Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
duk da ba ta ma samun ganin sa an mata shamaki dashi wanda har yanzu take cike da tsoron raba ta da mijin na ta kamar yadda aka raba ta da ɗan ta ƙwal namiji a cikin ya yan ta.Duk da ko yanzu ba haka a ka bar shi ba dan ta san wani abu Allah dai ya kyauta kawai. Numfashi ya sauke yana bin ta da idanun sa da suka ƙara runewa izuwa jaaa Dan tunda suka dawo ba a bunda take yi face kuka. " Me yake faruwa Najiba,Nadiya na raye,ɗan ku na raye,sai me kuma,ba shine damuwar ba "?. Kai ta girgiza masa hawaye na ƙara tsiyayo mata. kan sa ya girgiza sannan ya furta " to me ne ne"? " A gadon asibiti fa tana naƙuda baiwar ALLAH na naƙuda tsakanin rayuwa da mutuwa Tanim ya sake ta saki mafi muni saki na wulaƙanci saki mafi tozartawa,saki mafi zafi da raɗaɗi,Kuma da ace ta mutu shi ya kashe muna ita,domin shine wanda ya sanar mata da kan sa bayan Ni ya sanar mini,shin wane irin mutum ne Tanim mara imani duk wata cutarwa da yayi mata bata ƙare ba sai ya haɗa mata da sakin wulaƙanci,shin kasan irin uƙubar da Tawan ta sha a gidan sa,kasan rayuwa mafi muni da ya jefa ta ya saka dafi azuciya ta dalilin sa ta kamu da hawan jini,Fatana shine kawai Allah ya sa bai saka mata cuta mai karya garkuwar jiki ba "....... Kuka ne ya ci ƙarfin ta inda sai da taci mai isar ta Jamil dai bai iya cewa komai ba amma yaji Tausayin Nadiya matuƙa dama ya san hakan zata faru domin shi har ƙungiyar su ta ɓoye ya sani sai dai bazai iya faɗa ma Najiba ba kamar yadda ya tabbatar Nadiya bata faɗa mata ba kuma ya san tana da nata dalilin yin haka. " Ta so ta sanadin ta ya shiryu,ta shirya wa za ma da shi ba kamar baya ba da take neman takardar ta ido rufe ban san abinda ya chan za ta ba har ta so zaman dashi ,sai dai tace mini tana son kwasar ɗimbin lada ne. Shi ya sa ta so ta gwada sa,ar ta ko zai samu shiriya ta sanadin ta tun da shiriya Ta Allah ce, sai dai hakan be samu ba,Nadiya kiyi haƙuri Allah zai saka miki ".......... Kuka ne ya ƙara ɓarke mata hakan ya sa Jamil cikin mutuwar jiki ya rungumota jikin sa yana Rarrashi sai dai ganin ta kasa yin shiru hakan ya sa ya haɗe bakin su waje ɗaya sai da ya ɗauki lokaci yana kissing ɗin ta kafin zance ya chanza. Haka Raliya ma sai da Ibrahim yayi ta Rarrashin kayan sa sannan ta yi shiru. *** " Wai lafiya kazo nan kayi mini shiru ".? SHANTY ce tayi furucin wadda ke zaune halfnaked domin daga ita sai wata shegiyar riga ce mai kamar ba,a saka komai ba dan kamar net haka take komai nata a waje. Shiru ya ƙara yi mata kamar bai san abinda take faɗa ba. Daga inda take ta ta taso tana dawo wa kusa dashi cikin karairaiya da kisisina. Yanayin da yake ciki ba irin na ta bane amma duk da haka sai dai ta yi yan dabarun mu na mata cike da karuwan ci ta janye hankalin sa tun yana ƙoƙarin ture ta har ya kai shi ke jan ta daga nan kuma komai ya cigaba da wakana. ;;; A asibiti kuwa Nadiya bata farfaɗo ba sai kusan Gangar Asuba sannan ta buɗe idanun ta da suke mata nauyi.Bin ɗakin ta fara yi da kallo inda aka dawo da ita kafin ta sauke idanun ta kan Jazlan da Dr Abida ta masa sunan ta zuba masa idanu tana bin shi da kallo kamar bata taɓa ganin shi ba sai yanzu.Idanin ta ta ɗauke kansa tana mayar wa gefen Da Mama Hasiya take zaune a kan darduma tana lazimi tana jiran ɓullowar Alfijir. Idanu Nadiya ta rintse da ƙarfi dan sai yanzu komai ya dawo mata. Shesshekar kuka ta fara inda shi ya ankarar da Mama Hasiya farkawar ta cikin azama kuwa ta dawo kusa da ita cikin murmushi da gode ma ubangiji ta furta sunan ta. " Nadiyaaa ". Jin sunan ta da Mama Hafsatu ta kira ne ya sanya ta Ɗagowa tana zuba mata idanu kafin ta ƙara fashewa da kuka sai yanzu ta samu damar iya yin magana cikin shesshekar kuka da wata irin murya mai rauni da karya zuciya. " Umma ya cuce Ni,Umma ya cuce Ni,Ya kaini gidan sa kan buƙatar sa,duk da nasan ina da nawa kason a faruwar komai amma,Umma ya zalunce Ni,Allah bazai taɓa barin sa ba,banzan taɓa yafe masa ba,Allah ka ƙwatar mini haƙƙi na,Akan gadon haihuwa Umma yake ce mini bai da dangan ta ka da ɗan sa,Akan gadon asibi yake ce mini Ya sake Ni saki uku,Umma anya Tanim cikakken musulmi ne,Umma anya akwai zuciya acikin ƙirjin s...." Kuka ne ya ƙwace mata mai nauyi da taɓa zuciya ita kan ta mama Hasiya sai da ta zubar da kwalla a wannan karon lallai Nadiya ta ga jaraba,dukkanin su sun ga jarabawa daga ita har Najiba,abinda ta so nusar da su tun baya gudun irin faruwar wayen nan lamurran ta so ace Nadiya ta Auri ya sayyadi wanda yanzu haka shima matar sa na ɗauke da cikinsa kusa n time ɗaya da su Nadiya dan tun ranar da abun ya faru yan uwan sa suka nema masa mata aka daura masa Aure a ranar.Haka ta samu labari. Rungume ta Mama Hasiya ta yi tana sauke ajiyar zuciya kafin ta furta " Ya isa haka Nadiya kinji,Allah haka ya tsara muku dukkanin ku,babu wanda yake wuce ƙadddarar sa sai dai inda da Addu,a komai ya kan iya chanzawa,kuma tabbas wannan shine alkhairi a gare ku sakin akwai abunda Ubangiji ya sa ya raba ki dashi a dai dai wannan lokacin, ki cigaba da haƙuri ki raini ɗanki sannan ki dage da Addu,a komai zai wuce zaki samu farin ciki fiye da wanda kika yo a rayuwar ki ta baya in Sha Allah ke dai ki miƙawa Ubangiji lamurran ki kinji,ki cigaba da ambaton sunan Ubangiji da masa kirari zaki samu sanyi acikin zuciyar ki,Allah ya raya Jazlan ". Ta yi furucin kamar yadda ta ji kakar sa ta saka masa saboda sakaya sunan dan ko shi na sa ba kullum take faɗar sa ba. Kukan Nadiya kuwa ragewa yayi inda ta samu kan ta da sauke numfashi mai nauyi da ajiyar zuciya sai dai wani irin tabo ya zauna mata azuciya na cin zarafin da Tanim yayi mata bata jin har duniya ta naɗe zata yafe masa,koda kuwa duk jama'ar duniya zasu taru kan ta dan roƙon yafiyar ta a gare sa,ba zata yafe masa ba domin ƙarshen cutar wa ya cuce ta kuma ya tozarta ta,Amma babu komai kan sa yayi wa Allah zai saka mini ta furucin ƙasa ƙasa tana tsiyayar da hawaye na baƙin ciki.Tana kiran sunan Allah a cikin zuciyar ta inda take kuwa ta fara samun sanyi na ratsa ta. Da sauri ta juya jikin ta na wata irin tsuma bayan gama sauraren Duk maganganun da suke yi domin kuwa ita ma acikin asibiti ta kwana Dan sun gabatar da tiyata kusan biyu a daren basu mayi barci ba yanzu ta leƙo ne ta ga ko Nadiya ta farfaɗo sai Kunnuwan ta suka jiye mata wannan mummunan jawabi wanda take son ji daga bakin Nadiya ɗin. Tun da ta shigo office ɗin na ta take dar-zar kuka tana furta " Dama shi yasa ya ƙi bani amsa,Jamila kin kashe mini Ɗana,kin kashe shi kin raba Ni dashi,amma Ni musulma ce mai imani Dan haka na yarda ƙaddarar sa wannan Allah ka bani juriya,Allah ka bani juriya,Allah ka yafe ma Son kurakuren sa ,ashe matar sa ma zaman cutar da ita yake yi ban sani,Ashe Auren da yayi mata bana zama bane,yana sane,Yanzu Kunnuwan ta sun jiye mata abun da take son ji Tanim ɗin ta ne ya Auri mace dan kashe ƙishin sa badan zaman Aure na rayuwar Har abada ba,ashe zata ga wannan rana,ashe har haka yayi ƙauri,me yasa Jamila me na tare Miki,wannan wane irin rashin imani ne........ Kuka ne ya ƙwaace mata mai nauyi da raɗaɗi wanda yake fitowa har ƙasan zuciyar ta ita kaɗai ta san irin raɗaɗin da take ji ita kaɗai ta san irin ƙuncin da take ciki.,Allah ka bani ikon cinye wannan jarabawa Allah Ni mai imani ce a gare ka,na yarda ƙaddarar mu ce wannan na karɓa da hannu bibbiyu,Allah ka bani ikon jurewa ya Allah.Sai hawaye shar suka ƙara wanke mata fuska. Tausayin Nadiya ya mamaye ta domin ta san tayi ƙoƙari sosai dan ita har ta ga chanji akan sa ya rage shaye shayen sa,sai gashi ya babbaka ma kan sa wuta da kan sa,wadda bata san ranar cinyewar ta ba a gare sa dan Allah ya isar ta bazata ta taɓa faɗuwa banza ba ta sani. Alwallah ta faɗa toilet ta ɗauro jin ana kiyaye kirayen Sallah na farko.Nafila tayi tare da Raka'atanil fajr sannan ta fara korawaa Ubangiji Damuwar ta tana yi tana zubar da ƙwalla. Na baku page biyu 🙏 Ayi Manage. Daga Alƙalamin ✍️ Fa'eeh BG Firstlady 🙌 GIMBIYAR TASKIRA 👑 Share and react. *_Typing_*📱 *TEAM TAURARI HUƊU* ⭐⭐⭐⭐ https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y _Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chan zaku samu cigaban update.Farkon labarin masu neman sai a mun magana a numban dana sauke ƙasan wannan page, Dan samun document.☝️_ *🌸RAYUWAR MU AYAU🌸* Ƙarya ko sakin Aure Gajeren labari Na Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim ✍️*TEAM TAURARI HUƊU*✍️ ⭐⭐⭐⭐ _Fa'ee BG_ *RAYUWAR MU A YAU* _Matar Habibi_ *NIKEH DA IKO* _Haandy_ *NIKKAH ( MARRIAGE FOR RENT )* _Oum Amjad_ *RAYUWAR JANNAH* 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _*Daga marubuciyar littafin*_ _*A Mafarki Nasanta*_✍️ And now _*Rayuwar mu a yau*_ P.35 ✨💫✨💫 Bata ɗaga daga kan carpet ba har sai da aka yi sallah'n asuba sannan ta miƙe,Haske na fara fitowa ta gida dan ta kasa shiga ɗakin na Nadiya komai ya kwance mata nauyin su take ji matuƙa shin ta yaya zata basu haƙurin abinda ya riga ya faru ya zata fuskan ce su da nauyi da kunya. Hakan ya sa ta wucewar ta gida direct a chan gidan ma sai da ta sha kuka bayan sanar wa da Sahiba abinda ke faruwa inda ita ma da sauran yan uwan suke cikin jimami domin take suka hallara gidan dan Rarrashin mahaifiyar su da jimamin samu da rashin da su kayi,da muguwar hasarar da ɗan uwan su ya tafka, Dan wannan mutuwar Auren kan sa yayi wa basu tunanin akwai wadda zata maye masa gurbin ta saboda tayi haƙuri matuƙa. Zaune take kan kujerar Two sitter babbar mace ce mai ji da wanka aƙalla zata kai shekara hamsin da wani abu ta kafe glass a idanun ta wayar ta a hannun ta sai sakin murmushi take yi kafin kuma murmushin ya koma Dariya irin ta ƙetar nan.Da alama chat ne take yi. Wayar ta ɗaga sama ta na furta network na son ya katse muna fira bari kawai muyi vedio call naga ki zai yi inda tayi furucin tare da miƙewa ta bi wata hanyar da zata sada ta da bedroom ɗin ta. Mintuna ƙalilan ta isa bedroom ɗin na ta. Zama tayi kan lafiyayyen gadon ta na alfarma tana furta " Hmmm ai bari kiji wallahi yanzu ta fara gani Indai Tanimu ne yanzu ta fara ganin lalacewar sa,Naji Haushin abun da ya faru,karyewar allon tsafin nan,yanzu gashi komai ya na son sauya muna,yanzu tashin hankalin da nake ciki ma shine wallahi baki ji warin da Suke yi ba gabaki ɗayan su yanzu ɗan morewar da muke kam babu ta domin bazan iya mu'amala da su a hakan ba kinji warin wai,bayan faruwar lamarin Nima naje gurin numfashi ma kasa shaƙar sa nayi,Ga boka zube kasa kamar an yiwa gawar sa aman wuta lamarin ya so ya ɗan ɗaga mini hankali.Dole nayi maganin Abida,Yanzu dai ba cewa take yi Ni na ɓata mata yaro ba Ni da mahaifin sa muka sakan ta shi sannnan Ni nake goyon bayan sa da duk abinda yake ba na dai dai,yanzu ta fara gani kuwa zan cigaba da Juya Tanim a tafen hannu na,zan cigaba da nuna masa hanyar ɓata zata san shayi ba ruwa bane Jamcy kuma ba mutuniyar Banza ba ce,yanzu dai komai ya buɗe boka ya mutu amma zamu nemi wani Hajiya safina ta sanar mini tana da wani mai aiki da cikawa ya san ta kan aiki inka zube masa kuɗin sa sai ka dawo, Dan haka chan zamu koma,Ita fa Abida abinda bata sani ba shine na riga na raba ta da shi,in banda ma yanzu lokaci ɗaya komai ya ja baya har ta isa ma ta kalli fuskar sa da sunan cewa ita ta haife sa,Shi kuma wannan jinjirin na sa zan biyo ta kan sa shima,muga abinda ya dace dashi,Zata san dani take zancen,wallahi koda Alhaji ya faɗa mini na daɗe ina dariyar abun shiko soko jiki na rawa ya zo ya kwashe mini komai,zanyi maganin su duka zata rasa ɗan ta matacce da ta ke kira na ta dan na san na riga na illata rayuwar sa,Sai saura kuma ma ai shi ya fara neman matan sa,da shaye shayen sa, ni kawai na riƙa masa ne na goya masa baya Ni fa nake masa safarar manyan big ladies da wasu ƙwayoyi ba tare da ya sani ba shi iyakar sa ya ga mace ta zo inda yake bai san nice ke tura masa su ba,kuma Shegen sai yayi mui da baki,..." Dariya ta kece da ita har sai da ta kai kwance. " Yawwa Hajiyar Harka haka nake son ji a samo muna wasu majiya ƙarfi kamar Tanimu,Dan Ni wallahi dan boka ya gargaɗe Ni gudun tonon asirin mu da tuni na haiƙe masa mugun kwaɗayin son kasancewa dashi nake yi wallahi,shi ya sa ma nake raga masa wasu abubuwan amma da tuni na ma kawar dashi,dan bata isa ta haifa ba ina kallon ta,ta cika gida kai gaka daga kashi sai ci,Yanzu Kinga ko mutuwa Alhaji yayi komai na saka ya mayar dashi da sunan Muhammadu Tanim daga nan komai ya koma hannun mu ". Shewa aka yi daga chan ɓangaren ana furta " Se dake yar ƙunar baƙin wake,Uwar harka ikon ALLAH an buga dake an Barki,Kowa yace Jamcy ta wasa ce ƙarya yake yi,Ba gaba da gaba ta baya ma sai an shirya uwar tanɓele,Uwar yan iska,Ke ce Les,ke ce Uwar haɗin mazaje a malele dillaliyar harka a barki a huta sai dake ...."" Ire Iren wayen nan kirarin da take mata masu saka kan ta na ƙara girma su ta yi ta jera ma ƙawar ta ta. Ita ko Hajiya J dake jin ta sama saboda yadda kirarin ya ƙara kutsa ƙwaƙwalwarta ta kece da dariya tana furta " Yau kina da Yan Ruguza guda Biyu,zaki shaƙata da su ". " Wohoho sai bake ba Uwar tanɓele,uwar yan iska, uwar alkhairi. Ina godiya kice yau akwai Sha'ani " " Ayi harka kawai Jaruma ". Hjy Jamila Ta bata tana sakin dariya kasancewar haka ne sunan babbar ƙawar Tata mai suna Laraba.Suna mata laƙani da Jaruma. Haka suka cigaba da yin firar su a tsanake rabi da kwatar ta duk akan abinda ya faru ne da ƙungiyar su Tanim. Ko meye haɗin su da ƙungiyar oho 🤔🤔 To ma abinda yake asirran ce a ina suka sani.🤔🤔 *** A ɓangaren Nadiya kuwa Daƙyar Mama Hasiya ta ƙara rarrashin ta Dan wani babin kuka ta ƙara sakawa cikin zallar baƙin cikin da take ciki,Dan Jazlan ma da ƙyar ta yarda ta bashi nono wanda ya samu da wahala dan babu komai ciki saboda bata ci abinci ba har yanzu madarar bata sauka ba. Haka ta shayar da yaron cikin zafin zuciya ji take kamar ta aika masa da ɗan sa yadda take ji sai dai kuma ta san kan ta zata yiwa ga kuma shawarar da Mama Hasiya ta ƙara bata akan ta kula da ɗan ta kar ta duba komai atsakanin ta da mahaifin sa,ta kula sashi zata yi alfahari da shi wata rana . Sai dai duk ta tuna wanenen mahaifin na sa sai ta ji Wani irin ƙololon baƙin ciki na taso mata har cikin zuciyar ta har ya na saka ta rasa Numfashin ta,Sai dai kawai taji hawaye ya saukar mata.Ga soyayyar yaron da take shigar ta duk bayan seconni cikin Tausayin sa. Sallamar su Raliya ne da kuma Najiba ta sa ta ɗago kan ta tana zuba musu idanu babu ma kamar Najiba wadda idanun ta har yanzu basu saki ba sun ƙara yin suntum dan yau ma wani sabon babin kuka ta saka mai taɓa zuciya wanda ba na komai bane face na Tausayin Yar uwar ta. Shigowa ciki suka yi suka zagaye ta Kowannen su na ajiye abun hannun sa dan tare suka yi tafiyar Najiba ta samu Raliya har gida, Dan ta tsaya sayen wani abu maimakon ta wuce asibiti sai tayi gidan inda suka zo tare suka ɗauki napep ɗaya. Kan ta ta saukar ƙasa da sauri ganin yadda Najiba idanun ta suka cika da hawaye kamar yadda itama na ta suke cike da hawaye na baƙin cikin da ya kasa barin ran ta. " Tawan kiyi haƙuri haka Allah ya tsara,An ga Aure anga mutuwar sa ta yuyu hakan shine alkhairi kuma tabbas haƙƙin ki bazai taɓa barin Tanim ba sai ya fita jikin sa tun kafin aje ko ina,Ya nuna muna rashin imani kina gadon asibiti imagine zai baki saki har uku saboda mugun hali irin na sa da rashin tausayi "... Hawaye ne suka silalo mata masu zafi sai kawai tayi shiru ta kasa cigaba da magana. Nadiya kuwa dake ta sauke Ajiyar zucia tayi ƙoƙarin haɗe abun da ya taso mata sai dai ta kasa sai ma fashe wa da kuka da tayi inda suka haɗe kai waje ɗaya duk su ukun suna ta rusar kuka kamar anyi musu mutuwa,har RALIYA da ta samu labarin Sakin yar uwar ta yanzu. Da ƙyar Mama Hasiya ta Rarrashe su suka yi shiru,wanda itama jikin ta yayi sanyi matuƙa dan lamarin akwai tausayi cikin sa.Daga nan suka taimaka mata ta miƙe kan gadon ta watsa ruwa dan shima tun ɗazu Mama Hasiya ta matsa mata sai dai kuka take saka mata da ta yi zancen,sai ta ƙyale ta. Shi ya sa ta wanke Jazlan tsaff dashi ta shirya shi dan har kayan yara yan uwan na sa sun kawo a jiyan da na ta da duk wani abun amfanin ta da na sa. Tana fitowa an haɗa mata shayi mai kauri ta sha inda take zufa ya karyo mata ya wanke ta. Idanu ta Lumshe tana miƙe ƙafafun ta daga kan kujerar da take zaune jin sun ɗan mata nauyi kaɗan saboda kwanciya,sai dai jikin ta yayi mata sakayau musamman da ta yi wankan sai take jin ta kamar an zare mata ƙaya a jiki Damuwar ta ɗaya ce a yanzu shine cin zarafin da Tanim yayi mata da kiran bai haɗa komai da jinjirin da take jin sa har cikin ƙahon xucin ba,zata nuna masa bai haɗa komai dashi ba in sha ALLAH sai ya zubda ƙwalla a kan wannan zancen da idanun sa,badai akan Jazlan ba,ta ɗauka zata kula da abunta zata masa gata. kasancewar sunan ya mata daɗi jin Mama Hasiya na kiran shi haka wanda bata ma san wynada ya saka masa sunan ba amma ta ji daɗin sa sosai.Ta saka a ranta zata raini ɗanta tamkar marayan da baida uba,zata masa gata kamar na kowane ɗaa dai dai gwargwado da abun da Allah ya hore mata. Shiru tayi tana sauke numfashi mai cike da wata irin muguwar tsana ta Tanim da zafin sa da ya mamaye mata zuciya cikin ƙanƙanin lokaaci ɗan Tausayin sa da ya yi mata saura ya ɓace ɓatt a duniyar zuciyar ta. *** Suna zaune suna taɓa fira sai ga Ma ma Hafsatu ta shigo da sallaama ɗauke a bakin ta.Tana cewa. " Jika na na kaina ka, ka tashi lafiya ". Tana zancen tana dosar Inda yake a hannun Raliya yana ta buɗar ido irin na jinjirai masu wayau. Miƙa mata shi RALIYA tayi itama cikin ɗan murmushi bayan tayi mata ina kwana. Karɓa ta yi tana furta " Yaro ɗan Masu abun kaga kayan shi masu Shegen tsada,Yaro ya zo da goshi wannan uban kaya haka masu tsada,Yaro ɗan Masu Naira " Ta kai ƙarshen zancen tana taɓa kayan na sa tana sakin dariyar farin ciki dake nuna daɗin yadda ya kasance Mai kuɗin ne surukin ta kamar yadda take da buri gashi harda jika da zai zame mu su Hanyar ta tsar su.Lallai da ta bari Tanim ya zubar da cikin Nan da ba ƙamar hasara tayi ba da kuma Nadiya ta cire sa da bazata taɓa yafewa Tanim ba Ga hanyar arziki yana son yayi musu buƙulu sai dai ta Allah ba tashi ba Arzikin su ya sauka Duniya kuma bai isa ya tare shi ba.Hancin sa ta ja kaɗan tana sakin yar dariya bayan gama zancen zucin na ta tana bin shi da kallo. Sallamar Yan uwan sa mata ne su shida suka shigo a tare wanda suka zo daga gurin mahaifiyar ta su da ta kasa zuwa duba Nadiya ɗin.Sai dai suka haɗo duk abinda ya dace suka zo dashi.Jiki sanyaye dukkanin su suke gaisawa da su Mama Hafsatu da take ta yasar baki Dan ta gane su sune dangin Tanim yan arziki na jiya. Domin ta san basu rasa zuwa da wani abun.Bata ko gama tunanin ta ba sa ga shi an fara shigowa da manyan kuloli masu ɗauke da kayan ciye ciye na abinci kala kala kulolin har ɗaukar ido suke yi ga su na alfarma. Ya jiki suka yiwa Nadiya ta amsa musu a tsanake da fuskar ta da duk ta yi jawur ta ci saboda kukan da ta sha idanun duk sun kumbura tausayin ta ne ya kama su gaba ɗayan su wanda ya ƙara haddasa musu Mutuwar jiki gaba ɗayan su.Fahimtar bata wani gane su ba ya sa ɗayar su da take Babba mai suna Ummu Salma ta maata bayani wanda sai yanzu ta gane su dan wasun su sunje biko wanda suka zo da ƙyar Dan Momy hana su tayi.Momy itace Hajiya Jamila ita suke kira haka.Mahaifiyar su kuma suna kiran ta da.Mamana.A yadda ta ce ba sai an zo biko ba dan gidan talakawa ne zasu nemi gida su kawo yar su saboda tsiya gare su,da alama suna son rabuwa da yar su ma Dan taga yadda ake ta nan nan da su a gurin Kai lefe. Nadiya kuwa tun da suka yi mata bayani ta ɗaure fuska tamau kamar ba ta san farin ciki ba ga shi dama ga yanayin

Chapter 30 of 39