yadda zuciyar sa ta kasa ɗauka kamar farko.Cikin tashin Hankali Dr.Abida take kuka tana ƙara jijjiga sa domin take ta nemi nata ciwo ta rasa.Gadon da take kai ta sauko aka maida sa kai sannan wasu Doctors suka fara basa taimakon gaggawa domin ta kasa yin komai zuciyar ta duk ta hirgitse babu abun da take tsoro a yanzu face rasa ɗan ta.Rarrashin ta Alhaji Abdulkarim da suke kira da Dady ya ke ta faman yi da ɗiyan na ta amma bata saurara ba, tare da samun natsuwar ta sai da ta ga ya samu bacci an saka masa drip.
Tare da bayanin da Drs ɗin suka mata wanda ta riga ta sani dama shock ne sai dai na yau ya fi muni matuƙa dan zai iya leading ga tsayuwar zuciya ta daina bugawa kwata kwata daga nan komai sai yayi collapsed sai a samu mutun ya tafiyar sa.Haka suka zauna Jugum kowa da saƙe saƙen da yake yi da jimami tare da Bin Jamcy da kalmar Allah ya isar musu,ya hukunta ta dai dai da abinda ta aikata a gare su da wanda take da niyyar aikatawa.
**Yau Tanim satin sa ɗaya a sibiti yana samun kulawa ta ƙwarai tare da magani masu kau na cutar su dan haka ya fara murmujewa sai dai da ka gan sa kasan daga jinya ya dawo domin babu wani ƙwari a jikin sa.
Haka ya cigaba da gudanar da rayuwar sa cikin yana ƙoƙarin dawo da komai kamar yadda mahaifin sa da Mahaifiyar sa suka roƙe sa yayi kar yayi musu saurin karaya,Yana da chance da zai gyara komai a haka kuwa ya fara ayyukan gaban sa cikin ƙarfin hali domin shi kaɗai ya san ƙarfin halin da yake yi domin kuwa har yanzu Nadiya ta hana masa ganin Jazlan domin sun samu labarin yana da cutar HIV,wanda itama sai yanzu ta gane dalilin ɗibar jinin ta da Dr Abida tayi,Sai suka same ta asibiti ta tabbatar mata da negative take bata tare da cutar,Sannan hankalin ta ya kwanta.Wanda nan take Ta tuno yadda Allah ya kuɓutar da ita bayan samun cikin ta abin ya same sa.Ta san ko nan kaɗai aka tsaya haƙƙin ta ya fita.Dan har ta fara saukowa amma tsoron ta kar ya cutar mata da ɗa ko ya manna masa ita da gangan ta hana masa shi kuma iyayen su na gani sai dai sun zuba mata idanu saboda sun saka Nadiya gaba sai da ta faɗa musu irin zaman da tayi dashi.Wanda rayukan su sun ɓace matuƙa sai dai ta kanas malam Abdul Basiɗ ya manna laifin komai Akan Mama Hafsatu faɗa ranar kamar zai bata kashi duk da haka kuwa sai da ya bata takardar ta saki ɗaya da tsufan ta ga kai wanda hakan ya saka ta cikin mayuwacin Hali tayi kuka kamar zata siƙe gashi idan ta je Jigawa Ba iya zaman ƙauyen nan zata yi ba haka dai ta tattara ta bar gidan saboda yace bai buƙatar ganin ko sahun ta ne ta bar masa gida,duk yadda Malam Rabu'u ke basa haƙuri bai ji ba har sai da ta bar masa gidan sannan saboda matuƙa ran sa
Ya ɓaci domin a binciken da ya ƙara yi duk wata yar kadara Tata ashe chan take kai ta ta sayar da ita take yi anakkashe,duka wasu tarkacen ɗakin ta da ta rasa da ke rasa ina suke zuwa gashi babu halin magana.In ta sayar sai ta je gurin wani banzan Boka mai sunan Malam wai.Hakan ya sa ya ƙara fahimtar ba haka ta bar su ba dama ya daɗe yana hasashen haka,ganin yadda shi kan sa yake wasu abubuwan da ko a mafarki aka ce yayi su ba zai yi ba, Dan da ace suna cikin hankalin su Ko sisi na Su Nadiya bazaa su taɓa ci ba,sai ma ɗaukar musu matakin da ya dace saboda hanyar da suka ɗauko ta neman lalace musu a gida, wanda har yanzu suka tuna sai sunji zafi matuƙa na rayuwar da ya yan su suka yi cikin rashin mafaɗi domin gasu da bakun nan su amma an hana musu furta komai,suna ji suna gani kayan taikai ci ya yan su na fita cikin shigar da ko ba ya'yan su bane suka gani da ita sai sunyi Allah wadai bare ma nasu na kan su.
Kaɗan ya riga Bai ja mata Allah ya isa ba saboda tabbas tana da kaso saba'in A lalacewar ya yan su dan itace gishiri a tsakanin su, Wanda shima malam Rabu'u shiru kawai yayi ya san duk faɗan da ɗan uwan sa keyi akan gaskiyar sa yake yi.
Abu ɗaya ya hana sa shine jan Allah ya isa da ta ke cin harshen sa.Babu abinda ya fi ɗaga masa hankali irin rayuwar da Tana sane yar ta na yi amma taƙi bata dama ko sau ɗaya taji komai duk yadda ta bibiye ta face ma barazana da tilastawa da ta bita da ita.Har hawaye sai da ya share da ya tuna da yanzu yar sa ta nakkasa ta zamo mara amfani nan gaba.A ranar kowa jikin sa mugun sanyi yayi,kuka kam Nadiya ta sha shi haka ma Najiba da ta ƙara jin komai a lokacin,Mama Hasiya ma karan kanta sai da ta zubar da hawaye na tausayin Nadiya wadda ya kamata ace yanzu tana tare da Mahaifiyar ta tana Rarrashin ta sai dai gashi baƙin Halin mahaifiyar ta ne ya jefa ta a halakar da,da Allah bai Fiddo ta ba da bata san ranar da zata fita ba daga wanann masifar.Haka ta zauna tayi Rarrashin ta.Ko su Jazlan da Zehra kuka suka yi ta yi saboda rashin sabo da hayaniya da basu yi sai suka ji abun wani iri yadda kukan iyayen na su ya cika ɗaki da ƙyar dai suka samu kowa ya natsu.Haka ma RALIYA dake gidan ta, tana cigaba da rainon Ya yan ta da suka yi diɓil diɓil da su kulawa ta ko ina,domin suna samun kulawa ta musamman saboda zaman su tare da surikar ta da kuma yar uwar Ibrahim ɗin, Sai da ta zubar da hawaye domin ana gama suna Ta koma gidan ta dama haka Ibrahim ya tsara shida mahaifiyar sa duk da Raliya gidan su ta so ta zauna amma ganin ga Najiba ga Nadiya sai mahaifiyar sa ta zaunar da ita gidan dama shi ogan haka yake so.
***
BARI MU WAIWAYI SHANTY.
A ɓangaren shanty yau kusan sati Uku kenan take fama da matsanancin zawo da kuma zazzaɓi mai tsanani ta rasa abinda yake damun ta.Da farko tayi zaton cikin da take dashi ne wanda ta bincika a kwanan baya,domin da zuwan ta asibiti shi aka fara Aunawa a cikin fitsari ganin yadda tayi wani faya yau da ita kamar mai sabon shigar ciki ta faɗa ƙwarai ba kamar yadda ta saba ziyartar asibitin da ta saba kai kan ta ba kasancewar anan ne Family Dr na su yake kafin ya bar ƙasar ya koma Turai da aiki nan ta saba.Sai dai a bayan fitowar result sun tabbatar mata da tana da shigar ciki ɗan wata ɗaya da sati Uku ta rasa Dalilin da ya sa ta kasa zubar da cikin.Ga abubuwa sun cunkushe mata domin tayi neman Tanim bata gan sa ba,Haka ma wayoyin sa gaba ɗaya a kashe suke domin tun Dawowar sa America ya kai komai na sa gefe bayan samun kan sa ɗauke da cutar HIV ɗin,daga farko har ya manta da shanty sai daga baya ya tuna ta, kuma yana da tabbacin ita kan ta bata rasa cutar Dan haka ya rabu da ita inta gaji da jira dole zata kama gaban ta.
Shi ya sa ya fita sabgar ta Dan damuwar kan sa ta ishe sa,duk da ya san bai kyauta mata ba saboda cutar na iya yi mata muguwar illa saboda rashin sanin tana tare da ita har taci jikin ta ta kai ta ƙasa.
Amma Damuwar da yake ciki ta hana sa komai..
Haka ta kwasa taje a asibiti rai a cunkushe saboda ramar da ta ga tanayi ta fara bata tsoro yadda kuka san yanayin Jikin gabon na farko haka shanty take sai dai a yanzu Yadda kuka san ta yi slimming irin na gabon ɗin haka ta koma,Sai dai nata bai yi munin na Gabon ba sosai amma ta san yadda take zagwanyewa muddin ta zauna haka bata je ta binciki lafiyar ta ba to duka kayan ta sai sun koma mata idan ta saka su kamar mariƙar lema da zane, shi ya sa ta kwashi kan ta asibiti cikin tsoron lamarin nata bayan cikin da ke jikin ta da ta ƙwallafa rai kan sa saboda mahaifin sa domin duk da ta san gidan su Tanim ɗin ta kasa zuwa ta fi son sai ta haife jaririn sai taje a yi wadda za,ayi taji dalilin sa na gudun ta da ɓoye mata.
Da ƙyar ta kai kan ta gida tun bayan duba sakamakon tests da aka mata Wanda ya kasance duk su Malaria,Typhoid.. Negative suke amma abu mafi muni da gani HIV yana positive cikin matuƙar tashin hankali ta figi motar ta ta bata tsaya saurarar bayanin Dr ba.Dai dai wata haɗaɗɗiyar gate ta tsaya domin bata ma san ta Kawo kan ta gidan ba yadda idanun ta suka rufe cikin matuƙar tashin hankali da bugawar zuci da bata san wane hali rayuwar ta take ciki ba ko zata shiga a yanzu,bata san yadda Zatayi manage na rayuwar ta da tayi saura ba tashin hankalin ta bai wuce abun cikin ta ba yadda zasu bar shi yayi maraici kasancewar ta san wanda yasaka mata cutar bai wuce mahaifin sa ne ba,domin tun da ta fara tarewa a gidan sa ta yakice kowa ne tarkace na gwalajen ta.Horn ta yi ta bugawa wanda take aka buɗe mata gate ɗin ba tare da bincike ba sanin motar waye domin motar Tanim ɗin ce cikin ɗai daga manyan motocin sa take jaa ita ta mayar abun hawan ta.
Idanun ta jazir haka ta faɗa sashen Dr Abida da ta gani Asake wanda take da tabbacin nan ne zata samu Tanim ɗin.
Daga Alƙalamin ✍️
FirstLady 🙌💔
A gafarce Ni jina shiru da kuka yi na koma schl C/A sun sako Ni gaba da lectures ga exams in the next two week zan fara.Tou shiyasa zaku ga abun shan ruwan tsuntsaye.Amma in Sha ALLAH zan yi ƙoƙari page ɗaya ya rage mu ƙarƙare kowa ya huta kafin a dawo wata gwagwarmayar nagde.🙏
Like,share,vote,and comment pls 🙏
Domin magana da marubuciya sai a tura saƙo ta ñumban dake ƙasa.Ngde🙏
08069059746
*_Typing_*📱
*TEAM TAURARI HUƊU*
⭐⭐⭐⭐
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
_Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chan zaku samu cigaban update.Farkon labarin masu neman sai a mun magana a numban dana sauke ƙasan wannan page, Dan samun document.☝️_
*🌸RAYUWAR MU AYAU🌸*
Ƙarya ko sakin Aure
Gajeren labari
Na
Faiza Almustapha Murai
Daga Alƙalamin
Fa'eeh Bg ✍️✍️
Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin.
Bismillahir rahmanir Rahim
💪📚📚
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
> >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>>
_*Daga marubuciyar littafin*_
_*A Mafarki Nasanta*_✍️
And now
_*Rayuwar mu a yau*_
P.40
# First Lady#
# Ya Sayyid
# Nadiya
# Najmil
# Raliya Ibrahim
# NimShant
# Happy Family
# Ending🎊
***
Sahiba dake zaune a cikin haɗaɗɗen falon ganin an faɗo musu babu sallama kasancewar kofar a sake take,Hakan ya sa ta sauke duban ta kan ta, bayan ta gama ƙare mata kallo ne ganin bata ma cikin hayyacin ta da kuma son sanin dalilin ta na shigo musu haka babu sallama ta ce " Malama daga ina ".?Jin magana daga sama dan bata yi zaton ta samu wani a nan ba,ta juyo da sauri, tana kai duban ta ga Sahiba dake zaune, tare da ƙara kallon ta bayan ƙare ma falon kallo sannan ta furta " Ina Tanim".?
Kai Sahiba ta gyaɗa cikin ranta tana furta wata sabuwa Dan ta san duk a gama ta wannan ɗai daga cikin yan matan sa ne.
Hakan ya sa ta bata amsa kai tsaye ganin alamar da rashin mutunci ta shigo " Yana wurin Koyon sallama ".Ɗan kallon ta Shanty tayi kafin ta nemi guri ta zauna tana yin ƙwafa,wanda ko ba,a faɗa mata ba wannan yar uwar sa ce.
" Baiwar Allah ni ba rigimaa ta kawo Ni ba magana ce mai muhimmanci na zo da ita,Sannan akwai abun da nake son tantance wa idan yana kusa ki sanar dashi na zo,ina neman sa kice masa Shanty ce ".
Sahiba har ta buɗe baki da niyyar yin magana sai ta ji takon tafiyar sa koda bata ga shigar sa ba ta san fita zai yi saboda yanzu safiyar ta waye kwata kwata iya ka ƙarfe goma na safe da wani abu kai yanzu.
Tsaye yayi ganin ta ya kasa ƙara sowa cikin falon yana jin kan sa na sara masa domin ya san akwai rigimar da ta zo da ita ,ko da bata faɗa ba ya san ta gano tana ɗauke da cutar HIV a jikin ta ne daga yadda ya ga duk ta koɗe ta faɗa ƙwarai.
Numfashi ya sauke kafin ya taka da ƙyar ya ƙara sa cikin falon yana zuba mata idanu ganin yadda take ta faman girgizar ƙafafu sai idanun ta da suka hauye suka yi jawur ganin sa da baƙin cikin da ta ƙunsa na sa na watannin da tayi neman sa.
Hawayen da take riƙe wa ne suka zama kuka inda ta barke da kuka gwanin ban tausayi fuskar ta cike da dana sani da baƙin ciki sai yanzu ta ƙara yadda haƙƙin Nadiya ne ke bibiyar ta, ta sanadin ta tarwatsa mata gidan Aure,bata ji kunyar cewa ƙawarta ce ba ta biye zuciya ta riƙa Bibiyar mijin ta mijin ma,lalataccen miji wanda ita kan ta sai yanzu take dana sanin yin tarayya da Tanim da ita kan ta ya so illata ta ta rayuwar.Kuka tayi mai isar ta kafin ta saurara sannan ta cilla masa takardar ta awon HIV da kuma ta cikin jikin ta,da take ɗauke dashi.
Babu musu ya Ɗauki takardun ta farko ya fara dubawa bai yi mamaki ba sai ma ta biyun da ta saka shi ɗago kan shi da sauri jikin shi na wani irin rawa da bugawar zuciya cikin kiɗima ya ɗago jajayen idanun sa yana furta " Dagske ne abun da na gani anan,kuma kin tabbata nawa ne "..
Wata ƙatuwar harara ta bishi da ita da hawaye jage jage ga fuskar ta.Hakan da tayi ya bashi tabbacin cewa na shi ne ɗin dagaske wani irin farin ciki ya tsinci kan sa domin ya fidda tsammani daga ƙara samun wannan rahamar tun bayan zuwan jazlan yake tunanin daga shi ya gama ganin jinin sa saboda babu macen da zata Aure shi a yadda yake ya kuma sani sai dai ko mai irin cutar sa.
Hawaye ne suka silallo masa masu zafi da ƙuna ya saka hannu ya goge domin ya san wannan ma wani ƙalubale ne shima ɗai daga cikin sakamakon sa ne na abun da ya aikata kuma sai yayi gwagwarmaya matuƙa dan kare mutun cin yaro ko yarinyar da basu ji basu gani ba.
A hankali ya buɗa bakin sa da ƙyar ya ce " Na farko dama na san kema kina ɗauke da cutar saboda nine silar ta,kuma na san cewa idan kika samu kan ki ɗauke da ita zaki ɗauki mafita wa kan ki,Na so na waiwaye ki amma Damuwar da nashiga ta hana Ni yin komai sai na zuba Miki ido,da nufin kowa ya kama gaban sa ashe abun ba haka yake ba kana naka Allah na na, yau shi ke da ɗaa A jikin karuwar sa,kuma Babbar Abokiyar matar sa tabbas haƙƙin Nadiya ya bibiyi rayuwar su gashi suna kan girban sa dalla dalla.
Shiru yayi kafin ya ƙara furta. " kiyi haƙuri karki zubar da cikin Nan ina son sa,ki bar shi mu bashi tarbiyya mai kyau bamu san abinda zai zama ba a rayuwar sa ta gaba ,kuma na roƙe ki ki yafe mini ".
Shanty dake kallon sa ganin shi kan sa duk ya sauya sai ta ji Tausayin sa ya kamata da kan su gaba ɗaya,ta san gaskiya yake faɗa domin kuwa Sun cuci Nadiya matuƙa musamman ita ta ci amanar Ƙawancen su yau gashi ta na kwasar ɗimbin abun da ta aikata wai itace ɗauke da cutar Ƙanjamau.
Kuka ne ta ji ya kubce mata na wannan sabuwar ƙaddara da ta same su tausayin Nadiya kuwa da na su kamar an buɗe zuciyar ta wanda shine yake ƙara ma kukan ta gudu tana kaico da rayuwar da ta kaɗa kan ta ciki, ko a mafarki bata taɓa tunanin zata zamo cikin jerin mara lafiya na duniya da suke fama da wannan cuta mai karya garkuwar jiki a take ba.
Lallai dole ta nemi gafarar Nadiya.Kuka ne ya ci ƙarfin ta ya hana ta ƙara sa zancen zucin da take yi zuciyar ta kamar ta fashe da baƙin ciki da dana sani mara amfani.Sai kuma yafiyar Ubangiji domin Allah mai jin ƙan bayin sa ne dan haka ta sanya wa ranta zata dage ta nemi yafiyar ubangiji.
Dr.Abida dake tsaye tana kallon da sauraren duk abunda ke faruwa ta sauke numfashi tana takowa zuwa cikin falon.Zama tayi kusa da Shanty ɗin cikin yanke hukuncin da zuciyar ta ta zayyana mata saboda tashiga tashin hankali matuƙa najin tana ɗauke da ciki wanda ke ba,a bincika ba ga shi nan ya bayyana a gare ta a matsayin ta na Babbar likita zata iya gane hakan kai tsaye.Sai dai tana fatan Ace na shi ɗin ne tunda ƙaddara ta riga ta gifta dole a yi haƙuri a karɓa a riƙe hakan ya sa zuciyar ta cunkushewa da zafi da baƙin ciki.A hankali ta furta " Bani takardar " Tayi zancen tana kallon Tanim da ya lura da zaman ta ayanzu kusa da shanty ɗin.
Miƙa mata yayi wata irin kunya na ƙara dabaibaye sa,da baƙin ciki yau shi ne da ɗan Shege har cikin gida kuma agaban mahaifiyar sa lalle dole yaji kunya hakan ya sa ya kasa kallon ƙwayar idanun ta bare sahiba da ta yi zugumm tana kallon kowa da komai da ke faruwa gurin.
Tana gama duba komai da takardar har ta awon HIV ɗin ta furta " Y"ata".!
Tayi zancen tana ƙaƙalo guntun murmushi na dole.Ita kuwa shanty dake kuka kan ta cikin ƙafafun ta,ta ɗago jikin ta a sanyaye fuska jage jage da hawaye har ta kumbura abinka ga fari da ya haɗe da na Company take fuskar ta tayi jaa kamar Jan tumatir.
Hawayen ta share da hannu ɗaya sanannn jiki a mace ta " Na,am " Bayan ta samu kan ta da amsa sunan.
Murmushi Dr.Abida ta ƙara ƙaƙalowa ta saki sannan ta furta " Kiyi haƙuri kin ji,Zamu karɓi cikin nan da yardar ubangiji kuma zamu masa gata tare dake ki daina kuka kinji ".Ta kai ƙarshen zancen tana share mata hawaye.
Ita kuwa Shanty ƙatuwar a jiyar zuciya ta sauke jin abin da Dr Abida ta furta saboda dama shine Babban tashin hankalin ta rashin karɓar cikin ko wani ya ce a zubar dashi a ta ke.Sai hankalin ta ya kwanta rabin Damuwar ta yanzu ta gushe.
Sai matsala ta biyu tana fatan ya kasance itama tayi nasara a kan su domin bata san ina zata saka kan ta ba da wannan cutar Dan ya riga ya gama da ita,ko ta auri wanin sa mai lafiya cutar da shi kawai zata yi.Dr Abida kamar ta karanci zuciyar Shanty ta furta.
" Ni likita ce,Zan ɗaura ki akan magani mai kyau da zai inganta lafiyar ki,kamar yadda na daura shi akai,sannan zan baki na kariya ga abun da ke cikin ki,Sai Alfarma ɗaya da zan roƙa a gurin ki,itace Ki amince bayan kin haihu a ɗaura muku Aure tare,ku zauna ku rufa wa junan ku a siri,domin muddin aka san kina ɗauke da wannan cutar sai dai a yaudare ki amma ba zasu taɓa Auren ki ba,Haka ma Son Shi ne yasa na ga tun da kun san juna Kawai a rufe zancen ku zauna ku rungumi juna,Allah zai saka muku albarka,Kar ku manta baku Auren masu Negative sai dai positive to da aje inda ba,asani ba Gara inda aka saba,na roƙe ki Karki ce A'a ".
A yanzu ma a Jiyar zuciya Shanty ta sauke tana jin kamar matsalar ta ƙare duk akwai ɗimbin damuwa a ranta dan sai yanzu abun da tayi wa ƙawartata ya ke dawo mata,ace a gaban ta take nuƙurƙusa taka sa taimakon ta sai ma shigewa ɗaki da tayi da mijin,ɗakin ma ɗakin ta, agaban ta lallai ta cuta ma Nadiya ta san haƙƙin ta ne ya fara bibiyar su ɗaya bayan ɗaya,Lallai dole suje su nemi gafarar ta ko zasu samu rahamar Ubangiji da natsuwar zuciya.
Bata furta komai ba bayan sauke ajiyar zuciyar ta da dakatar da zancen zucin ta sai ma hannun ta ɗaya da ta ɗaura akan na Dr Abida ɗin da ke riƙe da nata tana jiran amsar ta.
Sannan ta ɗan kalli sashen da Tanim yake wanda yayi shiru kan sa ƙasa haka ma Sahiba tayi shiru sai dai idanun ta itama sun ɗan sauya.
Kai ta gyada ma Dr Abida bayan ta dawo da kallon ta kan ta.
Murmushi Dr.Abida tayi mai sanyi cikin ɓoye Damuwar ta sannan ta yi mata godiya.
Sahiba ta sanya ta cika mata gaban ta da kayan karin kumallo sannan ta miƙe ta tashi ta bar falon zuwa ɗakin Dadyn na su.
Shiko Tanim bai iya cewa komai ba sai ma wata sabuwar damuwa da ta ƙara dabaidabiye shi musamman zancen Auren nan shi dama yana da burin karbar abun da zata haifa idan ya tabbatar da na sa ne.
Amma shi bai shirya ma yin Aure ba yanzu,bayajin Akwai macen da zai iya Kallo Amatsayin uwar ya yan sa bayan Nadiya,ita kaɗai ce yake yiwa wani irin so a yanzu wanda bai taɓa tsammanin akwai shi ba,sai da suka yi nesa da juna kuma ƙaddara mafi muni ta ƙara rarrabe su domin har abada bazai taɓa saka rai da Dawowar Nadiya a gare sa ba saboda cutar da yake maƙale da ita wanda ta sa dole sai mai irin cutar zai mallaka a matsayin matar Auren sa idan har yana son kare kan sa daga faɗawa wata halalar.Tashi yayi ya fice jiki a saɓule zuciyar sa kamar zata yi bindiga saboda damuwa,amma muddin wannan Auren in shi zai saka iyayen sa a farin ciki musamman mahaifiyar sa zai yi kodan ya faran ta musu.A yau ma kafin ya wuce Office sai da ya biya gidan su Nadiya kamar yadda ya saba yan kwana biyun nan sai ya aika ko Allah zai sa ta fito amma har ya gama tsayin sa bata fitowa,sai dai Dan kan shi ya bar ƙofar gidan، su Malam Rabu'u da suke ɗan gaisawa dashi sama sama idan ya gaishe su basu taɓa kwatanta saka baki ba saboda sun ji zafin abinda yayi wa yar su matuƙa shi ya sa sai suke cigaba da firar su kamar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 37 Chapter of 39