ƙaunar da nake Miki ne ta saka ni na faɗa ga muguwar hanyar ƙarya ina tsoron rasa ki ne ganin ki yar masu kuɗi,wanda Ni ashe rashin sani."...
Rufe masa baki Tayi tana zubar da hawaye tare da girgiza masa kai tana tuno da komai yadda ya faru ta san tabbas laifin ta ne ta yarda ba halin sa bane,ita ma tayi tunanin bazai so ta a talakan ta ba dan ta ga masu kuɗi basa son ya yan talakawa ashe ma suke wahala dukkanin su abu ɗaya,domin talakan da ta ke tsoron Aure shi ta mallaka Lallai Allah azimun ne,Shi yake tsara ma bawan sa ya masa daɗi ko kar ya masa muddin ya san Alkhairiin bawan sa ne,kuma ya kasance bawan mai tsoron sa da tawakkali ne zai dube sa ya masa mafita ya tabbatar da ɗimbin Alkhairi a rayuwar sa,koda Sharri ke tunkarar sa sai ya musanya masa da Alkhairi muddin bawa ya kasance mai roƙon sa domin addu,a na chanza kaddara mara kyau iZuwa mai kyau.Tuna hakan ya sa cikin raunin da zuciyar ta ta ƙara samun kan ta ciki take fatan Allah ya yafe musu gaba ɗayan su kuma ya ganar da masu tafiyar da rayuwar su akan ƙarya.Tana fatan Allah ya kawo wa yar uwar ta Nadiya farin ciki fiye da wanda take ciki.Bayan tuno da ita yanzu.
Ganin ta fashe da kuka kuma.ya sa shi sakin yar dariya yana furta " Bari mu mayar da kyautar muce bamu so tun da kuka zata riƙa saka mini mata oum.zehra ".
Ƙatuwar harara ta cilla masa tana sakin dariya.Murmushi Ya saki kafin ya miƙe da check ɗin ya saka a ljihun wandon sa na jeans da ya koɗe,tare da yar su a hannu yana furta Bari na mata huɗu ba.
Kiran sallah yayi mata tare da duk abin da ya dace,sannan ya kira mata sunan ta da 'Fatima sunan mahaifiyar sa kenan.Haka suka tsara zasu saka mata kamar yadda yake so zasu riƙa kiran ta da Zehra ko zahra.
Yana gamawa yayi mata kiss a goshin ta sannan ya sumbaci leɓen Najiba ya bar ɗakin bayan yayi mata sallama da zummar zuwa sawo abubuwan buƙata. Yana ƙara faɗaɗa fuskar shi da murmushi cikin jin daɗi da farin ciki.
Yana fita nan ya tarar da mahaifiyar sa take ya faɗa mata abun Alkhairin da ya samu har da kuka ta yi tare da yin sujjada ga Ubangiji tana.Mama Hafsatu Hankalin ta ne yayi mugun tashi jin abun da bata taɓa tsammani ba ko gani domin zahiri ta gani,Take zuciyar ta ta fara yi mata lissafin banza.Ta kama wannan ta watsar da wanchan.Da ƙyar da ƙaƙalen murmushi tayi wa Mahaifiyar Jamil murna,da kuma shi kan shi Jamil ɗin.
Haka ma mahaifin sa yayi farin ciki sosai Gariti ma murna kamar ya taka kan jariri Dan ya san samun Jamil nashi ne bai da rowa ko kaɗan ya san su ne da riba suma zasu ci in sha ALLAH.Ba'a abun da yakai samun ɗan uwan ka daɗi musamman idan ya kasance mai Alkhairi.
Allah ya ƙaramuna ƙaunar yan uwan mu,da son kyautata musu.🤲
%%%
A Chan gida ma haka Labarin haihuwar Najiba ya same su inda gida ya kachame da murna,Mama Hasiya harda Hawayen murna,ba dan komai ba sai dan samun rabin kwanciyar hankalin ta domin tun da aka tafi da Najiba take jin ta wani iri gaban ta na mugun faduwa gani take kamar abun da ya faru ga Nadiya shine zai faru kan Najiba wanda kuma ita ba lallai ta sha ba.
Hamdala suka dinga yi itada Nadiya da take jin kamar tayi tsuntsuwa,Haka ma RALIYA da ke ta ƙar fin hali tayi farin ciki sosai sai ta samu kwanciyar hankalin ta da natsuwa,sai dai har yanzu marar na katsa mata ƙarfin hali kawai take yi.A haka aka kwasa suka yi asibitin bayan dangin Tanim sun watse,Har Nadiya da Najiba da akaso hanawa haka suka tafi asibitin cikin farin ciki,take ko labari ya kai Jigawa na haihuwar Najiba kamar yadda na haihuwar Nadiya ya isa dangi na ta murna.
Cikin farin cikin dukkanin su suka zagaye gadon bakin su washe da farin ciki kowa fuskar sa na fitar da annashuwa.Barka suka yi mata tare da Bin ta da Addua,a ita da zehra dan duk sun san sunan tun kafin a haihu take cewa sunan yar ta idan mace ce Fatima zehra idan kuma Namiji ne Abdul Basiɗ.Labarin haihuwar Najiba ya zaga dangin Ibrahim inda suka cika asibiti kowa nata sambar ka tare da bin Jinjira da addu'a mai kyau. Haka suka kasance cikin farin ciki awannan ɗan daƙiƙu.Sai dai wuraren Bayan Magriba suna gab da wucewa Gida har Ibrahim ya zo ɗaukar Raliya Su wuce gida,Abu kamar wasa ta taka ƙafafu suka ƙi motsawa sai baya ya riƙe.Cikin azaba ta kwalla ƙara Ibrahim da har yayi gaba ya dawo lokacin Nadiya har ta kira Nurses cikin kiɗima Dan bata ma zo da Jazlan ba chan ta baro shi ga Mama Hasiya tare da madara wai ba daɗewa zasu yi ba.Sai gasu har magriba.
Haka aka kwashi Raliya sai labour room Dan duk wanda yaga cikin ta ya san yau ko gobe ga shi ƙato da shi kamar cikin yan biyar.Ana shiga da ita Likitota suka hau kan ta ganin bata iya haihuwar su naƙudar taki yuyuwa sai wahala take yi domin Nishin bata iyawa,haka aka bawa Ibrahim da ya kasa tsaye ya kasa zaune hankalin sa tashe ya saka hannu a consent form aka shiga da ita CS saboda wannan hukuncin shi suka yanke Dan ceto rayuwar ta da abun cikin na ta.
Ko kafin a gama fitowa ma gaba ɗaya gurin ya cika da yan uwan Ibrahim da ya kira sannan ya je gida ya kwaso abubuwan da za,a buƙata kamar kayan yara,pad da sauran su.
A chan gida ma Nadiya da ta wuce gidan Badan ta so ba sai dan kukan da ta ji a jikin ta da Jazlan nayi ya sa ta yi musu sallama ta bar Mama Hafsatu da dangin Ibrahim ta wuce sai gashi kuwa tana gabda da isa gida Mama Hasiya ta kira ta ganin Jazlan ɗin yaƙi yin shiru tun yana karɓan rarrrashi har ya kai yanzu baya karɓa gaba ɗaya madarar ma ba ya sha kwata kwata ya hasala.Ta kasa tsaye ta ka sa zaune,haka ma Mama Hasiya tun da Nadiya ta faɗa mata take cikin zullumi sai salloli take ta rafkawa ga wani irin Tausayin Raliya da yake ƙara ratsa ta Dan bata jin Raliya na iya haifar yan biyun dake cikin ta,duk da bata mata zancen ba ita ta hango hakan.Haka ma su Malam Rabu'u sun duƙufa wajen yiwa yayan na su Addu'a Allah ya fitar da su lafiya.Ya sa a wanye lafiya.Shine Addu,ar su da fatan su.
Likitota sun tausaya ma Raliya matuƙa domin taci baƙar azaba saboda yadda abun cikin keta Shure Shure, kafin suka yi nasarar fara ciro ya'yan domin kuwa Yan huɗu ne jere rass a cikin na ta.Haka suka yi ta ciro su ɗaya bayan ɗaya cikin farin ciki da murna Dan suna son ganin irin wannan haihuwar Abar burgewa ce.
Cikin ikon Allah suka ciro su baki ɗaya suna ta challara ƙara macen ɗaya ce ma bata koka ba,tayi shiru sai Numfashin ta dake fita a jere kuma itace ta ƙarshen cirowa.Duk dabarun da Likitotan sukayi baya koka ba sai ma jikin na ta da ya ƙara saki numfashi sama daga nan kuma ya ɗauke baki ɗaya haka suna ji suna gani yarinyar ta koma ga haliccin ta.
Haka suka naɗe ta sannan suka ɗora mata sauran aƙirjin da ɗai ɗaya dan tana jin su sai dai bata da wani ƙarfi kasancewar ba,a yi mata allura ba,Bata san yara nawa aka ciro mata ba sai da aka fara ɗaura mata su ɗaya bayan ɗaya a ƙirjin ta sannan ta fahimci yara nawa ne suka zauna a cikin ta.Duk da likita ya taɓa faɗa mata tana ɗauke da cikin yan biyu bata ɗauki zancen da gaske ba shi yasa bata faɗama mahaifiyar ta ba ko su Najiba.Ashe yan uku ne take ɗauke da su a jikin ta.Tunanin ta ne ya katse bayan ɗaura mata Macen da ta rasu bayan zuwan ta duniya.Hakan ya sa jikin ta fara rawa ganin bata kukan ita gashi kamar babu numfashi a tattare da ita,Hawaye ne suka silalo mata masu zafi domin bata da ƙarfin yin kuka matuƙa hankalin ta ya tashi tana fatan ta tashi kamar Jazlan ɗin Adda Nadiya,Tabbatar mata da suka yi ta rasu ne ya ƙara sanya jikin ta yin sanyi duk da taga alama hawaye ta share masu zafi na wahala da na tausayin Yar ta,wanda suka tabbatar mata da ta sha ruwan naƙuda a binciken da suka yi mata kuma sunyi iya ƙoƙarin su abin yaci tura.Haka aka gyara ta tare da yaran sannan aka kaifa ɗakin Hutu bayan anyi suturing ɗin ta.Kukan zuci Raliya ta koma yi ta kasa mance fuskar Jinjirar da ta kwaso mahaifin ta sak duk da suna kama amma ita ta fi kama da Ibrahim sosai duk da kuma tana kama da yar uwar ta macen su ke yin kama da mahaifin su mazan kuma suke kama da Ita.koda aka fitar da yaran bayan an ƙara dudduba lafiyar su,aka yi waje dasu dan nuna wa dangin abun farin ciki.
Tunda aka bawa Ibrahim Macen guda ɗaya tare da namijin ɗaya sai ɗayan namijin a hannun Ƙanwar Ibrahim bakin shi ya ƙi rufuwa hawaye yake ta tsiyayarwa na farin cikin wannan kyauta da Ubangiji yayi masa,Ƙasa yayi bayan ya miƙa ma su Mama Hafsatu su da suke cikin farin ciki suma, yayi sujudu shukru yayi Hamdala ga Ubangiji cikin yabon sa.Haka ya rungume yaran bayan ya Share Hawayen sa bakin sa har kunne shi kan shi yaji babu daɗi matuƙa kuma ya tausaya wa Raliya,Ganin Jinjirar da aka kawo musu yanzu bata da rai wadda ita kaɗai ce ta zo babu lafiya cikin su.Haka suka kasance cikin jimami tare da godiya ga Ubangiji na baiwar da yayi musu,ɗan Ibrahim shi kan sa yan biyu yayi zato kamar yadda likita ya faɗa sai kuma ga saɓanin haka.Ibrahim har da kyautar manyan kuɗaɗe yayi wa team ɗin da suka karɓi haihuwar RALIYA kyau ta da su masu tsoka.Cikin ƙanƙanin lokaci a sibiti ta ƙara ɗinkewa da yan uwa da abokan arziki ko ina sai ɓullowa suke yi harda wayen da su kan su su Raliya basu sani ba kun san yan biyu da farin jini bare ma a ji yan hudu ne kowa sai albarka yake saka musu tare da bin su da Addu,oi da kyaututtukan masu kyau na burgewa dan tunda aka dawo da Raliya ɗakin Hutu bata samu hutun ba,jama'a ce ta ko ina suke ɓullowa duk da an hana su shiga daga farko ganin yadda suke ta isa ga yaran Amma saboda sanya Albarkar da masu zuwa ganin yaran suke yi sai aka bar kowa ya shiga sai dai ba,a cire su daga kan madaidaicin gadon su dake jere da juna.
Kuka kuwa RALIYA ita da Ibrahim haɗe kai suka yi waje ɗaya ita tana kuka shi yana zubar da wasu hawaye na farin ciki sai na tausayin Yar su da ta koma ba tare da sanin ɗai daga cikin su ba bare yan uwan ta da suka zauna mahaifa ɗaya.Kuka RALIYA tayi wanda har sai da ya koma Rarrashin ta sannan ta yi shiru tare da yi ma yar ta su Addu,a.
Su Malam Rabu'u da Malam Adamu,Malam Abdulbasiɗ,malam Ɗahiru Mahaifin Jamil ma sunzo sunyi wa yara Addua tare da shi masu albarka tare da yi musu kiran sallah da duk abinda ya dace wanda Ibrahim shi ya ce Malam Abdul basiɗ yayi sannan ya faɗa masa sunayen da yake son asaka musu.
Hassan shi ake kira da NA'IM Husaini kuma ana kiransa da NA'IF Hassana kuma ana kiran ta da NI'IMAH sai Husaina duk da bata da rayuwa amma sai da suka bata suna wanda za,a riƙa tunawa da ita, NAINARH.Arziki kuwa kamar an buɗewa Ibrahim domin kuwa ya samu manyan kyautukkan da bai taɓa tunanin zai same su ba,gwamnati da kan ta ta kira sa ta damƙa masa maƙudan kudaɗe kamar yadda ta saba tallafa ma mara sa ƙarfi idan an sun samu arzikin irin wannan aihuwar,duk da ko Ibrahim gwargwado ya ɗan fara tarawa haka yayi ta godiya.Har gida da mota ya chanza musu tare da Mahaifiyar sa kowa part ɗin sa da ban.A haka suka cigaba da rainon ya yan su cikin kulawa da so da ƙauna.
*Bayyanar Abun Alkhairin da ya samu Jamil su Nadiya da kuma sauran yan uwa da su malam Rabu'u sun taya shi murnar sosai inda suka ƙara yi masa nasiha ya zamo mai cin halal ɗin sa da kuma kasancewa mai riƙon amana da gaskiya.Kuma yayi alƙawari zai yi aiki da shawarar iyayen sa haka ma su mahaifin sa ya yi murna sosai tare da bashi shawarwarin da suka dace.
Haka rayuwa tayi ta tafiya suna cigaba da rainon ya yan su har Allah ya kai mu ranar suna Inda akayi taro mai kyau da tsafta babu ƙarya cikin sa dan basu son yin sa ba ma Amma saboda Yan huɗu sai aka yi.Haka akawatse taro lafiya.
***
A ɓangaren Dr.Abida suma haka sukayi ta jinyar Tanim ita da Saheeba har da yan sauran yan uwan sa da suke mugun jin Tausayin sa har ya fara samun sauƙi dan dagaske yana jin jiki sosai ga depression na son kama sa bana wasa ba,kuma a hankali ta fara ɗaura shi akan magunguna n H I V.da na zuciya kuma yana samun sauƙi gwargwado.
Sai dai a ɓangare ɗaya Hajiya Jamila da kawar ta suna sane da duk abinda ke faruwa,matuƙar tashin hankali Jamcy ta shiga bayan samun labarin wanzuwar Tanim ɗin asashen Mahaifiyar sa,sannan bugu da ƙari ga warin da ya tasar mata a jiki wanda ita kan ta damun ta yake yi wanda har ya kai Alhaji Abdulkarim baya kula ta ko zuwa sashen ta saboda yadda ko ina ya ɗume.
Har ta kai ko ina yanzu bata zuwa ko ince basu zuwa sabo da yadda warin yake hana su shiga jama'a har wajen wani boka sun tafi ya kasa iya komai a lokacin saboda yadda qarnin mai haɗe da wari yake hana su shiga jama'a,koda ace sun shiga ma cin fuska ne kawai da cin mutuncin ke biyowa baya.
Yau ma da ƙyar suka iya fitowa su biyu suke a mota kowa ce tayi shiru basu wani daɗe a hanya ba. kamar yadda suka saba haɗuwa suka sauka a nan gidan da suke ta,asar su tare da yan siyasar da manyan mutanen da suke yiwa aikin kai musu yan mata da kuma Gay.
Tun da suka shigo suka tarar da su Zazzau ne sai jikin su yayi sanyi ƙalau domin dukkanin su sunyi yaushi babu wanda bai chanza kamanni ba tashin hankalin da suke ciki duk ya firgitar da su.
Maganar wani daga cikin mazan ne ya katse shirun yana cewa " Uwar Harka muna cikin Masifa fa,yanzu haka Ni bana riƙe kashi wallahi,tun shekaran jiya na fara fama da matsalar Nan nayi yawo asibiti babu wani abinda suka iya yi mini,sai bani Shawarar cigaba da yin amfani da pampers ga wari idan na tafi asibiti ɗaki ɗaya ake ware mini fa,sannan likita sai ya ga dama yake shiga yana yi yana zuba mini turare a jiki ".Ya kai ƙarshen zancen hawaye na wanke masa fuska " Ni wallahi da na sani ban faɗa ma wannan harkar va na tsaya a neman mata na yanzu gashi mutun ya gagara ruƙe bayan gida,Yanzu gashi mutun ya kware kwarewa bata wasa ba,kayi ta rayuwa Da pampers kamar ƙaramin yaro wannan wace irin rayuwa na jefa kaina kai co na " Ya ƙara yin furucin nadama na taso masa mara amfani tunda mai sha ta riga ta sha,sai dai ayi ta neman gafarar Ubangiji dan samun gafara sakamaon kenan na Duniya kafin a je gaban Ubangiji da irin wannan mummunan aiki.
Allah ya yi muna tsari daga faɗawa halaka🥺🤲🤲.
Haka suka yi shiru kafin da ɗai ɗai suka yi ta bayyanar wa cewa abun da suke fuskanta kenan suma yanzu matsalar su ɗaya ce,jin hakan kuwa duk sai da ya basu mamaki gaba ɗayan su domin wannan Babbar magana ce,ga matsalar wari bare su matse ma hospital su gani ko za,a dace su samu lafiya.Kuma yanayin fuskokin su ya nuna cewa gaba ɗayan su sun yi nadama akan ƙurarren lokacin da suke girban wani kaso na daga laifin su,sauran kuma sai neman yafiyar Ubangiji.
" Ku kwantar da hankali mun samu wani bugaggen boka zai muna maganin komai karku damu ance babu abinda baya yi,Busa rai ne kawai bai iya yi (WAL IYA ZUBILLAH😭) duk nasan inda zan ɓullowa lamarin Ni uwar tanɓele na rantse da Allah duk sai mun dara kowa zai ji daɗi za,a cigaba da harka,Za,a hole,a yi sha 'ani,muna da sauran lokacin mu dan haka duniya yanzu muke kan juyata,zamu cigaba da shan ruwa da cokali " Ta kai ƙarshen zancen with her full confidence.
Cigaba da magana tayi tana cewa " Shi kuma Tanimu kubar Ni dashi Ni zai hargitsawa ƙungiya bai san yadda naji ba lokacin Auren nan nasa bai san ta yaya na amince da Auren ba,ban taɓa tsammanin zan samun ɗan iskan da ya zai lalata mini ƙungiya kamar sa ba,Tunda Bai saki yarinyar nan ba duk da yadda nake a angiza masa da sihiri iri iri nasan cewa akwai abinda kan iya biyowa baya, Dan haka shi da uwar sa duk zasu girbi a bunda suka shuka sai nayi maganin su,Ni ba mutuniyar Banza bace da zan bari wani ya hau sama na alhali yana ƙasa na Dan haka kamar yadda tsarin mu yake haka zamu cigaba da tafiya,Ɗan da yake taƙama dashi zai zamo namu nan da yan shekaru ƙalilan,Zamu more sa,Zamu yi harin sa kamar yadda bamu samu yiwa mahaifin sa ba,kuma sai ya ɗan ɗani kuɗar sa,Gobe zamu shiga Niger da Chadi kowa zai koma yadda yake kunji mazaa Warin mu zai koma ƙamshi da ikon Boka Bugagge ".
Ta kai ayar zan cen tana sakin wani irin murmushi mai nuna yadda kalaman ta ke fita haka take son su kasance,kuma su zamo burikkan da zasu kasance a cike.
Dukkanin su mazan jikin su a sanyaye suka amsa mata kuma bawai Dan basu yarda da ita ba a'a face sun san cewa bata da imani Babu abinda bazata iya ba muddin ta faɗa. Mutun ɗaya ce ke murmushi agurin ita ce Jaruma amma duk saura fuskokin su babu annuri face damuwa mai tarin yawa da har yanzu taƙi warware wa duk da hope ɗin da ta basu.Haka suka watse bawai Dan sun ji zasu yarda da duk abinda ta faɗa bane daga ƙarshe suka yanke shawarar ɗaukar mataki akan Tanim da kan su dan ganin suke yi kamar soyayyar da take masa bazata bari ta hukunta sa ba.
Tun asali Jamcy ne sunan ta da aka santa da shi awaje a wuraren harkar barikin su,sannan tun da Alhaji Abdulkarim ya Aure ta a haka ta shigo gidan sa sai dai duk abinda yake na magana an rufe masa baki ya zama bashi da bakin iya furta koma,dama kuma ita kaɗai ta san zagayen da tayi har ya Aure ta ba Auren Soyayya bane na gaskiya.Biɗe biɗe take yi bana wasa ba,Dillaiya ce ta manyan yan siya sada masu kuɗi,Indai zaka zube mata kuɗaɗe zata sauke maka telar matasan yan Maza da mata sai ka darje da duk wanda kake so, Asalin qungiyar ta su itace ta kafa ta sai tayi yadda zata yi ta nemo duk wasu yara marasa ji masu wominizing business ta haɗa guri ɗaya ta ɗaura su daga yadda take so,Sai ya kasance kuma duka ƙawayen Tanim ne da ta sani ya yan masu hannu da shuni da ba yan siyasa.A haka suka.kafa qungiyar har ta kai matakin da take har suka samu bokan da ya kafa musu allon tsafi tare da sharuɗɗan abun tsafin da Maƙaryacin bokan ya gindaya musu,da ɓoye duk wani aiki da suke yi da samar musu da kudade ta hanyar jini.
Allah ka muna tsari daga shirka (ƙarama ko Babba)🤲🤲
*(Gaskiya Jamcy tayi nisa ace duk yadda ta ga ƙarshen Bokan na su bata saduda ba,bata karaya ba ga su anfara girban abinda aka shuka amma banza.Lallai duk wanda ya tsinci zuciyar sa a irin wannan matsayi yana cikin Masifa,irin wannan zuciya bata da kyau ko kaɗan.
Allah ka ƙara tsarkake muna zukatan mu.Ka kare mu daga aikata,Zina,Luwaɗi, Maɗigo,Gamsar da kai ,Allah ka ka kare muna zuriyar mu da aikata ɗai daga cikin wayen nan munanan laifukkan.Allah ƙara muna ƙarfin Imanin mu ka ƙara muna jin tsoron ALLAH.)*🤲🤲🤲
***
A ɓangaren Dr Abida test ɗin da tayiwa Nadiya ya tabbatar mata da positive take bata ɗauke da wannan cuta wanda ke nuna tun farkon samun cikin ta bata tare da mijin kamar yadda watannin da cutar take jikin sa suka nuna.Hakan yayiwa Dr Abida farin ciki matuƙa.Sai dai bata mayar musu da sakamakon ba ta ajiye shi kawai tun da basu san da zancen cutar ba a gare sa.
Wai ina SHANTY???
DAGA ALƘALAMIN✍️
FA'EEH BG💔
FIRSTLADY🙌
Neman ƙarin bayani
08069059756
Chat only pls pls pls 🙏🥺
Ba sai an kira ba kina sauke saƙo a inbox ɗina in sha ALLAH zan duba,koda bana online ne in na zo zan duba..✍️
Ina ƙaunar ku masoya na.
Masoyina DADY SOJA na gaishe ku.
Kun san yanzu tsuntsun yabar kan AMAN (SARKIN JEDDA)😂🥱naga alamar Matar sa MALINI kaɗai yake kallo.
Kuma kar wanda ya rabani da ( Ummi )HUSAINAR UNNI.💔💔
🧘🧘🧘🧘🧘🧘🧘🧘🧘🧘
LIKE,SHARE,VOTE AND COMMENT ✍️✍️✍️
KUYI FOLLOWING ACCOUNTS ƊINA.🙏
@FAIZA MURAI ( WATTPAD)
@FA'EEH BG (AREWABOOKS)
@FAIZA ALMUSTAPHA MURAI (FACEBOOK)
*_Typing_*📱
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
_Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chan zaku samu cigaban update.Farkon labarin masu neman sai a mun magana a numban dana sauke ƙasan wannan page, Dan samun document.☝️_
*🌸RAYUWAR MU AYAU🌸*
Ƙarya ko sakin Aure
Gajeren labari
Na
Faiza Almustapha Murai
Daga Alƙalamin
Fa'eeh Bg ✍️✍️
Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨.Amin.
Bismillahir rahmanir Rahim
💪📚📚
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
> >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>>
_*Daga marubuciyar littafin*_
_*A Mafarki Nasanta*_✍️
And now
_*Rayuwar mu a yau*_
P.38
Tunda suka kama hanyar Chadi bayan barin su Niger suke cike da farin ciki badan komai ba sai dan yadda Sabon bokan su bugagge ya tabbatar musu da komai zai koma kamar ba,ayi ba nan da kwana biyar,bayan sun zube kuɗin da za,a saya jajayen akuyoyi da baƙaƙen bunsurra da maguna baƙaƙe kamar yadda yake so, wayenda za,ayi yanka da su a bawa Ɗan somiya Aljannin da zai kula da wannan matsalar ta su.Yadda suke ku tsa kai cikin jejen da kukan tsuntsaye kawai ke fita a cikin da na dabbobi n daji masu haɗari zaka fahimci zallar nisan da suka yi a wannan harkar babu shakka ko tsoro haka suke bin ƙasurgumin dajin dake cikin Chadi arewa maso gabas.
Tunka rowar su dai dai wata hargitsassiyar bukka mai haɗe da take rumfa,wadda take ɗauke da kaya kamar na hauka,Hakan ya sa su sakin murmushi domin duk yadda bukkar take
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 34 Chapter of 39