Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bata yi kewa ba na mijin ta ba shi ya sa take ta ƙoƙarin shanye Damuwar ta dan haka Mama Hasiya keta ƙoƙarin nuna mata saboda ta na kula da shigen ta da ficen ta taga ta koma sukuku wani lokacin zata zauna Falon ita kaɗai tayi ta tunanni kuma ta san bazai wuce na mijin ba ne. Itama zamewa tayi Ahankali tayi kwanciyar ta tana sakin murmushi musamman tuno da tayi yana nan tafe Anjima kamar yadda ya sanar mata kafin ya yanke kiran. RALIYA dake sauraren su murmushi ta saki itama tana gyara kwanciyar ta. Jamil kuwa kamar an biya masa hajji badan komai ba sai dan jin Muryar ta da yayi kewa ba kaɗan ba.Shi koda bata yi magana ba a hakan ma ta biya shi,babban Biya Ga Albishir Babba na Babyn su. Miƙewa yayi da sauri ya fice daga ɗakin inda Gariti ya nufa wanda ke zaune yana danna wayar sa shi kaɗai akan wani Dankali Zama yayi yana furta. " Albishirin ka Gariti ". Gariti dake kallon sa sake da baki ne ya sauke idanun sa daga kan sa yana mamakin inda wannan farin cikin na sa ya samo asali kodai Najiba yau zata koma ya tambayi kan sa. Sai kuma ya kawar da tambayar yana furta. " Goro " " Fari ko jaaa ". Jamil ya ƙara furtawa. "kaifa Jamilu ɗan iska ne,Nidai idan zaka faɗa mini ka faɗa mini haba sai kace wata mace". Gariti ya furta yana kallon fuskar Jamilu da take washe har yanzu. Hararar shi Jamil yayi yana furta" yan iska dai yau ina da lokacin ka ". Yayi furucin yana sakin murmushin da ke ƙara bayyanar da farin cikin da yake ciki. " Najiba na ɗauke da ciki har na sati Uku ". Jamil ya ƙara yin furucin. Gariti dake kallon sa kuwa baki ya washe cikin farin ciki yana furta. " Congratulations Jamilu mun kusa zama iyaye,Allah ya saukar da ita lafiya,ya raya,Kai kuma.ya baka abun kula da su.Amma waya sanar da kai ne ? ". "Ameen" Jamil ya furta cikin farin cikin addu'ar ta Abokin shi. Amsar tambayar shi ta ƙarshe ya bashi. Yana furta. " Ita ta tura mini saƙo da kan ta ,Harda haƙuri ta bani ma ". " Masha ALLAH,Jamilu an kusa angwancewa Angon geza,Allah ya ƙara haɗa kan ku Jamilu malam zai yi farin ciki". " Ameen ". Jamil ya furta. Kafin suka cigaba da fira yana tsara irin wankan da zai yi Anjima idan zasu tafi gurin Najiba. Su Najiba kuwa daga nan bacci suka yi gaba ɗayan su ba su farka ba sai wajajen la,asar. Suna tashi suka yi salloli sannan RALIYA tayi musu sallama saboda tana da practical 5_6. Tana fita itama Nadiya tayi wa Iyayen na su sallama bayan ta ci abincin da RALIYA ta kawo sannan ta bar gidan tuna cewa ko neman izinin sa ba tayi ba kafin zuwan ta nan ɗin. *** Da shigar ta gidan direct uwar ɗakin ta ta shige bata ma lura da yadda yanayin falon yake ba kamar a hargitse.Saboda Mai aikin ta kwana biyu ta daina zuwa bata san dalili ba sai ta barshi a bata da lafiya ne,ko wani uzuri mai girma,Dan haka ita take ɗan ayyukan ta wayen da zata iya,da girki. Sai da ta ajiye jakar ta da mayafin ta ta watsa ruwa sannan ta tuno da halin da take ciki zuciyar ta cunkushe ga wani irin faɗuwa da ƙirjin ta ke yi haka kawai ta rasa dalili tun bayan shigowar ta gidan. Ƙaramar doguwar riga ce ta saka mara Nauyi tana jin ta sakayau sannan ta fito falon tana tashin ƙamshin turaren da ta bulbula ma jikin ta saboda bata son jin warin sabulun da tayi wanka dashi,Haka kawai take jin ƙamshin turaren Tanim a tattare dashi dama ɗakin na ta gaba ɗaya. Abun da ta fara cin karo dashi ne a gaban ta ya san ya ƙirjin ta mugun bugu.Sai dai ta ɓoye hakan kasancewar tuno waye mijin na ta ta san ko mafarki ne wannan yana tare da wata mace ne a cikin gidan nan.Ƙurawa Bra ɗin idanun ta tayi kamar tana son gano wani abu a jikin ta. Tsaki ta ja mara sauti tana shure ta da ƙafar ta kafin kuma ta kai duban ta kan pant shima dai irin na bra ɗin shuri tayi da shi gefe ta na ƙara jan mugun tsaki zuciyar ta na wani irin ta fasa ga wani irin ƙyanƙyami da take ji na kayan. Kayan da ta gani ne wando da rigar jeans wayen da ta yiwa mai su farin sani ta kalla da kyau ko a mafarki taga kayan zata iya gane su saboda yadda mamallakiyar kayan take son su.Kirjin ta ne ya yi wata irin sarawa bakin ta ta rufe cikin tashin hankali tana son gasgata abunda ta ke kallo a yanzu da idanun ta. Shiru tayi tana nazarin yadda za,ayi a ce itace ɗin ce sai dai da sauri ta girgiza kan ta tana kasa yardar wa kan ta. Daɓass ta zauna a kan kujera tana dafe kan ta zuciyar ta na harbawa. Hawaye ne suka wanke mata fuska kafin ta share su da sauri tana kallon hanyar da zata sadaka da ɗakin sa inda taji motsi alamar fitowa za,ayi daga ɗakin. Sai dariyar da take ji tana doso ta Zubawa hanyar ta sa idanu tayi tana jiran isowar su dan gasgata abun da take hasashe. Ganin ita ɗin ce dagaske hakan ya sa ta miƙe da sauri hankali a ta she tana sauke numfashi a jere bakin ta na wani irin rawa na tashin hankali da mamaki da ya ƙara saka ta ruɗewa ta kasa ma iya ambatar sunan ta sai bakin ta dake cigaba da rawa kamar mazari. Da ƙyar ta samu bakin iya furta Shanty idanun ta na jiƙewa da hawaye masu zafi,wasu na sauka wasu na fita a kan kumatun ta.Ta kasa sanin irin tunanin da zata yi akan su ganin yadda Shanty ke ta ƙara maƙalƙale Tanim ɗin da ke nuna ko a jikin sa dan shi bai san kunya ba haka ma shanty ɗin da alama babu abin da ke damun ta bata ji komai ba sai ma ƙara baza kisisinar ta tana ƙara shige masa a jiki suna ƙyalƙyatar dariya babu Damuwar komai a tattare da su. Kallon ta Shanty tayi ta watsar a karo na biyu bayan kiran sunan ta da tayi murya a karye mai cike da baƙin ciki da ƙunci. Komawa tayi ta zauna akan kujerar daɓass saboda yadda zuciyar ta ke mata ga ƙafafun ta sun kasa ɗaukar ta saboda jin kalaman da SHANTY ta furta mata. " Honey yaushe Wannan Nuisance girl ɗin ta shigo ne,na zata wurin yawon ta na Otel zata kwana, Dan na Santa da Shegen yawon Otel Otel a garin nan babu wanda bata sani ba ". Inda tayi furucin kan ta tsaye tana bin ta da mugun kallo na wulaƙan ci. Hawaye ne suka ƙara wanke mata fuska Inda ta sanya hannu ta share su tana miƙewa tsaye tana kallon Su Shanty ɗin dake yiwa Tanim wani irin kiss akan wuyan sa yana Lumshe idanun sa. " SHANTY "! Ta ambaci sunan ta da ƙarfi Wanda hakan ya sa dukkanin su suka zuba mata idanu suna kallon ta kowa da irin kallon da yake mata. " SHANTY ya isa,na ce ya isa ". " Shin me kike son aikawa ta ne,ko nace me kika aikata ne,wace irin mace ce ke mara tunani,mara hankali da zaki bi biyi mijin ƙawar ki,zaki yi tarayya da mijin ƙawar ki,wace riba zaki samu a tattare dashi,me kike son ki girba,Kai cona da samun ƙawa kamar ki,dama na daɗe da sanin cewa ke ba ƙawar arziki ba ce,ki na cin dunduniya ta kuma na fahimci hakan tun daga kan shawarwarin da kika bani na fahimci hakan,Allah zai saka mini,dama Ance in zaka yi roƙo ka roƙi harda ƙawa ta gari bayan samun miji na gari " " Kin cuta Mani,kuma Allah bazai barki ba,muguwa Azzaluma mai fuska biyu, tangaririyar da aka saba akan hanya ashe ta dawo cikin gida na, karuwancin ki ashe ya biyo ta kai na,Sannan duka kaunar da kike mini ta ƙarya ce,kin cuce Ni matuƙa,koda yake ni na cuci kaina saboda Ni na saki baki na baki sirrin miji na ashe kin haka rame kin jefa Ni,Hmmm babu komai kan ki kika yiwa kuma ke kika jefa kan ki a rame bani ba,Zaki girbi a bunda kika shuka,wannan da kike gani ƙudan zumane shi ". Ta kai ƙarshen furucin tana nuna fuskar Tanim da ya zuba mata idanu kamar bai taɓa ganin ta ba.Sai dai furucin ta na ƙarshe ne ya sanya shi raba jikin sa da na SHANTY da ta ke cika tana batsewa saboda yadda Tanim ya riƙe ta ya hana ta zuwa ta ko yawa NADIYA hankali ta nuna mata zallar cutar da take magana da cin amana amma ko yanzu zata nuna mata ita ɗin riƙaƙƙiyar yar ta sha ce mai tangaririya a kan titi,karuwa mai lasisi. Da isar sa kusa da ita ya sauke mata mugun marin da ya sanya ta dafe cikin ta jin wani irin juya mata da yayi kamar zata zubar da yan hanjin ta. " Nine ƙudan zuma ko,niiii,zaki gani yanzu kuwa dama baki ga komai ba a ɗazu, a yanzu kuwa zaki ga komai da idanun ki,zan cije ki da cizon da bazaki taɓa warkewa ba kuma ba zaki taɓa mantawa da shi ba har ƙasa ta rufe idanun ki sha sha mara amfani,mayaudariya,makwaɗaiciya ke da mahaifiyar ki zaku samu abun da kuke so amma zaki ci wuya,Ina fatan kuma ki koma ki cire wannan ban zan cikin da kike kira da nawa sha sha kawai ban za,ballagaza,wannan da kike kira tantiriya ta fiki a waje na,ke ba komai bace face bola ta ko wane irin lokaci zan iya watsar dake ki shiga taitayin ki Karki ƙara taɓa mini Baby ta ko zagin ta,last warning ki cire cikin nan idan ba haka ba zan cire shi da kaina,kuma kin san zan iya ". Yana kai ƙarshen maganar ya ja mugun tsaki sannan ya ware hannayen sa biyu na farko da mai bi masa ya nuna idanun sa biyu alamar watch me. Bai bi ta kan ta ba duk da yaga halin da take ciki haka ya sunkuci Shanty a jikin sa da sauri ya wuce da ita Ɗakin na NADIYA yana sauke mata kiss mai zafi wanda take karɓa tare da mayar masa.Cikin jin daɗin abinda yayi ma NADIYA ɗin. Nadiya kuwa jini ne ya ɓalle mata nan gurin saboda wani irin juyi da cikin ta yayi wanda ya zo tare da zafin azaba mai matiƙar zafi a gare ta sai dai ba shine ya fi mata zafi ba irin marin da ta sha a gaban shanty ba da baƙaƙen kalaman da yayi ta furta mata wanda ya saka harda Mahaifiyar ta a ciki.Ga zancen cikin da yayi wanda ya fi ɗaga mata hankali sai tashin hankalin da ta samu kan ta aciki jin cikin na wani irin juyawa mata ƙara ta saki anan gurin tana yin ƙasa cikin zafin azaba dake ƙara mamaye ta ga baƙin cikin shigar su Tanim a ɗakin ta sanin manufar hakan ya ƙara girgiza ta.Cikin raɗaɗin azaba da zafi ta janyo wayar ta da kyar tana fitar da Numfashi kamar wadda ran ta zai fita. Tana dialing numban Najiba ta ɗaga. " Help me,Zai kashe ni ". Furucin da Najiba ta ji kenan bayan ɗaga kiran daga shi kuwa ta ji ɗiff babu magana ta gefen Nadiyan. Kuka ta saka mai ƙarfi tana ambatar sunan NADIYA cikin wani irin Tausayin ta. Mayafin ta, ta ja bata ko sanar da Mama Hasiya abinda ke faruwa ba kai tsaye, ta dai sanar mata Nadiya ce.Ta sa kai ta fice tana rusar kuka saboda hankalin ta yayi mugun tashi jin Nadiya shiru babu magana wanda hakan ya sa ta yanke kiran cikin tashin hankali da bugawar zuciya. Mama Hafsatu da idanu ta bi Najiba da ta fita da sauri bata ko kalli inda take ba,saboda a ganin ta kaso saba'in na abinda ke faruwa laifin Mama Hafsatu ɗin ne da saka hannun ta a cikin rayuwar da yar uwar ta take fuskan ta a yanzu. Tana fita kuwa ta samu napep ta tare ta yi sa,a ma iyayen na su maza basa nan sun fita. Direct gidan Nadiya ta faɗa ma mai napep ɗin. Nadiya kuwa dake cikin zafin zuciya koda ta yi maganar da ta furta ma Najiba da ƙyar ta iya furta ta saboda yadda zuciyar ta ke harbawa ga wani irin jini da ya ɓalle mata loka ci ɗaya tana gama furucin daga haka bata ƙara sanin abin da ke faruwa da ita ba,sai komai na ta yayi laƙwas alamar babu numfashi kwata kwata a jikin ta.✍️ Wayyo NADY 😥😭 Allah ya tada kafaɗun ki.😭😭😭 💞💋Daga alƙalamin Fa'eeh ✍️💞💋 Share,and react. Kuyi haƙuri da ganin update ya na zuwa ba yadda muka saba ba ina hidima ne ta ƙanwata shine dalili in sha ALLAH idan mun gama zamu koma kamar yadda muka saba.✍️✍️🙏 *_Typing_* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y _Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chan zaku samu cigaban update.Farkon labarin masu neman sai a mun magana a numban dana sauke ƙasan wannan page, Dan samun document.☝️_ *🌸RAYUWAR MU AYAU🌸* Ƙarya ko sakin Aure Gajeren labari Na Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _*TAFIYAR TAURARI HUƊU*_ ⭐⭐⭐⭐ _*ZAZZZAFAN LABARI DAGA*_ _*TAURARIN MARUBUTA HUƊU*_ *Taurarin marubuta huɗu masu aiki da hazaƙa da zallar ilmin Adabi* _*Daga marubuciyar littafin*_ _*A Mafarki Nasanta*_✍️ And now _*Rayuwar mu a yau*_ P.30 Har suka iso gidan kuka take yi babu ƙaƙƙautawa fatan ta da Addu,ar ta Allah ya sa Lafiya Nadiyar take saboda jin ta shiru. Da sauri ta shiga gidan tana dakatar da mai napep ɗin a nan ƙofar gida saboda ta san dole zasu neme shi. Da sauri ta shiga gidan har tana haɗawa da gudu sai dai hawayen na ta sun kasa tsayawa sai faman tsiyaya suke yi kamar famfo. Bata ko tsaya gaisawa da mai gadi ba ta Kutsa cikin falon. Ƙara ta sanya mai gigitarwa bayan ganin Nadiya kwance a cikin jini kamar bata numfashi kuma. Ruwa ta shiga kitchen da sauri ta ɗebo Dan ta yayyafa mata.Tana fitowa kuwa ta ci karo da su SHANTY da Tanim a half naked saboda dukkanin su zanen gado ne suka ɗauro a jikin su saboda suna kan aiki suka ji ƙarar ta,sun zata Nadiya ce sai dai suka ga akasin haka saboda ganin Nadiya kwance a gurin cikin jini wanda hankalin su ya ɗan ɗaga kar a ce ta mutu kuma ya zama na sune sila.Ganin Najiba kuma ya basu mamaki sai dai babu wanda ya nuna hakan akan fuskar sa.Ita ma Najiba turuss tayi tana ƙare musu kallo zuciyar ta na wani irin harbawa bakin ta ya kasa iya furta komai, take wata irin tsanar su ta shige ta da rashin ganin girman Tanim kwata kwata bata son ganin su bayan fahimtar abun da ke faruwa,zuciyar ta iya wuya ta kai ganin kofar da suke tsaye wanda ya tabbatar da ga chan suka fi to wanda ke nuna agaban idanun yar uwar ta suka shiga ɗakin,ko ta tarar da su ta san kuma shine silar kai ta ƙasa. Ruwan ta yayyafa mata tana runtse idanun ta da ƙarfi saboda yadda zuciya ke cin ta ji take kamar ta babbaka musu wuta duk su ƙone wai yau idanun ta ne suka gane mata SHANTY da tanim a tare ashe duk tsawon lokacin nan tana cin dunduniyar Nadiya ne biri yayi kama da mutum ita tasan zuwa gidan nan kullum da Nadiya take cewa tana zuwa da walakin goro cikin miya,Hawaye ta share masu zafi bayan ganin Nadiya ta ja Gwauron numfashi sai dai ta kasa buɗe idanun ta da suka mata nauyi sai hawaye da suke ta tsiyayar mata ta gefen idanun ta wayen da da ganin su kasan na baƙin ciki ne,ita kaɗai ta san abun take ƙullawa a cikin zuciyar ta ita kaɗai ta san zafin da take ji acikin zuciyar ta da irin wutar da ke ruruwa a cikin ta,ta baƙin ciki da ɗaci,Sanin yadda wannan zafi yake sai matar da ta kama mijin ta A irin Wannan yanayi na cin fuska da tozarci da wulaƙanci. Cikin farin ciki Najiba ta riƙa ta ta jinginar kan kujera sannan ta raɓa su SHANTY da suka yi shiru kamar an Manne bakunan su da gum sun kasa iya furta komai wata irin kunya ta kama su babu ma kamar Tanim da ya san yadda Najiba ke bashi girman sa da mutun ta shi. Rufe idanun ta tayi da mugun karfi kafin ta ɗauke su gaba ɗaya kan gadon,bayan ganin yadda gadon yayi kacha kacha kamar anyi wasan kura ɗakin ma gaba ɗaya an hargitsa shi ya chann za kamannni.Wani irin Tausayin yar uwar ta ne ya kamata ace lalacin har kan gadon ta bai tsaya waje ba,ya shigo gida,sannan duk ɗa kunan da ke gidan sai na ta ya ga damar shiga Dan tozarci da wulaƙanci. Allah ya kawo ma yar uwar ta mafita shine abun ta furta jiki a sanyaye bayan ta kwaso mata abun da zasu buƙata Dan ta kasa jan ta su shiga ɗakin ita kan ta ƙyamar shi take yi. Ɗai daga cikin ɗakunan dake falon ta ɗaga ta da ɗingishi da komai suka shiga sannan ta haɗa mata ruwan wanka ta shiga ta tsaftace jikin ta.Tare da sanya wa jinin maatari saboda har yanzu yana zuba sai dai ba sosai ba kamar ɗazu. Tana fitowa ta shirya tsaff cikin kayan da Najiba ta fito mata da su sannan ta sanya hijabin ta suka fice gidan,ba tare da neman izinin Tanim ba ko kallon inda yake babu wanda yayi dukkanin su. Nadiya kuwa ta kasa iya furta komai haɗiyar zuciya take ta faman yi kukan ma yanzu ya kasa fita baƙin cikin wannan cin amana take ta dunƙula,cin amana r ƙawar ta da ta san duka sirrinta.Hakan ya fi komai baƙin ciki da taɓa zuciya. Koda yaushe mu kasance masu riƙe sirrin mu,saboda gujewa irin wannan cin amana ko makamanciyar ta. Suna fita mai napep ɗin nan da ta tare bai ce ƙala ba saboda sun haɗu da mai haƙuri kuma dama ta sanar dashi komai tana da mara lafiya ne. Mai gadin da ke kallon ta cikin tausayi sai jera mata sannu yake yi har wajen ya biyo su saboda ya san akwai abun da ya faru saboda ya ga mai gidan tare da ƙawar ta da take yawan zuwa gidan.Shi tausayi Nadiya take bashi tabbas da ace yar shi ce da tuni ya raba Auren nan,ko da yake yana ganin iyayen na ta ba su san halin da take ciki ba.Da wannan tunanin ya shiga gidan bayan tashin motar ta ta su. Tafiya yar ƙalilan ta kawo su Asibitin da Nadiya ta taɓa zuwa. Kuɗi Najiba ta bawa mai napep ɗin sannan suka yi masa godiya. Suka shige cikin asibitin. Da shigar su kamar ranar babu taro direct aka lalabo file ɗin ta aka miƙa ma Dr.Abida Abubakar wadda yau ta kasance ma itace mai duty.. " Shiru tayi bayan gama duba Nadiya ". Aune Aune ta bawa Najiba ta je aka yi. Allah ya sa ma Ta fito da yan kudaɗe da basu san yadda zasu yi ba. Bata jima ba ta dawo tare da sakamako. Takardar ta kai wa Dr Abida har office. Dr. Abida Abubakar kuwa bayan karɓar takardar ta buɗe ta saka glass ɗin ta tana ƙare mata kallo Hamdala tayi sannan ta ɗago ta kalli fuskar Najiba da ke ta satar kallon matar wadda take ganin wasu kamanni na sani a tattare da ita. Ajiye takardar tayi sannan ta kalli Najiba ta ce " Mun samu tsayar da jinin,Sannan a binciken da kika kawo yanzu Akwai cikin jikin ta har yanzu,wannan ikon ALLAH ne saboda jinin da ta zubar dole ma yanzu zamu ƙara mata jini,na ɗauki nauyin nemo ma ta shi,Dalili kuwa shine saboda ta samu zubar jini sosai,Allah ya tsayar da abun nan,ai da farko na zata abun zubar da ciki ta sha kafin nayi bincike na fahimci cewa Razana ce ta sanya ta zubar jini saboda shock ɗin da ta samu ya so taɓa zuciyar ta ko yanzu bacciin da ta samu ne ya sanya bugun zuciyar ta dai dai ta". Ajiyar zuciya Najiba ta sauke sai dai ta so ace cikin ya zube gaba ɗaya kowa ya huta ya zama raba gardama. Ɗan murmushi tayi kamar yadda Dr Abida take sakin murmushi sannan ta furta" muna godiya Dr ". Kai Dr Abida ta girgiza tana cewa " Ai Nadiya ya ta ce babu abun godiya a ciki,kamar su Sabeera nake jin ta. " Muƙewa tayi suka fice zuwa ɗakin da aka kwantar da Nadiya ɗin. Jinin da ta ce har an maƙala mata shi ma saboda ta rubuta tun ɗazu ta bawa Nurses Dan ta san ta samu zubar jini. Da yawa kafin ma aka wo result ɗin sai kuma akayi sa,a result ya zo dai dai da hasashen ta. Duba ta ta ƙara yi sannan ta bar ɗakin. Najiba kuwa hawaye ta share masu zafi tana godewa wannan likitar mai mutun ci domin da bata san yadda zasu yi saboda basu da kuɗin sayen jini yanzu kuma bata tunanin iyayen su Maza na da jinin badawa tun da ba wani abun kirki suke.ci ba na gina jiki bugu da ƙari bata son ɗaga musu hankali suna zaman su ƙalau. Zama tayi tana bin ta da kallo cikin tausayin ta zuciyar ta cike da ɗaci da baƙin cikin abun da ta gani zallar cutar da aka yi ma yar uwar ta,abun ya taɓa ta Sosai ta ji ina ma ta illata Shanty ɗin da Tanim. Shigowar nurse ce ta sanya ta tsayar da tunanin ta tana kallon ta tare da yi mata " " sannu da aiki "Bayan ta zuƙe allura ta zuba wa Nadiya a cikin I v line ɗin ta.Iv injection kenan.Inda ta juye mata sedative drug yadda zata samu kwanciyar hankali tayi bacci isasshe.inda ta cika umurnin Dr Abida. " Dr tace ki zo ". Cewar Nurse ɗin kafin ta sa kai da niyyar ficewa. " Sister Ba kowa gurin nan,ba matsala ".? Najiba ta dakatar da Nurse ɗin da furucin. Murmushi Nurse ɗin tayi sannan tace. " Karki damu ba,abinda zai faru zan kula Miki da ita,jeki ". " Nagode Nurse ". Najiba ta furta sannan ta fice daga ɗakin ta bar Nurse ɗin da ta samu guri ta zauna. Numfashi Najiba ta sauke bayan gama sauraren tambayar Dr Abida. " Gaskiya likita bazan iya cewa ga abun da ya sanya ta razana ba,Ni dai kawai ina gida ta kira ni,Koda na zo na same ta kwance cikin jini,bayan ta farfaɗo shine muka yo nan ". Najiba tayi furucin. " Ba a yiwa likita ɓoye ɓoye kinji Nadiya na san cewa akwai abun da kike ɓoyewa,ba ki son faɗa dan haka ki faɗa,koda da shawara ce zaki samu a gare Ni,na ɗauki Nadiya matsayin yata har ke Dan duk na haife ku,sannan ciwon ya mace na ya mace ne.". Dr Abida tayi furucin.Najiba

Chapter 25 of 39