Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Wayen da zata ci buki dasu wayen da za,a kai ɗinki,daga cikin kayan lefen ta.Kasancewar Mama Haɗiyar tace a ajiye mata lefen ta gida.Ajiye yar madaidaiciyar wayar da ya sai ma ta tayi ƙirar Itel pop 2 tana sakin murmushi tare da rungume yar uwar Tata duk da ba zatar da lamarin ya zo mata.Raba jikin ta tayi da nata tana nuna mata screen ɗin wayar ta ta kafin tace " Lefe na ne,da aka kawo yanzu ". Murmushi Raliya tayi har haƙoran ta na bayyana sai dai jikin ta yayi sanyi da lamarin Yayar ta ta Lamarin kamar harda ƙarya a cikin sa ta gefen Angon shi kan sa duk da a cikin su babu wanda ya san shi itadah mahaifiyar ta.Su Mama Hafsatu ka kiɗin su suke rawar su ta zancen lefen sai dai gwargwado mama Hasiya na ta yin hidimar a duka su biyu ta san cewa duk inda za,a je a dawo Ita ce ta yi Na ƙudar Nadiya kuma duk wanda zai zo gurin ta a su biyu zai zo bikin dan taya ta murna. Jiki a saɓule tayi mata Allah ya sanya Albarka.Bayan ta gama ƙarewa kayan kallo.Ita kan ta Najiba jikin na ta yayi sanyi Ganin yadda yar uwar Tata tayi sai dai farin cikin da take ciki ya hana ta tambaye ta dalili wanda ta ke jin bai ma da na saba da Nata lefen.Mama Hasiya dake tsaye bakin ƙofar ta domin tun ɗazu ta fito tana son ganin kayan da Raliya ta sanar mata Ibrahim ɗin ya Turo mata.Ajiyar zuciya ta share kafin ta ƙaraso cikin falon tana bin su da kallo babu ma kamar Raliya da jikin ta ke nuna tayi wani irin sanyi idanun ta har sun ɗan sauya wani irin tsoro ke shigar ta fatan ta Allah ya sa ba ɗan ƙarya Yayar ta ta haɗu dashi irin ta ba,fatan ta Allah ya sa babu yaudara cikin lamarin na yar uwar ta mafi soyuwa agare ta .Ajiyar zuciya ta sauke Ahankali bayan zaman Mama Hasiya akusa da ita.Tana riƙo hannayen ta. Hmmm RALIYA ai kuma sai dai kar a ƙara,kura taci kura.🧐🥺 Najiba dake tsaye daburcewa tayi bayan haɗa idanun da tayi da mahaifiyar ta inda take wasu irin hawaye suka silalo mata tana son furta sunan mahaifiyar ta ta da suke kira da umma.Sai dai ta kasa hakan ya sa ta juya da sauri ta bar falon idanun ta na cika da hawaye ma su zafi.Wayen da bata san dalilin zubar su ba. Wayyo NAJ 😭😭 Anya babu Naj Akwai lafiya alamarin ki🤔 Me kuke tunanin Mama Hafsatu ke ƙoƙarin shiryawa🤔🤥 HMMMM Daga Alƙalamin ✍️ fa'eeh bg An samu long page. Idan har naga react da yawa zan yi muku typing next page a take. Idan babu kuma zan huta sai kuma lokacin da nake yin sa. Like share and react,vote pls 🙏 https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y _*Follow for more update.*_👆🏾👆🏾 *🌸RAYUWAR MU AYAU🌸* Ƙarya ko sakin Aure Short story Labari da rubutawa Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _*Daga marubuciyar littafin*_ _*A Mafarki Nasanta*_✍️ P.12 Hawaye Najiba ta share bayan shigar ta ɗakin kafin wani irin kuka ya kubce mata mai ƙona zuciya.Ta rasa farin cikin da take ji gaba ɗaya lokaci ɗaya. Da idanu duk suka bi ta.Kafin a hankali hawaye suka fara kwaranya a kan fuskar Raliya musamman jin yadda mahaifiyar su ta sauke Ajiyar zuciya a yanzun. Wani irin Tausayin Najiba ne ya kamata wanda ya ke tsarga dukkanin jinin jikin ta. Hankalin ta yana ɗagawa da lamarin Najiba. " Umma,kin ga Yaya Najiba,kuka take yi ". Raliya ta furta jikin ta asanyaye tana ƙoƙarin share wasu irin hawaye dake neman kubce mata. " Me ta nuna Miki ".? " Umma " Ta furta tana kallon Raliya ɗin. "Lefen ta ". Ta bata Amsa. Numfashi Mama Hasiya ta sauke kafin ta saki Murmushi wanda ya zo mata haka kawai. Amma Najiba ta san cewe murmushi ne da ya fi kuka ciwo. " Allah ya sanya Alkhairi ". Mama Hasiya ta furta a hankali. Kafin ta ƙara kallon Hannayen Raliya ɗin tana furta. " ki daina saka damuwa kinji akan yar uwar ki,mu cigaba da Addu,a kawai,in sha ALLAH komai zai zo ya wuce ". Kai Raliya ta gyaɗa mata kafin shanye Hawayen ta da suke neman silalowa idanun ta na Tausayin Mahaifiyar ta. Wayar ta ta miƙa mata tana furta " Umma,ga kayan ki gani ''. Murmushi mama Hasiya tayi, ta saka Albarka ganin irin ƙoƙarin da Ibrahim ɗin yayi. " Sunyi kyau Allah ya biya ". Ta furta tana kallon Raliya dake ɗan fitar da siririn murmushi. " Amin ". Ta furta itama tana sunne kan ta ƙasa. Miƙewa tayi tana furta. " bari inje in haɗa Miki maganin ki na sanyi naga kamar kin shanye wanchan ko." Kai Raliya ta ƙara sunnewa a ƙasa tana gyaɗa kan ta dan tana da kunya sosai maganin ya ƙare tun jiya tana jin kunya ne ta mata maganar shi.. Ɗakin ta ta shige tana sakin murmushi tare da ƙara ƙaunar yar ta Duk da gefe ɗaya tausayin Najiba na ƙara ratsa zuciyar ta da ƙaunar ta. A ɓangaren Su Nadiya kuwa kasancewar za,a kawo kayan ta itama a nan gidan su sai bata biyo Mama Hafsatu ba da wasu daga cikin manyan ƙawayen Hajiya Samira ɗin da suka zo Dan yi mata kara. Tunda suka shigo gidan, gidan ya hargitse da guɗa kasancewar harda kayan Najiba aka ɗauko aka zo dasu gidan.Inda aka wuce dasu direct ɗakin Mama Hasiya. Mama Hasiya wadda ke cikin ɗaki taji guɗa abun ya bata mamaki sai dai kuma ta Shanye mamakin ta ta tarbe su Hajiya Samira da suka saki fuska aka gai sa da juna duk da ba wani magana suke yi sosai ba dan Tana kama girman ta gare su. Mama Hafsatu dake jin zuciyar ta na wani irin zafi sai dariyar yaƙe take ta saki tana ɗaura fushin ta da baƙin cikin ta a fili saboda harga Allah bata ji daɗin hukuncin Hajiya Samira ba ta so a ce chan ɗakin ta aka kai kayan ita kuwa Hajiya Samira da ta ga dacewar a miƙa kaya hannun uwar ɗiya ko a jikin ta hakan ya sa ta saki jikin ta suka gaisa inda ta gabatar mata da kayan na Najiba dake ta ɗaukar idanu. Mama Hasiya bata nuna komai ba sai ma ɗan farin ciki da ta ɗaura akan fuskar ta cikin wani irin farin ciki dake mamaye ta haka kawai na yadda Hajiya Samira ta nuna mata itace uwar ɗiya ita ke da iko da ita. Ɗakin Mama Hafsatu suka koma wasun su na yatsinar fuska ba kamar yadda suka zauna a ɗakin Mama Hasiya ba.Da suka saki jiki sosai saboda yadda ko ina yake ƙal dashi a tsaftace. Suna a haka suka fara jin dirar manyan motoci Masu rai da lafiya a ƙofar gidan.Sai kuma.a hankali guɗa ta fara karaɗe cikin gidan. Manyan mata ne da suka amsa sunan su suka fara shigowa cikin gidan suna ya ƙunar fuska da bin ko ina da mugun kallo kamar sun ga kashi.Fuskokin su kuwa na nuna wani irin ɓacin rai a take da ganin wautar ƙanen na su da ya rasa inda zai nemi Aure sai a gidan ƙananan mutane irin wayen nan.Ƙofar ɗakin Mama Hasiya suka nufa da kayan da yake tsaff dashi sai dai fitowa suka yi bayan ta sanar musu ba nan ne za su kai kayan ba inda ta nuna musu ɗayan ɗakin. Haka suka yi sallama kamar ba zasu yi suna cigaba da ya ƙunar fuska inda guɗa kuma take ɗan ɗagawa a hankali.Cikin ɗakin suka shiga da aka ɗan ƙara gyara shi inji Mama Hasiya ɗin. Haka suka samu guri suka yi cirko cirko kamar wasu gunkunaye,duk da an tarbe su dai dai sun kasa zama saboda ƙyama da abinda na talaka da Mai kuɗi. kafin a hankali aka fara shigowa da kayan inda basu dakata ba sai da suka zube set na akwati kusan set huɗu sannan suka dakata.Haka Su Hajiya Samira suka ƙara haɗe gurin da guɗa.Ganin uban kayan da aka zube kamar wani shago komai na masu kuɗi da suka amsa kuɗin su. Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar Mama Hafsatu da ke ganin komai kamar a mafarki.Babu ma abun ƙarin farin cikin ta irin ganin yadda aka zuba gwala-gwalai tana jin yadda Hajiya Samira ke yabon su da furta tsadddun gaske ne. Suko dangin Tanim da suka gama zube kayan cikin jin haushin inda suka zube kayan su,Suka yi musu sallama suka wuce duk yadda Aka basu snacks da sauran soye soyen da aka yi sun ƙi karɓa dan sun nuna afili sun fi ƙarfin komai na gidan. Haka suka wuce ƙarshe ma dai Hajiya Samira tace a share su dan itama ba baya ba rashin mutun ci. Haka suka wuce da magana ƙunshe abakunan su.Suna Mamakin yadda akayi Tanim ya shigo irin wayen nan ghetto area ɗin neman Aure kuma ya sani ya bar su suka kashe maƙudan kudaɗe. Har suka isa gidan na su zuciyar su na yin wani irin zafi da baƙin ciki. Haka maƙota ma suka fara shigowa suma idan suka duba na Najiba sai su shiga su duba na Nadiya su fita suna santi da mamakin wayen nan kaya kamar su Mama Hasiya sun sayar da Yaran na su. Najiba da duk take bin kowa da idanu wadda ta fito bayan ta gama shan kukan ta ta fito jin yayaa tayi yawa hakan ya sa ta fito jin guɗa na neman fasa mata kunne. Kayan da ta gani take ta kallo ta na furta Masha ALLAH cikin ranta Dan ta san kayan kona waye saboda tana jin komai dake faruwa. Komawa tayi cikin ɗakin tana jin zuciyar ta ba daɗi saboda mahaifiyar ta datake son tayi magana ita sai dai tana ji tana gani ta kasa wanda bata san dalilin kasa wa ba. Haka su Hajiya Samira suka watse suka yi gida da zummar idan an gama ganin kayan Sai akwashe Amaryar gidan Hajiya Samira dan yafi safe gudun ɓata gari musamman da aka ga irin uwayen kayan da aka shigo dasu. Su Malam Rabu,U dake waje basu fahimci komai ba sai dai sun yi zaton kayan Najiba ne da suka san Jamil iyayen sa masu hali ne.Abun ya ba su tsoro matuka yadda suka ga ana shiga da manyan Set haɗaɗɗun trolley bags da kuɗi ke magana a cikin saboda Koda su Hajiya Samira suka shiga da na Najiba basu kusa sun ɗan zaga wata jana'iza ta wani bawan Allah da ya rasu a bayan layin su.Shiya sa basu ga wucewar su da kayan na ta ba. Har mutanen suka wuce kuwa basu gama mamaki da jimanin wayen nan kayan ba da ko a mafarki ba su taɓa tunanin akawo wa ɗai daga cikin ya'yan su su ba. Jamil kuwa zuciyar shi a cunkushe take shiya sa ya tura mata da text na ban haƙuri na rashin saka mata key na mota da yayi mata alƙawari yana nuna mata bata iso ba daga ƙasar da akayi order ɗin ta wanda wannan shawarar ta Gariti ce dan shi kan shi duka ya kulle masa,Haka Najiba kuma cikin ikon ALLAH ta fahimce shi ta nuna babu komai tare da yi masa godiyar kayan da aka zubo mata wanda har ga Allah sun burge ta. Jamil kuwa da ke sauraren ta tausayi ta bashi wanda yaji guwawoyin sa sun sage lokaci ɗaya yana hango yadda gaba zata kasance musu shida ita.Sai dai bashi da zaɓin cigaba da Aron jarunta ya ɗaura ma kan sa... A haka aka cigaba da hidimar bikin sai dai maganar lefe Sun fahimci akwai wani abu aƙasa kasancewar Mama Hasiya ta nuna musu na Najiba da aka kawo bada yawun ta ba bare mahaifin ta Wanda basu da wani zaɓi sai na karɓar su tare da bin su da Allah ya sanya Alkhairi. Abun da ya fara ɗaure musu kai shine lefen Nadiya da suke tunanin inda malam Sayyid ya samu kuɗin sayen su sai dai kuma lamarin hankali mai cike da hankali Bazai ɗauki zancen ba musamman ma ganin dan ƙara danƙaran motocin da aka kawo kayan dasu masu kyau har wani numfashi suke yi. Sai dai duk da yadda suke cike da mamaki basu maganta ba dan kamar an matsi bakunan su basu furta ko tambayar komai ba ga Mama Hafsatu ɗin harda Shi kan shi Angon. Hmmmm Ashe akwai kallo kuwa. Na taɓa ganin wannan rigima mai kawo lefe daban Ango da ban,shin ya abun yake ne.?🤔 Gaskiya akwai abinda Mama Hafsatu ke shiryawa.🥱🤥 Ba yawa a yi haƙuri Chaji ya min cikass.✍️🙏 Daga Alƙalamin✍️ Fa'eehbg 👑Gimbiyar taskira👑 https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *🌸RAYUWAR MU AYAU🌸* Ƙarya ko sakin Aure Short story Labari da rubutawa Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _*Daga marubuciyar littafin*_ _*A Mafarki Nasanta*_✍️ *# Najmil* *# Nadnim* *# Marriage* P.13 Hidima ta kan kama ta kowa ne gefe Amare da ƙawayen su kuwa an yi ladies party wanda ya haɗa manyan ya yan masu kuɗi da aka gayyato kasancewar Babban event center suka gudanar da shi wanda Tanim ne ya shige gaba kan lamarin.Sun so ace angwayen sun je sai dai sun nuna basa ra'ayi kaitsaye wanda basu san dalilin hakan ba.Sun dai barshi a bakin basu ra'ayin wanda Kowannen su nada dalilin sa mai ƙarfi. Duk wannan bidirin da ake yi kuwa Raliya bata taka ba hasali ma ɓoyewa tayi kasancewar bazata iya cewa yayar ta bata zuwa ba saboda harda ita suka yi ɗinki iri ɗaya. Duk wani abu da ya dace anyi na Shagalin bikin inda suka yi tarurruka masu armashi da tsayawa a zuciyar mai kallo domin sun zubar da kuɗi wayen da angwayen suka ba su,Duk da ma jamilu da ƙyar yafita kunya dan yan kuɗin da aka basu ne na Toshi ya haɗa ya ranto kusan dubu ɗari tara ya haɗa ya ba Najiba miliyan ɗaya. Wahala🤥🥺😁Jamil ka ɗebowa kan ka da yawa. Aiko Najiba aka yi ta busha busha da kuɗi. Rana bata karya sai dai uwar ɗiya tayi kunya inji ba haushe.Yau ta kasance asabar ranar da ta zamo ta ɗaurin auren su ko ina ka duba yan uwa da abokan nan arziki gasu nan ana ta shige da fice a ɗan zagayen gidan da ɗakunan iyayen na su dangin su sun kawo jiki Daga Jigawa wayen da suka ɗan yi musu saura a chan. Kowa ka kalla ya chaɓa ado na Musamman,gwargwado,babu ma kamar Mama Hasiya da yau asalin ta na cikakkiyar bafulatana ya bayyana tayi kyawun ta fuskar ta shar sai kai kawo take yi.Haka ma Mama Hafsatu an shirya tsaff anyi kyau itama sai buɗawa akai musamman da ta fahimci leshin ta yaci uban na Mama Hasiya da yake da yan madaidaitan kuɗi wanda ta ɗinkawa kan ta.Ita kuma Mama Hafsatu Tanim ne ya aiko mata da nata ɗinkakku tsaff da su har da iyayen nasu ma Maza sai dai An ɓoye musu wanda ya basu kayan sai dai aka sanar dasu Alhaji Ahmed ne kuma ya ce baya son godiya. Haka suka karɓa suna ta murna kuma ayau suka chaɓa ado da su ganin ba ƙananan kaya bane,duk da sun ɗinka na su suma.gwargwadon hali na talaka. A chan Masallacin da za'ayi Ɗaurin Aure ya kan kama sai dai Ɗaurin Aure ɗaya ya shayar da mutane ɗinbin mamaki sanin ba shi ne asalin Angon da sunan shi yayi yawo a Invitation card ba.Abun da ya faru kuwa shine komai ya sauya Dan ana gaf da ɗaurin Auren Nadiya wanda itace ta ƙarshe sai ga Kira Ya Sayyid ya samu daga mahaifin sa wanda ya fita yanzu bayan kiran wayar sa da aka yi.Yana fita kuma a hankali dukkanin wakilan sa suka sulale kamar dama chan jira suke yi bayan samun kiran da suka yi suma daga mahaifin na sa.Ganin hakan yasa liman ya daka ta.Inda aka ce uzuri ya ɗagar da su abasu nan da yan mintinan zasu dawo.Haka kuwa aka yi har lokacin da aka ɗibar musu yayi kuma a dai dai lokacin ne wasu irin manyan motoci na Alfarma suka faka a bakin masallacin inda jama'ar dake cikin masallacin suka fara fitowa a jere cikin shigar Alfarma kamar yanayin shaddar su Malam Abdul basiɗ.Alhaji Ahmad da ya san komai ayanzu ya miƙe cikin sakin fuska ya miƙa wanda yake ya san komai sannan ya san Alhaji Abdulkarim farin sani a wajen kasuwancin su.Kuma suna gaisuwar mutunci sosai da juna.Dan Har abota suka fara sai dai rashin zama waje ɗaya kuma Kasuwancin na su ya banbanta duk da hakan nan kuma suna communication through waya. Gaisawa sukayi inda yayi musu iso kafin ya fara gabatar musu da Alhaji Abdul karim amatsayin Mahaifin Tanim wanda kuma koda bai yi bayani ba sun san shi dan sun yi bincike kan shi da yaron na sa.Sai dai abin ya ba su mamaki ganin shi tare da yaron na sa da yake ta kallon kowa idanu tsaitsaye kamar wani ɗan hau.Ga wani irin ɗan sauyawa da idanun sa suka yi kamar mai kurkura wani abu ko wanda yake buge. Zama suka yi inda ya matsa kusa da su Malam Rabu'u suka Gaisa a sake kafin kuma suka koma gefe suka yi wata yar magana tare da Malam Amiru Da Adamu da suka saka amatsayin wakilan Auren da kuma Alhaji Ahmed da Hajiya Samira tace ya yi ruwa yayi gishiri aciki ya tsayu ganin An ɗaura Auren Tanim da Nadiya wanda ta yi hakan ne saboda matsi.da roƙon da ta ke samu Agurin Mama Hafsatu wanda kuma duk da wannan matsin ba haka kawai Mama Hafstu ke wannan shige da ficen ba.Ta raba hankali biyu ne kamar yadda aka bata umurni. Yanke shawarar kiran wayar malam Sayyid suka yi sai dai ba'a ɗaga ba haka ma ta mahaifin sa ba,a ɗaga ba mai da akaalar kiran aka yi a Layin da ya kasance na ɗai daga cikin yayyen sa cikin ikon Allah kira da suka yi ya shiga.Inda ya ɗaga wayar ranshi kamar ɓace bai ko jira anyi sallama ba ya fara Masifa yana furta. " An fasa,kawai ku Aura mata mai kuɗin da kuka yi ra'ayi,Allah ya tabbatar da alkhairi,ya basu zaman lafiya,kuma duk wanda yayi sanadin mutuwar mahaifiyar mu sai munyi Shari'a dashi,Azzaluman mutane,maciya amana ". Daga haka kawai Malam Adamu yaji hakan ya sa ya ƙara kira dan tabbatar da abun da yaji a cikin Kunnuwan sa sai dai kiran baya tafiya da alama an kashe wayar ko an saka ta Blacklist ko Planemode.Numfashi ya sauke kafin ya dubi malam Rabu'u da Malam Abdul basiɗ dake jin kan sa na wata irin sara Mishi haka ma gaban shi wani irin faɗuwa yake yi ba gaira ba dalili. " Bamu da zaɓi sai na basu wannan Auren,Amma ban sani ba ko kuna da abun cewa malam Rabu'u,tun da sun nuna a fili suna so,kuma yau da gobe yaro ƙila ya samu shiriya ta sanadin ta ". Alhaji Ahmad ya furta wanda shi kan shi bai san yadda akayi yake fito da zancen ba.Haka ma Cikin jimami malam Amiru take ya goyi bayan Auren.Malan Rabu'u ma bai da ta cewa duk da wani irin sanyi da jikin sa yayi.Malan Abdul Basiɗ kuwa numfashi kawai ya sauke kafin yaja wani gauro numfashi da yake jin ya taushe Mishi wuya sannan ya furta " Allah ya tabbatar da alkhairi ".Iya abinda ya iya furtawa kenan kafin ya ji bakin sa ya rufe ruff ta har aka gama ɗaurin kai ne kaɗai yake iya jinjinawa ga jama'a. Haka aka ɗaura Auren Nadiya Abdul Basiɗ Da Angon ta Tanim Abdul karim. Kamar yadda aka ɗaura Na Najiba Rabu'u da Angon ta Jamilu Tahir.Da kuma Raliya Rabu'u da Angon ta Ibrahim Muhammad. Haka taro ya watse jama'a na ta jimamin wasu harda zagin su malam Abdul basiɗ kasancewar babu wanda ya san abinda ke faruwa sai dai sunga ana ta shige da fice a cikin masallacin. Farin cike ne ya ƙara mamaye zuciya da fuskar mama Hasiya sai dai ta wani gefen ƙirjin ta kan ɗaga mata wanda ta rasa dalili tun bayan jin cewa an ɗaura Auren ya'yan ta guda biyu da take kallo hasken Rayuwar ta Hamdala tayi wanda sai da ta zubar da ƙwalla tare da bin su da addu,ar samun zaman lafiya mai ɗaurewa.. A ɓangaren Mama Hafsatu kuwa cikin wani farin ciki ta furta " Sai ba kai ba Na bakin lahira aikin ka dubu ba ko ɗaya da ke tafiya banza,Charbin ka sittin duban su na alkhairi ne ".Ta kai ƙarshen zancen tana sakin ƙaramar dariya kasancewar ita kaɗai ce a cikin ɗakin na ta ayanzu duk suna Falo. Zuciyar ta kuwa fess farin ciki yar ta ta samu abun da take so itama haka, ta samu, su da talauci har anaɗe duniya itadah yar ta da ma wani mai ƙashin lasa adangin nasu Duk da kuwa ta san dama abinda zai kasance kenan ta riga ta shirya komai da zuwan sa ta san ta gama aiwatar da shirin ta kamar yadda ta shirya.. Haka tayi ta saƙawa tana warwarewa idan Nadiya ta haihu a gidan Tanim.ya lamarin zai kasance kenan sune da gado sai wani irin farin ciki ya kamata tana Auna zancen ire iren wannan tunanin ta ke yi har ta gama ta dawo Falon tana wasar haƙora labarin ɗaurin Auren na ƙara faɗaɗa Murmushin ta na samun abinda ruhi ke so. Hmmm akwai kallo mama Hafsatu arage zagwaɗi sai kace ke ce Amaryar.🥱 Jama'ar dake ta ma ta Barka take karɓawa,sai dai wayen da suka samu labarin chanjin Auren sunyi mamaki matuƙa dan take gulma ta fara yawo sai dai ta rufe Kunnuwan ta duk da ta na ganin yadda maƙota ke ta sakin ƙananan maganganu ana furta sun ci Amanar Ya Sayyid sun ma ɗiyar su Auren kuɗi da sauran su. A bunda ya faru a lokacin da su ya Sayyid suka bar masallaci. A chan gidan su Ya Sayyid kuma abun da ya faru ba mai daɗi bane domin kuwa wasu irin mata ne Kamar karuwa dasu Mama Hafsatu tayo hayar su ta saka su suka isa har gidan su Ya Sayyid inda suka samu gidan tanƙam abunka da dangi nan take a ka azagaye su ganin irin yanayin da suka shigo dashi sai dai babu wanda ya buɗa baki ya ce musu ƙala an

Chapter 9 of 39