A'a malam labaran ya kamata ka fara tambayar raunin jikinta ne amma damuwarka wani abu daban? Ka san yaran zamani da kansu a koyaushe baya gayamusu daidai akwai wani yaro da ya sayi abincin 'yar wajenka yana cikin ci sai Allah ya turo da ajalinshi a take ya tafi shine suka yi yunkurin kasheta a cewar su ita ce ta cinye kur..."
Tuni ya katse su
"Ai da kun barsu don ni baku burge ni ba sam, da kun barsu don ko rantsuwa nayi ba zan yi kaffara ba ita ce nan ta kashe shi, sai ki shiga ai ki jira zuwan iyayenshi tunda ba kowani mahaukaci bane zaki mishi asarar rai ya barki ki sha ba"
"Ashshaa amma...."
"Babu ruwanku! Tunda kun kawo ta zaku iya tafiya" ya cigaba da mita kaman zai ari baki yarinya ba jari zata kawo mishi ba, ba auruwa za tayi ba babu wani amfanin da take mishi sai cin abincinshi amma kullum bacin ranta ya fi na kowa a ranshi.
Dattijan suka juya suka tafi ita kam kanta ƙasa zuciyarta na wani irin karta, hawaye kuwa sun ki kafewa a idanunta kafafunta da suka matuƙar yi mata nauyi take kokarin ɗaga wa ta shiga cikin gidan taji an fusgo ta har tana taga taga zata faɗi wuyan hijabin jikinta aka shaƙo
"Ina kudina da kayana?"
Kakari take don ko numfashi ta kasa shaƙa, idanunta da suke manya suka sake fitowa ainun sun rine sun chanza gabaɗaya.
Inna larai ganin zata yi kisa ya sa ta Hankaɗata bata damu da kokawar saisaita numfashin da take tayi ba ta daka mata tsawa
"nace ina kuɗina?"
"In...nn..a B..ban san ya ak...a yi ya fice daga ji..jikina B.."
Hayewa ruwan cikinta tayi ta shiga ɗirkarta kaman an aiko mata ita
"kaman kuwa yadda ya fice baki sani ba haka sai na rabaki da numfashinki baki farga ba, wlh dukan kuɗina yau sai na yi miki shi"
Ko karfin kare kanta bata dashi sai da dukan yayi yawa ne kawu Labaran da ke kishingiɗe yana sakace haƙorinshi ya fito ya ɗaga inna larai
"ke kar ki yi min kisa a gida"
Yana kai nan ya juya ya bar wurin ta cigaba da sababi da zage zage karshe ta tafi ta barta nan yashe.
Yaran gidan bayan sun gama kwasar dariya kowa ya kama gabansa
Inna Asabe ma na girki tana zaginta da tsine mata don yau ta yi mata asarar tallar yamma tunda yanzu ko ta fita ba su da tabbacin akwai mai sayan abin hannunta irin wannan suncewar zani a kasuwa da tayi musu, ta fi mintuna goma a kwance a wurin kan da rarrafe ta shiga akurkinta ta faɗi bisa taburma tana kuka kaman ranta zai fita.
Ko mintuna biyu bata yi da shiga ɗakin ba tana yashe a inda take ta soma jin hayaniya tamkar ana yaƙi, idanunta sun kumbure ko iya buɗewa da kyau bata yi, bata san ya aka yi ba sai ji tayi an janyota tamkar tsumma an fitar da ita, sama sama take jin mutane na ta hayaniya tana hangar sanduna da makamai na tashi sama ana ikirarin kasheta kaman yadda ta kashe musu ɗa matashi, bata san ashe rigimar har su kawu ya shafa ba don sun rantse in ba'a fita da ita ba gidan gabaɗaya za su ƙona, tashin hankalin da bata taɓa shiga ba ta shiga a ranar, bata san ya aka yi 'yan sanda suka iso wurin ba don ana ta janta tamkar kaya ko takarda Muryar kawu na ihun kar su ƙona masa dukiya ita suke so don haka ga ta nan su kashe ta. Fusgar ta aka yi aka wulla ta motar 'yan sanda suka ja suka yi ofishin su da ita...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*003*
Bayan tsawon lokacin da ba za ta iya cewa gashi ba ta ji sauƙar ruwan sanyi a kanta duk da ta farka sai dai bata da kuzarin ɗaga ko da yatsar hannunta ne.
" In ba kema da ja wa kai ba ina ke ina cin maita don janyowa mutane bala'i ki mutu a ce ai ba ma aikinmu ne yadda ya kamata. tashi my friend"
Ya ƙarasa yana kai mata kafa.
Laluɓe take har ta samu ta miƙe zaune gajimare ya rufe mata ido bata iya ganin komai. Maƙogoronta da ke bushe ko miyau ba ta iya haɗiyewa sai kartar ta yake da kyar ta buɗe baki ta ce
"R..ruwa..a don Allah"
Ruwan ya tura mata ta ɗauka ta afa a baki har kwarewa take sai da ta sha sossai cikinta ya murɗa don dama babu komai ciki ai sai amai tana jin ɗan sandan na zaginta amma ba za ta iya tsayarwa ba ya riga da ya zo, a lokacin idanunta sun washe tana gamawa ya tasa keyarta ta kwashe ta share wurin cikin layi.
A lungun cell ɗin ta raɓe tana ta aikin riƙe ciki saboda yunwa, ɗaya dan sandar ya taso yana ƙare mata kallo
"Ya dai?"
"Yunwa nake ji"
Murmushi yayi yana gyaɗa kai yana sake ƙarewa halittarta kallo Dukda rama ya yi mata yawa ainun albarkatun jikinta na daidai shekarunta ba su ɓuya ba sam.
"Zan sayo miki abinci amma kin san gomnati ta hana aikin banza ko? Nima za ki rama min"
Sam bata wani fahimta don yunwa ba ta da hankali samm kai kawai ta gyaɗa ya fice chan sai gashi da filate ya miƙa mata ta fusga ta shiga ci hannu baka hannu ƙwarya sai da ta fara koshi tukuna ma ta fahimci ashe gari ya waye kenan a cell ta kwana gashi har ana batun ƙiran sallar azahar tsabar rashin gata babu wanda ya neme ta, ta tabbatar ko shekara zata yi nan kawu ba zuwa zai yi ba bare ya cire kuɗin shi yayi belinta don sun ce sai an ba su kuɗin mai za su sake ta...
Bayan ta gama ta roƙi za tayi sallah basu hanata ba ta rama duk waenda aka bi ta. A nan ta cigaba da zama ita daya har dab Magrib wani matashin ɗan sanda ne ya shigo yana dubanta
"Ya Sunanki?"
"Afeefah"
"ba ki da kowa ne da zai zo yayi belinki?"
Ta girgiza kai
"Ni marainiya ce kawu na kuma na san ba zai taɓa zuwa ba ko shekara zan yi"
'dan shiru yayi
"Afeefah za ki iya komawa gida da kan ki?"
Ta gyaɗa kai
"tashi ki tafi to zan biya kuɗin belin naki, bana so dare ya sake samunki a nan muna da gurɓatattun 'yan sanda bare har kin bari kin ci abin hannun kopur DanJuma sai ya dawo, kuma ba ni da ƙarfi ko ikon kare ki"
Hawaye ne suka cika kumburarrun idanunta ashe akwai masu zuciyar imani da tausayi a cikin 'yan sanda? Godiya tayi ta mishi har da kuka a lokacin da zata fita ta ce
"Menene sunanka?"
"Sa'adu. Sa'adu Rabi'u"
"Allah ya dube ka ya shiga cikin lamuranka ya dafa maka"
Amsawa yayi ta fice da sauri lunguna tayi ta bi a tsorace kar ma ta haɗu da kopur Danjuma har ta isa gida.
"Uban wa yayi belinki?"
Kawu dake kofar gida ya daka mata tsawa
"Su...su suka sake ni"
Takalman shi ya wuwuro ya jefa mata
"shegiya natacciya dama shiyasa ake cewa mutum maye mana in ya cika naci, kin rantse sai kin kasheni ko? To kafin nan sai na yi ajalinki marar anfani kawai"
Da gudu ta shiga gidan don ya miƙe ya biyo bayanta kaman zai faɗi.
Ɗakinshi ya shiga ya haɗo tarkacen da ya karɓo na kare kai daga sharrin Mayu yayi ɗakinta dorinarshi ya samu ya rufeta da duka wai na hawan jinin da ta saka mishi jiya ta kusa ja mishi asarar rai da dukiya babu wanda ya kula su duk ihu da neman agajinta sai da ya gaji ya kyaleta. Ya sa aka kawo mishi garwashi ya turbune su da uban hayaƙi mai bala'in ƙauri bayan ya gama ya tafi ya barta nan yana cigaba da sababi.
Bata san iya adadin lokutan da ta ɗauka a kwance cikin yanayin ba, tun tana kuka da hawaye har suka ƙafe sai dai zuci na cigaba da zubar da kwalla cikin ƙunci da raɗaɗin da bata san ranar tsayuwarshi ba, yunwa ne kaman zai yi ajalinta hakan ya sa ta dole ta lallaɓa ta fito, yadda garin yayi shiru sossai za ka san cewa dare ya riga da ya tsala murhu ta isa akwai sauran gawayi ta dibo ruwa tana layi ta ɗora, a wurin ta zube tana kallon kicin ɗin babu alamar an ajiye mata wani abu da zata iya ci, busashen miyau da ya ƙafe a Bakinta ta lalaɓo da kyar ta Haɗiye.
Sai da ruwan ya tafasa ta juye hadari ne sossai a garin don har an fara iska da walkiya sai dai dayake zuciyarta a kafe yake yasa babu tsoron komai cikin ranta ta shiga ta gasa jikinta sossai ta fito, kicin ɗin ta koma da kyar ta samu wani kanzo ta ɗan bubbuga ta zuba ruwa yayi laushi ta ɗauka ta nufi akurkinta tana da ɗan maggi da yaji da mai kaɗan ta saka a ciki ta ci bata ma gama ci ba taji sauƙar ruwa kaman da bakin ƙwarya, ko da ta kwanta baccin sai ya ƙi zuwar mata sai tunanin rasuwar yaron jiya take ko wani hali iyayenshi ke ciki? Tana kuma tambayar kanta da gaske ita ɗin Mayya ce? Da ƙyar bacci da ya fi kowa iya sata ya lallaɓo ya sace ta...
Rayuwa ya ɗauki yi mata zafi a gidan fiye da baya saboda a yanzu tallar bata yi inna larai ta yi mugun tsanarta don ta karya mata kasuwa hakan yasa ko abin da zata ci a girkin inna larai gagararta yake, ba'a isa a aike ta ba haka zata dawo da hawaye saboda maganganun mutane da ma yunkurin illata ta da wasu kan yi, bautar gidan duk ya dawo kanta yanzu har girki ita ke yi musu su zo suyi rabo kuma a hanata don daga an sauƙe za'a aike ta kan ta dawo an raba in ta tambaya su ce sun manta da ita, ita dai gata nan amma rayuwar baya yi mata daaɗi ko ta wani ɓangare.
''Ina ma mutum na da zaɓi kan rayuwarsa! Ina ma a ce bawa ke da ikon rubuta ƙaddararsa! Da ban zaɓi maraici ba. Duk bala'i na san ko da kowa zai guje ni su ɗin ba zasu taɓa guduna ba" a hankali take furta hakan wani irin kewa da maraici na taso mata, har ƙasan ranta bata son yadda ta zama tamkar mujiya a cikin tsuntsaye, bata son wannan suna na Annoba da yanzu kowa ke ƙiran ta dashi... Kanta a duƙe ƙasa ruwan hawayen da bata rabo da su na sulmiyowa cikin ruwan kunfar wanke-wanken da take yi wani irin zafin da zuciyarta ke yi kaman zata fito daga madaukarta
"Wai zama kika yi kina maitar da kika saba na shanye kurwuwowin mutane ba za ki yi ki kawo mini kwanuka in raba abinci ba?"
Inna larai ta watso mata kalaman cikin hantara.
sharɓe hawayenta ta yi, cikin mintunan da ba su wuce biyar ba ta kammala.
Tattara kwanukan ta yi ta kai gaban murhu ta ja jikinta gefe ta tsaya tamkar jiƙaƙƙiyar kaza da ta rasa mafaka yayin ruwan sama.
"Ungo sayo min kuka da daddawa."
Kuɗin da ta wullo mata a wulaƙance ta sanya hannu ta ɗauka ta juya tana jefa singallin kafafunta masu kama da zaren lipton saboda rama tayi waje, ko da ta dawo zaune ta tadda zuri'ar gidan suna karyawa cikin natsuwa.
"Ga shi inna larai"
Fusga ta yi suka ci gaba da kai lomar zazzafan ɗumamen tuwon dake turiri ita da Inna Asabe
"Abinci...cina fa?"
Ta yi tambayar zuciyarta na rawa. Amsar da take tsoron ji ita ɗin dai ce ta ratsa kunnuwanta.
"Kin ga na manta da ke a rabo, sai ki jira na rana."
Wani irin raɗaɗi ne ya ziyarci idanunta tamkar wacce aka watsawa borkono. Ba ta sauya zani ba ba kuma ta tunanin za ta sauya ɗin abu ne da ta riga ta sani a kullum idan har za a raba abinci aka aike ta shi kenan rabonta ya faɗi ƙas.
Ita take kallo sai dai tuni zuciyarta da ƙwaƙwalwarta suka tafi nisan kiwo, hanjin cikinta jin shi take kamar ana daddatsawa tsananin yunwar da ta kwana da ita. Ba ta da shi ba ta kuma da wanda zai ba ta babu mai ɗigon tausayinta a gidan a cewarsu mayu sun fi cinye kurwan wanda ya ji tausayinsu ko ya taimaka musu.
Sauƙar ruwan zafin da ta ji a fuskarta yasa ta sakin ƙarar azaba a firgice ta miƙe daga durƙuson da ta yi a gabansu tana dirza fatar inda wani irin zafi ke ziyartar ta. A take ta ɗaile, daidai lokacin inna larain take faɗar
"Wallahi kurwata kur! Maye sai dai ya ci kansa."
Baya ta matsa ta sake zubewa bisa gwiwoyinta hawaye na sake tsinke mata cikin shessheƙa ta fara roƙon su taimake ta da abinci.
"Inna don Allah ko da loma biyu ne ku taimake ni da ita, cikina babu komai hanjina murɗa suke, yunwa za ta kar ni."
Kamar dabba haka ta sa ƙafafu ta hamɓare ta ba tare da ta ko damu da raunin ƙunar da ke jikinta ba.
"Ba za ki taɓa samun nasara a kaina ba, wuce ki fara shirin ɗaura mini abincin rana."
Jiki a saɓule ta miƙe ta nufi wurin murhu, a haka cikin raɗaɗin gangar jiki da zuci ta fara aikin. Bata yi nisa a aikin ba suka gama karyawa suka kai kwanukan mawanki kowa ya nufi ɗakinsa don hutawa. Ta rarrafa ta isa bigiren saboda ko ƙarfin miƙewa tsaye babu jikinta tsabar yunwar dake dawainiya da rayuwarta.
Ɗan sauran wanda suka rage take kwarfewa tana afkawa a bakin salati, ta haɗe da tukunyar ta kankare ƙasan tana ci tana zub da hawayen tausayin kanta da irin rayuwar da take. Ko kula inna Larai dake mata gargaɗin kar ta yi mata lamba a tukunya bata yi ba. Ta miƙe ba don ta ƙoshi ba sai don babu wani abin da zata sake samu ta ƙarasa ta kwalfi ruwa ta afawa cikinta. A gindin randar ta raɓe cike da fatan sanyin ya taimaki zuciyarta wurin kashe wutar dake ruruwa a cikinta har take neman kai ta ga kushewarta.
"Afeefah! Afeefah!!"
Sam bata san bacci ya sure ta a wurin ba sai da ta ji ana jijjiga ta tare da kiran sunanta.
"Lafiya kike bacci a nan?"
Idanunta da ba su da maraba da na mashaya saboda gajiya da jigata ta ware tana kallon mai maganar da muryarta yayi kama da wacce ta sani da jimawa, a hankali sanyi ya shiga ratsa ta. Sanyin farincikin sanya mace guda da ta rage mai ƙaunarta kaf faɗin duniya a idanunta, tashi ta yi cikin azama da 'yar fara'a ta rungume ta.
"Afeefah....!"
Kiran sunanta da ta yi tare da fincikar da tayi mata daga rungumar tana ƙarewa fuskarta da ma jikinta kallo ne ta ji tamkar ta sosa mata inda ke yi mata ƙaiƙayi. Dama me neman kuka ne aka jefe shi da kashin shanu. "Wa ya yi miki wannan lahanin?" Ita dai ba baki sai kunne don haka ta ci gaba da kukanta yayin da ta shiga rarrashinta itama hawayen take zubarwa. Da ƙyar Afeefah ta yi shiru kan matar ta buɗe jakar hannunta ta fiddo biredin da ta yo mata tsaraba. Kamar mayunwaciyar zakanya haka ta afka masa da ci ba ji ba gani har tana ƙwarewa, matar ta ɗibo ruwa ta ba ta hawaye na gangaro mata, daidai lokacin da kawu ya fito shirye da alama kasuwa za shi..
"Labaran ka ji tsoron Allah, wallahi ka kwana da sanin kai ma ba ka fi ƙarfin ƙaddara ba. Rayuwa da kake yi da 'ya'yanka ƙarƙashin kulawarka ba wayonka ba ne ballantana dabararka, a yau za ka iya faɗuwa ka mutu, shin za ka so a yi wa 'ya'yanka yadda kake mata?"
Kanwar mahaifiyarta ta jefa masa kalaman cikin jin haushin yanayin da ta zo ta iske Afeefar Kallon banza ya watsa mata.
"Kina da gida ko Zainabu? Toh ki tarkata ta ku tafi tun kan mu yi ɓacin ɓacina kuma ki daina haɗa yarana da wannan annobar... Ni ban haifi maye ko ɗaya ba, ban kuma shirya mutuwa ba. Zaman ma da kika ga tana yi saboda ba ni da yadda zan yi ne, amma yanzu tun da ga ki Allah ya raka taki gona...!"
Har ya nufi fita ya dawo ya sake kallon ta.
"Af! Idan ƙarshen saduwar kenan to ubangiji ya sa can ta fi miki nan."
Miƙewa tsaye ta yi a zuciye.
"Zan tafi da ita Labaran, dama rashin sani ne ya sa kaza ta kwana da yunwa a saman dami, idan ka ga na mutu lokacina ne ya yi. Ke tashi mu tafi."
Ta watso ma Afeefahn sauran kalaman nata tana kallonta, tun farkon rasuwar mahaifiyarta Aunty zainabu da ita kaɗai ce ƙanwar mahaifiyarta ta so karɓar ta sai dai kakarta ta ƙi har ma ya kai ga sun yi rigimar da ta sa tayi matukar fushi, sau ɗaya ta taɓa zuwa ta duba ta a gidan kakartata sai lokacin da take wurin innarta ma ta zo ta duba ta, haka ma tana gidan kawu ta zo sau biyu sai dai bata taɓa wuce awa ɗaya ba tana ganinta ta kawo mata tsaraba ta tafi don wani kauye gaba da su sossai take.
Duk da chan ta san Afeefahn na cikin damuwa sai dai bata san ya kai har haka ba, ganinta a yanayin da ta sameta ya matukar ɗaga mata hankali.
"Afeefah da ke nake yi!"
idanunta da kaman za su faɗo ta saisaita ta miƙe da sauri ta shige akurkin ɗakin nata. Wani tunani da ya ɗarsar mata ne ya sa ta nemi gefen kayanta ta tsuguna, hawaye ne ya cika idanunta Aunty Zee ce ta shigo tana ƙarewa ɗakin kallo cike da tausayawa ta duƙa gangarta tare da dafa kafaɗarta
Kaman ta karanci yanayin da take ciki da tunanin da zuciyarta ke yi.
"Sau tari ƙaddarorin da ke zagaye da mu su ke taimaka mana wurin tabbatar da imaninmu ko akasin hakan, ina so ki zama tuwon hatsi mai yawan juriya, dukkan tsanani yana tare da sauƙi. Mu tafi."
Taya ta tayi suka haɗa yar Ghana most go ɗinta da babu wasu kayan kirki suka fice, bata damu da ko sallaman su Baba Larai ba su ma kuma dariyar Allah ya tura ƙeya suka bi su da shi don yanzu Afeefahn bata da anfani a rayuwarsu.
Tasha suka tafi suka hau mota, ita dai jikinta ya matuƙar sanyaya damuwar da ke ranta ko kusa bai ragu ba saboda tsoron kar wani abu ya sami Auntyn nata da take ji da, ya haɗu da bata taɓa shiga mota ba a rayuwarta don bata taɓa barin garin nasu ba wannan ne karo na farko, bata san akwai titi kwantacce irin hakan ba sai da suka ɗauki titin cikin garin Anchau daga kauyensu chan cikin Dutsen-wai na Kaduna state, tun tana kalle-kalle har bacci ya sure ta, sai ji tayi Aunty zainabu na tashinta tana bude ido ta ga har sun iso inda za su sauƙa ba ma su isa tasha ba don Auntyn gidan ta na daga wajen garin Anchau duk under kubau LGA of Kaduna state ne, sauƙa suka yi ta ɗauki kayanta a kai suka gangara layin har zuwa gidan, layi ne na masu matsakaitan ƙarfi da rufin asiri gidan Auntyn ba wani babba bane sai dai ciki biyu ne da parlor sai tsakar gida da take da tarin shuke-shuke.
A madaidaicin parlorn ta yi mata masauki ta buɗe karamin frigde ɗinta ta fiddo mata ruwa
"Sha ruwa bari na samu na ɗora mana wani abu ko? Sannu. Ki sake jikinki a nan babu mai takura miki in shaa Allahu kin ji?"
Kai ta gyaɗa tana yaƙe dai, bayan ta sha ruwan ta fita zuwa kicin na tsakar gida don kamawa Auntyn nata aikin da take yi Dukda ta ƙi tace ta je huta amma sai da ta saka mata hannun suka shiga yi tare tare har suka gama, shinkafa fara da Miyar jajjage da tayi ta saka mata a filet
"ɗauka ki koma ƙasan mangoron chan ki shimfida taburma sai ki ci"
Yadda ta ce haka tayi Auntyn ta kawo mata ruwa again tuni ta yi nisa a cin abincin.
Aunty zainabu dai na ta kokarin haɗa na mijinta don ta san yana gab da shigowa shima cin abincin ranan, dama daga ita sai shi ne gidan Dukda ta fi shekaru goma da aure sai dai har yanzu bata haihu ba, ya sake aure bayan ita amma ba gida daya suke da matar ba itama dai har yanzu babu wani labari na haihuwa kam suna kuma zaman lafiya sossai.
Tana ƙoƙarin kai loma yana sallama, ta amsa ya ɗan yi turus yana kallonta gabanta ne ya ɗan faɗi don ganin fuskanshi ya ɗan sauya ko da ta gaishe shi da kalma ɗaya ya amsa kan ya nufi ciki yana kiran zainabu...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Ba lallai ku ji ni anjima chan ba saboda wani uzuri na so pls bear with me ku riƙe wannan as na chan anjima ɗin tunda Its already friday.*
*004*
A wurin ta cigaba da zama jiki a saɓule har dai Aunty zainabu ta fito tana kallon fuskanta da har ya ɗuri ruwa saboda ƙuna daga gefe zuwa ƙasan idanunta, Allah ya taƙaita ma bai taɓa idanun ba ta ce
"Har kin gama ci Afeefah?"
"Eh Aunty na gama"
Ta faɗa a hankali don yanayin Auntyn bai mata yadda suka dawo ba idanunta kaman ta yi kuka.
"Bari na ba uncle ɗinki abincinshi sai na zo mu tafi gidan mai mazari ya duba miki wannan ƙunar kar ya zama miki damuwa"
Daga haka ta yi kitchen, Afeefah ta miƙe ta shiga parlor zuwa ɗakin da ta ajiye mata kayanta daidai ta sauya hijabi zata fito ta ji mijin Auntyn nata murya a sama yana magana
"Babu inda za ki da ita zainabu idan ba mayar da ita inda kika ɗauko ta za kiyi ba"
Itama Auntyn a sama ta amsa shi
"sai dai kuma idan za mu bar maka gidan tare da ita Usman"
"Zainabu...!"
Da mamaki ya ƙira sunan don a zamansu ba zai ce ga sadda ta ɗaga mishi murya ba sai yau. Kuka ta fara
"Haba Usman na fa faɗa maka maganan nan a wurina bashi da matsuguni, Afeefah ɗiyar yayata ce daidai take da tawa wacce zan iya haifa a cikina tana cikin matsi da takurar rayuwa ina tsoron nima Allah ya kama ni a kan banzatar da rayuwarta don Allah ka kalleta da kyau ka ga depression na neman kasheta tun a kananun shekaru..."
Ya katse ta
"Zainabu ba wai 'yar uwarki na tsana ba ina tsoro ne, ina tsoron abin da zai je ya zo daga nan Anchau har Dutsen-wai babu wanda bai san da labarin yarinyar nan ba, ko kwanan nan ta ci kurwar wani matashi a kasuwa kowa tsoron hulda da ita ya ke sai ni zaki ɗauko ta ki kawo min cikin gida?"
Tana kuka sossai tace
"Wallahi duk babu gaskiya a lamarin mutane Allah ba zan taɓa yarda Afeefah zata yi maita ba, babu mai mutuwa sai wadda kwanakin shi suka ƙare idan ko don ka zauna da mutum kwana ya ƙare ka zama maye ne da dukkan mu nan Mayu ne don idan baka rasa iyaye ba ma ka rasa makusanta. Idan dai har Afeefah zata bar gidan nan zan bita mu tafi tare ba zan iya sake mayar da ita gidan labaran ba wallahi"
Numfashi mai karfi ya sauƙe
"shikenan zainabu ai sai ta zauna, amma duk abin da ya je ya zo babu ruwana"
"Babu ma abin da zai faru sai alkhairi"
A lokacin Afeefah ta sulale ta maƙale jikin gini kamar kadangaruwa ta chusa kanta cikin kafafunta, bata ga laifin mijin Aunty zainabu ba rayuwarsu yake karewa da ya wajaba a kanshi amma Meyasa ita ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 40