ganinka ba ashe da rabon sake ganinka kafin in bar duniya!"
Yana maganan yana ta duba jikinshi ko zai ga wani alamun wahalar rayuwa amma ya ganshi fes kuma fresh don ko daga tafin hannunshi da ya riƙe ya fahimci yana cikin hutu da jin daaɗi Dukda haka sai da ya tambaya zamanshi Uba mai cike da yunwar ganin ɗan shi namiji ɗaya tilo da ya mallaka a duniya.
"Abeey ka kwantar da hankalinka don Allah, ni ne! Sameer ne a idanunka ba zan jefar da sunan da ka yi min yanka ba sai dai Rayyan ne a idanun duniya wanda shi ne sunan da hasken rayuwata kuma wacce ba ni da kamarta a wannan duniya ta bani... Abeey Aisha tana chan hannun azzalumai shine abin da ya kawo mu duk wannan za mu yi daga baya na tabbatar Abokan aikina suna chan suna jira na"
Kallonshi kawai Abeey ke yi yadda yake jera maganan da rashin cikakken fara'a mai tsanani da ya kamata ya gani a fuskarshi.
"Aisha na da muhimmanci kwarai kasancewarta mace cikin miyagu amma kai ma kana da muhimmanci Ciroma... Mahaifiyark.."
Da sauri ya katse shi
"Abeey...!"
Sai yayi shiru don bai saba katse maganan mai martaba ba, duk jimawanshi wani wurin an haife shi ne cikin masarautar kuma ya tashi da horo mai tsanani da kuma jarumta na asalin 'ya'yan sarki waenda ake musu mafarkin sarauta a gaba don haka yana sane da komai bai manta ba.
"Abeeyy ka yi haƙuri ka gafarceni ka bar maganarta for a while ina cikin farin cikin ganinka cikin koshin lafiya, adu'ar da nake ta yi kenan duk ranar da zan riskeka in riskeka cikin lafiya da kuzari in ga wannan farin cikin dake shimfide bisa kamilallayar fuskarka, ka haske ni da annurinka, ka cika ni da kwarjininka ka min hirar tarihin Fulani masarautunsu da ma al'adunsu..."
Muryarshi ne ke rawa ya mayar da kanshi ƙasa yana datse harshe don kuka ne ke zuwa mishi mai ciwo, shi kaɗai ya san irin raɗaɗin kewar mahaifinshi da yayi a wannan duniyar, shi kadai ya san irin halin da ya shiga na rashin shi kusa dashi ba tare da ya bari damuwar shi ya fita fili ba don ya san shi aka fi cuta, an cutar mishi da mahaifi ainun da baya tunanin zai iya yafe wa.
Mai martaba ma hawaye yake zubarwa, amma fahimtar wani abu da yayi ya sa bai iya sake magana ba suka yi shiru. Chan da ɗan jimawa ya ce
"Aisha! Ta ya ta ɓace Abeey?"
"Makaranta suka tafi da 'yar uwarta Zara'u akan suna da jarabawa dake ƙaratowa za su kai yammaci Dukda sun san ban yardar musu kaiwa dare a waje ba Fulani Adama ce ta ba su go ahead a kan za su dawo ba tare da na sani ba hakan ya sa suka yi dare har wannan al'amari ya faru anan yankin makarantar tasu dayake daga su sai Driver shima a raunane yake yana asibiti kwance"
"In shaa Allahu za mu tabbatar babu abinda ya same ta, lafiya za ta fito."
"Ku tabbatar da hakan Ciroma. Allah ya taimaka amma za ka dawo ko?"
Ya kalli Abeey.
"Zan dawo ko don saboda kai Abeey..."
Kallonshi kawai Mai martaba yake yi yana ayyana abubuwa masu dumbin yawa a ranshi. Ya girgiza kai
"Ba saboda ni ba dole ka dawo Sameer saboda al'ummarka da suke jiranka dole ka dawo saboda ba zan iya cigaba da nesanta da kai ba tunda Alhamdulillah kana raye cikin koshin lafiya."
Ba tare da ya ɗaga kai ba ya ce a hankali
"Wannan magana ce mai tsawo ranka ya dade ya kuma ba ka yawan rai, ina da family ina da kanne da suka dogara da ni sannan ina da Mata duk basu san wanene ni ba..."
Murmushi mai ciwo mai martaba ke yi duk Sameer ya taka waennan matsayi har ya kai ga Auren wata a waje ba Zara'u da aka bashi tun daga ranar da aka haife ta ba, yana da wasu zuri'ar da suka zama priority a gareshi da har bai iya ɓoye wa ba hakan ya sosa mishi rai ainun haƙiƙa ba zai bar duk abin da ya nesanta shi da Sameer ya sha a banza ba, Sameer dake da sunan babanshi amma yake ture sunan yake makala Rayyan bayan ga asalinshi, da kyar ya hadiye wani abu mai ɗaci
"Ina jiranka Ciroma, zan jira har ka dawo da ƙanwar ka cikin gidan nan daga nan za mu ɗora"
Kai Rayyan ya gyaɗa suka sake yin shiru na tsawon lokaci kan mai martaba ya miƙe tsaye Rayyan ma ya miƙe kanshi ƙasa ya furta
"Allah ya baka yawan rai ya ƙara maka lafiya da imani!"
Kai kawai mai martaba ya gyaɗa bai ce komai ba ya fice dogarai dake bakin kofa suka fara zabga kirari har ya wuce.
Rayyan ya ɗauki facemask ɗin shi ya mayar, ya zare bakin shade dake gefen aljihunshi ya saka ya gyara hulanshi ya fito daga parlorn, yana bayyana a waje hadimai da dogarai suka shiga zubewa.
"Allah hokke jam (May Allah give you peace) Ciroma Sameer ɗan Laamiɗo jikar Modibbo... Girman ɗa gado, Ɗan sarkin da ya san Allah, Ɗan sarkin da yayi haƙuri Ɗan jarumi gadon jarumta Ruwan sanyi mai dafa ganda... Murucin kan dutse baka fito ba sai da ka shirya Gobara daga kogi magani naka Allah, Damisa ba'ai maka kallon banza, sarauta dole in babu ku gari ya watseee.."
Sossai ya sake kamewa wannan jinin na sake bayyana kanshi da kanshi, takawa yake kaman ba zai tafi ba cikin sarauta har ya isa ga motar sauran sojojin da suke jiran shi da kallon mamakin al'amarinshi musamman waenda suka san shi su ke Binshi bai cewa kowa komai ba daga hadiman har sojojin ya shiga ya zauna suka fice daga fadar.
Kai tsaye mai martaba sashen Fulani Faɗimatu ya nufa dayawa suna mamaki don baya zuwa sassan matan sai dai su suje amma sun mishi uzuri kasancewar sun san iyaye ne da suke cikin murnar bayyanuwar ɗan su namiji tilo, wasu daga cikin gulmammu har an fara tambaye tambayen Meyasa bai je ga mahaifiyarshi kuma ya bar masarautar? Wasu na ganin barin shi da Laamiɗo yayi ya tafi ganganci ne.
Tana zaune har lokacin kuka take ta fara jin sanarwan zuwan mai martaba sashen ta, da sauri ta miƙe tsaye daidai yana shigowa ya tsaya ya zuba mata idanu yana kallonta chan ya ce
"Faɗimatu Me kika aikata?"
Kanta ta mayar ƙasa tana sake sakin kuka cike da tarin nadama da kunyar mai martaba.
"Ashe kukan nan da kike shekara da shekaru ba na rashin ɗa bane sai na yunkurin lalata rayuwarshi? Me na miki da kika zaɓi azabtar da ni da hannayenki Faɗimatu? Me na miki da kika zaɓi gani na cikin ciwo da azabar rashin ɗa tsawon shekaru ashirin da shidda? Me kika mishi da ko magananki baya ƙaunar ya ji anyi? Kin san zuciyar bafulatanin da aka hasala?? Kin san yara nawa ne da zuciya ya dibe su suka tafi tafiya na har Abada sun ki waiwayan baya? Ba sai na faɗa miki ba kin san wanene Bafulatanin mutum... Amma ina so ki san abu ɗaya na gode Allah da ya amsa min adu'ar dawo min da Sameer ba zan taɓa mishi dole ya kalleki ba idan baya so..alhakin mu da kika dauka kuma wannan tsakanin ki da rabbissamawati"
Sossai take kuka tana girgiza kai, mai martaba masoyinta ne in ta ce bai kaunaceta ya ɗaga darajar ta cikin mata da kwakwarayenshi ba ta yi ƙarya, duk wata kulawa ya bata ya tausaya mata dukda yana cikin damuwan shima amma ya rarrasheta a lokacin da yake tunanin za ta fi shi jin zafin ɓatan danta, kwarai ta fishi ita da bata san inda yayi ba bayan nan ita da alhakin shi ke maƙale a wuyanta na tsawon wannan shekarun zuciyarta bai huta ba, idanunta basu tsagaita da zubar kwallah ba.
"Ranka ya daɗe ka gafarceni, ka tsaya ka saurari uzurina don Allah..."
Ɗaga mata hannu yayi
"Ba ki da uzuri Faɗimatu baki dashi..! Babu uzurin da zai wanke bakin cikin da nake ciki a yanzu you were the last person i've expected that from, am very disappointed..."
Katsewa magananshi yayi jin sanarwar isowar Fulani Adama, da kuka ta shigo
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah mun gode maka ya Allah da ka share mana hawaye ka amsa adu'ar mu ashe Magaji na raye? Ashe muna da rabon sake ganawa? Mai martaba sashen ka nayi don wannan babban abin murna ne sai ake sanar min kana nan ashe... Ina yake? Ina Sameer in ga yadda ya sauya ya zama mutum cikakke?"
Har yanzu idanunshi da suka sauya suna kan Fulani Faɗimatu kan ya janye ya kalli Fulani Adama yace
"Alhamdulillah yana nan lafiya Fulani, a yanzu ya tafi abinda ya kawo shi wato tseratar da kanwanshi."
"Alhamdulillah! Ashe rayuwa ya inganta Soja ne ashe?"
"A sojojin ma ba laga-laga ba. Na bar ku lafiya"
Yana kai nan ya juya ya fice.
Ta kalli Fulani Faɗimatu tana murmushi
"Barka na taya ki murna Faɗimatu"
"Ai ke ce uwa a gareshi Fulani ke ya kamata mu taya murna.."
"Kwarai kuwa! Gashi ya zo a gaɓar da matarshi ma ta isa aure gwara da muka jinkirta aurar da zarah ashe alƙawari zai cika"
Kai ta gyaɗa bata iya tace komai ba don a gigice take, ta sake murmushi tana ta kallonta kan ta juya ta fita, zubewa Fulani Faɗimatu tayi kan kujera bata zaci lamarin zai kai haka ba, kuruciya ne da buƙatar uwa na ganin ta ba abinda ta haifa kariya ya sa ta aikata bata zaci abin zai zama mata haka ba sam, tun daga ranar take nadama har yau.
Ko motsi bata sake yi ba sai ga Fulani Aminatou itama murna ta zo tayi mata bata kai ga fita ba sai ga Fulani Salimah itama ta mata murna duk amsawa take amma tana sane da wanda ya kai ciki da wanda bai kai ba Dukda duk yanzu ba sune gabanta ba.
Duk rubibin da ake
Madaki da Makama suna zaune ne tamkar a kan ƙaya fata kawai suke sarki ya ce ya sallame su su samu su keɓe aiko Galadima na sanar da tashin Fada kai tsaye su biyun ganawa suka nemi yi da Fulani Adama.
"Balki ki sanar da su ba yanzu ba da kifi ya riga ya ruɓe su bari sai ya daina wari za mu tattauna"
Da sauri amintacciyarta bilki ta amsa
"an gama Allah ya baki yawan rai"
Tana kai nan ta fice taje ta kai saƙon suka kalli juna suka juya suka tafi babu mai uhm bare uhm uhm.
****
Shi kam Rayyan komai ya watsar suka shiga kokarin ganin sun tsara yadda za su kubutar da su Aishatu cike da hikima irin ta squad ɗin tasu na musamman da aka turo wannan aiki, lokaci lokaci ya kan yi tsaki kaɗan har dai aka gama kuma akwai alamun nasara don sun samu haske sossai daga ƙiran da aka yi na biyu.
Bayan sun gama zaman ya nufi ɗakinshi kai tsaye wanka yayi saboda gajiyar da yake ji ainun jikinshi, ya fito ya shirya cikin kayan baccinshi ya nufi gadon ya kai kwance kaman jira ya fara jin ta jikinshi, emptiness da bai san na menene ba ke ratsa shi ji yake gadon yayi mishi faɗi ƙwarai, shafa cikinshi yayi da bai ci komai ba tun safe da tana nan da ta fara mishi puppy face tana roƙon shi ya ci wani abu wane cikinta ne tsintar kanshi yayi da ɗan murmusawa a fili yace
"Yarinyar ta cika tsoro"
Yana maganan yana tuna idanunta in ta ji muryarshi ko idan yayi mata tsawa. Daga karshe da ya ga ba zai iya bacci ba dole ya tashi ya sha coffee ya koma ya kwanta ya janyo wayanshi ya tafi numbern ta da ya karɓa da safe kawai ya yanke bin shawarar zuciyarshi na ko muryarta ne yaji ya danna wa ƙira.
Tana kwance tun tuni ko shirin bacci bata yi ba, takardu ne gabanta amma ta kasa karatu sai tunaninshi take ya je lafiya? Ya ci abinci? Sun fara aikin? Ta rasa natsuwa duk adu'arta na salollin yinin akan Allah ya kare mata shi ne ya bashi sa'a a duk abinda ya sanya gaba, tana nan tana juye juye a kan gadon sai ga ƙiran shi bata san Layin ba don bata dashi.
"Waye ke kirana ƙarfe sha ɗaya?"
Tayi tambayar tana sake kallon lokaci kaman ba zata ɗaga ba ta zo dagawa ya yanke, ya sake ƙira karo na biyu dole ta ɗaga ta makala a kunne bata yi magana ba shima sai bai yi ba suka yi shiru suna sauraron numfashin juna, chan tace
"Waye ne? Meyasa ake kira a irin wannan lokaci?"
Ya tsinci kanshi da wani kalar murmushin da bai fi second biyu ba, ashe ta iya tsiwa shi ne take yi wa puppy eyes na tsoro.
"Idan babu abin faɗa zan kashe don ina da abin yi..."
"Ba ki iya sallama ba?"
Daram gabanta ya faɗi tayi saurin Miƙewa zaune tana sake riƙe wayan da kyau Ya Saraki ne, tuna abin da ta faɗa da farko yasa tayi saurin cewa
"Kayi haƙuri ban san kai ba ne Assalamu Alaikum warahmatullah"
Ya amsa sallamar
"Me kike yi ba ki yi bacci ba har wannan lokaci?"
Ta kalli takardun gabanta tana mamakin yadda ya ƙirata har yana ɗan magana Dukda maganan kaman za'a yi kaman ba za'a yi ba yake jefowa.
"Abu nake yi ne shiyasa ban kwanta ba."
Shiru yayi idanunshi a lumshe yana sauraron muryarta.
"Abin babu suna?"
"Karatu!"
Ta amsa suka ɗan yi shiru ita dai har hannayenta sun haɗa zufa nervousness da kyar ta fitar da abin da ke ranta kan yayi magana ta ce
"ka isa lafiya?"
Buɗe idanunshi yayi ya zubawa wuri guda Mammi ce ke faɗo mishi a duk sadda motsin yarinyar nan ya shige shi sai ya rasa Meyasa yake tuna Mammi, yanzu haka abinda yaji Allah ne kadai ya sani. Mammi ce kaɗai duk inda zai je sai ta tabbatar da isan shi lafiya, ita ce yake yawan jin wannan kalmar daga Bakinta ba wata ba.
Jin shirun yayi yawa tace
"Hello!"
"Lafiya! Ki ajiye abin da duk kike ki kwanta"
Ta amsa da Toh
"Kar ki kashe!"
Chak ta tsaya da yanke call din ya ɗan kausasa murya
"Ke kika ƙira ne da za ki kashe?"
Ta haɗe lips ɗinta shi dai ba'a yi mishi ba za'a zauna dashi a wanye lafiya ba.
"Afuwan"
Ta faɗa chan ƙasa a hankali da ya saka shi sake lumshe idanu.
Miƙewa tayi da wayan a kunne ta tattare duk takardun ta saka a speaker kar yayi magana bata ji ba ta shiga uku ta chanza zuwa kayan bacci ta kashe wuta taje ta hau gado.
"Na gama."
Duk motsinta yana ji.
"Ba kya alwala ne idan za ki yi baccin?"
"Manta wa nayi!"
Bai ce komai ba taje tayi alwalan ta zo ta zauna tayi Adu'a ta shafa duk yana jinta kan ta kwanta tayi shiru.
Bacci ne ya ci karfin idanunta don bata saba hira ba saboda bata yin baccin da safe ko rana ta riga ta saba tun chan. Cikin Muryar bacci tace
"Sai da safe ya Saraki"
Ya ja numfashi a hankali don Muryar ya isa inda bai kamata ya isa ba, yana sauraron komai har tayi bacci kan ya katse ƙiran ya ajiye wayan kan kirjinshi da kyar baccin ya ɗauke shi cike da tunanunnuka.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*Masu tambayar daga farko a yanzu za ku yi haƙuri ku jira a ƙarasa don abin da ya saura babu yawa sossai a haɗa doc ayi distributing gabaɗaya because pages almost 50 ba abu bane mai sauki in ta forwarding please bare with me*
*46*
Kwanakin da suka biyo baya sun zo mishi da tarin ayyuka haɗe da zirga-zirga ta yadda ma wani daji suka koma suka yi camping don dai ganin an ceto su Aisha a hannun waennan Ƴan garkuwa da mutane, inda yake ko service babu hakan ya sa ya manta rabon da su yi waya ko da Abeeha ce kuwa bare Afeefah da sau biyu ya taɓa kiranta gashi har an ci tsawon sati uku suna abu ɗaya ba su ƙare ba, sun yi namijin kokari duka team ɗin wanda suka hada har da taimakon wasu airforce, polisawa da 'yan sa kai da ake cewa Hunters a cikin sati na huɗun suka samu gagarumar nasara bayan kubutar dasu sun kubutar da dayawa daga cikin waenda abin ya ritsa dasu kuma sun samu nasarar hallaka dayawa daga cikin miyagun.
A yau da ya kasance Juma'a suka iso cikin garin Fombina zuwa masarauta, kai tsaye aka musu iso don an san da isowarsu kuma an shirya musu tarba na musamman, ko bai nuna ya san Aishan ba ma itama daga ita har Zara da yake a tsorace suke har lokacin ba tantance kowa suke yi ba sai da suka gansu tsakiyar masarauta kai tsaye sashen Uwar ɗakinsu Fulani Adama aka yi dasu ta fito ta rungumesu tana hamdala nan suka saki kukan da ya gama cin su a rai.
Shi kam Rayyan na cikin baƙin fada inda sarki ya nemi da su koma masaukinsu su huta kafin ya gana da su ko zuwa dare don yanzu yana ta samun baƙin taya murna daga kananan hukumominshi da na shuwagabannin rugagen dake kewaye da Daular fombina, Rayyan ya tashi zai bi bayansu Laamiɗo yayi gyaran murya ya furta
"Ciroma!"
Chak ya tsaya, ya dawo da baya ya koma zaune
"Allah ya baka yawan rai!"
"Bisa tsarin umurnin da na yanke, ka shigo kenan Sarkin gida zai maka rakiya zuwa sashenka an tanadar maka duk wani abin da zaka buƙata ka je ka huta iyayenka na bukatar ganawa da kai."
Da wani irin hanzari ya ɗago ya kalli mai martaba sai kuma ya mayar da idanun ƙasa ganin duk idanun manyan fada na a kanshi, Miƙewa yayi
"Na barku lafiya!"
Daga haka ya fice sarkin gida yayi saurin mara mishi baya, a wajen ma dogarai shidda ya gani sun rufa mishi baya kuma ya san sune aka yi assigning don kare lafiyarshi haka kawai yaji kaman an takura shi.
Sashe ne na musamman tsararre ya ji furnitures da komai da komai masu tsada da ɗaukar ido amma shi bai wani burgeshi ba tunda ba tatse ɗin shi bane, ɗakuna huɗu ne a sashen ya nufi wanda sarkin gida ya nuna mishi shine nashi ya shige ba tare da ya ce mishi komai ba yayinda sauran dogaran suka kafe a bakin mashigar sashen.
Komai kuwa akwai ko da ya buɗe wardrobe kaya ne kala kala kawai gasu nan, manya da kananu Dukda ya san idan ba a cikin sashenshi ba a yanzu saka kananun kaya ma yayi yawo da su a cikin masarautar ya haramta mishi, kayan jikinshi ya zame ya shiga wanka ya jima sossai kan ya fito ya shirya cikin karamin three quater baka da wata karamar riga fara ta kama shi ta fitar da surarshi na cikakke kuma karfaffen namiji, wayanshi ya zara ya fito parlor sai ya samu an cika dining ɗin da kuloli na alfarma wanda ya san abinci ne ciki.
Gyaran murya yayi da hanzari dogarin dake dab kofa ya faɗo ciki ya zube ƙasa
"Allah ya ja da zamanin Ciroman fombina, Allah ya kare gabanka da bayanka ubangidana, gaba salamun baya salamun naka faɗa ne namu cikawa...."
Hannu ya ɗaga mishi
"Daga ina aka kawo wannan?"
Ya jefa tambayar yana ɗora kafa ɗaya kan ɗaya a lokaci daya yana dan karkaɗawa idanunshi zube a kan screen ɗin wayanshi
"kuyangin Uwar magajin sarki ne suka shigo dashi ranka ya dade...."
"Ku tattara ku fitar min, daga yanzu ban amince a shigo min da abincin ko wani sashe ba don ba na buƙata!"
Cikin ba da umarni yayi magana hakan ya sa dogarin sake zubewa
"An gama sadaukin maza..!"
Da wuri yaje ya fara tattare wa shi kam yana zaune shiru don ya gwada Layin Afeefah bai shiga ba na Abeeha kira daya ya mata bata ɗaga ba kuma bai sake kiran ba.
Damuwar shi yadda mai martaba ya ba da umarnin dawowanshi kenan ya san ba zai taba amincewa ya tafi ba amma kuma idan ya zauna kaman bai yi adalci ba, bai kamata kawai su Uncle Musa su ji cewa ya dawo gida ba dole yana bukatar komawa da su su san asalinshi ya tattauna da su da tsara yadda za'a tafiyar da rayuwar su Abeeha da yake jin banda aure babu wanda ya isa ya ce zai karbi riƙon Abeehar don kawai ya dawo gida har yanzu shi a jinin Maami yake kallon kanshi kuma a hakan yake so ya tabbata don haka dole ne ma ya ga sarki.
Time ya kalla karfe tara ne kwata kwata da mintuna ashirin, Dukda baccin da ya tarar mishi dole yaje ya ga sarki ya san karfe goma zai koma turakarshi don fara shirin tafiya masallaci, Miƙewa ya yi ya koma ɗaki ya shirya cikin wasu navy blue kaftan da ya sha ɗinki irin na sarauta, ya saka hular da ta dace da kayan ya zura takalmi ya fito hannshi riƙe da waya amma sai ya tattaresu ya goya a baya ya fice daga sashen dogaran na ganinshi suka rufu za su bi shi ya juyo ya kalli shugabansu.
"Sunanka?"
"Gaabɗo ranka ya dade" (Joy yake nufi)
"sauran su zauna kai ka biyo ni"
Yana kai nan ya juya da sauri Gaabɗo ya bishi har turakar mai martaba duk inda ya ratsa hadimai za su zube suna kwasar gaisuwa kai kawai yake ɗaga musu, sai da aka sanar da isowarshi kan ya shiga, ya ci sa'a mai martabar ma na son ganinshi da kallo yake ta Binshi har ya zauna a ƙasa kaman yadda me martaba ke zaune cikin shimfida na alfarma ya kishingida da tun tun.
"Abeey barka da wannan lokaci"
"Barka dai Ciroma, na san ka ji hukunci na kuma kana tunanin bai maka daaɗi ba amma abin da zan iya cewa kenan Sameer ba zan bari ko kusa ka sake subuce min ba, Kukan BOƊEJO da ma sautin kalangun gado sun isa su tabbatar maka da cewa kai ne mai jiran gado"
Numfashi ya ɗan sauƙe yace a hankali
"Abeey ka yi haƙuri da abin da zan faɗa ba zan saɓa umarninka bane amma zuri'ar da na ajiye a chan sun fi karfin na sanar da su cewa na dawo nan a waya, ɗiyar su ta zame min uwa da uban da na rasa a rayuwata tsawon shekaru ashirin da shidda bata taɓa gajiyawa da hidimata ba, bata taɓa min kallon banza ko Harara da sunan tsana ko kyara ba, ta gatanta ni ta fifitani fiye da komai da ta mallaka a duniya ciki har da miji da 'ya'yan cikinta, Abeey duk yadda zan fasalta maka irin son da Mammi tayi min ɓata baki ne duk kuma ta yi bata san ni waye ba har sai da take kwance a gadon mutuwarta a haka roƙona tayi da in dawo in samu farin cikin da na rasa, in dawo in ji uzurin...." Sai bai ce komai ba ya duƙar da kai.
Hadiye abin da ya taso mishi yayi kan ya cigaba
"Ban shirya dawowan ba na riski labarin ɓatan Aisha bayan ma ƙiran da shugabanmu yayi min na ina cikin team da aka yi assigning wannan aiki na taho ne ba da shirin dawowa b.."
"Muhammad Sameer"
Laamiɗo ya kirashi runtse ido yayi don ya san bai amince bane.
"Ka ba ni labarin abinda ya faru daga barinku gidan nan da mahaifiyarka, na dai san ta nemi izinin tafiya chan mambila wurin dangin mahaifiyarta kuma na bata izini da driver da kuma amintacciyar Kuyangarta sai labari marar daaɗi aka dawo min dashi da sunan ka ɓace a tsaunukan mambila an neme ka an rasa na kwashe tsawon shekaru ban bar kowani hukuma sun huta ba da neman ka har wasu suka zartar da cewa ka mutu ni ban yarda ba hakan ya sa a kullum nake Adu'a duk juma'a nake sadaka duk goman karshe na kan manta kaina ina rokar maka kariya da nasara a duk inda kake da Fatan Allah ya bayyana min kai ya tsare maka imaninka me ya faru? Meyasa daga kalamanka na yarda Ammienka na da hannu dumu dumu akan abin da ya faru?"
Kanshi na a ƙasa ya shiga magana kana jin ɗaci a saman harshenshi a kuma hankali yake maganan
"Abeey bayan mun yi muku sallama mun bar nan tafiya ne mai nisan gaske muka dauka ba tare
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 40