dasu suka yi mishi godiya suka nufi ciki.
****
Karfe 3:40 ya fito ya wuce masallaci sai wuraren 4:20 ya koma cikin gidan kai tsaye sashen Mammi ya nufa don ya duba ta, tana zaune kan sallaya sai dai kanta na kife ne a bakin gado, da ɗan hanzari ya isa gareta
"Mammi! Lafiya kike kuwa?"
Ta ɗago ta sakar mai murmushi ya runtse ido da ƙarfi, da gaske murmushi take sai dai a cikin murmushin wani irin ciwo yake hanga da damuwa haɗe da gajiya, a idanunta wani abu mai wuyar fassara yake karantowa, tausayi da rauni suka rufe shi wanda basu ɓuya ba sam don a kan Mammi baya iya danne damuwarshi.
"Saraki..! Ina lafiya, ka zauna za mu yi magana"
A gabanta ya zauna kasancewar akwai turkish center carpet mai tsananin taushi da tsada dake malale tsakar ɗakin.
"Ina muka kwana da zancen mu? Saraki babu lafiyayyen namijin da zai iya dawwama ba tare da mace ba, aure na sani ba dole ba ne amma babbar sunnah ce ta ma'aikinmu sannan akwai wani hadisi da Manzon Allah yayi magana akan bayan mutuwar mutum komai nashi zai tsaya chak sai abu guda uku, sadaka mai gudana, ilimin da ya samu ya kuma bayar da shi sai ɗa nagari mai mishi Adu'a ashe baka Fatan ka ajiye 'ya'yan da za su yi maka Adu'a bayan baka nan? Bana so in sake ji ka ce min ba zaka taɓa aure ba wanchan kuskure aka samu da akasin rashin sanin nagarta da kyaun halinka... Ba duka aka taru aka zama ɗaya ba"
Kallonta kawai yake idanunshi duk sun sauya sun zama red har jijiyar kanshi na tashi, sam baya so baya son jin zancen wani aure daga bakin Mammi, a baya dai ya so yi amma bai san mummunar taɓonshi zai sa a hana shi aure ba, bai san za'a iya kallon cikin kwayar idanunshi a faɗa mishi kalmar da har abada ba zai taɓa mantawa ba, baya so a maimaita baya so samm.
"Mammi..."
"RAYYAN...!"
A razane yake kallonta jin yadda ta katse shi, ta katse shi da asalin sunanshi da bata taɓa ƙira ba... Gabaɗaya sai hankalinshi ya sake tashi a raunane ta ce
"Rayyan kana so in mutu ban ga ka samu cikakkiyar natsuwa da kwanciyar hankali ba? Kana so in tafi wurin ubangiji ina tunanin rayuwar ka zai iya taggara bayan babu ni? Kana so in tafi in barka ban cika alkawarin da na ɗauka wa rayuwarka ba?"
"Yaaa ilaihil alameen..."
Ya faɗa a rikice sai ya miƙe tsaye don wani irin tashin hankali yake ji, taku biyu yayi gaba ya juya yayi biyu baya yana shafa kanshi zuwa fuskarshi ji yake kaman ya tsala ihu ko zai fahimtar da Mammi abin da yake ji a cikin zuciyarshi.
Zama yayi ya kalleta
"Mammi saboda ke don ke kaɗai zan amince da zancen aure! Amma ban san kuma ta yadda zan je in cewa mace ina sonta ba, ban ma san menene son ba, ban san ta ina zan fara ba kuma... Na bar miki, na bar miki wuka da nama duk abin da kika yanke ni mai karɓa ne"
Shiru tayi tana kallon shi, ya riƙo hannunayenta
"Mammi kin san yadda na ɗauki alƙawari, na miki alƙawari zan yi iya kokarina a duk abinda za ki yanke a kaina, wanene ni da ba zan miki biyayya ba a duk abin da kike so? Ki kawo ko wacece zan zauna da ita yadda kike so matuƙar hankakinki zai kwanta, matuƙar za ki daina yi min zancen tafiya ki bar ni... Mammi kika ci gaba zuciyata za ta iya tarwatsewa"
Hawayenta ne suka zubo, ta gimtse hannunshi dake cikin nata tana murmushi a lokaci guda ko babu komai zai tuna da ita ta zaɓar mishi mata, zai tuna da ita ya yi mata adu'ar alkhairi a duk sadda zai ga wannan mata ya ji farin ciki, in shaa Allahu ba zata yi zaɓin nan da kanta ba za ta bar wa Allah, za ta tsaya tsayin daka ta roƙi ubangiji yayi mishi zaɓi da kanshi ta san sai ya fi dacewa duniya da lahira...
Anan suka bar maganan ya miƙe ya fice, ta bishi da kallo ta tabbatar yau bacci rabi da rabi zai yi hannu ta ɗaga sama tana cewa
"Allah ga bawanka nan Rayyan! Allah ka sassauta mishi Allah ka yaye mishi matsalarshi Allah ka sada shi da duk wani farin cikin wannan duniya ka bashi dacewa a ƙiyama..."
Ta shafa.
Daga wannan rana Mammi ta dukufa adu'ar neman zaɓin Allah, ko sau daya bata yi tunanin wata mace ba damuwarta kawai Allah ya zaɓa mishi mafi alkhairi cikin mata, ya zaɓa mishi matar da za su tabbata har a aljannah wacce zai so ta, wacce idan ta tashi barin duniyar za ta kular mata dashi ta yadda ba zai yi kukan rashin ta ba don har a yanzu jin Rayyan take kaman yaro ƙarami da kan riƙe hannunta yayi kuka yayi kuka matuƙa idan an faɗa mishi abin da ya taɓa zuciyarshi, har yanzu ganinshi take kaman wannan dakakken yaron mai tsananin juriya da ƙarfin hali wanda duk wani abin da zaka mishi baya bari a ga rauninshi sai in yana gabanta.
Ta ɗauki tsawon sati biyu tana wannan roƙon Allahn a cikin uku bisa ɗayan dare lokacin da Allah ya ce mu roƙe shi zai amsa mana, lokacin da ubangiji ke sama na ɗaya yana neman bayinshi masu roƙon shi ya amsa musu babu hijabi, a yau daren Alhamis safiya juma'a bayan ta gama nafilfilunta ta kwanta kaɗan saboda dan ciwo dake damunta a ciki, dole bacci ya lallaɓa ya dauƙeta ana ƙiran farko na assalatu ta farka a ɗan firgice ta miƙe zaune, a hankali ta saki murmushi mai kyau kan tayi Adu'a ta miƙe ta nufi bayi don gabatar da Alwala.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Comments ɗin ku shi zai yi determining Page na dare🤸♀️*
*28*
Tun ƙarfe goma sha ɗaya na safe Rayyan ya bar office don ya je da wuri yau din saboda wani aiki da ya taso, gida straight ya koma yayi wankan juma'a don yana so ya fita da wuri yana so ya fara biyawa wurin salim da ya rasa gane kanshi a kwanakin.
A shirye ya fito cikin shigan manyan kaya don fa shi yana son manyan kaya haka kawai bai cika son sa kananun kaya ba kaman yadda yake saka manya ɗin, governors yard ne da aka yi wa dinkin zamani ya zauna mishi sossai da sossai, ko da ya fito ɗakin Mammi ya fara yi ya sameta zaune tana azkar ɗinta da bata rabo da shi.
"Sannu da hutawa Mammi"
Ya faɗa yana zama gefenta
"Sannu Saraki ashe ka dawo har ka yi wanka"
Ya gyaɗa kai
"Ina so zan fita da wuri ne zan biya wurin Salim"
"kwana biyu kam bai shigo ba, ko da shike lafiya shi ke ɓuya ko?"
Murmushi kawai ya ɗan yi zai yi magana sai ga Afeefah ta shigo hannunta riƙe da tray mai dauke da plate na abinci.
Bata san yana nan ba da bata shigo ba don fa ita duk abin da zai haɗa ta dashi kiyayewa take saboda yadda bata samun natsuwa a area ɗin da yake gashi abin laifi baya mishi kaɗan yanzu ya hau faɗa da masifa, a gaban Mammi ta ajiye tray ɗin ya bi trayn da kallo kan ya kalli Mammi dake godiya ya ce
"Ba dai wannan abin za ki ci ba?"
Daga ita har Afeefah kallonshi suka yi abinci ne ya zama abu?
"Me yayi?"
Bai amsa Mammi ba sai Afeefah da ya kalla da idanunshin nan yace
"Kashe ta kike son yi?"
Wani irin faɗuwa gabanta yayi jin zancen kisa, hankalinta sai ya so tashi idanunta duk ta zaro waje tana so tayi magana amma Muryar rawa yake, tana da trauma na batun kisa da ita kanta bata sani ba, amma yadda ake jefanta da kalmar kisa yayi affecting mind ɗinta ta yadda ko ya aka ambaci kisa aka danganta ta da shi sai hankalinta ya tashi.
Tsawa ya daka mata cikin muryarshi da ke razana ta
"Na ce kashe ta kike son yi? Me yake damun ki da za ki dafa kowani shirme ki kawo mata?"
Ganin yadda ta sake firgita Mammi ta dafa shi.
"Saraki...! Wai me haka ne? Meyasa kake haka? Idan ka bi ta a hankali ai za ta fahimta ba sai ka yi mata faɗa ba, kuma ni na saka ta dafa min ba gaban kanta tayi ba"
"Mammi ina Merry?"
Yayi tambayar ranshi a hasale, idan da bayanan sai Mammi ta ci abincin nan don ya tabbatar ko don wahalar da wannan yarinyar tayi ta dafa zata iya ko loma kadan ne don yarinyar ta ji daaɗi, Dukda Couscous ne amma akwai abubuwa masu yawa da bai kamata ta saka mata ba ciki.
"Merry bata ji daaɗi ba jiki da jini, Abeeha na school shiyasa nace ta dafa ɗin amma na tabbatar bata gane bayanin da na mata bane ba da gangan tayi hakan ba"
Tsaki ya ja ya ɗauki tray ɗin ya fice.
A ƙasa ta zube tana sauƙe numfashin tsoro yadda yake zaro mata ido kawai take gani, Mammi ta dafa ta
"Ki yi haƙuri Afeefah duk ya firgitaki"
"Mammi ban san akwai abubuwan da bai kamata ki ci ba ciki kiyi haƙuri laifina ne"
"ba wani laifin da kika yi na kirki Alaiyahu da kuma tomatoes da kika saka ciki duk are high potassium veggies da bai kamata in ci ba su ne fa kawai sai zubin da yayi yawa kasancewar Couscous ɗin daga wheat ake samun shi, amma ai ina da ido kuma zan iya miki gyara shi dai kawai zafin kanshi ne dayawa"
Dukda halin da take ciki sai da ta ɗan murmusa kaɗan, yau public holiday shiyasa bata je school ba itama Abeeha wani research take yi shiyasa ta tafi Merry wacce ke da karatu na musamman akan nutrition ɗin irin masu ciwon Mammin bata da lafiya shiyasa ta shiga kitchen ɗin ta girka ba wai don gwaninta ko nuna iyawa ba, jikinta ya yi sanyi bata ma zauna wurin Mammin ba ta fice kar ya dawo ya sameta.
Shi kam kitchen ɗin ya koma, a hankali masu aikin suka zame suka fice sanin kila da kanshi zai yi girkin kaman kuwa sun sani, a take ya fara shirya abincin Mammin, idan ka ga yadda yake aiki za ka zaci wani professional Cook ne cikin taka tsantsan da tsantsar tsafta da Allah yayi mishi, wanke hannu kuwa ko me ya taɓa sai ya je ya wanke hannu da handwash ya dawo, ko sau ɗaya kayanshi bai taɓa komai ba har ya gama ɗan small portion na chicken salad wanda da breast ɗin kawai yayi amfani duk wani ƙashi babu ciki, babu gishiri ya gasa da herbs kawai da lemon, ya haɗa salad din wanda lettuce ne sai cucumber da Bell peppers da albasa kaɗan, ba mayonaise ko cream ya saka ciki ba sai ya zuba man zaitun pure one a cikin dan karamin bowl ya saka 1 tsp na vineger ya kaɗa da 'yar habbatussauda kaɗan ya juye a cikin salad din ya gauraya ya zuba a cikin wani bowl mai kyau. Shinkafa ce 'yar kaɗan ya dafa mata half cup ya haɗa da ruwa don bata shan wani sugar ko juice ya ɗauka ya nufi ɗakinta.
Murmushi ta saki tana mishi godiya, ita bata yi mamaki ba don kafin yayi hiring merry da kanshi yake yi mata duk abinda zata ci shi ya uzzurawa su Abeeha har suma suka iya duk cimar ta da yanayin awon duk sun haddace, godiya ta mishi yace
"Mammi babu fa wannan tsakanin mu har Abada, abin da ya zama min dole ne nayi"
Daga nan ya mata sallama ya koma ɗaki ya sake gyara jikinshi kan ya kara turare ya fice daga gidan.
Kai tsaye gidan su Salim yayi, kasancewar yanzu ba kaman da ba ta babban parlor ya shiga da sallama, Mommy da ke zaune ta zabga tagumi ta ɗago ta amsa a hankali, ya zamu wuri ya zauna yana gaisheta
"Lafiya ƙalau Rayyan ka shigo?"
Samha dake kuka ya ɗan kalla kan ya kalli mommyn
"Lafiya kam mommy?"
"Ba ƙalau ba Rayyan, ban san me zan ce ba ban kuma san ta ina zan fara ba amma tabbas Salim baya cikin lafiya da natsuwar shi... Rayyan ko za ka bashi shawara? Ko zaka mishi faɗa? Don saleem bai ɗauke ni uwa ba kuma, saleem ya fi gane maganar matarshi akan nawa yanzu ya bar nan bayan ya fasa bakin Samha don kawai ta roƙe shi kuɗin makaranta suna shirin exams bata biya ba matarshi ta sa baki sai tace mata ba da ita take ba da ɗan uwanta take shikenan har ya kai abin duka kuma yace ba zai biya ɗin ba rashin kunyarta ya biya mata? Saleem dai ina mishi magana ya ɗaukeni banza? Innalillahi wainna ilaihi rajiun..."
Wasu irin hawaye masu zafi take zubarwa bata taɓa zato ko tsammanin irin wannan butulcin daga Sabrina ba, shi karan kanshi Rayyan yayi mamaki don kowa ya san saleem ya san yadda ya ɗauki mahaifiyarshi da ƙannenshi, shi ɗin mai biyayya ne ko da ko baya so zai yi don ya faranta ran mahaifiyarshi, ya san dai saleem ya chanza mishi amma bai zaci har mahaifiyarshi da yan uwanshi ba, sai ya kira shi ba zai ɗaga ba kuma ba zai kira shi back ba, sau biyu yana zuwa headquarter baya samun shi shiyasa ma ya yanke ya zo gida ya same shi, Dukda shi namiji ne kuma ba kaman sauran maza ba amma daga maganan mommy ya fahimci akwai ayar tambaya mai girma akan saleem.
Bai gama tunanin ba aka fara sallama, sameerah dake zaune shiru gefe ta miƙe ta nufi kofar.
"Mun zo daga companyn gadaje da kujeru ne mun kawo order ɗin da aka sanya wannan address ɗin..."
"Anya gidan nan ne? Ko zaka kira Layin da aka yi order ɗin?"
"Toh bari na ƙira"
Kira yayi cikin mintuna biyu sai ga saleem da Sabrina sun sauƙo, ganin Rayyan ya sa ya je ya bashi hannu suka gaisa
"Saleem kana lafiya?"
Yayi tambayar yana sake nazartar abokin nashi da ya ji wani irin tausayinshi ya tsarga mishi.
"Lafiya me ka gani?"
Girgiza kai kawai yayi ya ce
"Zauna za mu yi magana"
Babu musu saleem ya zauna Sabrina za tayi magana ya ɗaga idanu ya zuba mata haka kawai kwarjinin shi ya wani irin cika ta, duk yadda ta so tayi magana kasawa tayi sai ta nufi kofa ta fice tana kwafa.
"Me ya sameka? Me ke damunka abin da baka yi ba tun kana ƙarami zaka yi shi yanzu da ka mallaki hankalin kanka? Saleem uwa ba Abar wasa bace ba kowace uwa ba, ba irin mahaifiyarka da tayi dedicating lafiyarta, karfinta da kuruciyarta don ganin ta gina rayuwarka ba... Ta gina ka ne don ka girma ka tallafi kannenka, yau idan baka biyawa su Samha kudin makaranta ba wa kake tunani zai biya musu? Me ya hau kanka haka saleem?"
A tausashe yake maganan, saleem bai ce komai ba ya zauna shiru duk yadda Rayyan ya buga ya kaɗa akan ya faɗa mishi menene matsalar bai ce komai ba, daga karshe Rayyan ya ce
"Saleem ka ba Samha kudin makaranta yadda ka saba bata"
Ɗago ido yayi ya kalleshi shima shi yake kallo zuciyarshi na rawa, tabbas akwai ayar tambaya akan dabiun saleem sai dai ba zai yi saurin yanke hukunci ba, yana zaune nan sai da saleem ya dauki tsawon mintuna biyar kan ya zaro wayanshi yayiwa Samha transfer ɗin kudin yadda ya saba bata, mommy ta duƙar da kai tana kuka mai ciwo. Da zafi abin da zafi kana gani a sauyawa danka rayuwa daga yadda yake zuwa wani abu daban.
"Je ka shirya mu tafi masallaci"
Bai ce komai ba ya miƙe ya haura sama, Rayyan ya runtse ido a hankali sama da seconds goma ya buɗe sun dan sauya, Miƙewa yayi ya fice bai kula godiyar da mommyn ke mishi ba, a gaban motar shi ya tsaya yana kallon Sabrina da ke tsaye ana sauƙe wasu kwalaye cikin store nazarin ta sossai yake yi chan ya ɗauke idanu ya sauƙe kan saleem da ya fito, yana kallo sai da yaje wurinta suka yi magana ta ɗaga ta kalleshi kan ta gyaɗa kai saleem ya wuce ya zo ya shiga motar suka fice daga gidan.
"Saleem idan ka ga Afeefah a yanzu za ka iya aurenta?"
Shi karan kanshi bai san ya jefawa saleem ɗin tambayar ba don ya jima yana mishi yawo a rai kuma yana son tabbatar da zarginshi kan Sabrina. Sunan Afeefah ya sake maimaitawa a ranshi don dai bai taɓa ambatar sunan a fili ba ma sai yau.
"Aure? Ai ina da aure"
Ya amsa shi muryarshi babu wannan karsashin idan yana maganar da ya shafi Afeefah, kaman ma wata ce chan daban da bai wani sani ba.
Bai ja maganan ba ya yi shiru, dole su tashi tsaye akan Saleem da alama zautar da shi ake shirin yi, amma yayi matukar mamaki irin mamakin nan da bai taba zaton hakan zai iya faruwa da saleem daga aure ba, auren ma na dangi ba bare ba.
****
Zaune take gaban Mammi don sai da ta tabbatar ya fice kan ta dawo, abincin ta tsurawa idanu yadda ya tsara shi kaman wani chef tana mamakin yadda ya iya girki haka, Mammi bata ce komai ba ta shiga cin abincin sai da ta gama tsaf ta dubi Afeefah tace
"Afeefah akwai maganar da nake so mu yi da ke ko kuma in ce akwai alfarmar da nake so na roƙe ki ban san ko za ki iya yi min ba, ba abu bane da ya saɓawa shari'ar musulunci abu ne da muddin kika amince min Afeefah zan yi matuƙar farin ciki fiye da zaton ki"
Afeefah ta gyara zama jin maganar serious ne, kuma a yadda Mammi ta ɗauke shi da muhimmanci ya sa itama ta ji ta bashi muhimmanci itama
"Tashi ki dawo nan Afeefah"
Miƙewa tayi ta koma kusa da ita yadda ta roƙa hannayenta duk biyu ta riƙe
"Afeefah na dauke ki ne tamkar Abeeha, ba zan taɓa yin wani abu da zai cutar da rayuwarki ba amma ban san yadda za ki ɗauki maganar ba.."
"Mammi yanzu fa kika ce ni tamkar Abeeha ce a gareki nima kuma ba ni da uwar da ta wuce ki, wlh duk abin da kike so matuƙar zai faranta miki kuma bai saɓawa shari'a ba ni mai amincewa ne Mammi, faɗa kawai za ki yi in cika shi na san ba za ki taɓa cutar da ni ba."
Afeefah ta katse ta ganin kaman contemplating take na gaya mata abin da take so, ita kuma tana da yakinin koma menene Mammin za ta roƙa ba sharri bane.
"Afeefah za ki iya auren Saraki??"
Afeefah ji tayi kaman kunnenta bai ji mata daidai ba, bata motsa ba don bata gama fahimta ba jin Mammi ta yi shiru tana kallonta yasa tace
"Mammi ina sauraranki in shaa Allahu zan yi duk abin da kike so"
"Afeefah abin da nake so shine kafin na mutu in ga na haɗa aurenku ke da Saraki...! Shin za ki iya auren shi? Za ki iya yi min wannan alfarmar?"
Wani irin shock ne ya ratsa Afeefah daga kanta har cikin tafukan sawayenta, a matuƙar razane ta zare hannunta daga na Mammi ta miƙe tsaye zuciyarta na wani irin bugawa kaman zai ratso kirjinta ya fito
"a..ure? Ni Mammi? Ni... Ni Afeefah da Wanchan mutumin...??"
Don ji tayi ba zata iya ƙiran sunanshi ba ma ko Rayyan ɗin ko Saraki idan tayi hakan kaman wani zunubi ne da muddin ya ji ta sai ya sauya mata kammani, kallon kanta take yi daga sama zuwa kasa ta ɗago ta kalli Mammi kaman wacce ta zauce...
🖤Gureenjoh🖤
https://chat.whatsapp.com/BuI7cmoy3ed3C3IimZKZA0
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*29*
Hasaso Rayyan ɗin ta shiga yi a majigin kwakwalwarta, kallo ɗaya tak za ka yi mishi ka san cewa shi ɗin soja ne a sojojin ma na daban, yana da lafiyayyar jiki murɗaɗɗe kuma a tsaye yake fatarshi babu ɗigon baƙi ko guda ɗaya, Dukda ba zata ce ga yadda yake cikin khaki ba amma ko daga maganar shi zai tabbatar maka jajirtacce ne kuma gwarzon namiji wanda ko daga kallonshi za ka sha jinin jikinka.
Zaman shi, tafiyar shi da yanayin dabi'unshi kuwa za ka zaci wani babban sarkin ne na wani yanki na daban, yana da wasu irin idanu kyawawa da ko tuna yanayinsu tayi sai ta ji tsikar jikinta ya zuba kaman ba namiji ba, fasalta kyaun fuskarshi da sauran halittar da Allah yayi mishi ma wani tulin bayani ne na daban, don Allah ina ita ina irin gawurtaccen nan? Ta ina ma Mammi ta fara wannan tunanin?
Tazarar da ke tsakaninta da Rayyan kaman tazara ne da ke tsakanin sama da ƙasa ko ta amincewa aurenshi ita ce zata wahala daga karshe saboda ba zai taɓa son irin ta ba, ba zai taɓa kaunar mace kamar ta ba wacce ta fito daga kauye cikin tsantsar jahilai, wacce take da tambarin Maita kuma annoba, wacce ko wucewa ta zo yi gidajen mutane sai an zuba tafarnuwa, Ƙashin kifi da garin kukan miya a wuta don hayaƙin Mayu.... Ai ko da gami wane ita da Rayyan.
"Mammi kaman ban ji abin da kika faɗa ba"
Ta sake maimaitawa har yanzu a kidime.
Miƙewa tsaye Mammi tayi ta riƙo hannunta suka koma zaune.
"Ki natsu Afeefah kin ji? Ki ba ni hankalinki kar ki yi wani tunanin fin ƙarfi, namiji bai taɓa fin karfin mace ba in har ta amsa sunanta mace, ke kyakyawace kar kyaun Rayyan ya ruɗe ki, ke yarinya ce mai hankali, ladabi, natsuwa da kuma biyayya kina da zuciya mai kyau, you are the purest soul i've ever met... Afeefah ba zan hada ki da Rayyan bane saboda wani ra'ayi nawa ko buri eh ina da buri a kan ku duk biyu, sai dai burin ba na komai bane sai na son ganin rayuwarku duk ya inganta kun tabbata cikin farin ciki"
"Mammi shi ya ce miki yana so na?"
Ta tambaya a sanyaye don ba fahimtar kalaman Mammin take ba don abu ne da take ji ba zai taɓa yiwuwa ba.
"Ba shi ya ce ba, ni ce na ga cancantar kasancewarku inuwa ɗaya kar ki damu da halinshi ko yanayinshi na fushi da dacin rai Saraki na da wani tabo ne da ya mayar da shi hakan wanda dole zan faɗa miki Afeefah... Ina so in fada miki ba don tonon asiri ba, sai don ya zama dole ki sani kan ki yanke shawarar za ki aure shi ko ba za ki aure shi ba? Ba zan miki dole ba wlh kuma ba na so ki dube ni a yayin yanke hukunci ki yanke duk abinda ke ranki ni me karɓa ce don sai da na nemi zaɓin Allah kan na tunkareki"
Shiru Mammi tayi idanunta sun rine sossai har suka tara hawayen da ya fara bin ƙuncinta, ɗacin maganan da zata faɗa take ji har kan harshen ta maganan da bata taɓa faɗa da Bakinta ba bata taɓa ambata ba sai a yau da ya zame mata dole, idanunta na kallon gefe ta furta
"Rayyan ba ɗa na bane!!!"
Wani irin bugawa zuciyar Afeefah yayi da har sautin shi na fitowa fili ta zaro idanu gabaɗaya tana kallon Mammi dake ta zubar hawaye
"Eh Afeefah ba ni na haife shi ba, hasali ma babu abin da ya haɗa ni da shi na jini ko na kusa ko na nesa... Ni sunana Khadija ni haifafffiyar wannan gari ce ta Kaduna, mahaifina Alhj Isma'il mai rasuwa mutum ne mai tarin dukiya mai yawa a gaske kuma su biyu Allah ya ba wa iyayensu ɗan uwanshi ma na da nashi arzikin don gada suka yi, mahaifina mutum ne da dukiyar shi bai taɓa rufe mai ido ba, yana da kyauta tsantsa haka yana da taimako don haka ko da na zama ni kaɗai 'yar shi yana da ƴaƴa dayawa da suke karkashin shi don lakabinshi ma shine Uban marayu da masu uba... Yaran da ya biyawa suka karatu basu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 40