kwanta a wurin, sai Eight ta fito a shirye cikin Abaya Grey da yayi mata kyau sossai hula ne a kanta kai tsaye taje ta dubo abincin taga wanda zai iya ci ne ta kwaso ta kawo sashen nasu ta shirya dining ta saka turaren wuta a parlorn don a gyare yake tsaff yana kyalli ta juya zata koma ya buɗe kofa ya fito, kallonshi tayi yana sanye da wani Army Green riga tare Black wando da ya amshe shi, rigan ya kama shi ya fitar da kirarshi sossai bai mishi ruwa ba sam sai taji wani nauyin shi ya rufeta ta mayar da kanta ƙasa, ya kalleta ya ɗan shafa gashin kanshi kaman zai yi magana kuma sai ya nufi dining kawai.
Binshi tayi sai da ya zauna tace
"Ina kwana?"
"Kin tashi lafiya?"
Ya bata amsa ko numfashi bai bari ta ƙarasa saukewa ba idanunshi na akan fuskarta sai kawar da ido take daga kallonshi wanda hakan ma dariya ya bashi amma ko a fuska bai nuna alamu ba, ta haɗa mishi abin kari da yau English breakfast suka yi a gidan ta tura mishi, bata so ta tafi tayi laifi don haka ta ɗauki omlet ɗaya ta haɗa tea ta ja kujerar da take zama chan nesa dashi ta zauna tana karyawa, bai ce mata komai ba itama bata ce ba.
Bayan ya gama ya miƙe ya koma ɗaki ta bishi da kallo tana ɗan taɓe baki mutum kaman hawainiya, tattare wurin tayi tsaf kaman ba'a ci abinci yanzu ba ta wuce nata ɗakin, monday za ta fara waec don haka dole ta fara duba takarda kafin taje ta faɗi sai ta fara lalabo takardunsu na makaranta ta ɗauko wayanta ta fara bincike akan past questions da take son fara dubawa.
Shi kam kusan sai da ya gama haɗa duk abin da zai buƙata lokaci lokaci yana dan daakatawa ya tafi nazari kaman wanda baya kaunar tafiyar kan ya ɗauki keyn mota da wallet ɗin shi ya fito sanye da wata White sneakers da ta sake fito da shigar tashi idanunshi ya rufe da baƙar space sai ya zama kaman wani model ya san kan wanka ba laifi, a babban parlor ya samu su Abeeha suna ganinshi kuwa suka miƙe tsaye don dama sun shirya saboda sun sanshi yadda ya washi jira sai dai a jira shi...
Har sun nufi kofa yace
"Ina take?"
Duk tsayuwa suka yi Abeeha na so ta tambayi ita wa amma fuskar shi da ba'a sake ba yasa tace
"Afeefah ina ga bata san da ita za'a yi fitan ba bari na ƙirata"
Ta ƙarasa tana nufan sashensu a ranta tana adu'ar Allah ya sa ita yake nufi kafin ya fara mata masifa, sai taga ya fice daga parlorn jannah ta bi bayanshi.
Zaune ta sameta hankalinta kwance
"Tashi maza ɗauki gyalen ki muje"
"Ina za mu?"
"Shopping Ya Rayyan ya riga ya fita yi sauri kafin ya hasala"
"amma ni ba abinda nake bukata fa Adda Abee..."
"Ke wlh tunda ya neme ki sai kin je, gwara kin tashi"
Bata fuska tayi don wlh bata son zuwa ko ina, kai Abeeha ta gyaɗa
"Ki same mu a mota kuma ki yi sauri"
Miƙewa tayi ta chanza Abayar jikinta zuwa wani orange, ta saka farin takalmi tayi wrapping kanta da farin Jersey veil ta ɗauki wayanta ta nufi waje har lokacin fuskarta ba'a sake ba.
Tun da ta fito ya zuba mata idanu ta cikin glassses na idanunshi yana kallo, a fuskarta ya tsayar da idanu yadda take dan ɓata ran ya bi jikinta da kallo Dukda ko ina a rufe yake sai da ya ɗan ji wani iri, tafiyar ta kaman tana rausaya Dukda ita sauri take, bai ji haushi ba idan ma zai yi judging wani gefen na zuciyar tashi akan gaskiya zai ce he enjoyed the walking ba tare da ya san dalili ba, tuni su Abeeha suna baya dole ta buɗe gaba ta shiga ya ɗan lumshe idanu saboda kamshinta da ya shige shi ya buɗe tare da tada motar ya fice daga gidan.
Su Abeeha sun zaci ba zasu wuce shopping malls da suka saba zuwa ba na nan kusa kusa ko market square ko barnawa shopping complex sai suka ga ya miƙa ma yayi chan unguwar rimi bai tsaya ko ina ba sai Kaduna Galaxy Mall yayi parking suka sauƙa tana shirin sauƙa yace
"Ki ji!"
Ta ɗan kalleshi tana dawowa ta zauna
"Na'am Ya Saraki?"
Ya zare glass ɗin ya kalleta sai ta kawar da kanta, kaman zai mata gargadi akan wannan sarakin da take faɗa take motsa mishi zuciya sai ya fasa.
"Kina ɓata rai babu abin da kike buƙata ne?"
Ta Yi mamakin yadda ya karance ta Dukda tunda suka fito babu wanda yayi magana a cikinsu.
"Kin min shiru ina magana?"
Ya faɗa ba da faɗa ba...
"A'a akwai, za mu fara waec monday akwai abubuwan da nake buƙata na makaranta sai da na fito na tuna"
Bayan ta gama bayanin kuma sai ya mata shiru ta ɗan sake haɗe fuska shi baya son shiru amma ya ƙware a yi wa mutane banza, sauƙa tayi ranta ba daaɗi su Abeeha har sun shige ita yanzu ina ta nufa ba zuwa ta taɓa yi ba ganin a kyau da tsarin shi ya bambanta da wanda suke zuwa da Abeeha.
Wayanta ta duba don ta ƙira Abeehar ma ta ji inda suke su tafi da ita taga katin ta ya kare ta ɗan yi taku biyu tana furta
"Oh! ashe ba ni ma da katin, to yanzu ina zan yi??"
A karye tayi maganan tana sauƙe hannunta ƙasa, babu zato babu tsammani taji ya sanya hannunshi na dama cikin nata na hagu ya gimtse, da sauri ta kalleshi kaman ba shi ba dole ta fara Binshi sun zaga sossai har wurin kayan makaranta ta ɗauki duk abinda take so suka dawo wurin turaruka ya ɗauki turarenshi ita bata bukatar komai don kayan aurenta duk babu abinda ma ya dauki hanyar ƙarewa suna nan set set, a wurin biya suka ga su Abeeha.
Abeeha da ta hange su daga nesa ta taɓa jannah
"Addah Jannah kalli ki ga...!"
Jannah ta waiga tana kallonsu suna tahowa sun yi matuƙar kyau da dacewa fiye da yadda baki zai fasalta, da sauri ta ɗaga wayanta ta fara musu hoto tana murmushi ganin zai ɗagota tayi saurin sauƙe wayan tana cewa Abeeha
"haƙiƙa ba ƙaramin sa'a Afeefah ta taka ba, samun soyayyar namiji irin Ya Rayyan....Ya Allah i just can't imagine.."
With so much excitment tayi maganan. Abeeha ma tace
"Wlh shima yayi dace Mata Kaman Afeefah are very rare sun dai dace kawai duk su biyun they Look so breathtaking"
Gab da su ya saki hannunta ya zaro Atm ya biya aka hada musu komai nasu suka nufi mota, bayan ya shiga ya kunna Ac ɗin sai yaji baya ba da iska kaman gas babu tsaki mai ƙarfi ya ja ya kunna motar suka fice yana sauƙe glass a hankali.
Kwanciya tayi ta lumshe ido jikin kujera tana sauraron dukar da zuciyarta ke yi, hannunta da ya riƙe throughout ta kaishi fuskarta ta shafa tana sake sniffing kamshin da ya bar mata har lokacin tana jin softness na hannun cikin nata, bata san sun yi nisa ba sai da suka zo last danger na ɗaukar hanyar gidansu ta ɗan buɗe idanu sai taga wasu maza a cikin napep suna kallonsu kaman an ce ya kalli wurin ya sake jan tsaki ya miƙa hannu ya dage glass ɗin ɓangaren ta har sama, ta ɗan kalleshi bai ko kalli inda take ba ana sake su yayi kwana zuwa gida.
A yanzu bai ɓata lokaci ba don idan ya tsaya batawa zai iya makara gashi takeoff din nasu 12 ne dot. Wurinta ya fara shiga tana zaune kawai ta ganshi ta miƙe tsaye.
"Zan tafi."
Tayi mamaki kwarai don ita yana kasheta da mamaki a tsakankanin.
"Allah ya tsare ya ba da sa'a ya kuma dawo da ku lafiya."
Ya amsa da Ameen a kan lips ɗin shi yana kallonta.
"Ina fata kina sane da jiya ba yau ba ne, bana son yadda kike fita school anyhow make sure kin saka ko hijabi ko ma Abaya before going in ya so in kin isa ki cire, just focus on abin da ya kai ki. Ki kula sossai don ina da matuƙar kishi akan abin da nake so."
Yana kai nan ya ajiye mata bundle na 1k guda biyu a kan gadon ɗakin ya juya ya fita.
neman faɗuwa tayi ta samu wuri ta zauna tana jin kalaman nashi na dawo mata
"Kishi akan abin da yake so? Waye yake son?"
Da sauri taje gaban madubi tana kallon kanta sai ta girgiza kai ba dai ita ba kila bata ji da kyau ba ko kuma kariyar nashi irin na ya da kanwa ne.
Jikin Window taje ta tsaya tana kallonshi yana magana da duka ma'aikatan gidan sama da mintuna biyar kan ya shiga mota wanda ba ma dashi suka fita ba ya ja ya fice daga gidan, saƙon Shigowar message taji ta janyo wayanta sai ta ga kati ne mai yawa aka saka mata ta kama baki ta riƙe mamaki na so ya kasheta da ranta data ta kunna sai taga hoton da Jannah ta ɗauke su ne ta turo mata sossai hoton ya mata kyau har bata san ta saki kyakyawar murmushi ba tana shafa fuskar wayan...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*44*
*Laamu Fombina – Daular Gabas*
A yankin kudu maso gabashin ƙasar Arewa da bafulatani kai tsaye ke ƙira da Fombina bature kuma ya ce Southland, an yi wata Daula mai kafaffen tarihi da kuma mulki wacce ta samo asali tun daga jahadin Ɗanfodiyo ta hannun ɗalibinsa Muhammadu (Modibbo Adama) tsakanin shekarar 1809-1847.
Mafi akasarin mutanen wannan yanki Fulɓe ne ko kuma a ce musu Fula suna daga cikin manyan ƙabilun Africa musamman a yammacin nahiyar. Asalin su yana da matuƙar zurfi, masana tarihi sun taɓa jayayya kan inda suka fito amma dai an fi karkata kan manyan ra'ayoyi guda uku.
Ra'ayin Africa ta yamma, Yawancin masana sun ce Fulani 'yan asalin yankin
Senegal ne da Mauritania, daga nan suka bazu zuwa Nijar, Mali, Najeriya da sauran kasashe.
Ra'ayin Arewa(Africa ta Arewa), Wasu sun danganta asalin su da yankin Masar ko Sudan, suna ganin sun shigo cikin Sahara tun
zamanin da.
Ra'ayin haɗe da larabawa, wasu sun danganta asalin su da haɗewar 'ya'ya tsakanin mutanen Africa da Larabawa, musamman saboda musulunci da kuma tsananin tsarkin jini da suke riƙewa.
Gaskiya kusan duka Fulani Musulmai ne, tun da musulunci ya shiga Afirka ta Yamma ta hanyar su.
Sun taka rawar gani wajen yaɗa addinin Musulunci musamman Shehu Usman dan Fodiyo wanda ya kafa Daular Sakkwato a karni na 19.
Fulani suna da ɗabi'u da al'adu na musamman da suka bambanta su:
1. Rayuwar Makiyaya (Nomadic / Pastoral
Fulani)
Mafi shahara a duniya saboda kiwon shanu.
Suna yawo daga wuri zuwa wuri suna neman ciyawa da ruwa. Wannan ya sa ake kiran su Bororo'en.
2. Fulani Masu Zaune (Settled Fulani)
Su ne suke zaune a birane da kauyuka, suna noma, kasuwanci da neman ilimi tare da yaɗa ta. Su ake kira Fulbe Na'i ko Fulbe Gidda.
3. Mutunci da Tsarkin Jini (Pulaaku)
Pulaaku shine tsarin dabi'a da falsafar
Fulani. Kuma suna da ababen sha'awa da suka kunsa wanda sun haɗa da:
• Munyal (hakuri)
• Semteende (kunya da ladabi)
• Hakkilo (hikima)
• Ngorgu (jarumtaka).
A ƙarƙashin wannan yanki da mutanenta suka kasance rabi da kwata Fulani (Pulaaku) aka kafa Masarautar fombina, masarautar tana ƙarƙashin Lamidon farko ta ƙasar Modibbo har wa yau da jininshi ne ke mulkarta, ya kasance daga ragowar daulolin Fulani da suka wanzu tun daga Usmanu Ɗanfodiyo.
Ƙatuwar masarauta ce da idan na tsaya misalta muku girmanta da kyawunta zamu kwana muna abu daya bamu gama ba. Cikin Masarautar gari ne guda da ke ɗauke da ɓangarurruka daban-daban kama daga kan Fada, ɓangaren sarki da
iyalinsa, Galadima, madaki, wambai, Turaki, Makama sarkin faɗa, Sarkin yaki da ma kowani mukami mai matsayi da ƙima a sarauta, inda kowa sashinsa ke tareda nasa iyalin daidai matsayin kowa.
Kuyangu, bayi da Fadawa ma nasu gashin kan suke ci a Sashukansu na musamman inda suke gudanar da rayuwarsu bayan sun taso daga wurin ayyukansu na yau da kullum. Kitchen kuwa fankacece suke dashi inda ake general abinci a kai wa kowani ɓangare nasu dukda kuwa kowani ɓangare akwai kitchens ciki. Akwai asibiti mai zaman kanshi cikin wannan masarauta da ma'aikata ƙwararraru akwai kuma Makaranta da aka yi musamman sabida ma'aikatan masarautar da iyalansu dake amfanuwa.
Kodayaushe kashigo Masarautar za ka samu ko wani ɓangare ana hada-hada ana kai kawo. Fadawa na fada, kuyangu da bayi na wuraren ayyukansu, Dogaraye na aikin ba wa Masarautar tsaro dare da rana ayayinda Masu Masarautar daukansu ke aiki ka'in da na'in wurin ganin sun kawo cigaba a Masarautar da al'umman gari baki daya.
A zamanin nan da Garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a wasu yankunan, abu ne da kan tada hankali kuma matsala ce ga kowani zamantakewa da tsaro, babu ƙabila ko yare, babu namiji ko mace, babu babba bare yaro haka ta shigo cikin wannan Daula ta Fulani ta kutsa kai har cikin masarautar saboda an wayi gari da tashin hankalin garkuwa da Ƴa ɗaya tilo da Laamiɗo Muhammadu Modibbo ya mallaka a wannan duniyar.
Wannan matsala ta saka Laamiɗo girgiza har ta kai yana tuna wani al'amari da ya faru a chan baya da ya haddasa ciwon da yake fama da shi a tsaitsaye shekara da shekaru tashi, kasancewar shi nagartaccen sarki, Laamiɗo Mutum ne wanda ya gina al'umma mai gwaɓi, mutum ne da kowa ke rububin ganinshi don agajinshi, Mutum ne da kowa ke son haɗa alaƙa dashi don Arzikinsa. Kyawawan halayensa ya sa ya zamana kowa ya shiga jimami a tare dashi hakan kuma ya ba da gudummawar Gomnati na tura manyan ƙwararrarun sojoji don aiki akan wannan lamari.
Ko da Shigowarsu cikin masarautar a Motocinsu saboda an fara isar da su fada ne domin su huta su kuma fara bincike daga tushe, Rayyan ne ya zama na ƙarshe wanda ya buɗe murfin motar sanye yake da full khaki na sojoji fuskar nan kaman ko yaushe a matuƙar haɗe Dukda ma idanunshi masu ɗaukar hankali da kuma karan hancinshi ne ya bayyana kasancewar akwai facemask maƙale a fuskar tashi, yana ajiye ƙafa kan daɓen ƙasan masarautar Wani irin guguwa mai ƙarfin gaske da ƙura ya fara tashi a take wani kalar sautin kuka marar daaɗin ji ya karaɗe kunnuwan ahalin masarautar har ya kai ga gigita su.
"BOƊEJO!"
Kusan shine sunan da bayi, dogarai da kuyangi ke ta ambata a ruɗe, BOƊEJO wata macijiyace na gado wacce take da shekaru sama da ɗari tana kuma rayuwa a cikin wannan masarauta kaman laƙani ce na wannan masarauta kuma BOƊJO bata kuka babu dalili ta kan yi sau ɗaya idan yayi tsanani sau biyu a kowani bayan lokaci mai tsawo. Kasancewarta Jajazir a jiki da idanu masu firgici da banda sarki ko magajin sarki babu mai iya arba da ita ya wanye lafiya ya sa aka saka mata suna BOƊEJO dake nufin kalar JA.
Wasu da ba ma su taɓa jin irin wannan kukan mai firgici da tayar da hankali haɗe da ƙura mai tsananin duhu ba duk sun ruɗe, a take manyan fada suka ba da umurni mai girma na rufe kowacce kofofin masarautar kar kowa ya fita akwai matsala, abin mamaki BOƊEJO na yin shiru sansanin bai kai ga watsewa ba wani irin kiɗan Serewo (Algaita), Tambin (Ganguna) Da Hoddu (kalangu da sarewa) masu mafisar ƙarfi da daaɗi suka shiga tashi cike da sautin da idan ka ji ka san wannan ba dai mutum ke yi da baki ba, sojojin duk da yau ne karon su na farko a irin wannan yanayin sun yi tunanin ma sumame ne ko wani abu don kukan BOƊEJO babu biladaman da ba zai kaɗawa ƴar hanji ba.
Shi kam baya ya koma ya jingina da motar tare da lumshe ido kunnuwanshi na jiye mishi irin rububin da ake da umurnin da sarkin gida ke bayarwa na a binciko duk wani baƙo da ya shigo masarautar a yau ana son ganinshi a faɗa matukar namiji ne da gaggawa umurnin Laamiɗo ne, a take fadar ta zama babu shiga babu fita.
Wambai ne ya tuna da su don kusan aikin wambai kenan karbar baƙi da kulawa da al'amuran masarauta da sauri ya taho wurin shugabar tafiyar wanda General ne kuma abokin aiki ne ga Rayyan ba wai shugabanshi ba, hannu ya bashi suka gaisa yana bashi hakurin abin da ya faru da yadda aka manta dasu, General ɗin yace
"Ranka shi dade ai mu ba ƙaramin tsorata muka yi ba da wannan al'amari mun zaci sumame ne ake shirin kawowa hanyar sanarwar taku kenan!"
Wambai na murmushi mai nauyi da ma'ana mai tarin yawa yace
"Wannan kuka da kuka ji na macijiyar gadon wannan masarauta ce ta kan yi kukan nan a duk ranar da aka haifi Ciroma wato magajin sarki, haka ma wannan kiɗan kalangun kayan kida ne da suke zaune sama da shekara da shekaru da kansu suke buga kansu a duk ranar da aka haifi ciroman wannan masarauta."
Yana musu iso suka fara takawa zuwa ciki tunda ƙurar ya lafa sossai General ɗin yace
"Toh Masha Allah, an samu ƙaruwa kenan?"
"Ko kuma nesan da muka jima cikin tsumayi ta matso kusa ba, bismillah ku zauna za'a kawo muku ruwa"
Zama suka yi bai ba General din damar sake magana ba ya fice.
Laamiɗo dake tsaye har yanzu tun fara kukan BOƊEJO ne jiri ya kwashe shi ya tafi zai faɗi a sadda Sarkin ƙofa ya zo ya tabbatar da ba baƙin da suka shigo masarautar a wannan lokacin Galadima yayi saurin tare shi.
"Allah rene (Allah ya baka kariya) bi a hankali, Sannu!"
"Galadima ka fa ji kukan BOƊEJO ka ji kalangu taya za su yi motsi a banza tsawon shekaru talatin da ɗaya kenan basu yi kuka ba, dole ku je ku nema min Ciroma wlh shi ne!"
Dukda a hankali yake maganan kusan kowa a fadan na ji don sun yi tsittt ne, sun san ba lafiya ya cika ba a kwanakin sannan rabon da yayi dogon magana haka tun da aka sanar da shi ɓatan Gimbiya Aissatou(Aisha, na yi pronouncing yadda Fulani suke pronouncing ne).
Turaki ne da aikinshi ya zama ba sarki shawara yace
"Allah sene (Allah ya yalwataka da farin ciki) ko za'a bincika cikin baƙin sojoji da suka taho wannan ƙasa tamu? Don da alama baƙin cikinmu ne ke gab da yayewa."
Tsam ya miƙe a take dogaran da suke tsaye gefen hagu da damanshi suka fara jefa kirarin
"Gyaaaaraaa kintsi da kyau..! Taka lafiya mai talakawa"
"wambai kaini wurinsu"
"Allah ya baka yawan rai ba za'a yi ƙir...!"
Hannu kawai ya ɗaga mishi, a take manyan fada da duk suke tsaye suka rufa musu baya don tuni wambai ya shiga gaba.
Yalwataccen parlor ne mai cike da kayan alatu na sarautar zamani, an cika gabansu da tarin kayan itacuwa da ma ababen alfarma har da su ɓiradam ɗanyen tatsa, sun yi nisa da ci amma shi kam yana zaune ne kawai idanunshi zube a wuri guda, fuskarnan tayi ja idan ka zuba mishi idanu za ka fahimci baya cikin natsuwarshi don karfin hali ne ya ajiye shi wurin.
"Gyaaara kintsi da kyau..!"
Da ke ta ƙarato su ne yasa suka fahimci kaman mai martaban ne da karan kanshi ya taho hakan ya sa duk suka miƙe tsaye, General ɗin ne ya taɓa Rayyan hakan ya sa shima ya miƙe ya mayar da kanshi ƙasa yana jin yadda zuciyarshi ke tseren gudu, Laamiɗo ya shigo parlorn tuni kwarjini da girman matsayinshi ya saka su sake natsuwa, tsabar yadda yake jin a lokacin zai iya mutuwa idan bai yi ido huɗu da cikar Muradin shi ba binsu ya fara yi ɗaya bayan ɗaya yana kallon fuskokin su, jikinshi har rawa yake idanunshi sun cika tafff da kwallar marari da bege.
A lokacin da ya iso kan Rayyan ya tsaya kawai yana kallon irin tsawon Fulani da yake dashi, bambancin ya gina jikinshi hakan ya ɗan rage mishi tsawon kaɗan amma Dukda haka ya ma kere Lamidon da kaɗan.
"Babana!"
Laamiɗo Ya faɗa cikin wani karyayyen murya yana kai hannunshi ya dafa kafaɗar Rayyan da ya saka shi dolen ɗago idanunshi da suka cika da kwallah masu zafi suka haɗa idanu.
Jiri ne ya kwashi Laamiɗo ya tafi kaman zai faɗi tsabar wani abu da ya dake shi sai Rayyan yayi saurin sa hannu ya tare shi yana ɗaga idanunshi sama don hana hawayen shi zuba amma inaaa sun riga sun taho, Laamiɗo ya fusge facemask din dake fuskarshi cikin harshen fulatanci yake cewa
"Babana kaine? Da gaske kai ne a gabana? Sameeer..."
Za ka iya fahimtar ruɗu, farin ciki da tarin damuwa duka a cikin Muryar tashi.
A hankali Rayyan ya ce
"Abeey!"
Sai Laamiɗon ya rungumeshi shi kuwa ya ɗora kanshi a kan kafaɗar shi yana barin hawayen shi zuba cikin wani irin yanayi marar fasaltuwa, tuni jama'ar parlorn suka fara fita sai da aka watse tas aka bar su su biyu kachal rungume da juna, kan kace kobo kunnuwan masarauta sun fara aiki inda sashe sashe, bayi bayi, kuyangi kuyangi ake ta zancen dawowar Ciroma Sameer Muhammad Modibbo cikin masarautar bayan shekaru ashirin da shidda da ɓacewar shi.
Babbar macece mai cike da wani irin izza da ƙasaita da kana kallonta sai gabanka ya faɗi, bata da fara'a ko na miskala zarratin haka komanta tana yi ne cikin isa da wani irin mulki da ta saba shimfiɗawa cikin masarautar shekaru da dama, Fulani Adama kenan uwargida ga Laamiɗo kuma uwar ɗakin duk wata mace da zata shigo gidan ko a mata ko a kwarkwara tana da irin izza da har kan ba mutane tsoro, ga kafaffen zuciya da salo salo wurin shimfida mulkin son rai da samun duniya a tafin hannu.
Jeka-ka-dawo take a tsararren falon nata, sanye cikin shigan alfarma da kamshi na musamman tun kukan BOƊEJO na farko taji kaman an tsire mata zuciya ne hakan yasa ta kasa zaune ta kasa tsaye, duk wani abinda zai hana Fulani Adama natsuwa ba ƙarami bane, Shigowar Amintacciyarta da gudu yasa tayi hanzarin Juyowa tana zuba mata firgitattun idanunta masu kaɗa 'yar hanji.
"Allah ya ja kwanan Fulanin Laamiɗo, farin ciki masarauta, Uwargida kuma hasken zuciyar Laamiɗo uwar yarima da yardar..."
"Bana son ɓata lokaci Menene ya faru? An yi baƙi ne? Me ke shirin faruwa ne Balki?"
"Gobara daga kogi ranki shi dade..."
Baya baya tayi ta kai zaune cikin tsadaddun kujerunta hannayenta duk biyu dafe da Goshi.
A chan wani tsararren sashe cikin wasu kujerun alfarma Fulani Faɗimatu ce zaune fuskarta Jajazir idanunta har sun jirkice Dukda tsaf take cikin shiga ta alfarma da ƙawa kallo ɗaya za ka yi mata ka san cewa ba ta cikin natsuwar ta kukan BOƊEJO kaman ƙara mata damuwa cikin damuwarta yayi don ta gigice ta kasa zaune ta kasa tsaye a sadda Kuyangarta ta shigo ta zube ƙasa
"Allah ya kara miki lafiya da yawan rai, Allah ya kare gabanki da bayanki"
"Menene kande? Me ke faruwa?"
"GIZO BA YA HANA RUWA GUDU...! Zakarar da Allah ya nufa da chara..."
Dafe zuciyarta tayi tana fashewa da rikitaccen kuka mai tsuma rai.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*45*
"Babana...Sameer ka gane ni?"
Laamiɗo ya faɗa har lokacin gani yake kaman mafarkin da ya saba ne yana motsawa zai iya ganin Rayyan ya ɓace, rauninshi ne ke sake bayyana a gaban dattijon wanda dama tun yaranta shi ne mutum ɗaya jal dake ganin hawayen shi sai Baba Maudo wanda ke matsayin Galadima kuma ɗan uwa na jini ga mahaifiyarshi.
Hannun Abeey ya riƙe ya zaunar da shi tare da yunkurawa ya kai ƙasa kan gwiwowinshi gabanshi kanshi a ƙasa a hankali ya furta
"A gafarceni taƙawa"
Riƙo hannunshi Abeey yayi ya ɗago shi ya zaunar dashi gefenshi yana jefar da duk wani formalities na sarki don a yanzu uba yake.
"Da gaske ne kenan..! Kai ne da gaske nake gani Sameer? Ina ka shiga ka manta da asali? Me ya fitar da kai daga cikinmu ya nesanta ka? Wani irin rayuwa kayi a wani wurin da babu mu har zuwa wannan lokaci Sameer? Na yi nema! Na yi nema har yau ban fidda ran
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 40