Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
there on time Nonsense…! Wani irin rawa da jikinta yake ya sa tuni askar ya zame ya faɗi ƙasa yana ba da sautin kwankwataraaaan, yadda kalamanshi suke fita a hautsine cike da zafi da ɗaci mai tarin zallar gaskiya haka su ke hautsina mata 'yar hanji suna kaɗa hantarta kuma suna shiganta ba da wasa ba. Tun da idanunta suka sauƙa cikin nashi a karon farko ta yi saurin sadda nata ƙasa don ba za ta iya ko da gangancin jurar ganin cikinsu ba, ganin tana shirin zubewa a sume ya sa salim damke hannun Rayyan da har kaman zai rufeta da duka at any moment ya ce "Calm down please dude" Ya maimaita kusan sau uku don ya san hayaƙin kan rayyan ba kowa ne ke iyawa dashi ba, hatta shi karan kanshi wani lokacin shakkar shi yake saboda wani irin kwarjini da Allah ya zuba masa na ban mamaki, bare wannan yarinya da rubdugun rayuwa yayi mata ƙatutu. "Sister ku taimaka mata ko da allurar bacci ne samu ta huta ta kuma samu natsuwa please" Salim ɗin yayi directing kalaman to nurses ɗin, da sauri suka shiga ƙoƙarin aiwatarwa don babu wadda bai san Zafin kan Surgeon General Ryan Moh'd Khamis ba, a lokacin da suka roƙi ta kwanta ko uhmm bata yi ba ta miƙe flat zuciyarta har a lokacin tana jin shi a tsaye kyamm tsabar tsoro. Jan Rayyan da ke tsaye ya zubawa gini idanu yayi suka fice, haɗadɗen office ne mai cike da ƙawa tamkar ba asibiti ba suka shiga, fasalta kyau da tsaruwar office ɗin bata lokaci ne sai wani masifaffen ƙamshi yake fitarwa tare da sanyin Ac mai ratsa jiki. A doguwar kujera Brown mai cin mutum uku salim ya mishi masauki, ya nufi chan dungu wurin wani tsararren frigde ya buɗe ya ɗauko mishi ruwa masu sanyi ya taho ya miƙa mishi bayan ya ɓalle murfin ba tare da yayi magana ba ya karɓa kaman faɗa ya kafa kai, sai da ya shanye tasss kan yayi wurgi da goran "I need some space Salim" Maganan ya fito daga chan ƙasan maƙogoronshi in ba ma salim ɗin hankalinshi na kanshi ba ba zai taɓa cewa shine yayi maganan ba, dama kuma ya san za'a yi hakan dole ya fice ya barshi nan yana zamewa kwance cikin kujerar Dukda tsawon shi ya zartawa kujeran nesa ba kusa ba. Salim na fita ɗakin ya koma ya janyo kujera ya zauna tare da tsura mata idanu, duk da ba zai ƙira ta kyakyawa ajin farko ba sai dai tana da nata qualities ɗin na daban da ba kowa ke da shi ba kuma da matuƙar wuya a same su wurin wata macen, baƙa ce amma baƙin mai haske tana da doguwar tsiririn fuska da dogon hanci duk da idanunta ya musu kallo ne na tausayi don a rine suke a kuma firgice zai iya ƙiransu manya kuma farare, girarta kaman ita ta zana yanayin tsawon gashin idanunta da ma masu sheƙi irin na baƙaken Fulani dake kwance lublub bisa goshinta za su tabbatar maka da cewa tana da tarin suman kai, bakinta kalar peach da ya ƙara haskaka kalar skin ɗinta ya amshi fuskartata. Ta yi mishi yarinya kwarai da tunanin kisan kai, kuma ya tabbatar duk abin da zai saka mutum tunanin kashe kan shi ba ƙarami ba, ba zai ce ga iya adadin lokutan da ya ɗauka yana gwamutsa biyar da goma ba a kan matsalar yarinyar sai motsin ta ya ji, da ɗan hanzari ya mayar da hankalinshi kanta don dama tuntuni kallonshi na a gareta. "Sannu 'yanmata kin farka?" Tsura mishi idanu ta yi tana tariyo abin da ya faru a ɗazu da sauri ta shiga dube dube tana jin gudun zuciyarta na wani irin ƙaruwa ganin firgici a idanunta ya sa ya miƙe ya isa gangarta yana furta "Natsu 'yanmata dodon ɗazu ba ya nan, da ma matuƙar wuya ki sake ganinshi a gangarki." Numfashi mai nauyi ta sauƙe duk da tarin tsoron da take ciki hakan bai hana kalamanshi na ɗazu na sake bijiro mata ba, wani irin sanyin jiki da tsoron Allah na lulluɓeta a take ta fara tuba hawayenta na ɓallewa take furta "Allah na tuba ya Allah! Wallahi na yi nadama Allah na san kana sane dani da kuma halin da nake ciki ya Allah ka sassauta min, Allah ka ba ni ikon ƙarbar kaddara ta a yadda ta zo min Allah ka yafe min..." Sossai take kuka har tana shiɗewa, bai hana ta ba ya barta tayi kukan sossai har tana ajiyar zuciya kan ya ɗauki ruwa ya miƙa mata, sai da ta jima tana kallon hannun nashi kan ta sanya hannu ta karɓa ta sha sossai kan ta sauƙar tare da gintsewa cikin hannunta tana sauƙe numfashi ta sake ƙura wa bango idanu. "Ya Sunanki?" Ta ji tambayar ya zo mata, kallonshi ta yi yana da tausayi haka yana da sanyin hali duk da khakin sojojin da ta ganshi da shi ba irin wanchan ɗayan ba da ko a mafarki bata fata ta sake ganinshi don kila sai ta sume. "Afeefah" Ta furta a hankali "kina da suna mai daaɗi Afeefah". Shiru ta yi. "Ko za ki kwanta ki huta? Ko in samo miki abin da za ki ci?" Nan ma shiru tayi, a hankali kuma ko me ta tuna tace "Eh" "Eh wa wanne kenan? Kwanciya ko abinci?" Da wasa yayi maganan hakan ya sa ta sake kallonshi kan tace "kwanciya" "duk biyu dai Afeefah, yanzu kwanta ki na hutawa ni kuma zan je in samo miki abincin kin ga ina dawowa ke kuma kin gama hutawa sai cin abinci ko?" Ta gyaɗa kai "yauwa Afeefah" Kwanciya tayi shi kuma ya fice. Ya fi awa ɗaya da fita kan ya dawo, ya samu wani baccin ya ɗauke ta yadda kuma fuskanta da idanunta suka sake suntuma suka tabbatar mishi da ta sake wani kukan fiye ma da na ɗazu. Sossai ta bashi tausayi adu'ar samun sauƙi a ko ma menene dake damunta ya yi mata kan ya ajiye babbar ledan da ke hannunshi ya fice, office na Ryan ya koma sai dai ya samu a rufe girgiza kai yayi kan ya juya ya koma nurses station inda ya roki a duba mishi Drn da Ryan yayi referring ɗinta to don ya san ko mutuwa za tayi ba zai sake duba ta ba. Ganin Dr Sulaiman ya sa ya nufi office ɗin nashi. Dukda Captain Saleem zallar soja ne na ƙasa wato land army sai dai tarensu da Ryan ya sa kusan duk wadda ya san Surgeon General Ryan Moh'd Khamis ya san Salim, Salim shi ne ƙwallin abokin Ryan don shi kaɗai ke iya tolerating murɗaɗɗiyar halinshi da zafin Ranshi sam Ryan ba shi da hayaniya kuma ba ya shiri da mai hayaniya, ba ya dogon magana kuma ko da ido yana so idan yayi magana ka fahimce shi bare kuma in ya buɗe baki ya furta ko za ka mutu ba zai maimaita ba, yana da saurin fushi kullum a hasale yake ga ko in kula a koma menene matukar ba shi ya so yin abu ba babu mai mishi dole, sarauta da ƙasaitarshi wane sarki don har wasu kan tambayi ko shi ɗin jinin sarauta ne? A kofan office ɗin yayi knocking aka bashi izinin shiga ya sanya kai, Dr Sulaiman ya miƙe ya bashi hannu suka gaisa kan ya zauna yana dubanshi yace "Dr. Ka san yanayin aikin namu tafiya ce ta kama ni babu zato, zan tafi Kano kuma zan kwana biyu ban san ko za ka iya sallamar ta a yau ba samu in mayar da ita kar in tafi kuma aiki ya riƙeni in kasa dawowa da wuri". Dr Sulaiman ya buɗe file ɗinta ya sake dubawa sossai kan ya ɗago yana kallon Salim ya shiga cewa "A gaskiya cap. Sallama ba zai yiwu yau ba yarinyar jininta yayi ƙasa sossai matuƙa kuma ka san hatsarin hakan, ga damuwa dake dukar zuciyarta shiyasa take ta complain ciwon kai da kirjin dole tana buƙatar kulawar likita atleast na kwana uku zuwa huɗu". Ajiyar zuciya salim ya saki. "Dr Sulaiman ko za ka taimakeni don Allah ka kula da ita har na dawo?" Murmushi Dr Sulaiman yayi "Kar ka samu matsala In shaa Allah zan kula muku da ita, akwai wata tsohuwa dake mana aiki gida zan ɗauko ta ta zauna muku da ita har ku dawo" Godiya sossai salim ya mishi kan ya fice. Ko da ya koma ɗakin ya samu ta farka abinci ya sa ta ci yana ɗan janta da wasa yana mata hira har ta ce mishi ya isheta bayani yayi mata a kan bayan Magrib zai bar garin akwai mai zuwa ta zauna da ita har ya dawo in shaa Allah yana fata kan ya dawo ya samu ta yi sauƙi samu ya mayar da ita gida Fatan hakan ba zai haifar mata da matsala ba? Ta amsa da "uhmm" a ranta take raya a yanzu ko ɓata ta yi ɓat a duniya babu mai neman ta bare ya damu da wanzuwar ta ko akasin hakan, yanzu haka aka tambayeta ina za'a kaita bata sani ba don ko giyar wake ta sha ba za ta tunkari wurin uncle ba dolenta dai shi ne kawu, Nan ma kuma bata san abin da za ta iya riska ba Shikenan ta koma Square Zero? Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga zubo mata. "Afeefah!" 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh *FREE BOOK* *009* Captain Salim ya ƙira sunan nata cikin tausasawa, ta ɗaga ido ta kalleshi. "Akwai wani matsala ne?" Ta girgiza kai. "Na gode sossai Allah ya saka maka da mafificin alkhairi" Yayi mata murmushi, bai bar ɗakin ba sai ga dattijuwar matar kuɗi masu kauri ya fitar ya ba dattijuwar saboda sayan abinci ya nuna mata kaya kala biyu dogayen riguna da ya siyo da man shafawa, macline, brush, turare da soson wanka ya roƙe ta da ta kula da ita don Allah har ya dawo, kaman kar ya tafi haka ya fice a ɗakin domin haka kawai ya tsinci kanshi cikin tsantsar tausayinta da har yana so ya yiwa zuciyarshi yawa. Baaba jummai macece mai faram-faram da saurin sabo duk yadda Afeefah ta yi shiru sai ta saka ta magana har da murmushi, tana kula da ita sossai sossai, bata maƙe kuɗin da salim ya bata ba ta kan sayo musu kayan daaɗi ta bajo musu tana cewa "Ke 'yannan sa hannu maza ki ga mu ci kin ga ko mutuwa muka yi yanzu za'a ɗauke mu da nishi saboda nauyin mu ina amfanin kana da shi baka ci ba? Maza-maza sa hannu" Dole Afeefah take murmushi kuma ta biye wa Baaba ta ci sossai dare idan an gama duba Afeefar kan su kwanta bacci za ta shiga ba ta labarin aurenta da ma rayuwar da tayi har ma da irin kishin su na da chan baya da kissa kala kala da kan kashe Afeefah da dariya, kan kwana biyu ya zagayo har ta fara manta tarin damuwarta, duk Sallar ta kuwa bata taɓa mance iyayenta da Aunty zee ba ta kan kai wa Allah kukanta musamman cikin dare akan ya gafarta musu yayi musu rahama (Tana roƙon duk wanda ya zo across wannan littafi ya nema musu rahama domin Allah🙏) Kaman yau Dukda safiya ce bayan sun gama karyawa da doya da miya haɗe da shayi da duk a bakin asibitin Baaba ke sayo musu ta dubi Afeefar da ta ɗan yi shiru tana tunani tsoron ta ɗaya dawowar salim ina za tace ya kaita? Ina ta nufa? Ya zata yi? "Wai 'yannan kin kuwa san abin da ke ƙara ba ni mamaki ma a wannan zamanin?" Afeefah ta girgiza kai tana ɗan kakaro murmushi don ta san zancen baaba bai taɓa wuce kan taɓarɓarewar tarbiya a wannan zamani ba. "Mu a lokacin mu ina mace ta isa ta ƙira ko mai irin sunan mijinta? Kai ko bayan ya mutu ko kun rabu mu kam ba ma iya kiran sunan ko da kuwa da kuskure amma ki ji mace yanzu gatsal tana cewa Ummaruuu a gaban yara ma da iyayenshi ko nata kai ko a gyalen su" Dariya Afeefah ke yi sossai tace "Yanzu Baaba ko sakin ki yayi ba za ki iya ƙiran suna mai irin nashi ba?" "Eh mana! Ai da kunya 'yannan" "Tabb baaba ba dai irin sakin wannan zamani ba, komai fa akwai silar chanzuwarshi Baaba bai wuci mazan ma na da na yanzu ba ɗaya ba ne shiyasa ake ganin bambanci" "za dai ki kare su ni dai na faɗa miki ki kiyaye, kin ga maza suna matuƙar son a ba su girma, idan za ki ba namiji girma toh tabbas mutuncin ki ma zai zama daban ne a idanunshi ko da kuwa ya auri wata ne" Tana murmushi sossai tana tuna wato gidan kawu Labaran ban da rashin tarbiya har da tarin jahilci da suke dashi, daga mu'amalar iyayen har ta 'ya'yan gashinan dai gashi nan yo idan ta ciwo shi ai sai dai a ji suna dambe da mata... Fuskanta ɗauke da murmushi tana sake jinjina rayuwar da don baaba jummai na sake bata labarin yadda maƙota sai ya hukunta ɗanka baka sani ba idan ma ka sani ka je har gida ka mishi godiya amma yaran yanzu ko kanwarka ce ka mari yaronta gabanta sai ta maka Allah ya isa a gaban yaro to me yasa ba za'a lalace ba? Haka batun ƙarfafa zumunci Meyasa zumunci ba zai yi ƙarancin ba yara suna 'yan pendo da ɗan kawu amma idan wanchan sun fi kuɗi sai ka ga yana nuna bai san yayyunshi cousins ba ko ya fi karfinsu uwa kuma ta kasa kwaɓa saboda tana ganin hakan ce daidai daga mutum mai kuɗi ne level nashi ya fi karfin talaka ko da kuwa cikin umma ɗaya ne. Turo kofan yayi bakinshi ɗauke da sallama a kanta idanunshi suka soma sauƙa, ajiyar zuciya ne ya kufce mishi ba tare da ya san dalili ba murmushi na yalwatuwa a fuskar tashi ganin ko da suka hada idanu murmushin bai kau daga kan fuskanta ba, fara'a na yi mata kyau ya ayyana hakan a ranshi maganan Baaba ne ya yanke mishi tunani "Bawan Allah sannu da dawowa, lale maraba" Ya saki murmushi ya ɗan rankwafa ya shiga gaisheta ta amsa cike da kulawa tana tambayar shi aikin da sanya mishi albarka, Afeefah ya duba da ta ɗan duƙar da kai tana kallon yatsun hannunta "Na shigo kuna ta raha me yayi miki daaɗi haka Afeefah?" Ta ɗago tana murmushi "Ni da Baaba ne, barka da dawowa" Yana zama gefen gadon tuni ɗakin ya cike da sassanyar kamshin shi ya ce "Yauwa ya jikin? Hope kin samu lafiya?" Ta gyaɗa kai tana dorawa da "Alhamdulillah na gode" Da Baaba suka cigaba da hira akan jikin nata ita dai sai murmushi bata magana har Dr. Sulaiman ya shigo, sai da suka dan sake hira kan ya miƙawa salim takardar sallamar ta "My patient is good to go, kawai dai ta kiyaye sa damuwa a ranta and gaskiya ku kula da ita sossai da sossai Dukda SG Ryan yayi mugun ƙoƙari a kanta babu wani traces na guba a jikinta amma don Allah ku sake kula, ke kuma Afeefah ki saka a ranki komai yayi zafi maganinshi Allah. Manzon Allah S.A.W ya ce; "Wanda ya gangaro daga kan dutse ya kashe kansa, to yana nan madawwami a cikin Wutar Jahannama yana ta gangarawa har abada. Wanda kuma ya sha guba ya kashe kansa, to gubarsa tana nan a hannunsa yana ta kwankwadar ta a cikin Wutar Jahannama, yana madawwami a cikinta har abada. Haka wanda ya kashe kansa da wani karfe, to karfensa na nan a hannunsa yana ta soka wa cikinsa a cikin Wutar Jahannama, yana madawwami a cikin ta hakan har abada. (Sahih Al-Bukhaariy: 5778; Sahih Muslim: 109)". "Allahu akbarr" Baaba jummai ta zabga kabbara Afeefah dai kanta ƙasa zuciyarta na sake shiga cikin tsantsar nadamar wannan yunkuri da tayi da ta mutu ta shiga ukunta. Godiya sossai ta musu haka salim yayi wa Sulaiman da Baba godiya murmushi kawai Sulaiman yayi yana shaida wa Baaba akwai driver waje zai mayar da ita gida sai ga Baaba na hawayen rabuwa da Afeefah Dukda zaman nasu na kwana biyu ne amma sanin ranar sake haɗuwa sai Allah, Afeefar ma sai ta kama hawaye, a duk sadda ta ga wani ya kaunace ta Saboda Allah ta kan ji son shi fiye da yadda shi ya kaunace ta don masu hakan a gareta basu da yawa, bata yi shiru ba ko da Baabar ta tafi sai ma zuciyarta da ya tsinke, tsoro da fargaba suka lallaɓo suka rufe ta. Daram! Haka zuciyarta ya buga a sadda Salim ya ɗauki 'yan kayanta yana furta "Mu je ko Afeefah?" Jiki a saɓule ta sanya kafafunta ƙasa ta shiga takawa har ta wuce shi yana riƙe mata da ƙofa bayan ta fita ya ja kofan a bayanta ya rufe suka jera a tare har motar shi, ya buɗe mata gidan gaba ta shiga ya buɗe baya ya ajiye kayanta kan ya zagaya ya shiga ya ta da motar suka fice daga cikin asibitin, cikin natsuwa yake tukin kan ya ɗan kalleta "Anchau muka nufa ko?" Kamar mai karyayyen wuya haka ta gyaɗa kai gabanta na dukan tara-tara, bata fata Uncle ya raba ta da su suhail bata fata su tashi a hannun kishiyar uwa, daga shi har yaran wani irin tausayinsu take ji har ɓargonta bata ga laifin uncle ba don ta tabbatar dole mutuwar Aunty zee ta jijjiga shi fiye da ƙima tana fata da adu'ar Allah ya sa ya sassauto ya karɓeta kar ya kore ta. Salim ya gyaɗa kai shima, motar ya ɗauki shiru na seconds kan yace "Afeefah!" A hankali ta amsa "Na'am" "Na san kowa abinda yake faɗa miki jarrabawa, kaddara haƙuri. nima ba zan chanza ba don akan hakan Allah ya halicce mu haƙuri kuma da kaddara ibada ne kaman yadda ya halicce mu don mu bauta masa, idan kika ga na wani Afeefah sai kin yi hamdala wani jarabawar shi 'ya'yanshi, wani za ki samu jarabawarshi Mata ne, wani talauci, wani dukiya hatta Mahaifiya ta kan iya zama mummunar jarabawar ɗa, kaman yadda rayyan ya faɗa kuma Sulaiman ya ba ki har hadisi, da kashe kai shine mataki mafi sauƙi a yayin da duniya ta yi wa bawa tsanani da ba za mu tarar da miliyoyin mutane ba a raye, akwai wani hadisi da Manzon Allah S.A.W ya tashi tsoratar da masu yunkurin kashe kansu da ko tunanin aikata hakan ka yi to ka yi gaggawar tuba ka tsarkake zuciyarka daga shaidan. Ban san irin naki ƙalubalen ba amma ina sake jan hankalinki da ki kiyaye dokokin Allah ki duƙufa da Adu'a In shaa Allahu komai yayi farko yana da ƙarshe kinji ƙanwata?" Kai ta gyaɗa mishi a hankali cikin sassanyar Murya tace "Yaya Salim hakika ba ni da bakin gode muku, kun ceceni daga azabar Allah da baku zo ba a lokacin da ban san a yanzu wani hali nake ciki ba. Na gode Na gode Allah ya yaye maka naka matsalolin ya saka maka da gidan Aljanna" Ya amsa da Ameen yana ɗan murmushi. Kaman yadda ta zata isar su Anchau kai tsaye gidan uncle suka yi, ko da ya tura yaro yayi mishi sallama da uncle ba'a jima ba sai gashi ya fito idanunshi na sauƙa kanta yayi mugu-mugun ɗaure fuska bai tsaya ma salim ya gama bashi haƙuri da koro mishi jawabin da ya sa bai dawo da ita kan lokaci ba ranar ya shiga karta musu rashin mutunci yana kwashe mata albarka duk yayi wani irin susucewa, sai jefanta yake da munanan kalamai da suka zama tamkar rurin garwashi a zuciyarta, ya shiga tuna mata Alkhairin Aunty zee a rayuwarta da mugun sakayyarta, ya kuma yi alkawarin muddin bata bar mishi kofan gida ba wallahi shi zai kawo karshenta yayi ajalinta. Kokarin bashi hakuri salim ya shiga yi ganin tana wani irin kuka amma ina tuni ya soma tara musu jama'a babu arziki suka koma mota, ta haɗa kai da gwiwa tana ƙara fashewa da wani kukan mai taɓa zuciyar duk mai saurare. A hankali salim ya ja motar sai da suka yi nisa sossai yayi parking tare da jingina bayan sa da jikin kujerar ya lumshe idanu yana sauraren kukan nata da idan har ka ji ka san duniya bata yiwa mai yinsa daaɗi. Sai da tayi ma'ishi bai ce mata komai ba da kanta ta ɗago ya miƙa mata ruwa ta fita ta wanke fuskanta ta dawo ta sha kaɗan kan ta miƙa mishi ba tare da ta kalleshi ba ya sa hannu ya karɓa. "Ki yi haƙuri Afeefah!" Ta gyaɗa kai "Yanzu ina kuma kike da shi da zan kai ki?" Hawaye ne ya sake cike idanunta a sadda take furta "Akwai kawuna a Dutsen-wai" Cikin dasasshiyar muryarta da ya dishe saboda kuka. Motar ya ja tare da miƙa hannu ya kunna musu ƙira'a domin zuciyarta yayi sanyi. Awanni kaɗan ya sada su da kauyen, ita tayi ta nuna mishi hanya har gidan kawu Labaran. Yana zaune rumfar kofar gida yana cinikin Nono da wata bororuwa ganin tsayuwar mota ya sa ya shiga shafa rantalin kanshi da babu gashi ko guda sai maiƙo yake a rana, a tunanin shi ɗaya daga samarin yaranshi ganɗa-ganɗa da suke zaune ba aure ne domin sun rantse sai mai maiƙo iyayensu mata kuma sun ba su goyon baya alhali gidanshi ko keken hawa mai kafa biyu babu. Idanu ya ƙura mata bayan sauƙowarta yana tunanin inda ya santa kan ya zabura ya runtuma a guje sai cikin gida, ganinshi da gudu ya sa mata da 'ya'yanshi kowa ya fara yin ta kanshi don tsallake su kawai yake bai tsaya ba sai da ya dangana da ɗakinshi ya zaro sandar goran shi tare da wasu manyan layu ya zura a wuya, wasu ya saka a hannu kan ya fito ya nufi waje da saurinshi har yana kifawa.... 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh *FREE BOOK* *010* "Hohohooo! Da ma an gaya min za ki dawo, za ki dawo da shirin ki da ya ci uwar na da kuma sai ga ki, to idan ma junanki sammako ni a tafe na kwana yarinyaa! Namana guba a bakin ki dodanniyar Mayu!" Yadda yake maganan a kan muryarshi ya sa tuni su inna Asabe suka yo waje, abin ka da ƙaramin ƙauye tuni maƙota ma sun fara leƙowa, daga Salim har Afeefah sun kasa ko da motsi ne barin ma ita da wani tsoro ya sake rufe ta. Tuni matasa suka shiga neman makami don ma kayan sojoji ne jikin salim kuma harda ƙaramar bindigar shi a gefen ƙugunshi. Kawu ya nufa da yake zaro maganganu tamkar sabon kamu wai enchanting words ɗin kariya yake daga Mayu ya furta "Haba Malam! Ba ka gane ta bane? Ya duk ka firgice kaman wanda yayi karo da zaki?" Kawu ya gyaɗa kai ya kuma girgiza yace "Hayyyaa yaro yaro ne! Ni ko na santa farin sani, kai ma na tabbatar da ka san wacece ita babu abin da zai sa ka bari ta shiga motarka. Wannan mayyar da ta cinye min zuri'a ta je ta cinye na uwarta shine ka dawo min da ita kofar gida?" Waigawa salim yayi ya kalleta har lokacin tana kafe kyam kaman mutum-mutumi ya waigo ga kawu hes very confused da kalaman da ake jefa mata gwara wanchan ta ce mijin yapendonta ne amma wannan dake wa ga mahaifinta? Ji abin da yake kaman sabon kamun hauka? "Amma malam ka kuwa san yadda shari'ar maita take? Me yasa za ka jefeta da wannan kalma ta Ƙazafi? Ita ɗin fa 'ya ce a gareka kuma addini kai ya ɗora wa kulawa da ita da bata kariya tunda mahaifinta baya raye amma don Allah dubi abin da kake yi na ƙarancin ilimi, duk ka tara mana mutane? Me yayi zafi haka?" "Wuta! Na ce wuta ne yayi zafi, wallahi idan baka daina haɗa ni da wannan yarinyar ba kai ma sai na rotsa kan ka da wannan sandar bar ganin ka da kayan sojoji, tun muna shaida juna ka ɗauke ta sawunku a likkafa ka mayar da ita inda ka ɗauko ta ai

Chapter 5 of 40