bata umarnin tafiya suka fito a ruɗe sai ga Ameer tare da shi da wasu securities suka bi bayan su Afeefar cike da adu'ar Allah ya sassauta koma menene ya bata lafiya cikin gaggawa..
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*Don Allah ku yi min uzuri na so in bi comments in amsa kowanne amma na kasa, bana jin daaɗi ne kar ku yi expecting biyu gobe in na iya na yi ɗayan ma Alhamdulillah!*
*56*
Afeefah ta matuƙar jiggata kan aka samu aka shawo kanta da kyar, shi dai ba zai ce ga abin da yake yi musu a ɗakin ba yana tsaye ne kawai saboda matsayin shi na likita kuma mai muƙami da ba zasu iya kora ba, hannunshi na rike da nata yana tsaye kyamm idanunshi na zube kan fuskarta wani irin ciwo ne wannan lokaci ɗaya? Me ya sameta? Babu kalar sake saken da bai yi ba.
Kalaman da ya ji likitocin suke yi cikin harshen turanci cike da ƙwarewar aiki ya ƙara daure mishi kai ya jefa shi cikin tunani da damuwa lokaci ɗaya.
"Sir da ka je ka sauya wannan kaya saboda duk sun yi stains, za tayi bacci sossai kila sai zuwa midnight ta farka sai a sake running wasu tests"
Wani likitan ya faɗa bayan ya dafa kafaɗar Rayyan da ya jima cikin duniyar tsoro, mamaki da kaɗuwa.
Hannunta ya zame yana kallon kayan da aka kawo za'a sauya mata da wasu towels da za'a goge mata jikin da ya ɓaci Dukda mata ne karɓa yayi suka fita, shi ya goge mata jikin tas ya sanya mata kayan asibitin riga da wando ne kan ya gyara mata kwanciya ya duba tafiyar ruwan har lokacin fuskarshi Jajazir, kwakwalwarshi ya ƙi hutawa da saƙe saƙe a haka ya fito daga ɗakin sai ya tsaya chak yana kallon Ammi da take kallonshi itama a zaune.
Jikinshi ya bi da kallo yana tuna jinin ɗan shi ne nan ko ɗiyar shi, wani irin zafi da bai san ya zai fasalta ba na taso mishi a cikin zuciya bai san ya nufi Ammin ba ya samu wuri a gefenta dab ya zauna bai ce komai ba kanshi a ƙasa, dukkansu sun yi mamaki har ita kanta amma ta danne tace
"Sameer ya jikin Afeefahn?"
Ya yi shiru na seconds yana hadiye wani irin miyau ya ce
"Da sauƙi tana bacci"
Wannan ne karo na farko da maganan da ba gaisuwa ba ya shiga tsakaninsu hakan ya faranta mata kwarai amma damuwar halin da Afeefah take ciki bai barta ta nuna ba.
"Me ya sameta haka?"
"Ammi Afeefah ta ci wani abu a sashenku da safe?"
Abeeha da har hawaye tayi ta zubarwa tace
"A'a Yaya ko ruwa bata sha ba tace ta ci abinci kenan ta fito"
"Me ya faru da ita haka?"
Ameer da Ammi suka tambaya a tare, haƙorinshi ya sa ya datse lip dinshi na ƙasa kan ya saki zuciyarshi na tafarfasa yace
"Ɓari tayi... Zubar da shi aka yi! ta yi misscarrage ba tare da duk mun san akwai ma ɗan ba.."
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun..."
Abinda duk suka faɗa a tare kenan, Ammi ta sanya hannunta ta kama nashi sai ya kalleta
"Ammie ɓari biyar kika yi?"
Ta gyaɗa kai bata ce komai ba
"Duk wannan azabar da Afeefah ta sha haka kika sha?"
Ta sauke numfashi tace
"Na sha wanda ya fi shi ma Sameer, shi ina mai tabbatar maka azabarshi zai iya ɗara na haihuwa. Ka je ka sauya kayan nan haka kar ƙarnin jinin ya zauna maka a jiki"
Idanunshi ya ɗaga sama yana mayar da emotions dake taso mishi ya kalli jinin
"Ɗanki ɗan watanni biyar ma kin rasa shi ko Ammi?"
Nan ma ta gyaɗa mishi kai.
"Haka zafin yake?"
Bata danne ba tayi murmushi mai ciwo tace
"Duk wanda za ka ji daban yake da na uwa Sameer, uwa ce kaɗai za ta iya fasalta wannan zafin... Idan har ka ji zafin fitan ɗan da baka ma san da zamanshi ba ka fasalta da Aliyu da na rasa sai da na raini cikinshi na watanni tara na haife shi na shayar dashi na ga haƙorinshi na farko, na ga murmushinshi na farko na ga zamanshi kan Allah ya karɓi abin shi..."
Hawaye ne ya zuba mata a lokaci ɗaya da Ryan, shi likita ne amma bai taɓa kula da abinda ya shafi ciki ko haihuwa ba don duk abu da mata a baya ba kaunarshi yake ba, cikin jannah da Abeeha duk ba zai ce ga yadda Mammi tayi ba, idan wannan bari ya saka shi jin irin wannan zafin ya Ammi ta ji?
Bayan duk wahalar kuma aka yi ta yunkurin kashe shi mahaifinshi bai ɗauki kwakwaran mataki da zai sa hankalin uwar tashi kwanciya ba, motsin da suka ji yasa duk suka ɗago sai ya ga mai martaba ne da dogarai biyu don ya kasa zama dole ya biyo bayansu. Shima kuma a yanzu ya fahimce shi dole ba zai so rabuwa da ɗan shi guda da Allah ya bashi bayan tsawon shekarun da ya ɗauka babu haihuwa ba.
Dukkansu basu da laifi, uwar da ta zama distressed ta haɗa baƙin ciki, damuwa da wahala duk lokaci guda zai ga laifinta ko uban da baya so ya ga yayi nisa da gudan jinin da yake mararin samu? A yanzu ya fahimci damuwar Ammi ta sanadiyar Afeefah ya ji a ranshi zai mata uzuri ya ji a ranshi kaman Allah ya riga da ya rubuta ne Mammi ce zai yi rayuwa da ita har mutuwar ta ba Ammi ba, kaman yana ji a ranshi cewa Adu'ar Ammi ce Allah ya karɓa ya tura mishi Mammi. Ta wani ɓangaren he's grateful na barin shi masarautar don da bai bari ba da bai san Mammi ba idan kuma bai santa ba da bai samu Afeefah ba the 2 most important persons da Allah ya bashi su as his greatest gift.
Ƙasa ya kai ya riƙe hannun Ammi ya ɗora fuskarshi a kai ya ce a hankali
"Ammie ki yafe min, ki yi haƙuri na tuba!"
Ɗumin hawayenshi suna sauka ne da nata, kuka take sossai na farin ciki Allah ya amshi adu'ar ta, Allah ya karkato mata da hankalinshi cikin sauƙi. Ɗago shi tayi ta miƙe tsaye kawai ta rungumeshi Dukda tsawon da ya fita, duƙawa yayi suka rungume juna yana jin dumin mahaifiyar tashi na ƙara karya zuciyarshi, da kyar ya danne kukan da ke taso mishi.
Mai martaba ya dafa shi yana dan buga kafaɗar shi zuciyarshi fari tas na ganin abinda ya jima yana fata shima, komai ya wuce don Ammie ɗago shi tayi ta ce
"Sameer na yafe maka duniya da lahira baka yi min komai ba, ni ya kamata ma in nemi yafiyarka da wahalan da na saka ka... Haƙiƙa na yi kuskure mai girma wanda Allah ne ya dube ni ya raya min kai kan tafarki amma da ban san da wani ido zan isa ga mahallici na ba da rayuwarka ya salwanta. Ka yi haƙuri"
Kai ya gyaɗa.
Mai martaba ya ce
"Ya mai jikin yanzu?"
Cike da girmamawa Ammie tace
"Alhamdulillah Taƙawa tana bacci ne sai dai mun rasa ɗan cikin"
"ɓari tayi? How?"
Juyawa Ryan yayi ya fita Ameer ya bishi, Ammi ce ta mishi bayanin suma basu sani ba amma da yake asibitin kuɗi ne kuma kwararrun likitoci ne suka duba ta a bincikensu sun tabbatar da abu ta sha yayi sanadiyar zuban cikin.
"Tirƙashi! Kar fa tarihi ya maimaita kanshi!"
Shiru Ammi tayi ba zata so wa Afeefah wannan wahalar ba, Amma Allah ubangiji ya sa lokacin tonon asirinsu ne yayi haƙiƙa adu'ar da take ta tabbatar ba zai faɗi ba Allah sai ya bi mata hakkin cutar da ita da aka yi.
Suna nan zaune sai ga Ameer da Ryan sun dawo ya sauya kaya zuwa riga da wando english wears hannunsu rike da ledoji manya da alama ba gida ya je ba, ya dubi mai martaba.
"Abieey ya kamata duk ku je ku huta da safe Ammie sai ta dawo"
Sun amince don a yadda yake sun san ko me zai faru ba zai amince wani ya kwanan mishi da mata ba don haka bayan Ameer ya miƙa mishi ledar suka yi sallama har Abieey ya juya Ryan ya ce
"Abieey"
Sai ya juyo
"Abieyy ina so ka min wani alƙawari guda ɗaya"
Kai ya gyaɗa
"Abeey ka min alkawarin duk wani mai hannu a matsalar da Afeefah ta shiga zai biya kwatankwacin wahalar da ta sha kuma ba zaka hana ni yanke hukunci akan hakan ba! Idan kuwa har link ɗin wannan laifi ya haɗu da na mahaifiyata wanda yayi sanadiyar nesanta ni da ku gabaɗaya....."
Sai ya danne haƙorinshi da ƙarfin gaske yana dunkule hannu alamar bai ma san me zai iya aikatawa ba.
Numfashi mai martaba ya sauke
"In shaa Allahu za'a yi duk abin da ya kamata ai wanda ya kashe mutum ba shi da sauran alfarma, amma yanzu ka yi focusing kan lafiyarta tukun"
Juyawa kawai yayi ya nufi ɗakin don ya faɗa ne ma kar mai martaba yayi yunkurin hana shi daukar mataki idan har abinda yake zargi ne.
Wuraren karfe ɗaya na dare ta farka, yana zaune hannunshi ɗaya a cikin nata idanunshi zube a kanta ta buɗe idanu, ta lumshe ta sake buɗewa a hankali yace
"Boɗɗi kin tashi? Sannu!"
Ta lumshe ido alamun amsawa duk jikinta ba kwari a hankali tace
"Me ya same ni? Cikina bai taba irin wannan ciwo ba na ɗauka mutuwa zan yi Ya Saraki..."
Goshinta yayi pecking ya ɗago yana shafa kanta yace
"Ba yanzu ba Afeefah, ba za ki mutu ki bar ni ba"
Za tayi magana sai ga Dr da wasu nurses sun shigo, bai motsa ba har suka iso kanta likitan yayi ta mata tambayoyi tana amsawa kan nurses ɗin suka dibi jininta suka mishi sai da safe suka fice.
Tsabar kyaun asibitin da tsarin shi ba zaka ce ɗakin asibit suke ba don ya fi yanayi da ɗakin Hotel ɗaukar ta yayi gabadayanta yaje ya mata wanka suka dawo ɗakin, tea ya hada mata ya hau gadon yana bata a hankali har ta ce ya isheta ta sha wasu magunguna kan ya dube ta
"Gabaɗaya yau me kika ci da ban sani ba?"
Tunani ta tafi amma dai ta san duk abinda ta ci a ranar shi ne ya girka, gabanta ne ya faɗi ta ɗago tana kallonshi ganin kallon da yake mata na son fahimtar yanayinta ya sa ta kasa ɓoye abin da ta so ɓoyewan muryarta na ɗan cracking tace
"Na sha kindirmo a sashen Mam..."
"Afeefah Ban gargaɗeki akan cin komai a gidan chan ba?"
Calmly yayi maganan trying really Hard to control his self sanin ita karan kanta ta jiggata amma tana fara cewa
"Ka yi haƙuri maganganunta ne suka...."
"To hell with the maganganun Afeefahhh"
Ya katse ta da wani irin tsawa.
"Raina ni kika yi ko kin dauka ban san me nake ba ne da zan ce kar ki yi abu kiyi? Kin fini sanin me nake yi ne? Ke ga ki mai sanyin zuciya ko? Toh sai ki zuba ruwa a ƙasa ki sha tunda kin yiwa kanki asarar ɗan da ko sanin zamanshi ba mu yi ba, kuma kar ki zaci alhakin akan waenda suka aikata hakan ne har ke tunda na gargaɗeki..."
A razane take kallonshi bata san hawaye sun fara cika idanunta ba sai zubowar su taji ta kai hannu ta dafa cikinta muryarta na rawa sossai ta ce
"Ɓ..ɓari na yi?"
Ganin yayi shiru ta sake cewa
"Da gaske ɓari na yi Yaya? Wlh ban sani ba! Ban san akwai shi ba da ban sha ba, kawai kindirmon ya...ya ba ni sha..."
"Kin yi min shiru ko sai na tsinka miki mari Afeefah???"
Baya ta matsa don yadda ya harzuko ɗin nan duka ne kawai ya saura bai kai mata ba jikinta sai ya fara rawa, kuka take yi sossai ya cigaba da masifa cike da bacin rai
"Ban gaya miki duk abinda kika ji ya baki sha'awa ki sanar da ni ko menene ko a ina ne zan samo miki ba? Ko ban faɗa miki ba??? Amma da yake kunnen ƙashi ne da ke ga abin da kika janyo...."
Cikin kuka da rashin madafa take furta
"Am sorry...! Ka yi haƙuri na yi kuskure... Ban sani ba ne.."
Bai tanka ba sai ficewa da yayi daga ɗakin gabaɗaya don ya cigaba da tsayuwa ma karya mishi zuciya zata yi.
Kuka ta fashe dashi tana ambaton sunan Allah, wato ana cewa gidan sarauta na da kunne ashe ba kunne ba kadai har da ido? Cikin da ko su iyayen basu sani ba wasu sun hanga har sun cutar musu da shi? Laifinta ne wlh laifinta ne ta yi kuka har baccin wahala ya ɗauketa tunda a magungunan akwai na saka bacci bata ga Shigowar shi ba, shi ko yana zaune a reception ya jingina bayanshi kanshi a jikin gini kafafunshi a harde yana saƙe saƙe don abin nan ba zai taɓa tashi a banza ba.
Washegari ko da Afeefah ta farka bata ganshi asibitin ba sai su Ammie Aisha da Adda Abeeha da kuma wasu hadimai, yanayinta duk ba daaɗi suka raka ta bayi suka fito tayi wanka suka taimaka mata ta shirya kan suka zuba mata abin kari bata da wani apetite in ta tuna haukan da tayi sai taji hawaye na zubo mata, Ammi ce tayi ta bata baki dai har take jin zuciyarta yayi sanyi. Abin mamaki ta ƙara kwana biyu a kwance har wankin cikin aka yi Ryan bai dawo asibitin ba ko ma ya dawo bata sani ba don idanunta dai basu ganshi ba hakan ke nuni da cewa ba fushin wasa yayi ba, dare haka zata yi kukanta har tayi bacci da safe ayi ta tambayar me ya samu fuskarta tace babu komai a kwana na uku aka sallame ta suka dawo masarautan kai tsaye sashenta suka kaita nan ma baya nan.
Wata elderly woman Ammi ta turo tana kula da ita musamman cimarta don tana bukatar abubuwan da za su dawo mata da kuzari da kuma karfin jiki, ita dai duk abin da ta bata ci take kuma tana kiyaye dokokin matar tunda har Ammi ta ce mata da sanin Ryan ta turo matar sai bata ɗaga hankali ba, Dakon dawowanshi tayi tayi a daren sai dai abin mamaki har wurin ƙarfe 1 na dare ya shigo sashen ɗan kallonta yayi ya ɗauke kai tana sanye da riga da zani sai ɗan kwalin da tayi simple dauri da ya bayyana gashinta ta baya bayan dan kunne babu wani accesories da ta tula, bata ji sallamar shi ba kenan ciki ciki yayi abin shi ganin zai wuce ta miƙe tsaye
"Ya Saraki...!"
Chak ya tsaya, ta tako a hankali ta dawo bayanshi muryarta na rawa ta ce
"Don Allah ka yi haƙuri, ba zan iya cigaba da jurar fushinka ba. Ka gafarceni na san na yi kuskure don Allah ka yafe min"
Idanunshi ya runtse na seconds kan ya buɗe ya cigaba da tafiya bai ce mata komai ba, bayanshi ta bi tana kuka mai sautin dugunzuma hankali, share ta yayi ya cire kayanshi tsaf ya ɗaura towel ya shige bayi yayi wanka yana fitowa ya ganta tsaye again har lokacin bata bar kukan ba, zuciyarshi ne ya karye yana jin kukan har cikin kanshi.
Gaban mirror yaje yana goge jikinshi da ƙaramin towel ya ɗauki bodyspray ya feshe kirjinshi dake bayyane dashi yana ƙoƙarin Juyowa kenan yaji ta kwanta a bayanshi ta saka hannayenta a kugunshi tana kuka still har hawayenta na ɗiga a fatar bayanshi, kasa controlling kanshi yayi ya juyo gabaɗaya ya bata kyakyawar runguma.
"Kayi haƙuri ba zan sake kuskuren tsallake maganarka ba, fushinka na sake ɗaga min hankali don Allah ka y...."
Fuskarta kawai ta ji ya ɗago ya haɗe lips ɗinsu yana bata sumba mai zurfi baya baya yake yi da ita har jikin gini, ta sanya hannayenta biyu ta zagaye wuyanshi tana bashi support, sai da ya gaji don kanshi ya raba bakin nasu suna jan numfashi a hankali hankali ya haɗe goshinta da nashi yayi pecking lips ɗin still don baya taɓa gajiya da su a hankali yace
"Kar na ƙara ganin kin zubar da hawayenki wanda kika yi a baya sun isa, Allahn da ya bamu ba tare da sani ko shawarar mu ba zai bamu wani. Mu sa a ran mu haka ya kaddara wannan ɗin ba mai zuwa ba ne"
Kai ta gyaɗa mishi ya ja ta bakin gadon ya taya ta cire kayanta tas ya ɗaura mata towel don su sun fi gane kwana a haka, ya ja ta suka kwanta hannunshi na yawo jikinta cike da kulawa a haka suka yi bacci dukkansu kowa da abinda yake saƙawa.
Washegari da safe kan ma su tashi An shirya musu abinci wanda daga sashen Ammie ne, kuma ta yi mamakin ganin ya zauna suka ci tare don duk zamanta a asibiti Ammi ke mishi girki da kanta, bayan sun gama suka fito a tare gaisuwa yana sanye da wani Beige yard mai taushi da kyaun shi ya bayyana tsurar tsadarshi tana sanye da straight skirt and blouse da aka yi rigar da wani yadi mai sulɓi green za ka zaci fitted gown ne mai combination da lace idan baka sani ba saboda yadda ya zauna mata, alkyabbarta mai kauri ne hakan ya sa bata damu ba kuma akwai gyale Kasar shi hannunshi na riƙe da nata suka nufi sashen na Ammi, sai mamaki take da tunanin yaushe suka shirya kuma? Amma a gefe ɗaya farin ciki ne ya cika mata zuciya da har ta kasa boyewa sai murmushi take zabgawa yana kallonta bai ce komai ba har suka shiga.
Sun samu Ammi zaune cikin kujera Abeeha da Aisha na karyawa yayinda Ameer ke zaune yake jan su da hira da wasa, ganin su ya sa fuskar Ammi cika da fara'a, kai tsaye gangarta yaje ya zauna Afeefah ta samu wuri a ƙasa ta zauna tana ta murmushi Allah ya gani shiryawarsu wani abu ne mai muhimmanci a gareta da bata taɓa saka goshinta kasa ba tare da ta yi mishi adu'a ba kuma Alhamdulillah ko a yanzu waninsu zai faɗi ya mutu ta tabbatar ba za su bar abin nadama ba.
Gaisuwa suka yi tana tambayarta jikinta tace da sauƙi, suka gaisa da su Abeeha yayinda duk suka gaishe shi ya amsa cike da izzarshi ta jinin sarauta don fuskar a kame take tun abin da ya faru bai wani sake ba, sun jima anan kan yace ta tashi su tafi.
Babu musu ta miƙe suka fice yana riƙe da hannunta da dumbin mammakinta sai ta ga ya nufi hanyar Sashen Fulani Adama, gabanta ne ya shiga dokawa amma ganin babu fuska ya sa bata yi magana ba har suka isa. Tana zaune a parlornta ta yi zurfi cikin tunani sai ganinsu tayi ita kanta ganin Rayyan mammakinta ya kasa ɓoyuwa har bata san ta miƙe tsaye ba sai da yayi murmushi ya ce
"Mama barka dai mun zo ba sanarwa dole ki ji mamaki"
Yana maganan yana zama, itama komawa tayi ta zauna tana kakaro murmushi
"Gaskiya kam na yi mamaki ashe baka manta hanyar sashen nan ba?"
"Ɗa bai taɓa mantawa da uwa ba ai Mama, Fatan kina lafiya?"
Idanunta ta kawar don wallahi kallon da ta ga yana mata a take ya saukar mata da wani irin faɗuwar gaba har tana jin zufa na keto mata amma ta dake.
"Lafiya Ƙalau, ashe kuma abin da ya faru kenan? Allah ya mayar da alkhairi"
Afeefah da itama karon na biyu bayan zarah ta ji ta tsani matar ta gaisheta da kyar, ta amsa basu jima ba ya miƙe har sun nufi fita ya juyo ya sake kallonta ya saki murmushin da ya sake kaɗa mata yar hanji.
Jeka ka dawo ta shiga yi hannunta da waya tana ta danna kira sai dai karo na sama da ɗari da wani abu kenan daga jiya zuwa yau bata samu Layin ba, yaraf ta koma ta zube tana dafe goshinta dake sara mata...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*57*
*Ƙarshen Alewa...*
Satin da ya biyo bayan faruwar ɓarin ba zata ce bata ji daaɗinshi ba sai dai ta kula tarin soyayyar da yake nuna mata ya ragu da kaso talatin cikin ɗari wani sa'in ma sai ta ga kaman ya koma mata asalin Rayyan ɗin shi na baya da ta sani, Dukda bai rage ta a komai ba na kulawa sai dai tana ji a jikinta har yanzu bai gama sauƙa ba wanda ita kanta in ta tuna sai ta yi kuka, ta fara lectures online kuma yana bata taimako yadda ya kamata ta ɓangaren, ta zuba idanu ta ga sun koma yadda suka faro amma ta kula shi bai san zuru ba dole ta sake shirin bashi haƙuri.
Sannan a kwanakin ya kan daɗe a waje wani har ma tayi bacci bai dawo ba sai dai ta farka ta sameta kwance jikinshi, a yau ta yi niyyar sake tunkararshi ta sake bashi hakuri don bata kaunar wannan silent treatment ɗin nashi ko kaɗan, karfe goma ta fito wanka ta zauna ta ɗauki lokaci kwarai wurin sake gyare jikinta tsaf ta haɗa wani magani da wannan mata da Ammi ta turo mata take bata da madara ta sha, dama ta dafa mata goron tula ta zuba zuma shima ta sha kan taje ta fara neman abinda za ta saka, wani farin strapless lace bra mai haɗe da wando wanda ma kai tsaye zaka iya kiranshi bumshort ta saka ta ɗora rigar saman da ya bayyana duka fatar jikinta don bashi da maraba da raga.
Gashinta ta gyare tsaf ta fito ta nufi kitchen, a yadda dare yayin nan ta san ko ya dawo ba sake cin komai zai yi ba sai ta haɗa fruit salad ta cika mishi madarar ruwa ta saka a frigde ta fita ta kara karfin Ac ta sake kunna turarukan wuta a duka burners dake kusurwan gidan sai da ta ba kowanne mintuna biyar taje ta kashe kamshin na fita a hankali ba tare da wani hayaƙi ba, tana shirin nufar ɗaki ta ji ya turo kofar parlorn sai ta tsaye nan tana kallonshi.
Numfashinshi ne ya so barin shi na wucin gadi idanunshi manne da jikinta yana bin ta da wani irin kallo da ya sakata sakin murmushi ta nufo shi a yangace, gani yayi in ta cigaba da tafiyar kan ta iso za ta iya sumar dashi yasa ya yunkura kawai ya nufeta sai janta kawai yayi ya rungume yana sauke fuskanshi cikin wuyanta da wani irin salo ya sauke numfashin relief, ƙanƙameshi tayi kaman yadda shima yake sake riƙe ta cikin kirjinshi hannayenshi na sake matse ta.
"you are driving me crazy My Love"
Murmushi mai sauti tayi, ta raba hug ɗin tana sunne kai wai ita a dole kunya hakan kuma na sake tsuma shi tace
"You are welcome My king, ka bar ni ina ta kewa"
Ya saki murmushi
"Daga yau in shaa Allah na gama barinki da kewata mu je ki taya ni wanka"
Ya riƙe hannunta tace
"Ba ka jin yunwa?"
Yayi pecking bayan hannun nata yana sake bin jikinta da kallon dake rikitata ya furta
"Ke kaɗai nake buƙata a yanzu idan na sameki na ƙoshi"
Tayi murmushi a kunyace ta bi bayanshi zuwa ɗaki, a tsakiyar ɗakin ta tsaya chak ya waigo ya kalleta
"Menene?"
"Na tuna! ba fushi kake yi da ni ba har yanzu...Na baka haƙuri na baka haƙuri amma ka ƙi ka haƙura"
Da wani irin salon Shagwaɓa da sanyi tayi maganan, ya lumshe ido yarinyar tana shirin zauta shi a tsaye da sauri ya buɗe idon jin motsinta sai ya ga ta juya zata fita da hanzari ya saka hannunshi ta cikinta ya dawo da ita baya har kan kirjinshi bayanta ya sauƙa ya sauƙe kanshi cikin wuyanta yana bata wet kisses da suka sa ta fara kunnuwa don ya mugun sanin weak point ɗinta yace
"wa ya ce ban haƙura ba Boɗɗi? Ai na haƙura..."
A cikin kunnenta yayi maganan chan ƙasa muryarshi na sarkewa. Ba zai iya jurewa har yayi wanka ba hakan yasa ya chusa hannunshi cikin yare yaren
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 36 Chapter of 40