tana Miƙewa tsaye ta riƙo shi jin tana shirin faɗuwa wani Sharp pain na shigarta, ya ajiye tray ɗin yana saɓarta
Duk rigima da Shagwaɓar da tayi ta mishi dole suka yi wankan ta lura ita ce ke mutuwa da kunya shi ko a gyalen shi tattalin ta yake wane ƙwai, shi ya dubo mata wani kaya ta saka Dukda ma ba masu nauyi ba a parlor ya ajiye ta ya kunna mata Tv wai tayi kallo bari ya zo, har ya tafi ya koma yaje ya ɗauko mata popcorn ya zo ya bata yayi pecking goshinta kan ya koma ɗakin nashi ta bi bayanshi da kallon ƙauna tana murmushi cike da tarin farin ciki....
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*52*
https://chat.whatsapp.com/HUJI7tg9TOU941grP60r4S?mode=ems_copy_c
Kinaneman group din dazaki ringa sarinkayan kitchen cikin farashin sari...tayadda koda kinje kasuwa bazakisamu kasa d farashinmuba snn zaki iyazuwa har hargida kisayi dukkan kayan dakike bukata cikin kwanciyar hankali kokisaya ayimaki delivery zuwa dukkan inda kike afadin Nigeria da dama makotan kasashenmu kikarbi kayanki cikin farinciki da aminci!!!.....kiyi joining a mai nono kitchen utensils and household........gaskiya d amana sune takenmu!!!👏🏻
*****
Ga mamakinta bai fita ɗin ba ya tabbatar mata da gaske yake ya cewa Abeey bata da lafiya ba zai iya yin nesa da ita ba, kunya ya rufe ta amma shi ko a gyalen shi da kanshi ya gyare ɗakin tsaff ya wanke beddings da suka ɓata kan ya dawo yayi joining ɗinta a parlor hannunshi da mug yana sipping tea, da kanta ta kai kwance jikinshi ya mayar da hannunshi ɗaya bayanta ya rungumeta suna kallon a tare hasken parlorn a kashe Dukda hantsi ce amma yadda curtains suke rufe kirib rip hasken duk a kashe sai ya ba da wani yanayi kaman cinema.
Film din ya ƙare amma bata sani ba saboda ta yi nisa cikin tunani, hawaye kuma na bin fuskarta har take ji kaman zazzabinta zai dawo sabo, kula da hakan da yayi ya ɗaga mishi hankali ya ɗago fuskarta yana kallon ruwan hawayen da take yi
"Afeefah lafiya? Me yasa kike kuka haka?"
Yana maganan ne yana ɗauke hawayen da palms ɗin shi wasu na gangarowa, a hankali tace
"Twins na cikin film din nan sun tuna min da Suhail da Suhaila ne, ko ya suke? Na san yanzu sun girma, ko suna maraicin uwa kaman yadda nayi? Ko suna samun farin ciki duk ban sani ba..."
Fuskarta ya saka cikin tafukan hannunshi guda biyu ya matso sossai har suna shakar numfashin juna chan ƙasa cikin Muryar rarrashi yace
"Ba kin rabu da su ba kenan har Abada Bebe..! Za mu koma in shaa Allahu za mu je mu gansu a tare ki daina zubar da hawayen nan, they are priceless to me..."
Yana kai nan yayi leaning tare da fara ɗauke hawayen da harshen shi cikin wani salo da ya sa ta sake ƙanƙameshi, daga nan ya sauƙar da lips dinshi a kan nata da baya gajiya da su, sai da ta ga yana ƙoƙarin ɗaukar wani hanyar ta zame tare da kwanciya kan jikinshi ya rungumeta suna sauƙe numfashi a tare.
"I love you...!"
Ya raɗa mata a kunne, ta ɗan yi murmushi bata ce komai ba.
"Na jima ina son na baki haƙuri kan wani laifi da na miki"
Ta ɗan ɗago kanta tana kan jikinshin
"Me kayi min Ya Saraki?"
Ya kai hannunshi ɗaya yana wasa da gashinta da ya ki yarda ta saka hula idanunshi na a kan fuskarta yace
"Ranar da kika fara gani na i scared you alot da har na kan yi sensing tsoron ki a duk sadda kika ganni ko kika ji muryata, that time i was very upset sai nake ganin kaman idan da akwai wanda ya fi cancanta da kashe kanshi ni ne but why you? Ƴar karama dake da wannan ɗanyen hukuncin? Raina ya ɓaci da na yi kwanaki da takaicin da ban san na menene ba, i wanted to go back to the hospital ko in kira Saleem amma na danne kawai ban yi hakan ba, daga baya i saw you at saleem's place da yake ba ni labari i was shocked sai dai sanar da ni da yayi yana sonki ya sa na miki murna a lokacin bcs na san shi mutumin kirki ne ƙwarai sai kuma matsalar mommy ya yi striking"
Ta ɗan yi murmushi har lokacin tana kallon fuskanshi yadda yake magana da ma yadda yake wasa da gashinta na kara dulmiyar da ita a kaunarshi tace
"Dukda na ji tsoro sossai da reaction ɗinka to tell the truth shine yayi sanadiyar gane kuskurena, reaction ɗinka ya fahimtar da ni ba karamin kuskure nayi ba a yunkurin kashe kaina da nayi... A lokacin bani da yadda zan yi Afeefah Mayya ce kuma annoba ce ba Afeefar yanzu ba"
Yayi murmushi da yayi mishi kyau sossai
"Har yanzu ma ai ke mayyar ce!"
Ido ta zaro, ya kai hannu ya lalace mata hanci
"Eh mana! Gashi kin lashe min zuciya"
Bata san ta saki murmushi mai sauti ba tana ɗan hararanshi yayi pecking idanun yana sake rungumeta.
"Ka san kuma da gaske na riƙe ka? Har ma sunanka marar kirki a zuciyata.."
Ya ɗago ta ta zauna yana kallon fuskarta
"Seriously??"
Ta gyaɗa kai
"Na fahimceka ne a sadda Mammi ta sanar da ni wanene kai!"
Shiru yayi, ta sa hannunta ta riƙe nashi biyu
"I hope yadda komai ya wuce a tawa rayuwar kaima za ka bar komai ya zama tarihi Ya Saraki!"
Shiru yayi bai ce komai ba, ta san halin kayanta bata so tayi zurfi a maganan ranshi ya ɓaci amma ta fahimci yar tsamar da yake yi da mahaifiyarshi kuma rayuwa ba zai taɓa tafiya a haka ba, dole ne zai bar komai ya wuce kaman ba'a yi ba ta sani ba at once zai chanza ba amma a hankali dole zai wuce ɗin...
Baya baya tayi ta jingina bayanta da jikin hannun kujerar bayan ta saka pillow sai ta wara mishi hannu, a hankali ya kai kwance kanshi na sauka a kan kirjinta ta saka hannayenta biyu tana shafa kanshi zuwa bayan wuyanshi shi kuwa ya lumshe ido yana ji kaman ya ɗauketa su koma ɗaki don kunna shi take ba tare da ta sani ba.
Sun jima sossai a haka kan ya ce
"Kin san mene?"
Ta ce
"uhm uhm"
Tana cigaba da wasa da gashin keyarshi
"I love hugging you, a duk sadda kika rungumeni sai na ji kaman mu dawwama a haka a tare, I just wanna lay here on your chest forever"
Sake rungumeshi tayi tana jin kalamanshi masu tsada na sake samun matsuguni a ranta, ita kanta tana mamakin kanta amma an ce komai wuri yake samu a yanzu da yake nuna mata so da kauna sai taji she can go any extent don ganin ta faranta mishi itama, tsoron da take mishi ya kau sai taga kaman ba shine ke bata tsoron nan ba, kaman ba shine take shakkar ko tari a gangarshi ba.
Suna parlorn har azahar ya fice masallaci ita kuma taje ɗaki tayi Sallarta, bata so ya dawo yace zai yi girki don haka ta wuce kitchen kawai daga ɗakin bata cire hijabinta ba don rigar jikinta wani iri yake sakata ji bashi da maraba da babu, har lokacin ba wai ta dawo daidai bane amma tana ga responsibilty ɗinta ne samar masa abinda zai ci.
Mai ta ɗora a wuta ta kawo ƙoda da ta yanka 'yan daidai ta zuba, suna cikin soyuwa ta fara yanka sausage suma bayan ta kwashe kodar da ya soyu ta zuba sausage ɗin shima sai da yayi ta kwashe ta zuba shrimps da ta wanke tsaf ta soya su ta kwashe, ta kawo tomato patse ta zuba cikin man ta fara soyawa a gefe tana markada kayan miya da suke a frigde a gyare already sai da tomato din ya fara zaƙi kan ta juye kayan miyan a kai ta fara seasoning da su curry, chicken seasoning da dai duk abinda zata buƙata kan ta kawo soye soyenta na ɗazu ta zuba cikin sauce ɗin ta juya tare da rufewa ta nufi basmati Rice dake kitchen ɗin kofi biyu ta diba ta tafi bakin sink tana cikin zuba ruwa don wanke shinkafar ya shigo.
"Kin yi laifi!"
Ya faɗa yana nufarta, ta kalleshi ta saki murmushi
"Tuba nake Ciroman duk duniya!"
Hijabin ya zare mata ya koma ta bayanta yayi hugging ɗinta hannunshi ɗaya na zagaye kwankwasonta
"Meyasa kike girki a yau? Ba ki san na haramta ba?"
"Ba wani abu mai wuya bane kuma bashi da yawa, gashi na kusa gamawa!"
Wuyanta yake shunshunawa
"Shi wannan turaren kam kaman a fatarki aka haɗa so sweet"
Ganin ya fara bata kisses a wurin ya sa ta ɗauki shinkafar da ta gama wankewa
"Ya Saraki abincina zai ƙone"
Bai saketa ba haka suka koma bakin gas din ta juye shinkafar ciki ya lumshe ido yana shakar kamshin
"Hannunki daban ne a girki do you know that?"
Tana zuba tafasashen ruwa madaidaici ciki tace
"Lokacin da nake yi wa su Inna Larai Talla mutanen kasuwa kan faɗi hakan amma wannan training ɗin dai na abincin birni na same shi ne ta sanadiyar Mammi Allah ya gafarta mata"
Ya ce
"Ameen"
Fuskarshi na nuna rashin jin daaɗin halin da ta taɓa tsintar kanta a baya, suna kitchen ɗin har ruwan shinkafar ya ɗan tsotse ta juya kan ta rufe da foil ta rage wuta ya kara 15mins ta juyo musu a plate ta ɗora kan tray shi ya Karɓa suka koma parlor, shi ya ɗauki spoon ɗin ya shiga bata yana ba kanshi, a lomar farko ya lumshe ido ya buɗe yana taunawa
"Wow My love shi kuma wannan menene sunanshi?"
Tayi murmushin farin cikin ganin yana yabon abinda ta dafa tace
"Supreme Rice sunanshi"
"I love it, Allah yayi miki albarka"
Ta amsa da Ameen suka ci gaba da ci har suka gama ya bata ruwa ta sha kan ya tattare kwanukan za ta karɓa ya ture hannunta.
"Ya Saraki..."
Ya ma yi gaba bai saurare ta ba ta miƙe ta bishi
"Kar fa a kama ni dumu-dumu da laifin saka Saraki aiki"
Ya ajiye kwanukan yana ɗaukatarta gabadayanta
"Girmanki ne hakan, ina so har abada in zama mai hidimta miki har sai na kasance ni ne ma'anar farin ciki a rayuwarki"
She's just blushing daga jiya zuwa yau bata san matakin da zata ɗora farin cikin dake ratsa zuciyarta ba hakika tayi dace kwarai da masoyi, kai tsaye kan gadonshi ya shimfiɗeta ya zare rigan shi ya kwanta tare da janyota jikinshi sai ta fara zare idon tsoro.
Fahimtar hakan don har a jikinta ya ji hakan ya sa yayi murmushi yana shafa kumatunta dake kan kirjinshi yace
"Bacci za mu yi Gimbiya just stay calm okey ai na san baki warke ba, ko kin warke?"
Kukan Shagwaɓa ta fara ya saki murmushi mai sauti yana shafa bayanta a haka suka yi baccin kuwa, basu tashi ba sai la'asar yanzu ma da kanshi ya mata wanka duk yadda take dojewa ya ƙi barin ta, gudu wa tayi ta barshi a bayin don ta kasa natsuwa yayi tashi wankan gabanta sai take jin kunyar duniya na rufeta.
Ɗakinta taje ta shirya cikin wata atampha doguwar riga dinkin ya zauna mata tsaff ya fitar da duk wani sura na jikinta tayi wanka da turare isashe a ranta tana mamakin shine ya kori har su Adda Abeeha ko su ne suka yi tafiyar su yini guda basa nan, tana kokarin fitowa parlorn taji sallamar Gaabɗo sai ta koma don yanzu ranshi zai iya ɓaci.
Shi kuwa ya fito ma ganin Gaabɗo ya sa ya samu wuri ya zauna sai ya koma Sarakinshi ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya yana relaxing ba tare da ya kalli Gaabɗon ba yace
"Menene?"
"Allah ya baka yawan rai kana da baƙo ne babba, na sanar dashi ka ce baka son ganin kowa yau amma ya dai tabbatar min lallai lallai in ce yana son ganinka"
"Waye?"
Ya tambaya yana kallon Gaabɗon don bai san wani isashen bane zai ce lallai lallai sai ya ganshi bayan ya ce baya bukatar ganin kowa a yau.
"Allah ya baka yawan rai ranka ya daɗe Ameer ne na gidan Galadima"
Da sauri ya ɗago
"Ameer?"
Kai ya gyaɗa cikin tabbaci
"Kwarai da gaske ranka ya dade."
*****
"Fulani kin yi shiru baki ce komai ba, tun da abin nan ya faru muke ta so mu zauna amma baki ba mu dama ba yau kuma kin kira mu kin yi shiru...! Kar fa mu tsaya kallon ruwa kwado yayi mana ƙafa shekaru nawa muka ɗauka muna shiri ba zai yiwu lokaci ɗaya komai ya warware ba. Ba zai yiwu ba"
Ta kalleshi fuskarta babu ɗigon walwala tace
"Baka kai ni damuwa ba Yaya, baka kai ni baƙin ciki ba... Ba kuma ka kaini takaicin dawowar wannan shegen yaron ba mai idanu a tsakar ka, ni kaɗai na san gwagwarmayar da ni tsawon shekaru ba zan ga kwaba na yana son yin ruwa in ja baya in zuba ido ba, sai dai ba na so mu yi gaggawa ne komai ya zo ya ƙarasa lalace mana! Dole za mu yi maganin abin"
"A yanzu menene mafita Adda?"
Ɗayan namijin yayi magana
"Abu ɗaya ne tak, dole za mu gabatar da plan ɗin mu tun na farko a kanshi... A yanzu matsalarmu ɗaya ubanshi, amma zan san yadda zan yi dole ya amince da ƙudiri na mu kuma za mu yi amfani da daman mu salwantar da rayuwarshi da ta iyayenshi gabaɗaya don na tabbatar salwantarshi daidai yake da nasu salwantar don ba za su jure ba..."
Ƙulle ƙullensu suka cigaba da yi sama da awa biyu suna nan zaune kan suka mayar da badda kamarsu suka fice daban daban kowa yayi hanyarshi.
****
Yinin su Abeeha a sashen Ammi ya musu daaɗi don da kanta ma ta tsefewa jannah kai akan za su yi kitson Fulani tunda gobe akwai taron Matasa na Fuunange, hira suke yi sossai tun Aisha na ɗari dari da su har suka sake da juna Ammi kam kaman ta mayar da su ciki don kulawa musamman da suna bata labarin irin kalar rigimar Rayyan da Mammi suna ta raha da dariya. Ammin na jin kaman ta zama Mammi ko na seconds ne ta samu irin wannan kulawa da kauna daga yaron nata.
Jin ma mijin jannahn zai zo goben yayiwa Rayyan ɗin ma murnan dawowa Ahalinshi sai su koma jibi yasa ta kira a zo a mata gyaran jiki na musamman, sai yau suka ji kaman sun samu madadin Mammi don duk abinda Mammi zata iya yi musu gashi Ammi na yi musu, bayan Azahar da kaɗan suna cin abinci ne ma an gama yi wa Abeeha kitson da yayi mata kyau ainun sai suka ji an turo kofar parlorn.
Aisha ce ta fara kallonshi ta yi tsallen murna tana kwala kiran Ammi
"Ammi! Ammi"
Fitowa daga ɗaki Ammin tayi tana cewa
"Aisha bakya rabo da autanci ihun nan fa? Sai idanunta ya sauka a kanshi fara'arta ne ya ninku a hankali ta isa ta kama hannunshi
"Wa nake gani haka? Ko dai idona ne?"
Yana dariya ya ce
"Sam ba gizo bane nine Ammina, Na same ku lafiya?"
*Kun ga readers marasa cewa thank you ko yin comment nan kuna bani mamaki, na faɗa pages dayawa a baya na nanata Weekdays ina da ayyukan dake gabana sai dare nake posting amma idan na kai daren nan su masu ma comments ɗin ainun da nuna jin daaɗinsu basa damuwa kaman Marasa cewa ko ci kanki..Allah ya kyauta*
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*53*
https://chat.whatsapp.com/HUJI7tg9TOU941grP60r4S?mode=ems_copy_c
Kinaneman group din dazaki ringa sarinkayan kitchen cikin farashin sari...tayadda koda kinje kasuwa bazakisamu kasa d farashinmuba snn zaki iyazuwa har hargida kisayi dukkan kayan dakike bukata cikin kwanciyar hankali kokisaya ayimaki delivery zuwa dukkan inda kike afadin Nigeria da dama makotan kasashenmu kikarbi kayanki cikin farinciki da aminci!!!.....kiyi joining a mai nono kitchen utensils and household........gaskiya d amana sune takenmu!!!👏🏻
*******
"Ameer! Yaushe rabon da a gana? Ashe za ka zo?"
Ya shafa kanshi yana rike hannun Ammin yace
"Ammi abubuwan mu ne sai a hankali amma kuna raina wlh"
"Da muna ranka ba'a waya kaɗai zaka dinga jin mu ba da kana zuwa shekara nawa rabon da ka waiwayi gida?"
"Na tuba Ammi yanzu kam zan dinga zuwa, yanzu ɗin ma labarin bayyanar Sameer ya saka ni zuwa dole."
Suka kai zaune, Aisha ta kawo mishi ruwa yayinda jannah ta gaishe shi ya amsa, Abeeha ma ta gaishe shi ganin shi mutum mai fara'a kwarai da wasa ya burge su.
"Ammi ina kika samu wasu yaran babu labari?"
"Ƙannenka ne, Abeeha da Jannah ga wani yayan naku ɗan wajen babban yayana ne Galadima, abokin Sameer ne don tare suka tashi kaman 'yan biyu a ɗakin nan ɓacewar Sameer bai sa ya bar nan ba anan yayi rayuwa har ya gama secondary ya tafi karatu chan kasashen turawa ya gama da jimawa ya ƙi dawowa"
Sannu da dawowa suka sake yi mishi ya amsa da kulawa.
"Ammi ina Sameer ɗin? Wani sashe yake?"
"Ka ci abinci ka dan huta sai kaje yana chan tare da matarsa"
Wara ido yayi
"Har ma aure yayi abin shi"
"Eh ya bar ku da gaurantaka"
Yayi dariya, Abeeha ce ta taya Aisha presenting mishi abinci kan suka koma suka zauna suna ta jin hirar su da Ammi wanda suke tuna baya tasowarshi da Sameer, hakika zata iya cewa shine na uku a damuwar rashin Sameer don sai da yayi jinya tunda tun ba'a yaye shi ba ya yaye kanshi ya dawo wurinta saboda Sameer sun shaku sossai ta zama sanadiyar raba wannan ƙaunar.
Bayan ya gama sashenshi da bai da nisa da nata ya ƙarasa don ana gyarawa akai akai kuma zaman cin abincin nan da yayi ta aika wasu hadiman sun sake kakkaɓewa ya tafi yayi wanka yana fitowa ma yaji ana kiran la'asar don haka sai da yayi sallah ya fita ya tambayi wasu fadawa suka fada mishi inda sashen na Sameer yake ya nufi wurin.
"Amir Galadima..!"
Rayyan ya faɗa fuskarshi ɗauke da fara'a shima Amir cike da fara'a ya rungume shi suka raba hug ɗin suka tafa irin na mazan dai da aka manta rabon da a haɗu.
"Sameer kana duniya ashe? Baka kyauta mana ba! Ka ɓace babu traces? Hankalinmu ya matuƙar tashi har ka bayyana ban daina tunaka ba, saƙon bayyanarka na daga cikin news mafi jin daaɗi da na taɓa ji a duniya"
Murmushi kawai Rayyan yake.
"Mu isa ciki, wannan labari ne mai tsawo and ka san ban da bakin ba dashi"
Suka nufi yana furta
"Har yanzu ana nan da baƙin hali"
Murmushi yayi yana tuna kalmar Afeefah wai ta mishi shaidar Rashin kirki a baya yace
"Tunda matata ma ta faɗa hakan don ka faɗa ba komai bane"
Dariya sossai Ameer ke yi har suka ƙarasa parlorn suka zauna, nan hira ya fara don Ameer na daga cikin waenda a bayan ma suka san dariyar Sameer, daga shi har mahaifinshi suna da muhimmanci sossai a rayuwarshi Dukda tun dawowarshi sau ɗaya yaje wurin Galadiman kuma tun da ya kawo mishi maganan Ammi bai sake komawa ba.
Ita kam Afeefah jin hirar su yasa ta nemi gyale mai girma ta saka ta ɗora wata alkyabba marar nauyi shara shara a kai ta fito, tayi kyau sossai don ya kasa dauke ido a kanta Dukda bata shafa komai ba, gaisawa suka yi da Ameer cikin natsuwa da girmamawa kan ta kawo ruwa da su snacks ta ajiye mishi, ta kalli Rayyan
"Ya Saraki bari na je wurin su Adda Abeeha yanzu za mu dawo"
Bai ce komai ba don baya son abinda ke tsakanin shi da mahaifiyarshi ya shafe su dukkansu.
Ta juya ta fice, tana tafiya ana jefa mata gaisuwa har ta kusa isa sashen suka haɗu da Fulani Adama, ta ɗan rusuna ta gaisheta
"Lafiya ƙalau ya baƙunta Afeefah?"
Ta amsa tana ƙare mata kallo ganin yadda ta sake wani kyau da haske.
"Alhamdulillah Mama"
"Masha Allah."
Tana kai nan ta wuce ta itama ta wuce ta nufi wurin Ammin, zaune kuwa ta same su har lokacin ganinta yasa jannah fara cewa
"Amarsu ta ango"
Murmushi tayi tana sunkuyar da kai saboda Ammi dake wurin ta duƙa ta kwashi gaisuwa.
"Lafiya ƙalau Gimbiya Afeefah, ya zaman baƙunta da rashin sabo?"
"Alhamdulillah Ammi"
"Masha Allah, yanzu kuwa Mamanku ta kawo min ƙararku sai dai na bata uzurin da cewa laifina ne tunda ku baƙi ne baku wani san tsare-tsaren ba, ni kuma rigimar Sameer ne yasa ban yi maganan ba"
"Allah ya sa ba laifi muka yi ba Ammi"
"A kan zuwa gaisuwa ne, ya kamata duk safiyar duniya ku bi ku gaida iyayen naku musamman ke Afeefah da kike matar Ciroma"
"Ayi mana afuwa bamu san da tsarin ba amma za mu gyara in shaa Allah"
Ammi tayi murmushi tana yaba Yadda Afeefar ta iya magana.
"Adda Abeeha kitson nan yayi kyau masha Allah"
"Kin ga nawa ni ma, kitson na da kyau wlh"
Jannah ta faɗa tun kan Abeehar ta bada amsa tana nuna mata kanta.
"masha Allah duk sun yi kyau"
"Afeefah zo kema in tsefe miki sai a yi miki tunda duk gobe shigan al'ada za ku yi"
Tace
"Ai Ammi kaina a tsefe ne"
Wacce ta yi musu kitson ta kira aka kawo kayan kitso na musamman itama aka shiga yi mata kuwa suna hirarsu.
Dab Magrib aka gama yayi kyau ainun ya amshe ta don har a fuskarta zaka san ta chanchada kitso yadda ya ƙara sheki.
Ana gamawa kuwa sai ga wani hadimi ya nemi a sanar da Fulani Afeefah Ciroma ya aiko a yi kiranta, Miƙewa tayi ta kalli su Abeeha
"Adda Abeeha ku tashi mu tafi please"
"A'a yi tafiyar ki muna wurin Ammin mu"
Shagwaɓe fuska tayi
"Ni kaɗai za ku bari a chan? Ammi kina jin su?"
"Ba ke kaɗai ba kam, ki faɗi tsakaninki da Allah ko sanin mun taho ma kin yi in ba da kika ji shiru ba?"
Hararar wasa take yiwa Abeehar suka yi dariya har Ammi ganin ta kasa cewa komai yasa ta juya zata tafi sai ta juyo ta kalli Aisha da itama sun fara sakewa sossai da juna tace
"Ko za mu tafi kawai Aisha?"
Aisha ta zaro ido
"Ni?? Raba ni da shiga shirgin mijinkin nan yanzu su Adda Jannah suka gama labarin rashin mutuncinshi in je ya zane ni?"
Zaro ido tayi
"Yaya Sarakin ne bai da mutunci? A kunnenshi to!"
Miƙewa suka yi suna ce mata ta tsaya ta ji ta rufa musu asiri su ba haka suke nufi ba tuni tayi gaba tana dariya suma duk dariyar suke har Ammi, saura ƙiris ta ci karo da Zarah suka tsaya suna kallon juna, a hankali maganganun Fulani Adama suka shiga dawo mata kaman yanzu suke yi, barin ma da ta ga kyaun da Afeefar ke ƙarawa ga iya ado kaman sarauniya, ga kamshin ta da in ka shaka zaka san ka shaka ko ita da ta tashi a masarautar bata irin dressing da daukar ido haɗe da kamshin da Afeefah ke yi, abinda ya sake sa taji kaman da gaskiyar Adama shine dariyar da ta samu duk suke wanda take da tabbacin yana da alaka da Afeefar idanunta ta sauke akan Aisha dake tsakiyar su Jannah sai kawai ta juya ta tafi.
"Zarah kin tabbatar za ki iya aikata duk abinda za mu saka ki? Sannan za ki iya riƙe mana sirri?"
"Mama kin raine ni ne akan kafafunki kaman ɗiyar da kika haifa da cikin ki, har manta cewa ni ɗin ɗiyar dan uwanki nake don ban taɓa neman abu na rasa daga wurin ki ba, don na taya ki yaƙi akan cikar burinki na tsawon shekaru ban faɗi ba sai ma halarci da na mayar. Dukda Na ji Son Ciroma Sameer a raina hakan ba zai hana na isar da Manufarki yadda ya kamata ba"
"Masha Allah, haka nake son ji yanzu na san ban yi rainon banza ba. Zarah!"
Ta amsa
"Za ki auri Sameer dole sai dai bana so ko kadan zamanku yayi nisa"
Kallonta take da neman karin bayani
"Ba haka aka so ba kuma duk Shigowar wannan Afeefar ne ya ɓata mana komai amma a yanzu za mu gyara, za ki shiga a mata ta biyu amma ke za ki haihu za mu yi duk yadda za mu yi mu hana Afeefah haihuwa da Sameer, ke muke so ki sama mana ɗa namiji daga nan kuma za mu shafe
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 33 Chapter of 40