Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
aiki, ta ce "Talatuwa me kike dafawa?" "Tuwo ne da miyar egusi shi mutanen gidan suka ce a dafa musu" "Toh bari ki ɗora min fried Rice da kaji iyayena za su zo ganin ɗakina ba zan tarbesu da tuwo ba" "Amma S..." "Kin yi abinda nace ko sai na bi ta kanki? Har kin isa ja da ni typical 'yar aiki? Toh wallahi ki kiyaye ni" Sadiqa da ke shigowa ne tace "Haaa me ke faruwa da ihu haka?" Talatuwa ce ta mata bayani sadiqa ta kalleta sama da kasa "Amma ba ki da hankali yanzu su Gajen ne baƙi da har za'a dafa musu kaza da wani fried Rice? Dama shi suka saba ci a gida?" Sabreena ta riƙe baki tana kallonta na seconds kan tayi wani murmushi kawai ta juya fuuuuu ta fice. Mommy na nan zaune tana tunanin wannan lamarin da bata gane kanshi ba bare ƙasan shi ta ga wucewarta kamar iska, ba'a fi mintuna biyu ba sai Ga saleem rike da belt nashi na sojoji ko mommy bai kalla ba ya shiga kicin ya ya kuwa samu Sadiqa ya rufeta da dukar kawo wuka.... 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh *FREE BOOK* *Ku lallaɓa wannan kaina ciwo wallahi kaman zai faɗi* *26* Ihu take yi sossai na neman agaji, shi kuwa tamkar wanda ake zuga shi dukan ta yake kaman an aiko shi cike da wani haushi nasu da dama yana kwance ƙasan ranshi, Mommy da ta shigo da gudu ne ta riƙe belt ɗin a tsorace take cewa "SALEEM! SALEEM!! Me haka? Me ya hau kanka? Sadiqa fa kake yi wa wannan duka kaman wanda ya kama ɓarawo? Sadiqa fa ba sameerah ko Samha ba?" "Na kula rainin sun ya fara yawa ne, kuma wallahi kaɗan na mata ko kallon banza ta sake yiwa Sabrina ta gani bare zagin iyayenta sai na yi ƙasa ƙasa da ita, marasa kunyar yara kawai..." Yana kai nan ya wuce fuuuuu mommy dake tsaye kaman an dasa ta jiri ya kwashe ta ta tafi zaune. "Innalillahi wainna ilaihi rajiun me ke faruwa?" Sadiqa da baƙin ciki kaman ya kasheta tana dukunkune gefe tana kuka sossai don ba laifi ta bugu ta ce "Me kuwa mommy? Duk wa ya ja mana? Wlh babbar alamar tambaya ne akan yarinyar nan dama ni ba sonta nake ba kika saka shi dole aurenta yanzu wa gari ya waya? Tun fa ba'a je ko ina ba mommy wlh ba zan iya zama da yaya a wannan gida ba, ni zai daka? Akan Sabreena da take ƙanwar ƙanwar bayana?" Samha ta je ta kama sadiqa a tsorace take don jikinta duk rawa yake, ita dai Sameera bata ce komai ba ta juya ta fice, zuciyarta rawa yake kuma a cunkushe yake tana ji Mommy na fashewa da kuka tana tambayar me ke faruwa ita ta kasa gane komai me ya hau kan ɗan ta? Ko ci kanku bata ce ba. Samha ce ta taimakawa sadiqa da ruwan zafi yayinda ta dawo parlor wurin Mommy ta zauna suka yi shiruuu ita mommy tana tunanin me ya kamata tayi? Me yake faruwa ita bata gane komai ba, Sabrina ta sauƙo tana waka ta wuce su zuwa kitchen ta tabbatar Talatuwa ta ɗora mata abinda tace kan ta dawo ta haura ko kallon su mommyn bata yi ba. "Ashe yarinyar nan macijin sari ka noke ce?" Mommyn ta faɗa cikin mamakin duniya da ya rufe ta. Ina hijaban? Ina ladabin? "Mommy me ta yiwa yaya saleem? Ki dubeshi a kwanakin nan kaman ba shi ba duk ya zama wani iri ga faɗa da masifa ga saurin duka mu da tun muna kanana ma bai dake mu ba sai yanzu?" Samha ce me maganan zuciyarta har lokacin yana bugawa "Nima na kasa ganewa Samha kaina ya kulle tamau, kwakwalwana ba ya tunani daidai... Amma bari iyayen nata su zo mu ji me kenan?" A parlorn suka cigaba da zama chan kuwa sai ga Gaje da Yaya sun shigo, yanayin shigar tasu ma ba yadda suka saba zuwa ba a raɓe a raɓe a baya suna tsoro kar su yi ma mommyn ba daidai ba, kai tsaye suka zauna cikin kujerun parlorn yaya yana cewa "Hajiya Hussaina ashe ana nan, barka da gida" "Sannunku da zuwa" Ta faɗa tana ta kallonsu kaman sabbin halitta yadda suka shige cikin kujera duk ba haka suke yi a baya ba, bata gama mamaki ba sai da Sabreena ta zo da gudu ta rungume Gaje tana musu oyoyo "Masha Allah, Amarya kin sha kyau da kamshi" "kai Gaje, Baba sannu da zuwa" Ta faɗa tana daga jikin Gaje dake ta riritata. "Barka dai 'yar arziki irin albarka, ya sabon wuri? Babu takura ko?" "Ah baba wa ya isa ya takura ni ni da gidan mijina" Suka yi dariya. "Yana zuwa ya gaishe ku, sa kaya yake yi" "Ah ba komai ai muna nan" Mommy tana zaune tayi tsamo tsamo kaman ruwa ya daki babban zakara har Saleem ya sauko ya zo ya tsuguna suka gaisa da su Gaje sai albarka suke sa mishi kan ya miƙe ya kalli Sabreena yace "Na fita" Da sauri ta miƙe ta bishi muryarta na fita a lokacin da take cewa ka zo min da... Sai dai bata ƙarasa da karfi ba, bayan ya fita ta dawo ta saka su Gaje gaba banza suka yi da su Mommy kaman Allah bai halicce su a wurin ba, wasu irin hawaye ne ke zubowa Sameera tana ambaton sunan Allah kan ta tashi ta shige ɗaki tana fashewa da kuka. Samha dai da mommy sun kasa magana, suna kallo har ta musu iso dining suka ci suka yi nak suka dawo parlorn, mommy ta kasa shiru tace "Yaya...!" Kallonta yayi "Menene yake faruwa ne? Na rasa gane kan Sabrina tunda aka yi auren nan, ɗazu fa har sa wa tayi Salim ya daki sadiqa abin da ba halinshi ba, ba haka na saka shi ya aureta su zauna ba ba zan zuba idanu mu cigaba da tafiya a haka ba, Salim ko kallon mutunci ya daina min daga aure? Me hakan ke nufi?" "Hajiya Hussaina ke fa kike ɗaukar abu da zafi, yaro yayi sabon aure ai ba za'a saka musu ido ba, tarbiya daidai gwargwado mun ba Sabrina kuma idan Sadiqa tana mata gani gani da a matsayin ta na yayarta yanzu yayansu take aure ya kamata su san maganan da za su dinga faɗa mata ina ga hakan sai a zauna lafiya" Mommy ta saki baki da hanci tana kallonsu. Sabrina tayi murmushi tace "Abin da mommy ta kasa ganewa kenan, mu ajiye batun nan ku tashi mu je ku kalli sashena" Basu bi ta kan 'mommy ba suka bi bayan Sabrina, numfashi ne taji bata iya ja da kyau Samha ta riƙe hannunta "Mommy...! Mommyyyy!!" Hankali tashe take kiranta kiran ya fito da Sadiqa da Sameera ruwa suka dauka suna shafa mata a fuska har ta Fara sauƙe numfashi da ƙarfi, me su Yaya suka yiwa yaronta? Sai yanzu tunanin za su iya cutar mata dashi ya zo mata innalillahi kawai take ta maimaitawa a tsananin tsorace. Su kam suna hawa Sabrina tace "kun yi min komai iyayena, ba ni da abinda zan saka muku kun ba ni wannan daula da dukiyar sai yadda naga dama zan juya shi, a yanzu ma ina ragarwa uwar ne saboda wani dalili nawa amma itama nan kusa za ta gane ta ɗauki goruba ne ta damkawa kuturuwa don kwace saleem a hannuna sai mutuwa" Dariya suka sheke dashi Gaje tace "Ke gidan nan fa duk na mijin ki ne kina da ikon yin yadda kike so, sai na ga kaman wannan sashe yayi muku kadan kenan ku suka raɓa ba ku kuka raɓa su ba" Hakane kuma gaskiya Gaje, kai Sabrina ta gyaɗa "Zan san abin da zan yi akai, amma ko za ku dawo nan ɗin ne?" "Ta ya kenan 'yar albarka?" Baba ya faɗa, ta saki murmushi "Kar ku damu na san yadda zan yi saleem yayi musu korar kare a gidan nan" Hira suka cigaba da yi wane sa'anninta ba iyayenta ba duk wani tuggu sun haɗa shi a ƙarshe baban ke cewa "Ai duk yadda za mu yi mu yagi rabon mu kan a je lahira za mu yi, ko a gaban Allah laifin mu kadan ne ita ta ga dama ta bamu hanya zuwa cikin gidanta shekara nawa ina faɗi tashi akan ya kula ki sai da na hakura na cire rai kwatsam ta dawo da zancen ashe muna da rabon dangwalar arziki mu ma, bari mu je mu fara tattare" Sallama suka mata suka bar gidan ransu kal... **** "Saleem..." Ya kira sunan yana zama gangar shi, buɗe rinannun idanunshi yayi ya zuba su kan Rayyan ɗin ba tare da ya ce komai ba, duk wannan ɗin ba halin Saleem bane na Rayyan ne hakan ya sa Rayyan ɗin ya ɗan damu. Yana zaune kawai ya ga Shigowar saleem ɗin office ɗin kuma bai ce mishi komai ba bayan sallama ya samu wuri ya kishingida. "Menene? Me yake damunka?" "Ni ma ban sani ba Rayyan, kawai ina jin ƙunci ne raina babu daaɗi zuciyata na mini zafi ba na iya bacci" "Saleem kana karatun Alqur'ani?" Ya girgiza kai don ya fi 2weeks rabon da yayi karatu in ba a sallah ba. "Alqur'ani wani dafa'i ne na yaye ƙuncin zuciya saleem, idan ka ga ba zaka iya bacci ba kayi ta nafilfili kana karatun za ka ji sauƙi, ka fi kowa sani na har a yanzu bana bacci kaman na mutane amma da na riƙe ibada ban zauce ba... Ka roƙi Allah ya yaye maka dukkanin damuwowinka" Kai ya gyaɗa, Rayyan bai kara cewa komai ba ya tashi yayi playing karatu a office ɗin ya je ya ɗauko ruwa ya kawo mishi ya ɗan sha tare da kwanciya a three seater abin mamaki tun karatun na shigar shi har bacci mai tsananin daaɗi da natsuwa ya ɗauke shi ba tare ma da ya san yayin ba. Saleem ya yi baccin Awa biyu cip kan ya farka har lokacin Rayyan na office ɗin yana wani aiki a system ganin ya farka ne ya mishi sannu, kai ya gyaɗa ya miƙe ya shige toilet da ke ta tashin kamshi wanke fuska yayi tare da alwala don ana ta kiran la'asar, bayan ya fito Rayyan ma ya rufe duk abin da yake yi don baya tunanin daga masallaci zai dawo office ɗin ya shiga bayin yayi alwala ya fito yana gyara hannun lafiyayyar farar shirt ɗin shi da ya ɗora akan navy blue wandon jeans, rigar suite ɗin ya dauka da briefcase ɗinshi suka fice yana kulle office ɗin. Sai da ya zube abubuwan a mota suka isa masallaci suka yi sallah. "Za ka iya driving ɗin ko in mayar da kai" "No zan iya" Ya faɗa a hankali. Da kallo ya bishi har ya shiga motar shi ya bar wurin, ƙasa natsuwa yayi da yanayin saleem ɗin duk sai ya tsaya mishi, da wannan 'yar damuwar ya nufi gida horn yake dannawa a kofar gidan da gudu aka wangale mishi gate ya cusa motar ciki, idanunshi ne suka faɗa kanta sanye take da wani stylish crepe Adire ta haɗa shi da matching colour purple na Jersey, daga inda yake yana hangar labbanta dake shekin man baki sossai tayi kyau amma shi ba kyaun yake gani ba. Dr. Sulaiman dake tsaye yana mata magana ya ɗan zubawa idanu kan ya ƙarasa parking ɗin ya sauƙa sai ya ɗauke kai kaman bai san akwai halittu wurin ba, tafiya yake kaman ba zai taka ƙasa ba har ya ɗan gota su Dr. Sulaiman ya taso "Assalamu Alaikum warahmatullah Dr. Rayyan" Sai da ya ɗan lumshe ido ya buɗe kan ya ɗan waigo ya kalleshi ba don ya san muhimmancin sallama ba babu abinda zai sa ya amsa, hannu ya miƙa mishi suka gaisa ya juya ya shige ciki fuskar nan kaman an mishi mutuwa. Sai da ya ɓace ta sauke numfashin da ta riƙe Dukda ko kallon inda take bai yi ba, kwarjinin shi ya matuƙar cika ta ta tabbatar haka Sulaiman ma don babu wanda baya shan jinin jikinshi a duk sadda Rayyan ya matuƙar tsumewa, ita dai ta san Rayyan ba ya rasa nasaba da sarauta. "Afeefah me kika ce?" Dr. Sulaiman ya faɗa "Zan tambayi Mammi in shaa Allah in ta amince tunda gobe half day juma'a sai ka zo mu je in na tashi school" "Toh shikenan, ga wannan" Ya miƙa mata leda kin karɓa tayi sai da ta ga ranshi ya ɓaci kan ta amsa don bata yadda ta iya. Kai tsaye wurin Mammi tayi don ta bata ledar ba ma ta bukatar buɗewa kan ta kai mata, da kuwa ta san abinda zata tarar da bata shiga ba faɗa sossai Rayyan ke yi na shi baya son tarukuce idan abinda zata yi kenan ta tattara ta bi samarin nata yaushe har ta tafasa da zata ƙone? Haka ta ga Abeeha na yi? Toh shi ba irin tarbiyar da yake ba ƙannenshi ba kenan in kuma tana gidan dole tayi abinda ta ga su Abeeha na yi. Jikinta rawa ya ɗauka, Mammi ta riƙo hannunshi "Duk faɗar nan na Sulaiman ya zo ba tare da ka sani bane? Kayi hakuri ni ce na mata izinin fita ba haka kawai tayi fitan gaba gadi ba kuma ko mintuna biyar bai kai ba idan nima na yi laifi sai in ji..." Shiru yayi bai ce komai ba. Tana tsaye a gefe kaman yajin kosai kafafunta kaman za su kayar da ita saboda yadda suke rawa don mugun kallon da ya aika mata, ledan hannunta ya kalla "Ba kin ga kalar rainin da bana so ba Mammi? Mun ce ba mu dashi ne da zai kunso koma menene a leda ya kawo mata? Ko ta tambayi abu ba'a yi mata ba?" "Saraki...! Bana so! ka ga bana so don Allah, ka duba yadda ka firgita ta? In kuma hankalina kake so ka ɗaga ka cigaba" Da ɗan faɗa tayi maganan, haushin kanshi ya ji ina ma ruwan shi da zai damu da tarbiyar ta? Shi ba wani tsiyar yake dubawa ba sai kar ta lalace da tara samari tun bata kai lokacin ba, Miƙewa yayi ya nufi fita daga ɗakin ranshi a haɗe fuskar nan murtuk, wani irin chill abu ne ke bin jikinta na tsoro, bata san me yasa shi baya wani damuwa da damuwarta ba a ranta take jin kaman bai yi na'am da zamanta a gidan nasu ba, ita idan ba don mammi ba wlh ko inuwa ba zata so haɗawa da shi ba bare har magana, gashi nan tana ta aikata laifin da zai ji haushinta. Kamshinshi ne ya daketa a sadda ya wuce ba tare da ya ko kalleta ba ta lumshe ido sai da ta tabbatar ya tafi ta sauke numfashi ta isa wurin Mammi tana jin hawaye na tsinke mata "Mammi ki yi haƙuri ban san ba'a haka anan ba, na fita ne ba don wani abu ba sai don Roƙon da Dr yayi ta min a kan ko ba zan ɗauke shi Masoyi ba in ɗauke shi wa da zan iya neman abu a wurinshi yayi min, ya ce min Mamanshi ta damu tana so in je ta ganni ta ji lafiya ta don kaman 'ya itama ta ɗauke ni wlh ba ni na roƙe shi ba Mammi kin ga da kyar na karɓa har saida ranshi ya ɓaci..." Dafa ta Mammi tayi "Natsu Afeefah! Ki natsu kar masifar Saraki ya dame ki, haka yake wlh kin ga su jidda basu isa su kula saurayi ba sai ya fara zuwa ya ganshi yayi bincike ya amince mishi kan ya zo idan yayi bincike bai mishi ba ko wayanshi suka sake ɗauka mai karbar su a gidan nan sai ya shirya, na sani a yanzu babu zancen aure tsakanin ki da Sulaiman shiyasa na bari kika fita, kuma ai ba'a mayar da hannun kyauta baya... Goben ki shirya sai ku tafi da Abeeha in ta dawo school ku gaishe da mahaifiyar tashi kinji?" Tsoro ne ya sake rufe ta jin yana duka, itama kenan zai iya bugun ta in tayi ba daidai ba "A'a Mammi ba sai na je ba, zan bashi uzuri..." "Kar ki wani damu zan mishi magana" Ledar ta ajiye don ji take ko abin ciki bata sha'awar gani, hankalinta ba'a kwance ba ta tashi tayi ɗakinta ko da ta shiga sai da ta sakawa kofar key don ji take kaman zai biyo ta ya cigaba da faɗa. 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh *FREE BOOK* *FATIMA A MUHAMMAD Sirikata kuma namecyna ina so in yi amfani da wannan dama in miƙa saƙon godiya da kuma jinjina bisa irin kokarin da kike yi a kan wannan littafi, haƙiƙa ba ni ma da kalmar da zan nuna miki jin daaɗi na da kuma yabawa mai tarin yawa wannan shafin naki ne kiyi yadda kika ga dama da shi... Jama'ar gidan haihuwa da hanji conversation room ina ganin tarin comments naku sai dai lokaci baya bani dama a kullum na shiga a sha fira da ni amma ina matukar jin daaɗi kuma ina yabawa ku sani muddin Aminiyar ango(Fatima A Muhammad) ta amsa wallahi kaman ni ce nan na amsa. Ina kuma yi muku albishir gobe public holiday za mu samu damar jero shafuka biyu in Allah ya yardar mana. Na gode sossai* *27* Washegari friday har ta je school ta dawo bata daina tuna irin faɗar shi na jiya ba, ita kam ba don mammi ta tabbatar mata da sai ta je ai shi zumunci yake so da ita ba tsiya ba, wanda yake sonka da arziki kuwa ya gama maka komai da babu inda zata je ai zama lafiya ya fi zama ɗan sarki. Ko da ta dawo da ɗakin Mammin ta fara ta duba jikinta suka ɗan yi hira kan ta wuce ɗakinta aka biyo ta da abinci, sai da ta ci kan ta shiga tayi wanka da alwala ta zo tayi sallah, a gaban mirror ta zauna tana kallon kanta a yanzu ko ita ta san ta yi kyau, ta ɗan yi ƙiba skin ɗinta na wani irin yalki don man da Abeeha take shafawa ita ma shi ta saya mata kuma skin tone ɗin su ɗaya, ta sake cika tayi kumatu kaɗan sai ya mata kyau, kwalli ta zana a idanunta bata cika sakawa ba amma ta san yana mata kyau kawai dai bata son sakawa ne don yana sa idanunta hawaye sai wani ruwa ya kwanta ciki kaman mai, dama gasu da girma masha Allah, lip gloss ta shafa ta miƙe ta tafi gaban wardrobe. Abaya ta ɗauko wani blue da adon fari egyptian ne ya amshe ta sossai ta saka farar hula don farin gyale yake da shi sai ta yafa gyalen ta yi kyau sossai sai ta ji nishadi a ranta, wa zai ganta ya ce Afeefar Dutsen-wai ce, Mayya kuma annoba? Wa zai ce tagayyara aka so tayi Allah ya dube ta ya tallafi rayuwarta? Malamin islamiyyarta na makaranta na cewa Allah zai buɗe ma bayinsa kokafofin rahama da sauƙi cikin ko wani tsanani muddin ka saka tsoronshi da tawakalli cikin ranka, sannan zai buɗe maka kofofin arziki ta inda baka yi zato ko tsammani ba ko a mafarki bata zaci ganinta cikin irin wannan gida tana rayuwa ba, tayi tunanin za ta tabbata a bauta da wahala a kasakance amma da Allah ya ce ba hakan bane ga inda ya kawo ta a yanzu. Da kyar ta bar gaban madubin wurin Mammi ta nufa. "Masha Allah Daughter ta tayi kyau tabarakallah!" Murmushi tayi tana zama gaban Mammin "Mammi zolaya ta fa kike ina kyau anan? Ko fa powder ban shafa ba" Mammi za ta yi magana kenan Abeeha ta shigo kaman ta jima da Dawowa don ba da kayan da ta fita ta shigo ba. "Afeefah Dr. Sulaiman ya kira yana harabar gidan nan" Mammi tace "Abeeha gobe dai tunda saturday ne ku je ki nema mata waya mai kyau" Murmushi Afeefah tayi tana Miƙewa "Sai kun dawo a gaishe su, sannan a kula. Abeeha kar ku jima kin san Yayanku" Da Toh duk suka amsa suka fice daga parlorn. Ta jima sossai tana tuna Afeefah a ranta kan ta sauke ajiyar zuciya tana Miƙewa da kyar cikin yanayin rashin ƙarfi da cikakken lafiya ta shiga cikin ɗaki. A harabar gidan kuwa suna fitowa Rayyan na parking, gaban Afeefah ne ya faɗi zuciyarta ya shiga doka wa da ƙarfin gaske, a natse ya buɗe murfin motar ya sanyo jikinshi waje Farar jallabiya ce da daga ganinta zaka san tana da tsada sai maiƙo take yi kirar Kasar dubai don tana da wani ado mai yanayi da rubutun larabci daga gefen kirjinshi kaɗan har karshen hannun hagunshi, hirami ne baƙi mai layi layi fari ya mishi wani ɗauri a kai yadda Larabawa suke yi ya zauna mishi sossai yayi kyau, kafafunshi sanye da halfcover Milano baƙa, hannunshi na daure da wata silver agogo yayinda zoben azurfan dake yatsar shi na kusa da ƙarshe ke ta daukar idanu. Kallon duk a seconds biyar ta yi mishi don fargaba da ta kan tsinci kanta a duk arean da yake, baƙar shade na maƙale a idanunshi ba za ta san ya ko kalli iskar da ya kwaso su ba yau ko Sulaiman dake zaune cikin mota bai kalli sashen da yake ba ya shige gidan kamshinshi na buso musu, Abeeha ce ta iya yi mishi "Sannu da dawowa" Hannu kawai ya ɗaga mata wai shine amsar ya shige abunshi. Motar Sulaiman suka isa Afeefah ta shiga gaba Abeeha ta zauna baya suka fice daga gidan suna sake gaisuwa. Har suka isa shi ne yake hira da Abeeha ita kam tana zaune shiru, shi ya musu iso har cikin gidan Baaba ta taso ta rungume Afeefah dake ta murmushi a ƙasa ta zube tana gaishe da mahaifiyar shi Umma ta miƙa mata hannu ta je kuwa ta kama sai ta zaunar da ita gefenta tana ɗan rungumeta kaɗan "Ina ta jin labarin ɗiyata sai yau Allah yayi zan ganta! Barka da zuwa barka da zuwa" Murmushi Afeefar ke ta yi hakika ta ji matukar daaɗin irin tarbar da ta samu, kayan kwadayi da su drinks aka cike musu gaba da su ita dai kunyar Ummar take ji yadda take ta jansu da hira shi Sulaiman ya fice Sashenshi da a cikin gidan yake. Sun jima sossai har aka yi la'asar suka je suka gabatar suna dawowa parlorn Su Fauza suka fito shirye don wucewa islamiyya suka yi sallama akan su ma za su zo musu suka fice, basu jima da fita ba sai ga Sulaiman da matarshi sun shigo, kyakyawa ce kuma fara tasss bata da wani girman jiki a shekaru kuma da kaɗan za ta iya fin Afeefar kila su yi sa'a da Abeeha, zama tayi tana ce musu sannu. Gaisawa suka yi kadaran hadaran, tunda ya ce mata da Afeefah yake ta zuba idon ganin Afeefar da bata santa ba amma ta yi matuƙar haddace sunan saboda yawan Ambaton da Sulaiman ke yi musamman in tayi wani abu, sai ta ga Afeefar ma ba wai kyau ta fita ko ado ba haɗiye abin da take ji tayi ta yi musu sallama ta fice. Baaba ce ta kawo zancen su kawu tana tambayar Afeefah me yasa suke kiranta annoba? Shiru ta ɗan yi kan ta shiga basu labarinta daga farko har ƙarshe, Baaba da Umma sun sha kuka umma ta sake rungumeta tana cewa "Sannu Afeefah... Sannu! Allah ubangiji ya ƙara miki karfin zuciya da imani ya wanke miki duk wannan wahalhalun" Ta amsa da Ameen tana murmushi don a wannan karo bata yi kukan ba illa iyaka Adu'a da tayi ta bin iyayenta da Aunty zee. Sulaiman dai bai iya ya ce komai ba a ranshi yake ayyana Dole ta sha piya-piya don kashe kanta, dole ta samu saukar jini don damuwar, ya so da ita ce a ɗakin shi a yanzu matsayin matarshi ya bata duk wata kulawar da ta dace amma gani yake lokaci ya riga ya ƙure, Dukda haka zai zauna matsayin yayanta zai bata duk wani gudumawar da ya dace a rayuwarta daga yanzu. Karfe hudu ya maida su sun bar gidan da tsaraba niki niki daga Umma ta kuma roki Afeefar da ta dinga zuwa mata, har cikin gida ya dawo

Chapter 16 of 40