Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mace mai gata da zata zauna a wannan uban sanyin tana wanki ga tarin wanke-wanke dake jira a gefe, bai ga dacewar a ce kowa na ɗaki a ɓoye ita ɗin tana ƙasan pampo ba, bai gama tunanin ba ta saki atishawa har huɗu a jere ta ja hanci tare da ɗora goshinta a kan gwiwarta, wani iri yaji sai yaji yana son kallon fuskarta, hakan ne ya hana shi tafiya har ta ci seconds kan ta ɗago ya ɗan ƙurawa face ɗin idanu. Kawar da idanun yayi ya mayar hannunta dake wani irin rawar ɗari duk kakkarwa suke, sun sandare saboda sanyi ga hijaban da ta lafta rabi a jiƙe shakaf. Tunanin inda ya san fuskan yake sai dai ya kasa ya ɗan sake kallon gashin idanunta da suka yi fari fat ya ja tsaki tare da barin wurin gabaɗaya, mayar da takardun yayi ya fice daga sashen ya nufi harabar gidan don tafiya sabgar gabanshi sai ga Sadiqa ta fito taryar Ƙawayenta da Shigowar su kenan kowacce na ƙoƙarin sauƙa a motar ta, ganin shi ya sa ta wani zaro idanu shi kam kallo ɗaya tak yayiwa gefen da suke ya ɗauke kanshi ya cigaba da tafiyarshi with steez bai ma san su waye ba bare ya tantance mutane ne ko aljanu. "Ya Ryan" Ta ƙira sunan a hankali sanin baya son ihu ko hayaniya, in ka cika ko magana da ƙarfi ne sai Ranshi ya ɓaci kuma muddin nashi ya ɓaci kaima sai naka ya ɓaci haka yake, ya ɗan ɗago ya kalleta a kan rigar sanyi jibgege dake jikinta ya soma sauƙe ido kan ya ɗan ja tsaki matsalar shi kenan, da wuya ya ga abin da ke cutar da wani ya iya ɗauke kai, baya son zalunci sam a rayuwarshi Dukda ana yi mishi kallon miskilin mai murɗaɗɗiyar hali sai dai yana da tsananin tausayi, 'yan aikin gidansu sun shaidi hakan don shi mutum ne dake so ya ga an baiwa ɗan Adam haƙƙinsa na mutum cikakke kaman yadda Allah ma ya karrama dan Adam ya kuma ba shi daraja. Yanzu dubeta killace cikin shigar da ba zai bar iskar bazarar cutar da ita ba amma 'yar aiki zaune ƙasan pampo hannayenta da kafafunta duk cikin ruwa cikin halin rashin lafiya don a matsayinshi na likita kallo daya tak yayi mata ya san bata da cikakken lafiya hakan sai ya sake ɓata Ranshi amma sam fuskanshi na nan a yadda take bata sauya ba "Ina kwana? Ashe ka shigo?" Kai ya gyaɗa kawai ya zagaye ta ya wuce abin shi, da kallo ta bishi tana murmushi a fili ta furta "Miskili ka fi mahaukaci ban haushi" "Waye shi?" Ɗaya daga cikin Ƙawayenta da duk suka bi shi da ido yuuu tayi tambayar. "Ryan Khamis kike ji da gani, sojan da ko a cikin sojoji ake ji dashi, likitan da ko a cikin likitoci babu kamarsa... Ga sanyi ga zafi, ganin dariyar shi ko murmushinshi sai ka yanki tikiti" "Wow shi ne Surgeon General Ryan Khamis? Da gaske don Allah? Dama yana zuwa gidanku haka a bati?" Sadiqa ta saki murmushi "Abokin yayana ne, yana zuwa sossai ma musamman idan suka samu saukin aiki saleem na gida don ba'a raba su, mahaifiyarshi ma na zuwa har gidan nan, shine dai Ryan Khamis" No 1 matashi ne da ake ji dashi mata suke rububinshi don duk inda ya shiga akwai masu kyasawa amma fa shi duk basa gabanshi, yana flatforms sai dai babu wanda ya san handle nashi don akwai handles dayawa da sunayenshi na ƙarya ana yaudarar 'yan mata, shi dai kam kaman dutse yake mace bayan mahaifiyarshi duk a maza Ƴan uwanshi ya ɗauke su. Da zancen shi suka shiga parlor nan aka baje ana cigaba da hiranshi kala kala da kyar suka saki suka kama wata. Shi kam Rayyan yana tada motar shi ya danna ƙiran Salim "Don iskanci ko godiya ba za ka min ba ko?" "Afuwan Ryan ka san ina gani printing kawai nayi na tafi presenting don ana jirana, yanzu kenan fitowa ta ko wayan ban fitar ba na ji ƙiran ka" Driving yake slowly duk zantukan Salim ɗin bai tanka ba sai ya daka tsalle ya kama wani zancen da ya kasa bari a ranshi sai yake jin kaman shima Allah zai kamashi da laifin wulakanta dan Adam tunda ya gani bai yi magana ba "I saw someone familiar kaman na san fuskan but i cant recall" Salim ya ɗan tafi nazari kan ya ce "A gidan mu kuma?" Kai Ryan ya gyaɗa sai kuma ya tuna voice call ne suke yi a hankali yace "Yeah, choculate tall young lady haka" "Afeefah ka gani?" Salim yayi saurin katse shi, a ranshi ya maimaita sunan 'Afeefah' ba tare da yayi magana ba, Salim ya cigaba da magana "Ka santa mana Rayyan, yarinyar da ka ceta wacce ta taɓa shan poison a Anchau?" Sai lokacin ya tuna inda ya san fuskar but Meyasa take aikatau gidan su salim? Ina iyayenta da family ɗinta? Kaman salim ya shiga Ranshi wai aka ce sanin hali ya fi sanin kama bai wuce magana ne a bakinshi ya kasa fitarwa ba don haka ya shiga bashi labarin yadda ya mayar da ita da irin wulakancin da suka sha yadda ta bashi labarinta daga farko har karshe sai da ya gama tsaf Ryan dake parking tsakar gidansu ya ce "Hmmm" Ya ƙarasa yana dan taɓe jajazir ɗin laɓɓanshi ba tare da ya ce komai ba bayan nan, har salim ya zaci ya katse kiran sai ya ji Ryan ɗin ya watsa mishi tambayar "Then taimakonta kenan ka yi to be lowly house help?" "No! No!! Wallahi ba hakan bane a raina Rayyan na rasa yadda zan yi ne, mommy ta katange min duk wata ƙofa da zan iya inganta rayuwarta, abin is hurting me badly... Ka kuwa san akwai Allah ya isa a kaina muddin na yi magana da ita na fatar baki na sama da minti ɗaya?" Ɗan zare shanyayyun idanunshi Rayyan yayi "Wow! Why?" "Saboda kawai sun yarda da champin mutane da ƙagen da ake yi mata" nan ya shiga bashi labarin gumurzun da suka sha da mommy a kanta kan ma aka barta a house help ɗin. Rayyan ya ɗan lumshe idanu ya buɗe a ranshi mamakin mutane yake yi, Sai ji salim yayi yana cewa "Idan bata kashe ku ba ku ai kun ɗauki hanyar kasheta!" Yana kai nan ya yanke wayar don ya gaji da magana, ɓalle murfin motar yayi ya nufi cikin gidan cikin natsuwa da takunshi na ƙasaita haɗe da izza. Kasake salim yayi rike da wayan a hannu yana juyawa, jikinshi ne ke bashi ba haka kawai Rayyan yayi maganar Afeefah ba, ya kuma san a yanzu ko ya sake kiranshi ba lallai ya bi ta kan zancen Afeefah ba kuma bare yayi mishi bayanin me yake nufi da za su kasheta? Hankalinshi ne ya ji yana neman tashi. Allah ya sani daga lokacin da tausayinta ya yi tsanani a ranshi ya juye ya zama mishi so ba tare da ya farga ba, har ranshi sonta yake kuma so yake ya aureta saboda ƙaunar da yake mata not out of pity, ko da ya ajiye ta kaman yadda mommy ta umurta yayi iya kokarinshi wurin ganin ya manta da rayuwarta ya bar wa mommy ɗin sai dai hakan ya gagara mishi dole ta sa ya waiwayeta ya dawo ya kawo mata waya don ya dinga jin lafiyarta da bukatun ta, layinta ya lalubo ya zubawa idanu sama da mintuna uku kan ya danna mata ƙira sai da ya jera sama da 10missed calls bata ɗaga ba sai hankalinshi ya fi na da tashi ya tura mata text message sama da biyar ba reply. A lokacin tana ƙoƙarin tattara kwanukan da ta gama wankewa ta kai bakin kitchen, jikinta babu inda ba ya rawa har hakwaranta na haɗuwa, bayan ta ajiye ta koma inda ta tashi ta ɗauki wayan da karatun ma yau bata samu ta iya kunnawa ba ta nufi ɗakin tana tafiya da kyar, hijaban kawai ta zare ta zubar a wurin ta shige bargo tana hawayen tausayin kanta, jin kaman vibration na wayan nata ya sa ko ido bata buɗe ba tayi picking tare da maƙalawa a kunnenta, Sheshekarta ne ya fara shiga mishi kunne yaji wani abu ya sauka mishi har cikin zuciyarshi hakan ya rikita masa lissafin kwakwalwa... "Afeefah menene? Me ya sameki?" Shiru sai kuka da itama jin muryarshi ya sa ta ƙara karfin kukan, kaman shi ma zai fashe da kukan cikin sanyi ya shiga cewa "Don Allah ki yi min magana Afeefah, hankalina tashi yake da kukan nan naki talk to me please, menene?" Sauƙe wayan yayi ya kalli time saura seconds goma "Help me Afeefah ko ta text ne ki rubuta min Meke damun ki? Kar ki yi kisan kai ki taimaka" Yana kai nan ya sauƙe wayan ya kashe tare da jingina kanshi jikin motarshi, ji yake kaman yayi tsuntsuwa ya ganshi Kaduna sautin Muryar kukanta ke ta amsa kuwwa cikin kanshi... 🖤Gureenjoh🖤 HAIHUWA DA HANJI (A True life story) Fatima Muhammad Gurin (Gureenjoh) Wattpad-Gureenjo6763 Arewabooks-Gureenjoh *FREE BOOK* *014* Shigowar saƙo wayanshi ne ya sa da wani irin hanzari ya miƙe daga jikin motar yana duba wa. "Ba ni da lafiya" Abin da kawai ta iya rubutawa kenan, sai ya ji hankalinshi ya fi na baya tashi don bai san wa zai kira ya taimaka mata ba, idan ma ya ƙira su Samha ya san abin ba zai yi kyau ba mommy kuma za ta iya ɗaga hankali a kan ya aka yi ya san bata da lafiya yana Maiduguri tana Kaduna? Wani tunani ne ya faɗo mishi, nan ya shiga neman Layin wani friend dinshi da yake nan capital hospital Kaduna ɗin a kan ya taimake shi da Layin Dr. Sulaiman, cikin mintuna biyu sai ga Layin a take ya shiga ƙiran Layin ringing uku aka ɗaga "Dr Cap. Saleem ne don Allah wani taimako ne nake nema daga gareka please in ba damuwa" Ya faɗa bayan sallama da gaisuwa, Nan ya yi ta mishi godiya bayan sun gama disussing, ko gida bai iya ya je ba yana zaune ne kawai cikin motar shi cike da tsumayin sake ganin ƙiran Sulaiman. A chan Kaduna kuwa sallamar da ake ta doka wa ne ya sa sameera Miƙewa ta nufi ƙofan, Sadiqa suna dining da Ƙawayenta ana cin abinci ana hira, mommy ke karyawa a tsakiyar parlorn, Samha na wani research a system ɗinta hakan shine ma ya tilastawa sameera da ke danna waya Miƙewa tana mitar irin uban Sallamar da ake tayi, tana bude kofan ta yi niyyar masifa ne sai idanunta suka sauƙa kan Dr. Sulaiman da ke jingine ɗan nesa kaɗan da jikin motar shi, daga ganinshi ka san responsible matashi ne da yake kan ganiyar samartakarsa daga yanayi shiga da kuma tsarin motar shi zaka san ko shi ba mai kuɗi bane daga gidan kuɗin ya fito, Baaba jummai ce dake doka Sallamar ta katse ta "Har na fara tunanin babu mutane ne gidan 'yan nan ashe kuna ciki" Ta ɗan harareta a fakaice "eh muna nan, lafiya kam?" Ta ƙarasa tana sake kallon Dr. Sulaiman da har yanzu hankalinshi ke kan wayanshi. "Wanchan likitan Afeefah ne mun zo duba ta da jiki" Ta haɗe fuska kan tace "Ina zuwa" Ciki ta koma kafin mommy ta tambayi waye ta shiga ce mata "Mommy wai sun zo duba wanchan Mayyar da yaya salim ya kawo wai likitan ta" Ɗan shiru mommy tayi tana tunanin Allah ya sa ba salim bane ya aiko su, sai kuma ta tuna ai bai ma san halin da take ciki ba, kila ma ya zuwa yanzu ya mance da ita ko ma bai mance da ita ba ta san ba zai taɓa saɓawa umarnin ta ba itama kuma hankalinta ya fi kwanciya a yadda yayi uwar watsi da rayuwar yarinyar yake kuma mu'amala da ita da ƙannenshi lafiya ƙalau. "Tura Talatuwa ta kai su, su suka sani" Ta ɗan zauna kaɗan kan ta miƙe ta nufi ɗakin Talatuwa ta tura ta, Baaba jummai har ta gaji da tsayuwa sai ga Talatuwa, suka gaisa kan tace su tafi ɗakin Afeefar don yadda ta gantan nan ta tabbatar ba za ta iya fitowa ba, Dr. Sulaiman Baaba ta yiwa magana ya bi bayansu har ɗakin da Afeefar take su biyu ya bari suka fara shiga, Baaba jummai na ta sallalamin yadda ta gantan kan ta fito ta kira Sulaiman cikin sauri "Alhaji ƙarami zo ka ga yarinyar nan jiki babu daaɗi sam" Ita kaman uwa take wurinsu don gabanta aka haife shi har ya girma tana gidan su, kuma shine babba a yadda ya ɗauke ta kaman uwa haka ƙannenshi suka tashi suka gani su ma kuma suka yi following footsteps ɗin shi a girmama ta, shiga dakin yayi ya isa gabanta ya duƙa. "Afeefah" Ta amsa da "uhmm" ba tare da ta buɗe idanunta ba. "Menene yake miki ciwo?" Ta Nuna mishi kanta da kaman zai tsage. "Akwai amai?" Ta girgiza kai. "Jiri fa?" Ta gyaɗa kai. "Mura fa da tari?" Nan ma ta gyaɗa kai, plate na abincinta na safen da ke rufe a gefe ya buɗe ko spoon ɗaya bata yi ba. Ledojin da ya shigo dasu a hannunshi ya shiga buɗewa babu bukatar zuwa asibiti drip ya haɗa ya ɗaura mata ya haɗa allurai yayi wasu a jikin canular wasu kuma jikin ruwan, ya dubi Talatuwa "Kin san magungunan da suka shafi na mura da zazzabi da sa bacci, bare ma jininta ya yi ƙasa sossai tana ɗan buƙatar hutu na kwana biyu ba tare da ta yi hulda da ruwa ko abu mai sanyi ba" "Toh fa, ranka ya daɗe ni ma 'yar aiki ce kamar ta ba ni da ikon bata hutu da dai Hajiya da kanta ka yi wa bayanin da sai ya fi" Ita dai Baaba jummai ta zabga tagumi tana kallon Afeefah dake bacci ji take kaman ta yi mata kuka ashe itama aikatau take yi gidan su Saleem ɗin? Muryar Sulaiman ne ya katse ta yana cewa Talatuwa "ko za ki kai ni wurin hajiyar?" Duk da basu yi haka da Saleem ba amma ba zai iya kau da ido a kan yarinyar ba she's too young and fragile kaman she's having a lot a cikin zuciyarta. Fitowa suka yi Baaba dai kaman ta tsaya haka take ji Don Allah ya saka mata ƙauna da tausayin Afeefah kaman jikar ta. Talatuwa ta duƙa gaban mommy bayan ta bar su a waje "Hajiya da ma wai likitan ne yake son gani ki". Kan mommy ta yi magana ma sameera tayi saurin cewa "Ki ce ya shigo, mommy bari na ba ki mayafi" Samha ta ɗago ta kalleta, mommyn bata ce komai ba har sameerah ta kawo mata mayafin daidai Sulaiman ya yi sallama ya shigo. Kamshinshi ne ya cika parlorn duk yadda mommy ta so ta kame nagartarshi da kwarjininshi ya sa ta shiga mishi sannu da zuwa a dole, gaisheta ya shiga yi cikin girmamawa bayan sun gama Sameerah ta shiga gaishe shi, ya amsa da murmushi saman fuskanshi dole Samha itama ta gaishe shi itama ya amsa mata kan ya dubi mommy "Da ma akan patient ɗi ta Afeefah na nemi ganin ki Hajiya, na zo duba jikinta don ganin lokacin komawarta checkup ya yi ban ganta ba sai na samu ashe tana kwance rip da zazzabi mura da kuma low BP da ya addabe ta" Mommyn ta yi kaman bata san bata da lafiya ba tace "Asshaa ka ga aikin rashin wayaun Afeefar ko? Babu fa wanda ta sanar wa bata da lafiya, mutum kullum a maƙale a ɗaki ya ba za'a yi zazzabi ya dame shi ba? Allah dai ya kyauta" Sulaiman ya ɗan murmusa don wannan ba hujja bace a gareshi idan kai ka kula da mutum ba lafiya ba sai ka jira ya gaya maka ba, haka kuma idan baka ji mutum ba ana dai zaune tare kai ke da alhakin leƙa wa ka ji shin yana lafiya? "Ai duk alamun rashin lafiyar ne Hajiya, a likitance duk wadda ba ya son interracting da kowa ya fi gane kaɗaici da rashin magana yana shiga ƙuncin ko damuwa duk akwai alamar tambaya kanshi, Don Allah a taya mu kula da ita idan tana samun kulawa in No time za ta ji sauƙi ta komawa aikinta in Shaa Allah" Sameera ta riga mommy magana "In shaa Allahu Dr. Za mu yi duk yadda ka ce Allah ya bata lafiya" Yayi mata murmushi kan ya amsa da Ameen itama dai fuskar nan cike da fara'a take ta kallonshi. Mommy ta ce "Ba na son ka faɗawa Salim, ka ga yana wurin aiki kar ya zaci ba ma saka ido ne a kanta duk hankalinshi ya tashi, bills ɗin ka dinga turomin zan ke covering" Ya gyaɗa kai kawai yana kokarin Miƙewa Sameera tace "Ko ruwa baka tsaya ka sha ba?" Ya ce "No na gode, ai daga gida na fito" Daga an suka fice suka bar su. Wayanshi ya zare bayan ya yiwa motar tashi key ya ɗan zubawa Layin salim ido yana nazarin abin da ke faruwa, Salim ya ce kar mamanshi ta san shi ya turo su, mamansu ta ce kar salim ya san Afeefah bata da lafiya to me kenan? Ɗan shrugging Kafada yayi kan ya danna ƙiran salim yana ficewa daga harabar gidan, kaman jira ko ringing na farko bai yi ba salim ya ɗaga "Ya ya jikin nata Dr.? Is it worst? Sai an tafi hoapital ko?" "Calm down Captain jikin da sauƙi" Nan ya shiga koro mishi bayanin yadda suka yi da mommyn. Numfashi ya sauƙe bai wani ji damuwarshi ya ragu ba don ya san da matuƙar wuya su bi ta kanta, roƙon Sulaiman yayi da akan ya dinga zuwa yana duba masa ita kaman yadda yayi alkawari. Yana dan murmushi yace "ba ka da matsala in shaa Allahu" "Thank you so very much Doctor" "Ɗo not mention" Daga nan suka ajiye wayar. "Oh ashe wannan baiwar Allahn aiki take gidan su salim ɗin?" Baaba tayi maganan da alama dai har yanzu tana jimamin yadda suka tafi suka bar Afeefah ɗin. "Ni ma sai yau nake fahimtar hakan Baaba, kaman kuma mutanen gidan ba su ɗauki ma'aikatan su da muhimmanci ba" Ta ɗan juya kai cikin manyanta tace "ko kuma ita Afeefar ce ba su ɗauke ta mutum ba ba" Ajiyar zuciya ya sauƙe daga nan bai sake magana ba itama haka har suka isa gida, ta sauka kenan yana shirin ƙarasar da motan parking space ta juyo ta kira shi "Alhj ƙarami Don Allah idan za ka koma da dare ko ban bi ka ba zan baka kunun gyaɗa ka kai mata kila ta iya shan shi" Ya amsa da "Toh Baaba Allah ya kaimu dare ɗin" Ya ƙarasa da motan yayi parking kan ya nufi cikin gidan shi ma don bashi da aiki da safen sai dare za shi asibitin ya kwana, Salim ne ya fitar dashi dole. Da misalin ƙarfe bakwai na dare ya fito a shirye tsaf cikin kananun kaya da suka amshi kalarshi na baƙi, skin ɗin shi da yake kalkalewa tamkar mace sai shining yake don shi mutum ne mai tsananin tsafta, hannun shi rike da ninkakken labcoat ɗin shi, mahaifiyarshi Hajiya Amina da ke zaune cikin kujera ta ɗaga kai ta kalleshi "An fito kenan bokan Turai?" Yayi murmushi yana furta "Eh umma zan fara bi gidan su saleem akwai patient da zan duba kan na wuce asibitin" "A'ah ko dai wacce Baaba jummai ke ta jajenta tun safe?" "Ita fa Umma da safe mun fita kina bacci, ko da na dawo ban leƙo ba ashe Baaba kam tayi ta baki labarin Afeefah" Tana murmushi tace "Ai ina ga zuwa yanzu kowa ya san labarinta a gidan nan, Allah ubangiji ya bata lafiya. Sai ka leƙa kitchen ta yi mata kunu da ferfesu ka karɓa ka tafi mata dashi" Yayi murmushi kan ya amsa yana nufan kitchen ɗin baabar tana side ɗin su bai neme ta bane saboda ba gida zai dawo ba daga chan asibiti zai wuce shiyasa ma bai ba kanshi wahalar neman ta ba don sai yayi mata dogon bayani da kyar ta fahimce shi, kwando ne mai kyau da tsari ta shirya mata komai ciki, ya dauka kawai ya fito yana yi wa Ummarshi sallama take sanar mishi Abban su yace ta sanar mishi lallai lallai yana son ganinshi da safe saboda kullum a saɓani suke. Ko da ya isa gidan su saleem a mota ya cigaba da zama yana tunanin yadda zai nemi iso don bai ga gilmawan kowa ba, sai time yake dubawa ganin zai iya makara ya sa ya sauka ya nufi mudi dake zaune bakin gate da iliya. "Assalamu Alaikum warahmatullah" Yayi musu sallamar yana sake miƙa mishi hannu duk da sun gaisa Shigowar shi "Don Allah ku dan yi haƙuri zan shiga lokacin aikin ku, Afeefah nake son gani ko za ka min iso?" Shiru suka yi cikin tunanin wacece ma Afeefah a gidan, a tare suka tuna ta sai suka kalli juna suna zazzaro ido, mudi ya ce "A'a malam sai dai ko in nema maka Talatuwa ta maka iso amma mu kam magana ma da wacce ka ambata ya haramta tsakanin mu har Abada" Ya ƙarasa cikin yanayin jimami da tabbatarwa iliya ma na gyaɗa kai tabbacin hakan ne. "Magana ya taɓa haramtuwa tsakanin musulmi da musulmi kuwa Malam mai gadi?" Yayi maganan yana ɗan dariyar yadda suke reacting. "Kai dai in ana sallah ba'a magana" Iliya ya faɗa, tuni mudi ya nufi ciki ta baya ya bi ya tsaya daga kofan mashigan kitchen ɗin "Talatuwa akwai wadda ke neman iso wurin yarinyar nan mai wanke-wanke zo ki ji da shi" Sameera da ke shigowa kitchen ɗin ta ɗan yi jimmm kan tace "Talatuwa ci gaba da aikin bari na je" Da kallo Talatuwa ta bi ta har ta ɓace, sai da ta koma ɗaki ta dubi kanta ta kuma ƙara turare kan ta fito ta nufi waje, Sulaiman na ta bugar cikinsu don ya ji dalilin rashin mata magana kuma wai na har abada dole ya sa suka shiga bashi labarin abin da saleem yayi musu, Sossai Sulaiman ke dariya... Tahowar Sameera ta wani zuba mishi idanu tana tsintar kanta da murmushi. Kallon farko da ta mishi ya tafi da imaninta, ya shiga ranta fiye da yadda tarin samarin da suke bibiyar ta, a yanzu da ta ci karo da shi yana dariyar nan kuma sai taji tana narkewa, zuciyarta na wani irin macewa a kanshi, ganinta ya sa ya tsagaita dariyar shi, ta shiga gaishe shi ya amsa yana murmushi "Whats so funny haka Dr.?" "Ki bari kawai ni da su mudi ne, zan iya shiga?" Ta ɗan yi farrr "Sauri kake haka?" Ya ɗan duba time a agogon dake ɗaure bisa tsintsiyar hannun shi "Kusan hakan don kaman na shiga lokacin aikina" Ya ƙarasa yana nufar mota, ta bishi suka jera. "Ai ma kuna ƙoƙari SLT nake karantawa amma ji nake kaman na gudu bare likitance da aikinshi" Ya ɗan yi dariya bai ce komai ba, ta tsaya tana kallonshi har ya buɗe booth ya ɗauki kyakyawar basjet da Baaba jummai ta shirya mata kunu da ferfesu ɗin kayan ciki da suka nuna suka yi tuɓus cike da kayan kamshi, ganin basket ɗin sai da ya ba Sameera haushi amma ta danne, ta sake ganin ƙatuwar leda sai zuciyarta ya shiga tambayarta Anya alaƙar nan na likita da marar lafiya ne ko akwai abin da bata sani ba? Amma me Afeefah take dashi da guy irin Sulaiman zai so ta? Dukda haka zuciyarta bai huta da bugun tara-tara ba, kar dai ta faɗa soyayyar abin da ba za ta samu ba, ji tayi bata da ƙwarin gwiwar bin shi don tabbas matukar ta bishi ta fahimci akwai alaqa tsakaninsu zuciyarta zai iya bugawa ko ta shaƙe yarinyar har lahira, ba za ta iya bin shi ba sam bata da ƙwarin gwiwar. Ta manta cewa kwata-kwata ma yau ne ta fara ganinshi har da zaƙewa haka, wayar ƙarya ta ƙirƙira ya ɗan kalleta "Ka je Dr zan sameka" Tana kai nan ta juya tana cigaba da magana a ƙarya, shi kam bai damu ba ya nufi ɗakin Afeefah ɗin a kan varender ya tsaya yayi knocking, a jiran da ya ɗan yi ya fahimci maza ne cikin ainihin Boys quaters ɗin don ga wani murya na waya, kuma shine aka ajiye mace tare da su? Sam tsarin bai mishi ba... Anan ne kuma ya shiga tuna hirar su iliya sai ya fahimci

Chapter 8 of 40