ƙara narkewa idanun ta sun cika da hawaye dan yar tafiyar da suka yi zuwa wajajen awon ji take kamar ta datse kafafun ta huta.
Kallon Ibrahim yayi kafin ya Furta cikin murmushi " Congratulations ".
" Matar ka na ɗauke da cikin sati Uku da kwana biyar,Wannan ciwon ƙafafun da take fama dashi cikin ya sakar mata shi kuma yanzu na rubuta mata maganin da zai rage mata nauyin su da ciwon,in Sha ALLAH zata samu sauƙi idan aka riƙe su,sannan ta dage da shan maganin da zai ƙara wa abun cikin lafiya da yawan zuwa awo,suma na rubuta mata.Sannan ta ciga da cin abincin da ke gina jiki.Allah ya saukar lafiya Congratulations once again ".
Yakai ƙarshen furucin yana miƙawa Ibrahim hannu da bakin shi ya kasa rufuwa.
Wani irin farin ciki ne ya ƙara rufe Ibrahim bayan miƙa masa takardar Da Dr yayi a yanzu inda ya duba ya ga komai gashi nan a rubuce kamar yadda ya faɗa.
Hawayen farin ciki ya shafe yana ƙara riƙe hannun Raliya kafin ya yiwa likitan Godiya kamar wanda ya biya masa kujerar hajji sannan suka wuce.
Ita kan ta Raliya ta tsinci kan ta cikin farin ciki sai ta nemi ciwon ta rasa farin cikin da take ciki ya ɓoye shi.Suna fitowa ya rungume ta tsamm a jikin sa yana sauke Ajiyar zuciya yana furta " Allah yayi Miki Albarka My Halal ".
Haka yake ta furta wa har sai da ya gaji dan kan shi sannanya sake ta ya na sakar mata kiss akan goshi sannan ya riƙe hannun ta suka hau mashin sai gida.
Ya kasa riƙe farin cikin sa hakan ya sa ya kira yayyen sa mata ya sanar musu take zance ya bi dangi haka ma ya kira Najiba Tayi farin ciki sosai kamar ita aka ce mata ita ke da cikin.Dan yanzu ya fara sakewa da ita saboda farin cikin Raliya duk da dama chan baya ba ƙin ta yake yi ba halin sune baya so musamman Nadiya.Najiba cikin farin ciki ta sanar da mahaifiyar su duk da ba wani sakewa suke yi ba har yanzu amma gwargwado suna magana lafiya,kuma cikin dubara mama Hasiya ke ƙara bata shawarwari da mata nasiha wanda kuma gwargwado tana ɗauka.Mama Hasiya tayi farin ciki sosai haka ma su Malam Rabu'u da malam Abdul Basiɗ mama Hafsatu ma ɗan yi murna.Nadiya ma da ta samu labarin ta tsinci kan ta cikin farin ciki.
***
Sai da suka dawo gidan ne ta zauna ciwon ya dawo sabo inda Raliya ta saka kuka dake bayyanar da yarinyar ta da ƙyar ta sha maganin ta da Rarrashin da komai kafin kuma zazzaɓi ya saukar mata sauƙin ta ma likitan ya rubuto mata na Zazzaɓin shima Incase duk da ba tace ta na jin shi ba amma yasan aikin sa ya san kowane irin lokaci mai ciki ba a rasa zazzaɓi a jikin ta musamman idan sabon ciki ne,kuma ga sabuwar mahaifa wadda bata taɓa ajiyar ciki ba.Cikin ikon ALLAH tana shan maganin bacci yayi awon gaba da ita duk da ana kiraye kirayen salloli bai hana ta ba sai ma gyara mata kwanciyar da yayi ya fice cikin farin ciki.✍️
Yanzu dai gwargwado ana samun dogon page.🖊️
💃💃💃💃
Ƙarin bayani.
08069059746
*Fa'eeh✍️*
Share fisabilillah 🙏
*_Typing_*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chann zaku samu tun daga farko.☝️
*🌸RAYUWAR MU AYAU🌸*
Ƙarya ko sakin Aure
Gajeren labari
Na
Faiza Almustapha Murai
Daga Alƙalamin
Fa'eeh Bg ✍️✍️
Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin.
Bismillahir rahmanir Rahim
💪📚📚
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
> >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>>
_*Daga marubuciyar littafin*_
_*A Mafarki Nasanta*_✍️
And now
_*Rayuwar mu a yau*_
P.22
Tun daga wannan lokaci NADIYA ta fara gudanar da rayuwar ta da rainon cikin ta,sai dai,dai dai da rana ɗaya bata taɓa samun wata dama ba ta cimma burin ta ta hanyar yin amfani da shawarar yar uwar ta.Yanzu cikin ta itadah Raliya ya kai wata ɗaya dan na Raliya ma ya ɗan girmi nata.Tanim da Shanty sai abun da ya yi gaba domin kuwa yanzu har ƙasar yake bari tare da ita ba tare da sanin Nadiya ba,wanda shine ya kawo mata sassaucin yar damuwar da take ciki musamman ayanzu da Najiba da take a bokiyar shawarar ta take cikin alhini da su kan su akan abun da ya faru sati biyu da uku da suka wuce.Tarayyar ta da Nadiya kuwa babu abun da ya chanza tana nan tana shaƙar cikin ta sai dai yanzu kamar an yiwa bakin ta linzami tara ge faɗa mata komai nata sai kaɗan,saboda ko ta faɗa mata babu wata shawarar kirki sai ma ta lura kamar ta na ƙara jefa ta rami ne.
Mu koma baya.
Tun a hanya Najiba take yiwa Jamil complain gaban ta na faɗuwa bata san dalili ba kamar wani abu zai faru da ita haka take ji.Har suka isa gida kuwa haka take sululu.Suna shiga gidan na su bayan wangale musu gate ɗin gidan ƙirjin na ta ya ƙara yin mugun bugu wanda sai da jikin ta ya ɗauki rawa da addu,oi da komi ta samu komai ya lafa mata.Jamil kuwa duk da yana kallon ta bai iya furta mata komai ba sai ma ɗan sauke ajiyar zuciya da yake yi a ɓoye.
Har suka doshi hanyar falon tana ƙara tsintar kanta cikin faɗuwar gaba da mutuwar jiki ta rasa dalilin da yake kawo mata hakan.
Suna shiga ciki ta fara bin falon da kallo kamar mai neman wani abu kafin ta raɓa Jamil ta hayewar ta sama.
Tana shiga ɗakin ta toilet ta faɗa saboda a gajiye take jin ta tana buƙatar yin wanka.Bayan ta ɗauro Alwallah bayan gama wankan ne ta ja hijab ɗin ta dake maƙale a wata hanger dake Ajiye a gefen gadon ta shimfida sallaya bayan ta gama yan shafe shafen ta.
Addu,oin ta, ta gabatar tare da yin Azkar kafin ta fara ƙoƙarin sauya kayan jikin ta Sai dai me tana buɗe sif ɗin ta dake shaƙe da kaya kamar wani boutique ya koma wayam kamar ba,a taɓa halittar sutura a wurin ba.Sai yan tsiraran kayan ta da take dasu na ta na kan ta da ta zo da su gidan.Amma babu ko ɗaya na lefen ta.
Sai da ta gama bin ko ina da kallo tare da bubbuɗe sauran Siff ɗin ƙirjin ta yayi mugun bugawa tare da mamaki da tsoron da ya shige ta lokaci ɗaya.Haka take bin lokokin da kallo wayen da ta wangale tsaff kamar an ce za,ayi lissafin kayan ciki.
Kallon sashen da Manyan akwatayyan suke suma wayam haka ta gan inda suke a jiye kamar ba,a ta ɓa jera su ba.
Ficewa tayi da sauri tana furta Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un tare da ambaton sunan Allah da ya zo bakin ta.
Har ta sauko falon hankali a tashe bata daina furta kalmar innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un ba ga hawaye shaɓe shaɓe akan idanun ta..
Jamil da ya ga saukowar ta hankali tashe ya na zagayen falon rungume da hannayen sa a ƙirjin sa ya juyo Yana kallon ta domin abun da yake tsammanin jira kenan yayi mamakin da lokaci ya ja har haka bai ga fitowar ta ba.
" An kwashe komai, Beb,Ya Jamil ɓarayi sun shigo gidan nan,basu bar mini komai ba wallahi ,sun kwashe,kuma ɓarayin expert ne masu makulli kaga babu wata alamar shigowa anan".
Cikin tashin hankalin da yake ɓoyewa ya Kalle ta da idanun sa da suka rune lokaci ɗaya..
Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un ya ambata lokaci ɗaya har sau uku kafin ya furta " Muje ɗakin na gani tabbas Indai haka ne sun ƙware domin ban ga alamar hakan ba,babu wata alamar dake nuna an shigo gidan nan,gaskiya wayen nan mutane ƙwararri ne".Yana gama furucin ya taka sama ɗin da sauri kamar babu a binda ya sani kan case ɗin.Bayan shi ta bi hankali tashe Dan ta ji zafin ra sa kayan duk da ta san cewa zai iya yi mata wani sabon lefen ana ta tunanin kenan.
Shiru Jamil yayi yana ɗan kallon ta ta gefen ido zuciyar shi na mugun harbawa tsoron yadda safiyar gobe zata kasance masa dan ya san ogan na sa yayi haƙuri sosai..
Da ƙyar ya rarrashi Najiba dake ta kuka kamar ranta zai fita,Ko shi sai da ya yi mata rantsuwar da ya sha ma in sha ALLAH Zai haɗa mata sabon lefe,sannan ta haƙura ta saki ranta.
Ta yi murna sosai sai dai duk da haka ta kira Mama Hasiya da Mama Hafsatu ta sanar Mata take kuwa labari ya zagaye unguwar su,an shiga Gidan Najiba ankwashe mata lefe domin Mama Hafsatu bakin ta bai da saiti ana haka ta faɗa gidan maƙota ta barbaɗa zance,take zance ya bi gari an kwashe mata lefe a daren mutanen unguwa suka yi ta shigowa suna yi musu Jaje.
Da ƙyar ta shirya ta samu ta lallaɓa ta kwanta,haka ma Jamil da ƙyar bacci ya kwashe shi da tunanikka kala kala.Tun da asuba tayi ya miƙe bai koma gidan ba sai sai da safiya ta waye,Koda ya koma gidan kuwa ta shirya tsaff kamar yadda ta saba.Taci adon ta tsafta sai dai idan ka kalli fuskar ta da kyau zaka tabbatar da cewa har yanzu tana cikin damuwar rashin damuwar rashin kayan ta da aka kwashe mata dan dauriya kawai take yi domin ita haka kawai take jin bata wani ji farin ciki ayanzu ba kamar na farkon ganin lefen na ta da zuwan sabon da yayi mata alƙawari..
Wanka ya fara yi da taimakon ta Sannan ya shirya tsaff kafin ya dawo dinning ana suka ci a bincin da ta girka musu.Sai da ya tabbatar da ƙoshin ta sannan ya furta mata " ki haɗa kayan ki zamu yi tafiya yanzu ta taso muna ".
Cikin mamakin haka ta haɗa kayan na ta wayen da suma suke da ɗan hasken su tsaff ta shirya su a cikin wata ƙatuwar bag da ta sako kayan ta sannan suka fice daga gidan tana ta murna domin ta tambaye shi inda zasu je ya sanar mata ƙasar zasu bari irin wannan zasu koma ƙasar da ke cike da sahara Ta yita murna sosai koba komai yau zata hau jirgi itama yau zata ji yadda masu kuɗi suke ji ya daɗin jirgi yake.
Kasancewar ya riga ya gama shirye shiryen sa har motar driver ya ja ta domin Tanim ya nuna yanzu yake son komai na sa shi ya sa ya turo drivern na sa ya kai su inda zasu je.
Tafiya Suka Yi Mai Nisa Wanda Cikin Dubara Ya Rufe mata idanu da furta mata shi zai shigar da ita cikin jirgi Dan ya san zata ji tsoro shi ya sa ya rufe mata idanu.
Haka ta yarda ta zauna da idanu rufe tana ta faman sakin Murmushi.
Har motar ta tsaya murmushi take yi Idanun ta rufe.
Dai dai wani ginin gida suka tsaya mai kama da kan go gida ne da yake a cikin ɗai ɗai kun gidajen da suke gurin,Domin da alama guraren sabuwar unguwa ce kuma wacce take ƙarshen gari domin ko ina tsit kake ji maƙota ma daga ɗan nesa nesa suke da juna.Sai bishiyoyin da suke zagaye da unguwar.
Kayan ya ɗauka a hannun sa ɗaya,ɗaya kuma ya riƙo hannun ta dashi suka cikin ɗan madaidaicin gidan da ko filasta bai da ita bare fenti. Sai wasu guraren da suke a sake suma dai kamar toilet ne da kitchen da aka ɗan rufe da buhu,da wani ɗakin da ban da kuma, Sai dai shima Asake yake kamar yadda toilet ɗin yake tsarin gidan dai gwargwado na talaka amma yayi kyau sai dai rashin kammala shine ya hana ganin kyawun sa da bayyanar da ainahin tsarin sa.Sai uban yashi mai kyau da yake ta haske da bawa gidan wani irin ƙamshi malale a tsakar gidan kwance anzuba shi yadda ya dace kana takawa ƙafar takarmin ka sai ya shige.
Wani ɗakin da yake gefe ya dosa da ita ƙirjin shi na mugun bugawa da wani irin tashin Hankali da yake ƙara tsintar kan sa sai dai yana ƙoƙarin ɓoyewa.
Ɗan labulen da ke maƙale da ƙofar da ko ƙauren babu ya hankaɗa suka shiga a tare .
NAJIBA da ke cikin wani irin mahaukacin mamaki ne tun lokacin da dogayen takalmin ta da ke maƙale a ƙafafun ta suka fara taka ƙasar dake shinfiɗe a gidan,Numfashi ta tare da saurin yaye Abinda ya ɗaure mata fuskar ta dashi.
A wani irin slow haka take bin ko ina da wani irin mugun kallo,kallo irin na ƙyama da yatsinar fuskar ta.Wanda take ɗan murmushin da yayi mata saura ya ɗauke a kan fuskar ta. Ƙaf.
Cikin mamaki haka take bin ɗakin da yake tallin tal da kallo.Ɗaki ne mai Girma Kwango anyi silin da Kwalaye manya a sama,wani gefen.bai samu ba kana hango Rufin kwanon ɗakin.
Tare da hasken da Ubangiji ya fitarwa Rana.Sai shima ƙasan an shimfiɗa masa ƙaton Ledar buhu ( Kalo )Wadda ta mamaye ko ina na ƙasan ɗakin da ke ɗauke da ƙasar yashi itama.
Sai wasu robobi dake a jiye a gefe da alama shi ya saye su dan yin aikace aikace na gida.
Tana gama ƙarewa ɗakin kallo ta kama hanyar waje da sauri ƙarewa gidan kallo take yi a hankali bayan fitowar ta.Wata irin yatsinar fuskar ta tayi ganin labulen dake maƙale a ƙofa shi kaɗai ko ƙauren babu.Labulen ma ya ji jiki kamar na gwanjo kuma gwanjon yan Naira talatin da biyar,irin wanda ya ci uwar sa kafin a fitar da shi.
Ɗakin ta koma ƙirjin ta na mugun bugawa fiye da jiya da kuma hanyar su ta zuwa Filin jirgin da bata san yadda a ka yi suka tsinci kan su nan ba.Zuba mai idanu tayi sai dai ta na cike da tunanin kodai Jamil ƙungiyar asiri yake idan ba haka ba ya za,ayi ta samu kan ta a nan sida zasu je Airport.
Cikin wani irin tsoro da ya shige ta ta ƙara matsawa a kusa da shi taana yin guntun murmushi kafin ta furta " Ya Jamil kar mu yi missing flyied ya kama ta mu bar nan, ".
" Ban san mai ya sa nake jin tsoro na shiga ta ba a gidan nan ,tun shigowa ta gidan nan,Wallahi har ɗan ƙungiyar asiri na kallo ka a yanzu dan ka razanar da ni ".
" Please Beb nidai ina son tafiyar nan kar a fasa mu tafi,Ɗan har na hango kaina a cikin jirgin,kuma Ni gidan nan ko a ƙauyen su A,i mai Aikin mu ban taɓa ganin sa ba,Share ta kar na samu cuta Dan Allah mubar nan ya jamil,idan ma gidan gona za ka gina ya kamata ka ƙara gyara gidan,ko ina nagan shi wani iri ".
Ta kai ƙarshen zancen tana sakin murmushi tare da ɗan ƙara shigewa jikin sa tana rungume sa da iya ƙar fin ta.
Jamil kuwa shiru yayi ya kasa magana sai ma runtse idanun sa da yayi,ya rasa ta inda zai fara,mai ya kamata ya furta,wannan ranar ce Gariti yake hango masa,bai taɓa hangowa kan sa ba sai da lokaci ya ƙure masa,bai taɓa tsammanin mutun yana rasa abun faɗa ba sai yanzu,da ya san cewa zai ga wannan rana da yaje da talaucin sa a gidan su NAJIBA sai dai kash komai ya riga ya wuce bakin Alƙalami na wannan matsaala ya bushe
,Kuma jiƙa shi zai yi wuya,bare ya sake mayar da zanen ƙaddara mai ido iZuwa ga fahimtacciyar ƙadddara,Sai dai bazai yadda amaimaita ba shi yasa ya amince da barin gidan da duk da bai amince ba dole ya bar sa tun da ba nashi ba ne,aro ne.
Miyan bakin sa ya haɗiye muƙut sannan ya furta cikin cije bakin shi da ƙyar ya furta " Ki Yafe mini Najiba na cutar dake,Ni talaka ne,talak,,karki rabu dani NAJIBA ta,koda ni na zamo talaka Karki gujeni,ki zauna dani ina son ki,Rabuwa dake Masifa ce a gare ni,ina son ki saurare Ni da kyau ki ji abinda zan faɗa Miki,kimini kyakkyawar fahimta nayi duk abinda nayi badan na cutar dake ba sai dan soyayyar da nake miki "...
NAJIBA dake kallon sa ido cikin ido bayan ta raba jikin ta da na sa tun da ya fara magana ta raba jikin ta da na sa.Tsintar kan ta tayi a cikin manyan kalaman na sa da suke neman fin ƙarfin tunanin ta.Dan ta rasa mizanin da zata auna su zuciyar ta wani irin rawa yake mata da bata san dalili ba sai dai a yanzu ta ɗaura hakan akan zantukakkan sa da suke shiga Kunnuwan ta.
Shiru Jamil yayi kafin kuma ya sauke Ajiyar zuciya ya cigaba sa magana yana kallon ta cikin idanun sa shima Dan ya san baza ta iya ɗaukar abun da zai furta mata ba.Cikin ƙarfin Halin da yayi masa saura yayi amfani dashi ya furta " Ki yafe mini Ni maƙaryaci ne,Ni mai laifi ne a gake ".
" Komai da kike gani ki ɗauke shi amatsayin mafarki ".
" Suna na Jamilu Ɗahiru Almajir,na kasance mai wankin mota,sai sana,ar tuƙin mota da nake yi,Ni ɗan talaka ne talak "...
DUDMM DUMMM
Haka ƙirjin NAJIBA ya bada sautin ta hanyar ɗagawar da rigar take yi da ke nuna alamar ƙirjin ta na bugawa da wani irin ƙarfi Bayan ratsa ta da zantukakkan nasa da suka yi da take sauraren su amatsayin Almara.....
Hmmmm
Dama bahaushe yace ƙarya fure take yi bata ya'ya.🥺Sai ku ga kamar ba haka zancen yake ba,ƙarya bata taɓa tabbata komai daren da ɗewa.Wata rana gaskiya zata yi halin ta TABBAS.🖊️
Ƙarin bayani.
*08069059746*
💋*Fa'eeh bg*💋
React kawai nake buƙata da comments.
Share fisabilillah 🙏
*_Typing_*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*_Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chann zaku samu tun daga farko._*☝️
*🌸RAYUWAR MU AYAU🌸*
Ƙarya ko sakin Aure
Gajeren labari
Na
Faiza Almustapha Murai
Daga Alƙalamin
Fa'eeh Bg ✍️✍️
Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin.
Bismillahir rahmanir Rahim
💪📚📚
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
> >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>>
_*Daga marubuciyar littafin*_
_*A Mafarki Nasanta*_✍️
And now
_*Rayuwar mu a yau*_
P.22
Wani irin bugu ƙirjin nata ya ƙara yi wanda ya haddasa mata rawar jiki da sauyawar idanun ta da suke da haske izuwa jaaa,inda take hawaye suka fara saukar mata wayen da basu da lokacin daina tsayawa.Alamomin da ta gani na iyakar gaskiyar zancen sa ne ya ke faɗa mata yasanya ta fahimtar yadda tunanin ta ya juya mata da yake nuna mata abun kamar almara.A yanzu bugun zuciyar ta ya tsananta ta tsinci kan ta a cikin mawuyacin halin da bata taɓa tunanin zata haɗu da hakan a rayuwar ta ba.
Shin me yake shirin faruwa da ni.
Ta furtawa kan ta a cikin zuciyar ta.
Idanun ta,ta sauke ƙasa daga na shi kafin ta share hawayen da ya silalo mata a kan fuskar ta.Da ƙyar ta iya buɗe bakin ta ta furta masa cikin ƙarfin hali da danasin halin da ta jefa kan ta da kan ta ta biye wa son zuciyar ta ta kai kan ta a inda bata taɓa tunanin ta samu kan ta ciki ba.
Dan Gara ace tun farko haka ta Auri abun ta, kasancewar ita ɗin ma ba yar kowa ba ce kamar sa da ta sani a yanzu.
" Na tabbata wannan zancen naka babu ƙarya a cikin sa,sai dai ka sani daga yau babu Auren mu yadda ka dabaibaye ni da ƙaryar ka,ka yaudare Ni to tabbas ka yaudari Auran ka,Ka bani mamaki Ya Jamil,ace duka tsawon wannan lokaci kana zaune a kan ƙarya ne,Me yasa baka zomin a yadda kake ba,me yasa ".
Kuka ne ya ƙwace mata na baƙin ciki ba dan komai ba sai dan tuna itama nata a sirin na gab da tonuwa zata ji kunya kamar yadda ta san a yanzu Jamil yake jin ta,ina ma bata biyewa son zuciya ba.,
" Ni na jawa kaina,da na sani da ban yaudari kai na ba,me ya sa zan Ari rayuwar da bata dace dani ba,me yasa zan biye wa son zuciya da tarin ƙawaye,mai yasa na yi kitson wance banyi gashin ta ba ".
" Kenan Yaya Jamil komai na mu na ƙarya ne,motar da na saka raina akan ta itama duka ƙarya ce,lefe na ma kenan ba satar shi aka yi ba ɗaukar shi akayi kamar yadda na ga an tsame kayana har da suke sababbi an kwashe ba companyn da aka haɗa lefen ".
Najiba ta yi wayen kalaman cikin zubar da hawaye masu zafi.
Jamil da bai san inda zancen ta na farko ya nufa ba ya Kalle ta da runannin idanun sa cikin tashin hankali,babu abun da ya ɗaga masa hankali irin zancen rabuwar Auren na su da take furtawa wanda har yanzu shi bai hango hakan ba,koda kowa zai taru akan sa,yana tare da ita mutu karaba sai dai ayi mai yi,Amma bazai taɓa sakin Najiba ba,Auren su babu saki a cikin sa.
Ƙasa ya bi ta shima daga inda ta durƙushe yanzu ya furta " Najiba soyayyar ki ce sila,ba komai ya kai ni tsunduma a rayuwar karya ba sai ke, kasancewar ki yar masu kuɗi ya sanya dole na bi Miki ta hakan ke da iyayen ki,domin na san a talaka na ba bazaki taɓa bani dama ba,bare iyayen ki saboda na san yadda a wannan lokaci masu kuɗi suka tsani Aurawa yar su ɗan talaka ko Aurawa ɗan su yar talaka sai ma suka shafe hakan ta hanyar yin ƙwarya tabi ƙwarya atsakanin su inda Wannan haɗin ya zamo tarihi sai kaɗan daga cikin su.
Ni kuma duk da ina taɓa ƙaryar sai dai ban kai sosai ba kamar yadda na jefa kaina a ciki yanzu,kuma duk saboda ke ne NAJIBA,Ni masoyin ki ne na gaskiya NAJIBA,tsoron rabuwa dake ya sa na ƙara bawa wannan rayuwar zama a littafin rayuwa ta ya zamo a cikin jerin fejika dake tsare a ciki,Najiba tun da ga iyayen da suka nemi Auren ki har companyn har motoci da duk wani abu da kika sani na kuɗi NAJIBA ba na wa bane,wayar hannun ki ce kawai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 39