An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
FATIMA MUHAMMAD GURIN
*GUREENJOH*
*FREE BOOK*
*TSOKACI*
Wannan littafi nawa mai suna HAIHUWA DA HANJI ban san ta ya zan fasalta muku ba amma tabbas yayi matuƙar shan bambam da sauran littatafai na don labari ne na wata baiwar Allah da ya faru a gaske, kashi saba'in cikin ɗari duk ya faru sai kaɗan da za mu ƙara ta yadda zai ƙayatar ya kuma isar da saƙon da muke buƙata ba tare da tangarɗa ba. I promise it's going to be a hit kar ku ga don free ne yana daga cikin labaran da na jima ban rubuta irin shi ba don haka ku shirya shan karatu domin duk wacce bata karanta ba an barta a baya.
*GARGAƊI*
haƙƙin mallakar HAIHUWA DA HANJI na Fatima Muhammad Gurin ne ban amince ba ban lamunci a sauya min labari ko ta wani ɓangare ba ko a yi amfani da shi ba tare da sani na ba.
*SADAUKARWA*
Na sadaukar da littafin HAIHUWA DA HANJI ga ɗaukacin makaranta littatafai na.
*001*
Wani irin ruwa ake tsulawa kaman da bakin ƙwarya, kusan duka bil'adama suna kwance lub cikin tattausan katifa lulluɓe da bargo suna bacci kaman yadda dare ya zama mahutar bawa amma ita tana duƙe a kitchen ɗin dake tsiyaya saboda rashin kyaun kwanon da aka lulluɓe kai da shi.
Wuta ne take hurawa Dukda bayanta dake ta jiƙewa har hakwaranta suna haɗe wa saboda sanyin dake shigarta hakan bai sa ta damu ba sai ma ƙara mayar da hankali da ta yi ga haurawar da bata sarara ba sai da ta ga wutar ta kama yadda ya kamata, babbar tukunya ce da za'a iya naɗe ta a sanyata ciki kuma tsaf ya ɗauketa saboda rashin ƙiba da kumarinta ta shiga kokawar janyowa da ƙyar ta ɗora bisa murhun kan ta nufi wani bokiti ta fara aikin ɗibo ruwa a kimtace tana zubawa sai da ta tabbatar yayi yadda ta saba kan ta rufe ta fito, kifi ɗanye da suke sanyawa cikin ƙanƙara a wani babbar kula ta juye ta shiga wankewa don an riga an yi mata yanka tun jiya da Magrib a bakin kasuwan, sai da ta wanke tsaf ta ɗauko wani tukunyar ta zuba su sai a lokacin aka soma kiraye-kirayen sallah daga chan nesa.
Na yi mamakin yadda ko tsoro babu a fuskarta haka take ayyukan nan cikin ruwa a take ta sake haɗa wani murhun ta ɗora dahuwar miyan kifin nan, sai da ta tabbatar komai ya mata yadda take so kan ta shiga tattaro kwanukan gidan don ta san in ta bari ma gari ya yi haske ta shiga uku, wanke wanke take sauri-sauri yayinda ruwan da ya koma zuba chab chab ya cigaba da jiƙata, har ta gama jikinta babu inda ba ya kakkarwa sauri sauri ta wanke shinkafa ta zuba cikin tukunyar farko kan ta yi alwala har kuma lokacin babu mahaluƙin da ya leƙo a gidan Dukda kuwa wasu masallatan ma har sun idar da sallah.
Akurkin ɗakin da shi ne nata a gidan ta duƙa ta shige ta cire kayan jikinta bakkon kayanta ta janyo da kyar ta zaƙulo wata kodaddiyar doguwar riga ta saka ta janyo hijabinta ta ɗora tare da tada sallah, ga mamakina tsaf ta gabatar da Sallar ta yadda addini ya tanadar, bata jima tana azkar ba ta fito don gudun magana amma bata tsira ba domin a kitchen ɗin ta tarar da Inna larai da sauri ta duƙa ƙasa
"Ina kwana inna?"
Kallonta tayi ta taɓe baki ta buɗe tukwanen ganin miyan ya yi ta juyo gareta
"Uban me kika shiga ɗaki kike yi har miyan nan ya nuna saura ƙonewa baki shirya kwashewa ba? Asara kike son ja min ko?"
"A'a inna sallah ne na je na yi"
Tsaki ta ja tare da nuna mata kular da suke kwashe miyan tallar, ta je da sauri ta ɗauko inna larai ta kwashe tsaf kan ta ɗaura dumamen gidan a murhun, ita kuma ta wuce ta ɗauko kular kwashe shinkafa ta taho ta janyo ledar sugar ta buɗe a cikin kular kan ta shiga kwashewa turirin na Dakar ta yana ƙonata yadda ta saba har ta gama duk sanyin da ake ta jiƙe jagwaf da gumi, kwanukan tallarta ta cigaba da haɗawa a wani bokitin fenti har ta gama filate na roba da ruwa da gutsuren dollof da take wanke plates idan ta sayar aka ci aka dawo mata dashi.
"Je ki bugawa su Iro su zo su ɗaura miki a baro su kai miki yanzun nan"
Da to ta amsa cikin sanyinta ta nufi ɗakin na yaran mazan ta shiga bugawa, sai da ta kwashe sama da mintuna ashirin tana bugu da ƙiran suna kan wasu matsakaitan samari biyu suka fito ɗayan ya sa hannu ya hankaɗeta sai da ta faɗi ƙasa.
"Don uban ki bamu hana ki wannan bugun bala'in ba? Shegiya kullum ba ki da aiki sai na uzzurawa mutane ko wani farar safiya..."
"Ɗahiru ƙaniyar ka...! Kun wuce kun zo kun fitar min da abinci ko sai kun janyo min asara?"
Babu ruwanta da sun yi sallah ko ba su yi ba damuwarta kawai su kai mata kayan sana'ar ta.
A hankali ta miƙe tsaye tana kaɓe jikinta dama ta sani ba dai a yi musu faɗa a kan an ci zarafinta ko an zalunce ta ba, kowa a gidan na ganinta tamkar juji da in sun kwaso sharar su babu inda suke zubawa sai bisa kanta.
Sumsum haka ta taho suka kama suka ɗora suna ta mitar da kullum safiya sai sun yi haka har suka fice, tana shirin fita daga gidan kenan Inna larai ta kwala ƙiran sunanta.
"Afifah Ke!"
Waigowa tayi da sauri kuma cikin sanyinta
"Saura in ga ba daidai ba wallahi sai na lahira ya fi ki jin daaɗi kuma kika sake kika ci kai ko lasa kika yi Allah ya isa ban yafe ba ki je ki dawo ga dumamenki nan zan ajiye miki"
Girgiza kai tayi fuskanta ɗauke da murmushi mai nauyi da ciwo ta amsa da
"Toh"
Kan ta fice daga gidan.
A inda ta saba zama gefen rumfar masu tura finafinai nan ta zauna bayan sun sauƙe mata suka buɗe suka cika fillet biyu idanunta cike da hawaye tace
"Iro wallahi in..."
"Na uwarki ne ko na ta mu uwar? Ina ruwanki? Kuma wallahi ki sake ki faɗa mata ki ga yadda zamu yi da ke Annoba kawai"
Da ƙarfi ta runtse ido sunan ba wai sabo bane a gareta sai dai a duk sadda aka ƙira ta da hakan ta kan ji zafi da ciwon fiye da ɗanɗanon maɗaci a kan harshenta.
"Mai shinkafa sa min na ɗari uku..!"
Haɗiye abin da ya taso mata tayi ta karɓi kudin ta saka a Jakan ƙugunta kan ta fara zuba shinkafar kaman ko yaushe fuskanta babu ɗigon fara'a ko sassauci ba kuma don komai ta ɗauki wannan mataki ba sai don kare mutuncinta.
Hakan da take ya sa maza dayawa masu kawowa 'yan mata yan tallah wargi basa samun dama kowa ya santa duk tsiyarka tana da kwarjinin da in ta tsume hakan babu mai iya kawo mata wargi... Saboda tsafta da kuma natsuwarta yasa dayawa suke tururuwa wurin sayan abincinta.
Ita ɗin annoba ce kaman yadda wasu ke ƙiran ta dayawa sun santa a Mayya! Dukda ita bata taɓa sanin menene maitar ba amma ta wurin kasuwanci su kan saya abin hannunta don ko babu komai akwai zaƙin hannu muddin ita tayi girki.
Kan ka ce awa biyu duk ta sayar da abincin tas ta janyo baro ta ɗora kulolin a kai tana jin jiri na fusgarta saboda rabon ta da abinci tun jiya da rana gashi yanzu ana neman goma da rabi, haka ta turo wheelbarrown ta nufi gida...
Razana tayi ta daka tsalle tayi baya sun saba yi mata hakan sai dai ta kasa sabo ita
"Ina kudina?"
Inna larai ta miƙa mata hannu a zauren wanda ko kanta bata gama sanyo wa ba, Jakan ta sunce ta miƙa mata a wurin ta zazzage ta kirga ta ga riba yadda suka saba samu ta saɓi kayanta ba sannu bare na gode tayi cikin gida abin ta, Afifah ta bita da kallo har ta ɓace kan ta turo baron zuwa cikin gida ko sauƙe kwanonin bata yi ba ta nufi bakin kitchen inda inna larai ɗin ke zaune ta duƙa
"Abincina fa inna?"
"Laaaa kin ga mun manta da ke wallahi ina fa ta zuci zucin ajiye miki"
Runtse ido tayi da ƙarfi tana danne hawayen dake taso mata idan da sabo ya ci a ce ta saba, kusan koyaushe za su yi rabon abincinsu muddin bata gidan to za'a ce mata an manta da ita ne, wani lokacin ma sai an sauƙe sai a aiketa kan taje ta dawo an rabar kuma a hana ta, hanjinta har murɗewa suke saboda yunwa amma ya zata yi?
Miƙewa tayi ta nufi hanyar akurkinta inna Asabe ta kwala mata ƙira daga cikin ɗakin ta
"Ina za ki da baki karɓi kuɗin nawa aikar ba?"
Bata ce komai ba ta tsaya daga kanta leda da ke kunshe da kuɗi ta jefa mata a fuska
"rashin kunya za ki min ki tsaya min kerere bisa kai? Kin ɗauka kin wuce ko sai na tsinka miki mari?"
Duƙawa tayi ta ɗauka ta fice daga gidan ko ɗakin bata shiga ba ta riga ta san me zata sayo, ko kan ta dawo har inna Asabe ta gama tuka tuwon tallar tata na dare, ita ta zauna ta malmala tana jin kanta na sarawa ayyukan sun fi karfin shekarunta amma ya zata yi? Mutum ɗaya take da shi a duniya Aunty zee ita ma kauyen gaba da su take kuma ta kan kwana biyu bata leƙo mata ba bare ma hakkin riƙe ta na ga dangin mahaifinta ne ita kuma ga abinda Allah ya bata, sai dai ta tashi tayi sallah har ta gama malmalar tuwon na dubu goma sha biyu kaman yadda suka saba ta ɗora miyan ta kala biyu da Alaiyahu da kubewa, bayan ta gama ne inna Asabe ta tarfa mata sauran ƙasan tukunyar tukun a cikin tukunyar miyan Alaiyahun da ta gama kwashewa ganin sai kashe jiki take saboda yunwa bata son abinda ya samu kayan tallatarta sam.
Sai da tayi wanke wanke tas har da kwanukan safe na tallar inna Larai kan ta shirya ana kiran Magrib tayi sallah ta fice bakin kasuwa, yanzu ma bata kula kowa abincin kawai take sayarwa har wuraren takwas ya ƙare ta tattaro ta dawo gida dama tun shidda ta sayi kifin miyan safe ta ba almajiri ya kaiwa inna Larai za ta saka cikin ƙanƙara ji take kasusuwanta kaman ana sarawa, kuɗin kawai ta ba inna Asabe ta wuce ɗaki ta kwanta idanunta na kallon sama, shikenan ita kuma a haka rayuwarta zai cigaba da tafiya? Shikenan ita kuma haka za ta ƙare? Don dai ta san kap kauyen dutsen-wai babu namijin da zai tare ta da sunan soyayya babu kuma gidan da za su amshe ta yadda ake ganinta annoba kuma duk gidan da ta shiga sai ta wargaza kuma sai an yi mutuwa kan ta fita tayi zurfi cikin tunanin ta kawai taji ana dukan kyauren palangen dake kare kofar akurkin da ɗan banzan ƙarfi sai da ta razana ta miƙe tsaye ba tare da ta sani ba.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*002*
Nannauyar numfashi ta sauƙe sai kuma ta fita daga tsoro ta shiga fargaba, kawu ne! Me ta yi? Jikinta a sanyaye ta miƙe tsaye ta turo kofan ta fito.
"Iskancin naki ya kai ina ƙiranki kina ji na ki yi min banza ko? Ko har kin tafi meeting naku na cin ɗanyen naman mutane ne?"
Girgiza kai ta yi tana wasa da yatsun ta murya na ɗan rawa ta furta
"Ka yi haƙuri kawu bacci na fara ne"
Tsaki ya ja yana jefanta da mugun kallo, babu yadda ya iya ne kawai yarinyar ke zaune gidan shi in ba haka ba babu abinda zai sa ya ajiye makashiyar mamarshi da 'yan uwanshi har ya ke bata abinci tabbas da ana kashe mutum a sha a banza da tuni ya yanke wuyanta ya jefar da gawar daji tsuntsaye sun cinye, duniya in akwai wacce ya tsani ko inuwarta ya gani ya biyo bayanta.
"Ba dai a mawankin chan za ki bar mana kwanuka su kwana ba kan safe duk shedan ya bi ya fitsare mana kwanuka? Oh ko so kike duk ki kashe mu ne ki huta?"
Lip ɗinta na ƙasa ta ɗan datse a hankali kan ta saki ta furta
"Kayi hakuri zan yi"
Ya ja tsaki kan ya juya ya wuce ɗakin inna Asabe.
Mawankin dai ta wuce akwai ɗan guntun omo haka ta fara wanke wanken idanunta kaman za su cire saboda raɗaɗin bacci har kifewa take yi bisa kwanukan tana tashi sai da kusan duk kowa yayi bacci a gidan kan ta gama kifewa ta wuce nata akurkin sanyi kaman zai kasheta ta shige cikin zaninta bayan ta sauya hijabi zuwa busasshe dukunkune haka tayi baccin. Kaman jiya yau ma dai kowani ɗan adam na kwance yana bacci haka ta fita tsakar gidan ta shiga aikin abincin tallar inna larai.
Ba don ba'a sabo da wuya ba zata iya cewa wahala ya riga ya zama jininta, bata san yadda zata fassara rayuwa ba sai dai ta san ƙaddararta mai matuƙar zafi ne da ta kan rasa sanyi ko sama ko ƙasa a duk sadda ta rura wutar ta.
Bata da farin ciki ko ɗaya bata da mai tambayar damuwarta ko ciwonta har ma da bukatuwarta waenda suke tare da ita amfana da ita kaɗai suka iya amma ita bayan mafaka da kwanon abinci sau ɗaya a wulakance bata anfanuwa da su ko ta wani ɓangare, manyan su zaga, matasan su daka su kuma hantara yaran su wulakantata bata da bakin magana saboda ita ɗin ta riga ta zama annoba...
Eh annoba zata ƙira kanta kaman yadda kowa ke kiranta an haife ta da rashin sa'a tunda tana ciki watanninta basu wuci biyar ba Allah ya karɓi mahaifinta, a wurin haihuwar ta Allah ya karɓi mahaifiyarta ta zama cikakkiyar marainiya daga ranar da ta faɗo duniya, kakarta ta wurin uba ita ce ta raine ta kan madara ta bata tarbiya ilimin addini da boko har ta shekara takwas ita ta sani a matsayin uwa kuma uba, ta samu gata na iya tsawon lokacin da tayi da kakarta har makarantar gomnati na boko ta sanya ta kan kwatsam mutuwa ta yanke wannan ƙauna tun daga sannan aka fara jita-jitar ita ɗin Mayya ce! Kuma duk wanda ta raɓa zai mutu.
Tsangwama ya fara yi mata yawa a hannun ƙanwar babanta da ta koma Inna Amina ta sha baƙar wahala kasancewar inna Aminar ma cikin gidan yawa take, mijinta kuma ba wai ya karɓe ta bane zaman dole take mishi a gida hatta abincin gidan bai amince a saka mata ba duk abinda aka sanyawa inna Aminar suke taɓawa a tare, ta samu innar tata da ciki a lokacin kawunta ya ƙi yarda ya ƙarbe ta tunda su uku kawai kakarta ta haifa.
Kawu ne babba sai babanta tukuna innar dole dai wurinta take lallaɓa wa rayuwarta.
Wata rana inna Amina ta tashi da nakuda babu wani cima mai kyau, babu cikakken kulawa da ya kamata mace mai ciki ta samu, bata taɓa zuwa awo ba ana rayuwa ne cikin wahala haka ta tashi nakudar a gida aka kira unguwarzoma ta ci azaba ko da ta haihu babu rai ita ma bata jima ba jini ya balle mata ko kan a ce an yi wani yunkurin Allah ya karɓi abin shi, ko gawar inna da jaririyarta ba'a binne ba aka sanya Afeefah gaba da zagi, cin mutunci, baƙaƙen maganganu babu irin wanda ba'a jefeta ba a lokacin da take jin tashin hankali da damuwar rashin innarta Aminan.
Ta ga mutuwar kaka amma bai kaɗata kamar na inna Amina ba saboda yadda ta mutun a wulakance cikin sakacin miji da kishiyoyi ta yi kuka kaman babu gobe, har jifan ta da dutse ake yi in ta fita a haka kawu ya dawo da ita gidan shi tana da shekaru 10.
Matanshi basu karɓeta ba, babu wacce take yarda har yanzu ta shigar mata ɗaki ko na yaransu dole aka buga mata keji don ba shi da maraba da keji aka sanya buhu aka bata taburma saboda kar ta kashe musu 'ya'ya, bata sani ba ko tabbatar ta mayyar ce ta sa yanzu shekara shidda kenan da dawowarta gidan kawu bayan ɓari da matan suke yi babu wacce ta sake haihuwa, sun yi duka sun yi zagin duk a banza wai an tsikari kakkaura ita bata ma san ta yadda ake yin maitar ba, wani lokaci har ta kan yi adu'ar ya tabbata ita ɗin Mayya ce don tana so ta ba su kyautar kanta duniyar bata da anfani a gareta. bata ƙara zuwa makaranta ba ko na boko ko arabi tun bayan mutuwar kakar ta sai dai ta ga wasu da kayan makaranta, ta zama boyi boyi abin wulakantarwa, abinci wannan da kyar ake bata a gidan kan suka fara ɗora mata tallah ganin tana da wannan farin jinin ya sa suka dage kuma ake kishi a kanta don kaman yadda suke raba kwanan mijinsu haka suke raba ta.
Dole kuma a rana idan ta yiwa wannan sai ta yi wa ɗayar idan ta sayarwa wannan ko kwana zata yi waje sai ta sayarwa ɗayar kan ta dawo gidan in ba haka ba ta shiga uku, bata sani ba zata tabbata a haka Ko wani sauyi zai iya shigowa rayuwarta? Ita ɗin Mayya ce da gaske? Har yanzu tambayar da ita karan kanta bata iya amsawa kanta ba kenan bare ta amsawa azzaluman mutanen da suke zagaye da ita.
"Ke!!!"
A ɗan firgice ta ɗaga kai sai ta ga wani matashi na miƙa mata kudi
"tun ɗazu ina ta magana kin yi shiru kaman bakya duniyar? Saka min na ɗari biyar"
Abincin ta shiga sakawa shi ne ma na karshe don wuraren sha ɗaya na safe ne, bayan ta saka mishi ya koma cikin matasan da suke tare ya shiga ci ita kuma ta fara tattare wurin cikin natsuwa da sanyinta sai da ta gama zuba komai cikin wheelbarrown tana jiran matashin ya gama ya bata plate sai kawai ta fara jin hayaniya na tashi, ɗago kan da zata yi sai ta ga wannan saurayi ne dafe da ƙirji yana tari sossai da sossai har filate ɗin ya faɗi ƙasa abincin ya tarwatse ya bi abincin yana tumurmusa a ƙasa, kan kace kobo wurin ya cike da mutane wasu na cewa ya mutu wasu na cewa da sauran ranshi.
"Me ya ci ne? Me ya same shi?"
Abin da mutane dayawa ke tambaya kenan, ita dai Afeefah na kafe a wurin ko motsi ta kasa sai gangar jikin da mutane suka yi wa zobe kwance ta zubawa idanu kaman daga sama ta ji Muryar wani na cewa
"Daga fa sayan abincin yarinyar chan kun ga bai ma gama ci ba...! Ku taimaka mu kaishi asibiti kar ya rasa rayuwarsa kumfa ne a bakin sa"
Cikin jimami ya ƙarasa
Wata murya taji tana cewa
"hohoho asshaa dama na san aje aje sai ta fara yiwa mutane dauki ɗaiɗai shiyasa ban taɓa sayan abincinta ba, yarinyar da riƙaƙƙiyar Mayya ce an ce ma ita ce mataimakiyar shugaban Mayu yanzu?"
Ko motsi bata iya ta yi ba taji an damketa zuciyarta kaman zai fito waje ba na tsoron abin da mutane zasu iya yi mata ba sai na tsananin tsoron mutuwa, mutuwa na daga cikin abinda a yanzu yake gigitata dole duk mai imani ya tsorace mutuwa a yanzu yaron nan ke mata magana a yanzu ana cewa ya mutu? Ta yaya? Meyasa sai da ya sayi abinci a hannunta?
Wani mai ƙirar ƙarfi ya hankaɗata tsakiyar mutanen
"Ke tsallakeshi sau uku ki sakar masa kurwa yanzu wallahi ko mu sheƙa ki barzahu.."
Yayi maganan da karaji yana zaro wuƙa mutane suka fara kananun maganganu masu zaginta na yi, wasu har labari suke bayarwa na ta kashe iyayenta ai maitar gado ne tun a ciki ta fara kisa, hawaye masu zafi ne suka shiga gangaro mata a sadda take tsallakeshi a dole, kalaman da suke shiga kunnuwanta sun yi mata girman da ba zata iya ɗauka ba, abin tashin hankalin ma shine yaron bai tashi ba, ya tabbata ya riga ya rasa ransa ko kan ta gama fahimtar kanta har tayi wani yunƙuri an rufe ta da duka, ko yunkurin kare kanta bata yi ba don a yanzu ita ma ta fi ƙaunar mutuwar da rayuwa, da kyar wasu dattijai suka kwace ta fuskanta har ya fara sauya kamanni wasu sassa na jikinta na zubar da jini, kwanukan inna larai da kulolinta an yi daga daga da su, ko kasheni ka ɗaukanta (lalitar kuɗi) bata gani a jikinta ba.
Wani irin deep kuka take yi mai taɓa rai, dattijon ta kalla
"Don Allah baba ka bar su su kasheni kawai nima ina so in huta, don Allah ku bar ni su kasheni"
Abin da take ta maimaitawa kenan tana gunjin kuka ya riƙo hannunta
"Ki natsu yarinya babu mai kashe ki, shima kwananshi ne ya ƙare ya mutu kiyi hakuri ki tashi mu raka ki gidan ku"
Cikin in-inaa take cewa
"in naje gi..gidan ma ba..ba tsira z..Zan yi ba kuɗin inna larai da kwanukan ta duk babu"
Ta sake rushewa da kuka, tausayinta ne ya kama su suka haɗu suka tasa ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 40