Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ake yi aga irin maganin da ya dace da ita wanda zai taimaka mata ita da Jazlan.Hakan kuwa ta bi Nadiya ɗaki inda ta tarar da ita tana ta rusar kuka A ɗakin Mama Hasiya da ta shiga ɗin,Najiba sai aikin rarrashi take yi ga Jazlan hannun ta sai wasar shi yake yi.Bayan ta gama ƙare mata kallo ne ta furta " Nadiya bawa baya taɓa wuce kaddaararr sa na tabbatar da shigowar ki rayuwar Sa Tsarin Allah ne,kuma sanadin shiriyar sa ce,a.kullum Addu, a ta ita ce shiryuwar sa,sai gashi ya shiryu a dai dai lokacin da komai ya kusa ƙure masa duk da Allah mai jin ƙan bayin sa ne nasan har yanzu lokaci bai ƙure masa ba idan ya dage da neman gafarar Ubangijin mu zai yafe masa,Ina roƙon ki ki yafe masa ko ba duka ba,sannan ki rage wata tsanar da kike masa,ko dan samun kwanciyar hankalin sa ya ƙara sa sauran rayuwar da ta rage masa,Amatsayi na na mahaifiya da ta fuskan ci jarabwa ta lalacewar ɗaaa nake roƙon ki,ba matsayin likita ba,bani da tsimi bani da dubara ta a shiryuwar sa,da ina da iko,Da tuni na daɗe da cire Sa daga mummunan ɗabi'un da ya jefa kan sa ko ince aka jefa sa,tun tashin sa na san ya taso cikin gata,a gurin mahaifin sa kasancewar shine namiji kaɗai a gidan na sa, Dan kamar yadda kika ga yayyen sa duka mata ne Allah ya bani,ita Abokiyar zamana bata taɓa haihuwa ba ma,wanda sanadin hakan da take tunanin kamar Ni na rufe mata hanya Dan ita ce farkon zuwa gidan,ta yi duk yadda zata yi ta karɓe shi daga hannu na tayi amfani da rashin jin maganar sa ta ɗaura sa akan abubuwan da basu dace ba da ƙaramtar sa,na sha kama sa yana shan Taba yana karami kafin ma a ya koma hannun ta,idan na fito nayi magana na masa faɗa Sai mahaifin sa ya hauni da faɗa bana son sa,Bana Tausayin sa,saboda shi kaɗai ne bai da abokin shawara sai ya ƙara sakan ta sa yayi masa gata fiye da sauran ya yan mu,ta kai ta kawo idan yayi abu sai dai na zuba masa idanu,idan naga abun da zan iya ɗaukar mataki ko zane sa sai dai nayi ta kuka aɗaki ganin ya kama hanyar lalace wa kuma mahaifin sa ya mini kashedin masa magana,ko faɗa sai takai har ya janye sa aguna yana nuna masa bana son sa,Daga baya ma sai aka ƙwace sa hannu na,Allah ya gani nayi iya yina sai dai hakan bai samu ba,kuma yana faruwa ne da ga lokacin da ubangi ji ya so faruwar sa ,na san an cutar da mu domin kuwa komai da ya ƙara lalacewa ta gefen sa akwai saka hannun ta daga baya na fahimci itace silar komai dan tayi amfani da sangar cin sa da rashin jin sa ta gama da rayuwar sa,kuma alhamdulillah mun barwa Allah shine zai muna maganin ta tare da tonuwar asirin ta,duk wannan abun kuma bance itace kaitsaye ba,kawai zargi ne,duk da zargi zunubi ne koda ya zama gaskiya amma zuciya ta ta kasa gasgata cewa ba ita bace ta ƙara ɓata mini ɗaaa a lokacin da tunanin sa yake a Badai dai ba dan ko makarantar kirki ta islamiyya mahaifin sa bai barin sa zuwa wai acewar sa suna dukan ya yan mutane ba akan ƙa'ida ba, nice nayi da ƙyar na koya masa wasu abubuwan tare da karatu,kafin komai ya idasa kubce mini,kai co na, ni da kaina na saki tarbiyyar ɗaana akan wata wadda bata da maƙiyi kamata ko ince kamar mu nida zuri'ata bata da burin da ya wuce kamar taga ƙarshen zuri'ata "..Tana kai ƙarshen zancen ta sauke ajiyar zuciya hawaye na silalo mata masu zafi da ƙuna. NADIYA kuwa da tayi shiru yanzu duk da ta taji ɗan Tausayin sa bata ji zata yafe masa ba kuma bazata bar hakan yayi tasiri aranta da zuciyar ta ba, bata jin zata yafe masa a yanzu. Shiru ɗakin yayi na ɗan seconni Bayan gama zancen Dr Abida ɗin. kafin ta ƙara furtawa a sanyaye " Zan Miki sabon Aune Aune,Zan ɗibi jinin ki ". Ba musu kuwa Nadiya ta bata hannu ta ɗibi jinin ta duk da zafin da ta ji bata nuna ba dan ita yanzu ta ce ta tsaida hawayen ta macen da aka saka sakin wulaƙanci a gadon asibiti tsakiyar naƙuda wane irin kuka kuma zata koma yi na zafi wanda ya wuce zafin dafin dake cikin zuciyar ta na cin zarafin da aka yi mata. Tana gamawa tayi musu sallaama ba tare da ta saurare ko zasu yi wata magana ba sannan ta fice gidan gaba ɗaya. Dukkanin su da ido suka bi ta har Mama Hasiya da ta fito yanzu dan tana jin komai daga cikin ɗakin sai dai bata son ta katse mata zance,ta so ta fi to ko shawara ce ta bata domin kuwa da ga yanayin labarin kasan ta haɗu da ƙaddara ita kan ta domin lalacewar Ɗaaa mummunar ƙaddara ce Babba babu mai fahimtar hakan sai uwar da ta tsinci kan ta a cikin wannan jarabawar.Tana fatan Allah ya ƙara bata juria da haƙuri da tawakkali kamar yadda tayi a baya. Zama tayi kusa da su Nadiya ɗin sannan ta ce " Nadiya "! Ta ambaci sunan ta kafin ta cigaba da magana tana furta. " Nadiya kiyi haƙuri kinji da ga yadda naji yana kuka nasan yayi nadama, kiyi tunani akai kinji babu wanda zai tilasta Miki ki yafe masa amma ki tuna Allah yana son masu yafiya yana tare dasu yana kama hannayen su,yana musanya musu da Alkhairii mai tarin yawa,a lokacin da suke cikin tsanani suka gode masa,su kayi tawakkali,suka yi riƙo da Sunayen sa tsarkaka ". Takai ƙarshen zancen tare da karɓar Jazlan dan lokacin wankan sa yayi ta shige uwar ɗakin ta dashi dama ta haɗa masa ruwan wankan sa dan ita ce mai yi. Shiru ne ya ƙara ratsa ɗakin sai sautin ajiyar zuciyar Nadiya da ke fita.Matuƙa jikin ta yayi sanyi amma bata ji zata yafe masa yanzu.Najiba ma bata furta mata komai ba sai ma wayar ta da ta janyo jin kira ya shigo wanda kuma kiran bai wuce na Jamil ba.Cikin shagwaɓa ta ɗaga tana furta " Sai yanzu ko,tun ɗazu nake jiran kiran ka,da badan kace kar na kira ba da sai na yi maka kira da yafi dubu ". Ta kai ƙarshen zancen tana barin falon zuwa ɗakin da aka ware mata yanzu wanda zata yi zaman jegon ta nan. Nadiya kuwa kishingiɗawa tayi fuskar ta na nuna zallar damuwa da ɓacin rai wani gefe kuma Tausayin Dr Abida dan bata jin Tausayin mutumin da take wa kallon azzalumi ne wanda take fatan ko a lahira kar ta haɗu dashi.✍️ *Mun hau gangara fa*🧘🧘 *GIMBIYAR TASKIRA CE*👑👑👑 Like,share,Vote, comments .✍️ *08069059746* CHAT ONLY PLEASE 🙏🥺🥺🙏 *_Typing_*📱 https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y _Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chan zaku samu cigaban update.Farkon labarin masu neman sai a mun magana a numban dana sauke ƙasan wannan page, Dan samun document.☝️_ *🌸RAYUWAR MU AYAU🌸* Ƙarya ko sakin Aure Gajeren labari Na Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg✍️ Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim *✍️TEAM TAURARI HUƊU*✍️ ⭐⭐⭐⭐ _Fa'ee BG_ *RAYUWAR MU A YAU* _Matar Habibi_ *NIKEH DA IKO* _Haandy_ *NIKKAH ( MARRIAGE FOR RENT )* _Oum Amjad_ *RAYUWAR JANNAH* <<<<<>>>>>>>> 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _*Daga marubuciyar littafin*_ _*A Mafarki Nasanta*_✍️ And now _*Rayuwar mu a yau*_ ©️®️#Firstlady#Fa'eeh bg#Gimbiyar Taskira👑 Eid Mubarak 🎊Ta qabbalallahu minna wa minkum.🤲 🤭Na manta ban muku Barka da sallah 😏 ba.Sai yau na tuna,and naga sallah bata ƙara sa wuce ba shine nace a haɗo ma Fa'eeh yan barkan ta da Sallah.🥺😅💔🥰 Tou Allah ya maimaita muna muna masu rai da lafiya🤲🤩😍. P.37 A ɓangaren Tanim kuwa fitar sa kai tsaye cikin motar ya faɗa jikin sa na rawa.Kan sa ya kifa akan steering motar yana sakin wani irin marayan kuka mai cike da da nasani,kuka yake yi wiwi gwanin ban tausayi abubuwa biyu da uku sun haɗe masa musamman yanzu da ya tuno yana ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki,Sai yaji duniyar ta ƙara yi masa zafi ga wata irin ƙaunar ɗan sa da Nadiya yake jin suna ƙara kutsa jinin sa duk yadda ya ke kwaɗaice da son ganin ɗan sa Nadiya ta hana,abun ya taɓa masa zuciya sai dai ya san tabbas ko mene ne ta masa shi ya nema ya san tabbas ya cutar da ita matuƙa cuta mafi muni da tozartawa kuma yana fatan wata rana ta yafe masa dan yanzu halin da yake ciki yafiyar ta ce kawai abun da yake buƙata itace zata rage masa raɗaɗin ƙuncin da yake ciki. Koda Dr. Abida ta fito ta same shi yayi shiru sai ajiyar zuciya da yake saukewa kan sa jingine akan seat fuskar sa tayi jaa duk da shi ba fari bane amma da ka ga fuskar sa kasan maza sun sha kuka.Bata ce masa komai ba na na kalmar haƙuri.Sai ma jiki a sanyaye ta ce masa " fito nayi driving ɗin ".Ba musu kuwa ya fito ya koma extra seat jiki a mace ya shiga ya zauna ya rufe murfin a lokacin itama ta shiga bata ce masa komai ba ta tada motar.Tunda suka baro unguwar yake ta faman sauke ajiyar zuciya da sauke numfashi mai nauyi dan zuciyar sa ce ta yi masa wani irin nauyi gingiriigim a hankali kuma ya dafe saiti zuciyar ta sa sai Numfashin sa ya fara seizing yana kakkatsewa kamar mai cutar asma,Ganin haka ya sa cikin tashin hankali ta yi parking motar ganin yanayin da yake ciki tana tsoron heart attack ya kama sa ko depression ya halakar da rayuwar da ta yi masa saura.Taimakon gaggawa ta bashi wanda da ƙyar Numfashin ya dai dai ta.Ajiyar zuciya ta ja sannan ta ja motar sai gida tana parking motar a dai dai sashen ta.Da taimakon masu tsaron gidan aka shigar mata da shi dan jikin shi yayi yaushi bazai iya takawa ba da ƙafafun sa.Lokaci ɗaya ya ƙara fita hayyacin sa. Ɗakin sa da yake sama a ka wuce dashi direct a kusa da nasu,ɗakin da take ta Ajiya tun shekaru da shekaru wanda kullum cikin gyaran sa take da saka hope zai dawo gare ta sai dai komai Allah yake tsara shi duk lokacin da take jira bai zo sai yanzu kuma a hakan ta gode ma Allah ta san zai samu damar da zai iya gyara ɗabi'un sa. Maganunnuka ta basa da zasu taimaka masa ya samu natsuwa Dan ta fahimci zuciyar shi ta kasa ɗauka ta,ta haɗa masa da sedative drugs,bayan haɗa masa shayi mai kauri take kuwa saboda maganin mai ƙarfi ne bacci ya kwashe sa mai nauyi. Allah ya kyauta kaɗau zamu ce Tanim.🥺 *** A gidan su Nadiya kuwa duk da basu taron suna gidan ya ɗan cika da yan uwa da abokan arziki na sashen iyayen na su da na su Nadiya ɗin.An ɗan yi girke girke haka ma dangin Tanim sunje gaba ɗayan su,Haka ma Hajiya Jamila ta kai jiki ita da Jaruma tare da wasu daga cikin ƙawayen su ire iren su. Duk yadda suke ta nuna isa da iko akan Jazlan ɗin, da a yanzu Mama Hasiya ta basu shi Babu wanda ya kula su har Ya yan Dr. Abida ɗin da suka fito ciki ɗaya da Tanim ɗin.Raliya babu Babu yadda zata yi da Badan haka ba da basu isa su Kalli Jazlan ba,Dan ko yanzu tilas mata aka yi ta miƙa sa ga kuma yanayin da take jin ta ba bu daɗi komai nata haka take jin sa kamar ba na ta ba marar ta na ɗan juya mata kuma ta kasa faɗawa kowa tun tana gida take jin haka Ibrahim yayi suje asibiti a duba ta tace lafiyar ta ƙalau haka ya zo nan ya ajiye ta a mota kasancewar yanzu yayi mota 406 Blue mai kyau Dan buɗe sai bayyanar masa yake ta ko ina,sai dai kuma tana tunanin harda tsoron da ya kamata na kasancewar yar uwar ta a ɗakin naƙuda tana tunanin duk tsoro ne yake addabar ta da n haka bata damu da abun da take ji a cikin jikin ta ba.Gashu Hankalin ta duk ba kwance ba saboda an hana ta zuwa asibitin ita da Nadiya da ta aza ƙwafar sai taje sai da malam Abdul Basiɗ ya tsawatar mata ganin abun harda koke koke Dan ita kan ta ta san irin wahalar da ta sha ta so ace ta je,domin ganin ta ke yi kamar idan taje zata rage mata wani abu na daga raɗaɗin da take ciki da azaba ta naƙuda. Najiba kuwa dake asibiti tare da Mama Hafsatu da Mahaifiyar Jamil dan da safe naƙuda ta tasar mata dan tun daren jiya take ta fama bata faɗa ba sai yau tun da safe da wahala ta fallasa kan ta.Haka aka kwashe ta aka wuce da ita asibiti,wanda da zuwan su aka ce naƙuda ce ta ta fara yi sannan kowane irin lokaci yanzu zata ta sowa gadan gadan. Sai da ta ɗauki kusan awa bakwai sannan Allah ya taimaka naƙudar ta yunƙuro kuwa gadan gadan saboda ta kai last stage 7_8 Cm dan yi take tana kwantawa. Cikin ikon ALLAH da taimakon ruwan karatu na Addu,a da mahaifin Jamil ya rubuto mata ta haife Yar ta mace lafiyayya mai kama da ita dan kaɗan ta ɗebo Jamil amma gaba ɗaya ita ce kamar tayi kaki. Haka Nurses Suka gyarata tare da yarinyar ta.Bayan bincike da Likitota suka yi babu matsalar komai daga ita har yar ta hakan ya sa aka mayar da ita ɗakin Hutu. Tun da suka ɗora mata yar ta take wasar baki bayan fitowar ta duniya take cike da farin ciki musamman ganin yadda yarinyar take kama da ita. A haka har aka zare yarinyar daga jikin ta wanda aka yi haka Dan taji ɗumin jikin mahaifiyar ta,Yarinyar kuwa ta lafewar kukan da take tsalawa ya tsaya Chak. Har su Mama Hafsatu da ke ɗan ƙoƙarin sakin jikin su suka shigo ɗakin bakin ta washe da murmushi kamar ba wadda ta fito daga ɗakin haihuwa ba. Masha ALLAH suke ta furtawa ganin tsalleliyar Jinjira mai kama da ita sak mahaifiyar Jamil baki har kunne kamar ta faɗowa ubangiji Hamdala take ta yi tana jinjinawa Ƙoƙarin Najiba tare da saka mata Albarka. Jamil ma da ya samu dawowa yanzu saboda wani kiran gaggawa da akayi masa a chan sabon kamfani da yake neman aiki,ya tsinci kan sa cikin farin ciki,fiye da wanda yake zo da shi dama da fargaba ya fita ganin yadda aka shiga da Najiba a labour room kamar bazata fito ba.Sai gashi yana zuwa ya tarar da labari mai daɗi sai kuma yanzu ya zo ya tarar da wanda ya fi wanda ya tsinci kan sa a ciki.Haka ya cire kunya ya rungume matar sa agaban su Mama Hafsatu sai dai su suka fara rigen gin fita Mahaifiyar sa nata mita wai bai jin kunyar su a gaban su yake wannan Shegen takar.Itakam Mama Hafsatu bata iya cewa komai ba sai ma yanayin da yar ta take ciki ya faɗo mata a rai sai taji ina ma ita ce ta tsinci kan ta a irin wannan farin ciki dan ta hango yadda Najiba take cikin farin ciki ita da mijin ta.Ajiyar zuciya ta sauke tana ƙaƙalo murmushi jin Mahaifiyar Jamil na cigaba da mita. A cikin ɗakin kuwa Najiba ce ta ce " Beb ".! " Uhmm " Ya amsa mata yana rungume da ita aka faɗa Jinjirar tana rungume a jikin sa. " Dani take kama kuma kace idan Ni ta biyo bakai ba, zaka mini kyau ta ta tukwuici mai tsoka ". Murmushi Jamil yayi yana furta " Na rasa irin kyautar da zan Miki Qalbi shi yasa kika ji na yi shiru kyautar da kika bani ta fi ƙarfin kowane irin tukwuici,Haƙiƙa kin bani farin cikin da ban taɓa tsammanin zan kasance cikin sa ba ,Nagode Miki matar Albarka,Uwar yaya na Allah yayi Miki albarka dake da yar mu,dama ya yan mu masu zuwa gaba ''. Shiru yayi bayan Najiba ta amsa da. " Amin ". " Yanzu dai Albishirin ki " . Ya faɗa " Kujerar Makka ". Ta bashi amsa. Dariya yayi yace " Zata zo in sha ALLAH,Karki damu wifey " Yaja kumatun ta cikin so da ƙauna yana ƙara furta " Kice goro fari " Ya kai ƙarshe Zancen cikin murmushi ganin yadda ta ƙara shigewa jikin sa tana sakin murmushi mai nuna tana cikin farin ciki mai yawa wanda ya ƙara tsintar kan sa ciki shima har yana jin ina zai saka zuciyar sa saboda jin daɗin da ya samu kan sa. " Goro fari " Ta furta tana ƙara cewa " Nidai a faɗa kome ne naji kafin nayi fushi,ko Zehra ". Tayi zancen tana shafa kan Jinjirar su dake ta bacci hankali kwance. Shima murmushin yayi kafin ya furta. " Na samu Aiki a wani Babban Company sun bani matsayin Cashier,Yanzu haka daga chan nake,Kuma a kwai wani ihsani da suke yiwa Sababbin ma'aikatan su,Suna baka maƙudan kuɗaɗen da zaka gyara rayuwar ka ta wadata kafin fara aiki dasu,saboda gudun musu zamba ko cuta acikin aiki Dan haka yanzu duba wannan kiga check ne ". Ya kai ƙarshen zancen yana miƙa ma Najiba da ta zuba masa ido kamar wadda ta samu wani sabon shiri na Bollywood mai kyau.Wani irin Amsawa jikin ta yake yi ta rasa mai ya kamata tayi farin ciki ko akasin sa,sanin da ta yi dai zallar farin ciki ne ta samu kan ta a ciki hakan ya sa ta mai da idanun ta akan takardar da ya aza mata akan hannayen ta ta check. Zunzurutun kuɗin da ke nutse aciki ne ya sanya jikin ta fara rawa zuciyar ta na wani irin kaɗawa bakin ta yana son yayi magana harshen ta ya ƙi bata haɗin kai,hakan ya sa kawai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya,bakomai ta tuno ba face rayuwar da suka so cilla kan su a ciki,ko ma tace su kayi a baya,Rayuwar da kullum kake zullumin ranar tonon asirin ka,rayuwar da kunya ke hana mai yin ta motsi, rayuwar da Allah ma baya son ta domin duk inda Zallar ƙarya take cunkushe Ubangiji bai tare da wannan wuri,ubangiji ya tsani ƙarya,ya tsani masu aikata ta,saboda ƙarya hanya ce mai shiryarwa zuwa wuta.Yau da ace dukkanin su sunyi haƙuri da tuni sun samu kan su fiye da irin farin cikin da suke ciki yanzu,Sai dai ta gode ma Allah da ya sa soyayya ta rinjayi zaman na su,da ace duk a ƙaryar suke kwance har ason junan su ,da duk basu kai ga wannan ranar ba,Yau wai Sune keda Zunzurutun kuɗi har Miliyan Talatin wannan wane irin Company ne haka da suke bada kuɗi haka kamar hauka dole taji a ina wannan Company yake kuma me ake sarrafawa a wajen sa,? dan tana son samun gamsuwa a cikin zuciyar ta,dan zuciyar ta ta kasa gasgata mata zancen da take ji kamar almara.Cikin share hawayen ta da suka kasa tsayawa wanda shima bai dakatar da su ba.Ta furta " Wannan wane irin Company ne,Ya Jamil Ni bana jin na yarda da su gaskiya ka ƙara bincike kan su an ya ba sai da mutane suke yi ba ko shan jinin mutane idan ka fara aiki a tare da su,su fanshe kayan su ta jinin ka su tsafe ka ". Murmushi ya ɗan saki Sannan yace " sanannen Company ne,Qalbi Company ne na matashin ɗan kasuwa,Mahaifin sa shine shugan ƙasar mu fa na yanzu,Sannan Dan Companyn sun zubar da irin wayen nan kuɗaɗe ai ba wani Babban abu bane suna da su kuma inada tabbacin na halak ne,duk da akwai maganganu akan arzikin na sa,wasu sukan ce na ƙasar mu ne ya gina kan sa da su,Cikakken sunan Companyn shine MMG CARS SELLING NIG LTD KANO,A branch ɗin da na samu nawa aiki kenan saboda yana da companona da ban daban na sarrafe sarrafe na abinci da na kayan amfani na sutura,a jihohi da ban daban,a waje ma ance har da inda ake ƙera motocin yana da su,lokacin da suka bani check ɗin nima sai da na fita hayyaci na amma tuna cewa wannan kyautar a gun mai companyn ba komai bace,wai ita ce ƙarama yadda na samu labari,hakan ya sa sai na saka wa zuciya ta natsuwa,Na so naga ogan na masa godiya,Amma an tabbatar mini ba,a ganin sa,duk wannan hidimar fa ance wayen da suka gansa a fili a companyn ƙalilan ne ko P.A ɗin sa wahalar gani yake yi bare shi.💋(KURMAN ƘADDARA)💋 # KK story✍️ Haka na haƙura na musu godiya jiki na a sanyaye dan sun min bayani mai gansarwa sai na ƙara tabbatar da ba ƙaramin kuɗaɗe gare sa ba,Ɗan muna jin labarin sa matuƙa a majalisa.Koda na cika aikin da na ga sun saka a online suna recruiting ma'aikata wanda muka gani a kafar social media ta facebook awayar gariti wanda tare ma muka cika sai dai shi bai samu ba,ban faɗa Miki ba saboda banji ajiki na zan fito ba dan tarin al'ummar da na gani a wurin interview ɗin da muka je kwanan baya bayan fitowar sunayen mu,mahaifina kawai na faɗawa sai kuma Inna saboda samun Addu,ar su kuma Alhamdulillah tayi aiki,gashi an cimma nasara,duk gwagwarmayar da muka sha a baya zata yi kamar bamuyi ba,mun yi rayuwa iri iri azaman mu wanda na san da dama yan mata da samari da zasu ji da sun samu labarin ta zasu ɗauki wani ilmi a ciki domin yadda muka samu kan mu karatu ne mai zaman kan sa da ya kamata ya shiga kan matasan mu duk abinda Allah ya nufa akan ka bai taɓa tsere maka sai dai idan ka sanya rashin haƙuri kamar yadda muka saka wa kan mu,munyi rashin haƙuri Najiba,mun so mu bijirewa Ubangiji,mun ma sa laifi,mun nuna ni'imar da yayi muna bata muna ba,mun nuna rashin godiyar mu afili,mun zamo cikin fushin sa Najiba,Sai dai Allah mai gafara ne,zuciya ce da sharrin shaiɗan suka angaza mu da son ƙyale ƙyalen duniya mara sa amfani,Yau gashi Allah yayi muna kyautar da babu wanda ya isa ƙwace ta idan ba shi ba,ya kuma ƙara muna da kyautar arziki na duniya kuma na halal babu karya babu zamba cikin sa,Dole mu godewa Allah. ". Shiru yayi sannan ya cigaba da magana " Nagode Najiba,Nagode,kin juri talauci na kin jura bayan kuma kin gano gaskiyar da take gaskiya,kin zauna da Ni da zuciya ɗaya cikin so da ƙauna,kin zauna a gidana da ko flasta bai da shi bare silin abinci kuwa na safe sai ya kai rana na dare sai ya kai ki safe a haka kika cigaba da haƙuri da Ni kika kyau Tata mini,ga kuma soyayyar gaskiya da take wahalar samu a wannan zamani, Nagode ƙwarai NAJIBA Allah ya bani ikon kai ki Hajji kamar yadda kike so a matsayin goron ki,Kuma Najiba ki sani Wallahi

Chapter 33 of 39