kirguwa sai dai in baki zo wurinshi da kuka ba sai ya share miki hawaye, wannan dalili ya sa nima na taso da irin zuciyarshi Dukda rashin lafiyarmu don shi ma ciwon sugar ne ya kashe shi kaman yadda ya kashe baban shi, ƙannunshi ma Uncle Musa haka yake don suna da nasaba mai kyau suna da ilimi boko da arabi.
Akan irin rayuwar da na tashi kenan har na kamallah jami'a ta ina da shekaru ashirin da ɗaya a duniya, wata rana ina driving na zo daidai wurin ba da hannu sai na hangi wani kyakyawan yaro da ba zai wuci shekaru shida ba yana da irin kyaun da in ka kalleshi sai ka sake da sauri ya zo ya shiga gaban motana ya fara wanke mini glass don kaman sana'ar da yake yi kenan a wurin ake bashi goma biyar na cin abinci, Dukda fuskarshi a matuƙar haɗe ko alamun dariya babu kayan jikinshi kuma basu ji jiki chan chan ba amma sun dan yi duhu kaman ana yawan tsoma su ruwa, bayan ya gama ya dawo gefena ya tsaya tsantsar tausayinshi ne ya rufar mini, wannan yaro ƙarami da ke bukatar ingantacciyar rayuwa yaron da bai wuce a ce yana gaban mamanshi a kwance ba shine ke wannan walagigi yana neman abin da zai sanyawa cikinshi, sauƙe glass din nayi muka haɗa ido na sakar mishi murmushi
"Yaya sunanka?"
Na jefa mishi tambayar ga mamaki na ko ci kanki bai ce ba banda idanu da ya tsura min yana kallo, ganin an ba da hannu sai na zari dubu biyu na miƙa mishi kaman ba zai karɓa ba sai ya karɓa ya juya ya bar wurin bai ce min komai ba.
Har na dawo gida tunanin wannan yaro ne a raina bayan kwana biyu na kasa mantawa da shi haka na ɗauki mota na koma inda na fara haɗuwa da shi na ajiye mota na shiga yawon neman shi da ƙafa, na yi nema sossai kan na same shi zaune gefen wani juji ya haɗa kai da gwiwa Dukda uban ranar da ke dukanshi ko motsi bai yi ba, daga farin Fatan shi da yanayin sumanshi na gane shi don ya fi yanayi da Fulanin usuli, gangar shi na je na duƙa na taɓa shi ya ɗago ya kalleni da idanunshi da suke a matuƙar rine fuskarshi yayi jazir, dabiun yaron sai bai min yanayi da na sauran yara ba don idanunshi na nuna wasu al'amari da na kasa fahimta, maganan duniya na mishi bai ba ni amsa ba sai ido na miƙe na je wurin wani mai wankin mota a kusa da wurin na nuna mishi yaron
"Malam Don Allah wanchan yaron baya magana ne?"
"Hajiya yadda kika ganshin nan haka mu ma muka ganshi kuma in za ka mishi maganar duniya ba zai amsa ba amma kin ganshin nan idan ya kwana da kayan jikinshin nan da safe zai zo ya ba ni goma in bashi ruwa da bokiti ya kwaba omo ya wanke zai zauna daga shi sai karamin wando idan ya bushe zai saka ya cire wandon ma ya wanke ya mayar da kayan, kin ga inda yake zaunen nan idan ba zai fita neman kudin abinda zai ci bane bai taɓa barin wurin ba sai wanka ko wanki da ya kan zo nan"
Wani iri na ji har cikin raina, na mishi godiya na bar wurin na koma wurin mota na tafi na je na sayo duk wani abin makulashe da na san yaro zai buƙata na dawo na bashi ya ƙi karɓa a ƙarshe ajiye mishi nayi na tafi, Washegari na sake komawa don tausayi da kaunar shi ya riga ya samu gurbi a zuciyata, a ranar takalmina na cire na yi irin zaman da yayi nima Dukda ina jin zafin ranar minti minti sai ya ɗan waigo ya kalleni ban ce komai ba shima kuma bai ce komai ba, har dare ina tare dashi sallah kawai nake zuwa wani masallaci a wurin dake da ɓangaren mata abin da ya bani mamaki kuma shima haka zai je Sallar ya dawo ban tafi ba ranar ma sai da na sake cika mishi gaba da abubuwan cima kala kala, a takaice na jera kwana uku ina zuwa wurinshi a na huɗu ne ina zaune kawai sai na kama kuka, yayi shiru sai ya juyo ya kalleni kaman zai share chan dai na tsinci muryarshi kaman daga sama yana cewa
"Me ya same ki?"
Numfashi mai nauyi na sauƙe ashe ba kurma bane
"Ba ni da lafiya ne kuma bana son zaman rana"
Ga mamakina sai ya miƙe ya kama hannuna muka koma inuwa duk muka zauna bayan nan duk yadda zan yi yayi magana ya ƙi na sake yin kwana biyu muna zama a inuwa kan ranar kawai ya kalleni ya ce
"Me kike so?"
Ina mamakin yadda yake magana wane babba
"Kai nake so in taimaka kai nake so in ɗauke daga wannan jujin in kaika gidan mu kayi rayuwa mai kyau, za ka bi ni?"
Kallona kawai yake, ni kuwa ina hakan ne da zuciya ɗaya ba zan so rayuwar shi ya ƙare a kan titi ba ba zan so ya tashi a haka ba zai iya shiga ko wani hali.
Kai ya gyaɗa min na yi farin ciki kwarai na kira babana ina mishi albishir don ya san labarin yaron har ya yarda duk ranar da yaron ya tanka ni kuma ya amince ya biyo ni ina da kyautar kujerar umura na yi farin ciki sossai da amincewarshi Dukda ba don kujerar ba saboda ko a lokacin na je Makka so ba adadi, na dauke shi daga nan muka dawo gidan mu.
Ban barshi cikin ma'aikata ba na kaishi ɗaki na musamman na fita na yi mishi sayayya kan na dawo yayi wanka ya ci abinci na bashi kayan a hankali ya ce min
"Na gode"
Murmushi nayi a raina ina raya wannan yaro idan ya girma ba karamin mutum za'a yi ba don bashi da rawar kai irin na yara masu shekarun shi.
"Ya sunanka?"
"Ban sani ba"
Abin da yace kenan na yi mamaki ƙwarai kuma kaman akwai abinda ya ɓoye min amma ban bincika ba nace
"Zan saka maka suna amma sai na yi tunani sunana Khadija, mahaifiyata ta rasu ni kaɗai ce sai babana a gidan nan ka ɗaukeni tamkar mahaifiyar ka duk wani abin da kake so ni kuma zan cika maka shi ka ji?"
Ya kalleni nayi murmushi
"ban kai in haifeka bane? Shekarunka nawa?"
Ya ɗaga min yatsu shida nace
"To ka ga, da na yi aure ina 15 da na haifeka irin auren kauyen nan da ma ba'a kai hakan"
Ya ɗan yi murmushi daga nan na fahimci shi mai ɗabi'ar miskilanci ne tsantsa babana na samu da shawara shi ya ba da sunan Rayyan in saka mishi ni kuma nake ce mai Saraki don ko sarki bana tunanin ya kai shi sarauta..
A lokacin gab aurena da baban su Jannah ne ko da ya zo shima farar daya son yaron ya shiga ranshi yayi alkawari zamu rike shi kaman mu muka haife shi ko da zan kaishi makaranta tare muka tafi da Mahaifin su Jannah shi yayi mishi komai aka ba da sunanshi Rayyan Mohd Khamis, bayan aurena da baban su Jannah bai fi da shekara ba Allah yayiwa mahaifina rasuwa ta hanyar ciwon sugar da ya sha fama da shi, na shiga tashin hankalin da Saraki ne kawai ke iya saka ni cin abinci kan daga baya na zo na watsakke don dama wannan dole ne, ranar da na haifi Jannah a ranar Saraki ya fara kirana da Mammi don tunda muke bai taɓa kirana ba ko zai yi magana sai dai kawai yayi na ce ko Aunty ya ce min ya ƙi, Rayyan bashi da lafiya don yadda yake ganin rana haka yake ganin dare idan yayi bacci kuwa haka zai yi ta wani irin juye juye yana haɗa gumi daga karshe cikin wani mummunan yanayi zai farka tun yana ƙarami muka fara ganin likitocin psychiatric su ma da kyar da pills ake samu yake dawowa daidai idan abin ya zo mishi especially lokacin zafi kasancewar a tsakankanin ne muka hadu.
Baya so a mishi magana akan abin da ya kawo shi wurin ko iyayenshi tunda na fahimta ban sake yi mishi ba ko da wasa, irin kiyayewa da kular da muke bashi shine sanadin da ya sa ya samu ingantacciyar rayuwa yayi karatu mai zurfi har ya zama soja, bayan nan ne aka gano ina da Ciwon ƙoda Rayyan yayi fadi tashi kwarai har ƙodar shi yayi offering mini Mahaifinsu Jannah ya hana aka biya makudan kudi aka yi min dashe amma ba'a dace ba, a lokacin da nake jinyar Baban su Jannah ma ya rasu ga rashin lafiya ga rashin miji na yi ciwo sossai duk Rayyan ne yake tsaye tsayin daka a kaina ga ƙannenshi Jannah da Abeeha bai bari na tagayyara ba, yana mini son da iyakaci kenan ko da ni ce na haife shi.
Saraki ya taso mai tsananin jarumta gashi dama magana ma bata dame shi ba don ko abokai bashi da su, sannan yaro ne da idan yana abu dole ka kalleshi yana da jin ƙai ko magana yake dole ka kalleshi, dalili na ya tafi short service a harkar lafiya don dama science ya karanta a secondary school, ba'a fi shekara biyu ba na matsa mishi da zancen aure ya nuna akwai wacce yake gani zai iya aure, magana ta fara nisa ranar ya je wurinta babanta ya zo ya same shi ya ce mishi
"Ina so in ka koma ka tambayi asalinka sai a fara batun neman aure amma ba zan ba da auren ɗiyata wa marar cikakken asali ba"
Wannan magana ya dake shi sossai, wanda ni na ɗan lallaɓa shi na tura uncle Musa sai ce mishi suka yi ba za su bada auren ba basu sani ba ko ba ɗan sunna bane ko an same shi ta gurbattacciyar hanya, magana ce mai girma a gareshi wanda ya tado ciwon baya da kyar muka samu ya dawo daidai bayan tsawon wata shidda baya bacci kuma ya ki faɗa mini wani irin mafarki yake ko wa Dr ɗinshi, gashi Rayyan baya taɓa zubar da hawaye, tunda ya girma rabon da in ga hawayenshi kila da wani abu zai ragu a zuciyarshi, daga nan yayi alkawarin ba zai sake neman aure ba don duk wanda ya sake kallonshi ya mishi gorin asali sai ya kashe mutum har lahira.
Afeefah kin ji waye Rayyan, kin ji cewa bashi da cikakkiyar asali sai dai yana da tarin nagarta, ilimi, natsuwa da sanin ya kamata ga ibada tsantsa, yana da ni matsayin uwa da na bashi duk tarbiyar da uwa za ta iya ba yaro daga yarantarshi har girmanshi, ya samu gatan iyaye both uwa da uba don baban su Jannah har ya rasu bai taɓa nuna ko da da second daya cewa ba shine Uban Rayyan ba, kin ji cewa bashi da cikakkiyar lafiyar kwakwalwa ba na hauka ba sai na tsantsar damuwa akan abinda ya shafi rayuwarshi da ciwo a zuciyarshi wanda ya mayar dashi mai irin zafi da faɗan nan, tun yana yaro ba za ki taɓa ganin dariyar shi ba sai murmushi shima sai ya kama, shin za ki iya auren Rayyan a haka? Afeefah za ki iya yi min wannan alfarmar??
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*30*
**Tana tunanin da kashe kai shi ne hukunci mafi sauƙi ga bawa a duk sadda ƙaddara ta ruro wutarta za ta samu miliyoyin mutane a raye ne?"**
Da wani irin amo sautin muryarshi ke dawo mata a sadda yake faɗa farkawarta daga shan piya-piya, ashe da biyu yake yi mata irin wannan faɗan? Ashe shima duniyar ba daaɗi tayi mishi ba?
Wasu irin ruwan hawaye ne ke bin fuskarta babu kakkautawa, sai taji har gwara ita ma da shi kaman ƙaddarar ta ya fi nashi sauƙi tunda tana kwanciya tayi bacci lafiya ƙalau, kuka kawai take yi duk yadda mammi ta so tayi shiru ta ƙi, sai da tayi ma'ishi Mammi ta bata ruwa ta sha kan ta ɗago ta kalli Mammi bata ce komai ba.
"Za ki iya cewa Meyasa ban bashi Abeeha ko Jannah ba ko? Har raina na ɗauki Saraki ɗan da na tsuguna na haifa ne shiyasa har abada na haramta mishi auren 'ya'yana, uba yake a gare su a yanzu da basu da wani uba shi ya raine su bayan yana jinya na, shi ya basu tarbiya cikakkiya da har in sun fita ana sha'awar su. Wannan dalili ya sa ko da wasa wannan tunani bai taɓa darsar min ba don har in mutu bana fata ko sau ɗaya Saraki yayi tunanin don ba ni na haife shi ba zan iya ɓata mishi..."
A hankali Afeefah da idanunta suka sauya ainun ta riƙe hannun Mammi
"Ke mutumiyar kirki ce Mammi, kina daga cikin sahun 'yan aljanna in shaa Allah... Hakika kina da zuciya mai kyau wanda Allah ne yayi miki kyautar shi don samun irinki sai an tona"
Murmushi kaɗan kawai Mammi tayi zata yi magana Afeefah tayi saurin cewa
"Mammi ki bar roƙo na kin yarda da ni ni kuma in shaa Allahu ba zan ba ki kunya ba, wlh har raina na amince kuma zan yi iya kokarina in ga na ba da abinda ake so"
Rungumeta kawai Mammi tayi cikin farin cikin da yake ratsa zuciyarta.
****
Shi kam Rayyan daga masallaci ya mayar da Saleem gida bayan yayi ta mishi tuni akan mahaifiyarshi da 'yan uwanshi irin muhimmancin su a rayuwarshi duk yana ji amma amsawar wani iri, bai damu sossai ba don shima zai taya abokin nashi da Adu'a yana kuma da yakinin duk abinda yayi farko yana da ƙarshe musamman abinda ba don Allah aka yi shi ba.
Daga nan gidan Jannah ya wuce, tana zaune kawai ta ji ana knocking ta tashi taje ta buɗe sai ta ganshi tsaye, murmushi ta saki tana mishi sannu da zuwa ya amsa yadda ya saba musu ya shiga ya samu wuri ya zauna, cikin mintuna kaɗan ta cika gabanshi da kalolin abubuwa su snacks da su abinci kan ta dawo ta zauna
"Barka da juma'a Yaya"
"Barka dai ya gidan?"
Ta amsa da farin ciki
"Lafiya ƙalau ya su Mammi?"
"Alhamdulillah"
Ya faɗa yana shan zobo don yana matuƙar kaunar zobo bayan ya sauƙe cup ɗin ya kalleta
"ba ki da wani damuwa ko?"
Kai ta gyaɗa
"Babu komai Yaya"
Ya ce
"Masha Allah"
Miƙewa yayi ya zare kudi ya ajiye mata dukda tana aiki godiya tayi ta mishi ta raka shi har mota ya tafi ta dawo tana murmushi ya kan yi hakan tun bayan aurenta, haka kawai sai ta ganshi zai zo ya duba ta ya tabbatar tana lafiya ya ajiye mata kudi ya tafi.
Gida ya nufa kai tsaye, bai je Sashenshi ba don la'asar ya kusa yana so ya duba Mammi kan ya fita yayi sallah sai ya dawo ya huta gabaɗaya, ko da ya shiga yanayin wurin ya ɗan zubawa ido Dukda ya fahimci Mammi ta yi hawaye sai dai idanunshi da suka shiga cikin nata ya ɗan ji wani yanayi da har bai ɓuya ba, seconds ya kwashe yana kallonta kan ya ɗauke kai sai ta miƙe ta zo zata fita muryarta na cracking tace
"Sannu da dawowa"
Bata jira amsarshi ba ta wuce don ganinshi kaɗai tausayi yake bata.
Ɗan shiru yayi kan ya taɓe baki yana ɗaga Kafada ya isa wurin Mammi
"Mammi why did you cry? Yarinyar chan ne ko?"
"Ni ce dai na sakata kuka ba ita ta saka ni ba, ka dawo?"
Bai ja zaren zancen ba yace
"Eh, hope baki ji yunwa ba?"
"No ban ji ba, na san ma Abeeha ta kusa shigowa ko na ji ma zata zo ta sama min wani abin you should rest"
Kai ya gyaɗa ya ɗan jingina da kujera yana lumshe ido
"Ni ko ina son yin wata magana da kai"
Buɗe idanun yayi yana kallonta
"Saraki ka tuna kai ka ce in zaɓa maka mata ko ma wacece za ka aureta in dai ni ce na zaɓa?"
Ɗan shiru yayi kan chan dai ya gyaɗa kai.
"Toh mun samu Mata Saraki"
Bai wani nuna ya ji daaɗi ko zumudi ba sai ma runtse idanu da yayi ya ɗan buɗe.
"Baka tambayi wace ba kuma a ina?"
"Mammi ke fa kika shirya wannan aure duk abubuwan nan ba lallai sai na ji ba ayi duk abinda ya dace kawai"
"haka za ka aureta baku fahimci juna ba? Ai ba'a haka dole za ka nuna mata itama macece kaman sauran mata ka bata darajar ta na neman soyayya da ma kyautatawa da kan shiga tsakanin saurayi da budurwa"
Idanunshi kawai ya zubawa Mammi don jinta kawai yake baya tunanin zai iya yin ko abu guda cikin wanda ta lissafo.
"Mammi kin fa san duk ba zan iya wannan ba"
"Toh na ji amma ka san wacece yarinyar? Ka dai san ba zan zaɓa maka wacce na san bata dace da kai ba ko? Kuma ka yi min alkawarin ƙarbar ta yadda take ko?"
Ya ɗan matsa kaɗan ya riƙe hannunta
"Mammi duk zagaye-zagayen nan na menene? Kin fa san yadda na ɗauki girman alkawari wallahi zan amince, wacece?"
Yadda take ta zagayen ne yasa ma yaji yana son sanin wacece haka.
"Afeefah ce!"
Ɗan shiru yayi yana tunani don sai ya ji kaman ma bai san sunan ba, amma duk inda ya zagaya a kwakwalwarshi mace ɗaya tak ya sani da wannan suna, mace ɗaya da ya sani kuma buduruwar abokinshi ce salim.
Da sauri ya kalli Mammin yana girgiza kai
"A'a Mammi ki samo wata ba wannan ba"
Da zuciya ɗaya yayi maganan kuma kai tsaye.
"Ban gane in samo wata ba, Meyasa?"
"Mammi ni wannan ta yi min yarinya wlh ba na son hauka da raini, sannan Mammi buduruwar saleem ce fa! Ta ya zan fara zaman aure da ita?"
Murmushi Mammi tayi a maganan nashi na farko
"Ina saleem ɗin? Ina yana chan yayi aure yana zaune da matar shi? Ko ma bai yi aure ba ba zan amincewa Afeefah ta auri saleem ba ba kuma don shi a karan kanshi ba sai don mahaifiyarshi ba zan so ta koma inda zata sha wahala ba shiyasa na zaɓa mata kai ina da yakinin za ka kula da ita har karshen numfashi"
Tayi maganan cikin tabbatarwa, duk ya ɗan ruɗe mata kaman zai yi kuka ya fara magiyar ta chanza wata shi dai wannan yarinya bata mishi ba.
"Ba fa zan fasa ba Saraki sai ka bani kwakwarar hujjar da zan gamsu ban da buduruwar saleem, ban da kuma baka sonta itama bata son ka dukkanku za ku koyi son juna idan zama ya haɗa ku, banda kuma tayi yarinya don kaima ka san ba yarinyar bace"
Hangota kawai yake a idanunshi yana son tuna menene kuma aibunta wannan idanu farare manya da take zarowa duk sadda yayi magana yake hangowa kawai, da ɗan sauri yace
"Mammi baƙa ce!"
Dariya Mammi ta fara tana girgiza kai ya kwaɓe fuska shi da gaske yake
"Yaushe kuma ka fara zaɓar kala? Kenan ni da babanku bai aureni ba kenan ko kuma da Su Jannah ba za su auru ba"
"To ai ku daban ne ita daban Mammi"
"Ka san Allah idan ba legit hujja zaka kawo ba, maganan nan babu fashi ka fara shiri... Saboda yanayin jiki na ba za mu ɗauko wani hidima ba ɗaura aure kawai za'a yi ayi walima kowa ya shaida ta tare"
Duk yadda ya so ya zamewa Mammi ya kasa, don komai ya ce tana da amsa har aka kira la'asar ya tashi ya tafi, ta bishi da kallo tana murmushi idan ta ga yana hira da ita haka hakan na yi mata matukar daaɗi a rai, ta kan rasa Meyasa baya son Magana alhali ya iya ba bai iya ba, kawai dai ya zauna shiru ya fi mishi ko mahaifin su Jannah da yana raye sai dai ya ji dariyar ta ba zai ji maganan Sarakin nata ba yayi ta tsokanarsu kenan tana shigarwa Sarakin don shi bayan ita wasa da sakin fuskanshi babu mai gani gwara ma saleem da suka shaku sossai shima don salim ɗin ya karanci halayenshi ne tsaff kuma ya iya zama dashi.
Tana fata ko ba yanzu ba ya so Afeefah ya sake mata fiye da yadda ita take ganin wannan side ɗin nashi, hannu ta ɗaga tana roƙon Allah ya nuna mata wannan rana da zata miƙa shi ɗakin matarshi.
Daga nan ta miƙe ta shige don alwalar la'asar, bata yi ƙasa a gwiwa ba da daren ta sa driver ya kaita gidan ƙanin mahaifinta Uncle Musa dattijo ne sossai shima kuma natsatse mai tarin ilimin boko da arabi yana da zuri'a kuma duk zaman lafiya suke da su Mammi, sossai ta mishi bayanin Afeefah ta kuma roƙi da su je su nema mata aure a wurin dangin mahaifinta don a fita hakkin su, bata so su bada komai amma tana son A karɓi auren Afeefah daga shakikanta. Ya gamsu shima kuma yayi na'am da hakan sun yi hira sossai don tana kwana biyu bata je ba sbd jikinta shi ne ma ya kan zo har gida ya duba ta haka yaranshi da wasu jikokinshi, bata bar gidan ba sai da suka tsayar zai yi tattaki da kanshi da babban danshi su tafi Dutsen-wai su nemi a basu ranar auren daga nan sai a fara shiri.
****
Mommy ce kwance a kan gado tsabar damuwa da tunani da ta sakawa kanta ne ya sa jininta hawa sossai, su Samha ke zagaye da ita a yanzu ɗin ma hawaye take zubarwa na tausayin Saleem da damuwar halin da yake ciki wanda ta yarda laifin ta ne amma me yasa su Yaya za su rama alkhairinta da mugunta? Me ta musu da zafi haka?
Bata gama tunanin ba Sabrina ta shigo ɗakin ta samu wuri ta zauna
"Sannu Hajiya mommy ashe kuma jiki ya ƙi?"
Mommy ta danne tace
"Eh amma Alhamdulillah"
"Toh Allah ya kara sauƙi dama Saleem ne ya aiko ni"
Yadda ta kira sunan sai da suka daga kai duk suka kalleta.
"Wai cewa yayi ku koma wanchan tsohon gidan na gado ya riga ya tashi 'yan hayan yana son yayi renovating nan, kin ga yanzu mun yi yawa ga iyali zai fara tarawa ga su Gaje gininsun ya tsofe cikin ko wani minti zai iya rufta musu suma dai duk nan za su dawo"
Galala suke kallonta da kyar mommy ta iya cewa
"Saleem ɗin ne yace haka?"
"Ai kin san ban san yan hayan ba bare in tashe su, shine yayi komai kuma ya tabbatar min kar ku wuce yau don gobe masu aikin za su fara zuwa"
Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga sulmiyo wa mommy da su Samha, Sameera ce ta iya daurewa ta miƙe tsaye ta fara hada kayan mommyn don ba zasu zauna ba, gwara su tafi ɗin babban matsalar dukkansu babu mai aiki cikinsu karatu suke yi, mommyn sai kallonta take tana jin tururin zafi a zuciyarta tuni Sabrina ta fice, mommy tashi tayi ta fito kai tsaye ta haura saman su ta buga, su Samha duk suka bi bayanta jikinsu a matuƙar sanyaye sai da tayi mintuna biyu kan aka bude saleem ta ƙura wa ido sama da seconds goma kan tace
"kai ka ba matarka saƙo ta ba mu?"
Kai ya gyaɗa
"Duk abinda tace haka ne!"
Jiri ne ya kwashe ta ya yunkura zai tare ta ta ture hannunshi ta juya da sauri ta sauƙa su Samha ta cewa su hada kayansu duk suka hada suka fito a motar sadiqa suka zuba duk abubuwan buƙatar su ta ja suka fice daga gidan dukkansu suna kuka, basu sake jin tashin hankali ba sai da suka iso gidan duk 'yan haya sun lalata shi komai dai sai a hankali kuma dakuna biyu ne da parlor sai kitchen duk jiki a sanyaye suka zauna a parlorn mommy na dafe da kanta har lokacin kuka take yi.
"Mommy..!"
Sameera ta kira sunanta.
Sai ta ɗago ta kalleta
"Kina jin zafi a ranki ko? Kina jin ciwo da raɗaɗi ko? Kina jin baƙin ciki da tsantsar damuwa da tashin hankali ko?"
Mommy tace
"Ba sai na faɗa ba Sameera abin da nake ji ba zai misaltu ba ni saleem ya ɗaga daga gidan shi zai dawo da surukanshi? Ni
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 40