Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
suka yi sashenta suna 'yar hira yayinda Zarah da Aisha suka nufi ɓangaren Ammi. Rayyan bai tashi shigowa gidan ba sai yamma sossai, a parlor ya zauna ta kawo mishi ruwa ya sha hankalinshi duk a na kanta a koyaushe dressing ɗinta na kashe shi don yanzu fitted atampha ne a jikinta tayi ɗaurin ture ka ga tsiya da ya zauna mata tana kokarin ɗage tray ɗin gabanshi tace "Abinci fa?" "No sai anjima am not Hungry" Kai ta gyaɗa ta nufi kitchen shiganta ba jimawa tana ba kuyangin ta umurnin aikin da za su dan yi mata su yanke yanke na shirya mishi abincin daren bayan ta gama ta nufi fitowa daidai Gaabɗo ya shigo da wani paper bag ya zube a ƙasa "Ranka ya daɗe wannan saƙo ne daga Gimbiya zarah tace a baka" Da wani irin hanzari ya ɗago ya kalli kofan kitchen ɗin, bai taɓa jin tsoron wani ya ga ko yaji abinda babu daaɗi ba irin yanzu da yaji duk duniya tashin hankalinshi shine taji wannan zance. "Fita dashi, kar ka kara karɓan abu da sunan sako zuwa gareni matukar ba matata bace ko mahaifina" "A gafarceni ran..." "Fita nace!!" Da ɗan karfi yayi maganan da sauri Gaabɗo ya fice. Ya tashi shima gabaɗaya a parlorn ya wuce ɗakinshi a lokacin ita kuma ta fito hawayenta na zuba, Jannah da Abeeha dake daga chan jikin ƙofan ɗakinsu suka yi dariya. "Allah ya sa ta ji, don hakan ne kawai zai kawo musu kusanci idan tana kishin nan tana fusgar hankalinshi ne kanta" Jannah ta faɗa Abeeha tace "Amma kam za ki sakata kuka a banza Adda Jannah... Allah ka yafe mana baiwar Allah Zarah" "Eh gwara tayi kukan ta nemi mafita wa zuciyarta, ita kuma zarah dama kar tayi tunanin samun matsuguni a ran Ya Rayyan don shi ba namijin da zai iya da soyayya bane muddin Afeefah ta mishi dabaibayi a zuciya" Hirarsu suka cigaba da yi cikin nishadi don sun tabbatar ko Afeefah bata nemi Rayyan ba shi a yanzu ba zai jure nisantarta ba. Ɗakinta ta koma ta zauna bakin gado babu abin da bata saƙa ba kuma ta hana kanta kuka, dole ta yi me ɗungurungun wai haihuwa da hanji! Dole taje ta ji shin yana sonta ko da gaske baya sonta wata zai aura... Kiran Sallar Magrib ya sa ta miƙe ta gabatar da sallah don ta yi wanka tun rana, kitchen ta nufa ta haɗa mishi macroni da gasashen chicken breast tana cikin yi aka kira isha taje ta gabatar kan ta dawo ta ƙarasa taje ta shirya mishi a dining a yanzu hijab ne jikinta har ƙasa, daidai yana shigowa take cewa Sa'ade "Ki tattare kitchen nan please ban yi shafa'i da wutiri ba bari na gabatar" Bata ma kula da Shigowar tashi ba don ciki ciki yayi sallama ta wuce ɗakinta ya bi bayanta da kallo hannayenshi zube cikin aljihu, a natse ya ƙarasa dining ɗin daidai Fitowar Abeeha da Jannah suka mishi sannu suma suka zauna suka shiga cin abincin, ganin ta jima ya sa ya dubi Abeeha "ƙira min Afeefah" Ta miƙe ta nufi ɗakin ta samu ta idar tana zaune ne kawai, jin yana kiranta ta miƙe ta nufi parlorn zuwa dining. "Zauna ki ci abinci" Ganin fuskarshi ba fara'a yasa ta zauna ta zuba abincin kaɗan tana ci kaman bata so, karamin kwalin da bai jiman nan ba Gaabɗo ya zo ya ajiye mishi ya tura mata. "Na gode" Ta faɗa tana jan paper bag ɗin ta buɗe ciki sai ta ga waya ne dall a cikin kwali Iphone 17 Air ce, bata nuna zumudi ko farin ciki sossai ba sai ma su Abeeha ne ke ta santin wayan ta sake ce mishi ta gode ya bi fuskarta da kallo. Bayan sun bar dining ɗin su sa'ade suka zo suka tattare wurin tsaff. Ɗakinta ta koma ta bar su Abeeha da wayan a parlor suna mata setting ta yi wanka, ta duba wani orange and Black nigty silk ne mai hannun shimi ya bi jikinta sossai don Black lace ɗin ya kara haske kayan, hijabi ta saka a kai ganin yadda ko motsi tayi komai na jikinta na motsawa cikin kayan musamman hammatan dake bayyana tudun na shanunta time ta kallah almost nine. Fitowa tayi Abeeha ta bata wayan don jannah ta gudu waya da mijinta a ɗaki, ɗakinshi ta nufa kai tsaye da sallama ta kutsa kai rike da wayan a hannunta don tana so su yi magana. A tsaye take bisa kanshi yana kishingide cikin tattausan Italian cushion a hankali yake ɗan taune lip ɗin shi kaifaffun idanunshi zube bisa kanta "am...am just fed up, ba na tunanin zan iya cigaba da zama a haka i've had enough na san ba ka aureni ba ne saboda kana so na, ka aure ni ne out of pity da kuma am... Mammi. Muddin na cigaba da zama a haka zan iya mutuwa a yanzu bana jin zan iya cigaba da kasancewa matsayin ma..matar k..." "It's pretty!" Ya furta chan ƙasa cikin deep voice ɗin shi da ya sa ta kame, duk maganar da take yi ba idanunta yake kallo ba lips ɗinta da take motsa su a hankali ya ƙurawa lumsassun idanunshi yana wani kashe su yana buɗewa... "W...whatt?" "Ur lips... They are pretty" Ko kan ta farga ya yunkura ya fusgo hannunta guda ta tafi gabaɗaya kanshi tayi masauki a kan kafafunshi fuskarta ya sauƙa kan wuyanshi a tare suka ɗauke numfashi. A ɗan razane ta shiga mutsu-mutsun sauƙa ya sa hannunshi na hagun ya zagaye kwankwansonta yayi pinning ɗinta jikinshi, na daman ya sanya ya zare mata hijabin idanunshi na sauka kan jikinta, ya bi damtsen hannunta da yatsa biyu cikin wani salo har cikin tafin hannunta kar yayi baya ya riƙe wrist ɗin hannun ya ɗora saman heart ɗin shi da ke beating very very fast. A take nata ma ke ƙoƙarin sauya bugu numfashi na neman kwace mata idanunshi a saman fuskarta kaman zai tsagata da su ya furta "saƙon zuciya baki ne yake furta wa sai dai kuma wani lokacin yana iya fin ƙarfin harshe ya bar wa idanu nunawa, Lil angel saurari bugun zuciyata ki kalli tsakiyar kwayar idanuna na tabbatar sun isa sanar miki da cewa Ryan na ƙaunarki ba zai iya rayuwa babu ke ba, kuma yana tsananin buƙatar ki, you are like a Light in my darkness. You are not just my wife Afeefah you are my safe space, my solace...you are the key to my salvation..." Wani irin birkicewa ta nemi yi saboda nauyin zantukan nashi ga idanunshi masu kaifi da yake zagaye fuskanta da su yana wani lumshe su, maganar ma har cikin ɓargonta take ji saboda yadda muryarshi ke fita very deep nd husky. "A haka kike cewa in rabu da ke? Uhmm? Ki fahimta rashin ki a gareni masifa ne Afeefah" Ƙuri tayi da idanu kalamanshi suna samu matsuguni daram a cikin zuciyarta, sakinta yayi ta koma zaune kawai akan kafar tashi, kanta ta mayar ƙasa tana neman dulmiyewa tsabar yadda kalaman suke zuwa mata a bazata Rayyan ne fa gabanta shine yake fitar da waennan tsadaddun kalmomin daga cikin bakinshi? Anya ta ji da kyau? Ko dai yaudararta yake shirin yi ganin irin kallon da yake mata ba tare da ya sake furta uffan ba, shi ne zai so mace kamarta? Sake ɗago kai tayi ta kalleshi suka hada idanu. Sarai ya san kokonto take akan kalamanshi kuma hakan bai mishi daaɗi ba, ya kai hannunshi ya kama haɓarta ya ɗago fuskarta yana kallon cikin idanunta cikin karantar yanayinta bai furta komai ba. Idanunta ta mayar kasa zuciyarta na bugawa da tsananin karfi har tana jin kaman cikin ko wani lokaci zuciyarta zai iya yin bindiga ta mutu, amma shi ko a jikinshi kuma fuskar a kame yake magana idanunshi na yawo bisa jikinta ya ce "Idan kuma kin matsa da sai na rabu da ke, zan iya yin hakan ne kawai under 2 conditions Afeefah sai ki zabi wanda kike gani ya fi miki sauki ni kuma i promise zan rabu da ke!" A razane ta dago ta zuba mishi idanunta da har sun fara zubar da kwallah lips dinta dake rawa ya bi da kallo kan ya dauke idanu yana lumshe wa ya bude Da ma na sani baya so na tunda gashi zai iya rabuwa da ni amma me yasa nake jin zafi? Meyasa nake jin kaman karshen rayuwata ne ya zo? Abinda take ayyanawa kenan a ranta.. Da kyar ta iya furta "Menene conditions din?" Tana ji gwara ta sani gwara ta hakura ta nemi daidai ita. "It's either ki mayar da lokaci baya ki goge ranar da na fara sanin ki a rayuwarta don daga ranar ne zuciyata ta fara bugawa da Ƙaunarki ko kuma ki tsaga zuciyata ki sauya min da wata zuciyar don wannan ta jima tana sakar da jini mai dauke da kaunarki zuwa ko wani sashe na jiki da jijiyoyina...." Baki kawai ta saki hawayenta na zuba sossai da sossai, ya kai hannu ya janyota suka samu kusanci ainun, ya ɗago babbar yatsarshi ya shafa soft lips ɗinta dake ta rawa idanunshi na cikin nata yayi leaning a hankali ya ɗora bakinshi kan nata zuciyoyinsu na amsa baƙon yanayin nasu da karfin gaske....... 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh ADABI WRITERS ASSOCIATION *FREE BOOK* *Babu lallai ku ji ni da daddare manage this please, and na ga ruwan comments da Adu'o'i na gode kwarai Allah duk ya faranta mana ya hada mu da masu kaunar mu saboda Allah* *51* A hankali ya raba bakin nashi da nata, ya zuba mata idanunshi da suka matukar sauya ko da ta buɗe idanu sai suka sarke cikin nashin, ya riƙe natan sama da mintuna da suka fi biyu kan ya saukar da kanshi wuyanta yana goga mata gemunshi zuwa karan hancinshi a gefen kunnenta cikin wani irin salo da bata san ta mayar da hannayenta biyu bayanshi ta yi grabbing wuyanshi ba tana sauƙe numfashi. A hankali yake haurawa numfashinshi na sauka da zafi yana ƙarasa hautsina mata natsuwarta har ya isa cikin kunnenta cike da wani shauƙi mai dauke da mayen son da ba za ta iya resisting ba ya shiga whispering into her ears "Afeefahhh ke ce ta farko a zuciyata, ke kika buɗe shafin farko a soyayyata, a kanki jikina da zuciyata suka fara gamsuwa da cewa ni din namiji ne cikakke kuma ina buƙatar Abokiyar halitatta, ki amince min mu zama daya, ki yarda na baki ragamar rayuwata! dama ɗaya tak nake so ki ba ni...ni kuma zan killaceki a cikin zuciyata tsawon rayuwata, zan zama bawa a gareki mai hidimarki tsawon rayuwarmu zan tabbatar wa da duniya ke ce farin ciki na kuma hasken zuciyata..ina fata ba za ki hanani raɓa daga ni'imarki ba?" Hawaye ne ke zuba mata na rashin Makama, yanayin ya mata zafi kalaman sun mata tsauri ainun ta yadda take jin kaman tana duniyar halwa ne na soyayya ba duniyar mutane ba, bata san ta gyaɗa mishi kai ba yayi murmushi mai nauyi wanda sautinshi ya fita kaman numfashi, bata ankara ba taji ya tashi da ita a hannunshi ya isa ya mayar da hasken ɗakin dimmm sossai kan ya nufi gadon ya shimfiɗeta za ta yunkura ya bi bayanta his hands started to move inch by inch na jikinta, yana squezing ɗinta gently bakinshi is slowly kissing her and driving her nuts especially wuyanta da ya fi ko ina motsa shi, da baki yayi amfani ya saukar da sleeve na riganta cikin salon da bata taɓa sanin akwai shi ba, heavy breathes ɗin shi na sake birkitata. cikin natsuwa yake komai, Sai da ya tabbatar tayi laushi shima ya fara rasa kanshi a duniyarta kan ya nufi yin mai gabaɗaya, a sannan ne ya birkice ya gigice tunaninshi ya ɓace, jinshi yayi nisa bashi da buri a lokacin illa na ganin sun zama daya ta zama shi shima kuma ya zama ita, ko da ya ji shi a duniyarta ƙarasa haukace wa yayi a sannan ne ita kuma ido ya raina fata ta fahimci that pleasure da irin tarin iya sarrafa mace da yake dashi ne ya ruɗe ta har ta zaci abin mai sauki ne, duk irin magiya da roƙon da take mishi haɗe da kuka duk baya ji, idan hannunta ya sauka jikinshi ma sai yaji kaman zaburarwa ne cikin salonta. Bai sarara mata ba bai kuma saurara ba don yayi haukacewar da ko sunanshi ka tambaya a lokacin ba zai iya tunawa ba ita kaɗai ya sani, ita kaɗai kuma yake gani...Tsammmmm haka ya rukunkumeta yana binne kanshi a wuyanta a sadda ya samu cikakken natsuwa, Dukda irin halin da take ciki na fitar hayyaci da raɗaɗin azabar da bata taɓa fuskantar irinshi ba a rayuwarta tana iya jin ɗumin hawayenshi dake bin wuyanta, chan kaman daga wani uwa duniya take jin shaƙaƙiyar muryarshi na furta "Allah ya gafarta miki Mammi, Allah ya yafe miki kurakuranki Allah ubangiji ya sadaki da rahamarsa Allah ya jiyar da ke daaɗin aljannah fiye da yadda kika yi sanadiyar jin wannan daaɗi nawa na duniya....Thank you! Thank you Mammi" Sossai yake hawaye har numfashinshi na seizing ya mata riƙon da kaman ya tsaga jikinshi ya chusata yake ji ko zai samu saukin abinda ke shirin zauta shi, bai iya ya motsa ba kaman yadda itama bata da kuzarin ɗaga ko da yatsar ta ne, yana so ya ɗaga ta ya ji lafiyarta yana so ya gwada buɗe baki ko zai iya furta mata tarin irin kaunar da yake mata sai dai ya kasa, ya kasa sarrafa kanshi bare ya sarrafa jikinshi abu daya ya sani ta gigitashi a duniyarta ta goge mishi haddar da baya tunanin har abada akwai wacce ta isa ta kaishi inda ta kaishi, ta kashe mishi duk wani laka na jiki kaman ba tsayayye kuma jarumin sojan nan ba, ƙasusuwanshi sun yi laushin da ya kasa ko da lankwasa su bare ya sarrafa su har su miƙe a dole ya sake binne ta ya ja bargo ya rufa musu a haka wani irin bacci ya ɗauke shi ba tare da ya san halin da take ciki ba. Sautin kuka da turirin zafin dake fita daga jikinta zuwa nashi ne yayi sanadiyar farkawarshi, gaining courage yayi ya yunkura da ita a jikin nashi har lokacin banda bargon nan babu komai jikinsu duk su biyu, juyata yayi ta koma kwance yayi pecking goshinta a hankali ya fara ambaton sunanta "Afeefah... Bebe!" Bata amsa ba sai kananun kukan da take na zazzafar zazzabi idanunta a rufe kirib "Am so sorry...am sorry" Ya faɗa yana sake pecking goshinta kan ya sauka ya nemi wandonshi na bacci ya saka ya nufi toilet shi karan kanshi kafafunshi rawa suke kanshi ya mishi nauyi ainun, gefen cikinshi ya riƙe mishi sossai amma sanin dalili tunda shi likita ne bai wani damu ba ya haɗa mata ruwa mai zafi, ya dawo gadon ya ɗauketa kaman 'yar baby. "Matar Saraki..! Afeefah... Kina ji na? Zan saka ki a ruwa compose yourself kar ki ji zafin a bazata! Am so sorry Ya Saraki bai kyauta ba, Yafam boɗɗi am"(ki gafarceni kyakyawata) Da wani irin sloww tune yake maganan a kunnenta kan ya saukar da ita a hankali cikin ruwan, wani irin ƙara ta saki tana rirrikeshi za ta tashi ya shiga ciki ya danneta kawai ta kife kanta kirjinshi tana girgiza wa cikin azaba da kuka mai ratsa zuciya, hautsinannen gashinta da ya gama wargaza wa yake shafawa zuwa bayanta yana hura mata iska a kunnen yana whispering "sorry, am so Sorry My love." Sai da suka yi ruwa uku a tare tana liƙe bisa kirjinshi idanunta a rufe rufff kan ya sakata tayi niyya suka yi wankan tsarki, a towel fari ƙal yayi wrapping ɗinta ya sake ɗaukar ta zuwa kan cushion ya ajiye ta, har lokacin bata buɗe ido ba kuma bata bar kananun kuka ba shi kuma bai bar lallashi da ban haƙuri ba, gadon yaje ya chanza musu bedsheets. A gabanta ya tsuguna bayan ya ɗauko magani, bata ma san ya zo ba don har bacci ya fara fusgarta na wahala kawai taji hannunshi cikin towel ɗin ya shafa cikinta ta ɗan zabura sbd har lokacin hannunshi da sanyi ta buɗe ido sai suka haɗa ido tayi saurin rufewa yayi murmushi "Tashi ki sha magani 'yar albarka..!" Bata motsa ba shi ya ɗago ta zata fara kananun kuka ya sanyata jikinshi ya shiga bata tea din da ya saisaita zafin ta sha sossai kan ta sha maganin, a maimakon tayi shiru ma sai ta sake fara wani kukan. "Am sorry My love, har yanzu baki ji sassauci ba?" Ta gyaɗa kai tana hawaye don ita kaɗai ta san me take ji, shima kuma ya san jarumar mace yake tare da ita tayi matukar ƙoƙari, a hannu ya dauƙeta bai damu da su sa wani kaya ba suka koma kan gadon ya shimfiɗeta bisa kirjinshi "Sannu Chéri am(My darling) in duba in gani ko kina buƙatar stiches?" Ta maƙe kafada za ta fara kuka yayi murmushi mai sauti kan ya shiga shafa wet gashinta da yayi mishi laushin taɓawa saboda bai bushe ba, a kunnenta yayi whispering "Afeefahh kin san Bugawar zuciya alama ce ta mutum na raye ko? Toh kece bugun Zuciyata wanda hakan ke nufin idan babu ke a zuciyata babu ni zan iya amsa kowace irin tambaya a game dake saidai tambaya daya da ba zan iya amsawa ba ita ce wane irin so na ke miki, wannan tambaya ba zan iya amsata ba domin ni kaina ban san wane irin so nake miki ba abin da kaɗai na sani game da yadda nake jinki cikin jinina shine ba zan iya cigaba da rayuwa ba idan har ba'a tare dake ba. Afeefahhh idan har rayuwa ba za ta yiwu babu iska ba haka nima ba zan iya zama mai rai ba tare da ke ba, ke ce rayuwata Gimbiyata" Duk giyar soyayyarta ya saka yana jin kome ya faɗa mata yayi kadan wurin bayyana abin da yake ji, kuka take ba na bakin ciki ko ciwo ba kukan farin ciki take, tana kukan alfahari tana kukan isar ta macen da aka iya macewa a cikin begenta, tana kukan mallakar wannan gwarzo namijin da bakinshi bai yi nauyi ba wurin shimfide mata sirrukan zuciyarshi, rungumeta ya sake yi tsamm yana shafata cikin bege "Allah ubangiji ya kula min da dukkan lamuranki na rayuwa, yadda kika shayar da ni garɗi da zaƙin zumanki ubangiji ya shayar da ke ruwan alkausara... Thank you so much Habeebty a yanzu you are not just the part of my life you are the owner of my heart, ki yi bacci Habeebty kiyi bacci cikin salama" Da wannan kalamai haɗe da tarin lallashinshi mai tsadar gaske bacci ya ɗauketa. Ya jima sossai kawai yana kwance in ta motsa sai ya sake shigar da ita jikinshi kaman za'a raba su ne ya yi pecking tsakiyar kanta, sun so su makara don ƙarshen ta a gida ya ja su sallah bayan ya kaita tayi alwala, wani baƙin Oman jallabiyarshi mai adon gold ya saka mata sossai ya mata tsawo ya ɗauko mata hijab ɗinta ya saka mata shima ya saka jallabiya ya ja su sallah, suna idarwa ya janyota ta kwanta a kan kafafunshi ya zare hijabin yana shafa gashinta yake musu azkar duk su biyun don da kyar tayi Sallar saboda bacci da zazzabin da bai gama sake ta ba, tuni ta yi baccinta peacefully har ya gama ya dauƙeta ya mayar da ita gadon yana kallon pale fuskarta. Idanu ya lumshe yana sauke numfashi, a duk sadda zai ganta wani sabon ƙauna da mararinta yake ji yana kwarara cikin zuciyarshi, hannunta ya riƙo yayi pecking ya sake yi mata peck a Goshi kan ya miƙe ya fito, hadiman da suke share share da goge goge suka zube ƙasa suna kwasar gaisuwa, ya ɗan shafa kanshi ya ce "Ammm yau gabaɗaya na baku hutu, ina so ku koma sashenku kuyi duk abinda kuke so sai dare ku dawo" "Godiya muke Yariman Matasa! Godiya muke Ciroman fombina Allah ya kara girma da arziki Allah ya biya buƙatu" Kai kawai ya gyaɗa suka miƙe suka fice shi kuma ya nufi kitchen. Abeeha da zata fito kenan ta ji yana koran hadimai ta koma ta buga jannah da ke shirin komawa bacci "Wallahi barin sashen nan ya kama mu Addah jannah... Me afkuwa ta afku ga Ya Rayyan chan kitchen zai dorawa gimbiyarshi breakfast " Da sauri jannah ta miƙe zaune cike da zumuɗi tace "Keeee Ya Rayyan ɗin?" "Shi fa wallahi, hmmm ai na san jiyan nan ba lallai a wanye ƙalau ba, bawan Allah Saraki a waje Hadimin Afeefah a gida" Suka kwashe da dariya jannah na cewa "Kin ga irin su Yayan nan hmmm ki bar su kawai... Maza shirya bari nima na shirya mu koma sashen Ammi for today mu bar su su ƙone in sun ga dama" Abeeha na dariya ta shiga toilet wanka ji take zuciyarta kal kal, basu fi mintuna talatin ba suka bar sashen abin su. Shi kam bai ma sani ba yana kitchen, plantain yake frying amma minti minti zai saki murmushi yana tuna moments ɗinsu na jiya, ji yake ma yana kewanta a jikinshi daga Fitowar shi ɗakin zuwa yanzu, sai da ya gama ya haɗa mata spicy egg sauce mai ɗan yawa, ya yi toasting bread with butter very soft and simple kan ya shirya plate ɗin with so much love don burin shi kawai ya ga tana murmushi burin shi ya ga ta ji daaɗi kuma tayi alfahari, clean tray mai kyau garai-garai ya samu ya ajiye plate ɗin ya hada da tissue ko za ta bukata wrapped with cutlaries. Dube dube ya fara har ya samu wani drawer mai dauke da notepads masu yawa da Pen sbd specifying objects, rubutu yayi a jiki ya manna a gefen tray ɗin ya hada tea mai kauri sossai ya ajiye kan ya ɗauka ya nufi ɗakin. A gefen bedside ya ajiye ya yaye mata duvet ɗin har lokacin riganshi ne jikinta, ganin tana baccinta peacefully ya shafa fuskarta motsi ta fara a hankali har dai ta buɗe idanunta da suke kumbure ta sauke bisa kanshi ya sakar mata kyakyawar murmushi "Good Morning My Queen, My greatest blessing and the reason i believe in love..." Duk yadda bata so murmusawa ba sai da yayi escaping ta tsinci zuciyarta da dumbin farin ciki wane takarda. Miƙewa tayi zaune tana sauƙe kanta ƙasa haɗe da fara wasa da hannunta tace "Good Morning" Bai matsa mata ba ya san kunya ke ɗawainiya da ita shi ko a jikinshi ya ɗauko tray ɗin ya ajiye mata a kan cinya zai yi magana wayanshi ya shiga ƙira ganin mai martaba ne da kanshi ya sa yayi picking yana fita daga ɗakin don dole zuwa parlor. Note ɗin da yayi rubutun ta ɗauka ta shiga karantawa. "Na shirya miki wannan karin kumallon ne da tarin soyayya, kina da muhimmanci sossai a rayuwar Ryan. Allah ya albarkaceki da farin ciki da lafiya kullum, Ina ƙaunar ki!" Zuciyarta ta sa hannu ta dafe, kaunar ya mata yawa ji take ta ma rasa me zata yi sai sake karantawa take tana murmushi. Adanawa tayi ta dauki fork ta fara cin abincin da ya shirya mata da hannayenshi, loma biyu tayi sai gashi ya dawo yana zama gefen ta "Afuwan mai martaba ne ya kira ni ko yau zan samu fita ran gadi da shi" Kai ta gyaɗa tana sakar mishi cokalin bata ce komai ba don ya riga ya sanya hannu cikin nata ya karɓa ya cigaba da bata cike da kulawa yace "Kin san me na ce mishi?" Kai ta girgiza "Ce mishi nayi yau yini na, magana na da duk wata kulawa tawa naki ne ke kaɗai saboda kin bani abu mafi daraja a rayuwarki..." Da sauri ta kalleshi tana zaro idanunta waje gabaɗaya ya saki murmushi mai kyau har hakwaranshi na bayyana tace kaman za ta saki kuka "Da gaske haka ka faɗa mishi?" Hancinta ya lakace "Gashi na saka ki kallona da waennan idanun da suke kashe ni, kuma na ji wannan murya taki mai kaman sarewa..." Bata san tayi murmushi ba shima ya cigaba da yi har ya gama bata. "Mu je in miki wanka..!" Ta zaro ido "Zan iya wlh" Tayi saurin faɗa a Shagwaɓe ya kalleta "Ya daina zafi? Kin tabbatar za ki iya tafiya?" Kai ta gyaɗa ya dage tray ɗin ta sauƙo

Chapter 32 of 40