yana shafa lallausar Fatan bayanta
"Kika cigaba da fushin nan zuciyata za ta iya shiga matsala Ya Alami" (Duniyata)
Yana cigaba da shafata a natse ya cigaba
"A faɗa laifina in yi gaggawar tuba kin san Sameer mai biyayya ne a fadarki"
Ta ɗan yi murmushi ta isa? Sarkin gobe ya zama bawan ta?
"Shine har da yiwa wata murmushi a gabana har da karɓar gift ɗinta"
"O'ooo am very sorry ban san dalilin fushin ba kenan, kin fa san babu macen da take da daraja ko kima a idanuna bayan ke da Ammi, Afeefah ke ce mahadina daga ke kuma Ryan ya gama kallon 'yanmata"
Wani sanyi ne ke kwarara mata yana mata son da bata san adadin shi ba, ɗagowa tayi ta mayar da kanta kan pillown da yake sai ya juyo suna kallon juna tace
"Na sani ba zaka taɓa zama da mace daya ba amma na rasa Meyasa duk sadda wata macen ta kallar min kai sai in ji mutuwa ne kawai ya saura mini tsabar zafin zuciya"
Yayi murmushi yana riƙo hannunta a tsakiyarsu
"Wa yace miki hakan?"
"An ce sarakai ba sa zama da mace ɗaya"
"Za'a fara a kan Sameer Muhammad Modibbo don daga ke na rufe kofa a gidana"
Soyayyarsu suka cigaba da sha yana bata duk kulawarshi ta so ta tafi Kd ya hana don haka ta mayar da hankali kan lectures ɗinta da kulawa da shi da kuma cikinta har Allah ya kawo ta watan haihuwa, wani ranar Alhamis da dare labour ya saka su nufar asibiti babu shiri a safiyar juma'a ta santalo katoton ɗan ta fari tas mai kama sak da mahaifinshi wanda a ranar BOƊEJO ta sha kuka ganguna da kalangu sun yini dokawa kowa ya gifta Masarautar Fombina sai ya san ana cikin alkhairi dumu-dumu.
Yaro ya zo da tarin alkhairi don Mai martaba ji yake kaman ranar ne ya fara riƙe Sameer a hannunshi tuni lungu da saƙo sun samu labari hotunan kuwa har ya je Kaduna uwar jego ta sha ƙauna iri iri, ko da suka dawo masarauta sashenta take wata dattijuwa ta shiga hidimar kula da ita da bata cikakken kulawa na masu jegon gargajiya, ranar suna an yi bidiri Aisha ta zo da cikinta kuwa haka sulaimi ma ta zo da nata tamfatsatsen cikin Haihuwa yau ko gobe sai Jannah da take shirin zuwa amma labour ya hanata itama a ranar sunan ta haifi danta namiji, Abeeha ma na fama da laulayi aka yi hidimar suna na ji da gani kuwa yaro ya ci suna Muhammad Sameer Modibbo.
A daren sunan Rayyan ya tafi Kaduna don da Jannah ya yini, Ammi ma da kanta ta tafi da wasu hadimai duk basu dawo ba sai da aka yi suna suka bar mata hadimar da zata kula da ita mai martaba ya aika sha tara na arziki inda yaro ya ci sunan Rayyan.
Bayan sunan Muhammad da suke cewa Arham Sulaimi ta koma da sati biyu itama nakuda ya tashi mata sai dai she didnt survive bayan ta haihu Allah ya karbi ranta sun shiga tashin hankali dole Afeefah suka tafi Kadunan duk sun yi jimamin mutuwar ba kadan ba, inda Sameera ta samu Saleem ta roƙe shi ko don 'yar da ummu sulaimi ta bari tana so ta auri Sulaiman ta shayar da yarinyar kaman na ta.
Kan Sulaiman ya amince Umman shi ta amince aka daura musu aure kuwa babu wanda ya hanata shan kwayoyin da ruwan nono ya zo ta shiga kula da ummu sulaimi ƙarama don soyayyar da take yiwa Sulaiman shi ya dawo kan yarinyar kuma tana haƙuri don auren mijin matacciya wanda yake son matarshi sai a hankali. Baaba jummai da Afeefah kaman jiƙa da kaka don kusan kullum suna tare a waya kuma Daga ita har Rayyan da su Ammi su kan yi mata sha tara na arziki don kaman uwa take har a gidansu Sulaiman ɗin ba 'yar aiki ba.
Rayuwa ya cigaba da juyawa ba za'a ce ba'a saɓawa ba sai dai duk abu da fahimtar juna ba karamin lasting yake yi ba, sossai rayuwar Afeefah yake kan saiti har aka wayi gari ta gama karatu inda ranar da ta gama last paper ɗinta ta shigo masarautar ta sauƙa a sashensu kawai ta ga wata hadaddiyar tsadaddiyar Maybaach Ash Color an yi mata ado da furanni, Rayyan ta gani ya fito cikin kyakyawar shiga fuskarshi ɗauke da smile yace
"Congratulations Allah ya albarkaci abinda kika karanta My baby mama"
Tsallen murna tayi fuskarta dauke da fara'a ainun ta karbi keyn ta buɗe motar sai taga balloons na zubowa kaloli daban daban Juyowa tayi rungumeshi cike da farin ciki take cewa
"Thank you so much My love, My best friend, My for ever, My safe space. Thank you for being you and choosing me everyday.."
kan yayi wani motsi ko magana sai ta fara jin tashin trumpet ana yi mata congratulations tana juyawa ta ga abokan arziki na kusa da na nesa ta ma rasa yaushe suka zo kuma ta yaya?
Ameer da Abeeha sanye cikin shiga iri daya Abeeha na rungume da ɗiyarta mai sunan Mammi ana kiranta Mamah bata wuce shekara da wata biyu ba, Jannah da Rayyan ɗinta da yake ma wurin shekara uku da wani cikin a jikinta, Saleem da Aisha da suke riƙe da wani Rayyan ɗin dan wata huɗu kacal, Sameera na tura ciki ga Ummu sulaimi da tayi wayo sossai gefen ta Sulaiman, ga Samha Amarya wacce bikin ta ne next suke ta planning don abin bai zo da wuri ba, sossai take murmushi tana kallonsu yayyenta ne, Ƙawayenta ne kuma 'yan uwanta ne... Hawaye taji ma tana ji a daidai sadda su Suhail su uku cikin shiga iri daya na kananun kaya suka zo suka rungume ta.
"Congratulations Ammah"
Ta ɗaga Arham ta na dariya sossai take cewa
"Thank you love, na gode sossai"
Rayyan ya matso yana dauke mata hawayen farin cikin da take, nan suka isa parlor abincicikka da cakes iri daban daban an ci an sha an yi hira kaman ba gobe, Rayyan dai baya cewa komai sai murmushi dama sun riga sun san hali Afeefah ce mai shan maganarshi idan ta ciyo shi.
Sai dare suka watse ta fito cikin shirin kananun ƙaya wani half gown purple da ya amshe ta ya fitar da duk wani sura na jikinta, parlorn su kaman ba shine dazu kaca kaca ba hadimai sun gyare tsaff an cika turarukan wuta, ɗakinshi ta nufa bayan ta duba yaran sun yi bacci yana yana operating Phone ɗin shi hankalinshi ya ɗan dauku a chan jikinshi ba riga, tana isa ta sa hannu ta zame wayan ya ɗago ta jefa wayan kan gado tana murmushi sai ya saki baki yana kallon rigar na jikinta da ya fito da full chest ɗinta daga sama, rabin cinyanta duk a waje gashinta a ɗaure wuri guda sai sheki yake tana ta zuba kamshi bakinta da ta sa wani lilac lip gloss sai sheki yake, hannu ya wara mata ta kuwa tafi a slow suka yi baya baya tana kwanciya nashe nashe akan jikinshi don babu inda ya taɓa katifa a nata jikin, da hannunta take wasa da kirjinshi idanunshi a lumshe ya ce
"Boɗɗi"
"uhmm Boɗɗin Boɗɗi"
Idanunshi da suke ta lumshe wa a mayen ƙaunarta ya buɗe don sunan ya mishi daaɗi 'kyakyawan mai kyau'
"I love the name"
"kai wani suna ne baka so?"
Yayi murmushi mai sauti
"Ai duk sunayen ne daga kin faɗa sai sun motsa zuciyar maza"
Tayi murmushi tana tuna lokacin da yake mata masifa in ta kirashi Saraki ta ce
"Shiyasa baka son na ce Ya Saraki?"
Ya ja iska kadan yana furta
"Aouchhh sunan ya fi taɓa ni but sincerely wani irin fusgata yake zuwa gareki in kika faɗa cikin wannan voice din naki mai daaɗi"
Tayi murmushi yana zame ribbon ɗinta ya cusa hannunshi cikin gashinta ya ce
"Faɗamin abu mai daaɗi"
"I love you"
Ya tsinci kanshi da lumshe ido yana jin kalmar straight to his heart.
"Faɗi wani"
"Ina sonka!"
Tayi maganan tana wasa da sajenshi cikin susa mai daaɗi.
"Sake faɗamin"
"wani waƙa Naji da ya dace da kai in rera maka?"
Gira ya ɗaga ta gyara kwanciyar ta akan jikinshi ta shiga mishi wakan
"ka sace zuciyata!
Kana kai mini gatah!
Mata nai musu rata..
Ka ce in je in hutaaa..
Ga mijina mai tsafta
Mai halin girma na sarauta
Zama da kai sam babu wahalta..!
Cikin mazaje ka cire tutaaa
Mai adalci da nagarta..!
Fushinka shi ke sa ni ɗimautaaa
Mai haƙuri shi ke dafa dutsseee!!"
Numfashi ya sauke muryarta wane sarewa haka ya buɗe idanunshi da suka mace a so yana kallonta a hankali yace
"hakane kam mai haƙuri shi ke dafa dutse, nima na cire tuta tunda na same ki"
Tayi dariya mai yanayi da giggle ya juya ta yana shunshunar wuyanta ta zura hannunta gashin shi tana ɗan kame jikinta tace
"Toh ai ban gama waƙar ba fa Boɗɗin Boɗɗi"
Ɗagowa yayi yayi pecking lips ɗinta chan ƙasa yace
"Toh ƙarasa Babylove"
"Kaine tsanina...maqabulina!!
Kai ne rabin raina... Makasudina!!
Kaine muradina.. Kai ne
Farin cikin raina... Kai ne
Al'amari babba... Kai ne
Abin da duk zan ma.. So ne
Murmushi in kai kyau neeee"
Ya kuwa doka murmushin yana rasa wani baiti ne ma ya fi daaɗi, bakinsu ya haɗe ya shiga aika mata zazzafar Kiss cikin kiss ɗin ya ɗan zame yace
"Nima ke ce farin cikin raina, ke ce muradina kuma ke ce rabin raina My Hayateee... Help me mu samu Mammin mu a daren nan"
Kaman jira kuwa ta sakalo wuyanshi tana mayar da Bakinta cikin nashi.
*BAYAN TSAWON LOKACI*
Afeefah ce ke saukowa jirgi hannayenta rike da wasu 'yan mata kyawawa biyu, bayanta Suhail ne da Suhaila da za su yi shekara shidda zuwa bakwai sai Arham da yake huɗu da 'yan kai bayansu wasu hadimai ne guda biyu da suke taimakonta da yaran har zuwa wani prado baƙi wuluk a jere motocin huɗu suka fice daga airport ɗin sai fadar Fombina wanda a yanzu Laamiɗo Sameer Muhammad Modibbo ne ke kan mulki, Ƙashin bayan matasan Fombina, jagoran al'umma kuma jarumin Afeefah uba ga Ciroma Arham da 'yan uwanshi Garkuwa Fulanin duk Nijeriya.
Isarsu tamfatsatsen sashen na Fulani Afeefah ana ta baza gaisuwa da ban girma tana amsawa cikin kulawa da kaunar al'ummar nasu kaman yadda suke masifar ƙaunarta, Ɗaya daga kyawawan yaran nan mace tace
"Ammah mun dawo mu je wurin Abbu? I Miss himmmm?"
Girgiza kai Afeefah tayi
"Abbu na cikin taro Alhan, ki bari anjima idan ya dawo sai ki ganshi ko Mammin Abbu?"
Ta ɗan tura lips
Ɗayar tace
"Ammah to mu je wurin Jadda?"
"Ku fara yin wanka Ahlam sai ku je na san ta yi missing surutunku"
Da gudu suka yi ɗakinsu daman yan mazan sun jima da wuce wa yanzu haka bai wuce sauri suke suyi wanka su tafi wurin Abeey ba dake ji da su.
Ɗakinsu ta wuce ita da mijinta don bai wani yarda da raba sashe ba tunda har yau bai yarda ya karbi auren wata ba duk kuwa da tallar da ake mishi tun kan Abeey yayi murabus ya bashi har yau, ya ce duk abinda zai nema ya samu a wurinta to na me zai sake aure? Me kuma zata bashi banda ta nemi daga mai hankali? Afeefah na iya kokarinta wurin ganin ta bashi Kulawa, soyayya da lokacinta bata aikin komai banda gidauniyarta kuma duk ba ita ke kula da komai ba sai in ya kama don haka tana da lokacinshi full kuma bai taba neman ta ta ƙi ba a koyaushe burin ta ta faranta mishi ko da har ranta bata so.
Tana zame kayanta ta ɗaura towel zata shiga wanka kawai taji an yi hugging ɗinta kamshinshi da numfashin shi ya sanar mata waye, fuskarta washe da murmushi tace
"Sarakina"
"Matar sarki, barka da dawowa ga masoyinki"
Ta waigo tana Shagwaɓe mishi
"Ba wani bayan ka gudu ka baro mu Abuja"
"Kin san ba da son raina bane hakan da a sona na ne da kowa ya tafi ya bar mu mu biyu a duniyar nan"
Dariya tayi
Yace
"Ya taron na ganku a Tv i hope komai ya tafi lafiya?"
"Alhamdulillah wannan kam ya ƙare saura na Lagos"
Girgiza kai yayi
"Babu inda za ki je, ki wakilta wata ko wani su je miki"
Karkata wuya tayi
"Har kaduna? Ka ga fa akwai sunan Ɗan Samha ga yaye ɗalibai da za'a yi a gidauniyarmu na Dutsen-wai karo na wurin bakwai akwai kuma taron buɗe wani a Anchau"
Girgiza kai yayi
"Ba zan juri nisa dake ba, wai har ma gidauniyar nan nawa za ki buɗe ne?"
Tayi dariya yana daukar ta chak suka nufi toilet don yayi mata wanka yana tambayarta Ammi da Mamminshi fa tace sun tafi sashen Jaddansu(Ammin)
Suka shige cikin bahon wanka suna cika juna da kauna, tana daga cikin matan manya da ake ji dasu saboda taimako, iya ado da shigar kamalarta, haƙuri da iya maganar ta don duk tayi magana a taro sai ya kwana biyu yana circulating platforms, karama ce mai halin girma kaman yadda mijinta yake ƙarami cikin sarakunan yankunan Arewa sai dai akwai zuciya da kwarjini, idan suna tafiya a tare za ka zaci ɗawisu ne yana baza ado gaban 'yar budurwar ɗawisunshi, komai ya wuce a rayuwar Afeefah da har in ta tuna baya sai dai tayi murmushi su kawu na chan Dutsen-wai har yau sai dai ta kai musu ziyara ta dawo. Dafa ita har Rayyan sun yi sadakatul jariya da sunan iyayenta da Mammi har basu san adadi ba.
Ta samu akallah gidauniya 10 da ake bata taimako daga masarautu zuwa gomnatin jaha har na tarayya sun san da zamanta, kasancewar gidauniyarta dake tallafawa mata da yara akan neman ilimi, sana'o'i da tsayuwa akan kafafunsu kuma dama babban burin ta kenan mutane su samu ilimi kuma suna samu daidai gwargwado Alhamdulillah.
ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!! ANAN NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFI NA HAIHUWA DA HANJI ABINDA MUKA RUBUTA DAIDAI ALLAH UBANGIJI YA BA MU LADA WANDA MUKA KUSKURE ALLAH UBANGIJI YA YAFE MANA.
HAKIKA TAFIYAR NAN NA DAGA CIKIN TAFIYAR DA YA MATUƘAR YI MIN DAAƊI BISA GOYON BAYANKU DA COMMENTS NAKU, BAKI BA ZAI FASALTA MUKU IRIN DAAƊIN DA NAJI BA DA KALAR SOYAYYAR DA KUKA NUNA MIN NA GODE NA GODE KWARAI DA GASKE.
HASSANA SALLAU(MAMAN MUNIFA): DOLE NA AMBACEKI DON KINA ƊAYA DAGA CIKIN WACCE TA BA NI GOYON BAYA A WANNAN TAFIYA ƊARI BISA ƊARI BAN TAƁA YIN PAGE DA BABU COMMENT NAKI BA NA GODE KWARAI ALLAH YA RAYA ZURI'A YA BAR ƘAUNA TSAKANIN KI DA ABBAN MUNIFA.
FATIMA A MUHAMMAD: SIRIKA KUMA AMINIYAR ANGO INA GODIYA DA GUDUMAWARKI KWARAI DA GASKE. ALLAH YA BAR ZUMUNCI YA NUNA MANA RANAR DA ZA MU ZO SHAGALI KADUNA.
SIS NANAHALIMA KWARAI NA GODE DA GUDUMAWARKI ALLAH YA BAR ZUMUNCI.
HANIFA MUHAMMAD GURIN: YAYATA KUMA AMINIYATA KAWAR CIN MUSHE NA. MY SHAYLAAA🤸♀️🤸♀️ MY RIDE OR DIE🥰🥰NA GODE DA TAKI GUDUMAWAR DA SHAWARWARI AKAN KO WANI PAGE DA ZAN RUBUTA.
SAFIYA GALADANCHI: ƘAWATA MATAR HAMMANMU FATAN ALKHAIRI ALLAH YA KAWO MANA KE KASAR FOMBINA💃💃
OUM AMEER: MASOYIYATA KWARAI NA GODE DA ƘARFAFA GWIWA ALLAH YA BAR ƘAUNA YA RAYA MANA SU AMEER YA KAWO WASU 'YAN UKU SAU UKU☺️
DA MA DUK WAENDA BAN KIRA SUNA BA NA GODE SOSSAI DA SOSSAI, TAKU HAR KULLUM
🖤GUREENJOH🖤
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 40 Chapter of 40