Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
hope a kan samunta alhali mahaifiyarshi bata ɗaura wannan damara ba na mallaka wa yaron nata cikar burin shi hakan ya sa ya ɓoye mishi wanzuwar Afeefar a gidansu. Su Samha ko da suka zo sun ƙaraci zamansu ko ci kanku bai ce musu ba sun gaishe shi ma bai amsa ba, wani irin zafin su yake ji a lokaci ɗaya yana mamaki bai taɓa sanin inhumanity ɗinsu ya kai haka ba, suka gaji suka tafi. **** Washegari Da misalin karfe bakwai na safe Sulaiman ya fito shirye cikin manyan kaya, sallama yayi wa umma tana ta adu'ar dacewa Baba Jummai ma Adu'a tayi ta mishi har ya fice. Gidan Yaya Zubairu ya fara zuwa ya ɗauke shi kan ya wuce gidan babban Yayansu Abban Yaya Ummaru, dattijai ne masu mutunci da kamala kuma duk suna da dukiyar su daidai gwargwadon. Anan suka kama hanyar kauyen su Afeefah yana ta Adu'a da Fatan ya same ta chan Dukda bai yi ma tunanin rashin samunta ba don ina zata koma in ba gida ba? Tafiyan awanni kadan ya kawo su kauyen yana jin hirarsu Yaya Zubairu da suke zaune a baya, sai da suka ɗan shiga cikin garin kan ya ɗan tsaya jikin wani shago matasa ne zaune su wurin huɗu ya sauƙe glass "Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka" "Barka dai Alhaji" "Don Allah tambaya nake yi" "To Allah ya sa mun sani" "Gidan su Afeefah kamal" Tsittt suka ɗan yi wannan ya kalli wanchan wanchan ya kalli wanchan.. "Kai ko me zaka yi gidan su Mayyar yarinyar nan? Ai Annoba za ka ce sai mun fi gane ta" "Annoba" Ya maimaita sunan, abin da ta faɗa mishi kenan me yasa ake ce mata annoba? Dan kallon su Yaya Zubairu yayi duk fuskar su ya ɗan nuna mamaki. "Gidansu nake nema" Ya faɗa ba tare da ya ji daaɗin furucin su a kanta ba. "Ka ga kara gaba sai ka tambaya a chan, ba mu san ko laifi ta muku ba kun zo yi wa kawunta tijara abu ya shafe mu lalala bamu shirya rigimar Labaran ba" Babu wanda ya tanka a cikinsu har ya ja motan suka yi gaba, wasu yara 'yan daidai ya samu ya kira su su biyu "Gidan su Afeefah kamal nake nema" Ɗayan ya ɗan kalli ɗayan "Mayyar nan fa suke nema ta gidan su Auwalu" Ɗayan ya zaro ido "Wacce ta cinye Amadun gidan malam yahaya ta gudu duniya?" "Eh ita ce..." Sai ɗayan ya gyaɗa kai ya juya ga Sulaiman da kanshi ya sake mugun ɗaurewa. "Idan kayi gaba ka ɗauki Layin hagu gida na biyu in baka gane ba ka ce gidan su Annoba kake nema ajalin duk wanda ya raɓeki" Suna kai nan suka gudu. "Sulaimanu a wani irin gida ka nemo aure? Wace irin yarinya ce wannan bata da shaida mai kyau?" Shiru yayi shima amsar yake nema don kwata kwata ya kasa fahimtar komai. Gaba yayi don clearing doubt ya sake tambayar wata mata a yanzu annobar shima ya faɗa yana runtse ido aiko ta nuna mishi, Da gaske ne ko wasa? Ya kasa ba kanshi amsa, kaman mafarki yake kaman kuma duniyar halluscination ya shiga don abin ya fi yanayi da almara, wacece Afeefah? Tarin mutane da suka gani kofar gidan kawu ne ya ɗan basu mamaki, bayan yayi parking suka fito su uku suka tsaya suna kallon abin mamaki, dambe ake ci da Kawu da inna larai har kofar gida duk ana tsatsaye ana kallonsu don su in suna yi ba'a raba su in ma ka shiga karshe kai za ka ji kunya, kuma ba karamin dukan ta yake ba, Bakinta ya ƙi shiru duk yaransu na zagaye suna kwasar kallo. "Wani irin tsantsar jahilci ne wannan? Sulaiman a nan gidan ka ɗauko aure? Anya da hankalinka?" Kawu Zubairu yayi maganan kaman ya rusa kuka. Kawu Ummaru ne ya je ya janye kawu Labaran daga riƙon da yayiwa larai ya ce "Haba malam baka san wannan abin da kake yin ya saɓa shari'a ba? Musulmi ne fa kai sannan mutum ba dabba ba wannan ai ɗabi'ar dabbobi ne, ba matarka bace ta sunna?" "Kyale shi ai ni wandon roba nake daidai da kugun kowa, wlh ba zan yi wahala in nemi kudina Labaran ya dinga bin dare yana sace min ba shi ba ciyar da mu yayi ba kuma muyi wahala mu samu ya zama ɓera, Toh ni ba Asabe bace da ka gama kassarata ta koma cima zaune babu abin da take ba, kuma wallahi sai ka biyani kudina" "Ni kike cewa ɓarawo? Yau sai na ci ubanki Larai sai na zubar da hakwaran rashin da'ar nan Malam Sallau shi zai raba mu" Babanta yake nufi, ganin za su cigaba da rigimar su kawu Ummaru ya ja shi gefe. "Ashe baka san Annabi yayi mana hani da dukan matan mu ba? Yanzu kai ba abin kunya bane yaranka gode-gode suna tsaye suna kallon ku ba? Dambe har kan layi? Subhallah" Kwarjini mutumin ya mishi da sai ya yanko mishi magana amma sai ya Buge da cewa "Waye kai? Me kake so? In baka da abin faɗa zan kama gabana don ina da abin yi" Girgiza kai Kawu Zubairu yake Sulaiman kam ya mayar da kanshi kasa yana jin yadda zuciyarshi ke cigaba da tsitstsinkewa don tabbas da matukar wuya Su kawu su bari su yi surkuntaka da mutum irin kawu, yanzu wannan baban Afeefah ne? Innalillahi wainna ilaihi rajiun ya maimaita ya kai sau biyar. "Sunana Umaru Malami zuwan namu ya shafi 'yar wurin ka Afeefah" Zaro ido kawu yayi "Ba dai a yawon tambaɗarta ba ne ta kashe muku wani kuka zo nemanta? Ni fa na jima da yanke alaqa da yarinyar chan ba zai yiwu a dinga zuwa ana ɗaga min hankali akan kashe-kashe da take ba" "kashe-kashe?" Kawu Zubairu ya maimaita "Wai baku sani ba? Ai rikakkiyar Mayya ce da ta addabi al'ummar garin nan a ƙarshe korinta muka yi ta shiga duniya" Jiri ne ya kwashi Sulaiman yayi baya baya ya dafa mota, zuciyarshi na harbawa da karfin gaske tuni idanunshi suka sauya, kwalwarshi ya nemi tsayawa da aiki amma sai ya tuna farkon abin da ya kawo Afeefah asibitin su ta sha poison ne don ta kashe kanta! Afeefah tana da tarin damuwa da yake haddasawa jininta sauƙa sossai zuciyarta kuma na ta kokarin samun matsala, me kenan? Menene ke kunshe a rayuwarta haka? Duk ya rikice amsa yake buƙata sai dai ba daga bakin wannan kaskantaccen mutumin da ya kira kanshi kawunta ba. "Toh mun gode ko, sai anjima" Juyawa kawu yayi ya kada rigar shi yayi gaba. "Sulaiman wannan ƙasƙanci har ina? Yanzu inda ka zabi neman aure kenan? Toh ba'a zuriyar Malami ba" Kawu Zubairu ya faɗa yana bude mota ya shiga, kawu Ummaru ma ya shiga Sulaiman da kyar yayi composing kanshi ya zagaya ya shiga ya tada motar a hankali yace "Don Allah ku yi haƙuri kawu ku yi min uzuri, wallahi Afeefah ba haka take ba ita nake so ba kawu..." "Sulaiman ko Afeefah ta fi kowa musulunci a duniya ba za mu nema maka aurenta ba, ba za.mu taɓa hada zuri'a da irin mutanen nan ba, ban damu don an ce mata Mayya ba duba da irin kauyen da tarin jahilci ya musu yawa amma a yadda ta shiga duniya danginta suka watsar da ita har suke ikikarin yanke duk alaqa da ita, da kuma yadda muka sami wannan gida ba gidan aure bane, kana da tarin mata masu nasaba da asali cikakku waenda suke gaban iyayensu zaune don haka ka tabbatar baka kara tado zancen wata Afeefah ba, a yau ka fara dubawa cikin sauran yaran da iyayensu suke maka tayin auren su za'a hada aurenka da Munir" Kawu Ummaru yayi maganan. Muryar shi na rawa ya ce "Amma ka..w..." 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh *FREE BOOK* *Ina so na yi addressing wani issue, na yi kokari in share in yi kaman ba komai amma dai na kasa, wato muna zuwa wani mataki da za'a iya fara cewa Gureenjoh na wulakanci ban damu ba saboda Allah ya gani ba wulakancin nayi ba, babu yadda za'a yi na fara littafi na yi nisa ki zo ki ce in tura miki na amsa na kuma tura miki zuwa inda na tsaya, muna groups dayawa dake da nake posting a maimakon ki cigaba da tarawa ko ki cigaba da bi baki yi hakan ba bayan kwana biyu na sake yin nisa ki sake dawowa ki ce in kara tura miki daga inda na tura miki last zuwa inda na tsaya wallahi ba zai yiwu ba, ba zaman banza nake ba wani lokacin ni na san yadda nake squizing time ɗina ina typing, wallahi ba zan tura ba idan za ki jira na gama na haɗa document na tura groups ki gani ki karanta fine, idan ba za ki karanta ba duka a wurina daidai ne* *jama'a kuyi haƙuri da Page nan guntu ne pls, idanuna rufewa su ke da kyar na kai inda na kai saboda gajiya da bacci* *021* "Sulaiman?? Har za ka ja da maganan Yaya a kan yarinyar? Aaa lallai, yo ko mahaifinka ya isa ya sauya maganan nan?" Kawu Zubairu ya katse shi a hasale. Shiru Sulaiman yayi sai dai idanunshi tamkar garwashi, zuciyarshi yake jin ya wani matse ya mishi nauyi wane dutse aka ɗora mai, kawai don kawu bai da hali sai a hana shi auren Afeefah? Me laifin ta? Ita me tayi? Har suka shigo Kaduna bashi da natsuwa, da kyar ya kai kowannensu gida suna ta kushe wannan neman auren nashi haka ya nufi gida ko da ya shigo a parlor ya samu Umma, ganin yanayinshi kaman zai faɗi ta miƙe da hanzari ta riƙe shi "Sulaiman! Menene? Lafiya kake kuwa? Ko wani abin ne ya samu Afeefar?" Girgiza kai Yayi yana neman inda zai zauna ta ja shi kujera suka zauna tare, Baaba jummai ma da tun safe take ta adu'ar dacewa ta fito, ruwa ta je ta ɗauko mishi Umma na tsaye kanshi tana ta tambayar shi duk ta rikice ta sanshi da masifar migrine in ya fara kuma baya jin magani, ruwan ya karɓa ya sha sossai tamkar zai fasa ihun kuka yace wa Umma "Umma wai su kawu ba za su nema min aurenta ba, wai ba za su hada zuri'a da ita ba, Umma idan kenan kawunka bashi da halin kirki sai aka ce kaima haka kake? Me Afeefah tayi na kin aurenta? Don Allah ki yiwa Abba magana ya samu Yayanshi zan nemi Afeefah! Zan neme ta duk inda take ni dai don Allah ya bar ni in aureta a haka nake son ta" Duk sun kasa gane inda ya dosa, Abba da shigowan shi kenan ya ce "Ba da Miyau na ba kam, sai dai kuma idan kai zaka nemawa kanka aure wannan kam zaka iya amma tunda har Yaya ya kirani ya tabbatar min gidan chan ba gidan neman aure bane ba zan taɓa sake tado maganar ba don na san ba karya ya yi ba, da kai aka je ai ba da wani ba kuma kaima shaida ne" Idanun da suka sake rinewa sossai ya zubawa Abban yace "Abba ita wallahi ba haka take ba, nitsatsiya ce kuma tana da tarbiya daidai gwargwado, Abba aka auri karuwa da ta tuba ma bare Afeefah? Abba ko ladarta ba za ka bari na samu ba? Korinta fa suka yi bayan sharri da ƙage da aka lankaya mata a garin" A yanzu kam hawaye sai da suka zuba mishi. "Ko ma menene Sulaiman ba a zuri'ar mu ba, ban taɓa saɓa maganan Yayana ba kuma ba zan fara a kan ka ba Sulaiman, ku fara shirye-shiryen auren shi za'a hada da na Munir" Umma ta ɗago da sauri ta kalleshi "Alhj wata ɗaya fa kacal ya saura na Munir yaushe ya gama warke wannan ciwo da zai yi aure?" "Ke kenan kike goya mishi baya yayi abin da yake so ko? Toh shikenan kar yayi" Yana kai nan ya wuce abin shi. Baaba jummai kam har hawaye take yi, bayanin abin da duk ya faru yayi musu bayan ya gama ya kama hannun Umma "Don Allah umma ko auren za'a yi min ki taimaka ki saka baki a hada da Afeefah wlh ina son ta, tausayinta kuma yanzu ya sake kama zuciyata har ina jin kaman zai fashe" Duk sun tausaya mata, Baaba jummai ta sha kuka sai Allah ya isa take yi a madadin ta, abin da ya dame su ma kasancewar yanzu ba'a san inda ta dosa ba. "Yanzu ka je ka sha magani ka huta sai ka je ka nemo mana ita in har muka sameta komai mai sauƙi ne, rayuwar 'ya mace a haka hatsari ne komai zai iya faruwa, imma a yi mata mugun abu ko kuma ta jefa kanta halaka" Duk sun gamsu, Miƙewa yayi ya nufi Sashenshi cike da tunanin ta ina zai fara nemanta? ***** Saleem a Washegari aka sallameshi ya koma gida, shi ne ma ya matsa saboda ya damu da halin ko in kula da Mahaifiyarshi ke mishi, ƙannenshi kam ba ya kula su bayan ya dawo wanka yayi ya fito, har kicin ya shiga Talatuwa ta bashi abinci ya zo ya ci kan ya nufi ɗakin Mommy, sossai yake kokarin danne damuwar da yake ranshi saboda Rayyan da yayi ta ƙoƙari wurin ganin ya manta Afeefah ya cire ta a rayuwarshi. Zaune ya sameta bakin gado tana danna waya, sallamar shi kawai ta amsa amma ko ɗago ido bata yi ta kalleshi ba, a gaban kafafunta ya je ya zauna "Ban taɓa tunanin akwai ranar da zai zo da zan yi rashin lafiya har in kwanta na tsawon kwana daya gadon asibiti Mommyna bata zo ta duba ni ba, na san na miki laifi mai girma ne shiyasa na kasa bari in samu lafiya na nemi a sallameni don in zo in nemi yafiyarki, kiyi haƙuri in shaa Allahu na cire Afeefah daga raina..." Ya faɗa a raunane "Duk kuma abin da kike so zan cigaba da so matukar bai saɓawa shari'a ba ko da kuwa zai cutar da ni ne, ki yi haƙuri Mommy" Ɗagowa tayi ta kalleshi sai zuciyarta ya karye, wani sashe na cewa bata yi mishi adalci ba, wani kuwa na bata ƙwarin gwiwa a kan abin da ta aikata ɗin ai taimakonsu ne gabaɗaya. "Zan yafe maka in manta irin rashin kunyar da ka yi min matuƙar ka bi umarnina na karshe a gareka" Ta faɗa cikin tabbatarwa. "Mommy ko me kike so ki faɗa ni kuma zan cika miki ko da bana so" "Zan aura maka Sabreena nan da wata guda" Da sauri ya ɗago ya kalleta amma sai harshen shi ya mishi nauyi, uffan ya kasa cewa sama da mintuna uku kan ya ce da kyar "Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi" "Ita ce ma Alkhairin naka" Kai kawai ya gyaɗa ya miƙe ya fice fuskar shi babu walwala sam, a parlor ya ga Sameera na zaune, ido ya ɗan zuba mata ganin ta mishi rama kuma ta yi zuru zuru ga damuwa nan fal a fuskarta, kaman zai yi magana kuma sai ya wuce abin shi. **** Ta ɓangaren Afeefah ta tashi Washegarin jikin da kwari sossai, wanka tayi ta saka kayanta ta samu wuri ta zauna don bakunta ne fal cikinta da kuma tsoro, har yanzu Mammi bata san wacece ita ba shin wani abu zai chanza in ta san wacece ita? Anya shi ma Rayyan ya san wacece ita kuwa? Tunanin da yake ta kai komo kenan a ranta har ta ji an tura kofan an shigo. Ɗaga kai tayi tana amsa sallamar Abeeha. "Alhamdulillah jiki yayi sauƙi sossai Aunty Abeeha" Ta amsa mata bayan ta jefa mata tambayar yaya jiki, Zaro ido Abeeha tayi "Lallai Afeefah ni ce Auntyn taki? Kin ga kirani Abeeha na bana wani son Aunty na san ko da zan girme ki ba zai wuci da shekaru biyu ba" Afeefah ta ɗan yi murmushi "Toh ai ko da kwana ɗaya ne kin cancanci na ce miki hakan bare har shekaru biyu" "Ni dai bana so na bar miki" Ta faɗa da dariya, Afeefah ma tayi murmushi "Kin karya kuwa?" Abeeha ta tamabaya don ita ta tafi lectures 6 yanzu kenan dawowanta 9 ɗin nan. "Eh sun kawo min har nan na karya, ina dai so in je in duba jikin Mammi ne kuma ban san ta inda zan ganta ba" "Nima chan nayi daga nan, na fita duk kuna bacci. tashi mu je" Miƙewa Afeefah tayi Abeeha na cewa rigarta ya mata kyau tayi murmushi tana mamakin saukin halin Abeehar da saurin sabon ta. Sai kallon gidan Afeefah ke yi tana ƙara yabawa abin da ya fi burgeta yadda ko ina kalkal sai kamshi da sanyin Ac ke tashi, ga nan chandliers design daban daban masu kyau kowanne da kalar hasken shi da tsaruwarshi, silifas ɗin kafafunsu mai taushi kaman ka nitse ciki take ta jin daaɗin shi don duk basa yawo kafa banza a cikin gidan da lofas ɗin su masu kyau itama kuma har ɗaki aka kai mata saboda sanyin tiles, ɗakin Mammin suka tura da sallama suka shiga. A kan kujera suka samu Mammi gabanta fruits ne masu low potassium tana sha shima kuma in portion ne akwai yawan da ba zai yiwu ta sha ba, Daga kan gadonta Rayyan ne yana cikin bargo Dukda ba bacci yake ba idanunshi lumshe yana tunanin maganan da Mammi ta gama faɗa mishi yanzu, numfashi ya ɗan sauƙe ya buɗe idanunshi ya kalli inda suke a lokacin Afeefah ta kai ƙasa Mammi na ce mata "Tashi! Tashi a ƙasan nan Afeefah ga kujera zauna ko ki zauna bakin gado ina ke ina zaman wannan sanyin" A bakin kujera ta ɗan dosana tana gaishe da Mammin, Mammin ta amsa cike da kulawa tana tambayarta jiki ta ce ta ji sauƙi, Abeeha ma ta gaisheta tana tambayar karfin jikinta duk adua suka dinga yi wa Mammin tana amsawa, sam Afeefah bata kula da Rayyan ba Mammi da ta kosa ta ji Afeefar daga ina take kuma ina danginta tace "Afeefah ki yi haƙuri da tambayana, ba wai zan tambayeki bane saboda mun gaji dake ko muna so ki tafi ba, yana da kyau ne tambayar saboda mu san asalinki mu san me ya rabo ki da danginki, in kika duba yadda wannan zamani ya zama har wasu tsoron taimakon suke saboda dayawa an fi janyo su inuwa su tura mutum rana. Idan har baki shirya sanar da mu ba kuma za mu hakura mu cigaba da zama dake har ki ji kin gamsu kina son sanar da mu ɗin. Na yi ta tambayar Saraki bai ce min komai ba" Afeefah ta ɗan muskuta gabanta na tsananta faɗuwa ta ce "Mammi don Allah ki daina ba ni haƙuri, ya zama dole in sanar da ku wacece ni! Ina tsoron saka ki cikin damuwa alhali ba lafiya ce ta ishe ki ba don labarina bashi da daaɗi, bashi da abin burgewa ko karsashi, babu abin da ke ciki sai tarin baƙin ciki, kuka da damuwa, Mammi Sunana Afeefah kamal na buɗi idona ne kawai na tsince ni gaban kakata wacce ta haifi babana...." A hankali ta cigaba da basu labarinta tun daga farko har ƙarshe, ta gaji da kuka a kan labarinta hakan ya sa a yanzu ta danne kwarai bata yi kukan ba sai idanunta da suka rine matuƙa gaya, bayan ta gama ta ɗago ido tana kallon expression na su Mammin gabanta na faɗuwa zuciyarta na duka da ƙarfin gaske.... 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh *FREE BOOK* *22* Ga dumbin mamakinta dukkansu biyu kuka suke yi, Abeeha kam ma da sauti yayinda Mammi ke zubar da hawaye, ko kan tayi wani yunkuri Mammi ta miƙe ta iskota ta ɗago ta sai ta sanya ta jikinta ta rungume tana shafa bayanta, wannan dalili! wannan ɗumin jikin shi ya saka Afeefah fashewa da sassanyar kuka mai sauti. Sun fi mintuna goma a haka tana wannan kukan, tuna komai take yi tamkar yanzu ne ya faru ji take duk mace-macen yanzu ne suke dawo mata sabo, taji tana kewar mahaifiyarta da Aunty zee, wannan tausayi da kauna da ta gani daga Mammi sai ya tsaya mata a rai ta ji itama tana ƙaunar matar tamkar mahaifiyarta. Rayyan da tun kan tayi nisa ya lumshe idanunshi bai buɗe ba sai da ya ga kukan na yawa, duk tsikar jikinshi jinshi yake a tashe, ko da ya miƙe zaune sai da ya ji kanshi ya sara ya ɗan runtse idanunshi ya buɗe kan ya ja tsaki ya sauka daga gadon, ya taka ya dafa kafadar Mammi da har lokacin take rike da Afeefah. Mammin gabanta ya faɗi tuna yana ɗakin ta tuna labarin Afeefah sai tayi sauri ta saki Afeefah ta waiga tana kallon yanayinshi, idanunshi ya sauƙe kasa a hankali yace "Mammi please ki bar kukan nan, you are sick already kukan nan bashi da amfani, dole ne sai mutum ya rayu da dangi? Dole ne sai sune kaɗai za su baka farin ciki da kulawa? Na Allah na nan dayawa Mammi..." Yankewa maganan yayi ya ɗago garin kaucewa idanun Mammi sai nashi suka sarƙe cikin nata, sama da seconds huɗu yana kallonta kan kawai ya juya ya bar ɗakin. "Saraki.! Saraki....!!" Bai juyo ba ya fice, ta duƙar da kanta tana ambatar sunan Allah... Chan ta sauƙe numfashi ta waigo ga Afeefah da tunda taji sauƙar muryarshi da yadda yake magana da amo kukanta ya tsaya chakk, haɗa idanun da suka yi ya matuƙar Dakar zuciyarta idanunshi abin tsoro ne a gareta amma a yanzu sai taga ya zama wani iri duk yadda zata fassara ma'anar kallon nashi ta kasa, maganan Mammi ne ya dawo da ita tunaninta. "Lallai Afeefah kin ga rayuwa, haƙiƙa na kaɗu da labarinki abin mamaki kika iya daurewa kika cije kika tsallake wannan jarabawa duk da kananun shekarun ki, Afeefah rayuwar nan duk jarabawa ce kuma ko wani lokaci yana da karshen sa, za mu yi ta shan wahala a duniya amma sakamakon yana hannun Allah kuma ya fi jarabtar wanda ya fi kauna daga cikin bayinsa, Afeefah ina so ki san idan dai har ni, Abeeha, jidda ko Saraki muna raye a wannan duniya kin gama kuka, zan cigaba da rikeki har karshen numfashi na haka zan yi musu umarnin cigaba da kula da ke da baki kariya har nasu karshen numfashin, in shaa Allahu kin gama zubar da hawayen baƙin ciki Afeefah... Sannu! Sannu da juriya" Sabon hawaye ne suka cigaba da silalo mata ta sake rungume Mammi tana fashewa da kuka, Abeeha ta taho ta ɗago ta tana riƙe hannunta "In shaa Allahu ba za mu taɓa kyamatarki ba Afeefah ai duniya ce idan wani ya ƙi ka dole wani ya so ka haka Allah yayi rayuwar, ni na yarda ki ƙirani Addah don ko kowa zai guje ki in shaa Allahu ni ba zan taɓa gudar ki ba" Sossai take kuka, a ranta Adu'a take tana tuna irin kaunar da Aunty zee ta nuna mata a ƙarshe ta tafi ta barta, anya ta zama mai adalci? Anya zamanta a gidan zai haifar da ɗa mai ido? Karshen wahalar kenan ko kuma akwai saura? Duk ta bar wa Allah. Sossai suka rarrasheta ta natsu kan Mammi ta miƙe tayi sashen Rayyan don duk yana cikin ranta tun ɗazu, a kwance ta same shi hallau dai idanunshi a lumshe, kai tsaye ta je ta sa hannu a goshinshi ganin jijiyoyin kanshi raɗa-raɗa a waje, jin hannunta ya sa ya buɗe idanun da suka sake sauyawa ya zuba mata "Saraki ciwon kai ne? Ko za ka je asibiti?" Girgiza kan yayi kaɗan yana yamutsa fuska "Ba sai na je ba Mammi" "Saraki in na barka haka dare ba zaka iya bacci ba, ka taimakeni ka je ka ga psychiatrist din ka" Shiru yayi bai ce komai ba. Ta sauƙe numfashi ta fara duba wayanta cikin mintuna kaɗan sai ya ji muryarta tana magana da likitarshi, buɗe ido yayi ya kalleta bata damu ba har suka gama wayan. "Za ta zo, don Allah ka tashi ka saka wani abu a jikinka mu je parlor" Ta faɗa cikin kulawa kaman yadda yake damuwa da ciwo da damuwarta, shi ma bai san yadda zai yi bane, bai san ya zai yi ya hana kwakwalwarshi tsayar da

Chapter 13 of 40