ya same ni, ba dai a kan wanchan Mayyar ba ce? Zai yi ya gama Rabuwa kam sun rabu na har Abada"
"Amma mommy ya kamata dai ki je ciwo ai ya kore komai"
Sadiqa ta faɗa, Samha tayi fuskar tausayi bata san haka abin zai kasance ba da bata janyo wannan rigimar from First place ba, suna son dan uwansu basa son ganinshi cikin wani hali.
Duk yadda suka yi da mommy akan ta je ta ƙi haka suka tafi su uku, suna ficewa ta sabi gyale itama ta dauki mota ta bar gidan.
Tafiya mai nisa tayi kan ta iso inda ta nufa, wani gida ne tayi parking gidan dai daga gani Talaka ne mamallakinshi don ya tsufe har ya gaji, ta sauka ta shiga ciki da sallama.
"Ah Hajiya Hussaina ce tafe? Maraba sannu da zuwa sannu da zuwa"
Matar da daga ka ganta ka san suna cikin wahala daidai gwargwado ta faɗa tana ɗauko taburma sabuwa ta shiga shimfida mata zama tayi suka shiga gaisawa, bayan sun gama tana ɗan kallon cikin gidan tace
"Yaya fa? Allah ya sa dai bai yi nisa ba"
Tace
"Yanzu kuwa ya fita amma babu jimawa zai dawo don abu ya je karɓo wa nan kusa da mu"
"Ina yaran? Ina sabreena?"
"Duk fa sun tafi Allo, ita sabreena suna bukin ƙawarta ta fita"
Bata gama magana ba kuwa sai ga Yayan ya shigo.
"Hajajju ke ce a gidan maraba sannu da zuwa"
Gaisawa suka yi Dukda yayanta ne sai dai shi ke bata respect duk saboda kuɗi masu gidan rana.
"Ina soja marmari daga nesa? Sati biyu kuwa da ya shige ya aiko mana da kayan abinci wane Allah dai yayiwa rayuwa Albarka ya cigaba da buda mishi"
"Ameen yaya, dama maganan da ta kawo ni kenan ma akan shi... Ka san akwai batu a kanshi da sabreena da take ta mutuwar sonshi shi kuma yana nuna baya so, to yanzu zancen da nake maka wata yaje ya ɗauko chan wani kauye ta asirce shi tun kan ma ayi auren sai maganarta yake ji yanzu haka saboda na raba su yana chan kwance gadon asibiti"
Gaje da Yaya suka hada baki suka ce
"Eyeee ka ji min yaran zamani ki samu mutum da uwar shi ki so raba su? Amma Saleem dai yayi ragon azanci ina shi ina irin waennan matan?"
"Shiyasa nake so a tado magananshi da sabreena da na ɗauka wata mai hankali zai ɗauko mana ashe dai shima hankalin bata ishe shi ba, na kuma ga gida bai koshi ba ai ba za'a kai waje ba, idan ba damuwa ma bana son auren nan ya ɗauki lokaci ko wata bana so ya rufa ta zo tayi jinyarshi"
Gaje ta washe baki, Yaya dai ya ɗan yi shiru kan yace
"Toh ai wani hanzari ba gudu ba, kin san bamu ajiye komai ba na shirin aurar da sabreena"
"Yaya duk wannan ba komai bane, ni ce nan uwarta ni ce ubanta ita kaɗai nake so"
"Toh ai shikenan Allah ya shige mana gaba"
Suna cikin maganan sai gata ta shigo sanye da hijabi har ƙasa ganin mommy ta tsuguna
"Sannu da zuwa mommy"
"Sabreena ba zan amsa ba, yaushe rabon ki da gidan mu? Tun su Samha na jaje har suka gaji"
Baki ta ɗan taɓe tana ayyana su kuma dayake basu san inda nake ba ba, ai ina sane da kyamar gidan mu suke ji shiyasa basa zuwa.
"Mommy islamiyya ne duk ya riƙe ni kin san muna ta shirin sauƙa"
"haka ake so ai Allah ya taimaka"
Daga nan bata wani jima ba tace zata tafi suka raka ta har mota kan suka juyo gida.
Wani irin guɗa gaje ta saki
"Malam!!! Kukanmu ya kusa yankewa nesa ta matso kusa"
Shi dai wani kalar murmushi yake, Sabreena ta cire hijabin jikinta ta jefar
Sanye take da wata fitted gown na lace da aka yi wa arniyar ɗinki da ya bayyana komai nata, kanta attach ne da ya zo har duwawu ta ja tsaki.
"Ke 'yar gari ya aka yi kika ankare tana nan?"
Gaje ta faɗa tana kai mata duka kamar kawarta
"Motar ta na gani nayi maza na shiga makota na ari hijabi na wanke fuska na cire eyelashes da nails ɗina gashi a banza bata bani ko biyar ba mata sai makon bala'i"
"maganar aurenki ya kawo ta, nima zan so a zo ayi saboda na gaji da gani gani da ake yi min a unguwar nan, ita kuma Hussaina a zaton ta banza ya faɗi ne zata ɗauka bata san ta daukawa kanta wuta ba... Ai yadda uwata bata taɓa kaunar nata uwar ba nima ban taɓa ƙaunarta ba kuma ita ma haka da tana ƙaunata da bata barni nan cikin wahalar talauci ba"
Haka suka dinga tattauna yadda za su ci arziki don mommy ta jima da tsaya musu a wuya kaman kashin kifi, don ma saleem mutumin kirki ne mai son zumunci baya wata bai turo musu wani abu ba amma ita kam bata tunawa da su sai in bukatarta ne ya tashi, ta watsar da dangin tamkar kashi an ɗauki Ƙawaye masu kuɗi an manna a jiki har kunyar nuna su take.
Sabreena dai da farko yarinya ce natsatsiya amma zamani ya zo mana da wani abu, iyaye ba ruwansu bane yaro ya tsaya yayi karatun islama ko kar yayi, damuwarsu dai a nema ko ta wace hanya, babu kwaba babu cikakkiyar tarbiya, tun tana dai yin abin saffa saffa yanzu babu wanda bai san Sabreena 'yar karya ba, barta da son karya yau wannan saurayi gobe wanchan don tana da kyau kuma suna kashe mata amma dai ita ta riga ta saka saleem ne mijinta tunda iyayenta suka kwadaita mata hakan a ganinsu duk samarin ta ba zata yi mai kudin saleem ba.
Ita kuwa mommy tana shiga mota tayi murmushi
"Gwara ka auri wacce ko kwanciya na ce tayi in bi ta kanta zata kwanta, wacce dole ku haɗu ku bi umarnina tare akan ka kwaso wacce zata raba ni da kai ko ta hanyar soyayyace kuwa bare uwa uba asiri"
Daga haka ta ja motar ta bar unguwar tana kwafa.
****
Afeefah kam suna shiga ɗakin da Abeeha ta kaita ta tsaya tana karewa ɗakin kallo, ɗakin yayi kyau kwarai kuma full furnished don kayan ɗakin milk da gold a gyare yake kaman akwai mutum ciki alhalin ba mai zama ɗakin tunda mai dakin tayi aure.
"Feel free Afeefah ki yi wanka bari na sa a kawo miki abinci, in kin ci sai ki hau gado ki huta ko?"
Ta kalleta sai taga murmushi take mata saɓanin ranar da ta fara haɗuwa da Samha ta tuna har wanke bayi Samha tayi da sunan tana kyamarta don kawai ta shiga tayi alwala, murmushi ta mayar mata tace
"Na gode"
"Mind not"
Ta faɗa tana ficewa, a ƙasa Afeefah ta zauna tana dafe kanta da kaman zai faɗi, ta fara tunanin halin da Saleem ke ciki sai dai kuma tayi tunanin ba zai damu sossai ba idan Ryan ya faɗa mishi tana gidan su, jiri sossai yake damunta a haka ta lallaɓa ta miƙe ta shige bayin, wanka tayi tana raya a komai ma fa gaba da gabanta tana tunanin abubuwan bayi da ƙawa na gidansu saleem ne ƙarshe bata san akwai irin wannan ba, sai kuma ta fara tunanin kila suma akwai wanda ya fi nasu shiyasa Allah ma da ya tashi bai yi yatsun hannu daidai ba kowa da matsayinshi.
Amma me yasa kirkin waennan ya bambanta da waenchan Dukda waennan sun fi su dukiya? Bata da amsar wannan tambaya ta wani ɓangaren kuma tana da shi don uwa nagartaccciya da suke dashi ya gama amsa mata komai, dafe da gini ta fito riga kawai ta saka ko abincin da aka kawo mata ta fito ta samu shirye a babban tray bata iya ta bi ta kai ba ta hau gadon ta dukunkune, zazzabi ne ya saukar mata ciwon kai da jiri kuma suke contributing.
Kusan awa biyu tana cikin wannan yanayi tana ta hawaye, hawayen tunanin saleem bata san itama tana jin wani abu a kanshi ba sai da suka rabu, ko babu komai shine mutum na farko da ya bata dukkan kulawa da lokacin shi, ya nuna mata itama mutum ce kamar kowa, tana kukan maraici da tsananin kewan iyaye saboda shi ne sila tun farko.
Knocking aka yi mata sai aka turo kofar da sallama aka shigo Abeeha ce
"Afeefah"
Ta ƙira sunan tana zagayawa ta kanta, ganin halin da take ciki ya bata tsoro
"Subhallah! Baki da lafiya ne? Sannu bari na faɗawa Mammi ta kira Ya Rayyan ya zo ya duba ki"
Bata jira amsar Afeefah ba ta fice da sauri.
Ɗakin Mammi tayi ta shiga da sallama ta samu mammin ta idar da la'asar tana zaune ne kawai tana lazimi a hankali.
"Mammi Ya Rayyan bai dawo ba? Ko za ki kira mana shi?"
"Me ya faru? Ke fa kin iya rudewa a karamin abu"
"Mammi wannan yarinya da kuka dawo tare Afeefah kin ji jikinta? Kaman wuta sai kuka take yi tana bukatar a duba ta ko mu tafi hospital?"
"Subhallah! Tashi mu je in ga jikin"
Har sun miƙe Mammi tace
"Taho min da wayata"
Taje ta ɗauka a bedside suka fita, a ta babban parlorn nan suka yi sashen da take ɗin wanda na 'yan matan biyu ne Jannah da tayi aure bai jima sossai ba sai Abeeha su suke rayuwa anan.
Suna shiga Mammi ta hau gadon da taimakon Abeeha suka ɗaga Afeefar Mammi ta jinginata da kafaɗarta tana yi mata sannu cikin kulawa, wannan dumi na jikinta da kulawar sai ya sake karya zuciyar Afeefah tana tsoro! Tana tsananin tsoron su san tarihin ta suma su guje ta, tana son wannan dumi da kauna a tare da ita in ba haka ba kila mutuwa zata yi kawai sai ta fi hutawa, ta gaji haka zuciyarta ya fi glass tarwatsewa a yanzu haka.
"Kira min Yayanku"
Layin shi ta nemo a wayan mammin ta ƙira ringing na farko ya ɗaga da sallama.
"Mammi jikin ne?"
"No Saraki! Na ma ji ƙarfin jikin ka san abin kaman tashin aljannu yanzu sauƙi anjima babu sauƙi sai na Allah, ya jikin saleem ɗin?"
Ya amsa cikin muryarshin nan
"Ya ji sauƙi though he's still on admission, amma komai zai daidaita in shaa Allah"
"Toh Allah ya bashi lafiya, ina so ka zo ka duba Afeefah fa ashe itama bata jin daaɗi jikin nan rau sai kuka take"
Shiru yayi for seconds kan yace
"Mammi bai wuci yunwa ba and stress she should just eat nd get enough sleep"
"Ta ya mutum zai iya bacci with this temperature? Idan ba zaka zo ba in ɗauki mayafi in kaita asibiti"
Zaune ya miƙe daga kishingiden da yake a office nashi yana wara ido, yaushe Mammi ta san yarinyar nan da har take mishi irin maganan nan a kanta? Yamutsa fuska yayi ko dai da gaske asirin take yiwa mutane da har ta asirce mishi Mamminshi?
"Ina zuwa"
Abin da ya fada kenan da kyar, Mammi ta kashe wayan Abeeha tace
"Lallai Mammi kina so Ya Rayyan ya tsani yarinyar nan, tabbb he sound upset fa da yadda kika mishi maganarta yo ko mune bamu da lafiya ba sai ya gama shan kamshin shi yake duba mu ba, wani sa'in ba sai dai mu haƙura mu tafi asibiti ba ma"
"Abeeha yarinyar nan haka kawai nake jin she gets special place in my heart, kin san taimakon da tayi min?"
Nan Mammi ta shiga bata labarin abin da Afeefah tayi mata
"Mammi wlh har Naji ina sonta sossai nima, to ina 'yan gidansu ina parents ɗinta?"
"Ina ga sun yi magana da Saraki while i was unconcious don shi ya ce min bata da kowa"
Afeefah dai na jinsu, tunda Mammi ta kira Rayyan tsoro ya rufeta, gashi ya ji haushin yadda mamanshi ta mishi magana a kanta kar ya zo ma yayi mata allurar da baƙar mugunta ita dai da an barta kawai.
Suna ɗakin suna ta hira kadan kadan don Abeeha bata son zama baki shiru har Afeefah na mamaki kaman ba ƙanwar Rayyan da magana ke mishi wahala ba, ita ma dai bata ga kamanninsu ba sai dai Abeehar kyakyawa ce kuma ta fi Mimmi haske amma ba ta kai ko farcen Rayyan ba, bata gama nazarin ba ya shigo ɗakin hannunshi rike da karamar Red briefcase.
Dammm haka gabanta ya buga, ya kalli Mammi da har lokacin Afeefah ke kan kafaɗarta ya wara kyawawan idanunshin nan kan ya ce
"Me wannan? Mammi yaushe kika yi lafiyar daukar wata? Watan ma stranger?"
Da sauri Afeefah ta miƙe zaune jiri ya kwashe ta ta koma jikin gadon ta jingina idanunta a lumshe zuciyarta na harbawa da tsoro.
"Haba Saraki ji yadda ka tsoratata?"
Ganin sossai ranshi bai mishi daaɗi ba yasa bata sake cewa komai ba, ya dubi Abeeha
"Wawuyar banza come on raka Mammi ɗakinta she should be resting ba stressing kanta ba"
Tura baki tayi ya nufeta ta miƙe da gudu ta koma kusa da Mammi sai Harare Harare yake.
Mammi tayi dariya
"Zan je in huta Saraki don Allah ka yi mata a hankali, she's suffering"
Ta dubi Abeeha
"kin ga kama ni mu tafi tunda overprotective Yayan naki ya kore mu"
In ta shi ne fa tafiya ma zai iya yi mata, itama kuma son da take mishi bata hada da kowa ba, kuma babu wanda ya kaita saninshi don ko kallon abu yayi ta san ma'anar kallon, Dukda fuskarnan ya fi zama a haɗe amma ita tana gane idan yana cikin farin ciki, damuwa ko bakin ciki, yanzu haka ta karanci akwai 'yar damuwa a ranshi sannan har da rigima irin tashi don baya so yaga tana fifita wani a kanshi, su Jannah kan ce Ya Rayyan idan ya samu wacce yake so kamar rai za'a ga kishi kamar hauka.
Bayan fitan su ɗakin ya zama shiru sai su biyu kawai hakan ya kara tsinka Afeefah.
"Kwanta"
Ta ji muryarshi ya daki dodon kunnenta duk da ba da ƙarfi ko tsawa yayi maganan ba.
Da sauri ta kwantan tana kara jan bargo, hannunta dake kan cikinta kawai taji sassanyar tafin hannunshi mai taushi ya kama babu shiri ta buɗe idanunta sai suka faɗa cikin nashi da shima a lokacin ya kalleta...
****
Ta ɓangaren Sulaiman yana ta gwada Layin Afeefah don ya ji ya jikinta har yamman ya kasa samunta, ya ajiye kila network ne don haka ya cigaba da huldar gabanshi har Magrib baya samunta, yana gama shirin asibiti ya nufi gidan don ya ji ko lafiya baya samunta haka bayan ya isa suka gaisa da su mudi.
"Don Allah ko za ku dubo min Afeefah?"
Iliya ya ce
"Ai Afeefah bata gidan nan, ina zato ma ta barshi gabaɗaya don da akwati ta fita tun safe"
Gabanshi ne ya faɗi
"wani irin tafiya ba dawowa? An taɓa tafiya haka babu shiri? Gida ta koma ne?"
Mudi yace
"Wallahi bamu sani ba amma dai kaman gidan dai ba lafiya dai, don Oga saleem ma yanzu haka yana kwance Hajiyar na a hasale, 'yan matan kuma sai kuka Toh ita ma Afeefar da ta fito a chan ta tsuguna ta ci kukanta isashe kan ta tashi ta tafi"
Sossai damuwa ya nuna a fuskanshi, idan tunanin shi ya bashi daidai Saleem ya faɗawa Afeefah yana sonta mamanshi ta ji shine suka kore ta, godiya yayiwa su Mudi ya juya ya nufi gida, kila ta koma kauyensu yana ji a ranshi da sauƙi ma tunda har ta faɗa mishi sunan kauyen kan su rabu da bai san inda zai sa kanshi ba, dole ya je ya neme ta.
Gida ya dawo Umma na ganinshi tace
"Ah Sulaiman ina asibitin? Me ya faru na ga kaman kana cikin damuwa?"
"Umma su saleem sun kori Afeefah a gidansu, mamanshi ta kore ta ta koma kauyensu dole gobe in nemi leave in je in sameta ban san ya take ba kuma wayanta baya shiga"
"Wacece haka?"
Suka ji Muryar Abba!
Umma ce ta mishi bayani yana murmushi yace
"Toh ai Alhamdulillah! Dama da niyyar aura maka mata na dawo a yau na gama maka uzuri goben da su Yaya Zubairu za ku tafi a yi maka tambaya gabaɗaya tunda Allah ya sa ka samu wacce kake so kuma mahaifiyarka ta gamsu da tarbiyar ta"
Murmushi ya saki yana jin sanyi a ranshi Dukda ta wani ɓangaren yana tunanin kar Afeefah taji ba daaɗi tunda bata sani ba kuma ba wai soyayyarsu yayi zurfi bane ita ke ture shi yana sa kai amma dai ya ji daaɗi don da farin ciki ya koma asibitin da bai yi niyyan zuwan ba ya tafi saboda ya samu leave a gobe ɗin don su tafi Dutsen-wai.
A waya Abba ya sanarwa yayyenshi biyu akan za'a je wa Sulaiman tambayar Na gani ina so a kauyen Dutsen-wai, basu wani damu ba don duk su burin su ba su hada zuri'a da masu kuɗi ba sai su hada da gidan mutunci gidan tarbiya da sanin ya kamata shi ne abin da suke dubawa.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Gobe in muna raye sai dare za ku ji ni da yardar Allah*
*020*
Harara ya sakar mata da sauri ta mayar da idanun ta rufe ruff tsaki ya ja a fili, ya fara ƙoƙarin neman vain ɗinta... 'Asshh' ta faɗa a hankali jin ya soka allurar sai ta fara kokarin janye hannun.
"Kina janye hannun nan sai na wanka miki mari akwai wanda yace ki yi ta tuna samarin ki kina kuka har ciwo ya kama ki?"
Tsit tayi bata kuma motsan ba, kila Rayyan shine ajalinta wa ya sani don tunda ya daka mata tsawar nan ko numfashi mai kyau ba ta iya ja har ya gama ɗaura mata drip ɗin, bata ji fitan shi ba ita kam tun tana pretending har baccin gaske ya ɗauke ta a haka, don dama jiya ba baccin ta samu ba na kirki gashi yau ta yini a kan hanya tana galantoyi.
Sashenshi kawai ya miƙa daga nan don ya matuƙar gajiya hutu kawai yake buƙata, wanka yayi ya fito da alwala ya zo ya shirya cikin wani morrocon jallabiya baƙi sidik mai sheki wanda ya fito da ainihin kyaunshi fatarshi ya haska jallabiyar, masallaci kawai ya wuce bai dawo cikin gidan ba sai da yayi isha, time ya kalla ya ɗauke ido ya nufi cikin main parlorn kai tsaye ɗakin da take ya wuce, ta miƙe zaune bayanta jingine da jikin gadon kafafunta na cikin bargo, idanunta sun kara girma sun dan sauya saboda kukan da ta yini yi ga kuma bacci da tayi tayi, hulan kanta ya zame sosai ya bayyana rabin gashinta mai sulbi, tunani take ya zata yi in ruwan ya ƙare sai taji an yi knocking seconds uku zuwa huɗu ya turo kofan ya sanyo kai da sallama wadda iya shi kaɗai ya san yayi kayanshi.
Kanta tayi saurin mayarwa kasa Alamu sun nuna bashi da niyyar magana don har ya zo ya cire ruwan da ya ƙare ya bare wani allura ya fasa yayi mata a canular bai ce takk ba itama bata ce ba, kamshinshi duk ya cika ɗakin har ya gama ya juya zai fita ta furta
"Na gode"
Bai ce komai ba ya fice daga ɗakin, kai tsaye wurin Mammi yayi, tana daga parlor a zaune cikin kujera abinci ne a gabanta wanda ta gama ci yanzu cikin kula sossai da cimar tata ɗin don professional cooker ya samo mata wacce take kulawa da zallar abincinta kuma take da karatu na musamman akan cimar da ake ba wa masu ciwon ƙoda da kan tafi da diabetes, ba'a so ta ci late kuma da ta gama ta sha magani tana so ya ɗan saketa sai taje ta duba Afeefah.
Bai yi magana ba kawai ya zo ya zauna gefenta, ta kalleshi tayi murmushi
"Gajiya ne a jikinka sossai Saraki, ka ci abinci sai ka je ka huta"
Kai ya gyaɗa kawai don bashi da niyyar magana, da intercom tayi amfani ta kira su a kitchen a kan a kawo abincin Saraki, simple abinci ne marar nauyi yake ci da dare suka kawo suka jere a gabanshi, har lokacin yana kishindige kusa da ita idanunshi a lumshe.
"Tashi ka ci kar yayi sanyi babana ko in baka?"
Ya buɗe ido a hankali ya ɗan yi murmushi kaɗan sai wani sirrin kyaunshi ya bayyana Dukda murmushin bai jima ba sai dai tabbas duk wanda yayi wa irin murmushin zai jima bai manta ba.
Itama murmushi tayi don ita kam akwai fara'a masha Allah, abincin ya ɗan ci kaɗan ya kalleta jin tana cewa
"Ina zuwa zan duba Afeefah"
Da Kai ya amsa ta fice, ta samu Afeefar ta idar da sallolinta tana kokarin cin abincin da aka shigo mata dashi Abeeha na zaune cikin kujera daya daga cikin huɗu dake gefen ɗakin tana danna waya ganin Mammi ya sa ta taso
"Afeefah ɗiyata ya jikin?"
Murmushi ta saki a kunyace tace
"Alhamdulillah da sauƙi sossai Aunty na gode"
"Bana son sake ji kin ce Auntyn nan baki ji Abin da su Saraki ke faɗa bane?"
Murmushi tayi.
"Abeeha ki kula da ita har tayi bacci zan je Saraki na jirana in na sha sauran magungunan kuma kin san bana iya taɓuka komai sai da safenku"
"Toh Mammi sai da safe Allah ya kara sauƙi"
"Allah ya baki lafiya sai da safe Mammi"
Afeefah ta faɗa ta amsa da murmushi kan ta fice.
"Na ga dai baki da niyyar sa abincin nan bari na zuba miki"
Abeeha ta faɗa tana zuba mata Afeefar ke cewa yayi amma sai da taji ya mata a ranta kan ta bari kuma tace sai Afeefar ta cinye, sossai moment ɗinta a gidan na yan awannin nan yayi mata daaɗi in ka cire arangamarsu da Rayyan amma Mammi da Abeeha mutanen kirki ne da suka yi ƙarancin samu a wannan zamani.
Mammi na komawa ta samu ya gama, ɗaki ta shige ta fara shirin kwanciya cike da dauriya take komai fuskarta dai baya nuna wa amma ita ta san me take ji, sai da ya bata mintunan da yake da tabbacin ta gama yayi knocking ya shiga ɗakin tana zaune bakin gado sanye da doguwar rigan bacci har ƙasa mai kauri, frigde yaje ya ɗauko mata ruwa tulin magungunanta da suke cikin wani basket guda mai kyau ya ɗauko ya zaɓi na daren ya bare ya sanya mata a tafin hannunta, babu musu ta sha yadda ya buƙata kan ta kwanta, ya ja mata bargo ya zauna daga gefenta tare da riƙe hannunta ɗaya.
Adu'a yayi ta mata tun tana kallonshi tana danne hawayen da suke ta yunkurin zubo mata har tayi bacci, idanunshi da suka rine ya ɗan rintse yana jin azaban da zuciyarshi ke yi, da yana da yadda zai yi ya mayar da ciwon Mammi jikinshi da bata shekara takwas tana fama da kidney failure ba, da kuɗi za su yi mishi maganin ciwon Mammi da ko zai yi yawo tsirara sai ya samar mata lafiya, sai dai yana roƙon Allah a koyaushe yadda aka bata wa'adin watanni uku za ta mutu amma yanzu shekara har bakwai da abin ya san ba yin su bane ba kuma dabararsu bace Allah ne mai yadda ya so, sai dai a tsananin tsorace yake hakan ya sa sadaqa da duk adu'ar shi yake kan Mamminshi itama saboda rage mishi damuwa take danne wani abin.
Sai da ya tabbatar komai intact kan ya fice daga ɗakin yayi Sashenshi, Saleem ya ƙira da har lokacin yana asibiti yana samun kulawa
"Har yanzu babu labarin Afeefah ko Rayyan?"
Ajiyar zuciya Rayyan ya sauƙe
"Na ce ka daina ɗaga hankalinka za mu same ta, ina kan bincike dai in har tana cikin Kaduna ba zata ɓace ba just focus on your health"
Kai saleem ya gyaɗa sai yake ganin kaman Rayyan bai yi niyya bane, da yayi niyya ba zai kai zuwa lokacin bai same ta ba, damuwarshi ya zata kwana? A ina zata kwana? Me ta ci? Duk ya kasa kwantar da hankalinshi a gefe ga damuwar rashin ganin mommy Dukda ta mishi abin da ya zama gyambo a zuciyarshi sai dai uwa ce babu yadda ya iya kuma yana ƙaunarta bata da mahadi a wannan duniya.
A ɗan sanyaye yayi sallama da Rayyan, Rayyan ya bi wayan da kallo baya jin zai gaya mishi inda Afeefah take saboda yana son Saleem ɗin ya manta da ita once and for all yanzu in ya san tana nan zai cigaba da sa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 40