Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kan ta ne a ciki,ba tun yau ba sun san tana zuwa gidan Hajiya Samira,Wanda basu san dalili bama Mijin Hajiya Samira ya yi karan tsaye akan lamarin ashe wannan ne dalili. Sai yanzu suka ƙara fahimtar komai. Numfashi malam Rabu'u ya sauke da malam Abdul Basiɗ kafin suka kalli juna sannan malam Rabu'u ya gyaɗawa malam Abdul Basiɗ kai da alama akwai abun da yake son furtawa shine dalilin kallon ɗan uwan na sa yana neman izinin sa duk da ya san cewa ya isa da NAJIBA amma yana son jin ta bakin ɗan uwan sa. Ɗan gyaran murya Malam Abdul basiɗ yayi kafin a hankali ya furta.. " JAMILU ''! " Wannan shine mahaifin NAJIBA,Ni kuma nine mahaifin yar uwar ta NADIYA,wan mahaifin ta kenan "..Yakai karshen yana nuna malam Rabu'u dake zaune fuskar sa sai sa sai sa.Bazaka iya furta abinda ke zaune acikin zuciyar sa ba.Sai dai da alama hankalin sa kwance yake baya tare da wata damuwa sai ɗan Tausayin yar sa da ta tsunduma kan ta a rame mai zurfi. Abinda ta ke guje ma shine take tare dashi ba tare da ta sani ba.Talakan da ta guje ma yau shine mijin ta,mijin ta da take ma kallon wani shahararren mai kuɗi sai gashi rana tsaka ta fahimci bashi da komai talaka ne talak ashe sai ɗan kwangon da yake da shi. Wani irin rawa jikin Jamil ya ɗauka mamaki ya hana shi motsawa zuciyar shi ta shiga shawagi na tunanin lokuttan da suke da NAJIBA duk tsawon lokacin da suke tare tana bisa ƙarya ne itama.Shin me yake shirin faruwa ne...? Ya tambayi kan shi. Kafin ya rasa mai bashi amsa.So yake ya ɗaga idanun sa ya Kalle su sai dai ya kasa yana da tarin tambayoyi abakiin sa amma ya kasa iya furta musu. Numfashi ya sauke a hankali wnada ya fita da wani sanyi da zuciyar sa tayi masa nauyin da ke danƙare da zuciyar sa ya sauka. Ko me JAMIL zai furta oho🤦🥱 Yau dai KURA TA CI KURA NAJIBA.😂😂😂 ANKWASHI KUNYA KAMMM. Fa'eeh✍️ Chat me via WhatsApp or Telegram. No call... 08069059746 React,share,and comment pls 🙏 *_Typing_* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y _Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chann zaku samu tun daga farko._☝️ *🌸RAYUWAR MU AYAU🌸* Ƙarya ko sakin Aure Gajeren labari Na Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _*Daga marubuciyar littafin*_ _*A Mafarki Nasanta*_✍️ And now _*Rayuwar mu a yau*_ Typing date,and time. 1/16/25 7:39AM P.24 ☆☆☆ " To shi kuma wanchan Familyn fa Baba su waye,Dangin ku ne ko su waye ".? Jamil yayi tambayar kan shi ƙasa yana neman amsar zancen sa domin kan shi ya ɗaure masa da lamarin kallon abun yake kamar Almara. " Gidan ƙawar mahaifiyar Nadiya ne,Hajiya Samira ". Malam Abdul Basiɗ dake ta sakin ɗan murmushin yaƙe bashi amsa kans shi tsaye. Idanu Jamil ya ƙara zarowa sai dai bai furta komai ba.Jikin shi ya ƙara yin sanyi sai dai kuma yaji sanyi a ransa ya san bazai taɓa rabuwa da NAJIBA ba kasancewar ta yar talaka itama,kuma ya san iyayen nan na ta Bazasu taɓa barin zancen ta na saki yayi tasiri ba, Dan ya hango tsabagen Mutuncin da suke da shi. Sallama yayi musu ya juya yana son ya nemi wata alfarma sai dai ya kasa haka ya juya bayan yayi musu sallama tunanikka barkatai a cikin zuciyar sa. Shi har yanzu ga ni yake kamar NAJIBA ba yar su ba ce amma kamar da suke yi wadda ke bayyanar da asalin jinin su dake gudana iri ɗaya ya sa dole ko kai waye ka yarda.Dan idan bai manta ba ya taɓa mata wannan zancen na rashin kamar ta da Hajiya da Alhaji ta ce kakar ta,ta biyo Wadda ta rasu shekara biyu da suka wuce.Dan ko kaɗan bata kama da Hajiya Samira. Yoo ya za,ayi a samu kama babu wani haɗin jini,sai kuma wadda Ubangiji ya tabbatar Dan nuna ikon sa ga bayin sa. Haka ya kama hanya har ya fita tsallake kafin ya samu abun hawa domin ya san ko ya matsa NAJIBA ba fitowa zata yi ba sannan ba bari ma zata yi suyi maganar fahimta ba dan tayi fushin da bai ta ɓa gani ba,sai dai ai shima ya kama yayi fushin tunda shima an yaudare sa,saboda ita ya tsunduma kan sa a halin da yake ciki duk wata yar kadara tashi nan ta tafiyar ta,yar wata sana'a da yake ƙulla ƙulla ta wargaje.Sai dai dole zai shanye komai ya ɗauki fushin ta ya saki nashi. Tun da babu yadda zai yi,domin rabuwa da NAJIBA kamar rabuwa da rabin rayuwar sa ne. Napep ya Tare ya faɗa ya na sanar ita inda zata ajiye shi. Napep kuwa ba ta zame dashi ko ina ba sai a ka buga tsallaken titi. Direct yana Sallamar mai napep ya kama hanyar ɗan ƙaramin ɗakin na su.Duk yadda jama'a ke jan shi da tsokana ana ango ango haka ya ke sakar musu murmushin yake yana gaisawa da su tare da ɗaga musu hannu. Numfashi ya sauke daga zaunen da ya kai yanzu yana sauke a jiyar zuciya ya rasa wane irin tunani Zai Yi,Shin yanzu da gaske NAJIBA ba yar kowa bace,ba yar Alhaji Ahmed Zinari bace da Hajiyar Dubai,ana nufin bata haɗa komai da su ba.Wayen nan tambayoyin sune yake jefawa kan sa sai dai bashi da mai bashi amsar su,sai ita.Sai dai duk yadda yake son ƙin yadda bai da dalilin yada zancen domin gaskiyar sa a fili take. Dan yakan tuna wasu lokuttan,Ya taɓa kai ta gida yana sauke ta Bayan ta shige shi ko ya ja motar sa sai dai bai ko yi nisa ba ya hango kamar ta, ta shiga napep da sauri,da ya kira ta tace ba itace bace,mai zai saka ta shiga napep ga motoci birjik a gida,sai ta rufe bakin sa da Baƙuwar hajiya ce ta wuce wadda tayi ɗazu.Tun da ta furta masa sai bai ƙara tambayar ta ba domin shi ba mutun ne mai ƙwaƙwaƙƙwafi ba.Anan ma ya saki maganar ya kama gaban sa. Numfashi ya sauke bayan tuno da lokacin sai yanzu ya ƙara tabbatar da ita ɗin ce,kenan mai napep ɗin shi yake juye da ita ya kai ta asalin gidan na su.Amma taya bai taɓa fahimtar komai ba.Sai dai bai ji komai ba domin ya fahimci cewa dukkanin su sun yaudari kan su ne ba tare da sun sani ba. Ɗan Numfashi ya sauke yana kallon Gariti da ya lura dashi a ayanzu dan bai ga lokacin da ya shigo ba kasancewar ya bar shi a waje yana wankin motoci. Kallon cikin ido Gariti yake bin shi da shi kafin ya zauna a kan yar ƙusassshiyar katifar su inda Jamil ɗin ya ke zaune sannan ya furta. " Lafiya dai ko "?? " Daga ganin yanayin ka na san cewa ba lafiya ba,Naga yadda kake ta karɓa musu magana,gashi kuma na tarar da kai ka ka faɗa duniyar tunani domin na daɗe nan tsaye kuma na fahimci baka san da shigowa ta ba,me yake faruwa Angon NAJIBA ".? Ya kai ƙarshen zancen yana sakin ɗan Murmushi. Numfashi Jamil ya sauke yana sauke kan sa sai kuma ya saki guntun murmushi na yaƙe.Amsar da yake son bawa Gariti yake nema ya ra sa.Baya son tona mata asiri sai dai bazai iya ɓoye ma Gariti komai ba domin dashi aka yi komai dan haka ya sauke ajiyar zuciya sannan ya fara zance. " Gariti NAJIBA ba yar Alhaji Ahmed mai zinari ba ce,Alhaji da Hajiyar Dubai bata haɗa komai da su ba,Hajiya Samira su ruka ta,ta da,ƙawar mahaifiyar Nadiya ce matar yallaɓai gwaska,Amma abin da yake bani mamaki shin shi oga Tanim ta hakan Nadiya ta mamaye shi ko da sanin sa". " NAJIBA ta bada ƙofar gurɓata rayuwar mu,kuma Allah ya ne ya tsamo mu,Na fahimci rayuwar da na jefa kan mu a ciki bata da kyau tun ba yanzu ba sai dai haɗuwa da NAJIBA ya ƙara mini ƙaimi Dan samun farin cikin ta,kasancewar ta yar su masu hannu da maiƙo,Duk wata fargaba ta ta gushe tun taƙaitaccen bayanin da na samu ga mahaifan ta,Zan bi komai a hankali har na samu Dawowar ta hannu na domin babu saki a cikin tsari na ". Shiru yayi bayan ya kai ƙarshen zancen. Gariti kuwa sumar zaune yayi ya kasa furta komai yaji gaba ki ɗaya notikan sa kamar sun warware ma sa.Da ace ba Jamil da bakin shi yake faɗa ba da bazai yar da ba Amma tabbas ya shaida hakan domin kuwa ya san bazai ta ɓa faɗa masa ƙarya ba kan matar sa da yake mugun so da ƙauna. Da ƙyar ya haɗo zancen yana tsaida zuciyar sa da ke ta shawagi da zancen. Ya furta. " Kana nufin itama maƙaryaciya ce kamar kai ".? Yar hararar shi Jamil yayi kafin ya share zancen. Gariti fahimtar da yayi zancen yadda ya ɗaura shi bai masa daɗi ba hakan ya sa ya ƙara furta " Ina nufin,Dukannin ku turba ɗaya kuke bisa ba tare da ɗaya ya sani ba ". " Wannan shine abinda na guje maka Jamil ban san dalilin da ya sa nayi ta baka magana ka tsaya kan gaskiyar ka ba,Ni na san wannan ranar zata zo wata rana,gashi kuwa tun ba,aje ko ina ba,komai ya buɗe maka,ba kai ɗai ba har ita kan ta,Shin wa gari ya waya yanzu,Ni na san ko ku kan manta jama'ar gari baza su taɓa mantawa ba domin Wannan wani lamari ne babba,sai dai lamarin yayi mini daɗi domin kura ce ta ci kura kowa ya faɗa ma ramen da ya gina,babu batun a zame ɗaya gefe,sai ku rungumi junan ku ku zauna lafiya.Wannan shine fatana.,Ina roƙon Allah ubangiji ya shiryar da masu irin wannan hali naku,kuma ya kare mu daga shiga irin wannan kunyar,domin na san kaji kunya matuƙa a gaban iyayen nan na ta duk da ba laifin ka ne kai kaɗai ba,har da nata, Dan haka ka sanya haƙuri ka jira ka bada lokaci komai zai zo ya wuce in sha ALLAH ". " Yanzu muje kasanar da Iyayen ka,sannan ka basu haƙuri ka samu Addu,ar su ". Kai Jamil ya gyaɗa masa yana sauke Ajiyar zuciya ya san Gaskiya Gariti ya faɗa masa dan haka idan akwai kalma mai zafi acikin bazai tanka ba domin masoyin shi ne na gaskiya,wanda yake son ka tsakani da Allah ne zai iya kallon tsabar idanun ka ya faɗa maka gaskiya komai ɗacin ta,tabbas Kuma Gariti ya wuce nan domin ba tun yau ba yake bashi shawarar zama akan turbar da ta dace dashi amma ya rufe idanu yau gashi yana cikin wata irin kunya mai nauyi musamman ma ta iyayen ta,bai san yadda zai kalli mahaifiyar ta ba,ita ce kawai ayanzu yake ji domin ya san ya cuta ma yar ta Duk da ita ta buɗe ƙofa wa kan ta. Shiru ne ya ratsa su sai dai Kowannen su da tunanin da yake yi a cikin zuciyar sa. *** Kiran sallah ne na Azahar ya miƙar dashi daga kishingiɗen da yake bayan fitar Gariti daga ɗakin bayan sun yanke lokacin da zasu je su gidan su Jamil ɗin. Tsayar da tunanin sa yayi guri ɗaya ya fito ya ɗaura Alwallah domin tun fitar Gariti abu ɗaya yake yi babu ma abinda ke dawo masa a rai irin rayuwar su da Najiba kafin su zamo sirrin junan su. Har yanzu ganin abun yakai kuma kamar Almara ko ta tsuniya,labarin na su kamar ba Novel,ba zaka taɓa cewa a fili ya faru ba,sai dai shi ya san cewa akwai dubbanin su da ta su ma kalar ƙaryar inta fito sai ka rantse gaskiyar karyar ce saboda yadda suka zauna kan turbar.Saboda zai iya rantse wa a kullum ana rancen mota kusan arba'in ba tare da sanin oga Tanim ba,kuma motocin ba ƙana na nan bane irin wayen da matan gwamnoni da su kan su suke hawa ba ne.Irin dai ta masu kuɗin da suka amsa kuɗin su. Ana gama sallar Azahar suka haye mashin na Gariti sai ƙofar gidan su Jamil.Gida ne na ƙasa,sai wata ƙatuwar rumfa da aka killace da da kwano da wasu ƙofofi a cikin ta.Yara ne matasa da manya suke zazzzaune acikin ta suna karatu kasancewar Almajiran suna karatun rana Dan idan lokacin kaka ne bayan an cire abun gona iyayen yaran na kawo abinci abawa ya yan su sai ake basu da rana da dare su nemo,bayan an gama karatun maraice. Malam Ɗahiru Almajir dake Zaune a gefe ne ya ɗan saki murmushi bayan da dosowar su Jamil ɗin kafin a hankali ya miƙe ya isa inda suke. Tsoho ne ba chan ba sosai ba sosai sai dai ya girmi malam Abdul Basiɗ sosai.Dan ba na yau bane. Yana da gemun sa irin na manyan malaman karkara yayi jaa dashi sai dai irin jan nan ba mai yawa. Kamar sa da Jamil kamar an tsaga kara. Shima kuma baƙar fatar ce mai kyau. Zama yayi akan yar shinfiɗar shi ta fatar sa domin ɗazu yana cikin Almajiran ne sai yanzu ya baro chan ya dawo a salin wajen zaman sa. Ƙasa suka kai kafin suka gaidashi ya amsa musu cikin mutun ta juna tare da murmushi yana tambayar su aiki. Suna amsa masa da Alhamdulillah. Sai dai abinda ya ɗaure musu kai tambayar ya Iyali kuma ya da ya jefa musu aƙarshe wanda babu wanda ya amsa masa sai ma yin ƙasa da suka yi dukkanin su da kan su cikin fargaba. Murmushi malam Ɗahiru Almajir ya ƙara yi kafin ya furta " Allah ya sa lafiya dai naga alamar da magana a bakin ku ". Kamar kuwa jira Gariti yake yi ya buɗe bakin sa da daƙyar ya na furta " Eh to Malam magana ce mai girma ta kawo mu,A farko muna neman afuwar ku kai da Inna kafin na faɗi abinda ya kawo mu ". Murmushi malam Ɗahiru Almajir yayi kafin ya sauke Ajiyar zucia sannan ya furta." Kullum cikin yi muku yafiya muke Garba ".Dan haka ne sunan Gariti na gaskiya wannan Garitin sunan na ƙuruciyaa ne. Numfashi suka sauke dukkanin su jin yana furta Allah ya yafe muna baki ɗaya bayan gama zancen . Hakan ne ya bawa gariti damar furtawa a hankali. " Baba kamar yadda zan sanar dakai ina son ka ƙara yin haƙuri,mun san munyi kuskure kuma mun gane kuren mu Dan haka muke nema afuwar ka ". Malan Ɗahiru Almajir da yake sauraren su bai ce ƙala ba duk da ya ɗago kan zancen domin babu abinda bai sani ba. Ɗan kallon gariti yayi wanda yake furta " Jamil yayi Aure,tun wata ɗaya da ya wuce,shine maganar da muka zo yi dakai yanzu mun san munyi kuskure Malam A gafarce mu ". Malan kuwa da bai tanka ba haryanzu shiru yayi yana kallon su ɗaya bayan ɗaya bayan gama maganar ta Ta Gariti kafin ya furta " Yaro man kaza,wai me kuke tunani ne,ko kuna tunanin ku kuka haife mu ne,bamu muka haife ku ba Garba,duk shige da ficen sa babu wanda ban sani ba har iyayen daya saya suka nema masa Auren yarinyar na san da su kuma da izinin na suka yi hakan Ɗaurin Auren ka ne kawai Ban je ba ". " Mahaifiyar ka ce kawai bata san halin da ake ciki ba,Amma komai ina sane dashi,tun zuwan da ka yi a chan baya naga chanzawar ka sai na saka ma rayuwar taka alamar tambaya har na gano kana bin wata turba ce maara gaskiya, Dan haka na zura maka idanu duniya ta koya maka hankali,kuma Alhamdulillah tun ba,a je ko ina ba naga hakan a tattare da kai sai dai ban taɓa yi maka zancen ba saboda na san baka san ina sane da komai ba ". " Na yafe maka,kuma ina fatan haka a gurin mahaifiyar ka itama,kuma ina hasashen zata yafe maka kamar yadda na yafe maka,Allah ya shiryar da muna daku,ya baku ikon cin halaliyar ku,kuma ya sawwaƙa muku abun da ya tsananta a gare ku,Allah ya baku zaman lafiya mai ɗaurewa kai da Iyalan ka. ". Ameen gariti da Jamil suka amsa wayenda jikin su yayi mugun sanyi basu taɓa tunanin mahaifin na sa yana sane da komai ba,amma a mamakin su komai ya waka na akan idanun su.Lallai iyaye masu kulawa da amanar su ce. Nikam na ce. " Malam Ai Auren na su ne yake rawa yarinyar ta yi yaji saboda ta gano gaskiya". Gariti yayi furucin. Murmushi malam ɗahiru yayi sannan ya furta " ita Najibatullah ɗin ". Kai suka ɗaga masa sannan a hankali ya ɗan jinjina kan sa sannan ya furta '' Zata dawo in sha ALLAH,Lamarin su Ubangiji ne ya nuna ma kowannen su aya,Kuma ina fatan hakan ya zamo shiriya ga wasu Dan rayuwar da kuka dauka a baya ba mai kyau bace,Ni na dade da sanin Yarinyar yar wajen Malam Rabu,U ce,Sun taɓa yin karatu anan Achan baya a lokacin muna manyan su suna bi muna a karatu ma mun wuce su ". Shiru yayi bayan ya kai aya da maganar sa.Sannan ya basu izinin shiga Wajen Inna. A tare suka shiga sai dai dukkanin su mamaki ne har yanzu a cikin zukatan su,sai dai sanin waye malam da saurin ɗago mutun a duk yanayin da yake ciki sai basu damu ba suka yi ta jinjina lamarin. Bayan Gaisawa da Inna da ke ta murnar ganin su,inda take ta cika musu gaban su da da ruwa da yar fura mai ɗan sanyi dake a cikin ɗan tulu sai kwaɗon Tuwo da tayi ta ci Dan Malam baya cin sa. Ita ko saboda tana son kwaɗon koda Jamil ya ɗan kawo musu wani abun takan ci abun ta. Kai Inna ta ke ta gyaɗawa cike da mamaki bayan gama jera mata bayanin da Malam Ɗahiru yagama cikin natsuwa da kwantar mata da hankali,sai dai bai sanar da ita Komai ba bayan zancen Auren Hakan kuwa yayi ma Jamil daɗi sosai har hakan sai da ya nuna akan fuskar ta sa. Allah ya sanya Albarka ta yi masa,sa furta masa kalmar ya fiya sannan ta ce su kawo mata yar ta su gana da juna.Haka suka fice cikin ɗan annashuwa da farin ciki . Nasiha malam ya ƙara yi musu tare daƙara kwantar wa da Jamil hankali sannan suka fice daga unguwar gaba ɗaya. Jamil kuwa Nasihar mahaifin sa ce ta ƙara natsar dashi har yaƙara samun ƙwarin gwiwar fafutika akan dawo da matar sa. *** A ɓangaren NAJIBA kuwa da kuka ta shiga gidan turuss tayi hakan suma da suke ɗan aikace aikacen su a tsakar gidan. Ganin ta bazata ta faɗo cikin kuka hakan ya sa mama Hafsatu dake ta kallon ta kamar wadda ta ga sabuwar halitta ta furta " Lafiya ke kuwa NAJIBA kin shigo gida babu ko sallama,ga kuka kamar kin zo gidan mutuwa ".? Shiru Najiba tayi kafin ta share Hawayen da ya ke son silalo mata,bata iya tanka ma Mama Hafsatu ba sai ma kallon Mahaifiyar ta da take yi wadda itama take kallon ta ido cikin ido ƙirjin ta na wani irin bugawa tsoron ta Allah,tsoron Ace NAJIBA saki ne ya rabo ta da gidan ta. Hawaye ne suka ƙara silalo mata tana son mahaifiyar ta ta,rarrashe ta sai dai ta san hakan bamai samuwa bane. Wata zuciya ce ta ce mata ta je ɗakin Mama Hafsatu zata fi samun Natsuwa a chan hakan ya sa babu wani musu ta miƙa hanyar ba tare da ta ƙara furta komai ba. Hannun ta da aka riƙo ne ya san ya ta ɗan ɗaga kan ta ta kalli fuskar mamallakiyar hannun.Numfashi ta sauke ganin mai hannu.Mama Hasiya kuwa bata ce mata komai ba face jan hannun yar ta iZuwa na ta ɗakin domin ta san akwai abun da ke faruwa kuma bazata ta ɓa yarda ginin da ta fara ya ruguje ba, Dan haka ta kasa barin Najiba shiga ɗakin ta san cewa tana shiga channe zata zauna har komai ya dai dai ta Dan yanayin Najiba ɗin yayi kama da na wadda tayi fushi. Mama Hafsatu kuwa da idanu ta bisu har suka wuce idanun ta kamar su zubo ƙasa saboda harara.Sannan ta kyaɓe bakin ta. Tana jin Haushin rashin jin cikakken abun da ke faruwa wanda zata kama anan gurin. " Ƙilama sakin ta akan yi shine zata yi muna ɓoye ɓoye ta gado halin uwar ta ta ". Furucin Mama Hafsatu ne wadda ke ta faman wankin yan kayan ta da suka daɗe jiƙe har sun fara wari ma. Suna shiga ɗakin ta zaunar da ita kafin ta sauke a jiyar zuciya tana share mata Hawayen da suke ta tsiyaya akan idanun ta sannna ta ambaci sunan ta cikin sauti na uwa mai daɗi da kwantar hankali da natsuwa. " NAJIBA "!. _" ME YAKE FARUWA?,INA FATAN BA ABUNDA ZUCIYA TA KE SANAR MINI BA NE,WANDA TAKE HASASOWA A GARE KI,DAN ALLAH KAR KI SANAR MINI MAKAMANCIN IRIN ZANCEN DA NAKE HASASOWA "_ Ƙarin bayani 08069059746 Fa'eeh ✍️ Like,share,and comment. *_Typing_* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y _Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chann zaku samu tun daga farko.☝️_ *🌸RAYUWAR MU AYAU🌸* Ƙarya ko sakin Aure Gajeren labari Na Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _*Daga marubuciyar littafin*_ _*A Mafarki Nasanta*_✍️ And now _*Rayuwar mu a yau*_ P.25 Hawaye NAJIBA ta share bayan ɗan kallon fuskar mahaifiyar ta da tayi wadda ta fara sauyawa alamar tana cikin tashin hankali ba kaɗan ba.Amsar Najiba kawai take jira wadda take fatan ta kasance Alkhairi. Kuka ne ya ƙwace mata na tausayin kan ta,da yar uwar ta Nadiya da kuma na mahaifiyar ta badan komai ba sai tuna yadda ta nusar da ita rayuwar da ta je fa kan ta a ciki yau gashi rashin sauraren mahaifiyar ta ya kai ta ga jin kunya da kuma dana sani da kuma tulin baƙin cikin da take kan kwasa har yanzu. Mama hasiya bata rarrashe ta ba har sai da ta tayi mai isarta sannan ta ƙara share mata hawayen

Chapter 20 of 39