riƙo ta da ƙarfi.
Tanim dake bayan mota kuwa murmushi kawai yayi tare da kallon Nadiya yana furta " Me zan samu nan wallahi My Nadi a matse nake baza,a ɗan rage mini zafi ba " yayi maganar ƙasa ƙasa.
Murmushi tayi kafin ta furta " A motar ". itama ƙasa ƙasa.
Kai ya gyaɗa mata yana sakin wani shegen murmushi kafin ya jawo ta jikin sa yana nuna mata motar ma shi lafiya lau ne Agare sa. suka fara aikawa juna da kiss kamar wasu Mayu haka kake jin sautin sa na fita inda duk sun cika motar da ƙarar sa da nishin su Jamil kuwa dake ɗan hangen su ta madubi ganin abun bana wasa bane ya sanya shi sauke musu cover ta gurin mai kama da labule wanda ko sound ɗin ba a jin sa sosai.Gaban sa dake faɗuwa kuwa har yanzu yana bugawa yana fatan ba abinda yake zargi bane jin cikkaken sunan nasa da ya kira.
Najiba dake satar kallon sa ce cikin ɗan yanayin da ta fara tsintar kanta na aika aikar su Nadiya ta ɗaura hannun ɗaya akan Nasa inda da sauri ya janye nasa hannun yana mayar wa kaan steering motar tare da ɗan ƙaƙalo murmushi domin fahimtar abunda take nufi domin shi kanshi awannan yanayin da badan tsakanin sa da Allah yake ƙaunar Najiba ba kuma da Aure yana son ya killace ta agidan sa da babu abinda zai hanasa ko yin shan minti da ita.
Najiba kuwa numfashi ta sauke kafin ta furta "Ya Jamil ustazu ".
Murmushi yayi sannan ya furta" Najiba matar Ustazu shikenan mun raba sunan ".
Murmushi dukkanin su sukayi cikin wayen cewa dan ta ɗan ji kunya yadda ya nuna mata kai tsaye baida ra,ayi kan hakan wanda bashi ne na farko ba takan ɗan nuna masa wasu d'abiun wayenda take ganin Nadiya nayiwa Tanim ɗin.Saboda ita dai rayuwar ta Nadiya da take gudanar wa tana burgeta duk da ta san illar hakan tun da duk sun karanta sun gani.
Kuyi haƙuri banda isasshen chaji ne shiyasa jiya ban muku update ba kamar yadda na alƙawarta.
Yau ma ansamu kaɗan kasancewar Bamu da wuta tun da rana.
Faiza Almustapha ce 🤙
*Daga Alƙalamin fa'eeh Bg*✍️✍️
Sharing pls 🙏 vote, comment and react.
🌸*RAYUWAR MU AYAU*🌸
Ƙarya ko sakin Aure
Short story
labari da rubutawa faiza Almustapha
Daga Alƙalamin fa'eeh Bg ✍️✍️
Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin.
Bismillahir rahmanir Rahim
💪📚📚
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
> >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>>
💤A MAFARKI NASANTA WRITER 💤✍️
Free book
P.4
Not edited🙏
Har suka ajiye Nadiya da tanim agidan nasa babu wanda ya ƙara furtawa wani ƙala kowa da tunanin da yake aransa,ko restaurant shiga kawai yayi ya dawo mata abinda yayi ra,ayi ya bata suka wuce.
***
Ɗan kallon sa tayi yadda idanun sa suka chanza lokaci ɗaya ɗan romance kawai da sukayi ayanzu bayan shigowar tasu cikin gidan wanda tun afalon suka fara sai da halin sai dai ganin yana neman wuce gina iri hakan ya sanya Nadiya nemawa kanta mafita inda ta ƙwace kanta da ƙyar wanda tasan sun saba hakan dai dai taga alamar yau dagaske yakeyi dan da alama ko fyaɗe zai iya yi mata a stage ɗin da yake.
A hankali cikin shagwaɓa bayan gama zagin sa acikin zuciyar ta ta furta " Haba my boo Kai bazaka iya haƙuri ba Ni gaskiya na gaji gida zanje kaina ke ciwo ".
Idanunsa da suke arikid'e kamar wanda ya shawu ya kaɗa mata dan haryanzu ba komai yake ganewa ya furta cikin ƙanƙance idanunwana " Nadi ba kya Tausayi na ko,shekara nawa ana ta magana ɗaya amma kiyita guje mini sai kace mai wani mugun abu wani kallo ta sauke masa kafin ta yi ƙasa Muryar ta cikin shagwaɓa ta furta " Nifa ajiyar nake maka ka bari sai lokacin yayi ".
Jin kalamin nata hakan ya sanya shi yin mugun murmushi acikin zuciyar sa yana furta sakarya kawai zaki gane kuren ki badai kuɗi ba zaki ci su kam zaki sha wuya ina gama samun abunda nake so zaki komai a aikace Inda A fili kuwa ya furta " to shikenan my nad muje na kai ki gida Koh ai cikin murna ta faɗa jikin sa ta rungume sa kamar wata yarinya ta zata yayi fushi inda nan ma daƙyar ta ƙwaci kanta ta fice tana dariya tare da jan mugun tsaki bayan fitar Tata.
Ƙaton gidan take ƙarewa kallo kamar yau ta saba ganin sa komai nasa sai take ganin kamar yana ƙara mata kyau tana fatan ace ta shigo wannan gida ta malle ka sa ita da Babyn da zata haifa wanda take son inganta rayuwar sa ba kamar rayuwar da suka taso ba ta talauci duk da kuwa suna da rigima asiri agidan dan ba,a kwana ba,asaka wani abaki ba sai dai bai zama dole sai mai daɗi kamar yadda yanzu suka sabarwa da kansu bakin kwaɗayi har ya zamana basa iya cin abincin gidan kwara kwata.ko an tuƙa tuwo yadda aka ajiye musu shi haka Za,a kwashe sa.
Sallama sukayi bayan ya ajiye a ƙofar gidan sai dai bai wani tsaya sukayi doguwar magana ba yayi wa motar reverse ya kama hanyar sa kasancewar a tsorace yake hankalin sa ya kasa kwanciya so yake yaga yadda komai Zai kaya masa zuwa da safe.
Bayan shigar ta gidan kuwa da sauri ta haɗo kayansu inda ta fito cikin leƙe dan ta tabbatar idan babu shi akusa ko ya dawo bata sani ba hakan ya sanya da sauri ta faɗa cikin napep ɗin da ke yin wannan saɓatta juyatta da ita.kasancewar ta riga ta faɗa masa tun kafin su fita gudun kar Asamu matsala kamar juya da yaso kamata,inda ya tsare ta da tambayoyi.
🌺🌺🌺
Cikin murmushi ta kalli mahaifiyar Tasu sannan ta furta " ehh Umma yanzu zaizo yaune ranar da yake zuwa yanzu haka ma shirin nake yi ".
Kai Mama Hasiya da suke kira da umma ta gyaɗa kafin ta furta " Raliya kar adaɗe Dan Allah duk da nasan halin Ibrahim mutumin kirki,"
Murmushi Raliya tayi kafin ta miƙe tana furta " in sha ALLAH Umma ".
" Yawwa to Raliya ke ko ko yar powder ɗin nan bazaki mirza ba kamar ba mace ba mu Alokacin mu duk da babu irin wayen nan kayan muna ɗan saka ɗan kwalli sai kiga munyi tass damu ".
Murmushi Raliya ta sake yi akaro na biyu ce cikin yanayin hayaniyar ta sannan ta furta " Zanyi Umma ".
Murmushi mama Hasiya tayi kafin ta ƙara furta " Allah yayi Miki Albarka Rale le ta kuma ya karkato mini da hankalin shashar yar uwar ki ".
" Amin " Raliya ta furta.
Tana shigewa ɗakin su inda ta shirya tsaf kuwa cikin hijab ɗin ta madaidaici milk mai kyua wanda ya ƙara Haska baƙar fatar ta domin irin Raliya irin slim Black beauty ce Masha ALLAH kam akwai kyau dan zan iya cewa sai dai sununa mata haske ko shi dan suna haɗawa da na kanti ne.
A hankali ta fice tare da ɗaukar kujerun roba guda biyu inda tayi ta fita dasu da ɗai ɗai adashen na mahaifiyar ta.Sannan ta yiwa mahaifiyar ya sallama ta fice inda ta fita cikin jin dadi yadda Mama Hasiya ke ta sambaɗa mata Addu,oi.
***
Wata dalleliyar ce fara ta ratso layin inda ta haske dattijawan dake ta zaune bayan gabatar da sallah ta magriba suna ɗan taɓa kasancewar nan ne dai majalisar ta su awasu lokuttan.Duka zuba wa motar idanun su sukayi suna kallon ta sai dai sun san zan cen gizo baya wuce na ƙoƙi.
Sai dai su Nadiya suka gama taɓarar su sannan suka saki juna inda kuma hasken motar daga ciki akunnen yake kamar waje da suka haske tsofaffin nan daga ciki kuwa harda mahaifin ta Malam Abdul basiɗ da ɗan uwan sa malam Rabu'u.Sai dai dukkanin su kansu aƙasa yake tun bayan hango wani lamari da ke shirin faruwa acikin motar wanda suke ganin komai ƙwar idan ka zuba ido kuma kai mai lafiyar idanu ne.
Nadiya kamar ta ce ya kashe hasken ganin kamar iyayen nata sun ta kura Amma cikin jakancin ta kyaɓe baki tare da sharewa tana yin kamar bata sansu ba ma.
Shikan shi tanim lamarin yana bashi mamaki sai dai ko ajikinsa tunda ita bata iya kare mutunci ba tana gani yadda ya haske iyayen ga amma takasa yin ƙorafi kar yace zai rabu da ita ta rasa wata madogara.
Shiru yayi yana ƙara shigar da jikin sa anata kafin ya buɗe motar.
Wanda koshi sai da sukayi kusan minti talatin kafin ya buɗeta.
Nadiya ce ta fara fitowa ta gaban motar inda ta daama akan jikin sa take zaune dan haka bata wahalar da kanta da fita ta asalin ƙofar ta ba.
Raliya da Ibrahim ɗin ta suna tsaka da fira suka ji andalle su da hasken mota kafin kuma haske yabar kansu.Da farko shi Ibrahim bai gane ko waye ba ya zata ko baƙi sukayi sai dai yanayin yadda yaga fuskar Raliya wadda ke damuwa da yan uwanta sosai ta chanza ya fahimci ɗai daga cikin su ce.Fitowar Nadiya ta ƙara sanya tabbatar wa da kansa fitsarewar Nadiya da ake bashi labarin kasancewar malamin su ne na tahfiz kafin suyi graduaton da kansu,subawa zaman gida da yawon ta biɗi ɗi agari.
Raliya kuwa hawaye ne ya silalo mata ga kunya ga baƙin ciki da tausayin iyayen nasu da yan uwan nata.Sai taji duk gurin ta gundure ta musamman yadda taga Nadiya bayan ta fito ta gaban motar Shima Tanim ya fito yana ta hurar hanta sannan hannun sa ɗaya yana gugar hips ɗin Nadiya wanda kuma da gangan yakeyi kuma yasan tana jin sa tunda har ta ƙyale shi tana enjoying abun.
Ahankali kuma ya ɗaura wuyan sa akan nata tare da zagaye ƙugun nata gaba ɗaya ya haɗe da jikin sa sannan A hankali cikin Lumshe munafukan idanun sa da suke jawur tun ɗazu har sun ƙara runewa ya furta " My Nadi wannan ƙanwar taku ta cika shiru shiru ita bazata waye ba ne wai tafi son ta zauna da wanda basir ya rage na zaman banza a unguwa ,duk da kunce malamin islamiyya ne,for god sake Mai yaci mai ya bata yariinya ƙarama ".yakai ƙarshen zancen yana lashe baki kamar wani tsohon maye ya na ƙure Rakiyar da idanun sa kasancewar suna facing da juna sosai.
" Nace ta waye My boo taƙi gashi nan ta zauna da wanda ko ke ke ta arziki bashi da ita me akeyi da tsiya wai shi mai ilmi to ilmin zata dinga ci Dan tana sha sha naso na janyo ta taƙi dan kafaffiya ce daka ganta da ita ma ai taci arziki ta rabu da tsiya ".
Tanim dake jinta ayanzu ya ɗaga jikinn na ta sai ma Bin ta da yayi da wani mugun kallo wanda ita Raliya ta gani da idon ta akan idon ta yayiwa Nadiya kallon.wanda take ta fahimci kallon na mene bai wuce zancen ta yake awulaƙance cikin zuciyar sa ba.
Hawaye Raliya ta share da suka zubomata kunya nasake dabaibaye ta fahimtar hakan da Ibrahim yayi hakan yasanya shi ƙoƙarin furta.
Sai dai zancen Tanim ne ya katse shi inda yake furta " gata so innocent Babu ruwan ta".Yana gama furucin sai ya sauke numfashi tare da ƙure ta da idanunsa.
Ai kuwa cikin ɓacin rai Ibrahim ya miƙe yana jin zuciyar sa kamar zata buga ya kai tsabar idanun Tanim ya furta masa cikin " kai shasha ka fita sabgar iyalina Bazan lamunta ba ka kiyaye Ni duk abinda zaka furta kai da ita ballagazar ya tsaya iya ku ".yakai ƙarshen furucin yana ƙara haɗe ransa sannan ya juyo a hankali ya ce ta shi kije ciki zamuyi waya kuma bana son koken nan.
Yabawa Raliya umurni inda ba musu kuwa ta kwashi kujerun nan duka biyu duk da bata i musu ta faɗa cikin gidan hawaye shaɓa shaɓa gashi yar uwar ta tajawa kanta zagi abanza Ibrahim ya furta mata ballagaza wanda ita aka furtawa amma ita taji Haushin zancen da baƙincikim sa da ace ba Ibrahim ɗin ta bane da kowa ye sai ta mishi rashin mutun ci.Tunda ta lura shi wanda take tare dashi munafuki ne.Mai makon yaji Haushin kalmar da aka kira mata sai ma taga yana sakin murmushi.
Najiba kuwa duk da taji Haushin kalmar sai dai ta basar taƙi ce masa ƙala dan bazata manta yadda ya iya bulala ba a tahfiz.kuma mutun ne da baya wasa ko kaɗan da daliban da shiya sa haryanzu take ɗan shakkar sa.
Ibrahim kuwa wucewar sa yayi batare da yayiwa iyayen nasu sallama gani yadda Kowannen su yayi kasa da kansa.haka ya wuce ya bar layin cikin tausayin iyayen nasu Raliya da suka haɗu da mummunar jarabawa dan duk wanda aka jarabta da wayen nan irin yan mata sai dai muce Allah ya kyau.
A gurje sukayi sallama bayan ta ɗauki ƙaruwar trolley da yayo mata tsaraba da ita sai wasu manyan ledoji na kamfani haka ta shiga gidan cikin farinciki babu ko sallama da kaya niƙi kamar wadda tayi tafiya.
Kamar yaje ya gaida iyayen nasu sai kuma kawai ya Kada yana tada motar sa tare da barin unguwar tasu yana ƙara haske su da fitila tarr inda yanzu sun rage su huɗu kasancewar masu zuciya da haushi da ya cika su sun kasa zama gurin dan wannan abun vaƙin ciki ne ace gaka ga ɗan ka yana aikata abinda bai dace ba ka kasa cewa komai abu kamair aikin jinni.
Da shigar ta falon babu ko sallama mama hafsatu ta karɓe da yi mata lale marhaba domin dama ita take kira tasan yau zata ci daɗi hakan yasan ya bayan gama yi nata kirari n da ta saba tana fasa mata kai shi suka fara bubbuɗe manyan jakunnuna wayenda wasu a haɗe suke biyu.Inda cikin farin ciki suka taru da wanda Najiba ta zo dashi suka cinye kamar wasu Mayu kafin kuma aka buɗe ƙwmalashen Tanim suka saka gaba sai da duk sukayi nak sannan aka saka saura afridge.
Sannan aka fara buɗe tsaraba inda ta fito da wata haɗaɗɗiyar doguwar mai kyau a ledar farko ta kaya wadda aka rubuta wa Najiba murmushi tayi ta nunawa Najiba rigar mai haɗe agogon ta kamar irin abayoyin nan na manya mata.
Sai leda biyu Raliya tagani arubuce inda cikin sauri ta buɗe doguwar rigar wadda ke ta walƙiya dan ko ba,a faɗa musu ba sun san taji kuɗi bana wasa ba kam yadda ma aka jera duwatsun ta abun kallo ne sai ɗaukar idanu takeyi sai kuma takalma da jaka da yan kunne.Cikin mamaki suke kallon kayan kafin ta furta " Amma Tanim munafuki ne shida yace mini baya gane Raliya ma amota amma Mama duba kiga harda size ɗin ta da komai to gidan uban wa yasani".Takai ƙarshen zancen tana shirin fashewa da kuka ganin ko rigar Raliya tafi ta ta kyau da tsari.✍️✍️✍️
Ba yawa ayi manage ban da chaji.
Pls Ina batar Addu,arku yan uwa.
Allah ya biya mini da buƙatuna na Alkhairi da dukkan Musulmi 🤲🤲
Share pls vote and comment ✍️✍️
A wahtsapp channel ɗita sai Wattpad kawai nake posting ɗin sa idan kina ra,ayi ki yi following kuma ki riƙa yin react
Tabbas idan babu react da vote zan daina update nasa na ajiye book ɗin AGEFE.
Faiza Almustapha ✍️✍️
GIMBIYAR TASKIRA 👑.
Daga Alƙalamin
Fa'eehbg✍️✍️
Ƙarin bayani
08069058746
First lady🙌🙌🙌🙌🙌🙌🙌🙌🙌🙌
🌸*RAYUWAR MU AYAU*🌸
Ƙarya ko sakin Aure
Short story
labari da rubutawa faiza Almustapha
Daga Alƙalamin fa'eeh Bg ✍️✍️
Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin.
Bismillahir rahmanir Rahim
💪📚📚
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
> >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*💤A MAFARKI NASANTA WRITER 💤*✍️
P.5
Note edited ✍️✍️
À ɓangaren Raliya kuwa bayan shigar ta gida ta sakawa mahaifiyar ta kuka Mama Hasiya,inda ta lalllashe ta daƙyar Sannan ta sanar mata duk abinda ya faru a wajen da cin mutuncin da Tanim ya yiwa Ibrahim ɗin ta ga kuma kunyar da suka saka ta ji agaban sa tana tsoron wata rana yayi mata gorin haka duk da an san jarabawa ce kowa da kalar tasa,abun baƙin cikin ta gaban iyayen su.
" Kiyi haƙuri kinji yanzu tashi ga tuwo chan kici karki zauna da yunya kiyi haƙuri komai zai wuce kuma kibar damuwa da matsalar su malan lamarin su ba zan mishi katsalan da ba amma akwai alamar tambaya a ciki sai dai ba,a saurin yanke hukunci,Sai dai muyi ta yi musu Addu,a ALLAH ya shiryar da su kuma ya musu mafita damu da dasu baki ɗaya ".
Miƙewa kuwa Raliya tayi bayan ta share hawayen ta Amsa ma mahaifiyar ta da "Amin " sannan ta cire hijab ɗin da ta shigo dashi tana naɗe shi tare da wanke hannun ta sannan ta fara cin tuwon ta hankali kwance suna taɓa yar fira itada mahaifiyar ta.
"'''
IKon ALLAH dukkanin su suke kallo domin kuwa rigar kamar an gwada da jikin Raliya tun da duk sun san size nata na Abaya Alokacin sun taɓa zaɓo mata wata kafin kansu ya waye gurin yan gwanjo.
" ALLAH kuwa Bazan bada ita ba koda bata zanyi sai dai na bata wata daga cikin tsofaffi na"
Nadiya ta ƙara yin furucin tana janyo wayar ta dake gefen ta cikin ɓacin rai.
" Ikon ALLAH harda Raliya a yan tsarabar ashe yana gane ta duk da ba ta ma fiye fita ba daga gidan ba,To ai ya kyau ta ".
Mama Hafsatu ce tayi furucin kai tsaye cikin murmushi ganin yadda Najiba ke ta bin Nadiya da kallo da alama zancen nata bai mata daɗi ba.
" Hello boo kana ji na,Naga harda Raliya acikin masu tsaraba,ina mamakin kai da kace baka wani gane ta yanzu amma naga komai size nata tun daga takalmin har rigar ".
Ta ɓangaren Tanim dake a wani yanayi yana sheƙe Ayar sa da wata karuwar sa bayan ficewar ta ya furta mata cikin murya kamar mai bacci " Shine dalilin kiran Ni nazata ma kece zaki zo ki bani '' Ya iyar da maganar kamar wani wanda yayi gudu yana sauke numfashi
" Ba fa maganar wasa nake maka ba shin wai baccin ne har yanzu surutun da nake yi bai sake ka ba ".
" Kin fiye matsala nifa kawai kwatanta wa nayi da naku size ɗin saboda naga ƙanwar ku ce sai na yi komai kwatancin ƙaramin naku kaɗan shikenan kawai".
Murmushi ta saki tana furta " to shikenan na zata dai ko ka ƙare mata kallo ne da maitar nan taka".
Murmushi yayi yana ƙara sauke numfashi kafin ya furta " Bye zan koma bacci ".
Sannan ya katse kiran.
Bayan ajiye wayar kuwa suka cigaba daga inda suka tsaya ana ta ɗaurawa kai Azaba.
In da yake ganin fuskar ƙaruwar ta sa na rikiɗe masa tana koma masa ta Nadiya sai kuma ta koma ta Raliya.
ALLAH kayi muna tsari daga sharrin shaiɗan.🤲🤲🤲
***
A ɓangaren Najiba kuwa shiru tayi tana jin duka zantukkan da Nadiya ke yi Wayen da basu yi mata daɗi ba ko kaɗan saboda ko ba komai Raliya ciki ɗaya suka fito da ita kuma tana ƙaunar yar uwar ta dan haka sai bata furta komai ba domin daga farko har ta fara murna ita ma yar uwar ta zata saka mai tsada sai taga Nadiya ta nuna rashin son hakan.Sai komai ya fice mata arai na kayan da ace bata san masu tsada bane da ita ma bazata karɓa ba sai dai tace ta gode kawai.
Mama dake sauraren Nadiya ne tayi murmushi tana furta " Ke Koh Nadi baby ai wannan ba wani abu bane kawai bari akai mata ita ma ta sabun ta ko banza kina da buhu buhun su,kuma tunda ita ya sawo ma bari na kai mata kawai ".
Turo baki gaba Nadiya tayi kafin ta saki Murmushi dan taga signal ɗin da mama
hafsatu tayi mata.
Haɗa kayan ta yi acikin haɗaɗɗiyar ledan da suke sannan ta ɗibi yan chocolate da su snacks ɗin nan masu Shegen yawa da lemuka ta haɗa ta fice daga ɗakin.
< <<<>>>>><
" Assalamu alaikum Maman Najiba "
Mama hafsatu ce tayi Sallamar tana shigowa falon bayan an karɓa mata.
" Wa, alaikassalam,Barka da dare Mama Hafastu ".
Raliya ce tayi zancen cikin girmamawa Tana zaune akan sallaya bayan gama sallar ta isha'i yanzu.
Karɓa mata Mama Hafsatu tayi tana furta
" Ahh Raliya har Malamin islamiyyar ya tafi kenan ".
Kai Raliya ta saukar ƙasa tana ɗagawa Mama Hafsatu kan nata.
Murmushi mama hafsatu ta ƙara saki da faɗaɗa fuskar ta dashi tana zubawa Mama hasiya idanu wadda ta ɗaga hannayen ta sama tana ta kwararo addu,oin da baka jin asalin me ta ke roƙawa sai dai bakin ta dake motsi.
Ganin ta shafe ne ta juyo tana fuskan tar ta hakan yasa ta janyo kayan dake gefen ta tana A jiyewa a kusa mama Hasiya ɗin.
" Ah ah Yaya Hafsatu ke ce a ɗakin namu yau ". Tayi zancen tana sakin murmushi.Dan tana iya rantsewa an yi watanni huɗu yanzu da Mama Hafsatu ba ta shigo ɗakin na ta ba kasancewar ansamu duniya.
Mama Hasiya ce tayi furucin.
" Eh wallahi Arziki ne ya kawo Ni yanzun ma,Kinga kaya nan Tanim ya yo musu tsaraba daga Abiread (Abroad ) shine da y dawo tafiyar ya yo tsaraba harda yar ƙanwar ta su,Shine nace bari ko in kawo mata itama ta ɗan sabun ta ta Haska tun da naga bata ma da irin wayen nan kayan masu tsada haka,kin gansu masu kyau dasu,sai kuma kayan maƙulashe nace kema Kya ɗan motsa baki ayi mutun kullum kuka babu wani ɗan jin daɗi ga dai komai Allah ya Bamu ya ran nan na iyakar ƙoƙarin su ". Inda ta fito da kayan duka tana bubbuɗe su tare da nunawa Mama Hasiya da ta saki baki tana kallon ta.
Mama Hafsatu ce tayi zancen.
Murmushi ta saki kafin ta numfasa bayan watse kalaman na mama hafsatu da tayi Amfani da su gurin kwararo zancen wasu ta san da gayya ta furta mata su.kasancewar tun farko ta so su riƙa cin arzikin na yan yan su da yanzu ita sun zame mata jari bata rasa komai ba a ci mai daɗi asha mai kyau sutura ma gwargwado tana samu domin Tanim yana kashe ma Nadiya kuɗi sosai shima Kuma Jamil duka in yayo tsaraba yakan haɗo da wani abun yace abawa umma duka da har yanzu bai san Wacece mahaifiyar Ta ta ba.
***
" Kai Yaya Hafsatu ai babu komai ba abinda damuwa bane kin san ita duniya juyi juyi ce yau in baka Saka mai kyau ba agobe zaka saka abinda kake gani A hannun wani wata rana zai dawo kan ka,Rayuwa tana tafiya ne abisa ƙudurar Ubangiji Dan haka Amaryar masa kawai Raliya ta gode ,ko kuma Nadiyan ta ƙara. Wata rana zata saka wanda yafi wannan in sha ALLAH,Kin san Ance mai haƙuri shi yake dafa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 39