Sameer"
"Mama ko da yaron bai girma ba? To waye zai yi sarautar?"
"Mahaifinki shine first cousin na sarki kuma yana da ikon yin sarauta zai iya riƙon ƙwarya har dan da zaki haifa ya girma ya bashi kin ga kenan Sarautar gabaɗaya ta dawo gidan mu kaman yadda dama tun chan yake a tarihi aka yi mana fin karfi aka hana mu"
Shiru zarah tayi Fulani Adama tace
"Ke kar fa ki tsaya wani kokonto don a sarauta babu kokonto ko tsoro, sannan kar ki bari wani soyayya yayi tasiri saboda babu wannan a tarihin jajirtaccun da suka yi mulki, ko ni na auri mai martaba ba don ina so ba sai don burin haifar Sarkin gobe, a yadda ban haihu ba na so kowa ma ya rasa har shi mai martaban ya mutu a haka dole 'yan uwana su karɓa amma Yarinyar chan Faɗimatu ta lalata min shiri don haka dole ne ta ga ba daidai ba"
Waɗan nan sune maganganunsu da Fulani Adama da farko tana wasu-wasi amma yanzu ta ji lallai zata iya, za ta iya aikata hakan ba ɓata lokaci.
Afeefah na isa ta samu yana zaune a parlor kafanshi ɗaya a kan daya yana ɗan karkadawa ganinta bai sa ya saki fuska ba tace
"Barka da hutawa Ya Saraki"
"Sai yanzu?"
Ya faɗa yana kallonta, tuna irin kirkin Ammi take da irin damuwar da take ciki ko a murmushinta za ka iya fahimta hakan yasa ta miƙe daga inda take ta dawo kusa dashi tare da zame alkyabba da gyalen kanta haɗe da ɗan kwali tace a Shagwaɓe
"Wai fushi ka yi na jima Ya Saraki? Kitso fa nayi kalli ka ga bai yi kyau ba?"
Ya kasa ɗauke ido a kanta ta mishi kyau da Kitson sossai ya riƙo hannunta
"vooɗi masin boɗɗiyel am"
Dukda bata ji ba ta ɗan yi murmushi
"Me ka ce kenan?"
"Mai kitson Fulani bata iya yaren ba?"
"Toh ai bana ji, kaima na yi mamakin yadda na ji kana yi fluently"
Ta ɗan kwanta a jikinshi yana sake kallon kitson da ya fidda fatar kanta fesss yace
"Tun daga ranar da na bar gidan nan ban sake yi ba sai da na dawo"
Ta sa hannu ta zagaye cikinshi kanta na a kafaɗar shi duk tausayi suke bata daga shi har Ammin.
"Toh ka faɗa min me ka ce?"
"Ya yi kyau sossai kyakyawata. Abin da na ce kenan"
Tayi murmushi mai sauti tana ƙoƙarin maimaita abinda yace da fulatancin, yadda ta shirmata dole ta saka shi murmushi har ma ya manta da yana kokarin yin fushi ne ta tafi sashen Ammi tayi zamanta.
Bayan Magrib ya zo ya ja ta suka fice daga masarautar a wata BMW baƙa ya hana su Gaabɗo Binshi ta chanza zuwa wani blue Abaya da ya karɓeta sossai, shima navy blue Jean ne jikinshi da coffee shirt da ya fitar da hasken shi ainun sai ya saka facing cap navy blue saboda mutane baya so a gane shi a wajen don yanzu sai a fara maganan yana fita da kananun kaya, Sossai ya zaga da ita hannunta na cikin nashi yana driving da hannu ɗaya ba wani hira sossai yake mata ba amma in tayi magana yana kokarin amsawa bar shi dai da kallonta sai kuma pecking expecially bayan hannunta dake cikin nashi.
Shopping sossai suka yi suka je suka ci abinci daga nan suka dawo suka sayi popsicle don tace tana so, sai wuraren 9 suka dawo gida hankalinsu kwance shi yayi sallah already ta shiga tayi nata kan ta shirya kwanciya, kaman jiya riga da wando ta saka masu yauki na kayan baccin cream colour da ya amshe ta sossai hannun rigan na singlet ta feshe jikinta yadda ya kamata, tsoron zuwa ɗakinshi take don bata san me zai faru ba kar a yi irin na jiya don ma shi likita ne yana da tarin sani akan yadda zai bi da ita ko da ta gurzu yayi jinyar kayanshi amma tana tsoron zafin don har lokacin tana jinta a kumbure.
Gadonta ta hau ta kwanta shiru tana jin kewan jikinshi da har ta fara sabo da hawa, bata yi mintuna talatin ba ya tura kofan ya shigo ganinta kwance ya saka shi murmusawa ya isa gadon ya yaye rufan da tayi
"Lallai ma yarinya ni za ki bari kaman gauro?"
Dariya maganan ya bata ta kama murmushi Dukda yadda ta so tayi pretending ta yi bacci dole ya dauƙeta suka yi nashi ɗakin daga shi sai wani cotton wandon bacci chest dinshi duka a bayyane haka ya rufeta ciki, yana shafa bayanta yace
"Wasu sun ce zazzafar soyayya tana zuwa ne a bazata! Na yarda Boɗɗi saboda a sadda na fara ganinki ban zaci zan so ki kaman yadda nake jinki a yanzu ba, ban san za ki zama abu mafi muhimmanci da daraja a rayuwata ba, I just fell in love with you and am still falling even harder cikin kowani dakika"
Tana tare dashi amma tunaninta yake, tana a jikinshi amma kewanta yake bai taba sanin haka so yake ba, bai damu da yaji ta Bakinta ba shi dai ya san yana sonta daga shafata da yake ya nemi zarcewa, za tayi magana ya haɗe lips ɗinsu yana bata wani irin kyakyawar french Kiss da ya gigitata, tuni rigar ta yayi wani wurin ganin da gaske yake yasa ta kawo kuka ta saka mishi mai tsuma rai dole ya haura a hankali zuwa wuyanta yana ajiye wet kisses slowly ya isa kunnenta.
"Am sorry boɗɗiyel am! Ki yi haƙuri kaɗan zan yi ba dayawa ba i promise ba za ki ji zafi ba"
Girgiza kai take sai dai bai bari ta sake wani yunkurin ba ya shiga wasa da harshenshi a kunnenta, Tsam ta tsume sai da ya tabbatar ta gama rikicewa kan yayi abinda zai yi duk suka samu natsuwa cike da tarin soyayya da tsantsar kulawa kuma bata ji zafin kaman na farko ba, a tare suka yi wanka yau ma nade da towel kawai suka shige bargo yana sanya mata albarka a kunnenta haɗe da godiya.
Washegari da safe kaman yadda Fulani Adama ta faɗa bayan ta gama mishi abin kari ya ci ya fita ma wurin mai martaba ta shirya ta nufi wurin Ammi don da gaske su jannah basu kwana sashen ba, bayan sun gaisa suka dunguma wurin Fulani Adaman suka gaisheta Madarar shanu ta basu akan su ɗuma ciki sabo ne da zafin shi, ita Afeefah bata sha amma don kar su yi laifi Jannah ta karɓa ta sha, Abeeha ma ta Sha Afeefah na ta wasa dashi har suka ce zasu tafi suka ajiye mata suka fice, sauran sashen suka je suka miƙa gaisuwa kan ta koma sashenta su jannah suka koma wurin Ammi.
Bacci tayi sossai sai azahar ta tashi ta shiga shirya mishi abinci inda ta haɗa mishi White Rice da kidney sauce sanin yana son abin sossai, bata ma gama shiryawa ba ya dawo ɗakinshi ta kai ta ɗale kafafunshi yana ci yana bata har suka gama ta fitar da kwanukan. Bayan Magrib aka zo shirya ta zuwa wurin Taron da Matasan Fulani suka shiryawa Yariman nasu na murna.
Kayan saƙi ne Fari aka bata ta shirya ciki a ƙasan rigan ta saka bodyhug mai dogon hannu fari ƙal kan ta ɗora rigan ya zauna mata sossai ta ɗaura zanin a ɗan sama kaɗan suka shiga cika mata kayan adon Fulani bayan an yi mata dauri mai kyau, goshinta, wuya, hannaye har kafa kayan ado ne irin na al'ada sai aka ɗora mata alkyabba fara kal tayi kyau sossai tana ta kallon kanta tana murmushi, bayan sun fita tana nan zaune sai gashi ya shigo.
Miƙewa tayi tana kallonshi kaman yadda yake kallonta da tarin ƙauna, farin wando na saƙi shima shine jikinshi sai wani farin shirt kan rigar sakin har da hula yana rike da sanda yayi kyau har ta rasa wani irin kyau za ta ce yayi, wayanta da bata taɓa daukar ma hoto ciki ba ta ɗauko ta ja shi gaban door size mirror ta shiga yi musu mirror selfie, ya biye mata sossai akwai wanda ya ɗora sandar a wuyanshi ya riƙe da hannu ɗaya ya ɗan karkato ya ɗora hannunshi ɗaya akan cikinta bayanta na jingine a kirjinshi sossai posture ɗin yayi kyau amma bai yi dariya ba sai ta Shagwaɓe
"Kayi murmushi mana Ya Saraki ka ga fa shiyasa ake cewa baka da kirki"
Bai san yayi murmushin ba ta ɗauka duk hakwaransu waje da ya gaji ya ja ta suka fice tana kallon hotunan nasu na karshe daga ma baya ma shi ta mayar wallpaper wayan ya karɓa yayi air dropping shima ya mayar nashi wallpaper ɗin, sun isa katoton zallar filin taron dake cike da haske an kawata wurin da kujeru.
Kusan kowa a wurin shirye yake da kayan saƙi na fulani sai a wurin suka haɗu da Jannah da mijinta shi Rayyan sun haɗu tun da ya fita da safe ita ce dai Afeefah sai lokacin ta ganshi, wurin yayi kyau sossai kujeransu na a haɗe, gefe yan mata da ƙwairen Nono da wasu kananu masu kyau a tsaftace wanda shine za'a sha a taron
Matasa da yan mata cike da wurin kida da fulatanci na tashi daga wannan ya kare za'a saka wannan wasu na soyayyarsu yayinda Afeefah ke bin komai dake gudana da kallon burgewa, wasan kiwo da shanu aka fara inda aka ajiye shanu aka shirya Matasa biyar aga mai dabarar da zai iya tada shanu tsaye, sossai wasan ya kayatar bayan an gama shi aka yi shaɗi sai wasan Matasa na sanda, aka yi rawa kala daban daban su dai basu tashi ba Dukda ta so ta tashi amma ganin gogan ya ƙi bada dama sai ta natsu an saka waƙar wani mawakin Camero Jaamali Na Lara saftata ya waiga ya kalleta tace
"Me ake cewa?"
Ya ce
"Zan fada miki sai mun je gida"
Kai ta gyaɗa amma da aka kira wata mawakiyar Fombina Rukayya aka saka waƙar ta sai ya waiga ya kalleta
"Akwai inda zan fassara miki amma da sigar namiji zuwa mace"
Kai ta gyaɗa.
"kin san me amshin ke cewa?"
Ta girgiza kai
"Ni fa ko zo in kashe ki aka ce ba sani zan ba bare na shirya guduwa"
Murmushi mai kyau yayi hannunshi na cikin nata yana wasa dashi a yadda suke maganan kallo ɗaya zaka musu ka san masoyan Juna ne kuma exchanging kalamai suke don fuskarsu a sake musamman ita dake ta doka murmushi.
Ya fara yi mata
"Mi ɗon yidi ma a anda mi don yiɗi ma na? Mi ɗon yidi ma Yideyel am nder bernde am.
(Ina sonki baki san ina sonki Ba ne? Ina sonki masoyiyata har cikin zuciyata)"
Sossai take blushing tana jin kidan wakan na mata daaɗi barin ma rawan da Matasan suke. Bai sake magana ba sai da aka zo wani wuri yana wasa da hannunta idanunshi a kan fuskarta yace
"Ki ji! Yiide ma nde nangi am mi warti bumɗo!(Sonki da ya kama ni na zama makaho)
Yiide nangi am mi warti ginnaɗo..!
(Sonki ya kama ni na zama mahaukaci)
Waru nangam giɗɗo am saklare hosi am!
(Zo ki riƙe ni masoyiyata jiri/hajijiya ya kama ni)
Mi ɗo numa ma jamma be nange mi nyamataa!
(Kina cikin tunanina dare da rana bana iya cin abinci)
Mi ɗo numa ma nange be jamma mi ɗanataa!
(ina aikin tunaninki rana da dare bana iya bacci)"
Hannunshi ta sake gimtsewa tana sake faɗada murmushinta ta ce cikin yanayin 'yan koyo
"Mi ɗon yidi ma a anda mi ɗon yidi ma naa mi ɗon yidi ma yideyel am nder bernde am"
(Ina sonka baka san ina sonka bane? Ina sonka masoyina har cikin zuciyata)
"Da gaske ko a waƙa?"
Yayi tambayar yana ɗage gira daya cikin salo
Ta saki murmushi
"Da wanne kayi kai?"
"Na taɓa miki wasan ina sonki? To ina sonki Afeefah! idan na kalle ki sai na ga cikakken kwanciyar hankali zuciyata ta samu natsuwa, kin kasance Abar alfarina!"
A hankali in a whisper tace
"Nima da gaske nake, ina sonka har cikin raina zan kuma zame maka macen da zata baka duk wani so da kulawar da ba'a taɓa baka irinshi ba, zan zame maka macen da ba zata taɓa ɓata maka da gangan ba, zan zama mai baka goyon baya a dukkan lamuran rayuwa, zan zama mai maka uzuri kuma zan kasance haskenka a duk sadda duhu ya nemi mamaye maka hanya, the girl you never want to argue with but communicate things out, the girl who love you for you ba don kudi ko mulki ba"
Miƙewa tsamm yayi
"Tashi mu tafi"
Bai jira cewarta ba ya janye ta don tana cigaba da maganganun nan zai iya tafka abin kunya a bainar nasi duk nema take ta rikita shi ko ta kan Abeeha da ya hanga da Ameer yake so yayi magana bai bi ba ya buɗe mata ta shiga ya zagaya ya shiga aka ja su sai gida.
🖤Gureenjoh 🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*54*
https://chat.whatsapp.com/HUJI7tg9TOU941grP60r4S?mode=ems_copy_c
Kinaneman group din dazaki ringa sarinkayan kitchen cikin farashin sari...tayadda koda kinje kasuwa bazakisamu kasa d farashinmuba snn zaki iyazuwa har hargida kisayi dukkan kayan dakike bukata cikin kwanciyar hankali kokisaya ayimaki delivery zuwa dukkan inda kike afadin Nigeria da dama makotan kasashenmu kikarbi kayanki cikin farinciki da aminci!!!.....kiyi joining a mai nono kitchen utensils and household........gaskiya d amana sune takenmu!!!👏🏻
*****
"Duk wanda ka ga ya lashi zumar nasara, to tabbas ya ɗanɗani maɗaciyar haƙuri."
Wannan ɗin wani zance ne na masu hikima. Bahaushe ya ce haƙuri gishirin zaman duniya, Yayin da ubangiji ya koya mana cewa duk inda abu ya je ya dawo kayi haƙuri! Duk ƙunci ka yi haƙuri, Duk damuwa ka zama mai haƙuri, Duk mai haƙuri shi ke galaba kuma duk mai haƙuri shi ke cin riba da wannan aya ta;
"Ista'eenuu billahi wasbiruu" (Ku nemi taimakon Allah kuma ku yi haƙuri).
Haƙiƙa da a shekarun baya za'a iya cewa zata taka wannan matsayi da take kai a yanzu za ta ce karya ne amma dayake Allah mai jin ƙan bayinsa ne da jiɓantar lamuransu gata a cikin ni'imarsa marar yankewa. Hakan ya sa cikin waennan watanni uku da suka biyo bayan tariyarta gidan Sarautar Fombina Bakinta bai taɓa hutawa da godiya ga ubangajinta ba saboda shi ya ce mana ka gode mishi a dukkan ni'imominsa shi kuma zai ƙara maka.
"Alhamdulillahil lazee bini'imatihi tatimmus salihaat... Alhamdulillah ala kulli haalin... Alhamdulillah hamdan hamda... Hamdan katsiran dayyiban mubarakan fihi"
Sun kasance kaman ruwan sha a Bakinta, ta samu duk wani gata da zata nema ta uwa irin Ammi da uba irin mai martaba. Waenda a yanzu suke tabbatar da cewa bata yi kuka da sunan maraici ba.
Ta samu ɗumbin soyayya marar fasaltuwa daga wurin jarumi kuma gwarzon mazanta, a wannan watanni uku ba zata ce ko kallon banza ya taɓa shiga tsakaninsu ba bayan tattali da nuna kulawa, bata taɓa neman wani abu ta rasa ba zata iya cewa rayuwar da tayi a gidan na watannin ukun farko suna daga cikin waenda ba zata taɓa iya shafe su a tarihin rayuwarta ba, Dukda sau biyu yana tafiya akan aikinshi hakan bai dakile mata dukkannin abinda ya saba ba.
Jannah ta koma sai dai su yi waya, Abeeha ta yi transfer ta dawo nan Fombina da karatun ta yayinda ta yi kane kane zuciyar Ameer Galadima ta hana shi komawa wurin aiki, a gefe ɗaya kusan duk waenda suke kusanci da Aisha da Saleem sun san cewa sun mato akan son junansu, daga mommy har su Sadiqa har Umman Sulaiman da ma matarshi su kan kira ta su gaisa sa'i da lokaci don yadda suka mayar da ita ɗaya daga cikinsu itama haka ta ɗauke su tamkar yan uwan da ta rasa, abu ɗaya ta kasa shine ƙarasa shirya tsakanin Rayyan da Ammi, yana da taurin zuciya irin na Fulanin Asali iyakancinshi da ita idan sun haɗu gaisuwa ne amma bayan nan baya ƙara komai Ameer yayi, mai martaba ya yi, Yaya Maudo(Galadiman Fombina) shima ya yi itama tana kan yi Dukda duk ranar da tayi maganan sai sun ɗan samu saɓani ya nuna mata baya so bata taɓa dainawa ba lokaci lokaci.
A gefe ta kan tuna kawu da su inna Larai don an ce jini ko ya yake ya fi ruwa kauri duk abinda suka yi mata gashi bai katangeta da samun farin ciki ba, sai ma kusanta ta da yayi da farin cikin mai tarin alkhairai, Result ɗinsu na Waec ya fito kuma ta ci sossai tayi ƙoƙari Dukda shi gogan nata bai ce komai a kai ba hakan ya sa ta fara sanyawa zuciyarta cewa ba lallai tayi karatu yadda take so ba, ta sakawa zuciyarta ba komai kake so kake samu ba kila karatun ba alkhairi bane da haka ta danne ranta bata taɓa yi mishi magana a kan makarantar ba.
Yau ya kama Friday haka kawai take cikin nishadi tun da ya sauƙe mata zallar madarar ƙauna ya fice da safe sa'i da lokaci ta kan saki murmushin da baya rabo da fuskarta, bayan tayi Sallar la'asar ta gabatar da duk abinda ta saba kowani juma'a a irin lokacin na karatun suratul kahf da adu'o'i ta tashi ta nufi kitchen. Ta ɓata lokaci sossai wurin gasa mishi kifi da yake matuƙar jin daaɗin gashin nata ta soya plantain da irish ta shirya table ɗinta tsaf kan taje tayi wanka, kananun kaya ta saka wando ne da bai kai ma gwiwa ba rabin cinya Black sai White Shirt da ta saka tayi wani irin kyau kaman ka sace ta.
A kwanakin ita kanta ta san ta sake chanzawa ta yi kubul kubul fatarta yayi fresh kaman mai wanka da madara, ita kaɗai ce don tun gama taya ta aiki ta tura su Sa'ade sashen baya da ya sa aka gyara musu na cikin ɓangaren nata saboda shi ba mutum bane da yake son takura a sadda yake tare da iyalinshi, Abeeha ta jima da komawa wurin Ammi wai in ta cigaba da zama za su iya makantata cikin ko wani dakika don haka tayi ta kanta. fitowa tayi kai tsaye zuwa kitchen tana tuna wani haɗi na musamman da aka koya mata tun kafin aurenta dashi yau kam ta yi niyyar gwadawa, ayaba ta ɓare guda huɗu ta dauki tafarnuwa guda ɗaya ɗan daidai ta haɗa ta zuba a blender ta markade ta juye a cup, zumarta na asali ta zuba a kai tana jin haushin rashin kankanrar matar da bata dashi amma ko a haka ta san emergency ne mai kyau kaman yadda matar ta yabe shi, shanye wa tayi a tsaye a kitchen ɗin kan ta koma ɗakinta tayi ruf da ciki tana danna waya.
Shigowar shi gidan jin bai ji motsinta ba yasa ya nufi ɗakin nata, sanye yake da khakinshi full don wani aiki ya fita akan tsaro tun safiyar yana tafiya yana ɓalle botiran ji yake kayan sun ishe shi, tura kofar ɗakin da kafewarshi a wurin lokaci ɗaya don ji yayi ruwan jikinshi na neman tsiyayewa, surar jikinta na neman zauta shi kafafunta zuwa cinyar ta dake a bayyane suka tasar da mazan dake jikinshi a lokaci guda, harshenshi ya fidda ya ɗan jiƙa lebanshi da yake ji sun bushe kan ya nufi gadon, ya ajiye kayan hannunshi ya kai zaune bakin gadon ya ɗora hannunshi kan cinyarta, tun shigowanshi kamshin turarenshi ya gaya mata wanene da gayya ta ƙi juyawan, ganin har lokacin bata juya ba ya sa ya saki murmushi mai sauti.
Hannun ya ɗago ya kai kan rigan ta ya yaye ya kai fuskarshi yayi kissing fatar bayan yana shafawa a hankali, kan ya ɗan kwantar da kanshi yana jin yadda ta sauƙe ajiyar zuciya, bai yi magana ba ya cigaba da goga mata gashin gemunshi a bayan yana shafawa da hannunshi tuni ta kasa natsuwa ta juyo sai yayi mata rumfa yana haɗe goshinta da nashi ya lumshe idanu yana shakar daddadan kamshin turarenta dake ƙara hautsina shi.
"Debbo boɗɗo am! Fushi kika yi?" (Kyakyawar matata)
Yayi magana yana dan hura mata iska a idanun da ta rufe.
"Shi ne ka je kayi zamanka ka manta da ni tun safe ko waya baka yi min ba.. Kuma ai ka ce za ka dawo da wuri amma sai yanzu? Kwalliyana har ya goge"
"Ya subhallah...!"
Ya ambata a chan ƙasan makogoronshin, peck yayiwa bakin Shagwaɓar ta sanya hannu akan dantsenshi dake bayyane don daga shi sai vest ya zame rigar ta riƙe shi da kyau.
"Na isa in manta da bugun zuciyata? Ko kin san mintuna biyu a nesa dake kaman shekara biyu ne a gareni yayinda shekara biyu a tare da ke zai zama tamkar mintuna biyu? Sam bana sanin gudun lokaci idan ina kusa dake Matar masu sarauta"
Murmushi mai sauti kaɗan ta sake da ta sake motsa zuciyarshi.
"Ni ce addiction ɗinka yanzu kenan?"
Tayi maganan tana ɗan yawo da hannunta slowly a kan damtsenshi zuwa ƙirjinshi, ya ɗan taune lip.
"Yes you really are my dear.. Craving ɗinki nake kaman mai ciki"
Dariya ta ɗan yi, ya kama lips ɗin da nashi yana kissing slowly kan ya saki ta ɗan yi murmushi
"Always remember that zan iya gajiya da komai a wannan duniyar amma banda ke, even when am tired all i want is you.."
Hannayenta ta mayar bayan ƙeyarshi tana mishi susa ita kanta ta san tana yin hakan ta gama kunnashi, tuni hannunshi ya kai ga kwankwasonta yana yin sama da rigar bakinshi is kissing her like his life depend on that, ba zai iya haƙuri sai dare ba he just want to feel her bukatarta kullum sabo yake zama mishi, kaman yadda mutum ba zai iya rayuwa babu iska ba haka yake jin ba zai iya rayuwa babu ita a gangarshi ba.
Ya kuwa ɗanɗani abin da ba zai iya janyewa cikin lokaci kankani ba, rikice mata yayi sai da ta fara dana sanin shan abinda ta sha da yamman don bai barta ba sai da ta fara mishi kukan gaske, ya rungumeta yana sanya mata albarka.
Tayi lub a ƙirjinshi suna sauƙe numfashi a hankali hankali, wayanshi ya duba sai ya ga dab ake da kiran sallah dole ya miƙe da ita zuwa bayi suka yi wanka duk jikinta a mace suka fito daure da alwala, bai iya ya je masallaci ba don an fara kiraye kiraye kan ya isa ma za'a iya idar wa jallabiya ya saka ya ja su suka idar, ya waigo yaga sai ɓata fuska take ya janyota jikinshi ta kwanta suka yi azkar a haka kan yana shafa fuskarta yace
"Raguwata zan ga ranar da zaki gama sabo da jaruminki"
A Shagwaɓe tace
"Ni dai a'a na yi fushi!"
Murmushi ya saki ta kalleshi
"Murmushi na yi maka kyau kar ka daina kwata kwata ka ji Ya Saraki?"
Yana shafa girarta yace
"Yau jinki nake na musamman Boɗɗi garɗinki wane zuma farar saƙa don haka dole ma in yi ta miki har sai kin gaji. Tashi ki ga wani abu"
Miƙewa tayi ya tashi yaje ya dawo manyan paper bags da ya shigo da su ya ajiye ya koma ya zauna, buɗewa yayi ya ɗauko wasu papers ya miƙa mata.
"Congratulations wannan admission naki ne"
Hannu ta sa ta rufe bakinta tana zaro idanu fuskarta cike da wani irin tarin expression tace
"No..No you can't be Serious! Don Allah da gaske kake ko wasa? It can't be..."
Ta ma rasa me zata faɗa tsabar farin ciki and ganin irin wannan tarin farin cikin da shine sanadin ya saka ya ji shima zuciyarshi ta yalwata da farin ciki, ta ajiye papers ɗin ta rungumeshi tana hawaye
"Ban zaci za ka barni nayi karatu ba, har na cire rai ashe kana chan kana nema min thank you My love! Thank you so so much rabin raina"
Ya rungumeta shima har ta gama farin cikin kan ya ɗago ta ya riƙe hannunta.
"Maganan gaskiya Afeefah ina matuƙar kishinki, ina jin zafi idan na ga idanun wani namiji ya kalleki ko da da second guda ne, don ke ɗin tawa ce! don ni kaɗai aka halliceki kaman yadda aka halliceni don ke! At First ban yi niyyar bari kiyi karatu ba ko ba don kishi na ba sai don kasancewarki Matar Ciroma mai jiran gado, ba Girmanki bane chakuduwa da maza don neman ilimi hakan yasa na nema miki Open university"
Sakin hannunta yayi ya buɗe jakar Apple Mac book ne
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 34 Chapter of 40