Zainabun ma sai da na gargaɗeta taurin kanta ya ja mata... Ni ma zaman da nayi da ita shekarun baya ban huta ba da neman kariya da yanzu babu wanda za ka tarar anan da duk ta lashe kurwowinmu"
Ya hayayyaƙo wa salim da baƙin ciki haɗe da wani irin takaicin su ke shirin kashewa, ita dai ban da kuka babu abin da take kaman ranta zai fita hannayenta duk biyu bisa kanta jikinta na wani irin rawa.
Ya godewa Allah da ba da Rayyan ya zo ba yau da kuwa yanzu wani zancen ake ba wannan ba, duk haƙurin salim sai da su kawu suka kai shi bango, ya kaɗa ya rawa a kan su karɓeta sai dai cin mutunci kawai suka karta musu da kalamai masu zafi suka ma fara yunkurin far musu da sunan haushin ta dama suke ji haka ya dauƙeta suka wuce suka bar garin gudun fitinar da zai iya kunno kai idan suka ci gaba da tsayuwa.
Shiru ne ya ratsa motar sama da awa guda sai tsula uban gudu yake ita kuma tana ta aikin kuka.
"Afeefah ya isa haka don girman Allah ki yi haƙuri, ki karɓi wannan ma a jarabawa. Akwai inda zan kai ki kuma?"
Yayi maganan yana kallonta, ɗago ido tayi ta kalleshi sai da ya ji wani yarrr a jikinshi ganin yadda idanunta suka koma tsabar kuka, ɗauke kai yayi har ƙasan Ranshi yana jin ɗacin da bai sani ba baƙin cikin su kawu ne ko menene oho.
"Ba Za ka tambayi wacece ni ba? Ba ka ji kana son sanin ni ɗin Mayyar ce da gaske ko akasin hakan ba? Ba ka ji kana tsoro da shakkar taimakona ba?"
Ta faɗa cikin dasasshiyar muryarta har lokacin idanunta na a kanshi.
Ya samu wuri yayi parking kan ya waigo gabaɗaya yana kallonta
"Ki gane wani abu Afeefah, Na riga na saka a raina taimakon ki ya zama min dole. Batun sanin ko ke wacece ba zan ce miki bana son ji ba amma ba na son tilasta ki ba ni labarinki, idan muna tare watarana zan sani. Ba na tsoron ki don ke ɗin ba Abar tsoron ba ce ba kuma na Fatan yin da na sanin taimakon ki"
Yana kallon cikin idanunta ya ƙarasa maganar, zuciyarta ne ya sake karyewa hawayen da suka tsagaita sai suka fara shirin dawowa sabo, kaman da wasa ta shiga sanar mishi da tarihin rayuwarta daki-daki tun daga farko har kawo ranar da ta sha guba don ta kashe kanta. Numfashi ta ja sam bata duba yanayin shi ba ta cigaba da cewa
"Na gode kwarai da taimakon ka da kuma yarda da ni da kayi ba tare da ka san ni din wacece ba, ba na so in sake ɗora maka wani nauyi ko damuwa ba kuma na son wani abu ya same ka ta dalilina. Za ka iya ajiye ni anan kawai ka bar ni ka koma gida Na gode sossai..."
Idanunshi da suka sauya sossai suka cika da tarin kwallar tsananin tausayinta da rauni ya ɗauke bisa kanta yana lumshe su da ƙarfi, ya rasa ma kalar tunanin da zai yi wani irin tausayinta ke bin gaɓoɓin jikinshi yana kassara su, ji yake kaman ya taya ta kukan ta ɗauki abubuwa dayawa fiye da shekarunta, tabbas dole tayi yunkurin kashe kanta don duniyar bata dandana mata daaɗi ba sai akasin hakan, hakika ya yabawa hakurin ta da tarin juriyarta da wani ne ko guba bai kashe shi ba damuwa sai yayi bindiga da zuciyarshi.
Sama da mintuna uku ta sauƙe numfashi ta sa hannu ta buɗe kofan tana shirin sauƙa ta ji ya kira sunanta
"Afeefah!"
Waigowa tayi tana kallonshi, ya rankwafa ya janyo murfin da ta buɗe ya rufe kirib kan ya kalleta
"Ba zan iya barin ki anan ba Afeefah! In na ce ma ki sauƙa anan za ki yarda?"
Ta Yi shiru ya sauƙe numfashi kan ya ta da motar yana mayar da idanunshi bisa titi ya shiga ja a hankali.
"Sunana Salim Mahmud ni haifaffen nan jahar ne na Kaduna, ni ne ɗa na farko a wurin iyayena kuma namiji tilo ina da ƙanne mata uku Sadiqa ke bi na Dukda akwai tazarar shekaru masu dama tsakanin mu sai Sameerah kan Auta Samha dukkansu suna jami'a ne presently. Tun Samha na da shekaru uku a duniya muka rasa mahaifin mu ya saura daga mu sai mommy, dangin mahaifin mu suka watsar da al'amurranmu duk da kasancewar mahaifina mai karamin ƙarfi bai tara mai yawa ba, kuma duk yawan da zai tara akwai hidimomi gabanmu ya sa tun ba a je ko ina ba komai ya ƙare, mahaifiyar mu ta matukar shan wahala da mu kuma ta yi ɗawainiya mai yawa da ba don tayi karatu ba ma da bamu san halin da muke ciki ba a yanzu, bata huta ba sai da ta ga ta kafa ni ta yadda zan iya taimakon ƙanne na. Mahaifiyar mu macece mai tausayi sai dai duniya kuma ta koya mata son nata don bata haɗa soyayyar yaranta da kowa ba.
Ban sani ba ko za ki iya zama cikinmu idan kin amince zan je na roƙe ta, zan bata labarinki za ta ji tauaayinki kuma in shaa Allah za ta haɗa ki da su Samha ta rungume mu cigaba da rayuwa har Allah ya kawo miki miji ki yi aure".
Kuka take mishi mai sanyi, ashe har tana da zaɓi a yadda taken nan? Har sai ta ce ta amince zata zauna da su ko da naman jikinta za su dinga yankewa da tayi bulayi a titi? Kalaman godiya tayi ta jera mishi yana hana ta don gabaɗaya rauni da tausayinta sun sassara mishi gaɓoɓi da yake jin zai iya joining ɗinta su yi kuka tare.
Yamma sossai suka dawo cikin Kaduna, daga ita har shi babu mai magana idanunta zube a titi, masu hidimar komawa gida kawai take kallo Dukda zuciyarta ya jima cikin nashi duniyar, kwakwalwanta ya zurfafa a tunanin wani irin ƙaddara ne kuma ya dawo da ita cikin Kaduna? Shin za su amshe ta bayan sun ji labarinta ko za su kore ta? Idan suka kore ta ina ta nufa? Akwai mai sake mutuwa sanadiyar ta? Anya ta yi mishi adalci da ta biyo shi? Har suka isa cikin Unguwar rimi bata sani ba, jin ƙarar horn na mota ya sa ta ɗan yi firgigit ta dawo da hankalinta kan inda suke sai ta tsince su a wani layi mai jerin rukunin gidaje iri ɗaya.
Gidaje ne masu kala ɗaya kusan komai na gidajen Layin iri ɗaya ne bambancin kawai lambobin da ke maƙale gefen kyauren ko wani gida, Baƙin gate ɗin aka zuge wani matashi ya shiga yiwa salim ɗin barka da dawowa hakora a washe, Salim ya tsaya suka gaisa kan ya nausa cikin tsararren madaidaicin gidan da ya tafi da imaninta, harabar shimfide da interlocks an ƙawata gidan da shukoki jajaye, shudi, kore da ma wasu kalolin ma su ban sha'awa. Ginin da kaman an zana ne ba a gine yake ba saboda yadda yayi mata kyau gidan sama ne, harabar gidan shiru babu kowa har ya shigar da motar cikin ma'ajiyarta tsakanin wasu motoci madaidaita guda biyu. Hamdala yayi yana zare keyn ya dube ta
"Mu je ko?"
Babu musu ta gyaɗa kai ta buɗe kofan ta sauƙa, shi ya buɗe bayan da ya fito ya zaro ledar da 'yan kayanta ke ciki suka nufi cikin gidan yana gaba tana biye da shi a sanyaye, a gaban mashigar gidan suka dakata ya danna doorbell, babu jimawa aka buɗe Brown security door ɗin wata kyakyawar yarinya da za ta iya girme mata ta gani tsaye, haɗa idanu da suka yi da Salim ya sa ta saki ƙarar murna kan ta sauƙo da gudunta ta faɗa mishi tana dariya sossai shima yana murmushi ya tarbeta ya ɗan yi hugging ɗinta kaɗan ya sake ta
"Welcome home bro"
"thanks Autar Hajiya mommy"
Ta saki murmushi tare da jan hannunshi suka yi ciki tana ihun sanar da isowarshi, hakan ya sa wasu 'yan mata biyu suka fito su ma a guje suna mishi maraba, yanayin kamanninsu ya sa ta tabbatar da su ne ƙannenshi da ya bata labari, murmushi take saki don sun matuƙar burgeta har tana jin ina ma da ba ita kaɗai aka haifa ba, ita kam ba ta da wannan gatan Allah bai ba ta ba bata gama tunanin ta da murmushi ba ta ga Fitowar wata dattijuwar mace da suke matukar kama, fuskarta cike da fara'a har hakwaranta biyu na hajji na bayyanuwa, doguwa ce kaman su salim da suke dogaye, haka ba ta da wani ƙiba don idan ba a yanayin fuska da ya bayyana girma ba ba za ka ce ta haife su ba.
Ganinta ya sa salim ya ture ƙannenshi ya isa yayi hugging nata
"Oyoyo Mommyna"
"Welcome home my son, idonka kenan?"
Ya sake ta yana ɗan shafa kai, ta saki murmushi ta san ya kan shigo cikin Kaduna amma sungulollinshi ba ko yaushe yake bari ya ƙaraso gida ba, kusan satin shi uku zuwa huɗu rabon shi da su sai a waya.
"Wannan kuma wacece yaya? A ina ka samo ta?"
Samha da tun bayan gama murnar su ta ƙure Afeefar kur da idanu tayi tambayar.
"Samha Afeefah sunanta, ki kaita ɗakin ki ta yi sallah ki ba ta abinci idan na sauƙo bayan isha za mu yi magana"
Babu wanda ya sake tankawa a cikin su har ya haye sama inda nan ne sashen shi, ta duƙa ta shiga gaishe su ɗaya bayan ɗaya sai ƙare mata kallo suke suka amsa ba yabo ba fallasa.
"Mu je"
Samha ta furta mata, ledan ta da samhar salim ya ajiyewa ta ɗauka mata ta nuna mata, babu musu ta sa hannu ta ɗauka ta bi bayanta. Bayi ta nuna mata ta shige a lokacin har an fara kiraye kirayen Sallar Magrib, Allah ma ya sa ta zauna da Aunty zee da take da 'yan abubuwan zamani Dukda bai kai na gidan ba amma ta iya ta buɗe tayi alwala ta fito. Samhar na zaune bakin gado tana latsa waya ganin Fitowar ta ya sa ta nuna mata gabas ba tare da ta bata sallaya ko ta motsa daga inda take zaune ba, sai da Afeefar ta shimfide dankwalinta a saman tiles ɗin kan Samha ta miƙe ta shige bayin. Afeefah na sallah ta ji samhar na wanke bayin ko da ta idar samhar ta fito ta shimfida sallaya daga chan nesa ta tada Sallar ta, ko motsi Afeefah bata yi ba tana ta Adu'a da roƙon Allah a kan wannan rayuwa da za ta yi a wannan gida, har aka kira isha kan ta miƙe ta gabatar Adu'a ta cigaba da yi a kan kar Allah ya kawo ajalin wani tana cikin gidan, tun bayan Magrib Samha ta fice daga ɗakin bata wani jima da idar da Sallar ba tana zaune kawai sai ga samhar ta turo kofa ta shigo.
Plate na shinkafa jollof ne ta ajiye mata da wani karami mai dauke da ruwan leda guda biyu.
"Na gode"
Ta faɗa, kai kawai ta gyaɗa ba tare da ta buɗi baki ta amsa ba ta sake ficewa.
A chan parlor kuwa bayan salim ya shigo daga Sallar isha suka ajiye mishi nashi tray ɗin dake ɗauke da plate na shinkafar da wani an yi wrapping salad da wani saucer mai ɗauke da pepper chicken da ke fidda kamshi haɗe da zobo jug guda. Bismillah yayi ya shiga ci a natse don ya tara yunwa sossai a cikin nashi, sai da ya gama yayi hamdala hajiyar su da tuntuni idanunta ke kanshi ta ce
"Salim yarinyar chan da ka shigo da ita daga ina haka? Meyasa take a waje har bayan Magrib ba za'a nemeta a gida ba?"
Ya ɗan gyara zaman shi
"Wallahi Mommy yarinyar ce rayuwarta abin tausayi, na rasa me yasa mutanen mu suke haka a wannan rayuwa ashe don ajalin bawa yayi ya amsa ƙira sai ya zama lallai lallai wani ɗan uwansa mutum ne ya kashe shi? Duk mun manta cewa idan ajali ya zo babu mai jinkirta wa ko da da second guda ne sai ya tafi?"
Hajiyar ta gyara zama tana katse mishi hanzari
"Hakane idan har mutum ya mutu ajalin shi ne ya riga yayi amma a komai akwai sanadi"
Ya ɗan yi jimmm yana kallonta for seconds kan ya shiga magana
"Mommy Afeefah Marainiya ce! Mahaifinta ya rasu tun tana ciki, mahaifiyarta ta rasu wurin haihuwar ta...."
A hankali ya cigaba da ba su labarin Afeefah kaman zai zub da ƙwallah har kawo yanzu, yana sauke aya Samha ta miƙe hannunta duk biyu dafe da ƙirji idanu waje ta ce
"Mayya Yaya Salim???"
🖤Gureenjoh🖤
https://chat.whatsapp.com/Ef0BFnE69VjAhuWCV9Fxbe?mode=ems_copy_t
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Kun ga comments? To ku dage da comments za ku sha mamaki amma idan bakwa yi haka nima zan ke shantakewa. A takaice dai ina roƙon ku da ku ba ni haɗin kai mu ga mun gama labarin nan cikin watan nan don kowa ya sanni ya san ba na Littafi mai tsawo*
*011*
Wani irin kallo ya watsawa Samha da ya sa ta koma ta zauna sai kuma ta fara hawaye, juyawa yayi ya kalli hajiyarsu da tunanin za ta yi mata faɗa sai ya ga ma kallon shi take da expression na mamaki a fuskanta.
"Mayya fa ka ce Salim? Shi ne za ka tura ta ɗakin autana ta fara da ita? Me ya hau kanka da za ka kawo mana cutarwa gida after all faɗi tashi da muka sha don mu ga mun inganta rayuwar mu?"
Kasake yayi yana cigaba da kallon mahaifiyar tashi bai taɓa tunanin zai fuskanci wani matsala daga Mommy ba, ya zaci ta san zafin ɗa kuma ɗan wani ma zai iya zama nata musamman idan ta ji cewa Marainiya ce don ta fi kowa danɗanar wahalar da maraici ke janyowa.
"Mommy na ɗauka Afeefah Abar tausayi ce da muddin na ba ki labarinta za ki karɓeta hannu bibbiyu, ki rungumeta tamkar su Samha wallahi mu ma Allah zai dube mu ya ba mu ladar kula da ita"
"Dakata Saleem! Dakata min don Allah! Ka kawo yarinya kana ikirarin danginta sun guje ta saboda Mayya ce da tun tana ciki take cin maita ta ci har uwar da ta haife ta da ubanta ka kuma yi expecting in karɓeta? Ta cinye min ku kenan? Ko ni kake so ta cinye maka? To ba da ni ba salim... Ba a gidan nan ba maza maza tun dare bai ba tarkatata ka mayar da ita inda ka ɗauko ta tun muna shaida juna je ka fitar min da yarinyar nan a gida ba za mu taɓa shiryawa ba..."
Hankali tashe ya ɗan kalli kofar ɗakin Samha kar Afeefahn ta ji ya matso ya riƙe hannun mommyn.
"Mommy wallahi ba gaskiya ba ne duk fa zargi ne da Ƙazafi irin na mutanen duniya, wallahi Afeefah is innocent mommy ki tausayawa rayuwarta don Allah. Mu ma fa marayu ne ki saka ta a sawun su Samha idan da ɗaya daga cikinmu ne ake yiwa wannan kazafi za ki iya jura? Za k...."
A hasale ta katse shi
"Na rantse da Allah zan tsinka maka mari salim ka sake alaƙanta yarana da wanchan Abar, eh ku marayu ne amma da ba ku ci naman kowa ba uban wa yayi muku Ƙazafi? Bari ka ji ba'a taɓa yaɗa jita-jitar da bashi da kamshin gaskiya ba. Kafin na hasala na haɗa da kai ka je ka fitar min da yarinyar nan a gida..."
Samha da har lokacin take hawaye tace
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun ni dai mommy wallahi ba zan iya sake shiga ɗaki na ba"
Sadiqa tace
"Ni dama daga ganinta na ji har ga Allah bata kwanta min ba, sai nuƙu-nuƙu take ashe babu gaskiya a lamarin ta"
Sameera ta yi kwafa
"Nan ma ba ki ga idanunta bane, duk abin tso..."
"Kun yi min shiru ko sai na sassaɓa muku? Da ku nake magana ne? Ko na kira sunan dayanku anan? Kun ga kun yi kama da waenda zan nemi izininku kafin aiwatar da abin da yake daidai? Duk cikinku akwai wacce ta isa ta hanata zama a gidan nan ne?"
Ya daka musu tsawa Ranshi ya kai ƙololuwar ɓaci duk mommy ce ta ba su wannan ƙofa amma ya zai yi?
Gaban mommyn ya koma ya kama hannunta idanunshi kaman garwashi don saura kiris ya fara yi mata kuka a yadda yake jin zuciyarshi ya ce
"Don girman Allah mommy kar ki koreta, ba zan iya bari ta tafi ba mommy in ta fita a gidan nan ina za ta je? Musulma ce fa 'yar uwarmu kuma mace, ko don aikina na kare lafiyar al'umma mommy ba zan iya tura Afeefah waje ba, Don Allah mommy ba don ni ba ki sake nazari akan hukuncin ki kar ki saka ni yin abin da zai yi hunting ɗina for life please mommy"
Ganin zai kai gwiwar shi ƙasa yana cigaba da roƙon ta ya sa ta riƙe hannunshi suka koma zaune, wuri guda ta tsurawa idanu sama da mintuna biyu ta sake kallonshi duk ya marairaice yana roƙonta, Salim a yaranta yana da haƙuri yana kuma da kawaici don da wuya ya roƙe ta abu ko ya tambayeta ko da kuwa yana matuƙar bukata ko da kuwa buƙatar kuɗi ne, yana tausayinta ƙwarai gani yake har yanzu bata huta da ɗawainiya ba alhali, gidan gadon su ma 'yan haya ne ciki bai san ya suke kashe kudin ba a haka shi yake daukar ɗawainiyar karatun ƙannenshi da cin su, tufafin su da ma sauran hidima na rashin lafiya bai taɓa gazawa ba tun da ya riƙe ƙasa to Meyasa za ta kasa yi mishi wannan alfarma guda? Amma kuma idan yarinyar ta kashe mata shi fa? Numfashi mai matuƙar nauyi ta sauƙe ta ji ana cewa Mayu sun fi cinye kurwan wanda ya taimaka musu ya ji tausayinsu kenan muddin yarinyar za ta zauna gidan sai ta cire wa salim tausayinta? Amma ta yaya?
Ta sake jan ajiyar zuciya cikin gamsuwa da shawarar zuciyarta
"Shikenan Salim na amince ta zauna amma fa ina da sharuɗɗa, sharrudan da zan gindaya maka wanda matuƙar ka tsallake Allah ya isa ban yafe maka ba"
A firgice yake kallonta, zuciyarshi kaman zai fito waje jikinshi har yana wani rawa don ba ya wasa da Abin da ya shafe ta, me yayi zafi da Allah ya isa? Da kyar ya iya buɗe bakinshi da yayi masa nauyi ya furta
"Allah ya isa mommy? Ni??"
Ta gyaɗa kai cikin alamun tabbatarwa tana kawar da idanunta daga kallonshi kar ma ya bata tausayi kuma ta san muddin ya amince ba zai taɓa tsallakewa umarnin ta ba.
"Sharuɗɗan su ne babu ruwanka da abin da ya shafe ta, za ta zauna zan bata abinci sau uku kaman kowa, za ta yi aikin da ya kamata a ce kowacce mace na yi saidai duk wani abu da ka ga na yanke a kanta babu ruwanka, do not question me a kan duk abin da ya shafe ta i repeat! Magana ta fatar baki tsakanin ku in har ya wuce minti ɗaya ban yafe maka ba, ni zan duba in ga cancantar saka ta makaranta ko akasin hakan idan zaman ba na ɗore bane dole za ta bar gidannan ka kuma yanke kowace alaqa tsakanin ku, ko da ko sannu ne"
Ya yi jimmm kanshi ƙasa duk ya damu kan ya sauƙe numfashi
"Shikenan mommy in shaa Allahu zan kiyaye umarnin ki"
Yana kai nan ya miƙe ya bar musu parlorn Ranshi na ƙuna, da yana da mata babu abin da zai hana shi riƙe Afeefah tamkar 'yar sarki ya ba ta ingantacciyar rayuwa, a yanzu ma bai fidda tsammani ba ya amincewa mommy ne da tunanin with time za ta sassauto daga kudurinta.
Tuni suka cika parlorn da hayaniya bayan barin shi suna uzzurawa mommyn akan me yasa ta amince da zaman yarinyar gidan?
"ku yi shiru ku bar ni da shi, ai in bata ga wurin zama ba da kanta za ta fitar da kanta daga gidan ba sai wani ya kore ta ba."
Ta miƙe ta nufi ɗakin Samha tana jin abin da zuciyarta ke gayamata daidai ne, duk suka rufa mata baya wane sarauniya da fadawarta.
Suka sameta zaune inda take tun bayan idar da Sallar ta idanunta suna zube a farantin abincin da ko loma uku bata yi ba saboda tunani da ya ci karfin kwakwalwanta, tsoro ne sossai da fargaba suka danne yunwar da take ji don rabonta da abinci tun da suka karya da Baaba da safen a asibiti.
"Ya ma Sunanki?"
Mommyn ta tambaya tana sake ƙare mata kallo.
"Afeefah" ta amsa a hankali.
"Ban san wani kalar tsafin kika yi wa Saleem ba da har karo na farko ya zaɓi bijirewa umarni na a kanki, amma bari mu ga ko ke kin san hallaci? Zan ja miki federal warning akan yarana don ni karan kaina ban san abin da zan iya aikatawa ba a kansu, hawainiyarki ta kiyayi ramata idan kina cin ƙasa to fa ki kiyayi na shuri wallahi ko da wasa 'ya'ya na suka yi ko da ciwon kai ne hmmmm"
Ta kara hmm ɗin da wani irin siga na razanarwa,
"ana magana ba za ki amsa ba?"
Sadiqa tayi maganan tana hankada ta da kafar ta
A ɗan razane ta gyaɗa kai.
"Tashi in kai ki inda za ki zauna, ki ɗauki farantin nan don daga yau a ciki za'a na baki abinci har Allah ya raba mu da ke, kuma ba ki isa a saka miki abinci ki bar mana ba don a nan ba ma almubazzaranci da gumi muke nema don haka dole duk abin da aka saka miki haka za ki cinye. Shara, mopping da wanke-wanke su ne aikinki. Am I clear?"
Sameera tace
"Kai mommy ke ma ina wannan ina jin turanci? aka ce kin fahimta?"
"Eh na fahimta"
Ta amsa cikin rawar murya.
"Tashi mana ni ki bar min ɗaki, ko za mu tsaya muna jiran ki ne?"
Dole ta miƙe da sauri ta ɗauki kayanta da plates ɗin ta bi bayansu, ta kofan baya suka fita suka miƙa har Boys quaters jin hayaniya da hira haɗe da dariya kuma Muryar maza ya sa ta sake tsorata, isan su varender ɗin Hajiya ta shiga buga cikin aihinin main building ɗin ɗaya daga cikin su ne ya leƙo ganinta ya sa ya koma da gudu ya ƙira sauran suka fito su uku. Ba manya bane chan matasa ne duka masu jini a jika da fafutukar neman halal, Ishaq shi ne ke musu wanki da guga sai iliya da shi ne driver sai mudi mai gadi, ganin duk maza ya sake tsorata Afeefah me hajiyar take nufi? A sama ta ji muryarta tana cewa
"ke! Ga ɗakin ki nan"
Tq nuna mata wani single room dake kan varender ɗin. Da gaske a waennan garadan za ta haɗa ta, ganin yadda suke kallonta kaman kura ya ga nama ya sa hawaye ɓalle mata a take tana ji hajiyar na cewa
"Mudi wannan itace mai wanke-wanke da share share za ta zauna a ɗakin nan kar in ji kar in gani"
"To! To hajjaju in shaa Allah za mu kiyaye"
Suka juya suka tafi suka barta nan tsaye kyam.
"Sannu kyakyawa"
Bata tanka ba sai shige wa ɗakin da aka kira da nata da tayi da gudu ta datse kofan tare da zamewa a jikin kofan tana fashewa da kuka sossai.
Dariya suka sheke da shi don tayi mugun basu dariya suna shiga ɗaki kuma suka fara gulman kyaunta, kaman daga sama suka ga an turo kofa da ƙarfin gaske duk razana suka yi sai kuma a take suka wani irin zubewa ƙasan ganin Saleem riƙe da bindiga muraran, fuskan nan yayi Red babu wanda zai iya cewa ya taɓa ganinshi cikin wannan yanayin a take jikinsu ya tsume cikinsu ya shiga ba da ƙarar tsoro suna tunanin me suka yi?
Iliya ke ta maimaita
"Yau mun shiga uku mun lalace allurar ce wallahi ta tashi a kanmu ya Allah ga mu gareka.."
Kuuuuu haka kowa cikinshi ke ba da sauti ganin ya sake haɗe fuskan nan tamau, ya samu hannun kujera ya zauna tare da ɗora kafan shi daya kan kujerar ya sa bindigar ya ɗan sosa goshinshi yadda za su sake gani da kyau su tabbatar, ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 40