Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
saka karatun qur'ani tana aikin har la'asar kan ta gama ta adana akwatunan ta tafi tayi alwala ta zo tayi sallah, tana zaune taji ana mata knocking ta miƙe taje ta buɗe sai ta ga Abeeha ce murmushi suka sakarwa juna ta shigo ciki. "Cigiyarki na zo yi tun fa jiya rabon da mu haɗu matar bross" Tana ɗan murmushi tace "Da kin taimakeni in kika daina dangantani da wannan Yayan naki, Mammi ma da take faɗa bani da yadda zan yi ne" "Toh Meyasa? Ke ba matar tashi bace?" Abeeha ta faɗa tana zama kan couch na ɗakin. "Gabana faɗuwa yake a duk sadda aka dangantani da shi, ban sani ba tsabar yadda nake jin shakkarshi ne ko yaya" "ke fa ba mu bane Afeefah, ya kamata ki rage wannan tsoron nashi wlh ko mu bama mishi irin tsoron da kike mishi ke matarshi ce sirrin shi, a ina kika taɓa ganin matar dake shakkar mijinta? Lalalalala idan kika tafi a haka ke za ki cutu" "Adda Abee ba za ki gane bane ke kam, ya saleem ɗin ya shigo? Kin ganshi? Ya ci abincin?" Kallonta Abeeha tayi "Eh ya shigo, sun ci har ya tafi ma tun azahar" Ajiyar zuciya ta ɗan sauƙe suka cigaba da hira da Abeehar, Abeehar na nuna mata tayi amfani da trainings da aka yi mata kar kudin Mammi ya tafi a banza ita dai sai dariya take don ko tsireta za'a yi ba za ta iya ba wlh, sai Magrib Abeeha ta tafi ita dai Afeefah bayan tayi isha ta fito ta samu an kawo musu abinci kaɗan ta ɗiba ta koma ɗakin don ko haɗuwa bata so su yi. Daga ranar kullum Saleem sai ya shigo kuma Mammi bata taɓa ƙasa a gwiwar basu tofin ba yayinda bayan an gama abin kari Abeeha ke shiga kitchen da kanta ta musu girki tunda anan yake cin abincin rana har kwana bakwan, kafin ta gama girkin take zuwa ta gaishe da Mammi bayan ta gama ma ta kan leƙa ta kan ta wuce sashenta bata sake zuwa sai gobe tunda ya hana gwara ta bi umurninshi ba tare da ta san dalili ba, a sashenta take zama tayi karatu tayi bacci ta gaji gashi bata iya zaman parlorn don bata so su haɗu kuma kaman ka'ida tun daga ranar basu sake haɗuwa da shi ba har kwana bakwan ya wuce don ko abincin dare ana kai musu zata je ta diba ta shiga ɗakinta ta rufe. Adu'ar ta kuma a koyaushe shine Allah ya dubi Saleem ya yaye mishi wannan bala'in. Ta ɓangaren saleem tun daga ranar da ya fara zuwa wurin Mammi yana shan tofin kuma yana ci a abinci ya fara jin wannan nauyin na zuciyarshi na raguwa, kanshi da kaman an daddaure baya wani tunani mai kyau ya ji kaman ana kwakwance jijiyoyin, bai dai nuna komai ba don tun bayan kwana biyu da ya fara zuwa Sabreena ta saka shi gaba Meyasa yake zuwa gidan aboki yake cin abincin rana bayan bata Gaza ba wurin cinshi? Meyasa ma yake zuwa gidan su Rayyan ɗin abin da baya yi da kaman ka'ida kullum sai ya je? "Sabrina yaushe ya zamana in zan fita ko zan yi mu'amala da wani sai na bi ra'ayinki ne kam? Meyasa za ki damu da abin da bai shafe ki ba? Yau na fara cin abinci a gidan aka ce miki? Toh bana son damuwa da ciwon kai idan maganan da zaki cigaba da yi kenan ki tashi ki bani wuri" Da wani irin tsantsar mamaki take kallonshi Za Ta yi magana ya daka mata tsawa "Ki fita nace!!" Da sauri ta miƙe ta fita har tana haɗawa da sassarfa bata tsaya ko ina ba sai wurin Gaje don babanta baya nan ya fita. "Mun shiga uku! Gaje Ya Saleem yau ni yake yi wa tsawa! Me yake shirin faruwa?" "Ke ki natsu dallah chan me zai faru kuwa? Ya wuci kin je kin dameshi ne yana so ya huta, ki fa sani ko da mallakarshi da muka yi sai kina bin shi a hankali" "Gaje bai fa taɓa ɗaga min murya ba tunda na shigo gidan nan ina tsoron kar wani abu ya faru ne" "Babu abin da ya faru daga ni har mahaifinki muna da yakini kan aikin da aka mana har abada ba zai kwance ba, ki bashi lokaci sai ki koma" Ko da ta bashi lokaci ta koma bai yi mata magana ba, sai ta yarda da cewa ita ce ta takura mishi don haka bata kara magana akan zuwa gidan su Rayyan ba, yau ya shigo gidan sai ya tsaya chak a parlorn yana bin sababbin kujerun da kallo, a hankali ya tsayar da idanunshi kan kujerar da mommy ke yawan zama, tunanin mommyn ya fara sai yaji kanshi ya wani irin sara gabanshi ya shiga faɗuwa zuciyarshi na bugawa da ƙarfi da ƙarfi daidai Sabrina ta fito ganinshi dafe da kujera ya sa tayi hanzarin isa kanshi "Ya Saleem lafiya? me ya sameka? Menene?" "Ƙira min Mommy!" Darammm ta ji zuciyarta ya buga... **** Kawu Labaran ne riƙe da Ghana most go yana kallon Inna Larai dake ta juya kai tana fama da suntumemen ƙafarta da kudaje ke ta sukuwa a kai yace "Ki yi min adu'ar dacewa ai na ji unguwar da ɗaya kawun nashi ya ambata chan zan je in tabbatar da gidan da Afeefar take sai na dawo da ita ta kai ki asibiti don ni dai ba ni da wani kudin asibitin birni! Kin ga dama ke ce uwar ɗakinta..." Inna Asabe ta katse shi "Malam anya za ka yi hankali kuwa? Wani irin zance ne kake yi hakan? Taya Afeefah zata fara taimakon mu bayan duk abubuwan da suka faru? ka manta ita da kake ikirarin itace uwar goyon nata ko ɗakinta bata taɓa bari Afeefar ta taka ba?" "Amma dai mun ciyar da ita kuma mun tufatar da ita, har ɗaki sukutum muka ware mata tayi rayuwa kaman 'ya'yan gidan nan ni ko hassada kike yi min ne ma kin ga zan je birni?" "Allah ya kyauta in maka hassada, ina dai tunatar da kai ne ita Larai ɗin me ya hana 'ya'yan ta yi mata? Mugun alkaba'in da muka bi yarinyar nan dashi shi muke gani a wurin namu yaran daga masu shaye shaye sai masu cikin shege ana ɓararwa a maimakon mu fara tunanin laifin mu mu fara neman hanyar gyara ka sabi jaka don son zuciya zaka tafi neman kudi wurin wacce ka yiwa korar kare a gidan nan..." "Na rantse ko ki min shiru ko in saka sandata in Buge ki, ni zaki faɗawa maganar banza? Idan wulakanta Afeefar ne duk wa ya more ta bayan ku? Ina ce anan kullum take dawo muku da kudaden da take samo muku ni me na taɓa sakata sayar min? Ko ba kece kullum dare kike hayaƙin tafarnuwa da kuka da Ƙashin kifi ba duk saboda Afeefar? Idan akwai waenda ba zata yiwa abu ba sai dai ku, ni kam dolenta idan ma bakin ciki kike min sai na je... Ke kuma Larai ki jirani in dawo" Yana kai nan ya juya ya fice, inna Asabe ta bi shi da kallo kan ta mayar da kallonta kan Inna Larai dake zaune varender ɗinta a yanzu ko tafiya bata iya yi, komai sai an yi mata ga yaran nata kan su yi mata sai ran kowa ya ɓaci sun yi ta mita da kananun maganganu kenan, abinci wannan tunda kawun ba wani ciyar dasu yake ba sai in Asaben ne taji tausayinta ta bata daga wanda ta dafa a 'yar sana'ar da take yi na cikin gida. Wa'azi taji a redio ranan da ya sakata zurfafa tunanin akan sharrin dake bibiyar 'ya'yensu gashi dai sun haifa amma a yanzu babu ɗaya da za'a cire na ƙwarai, sai yanzu wani abu ke shiganta akan neman ilimi barin ma da taji neman ilimin addini farilla ne kan kowani musulmi kuma baka da hujjar kare kanka da rashin sani a wurin ubangiji muddin baka nemi ilimi ba, tunda ta san lokacin da ake sa wa'azuzzukan sai ya zama kullum da hantsi sai ta ji anan ta fara tunanin daga ina ne rayuwarsu ya kuskure tun farko...? Shi dai Kawu Labaran machine ya hau har ya fito kauyen gaba da su ya samu mota da ya kawo shi farkon garin Kaduna ya dire, nan ya tsaya zare ido tunda yake bai taɓa shigowa cikin Kaduna ba bari dai kauyuka yana zuwa sossai musamman na bayansu amma bai taba zuwa babban birni haka ba, zare ido yake tayi yana kalle-kalle wani mota ya tsaya kusa dashi wasu maza huɗu ne ciki "Ya dai ina ka nufa?" "Na zo wurin 'yata ne tana nan cikin gari" "Wani unguwa?" "Ni dai ban tabbatar ba amma kaman unguwar masu kuɗi ne wai G....A...R" Da kyar ya fadi alpabets ɗin suka tuntsure da dariya "GRA kake son cewa?" "Yauwa eh nan fa dai..." "Shigo" Shiga yayi yana washe haƙora yau dai Allah ya nufa gashi a birni basu yi nisa ba ya ga duk sun saka facemask kan yayi magana sun ja window suka fesa mishi wani powder nan ya sulale ya sume... **** Tsaye yake gaban madubi, wanka ya fito daga shi sai towel jikinshi, ginannen jikinshi fari tasss sai daukar ido yake saboda ruwan dake bin murdaddun damatsanshi zuwa parks da ya tara a ciki, madubi ya kurawa idanu yana tunanin irin yanayin da ya shiga a daren jiya wanda rabon da ya ji kwatankwacin hakan sama da shekaru ashirin da biyar, da ƙarfi ya runtse idanunshi da suka yi wani irin jajazir yana fesar da huci daga bakinshi tsaki ya ja a karo na babu adadi ya miƙa hannu zai ɗauki mai kenan aka turo kofan aka shigo da sauri ya ɗago sai idanunshi suka sauƙa kan....! 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh ADABI WRITERS ASSOCIATION *FREE BOOK* *Alhamdulillah na gode sossai da adu'o'inku gare ni jiki da sauƙi sossai ku lallaɓa da wannan kafin gobe na sake samun ƙarfin jikin, Allah ya bar ƙauna masu kira duk na gode sossai* *36* Ƙoƙarin buɗe idanun da suka yi mishi wani irin nauyi ya fara yana jin yadda fatar jikinshi ya ɗauki raɗaɗi tamkar wanda aka ɗora saman tukubar tsire, kaman ruwa haka tunanin abin da ya faru ya kwararo mishi cikin kwakwalwa har bai san ya buɗe idanun ba tare da yunkura wa ya zauna yana zaro su waje. Wasu garadan matasa ne tsaye kusan su huɗu cikin ɗakin daga kawunansu har kafafunsu a rufe "Su...su su waye ku?" Kalaman suka fito fitt ba tare da ya shirya ba, babu wanda ya amsa sai chan bayan ya gama zare ido yana jin cikinshi na ɗurar ruwa kan ɗaya ya matso ya ja wani kujera ya zauna tare da riƙe haɓar kawu Labaran cikin hannunshi "kai kalle ni nan! Nan ba wurin wasan ka bane idan ka yi abin da muka umurceka lafiya lau zaka fita amma idan ka yi akasin hakan hahahahaa" Ya saki wani dariyar bosawa "za ka yabawa Aya zaƙin ta don ungulu muke bama jewar banza" Wani irin kuuuuuuuuu cikin kawu ya bada ƙara jiki shi ya shiga rawa kar kar kar "Me ku..ke so" A rarrabe yayi maganan harshen shi har yana sarƙewa. "Ba ni lambar yarinyar taka dake GRA!" Ya faɗa yana zaro waya. "Ba ni da shi wlh bani da shi..!" Kawu ya basu amsa har lokacin jikinshi bai daina rawa ba. Kallon kar ka raina min hankali yayi mishi kafin yayi wani yunkuri mutumin ya sauke mishi wasu zafafan maruka da ya sa ya daina ji da gani na mintuna, wani ƙaraa yake ji suuuuu a cikin kunnenshi da kyar ya iya jiyo zancen mutumin cikin hargagi "Ni za ka rainawa wayau?? Ka manta abin da na gama ce maka ko? Toh kan in sauya kamanninka maza maza ba ni layinta" Kuka kawu ya fashe dashi da karfi bayan dawowa hayyacinshi yana rantse rantse babu irin azabar da ba su mishi ba amma shi ya san bashi da wani Layin Afeefah, da kyar suka kyale shi "Ka yi maza ka fara tunanin Layin nan in ba haka ba sai na tabbatar na sauya maka kamanni yadda babu mai iya gane ka! Kuma zan saka flyer in tsige faratunka ɗaya bayan ɗaya kan in jefawa kungiyar mu kai su san yadda za su yi da jini da tsokar ka don na faɗa maka idan ma kana kokarin ɓoye kudinka ne za ka ba da jiki da jininka...." Kawu bai san yana fitsari ba don tsabar tashin hankali, bilhakki yake kuka yana neman afuwa sai da suka gama azabtar dashi suka juya suka fice suka bar shi nan yashe. Bai san adadin lokutan da ya dauka cikin azaba ba, chan ya ji ana kwarara mishi ruwan sanyi a razane ya farka "Wlh zan...zan ba da Layin... Zan ba da layi" Numbern su Larai ya bayar aka ƙira aka saka shi yin shiru. "Yanzu haka mijinki na hannun mu muna bukatar kuɗi kimanin Naira Miliyon goma ko kuma ku da ganinshi har gaban Abada..." Salati ta kwarma da ya ja hankalin Inna Asabe da sauran yaran suka taho. "Ke! Natsu!!" Ya sake daka mata tsawa tuni ta shiga taitayinta ya miƙawa kawun waya a rikice cikin tashin hankali yake cewa "Larai ku taimakeni... Akwai kudi a ɗakina ƙasan gado ina da 'yar rami a ciki akwai tulu na binne za ku samu kuɗi...ku..ku haɗa har da gonan gado na ku sayar da gidan da muke ciki ku basu duk abinda suka roka don Allah...zasu kashe ni ku taimakeni" da kuka sossai ya ƙarasa. Inna Larai manta halin da suke ciki tayi "Au dama kana da wannan uban kuɗin ka ƙi kaini asibiti? Lallai ka cika azzalumi..." "Ke kina da hankali kuwa?" Ya ƙare maganan yana sanyawa kawu bindiga a makoshi wani irin ihu ya kwarma yana cewa su taimake shi kar su kashe shi "kun ji abin da yace ai ko? Toh idan kuna son shi ku aikata ku kawo mana kuɗin idan kuma akasin haka za ku tsinci wasu sassa na jikinshi a cikin Ghana most go...kuka sake kuka sanar da 'yan sanda dukkanku sunayen ku gawarwaki..." Yana kai nan ya katse wayan suka fice suka bar kawu cikin halin ha'ula'i sai kuka yake wane karamin yaro don bai taɓa zaton haka tashin hankalin kidnapping yake ba. A chan kuwa Dutsen-wai tunani suka fara na yadda za su nemi masu sayan gona da gidan da suke ciki, inna Asabe ta tafi ta ɗauko kudaɗen da yake magana duka duka basu fi dubu dari biyar ba a hakan ma mamaki suke na yadda ya iya boye irin kudin suna cikin talauci da wahala, nan yaran suka tashi akan ba za'a sayar da komai ba idan kwananshi ne ya ƙare Allah ya ji kanshi amma ba zai mutu ya bar su basu da komai ba idan ya mutu su yi yaya? Zazzafar kace-nace ne ya barƙe har suka manta ma Ubansu na chan hannun 'yan sari. Kwanan kawu ɗaya a wurin ruwa kawai suke bashi duk ya firgice ya jeme ga yana dakuwa don lillahi in suka tashi jibgar shi kaman buhun hatsi suka samu, a rana na biyun ne suka sake dawowa sai dai duk kiran da zasu yiwa su inna Larai sun ƙi picking. "Banza marar Amfani iyalan naka ma ba kaunar ka suke ba..." Ya faɗa yana ball dashi ihu ya kwarma yana basu haƙuri inaa suka saɓe shi suna zura mishi wani bakin kyalle a kai sai wani ɗakin na daban, ko da suka buɗe mutane uku ya gani a tare da shi zaune duk a jeme kawunansu kwal-kwal, shima aski aka yi mishi tal aka bashi wani riga mai kaman dogon riga ya saka a kausashe waenda suke gadin wurin alamu sun fi waenchan zafi suka ce "Jininka ya halalta a yau zaka bakunci lahira..." Bai san wanchan tashin hankalin da ya shiga mai sauki bane a yanzu ba zai iya fasalta halin da yake ciki ba barin ma da mutanen da ya samu suka ce mishi tunda har sun furta zai mutu yau sai ya mutu basa magana biyu, yankashi zasu yi su ba dodo jinin shi naman kuma suyi romo su cinye don matsafa ne wani irin zawo ya barƙe dashi tsabar kaɗuwa ya gigice sai haƙuri yake basu kuka kam har ya rasa hawaye amma sun ƙi kula shi a gigice yake cewa "Yanzu na san asalin tsafi...ashe Afeefah babu abin da kike yi? Na shiga uku wayyo Allah! Afeefah baki isa yin irin wannan ba...wannan ya fi karfin tunaninki...Na shiga uku na lalace wayyo Allah na..." Kuka bilhakki yake yana kiran sunan Afeefah a gigice don dai gashi nan da layun kariya daga mayun ya fito daga gida incase mijin ma maye ne kar su cinye shi sai gashi yana kallon asalin maita, suna shirin cinye shi banzar layunshi sun kasa mishi anfani, bai san adadin kuka da magiya da yayi tayi ba babu sunan wanda bai kira ba har aka zo aka sake fita dashi zuwa ɗakin tsafin nan ya ƙara firgita ganin wasu irin halittun dodanni ga wasu masu jajayen kaya da baƙake marasa imani jibga-jibga sai muzurai suke suna ganinshi kaman sun ga nama ko kuma ya ce naman ma suka gani, yana tirjewa yana tsandara karar a taimakeshi amma chadak suka ɗaga shi kaman kayan wanki har gaban shugabansu. A tsaye yake amma suna haɗa idanu bai san ya zube ba. "Ka taimakeni ka ji kaina wlh ni maraya ne, ba ni da kowa iyalina ma basu da kowa bayan ni kar ku kashe ni, kar ku sha jinina na tuba...!" Har a ranshi magiya yake yana kuka da majina dariya suka sheke dashi wata murya dake fita bibbiyu ya daka mishi tsawa... "Yi mana shiru!! Ka riga ka shigo nan babu fita ka sa a ranka za ka bakunci lahira a yau jininka kuwa zai zama abin sha mafi gardi ga shugabanmu a wannan dare yayin da za mu kashe dare cikin party da namarka..." Suuuuu haka kawu ya sume sai dai duk yadda zai sume baya seconds zai farka da karfin tsafi... A haka aka ɗauke shi zuwa gaban wani tukunya dake bararraka da baƙin abu aka zaro wata shirgegiyar wuƙa dake sheƙi aka ɗora mishi a wuya, ya gigice! Ya ruɗe! Ya fice daga cikin hayyacinshi! Zuciyarshi kiris ta rage ta fita daga madaukarta, kashi da fitsari kam bai san adadin da yayi ba barin ma da ya ga da gaske mutuwar zai yi... **** "Mommy...! Mommy...!!!" Da ƙarfi yake kwala kiran sunan yana zagaye gidan don jinshi yake kaman zai yi hauka idan bai sanya mahaifiyar tashi a idanu ba sai dai yana buɗe ɗakin mommy gaje ya gani zaune tana ma cin nama ne soyayye a plate. "Ina mommy?" Shiru tayi daidai Yaya ya fito shima daga ɗakin da ya san dai na Sadiqa ne. "Ina 'yan uwana? Ina mahaifiyata?" Ya yi maganan da ƙarfin gaske da ya sa suka zabura suna dawowa hayyacinsu ganin yadda ya zama lokaci guda Yaya ya dafa shi "ka natsu mana Saleem, mu ma ai iyayenka ne tunda iyayen matarka ne ka manta kai ka fitar da su mahaifiyar taka daga gidan nan ka ce mu dawo mu zauna tare?" Wani irin riƙe kanshi yayi dake flashing mishi duk abubuwan da suka faru tun daga auren Sabrina, ji yake kaman zai yi hauka da kyar ya fara ambaton "Innalillahi wainna ilaihi rajiun! Hasbunallahu wani'imal wakeel...!" Kai tsaye gaban Sabrina da jikinta ke rawa ya ƙarasa yayi mata wani irin mugun riƙo da tana tunanin kila hannunta ya karye a tsawace yace "Me kika min? Me kika aikata min!!" Yadda yake zazzaro idanunshi da suka zama Red ya sa ta sake firgita. "Saleem me za ta yi maka k...." "Shuttt up!! Ku yi min shiru a yau na rantse da Allah sai kun faɗa min me kuka yi min? Me kuka yi min da ya sa na zaɓe ku kan uwata da 'yan uwana??" Sabrina zata yi magana yayi wurgi da ita har ta bugi kujera tana zubewa ƙasa, kofan parlorn yaje ya rufe da key ya koma da hanzari ya rufe na baya ya zo ya haura ɗakinshi kaman zararre ya samo belt ya sauƙo da gudu ya rufeta da duka yana ihun tambayar me ta mishi me suka mishi? Don ko jikinshi kunnuwa ne ba zai yarda da gangan yayi duk abin da yayi ba ta gigice duk inda zata gudu ta ɓuya ta gudu amma sai ya fusgota yana dukan yana tuna irin dukan da yayiwa Sadiqa, babanta da mamanta suka makure wuri guda suna kallon yadda yake jibgar 'yar su idan tayi wurinsu da gudu suma sai su runtuma kar bulala ya same su da ta ga no go ta fara ihun "ba ni ce nayi ba wallahi su ne... Su gaje ne su suka yi komai su suke karɓo magani wurin bokaye muka mallake ka wlh su ne...." Dakatawa yayi yana kallonsu "Me take cewa?" Duk ya haukace tsoro ya rufe su, bindiga ya zaro "Ko ku faɗa min me nayi muku da kuka zalunceni ko kuma dukkanku in kashe ku... Me na muku???" Da wani irin tsawa yayi maganan duk suna zube a ƙasa a gigice don yadda yaken nan tsaff sai ya harbe su, a darare Yaya ya fara cewa "Kayi haƙuri Don Allah ka yi haƙuri.." Gini ya harba karar bindigar ya saka Yaya fitsari Sabrina da Gaje suka tafi a sume, ruwa ya kwaso ya zo ya kwarara musu yana nuna gini "Kun ga yadda ginin nan ya fashe ko? Toh billahi ko ku faɗa min ko in fashe kawunanku haka" "ka saurareni ka yi hakuri zan faɗa wlh zan fada maka..! Mahaifiyarka da ni mun kasance 'yan uba tun da muka tashi iyayenmu mata ke nuna mana ba ɗaya muke ba, hakan yasa muka tashi da wani irin ƙin juna a zuciya, sai kuma Allah ya daukaka Hussaina hakan ya ƙara mini hassada da kyashinta barin ma da muka rasa iyaye bata daukeni dan uwa kuma abokin shawarar ta ba, bata kula ni ko 'ya'yana sai in bukatarta ne ya kawo ta wurin mu, ta daukeni tamkar ɗan gidanta bata girmamani babu ruwanta da kyautata mini tana nuna min itama wahalar ta ya sama mata in tashi in nema anan na ƙudiri aniyar mayar da dukiyar ta nawa, mun yi shige shige dayawa a baya kasancewar kana yawan zuwa duk ruwan da za mu baka akwai wani asiri ciki sai dai duk basa kama ka saboda kana neman kariya kuma kana Adu'a, har ma mun fitar da ran samunka muke tura yarinyar mu nema mana kuɗi da surarta don muna so itama ta auri mai kuɗi mu kerewa Hussaina(Mommy) sai kwatsam ta dawo da son zuciyarta garemu... Mun yi amfani da hakan Allah kuma ya bamu dama saboda ba don Allah ta neme mu ba muka juye ka ka zama sai abin da Sabrina ta ce..." Hawaye ne ke sauka mishi a haukace yace "Ni na zama kwallonku kenan?? Ni ne da nake tausaya muku nake taimakonku daidai gwargwado kuka zaɓi salwantarwa da tura ni cikin fushin ubangiji??" "Kayi hakuri don Allah! Ka yi hakuri..." "Ku tashi ku fita a gidan nan har abada kar ku bari fuskata ta kalli naku... Duk ranar da hakan ta kasance sai na sa bindigata na harbe ku ku fita nace!!!" A gigice suka miƙe suna ji suna gani suka fita da kayan jikinsu kawai don ko cokali ya hana su ɗauka duk tatsarshi da suka dinga yi na kuɗi suna boyewa duk yana cikin gidan, ko takalmi babu kafafunsu haka suka fita rike da Sabrina da ta sauya kamanni tana ta kuka barin ma da ya furta ya sake ta saki biyu ta je ta ƙarata.. (Ƙarshen alewa ƙasa!) Su mommy suna zaune suna kallon sunna Tv da ake hasko wa'azin likitan zuciya wato sheikh tijjani Ahmad yusuf guruntum kawai suka ga an turo kofa an shigo, a razane suka miƙe tsaye sai ganin Saleem suka yi yana tahowa yana haɗa hanya a rikice mommy ta nufe shi "Saleem..! Saleem...!! Kai ne? Kai ne da gaske.." Taro shi tayi ganin zai faɗi yana furta "Mo..myy" Sai ya sume musu.. 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763

Chapter 22 of 40