Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Nadiya ke yi ba wanda ba wani sosai take samun kan ta babu lafiya ba rashin ƙarfin jiki ne kawai sai yan ciye ciye na kayan ƙwalam irin su chocolate da su biscuits wanda dama tana da abunta. Haka ma uban gayyar duk da ya fahimci bata da lafiya ɗin bai nuna ba bai kuma yi mata ya jiki ba domin a cewar sa wannan matsalar ta ce ba ta shi ba.Shidai kawai in buƙatar shi ta tashi ta ta zai je ya ƙwata da ƙarfin sa,wanda shi ya fi komai ɗaga ma Nadiya hankali dan shine maganar da ta kasa furtawa NAJIBA a ranar da ta zayyane mata komai,bi ta hanyar da Allah ya haram ta da yake.Cikin jikin ta kuwa har yanzu bai san da zaman sa ba. A na haka ne suka bar ƙasar shida SHANTY aka lula duniyar turawa Dan baje hajar iskan ci. Zancen Najiba kuwa take ya zagaye unguwar kamar yadda aka kwashe lefen ta domin kuwa Mama Hafsatu babu inda bata shiga da zancen ba cikin maƙwabtan su. Take abu ya zama na gulma har ya Isa kunnen RALIYA dan har cewa ake yi Auren na ta ya mutu duk inda aka yi maganar sai ace Auren ta ya mutu. Lamarin ya tayar wa da Najiba hankali yadda ake ta shigowa ana sakar musu magana itadah mahaifiyar ta.Har ya yi sanadiyar saukar mata da zazzaɓin da yake damun ta tun zuwan ta gidan. RALIYA da kuka ta shiga gidan cikin tashin hankali. A zaune ta isko su a cikin falon Najiba ta buga tagumi ita kuwa Mama Hasiya shiru sai jan charbi take yi. Kallon idanun Najiba tayi wayen da suke jawur inda take wani irin kuka ya ƙara kubce mata na tausayin yar uwar ta.Dukkanin su babu mai ƙarfin halin Rarrashin ta shi ya sa duk da sun ga shigowar ta basu motsa ba zukatan su babu daɗi. Zama tayi a kusa da Najiba a hankali tana sauke numfashi da ajiyar zuciya wasu hawayen na sake sulalo mata. Sannan ta furta A hankali. " Adda NAJIBA abinda naji da gaske ne ya faru ko kuwa zancen mutane ne,duk da nagan ki cikin wannan gida a dai dai lokacin nan bana jin zuciya ta,ta yarda cewa abun da na samu labari gaskiya ne, Dan Allah kice ba haka bane Adda NAJIBA ".Hawaye ne suka silalo mata masu zafi bayan kai ayar zancen nata. Hawaye ne suka silo ma Najiba wadda take ta tsumayin yadda zata iya sanar da iyayen ta hukuncin da ta yanke kasancewar babu wanda ya furta mata ƙala a cikin su. " Kiyi haƙuri RALIYA kin san kowa da ta sa kalar ƙaddarar,kuma nayi ruƙo da tawa,duk da ta wa mai ido ce ". Shiru tayi tana sauke a jiyar zuciya da numfashi sannan ta ƙara furta " Nasan dama Dole zaki ji komai duk da umman mu ta kasa sanar Miki haka Ni ma , RALIYA komai zai wuce Ni na jawa kaina duk wannan zagin da nake sha Ni naja wa kaina,Ni na nema da kuɗi na, na yi abun da kowa zai mini Allah ya ƙara Allah wadai da ni,ki min Addu,a kawai nida Addar ki Nadiya ita kaɗai muke buƙata,yanayin da na ganki ya ƙara tabbatar mini da irin jin daɗin da kike ciki da talakan da muke kira wa mijin ki cikin rainin wayau Bama kamar Nadiya da ta raina su shida Ya Sayyid da take ganin su kamar tana iya taka su,ƙaddarar mu ce haka bamu da gurin tsere mata sai dai muce Allah ya sa mudace,kuma ya tsare na gaba,sannan ki yafe muna Dan Allah ". Tana gama zancen ta sauke numfashi Dan tana Tausayin yar uwar ta sosai gashi yanzu ma sun daina waya sosai tun ranar da ta sanar da ita halin da take ciki yanzu bayan dawowar ta gida,inda suka haɗe waje ɗaya suna ta kuka babu mai Rarrashi wani kuma tun daga lokacin kuma Nadiya bata ƙara sanar da Najiba halin sa take ciki ba saboda ta san magana ce mai girma . Nadiya ta daɗe tana mamakin zancen wanda har sai da tayi zazzzaɓi akan yar uwar ta kukan da ta sha ya zama ta mugun ciwon kai wanda har sai da ta sha ƙwayu na saukar da zazzaɓin da take fama dashi a lokacin wanda ya ƙara ƙarfi *** Jikin Najiba Raliya dake sauraren ta faɗa cikin tausayin ta domin zantukakkan ta sun ratsa ta sosai. Tausayin yan uwan nata ya kama mata zuciya duk da bata san halin da Nadiya take ciki ba amma ta shaidar akwai wata a ƙasa wanda hakan ya ƙara mata Tausayin ta bayan jin zancen na yar uwar ta yanzu. Share mata hawaye Najiba tayi kafin suka sakar mata murmushi tana sakin a jiyar zuciya.. Mama Hasiya bata furta musu komai ba sai murmushi da take bin su dashi tana godewa Ubangiji da ya sanya ma yan yan ta son junan su.. A haka suka haɗu suka ɗan taɓa fira sama sama. Kafin suka shige ɗakin su suka bar mahaifiyar su anan. Wadda ta bisu da idanu kawai cikin murmushi. Suna zama RALIYA ta riko hannun Najiba Ta furta. " Adda NAJIBA dan Allah kar ki ce zaki raba Auren nan ki yi haƙuri ki zauna da mijin ki,ki rufawa umma asiri yanzu zancen yana fita da gaske cewa an sake ki ɗin bayan wannan jita jitar za,a ƙara furta munanan kalamai kan umma ne da kuma Su Baba,dake kan ki,tun da naji baki ce komai ba kan rabuwar Auren ke da umma na san cewa Auren bai mutu ba,kiyi hakuri ki karɓi rayuwa a yadda tazo miki Adda NAJIBA,ki rage damuwa ". Shiru Najiba tayi kafin ta sauke Ajiyar zuciya sai dai bata furta ma yar uwar Tata komai ba sai dai murmushi da ta ɗaura akan fuskar ta. " Zan yi tunani akai RALIYA ". Ta furta a hankali bayan har Raliya ta cire tsammanin zata magantu. Murmushi ta saki tana kallon yar uwa ta. NAJIBA ma Murmushin ta sauke a hankali. Sannan kamar an tsire ta, ta tashi da sauri ta fice tana daɗe bakin ta Dan wani irin Amai ne ya taso mata wanda bata san dalilin zuwan sa ba. Nadiya ma bayan ta ta biyo da sauri sai dai kafin ta fita ma aman ya kubce mata. Nan tayi ta kwara kwara shi kamar zata amayar da kayan cikin ta. Da taimakon RALIYA ta samu ta kai kan ta a ɗakin na su. Cikin tausayin ta Mama Hasiya ke bin ta da sannu ita da Raliya. Tsaff RALIYA ta gyara gurin ita kuwa Mama Hasiya ta bata maganin amai wanda ta sha da ƙyar. Alwallah Raliya tayi kafin ta tada sallah kasancewar Isha tama wuce gashi bata samu tayi Sallah ba. Tana gama sallah sai ta koma wajen yar uwar ta a chan ta tarar da umman su na bata abinci kaɗan tana tsakura. Tana furta " Najiba sai andaure dama shi sabon shigar ciki haka yake shibinbiɗi gare shi,zaki samu lafiya ai ina ga wannan ne aman ki na ƙarshe dan Nima bazan manta ba a lokacin cikin Ƙi Haka nayi fama,Allah ya sauke ku lafiya,ya bada rayayyu masu albarka ". Tana zancen tana sakin murmushi bakin ta har kunne ga fuskar ta na fitar da wani irin kyau. Tana gama zancen kuma ta miƙe tabar su nan. Murna Raliya tayi ta tayi har Ibrahim yazo ɗaukar ta domin bata ma nemi izinin shi ba sai da ta iso gidan,ta kira shi ta bashi haƙuri,kasancewar hankalin ta tashe yake ta kasa ko kiran shi ta kwaso ƙafa sai gida. Ya jikin yayi wa Najiba da kuma jajen abinda ya faru domin babu abinda bai sai Ni ba sai dai bai taɓa faɗa ma RALIYA ba kasancewar ɗan ƙaramin cikin dake jikin ta bai wani samu ƙwari yadda ya dace ba,baya son ya ɗaga mata mata hankali. Najiba cikin kunya take amsa wa da Amin na Addu,ar da ya riƙa jera mata,kunya bibbiyu ga wulaƙancin da suka yi mishi ga kuma kunyar da take cikin ta.Sai ikon ALLAH take ta kallo yadda Ibrahim ya koma kamar wani Bature yayi ƙiba daga nin sa kasan akwai natsuwa tattarare dashi kamar dai yar uwar ta. *** Najiba kuwa cike yake da mamaki da al'ajabi,na wanzuwar cikin na ta sai yanzu ta tuno da rashin ganin baƙon watan ta Ashe shine sila,ga ciwon kai da barci ashe shine ke son bayyana.Sai taji kamar a ce suna tare da uban yaron sai dai ta san hakan ba mai yuyu ba ne.Tuno da Jamil ɗin da rayuwar da suka yi a baya dake yawan ta so mata ta sauke numfashi Dan tayi kewar sa saboda ta rufe duk wata ƙofa da zata basu damar haɗuwa ko shiga gidan duk yadda ake aikowa Ga Jamil nan a ƙofar gida yana kiran ta ta rufe Kunnuwan ta,kuma iyayen ta sun zura idanu akan Ta lokaci kawai suke jira. Mama Hafsatu dai bata ga fuska ba duk da tana iya ƙoƙarin ganin ta shige zurumm a cikin lamarin,sai dai Mama Hasiya ta rufe ko ina. Numfashi ta sauke tana shafa ɗan ƙaramin cikin na ta tare da binshi da Add,oin kariya.Hawaye suka silolo mata hannu ta sanya ta share hawayen Sannan ta miƙe ta yiwa yar uwar ta da ke ta mata Sallama itadah daga chan falon, Wayen da ke Falon su da Mama Hasiya kasancewar ta dawo ciki ita.Su Malam Rabu,u ba su kai ga shigowa ciki ba suna ɗan shan iska a wajen. A haka suka bar gidan RALIYA naji kamar kar ta rabu da mahaifiyar ta da yar uwar ta. ✪⁠㉨⁠✪ A ɓangaren Jamil kuwa duk hanyar da zai ga Najiba ta toshe bawan Allah sai ya koma kamar wani Maraya kullum zai zauna yayi shiru ba uhm bare Uhmm ƙewar matar shi ta dabaibaye shi ta ko ina ,Kuma ya kasa tun ƙarar iyayen ta. Sai dai ya je yayi ta jiran ta a waje bazata fito ba Gariti har mita yake masa ba zai ƙara zuwa ba ya gaji dan kullum haka zasu wanke ƙafafu su dawo,har ta kai ta kawo shi kaɗai ke tafiyar sa.Har wajen Mahaifin sa ya koma sai dai ya ce yayi komai da kan sa kamar yadda ya ɗaura wa kan sa Aure. Hankalin Jamil kuma ba ƙaramin tashi yayi da zancen mahaifin na sa ba duk da yasan ba da wata manufa yayi furucin na sa ba,ya san ya yafe masa tunda ya furta. Saboda ya wan zuwan Jamil har an gano shi mutanen unguwa haka za,ayi ta tsincen sa suna zagin shi wasu a ɓoye,Wasu a fili ma sai kaji suna furta ga Mayaudari chan,ko kaji ana furta kunga ɗan ƙaryar chan,har fitowa mata ke yi suna kallon sa asace. Duk da haka bai taɓa tanka musu dan shi Damuwar da yake cikin ita ta dame shi,kuma baya da kunyar kowa bayan iyayen NAJIBA da ba dan haka ba ma da tuni ya ci zarafin masu mishi wannan shigen Hancin.. Suku su Malam Abdul basiɗ ba su matsa mishi ba suka zuba mishi ido suna jiran lokacin da suka ɗibar wa Najiba yana cika kuma zasu maida ita ga mijin ta,idan ya zo iyakar su gaisuwa dashi. Tunda ga lokacin ta fara rainon jinjirin cikin na ta.Nadiya tayi murna sosai da jin labarin har da hawaye sai da ta zubar na tausayin Najiba da take kan bakan ta babu inda zata koma, Dan ta faɗa mata raba Auren zata yi bazata iya kayan kunya ba.Ita bata ma san ta inda zata fara haɗa ido da Jamil ba. Wannan kenan. Mu koma cikin labari... Shiru take zaune kamar wadda ƙwai ya macewa a ciki saboda yau ne malam Abdul basiɗ suka zauna da ita akan matsayar da ta kai kan Auren. Kai tsaye kuwa Najiba ta nuna musu bata ra,ayin komawa. Sai dai kamar yadda take tsammani bata samu goyon baya ba domin kai tsaye suka furta sun bata nan da yan kwanakki ta kai matsaya idan ba haka ba su da kan su zasu mai da ita gidan na ta. A jiyar zuciya ta sauke a hankali ta na shafa cikin ta da ya ɗan fara tasawa sai dai ba lallai a iya gane hakan ba saboda ba wani fita yayi ba sai ita kan ta da take ganin chanjin a kullum. Duk lokacin da ta ke kallon cikin sai kewar mijin ta ta so mata Satin ta biyu yau a gidan nasu,amma har yanzu bata saka idanun ta a na Jamil ba kuma matuƙa tana azabtuwa da hakan bare shi.Bawan Allah yan zu ya koma kasuwancin sa yana ɗan tarawa tare da jiran tsammani kiran ta Dan kusan kullum yana mata waya fiye da goma bata ɗagawa ko da by mistake ne. Tun Gariti yana mishi dariya har ya fahimci abun yana taɓa shi domin yayi wata iriyar rama kamar ba Jamil ba ɗan gayu da ƙarya.Dan shi ya samu mahaifin sa ya nemi ya saka baki asamu matar sa ta dawo.Malan Ɗahiru Almajir bai musa ba ya amince.Ya wanke ƙafafu ya samu su malam Rabu'u cikin sanayya suka gaisa da juna ana ta firar yaushe gamo dan sun daɗe basu haɗu ba saboda ba unguwa ɗaya suke ba. Sunyi mamaki matuƙa jin Shine mahaifin Jamil,sai yanzu suka fahimci dagaske shi ne domin ya faɗa musu sai dai bai saka musu Almajir ba a cikin sunan shi ya sa basu gane ba kai tsaye.Anan suka yi zantukakkan fahimtar juna tare da kai matsaya sati mai zuwa zasu mayar da Najiba gidan mijin ta in Sha ALLAH. Haka suka watse suna bin Ya'yan na su da Addu,ar shiriya domin sun san Kowannen su yayi kuskure Babba,sun kafa rumfa sai dai ta rufta da su.Musamman Najiba da bata iya tarayya da talaka dan dukkanin samarin ta ya yan masu shuni ne sai dai ƙaryar ta ita ke korar su a gare ta koda sun shigo dagaske suke son ta suna gane gaskiyar Wacece ita zasu tafiyar su.Su bar ta da kunya. Murmushi ta sakarwa Mama Hasiya da ta shigo yanzu tana furta wai har yanzu baki fito ba kika ci abincin nan sai ya huce. Murmushin ta mayar mata tana furta " Bana jin Yun wa yanzu sai Anjima ". Kai Mama ta gyaɗa tana sakin ajiyar zuciya dan mugun Tausayin Najiba take ji domin duk wanda ya haɗu da irin wannan ƙaddarar dole a tausaya masa musamman yanzu da ta fara sabawa da rayuwar da ta mata Nisa a yanzu,duk da kuwa ita takai kan ta ga ramen.Ahto rame kam kana cewa dole sai ka Auri mai kuɗi,Dan samun jin daɗin rayuwa,kowa Ba Allah ke zaɓar mishi abokin rayuwa ba,komai tazarar dake tsakanin ku da wanda Allah ya zaɓa miki sai kun kasance a rumfa guda,koda ace tazarar dukiya ce,ko ta Ilmi.Rayuwar nan da ba ta da tabbas,Kuma ba kowane mai kuɗi ne kike samun shi a gida yadda kika Gan shi a waje ba wasu kuɗin na su a waje ne suke moruwa,daga lokacin da kika shiga gidan sutura ma sai ta Miki wuyar samu,Kinga abun da kika yi wa gudu Na Auren talaka da kike gani bai iya sama Miki jin daɗin rayuwa da biya Miki da buƙatocin ki na kuɗi shima mai kuɗin ya kasa,Wata ga abinci ga komai a sake ta ko ina sai Masha ALLAHU Amma babu natsuwar zuciya duk yadda take neman jin daɗin rayuwa ya gushe mata saboda bata dace da mijin ba dukiyar ce kawai ta dace da ita. Bafa Najiba ce kaɗai ce mai wannan burin ba suna da yawa a wannan zamanin,Wata idan ba mai dukiiya wadda ta amsa sunan ta dukiya,Bata iya Aure sai irin wannan namijin,Zaki ga mutun ya zo da Rufin asirin sa,amma sai kiji ana faɗin ba mai kuɗi bane,shin shi ya'yan naki da ke gidan ku,wakike son ya Aure muku shi idan har ya zamo kowa na da irin wannan baƙin burin na ki.. Yan mata mu hankalta. Iyaye mu hankalta. Samari mu hankalta. Domin a MAZAN ma akwai masu burin Auren Yar masu kuɗi. Hmmm a tambayi dakai da ya sha kashi. Ka Auri yar masu kuɗin da kake so,sai dai babu natsuwa,bata girmama ka,babu biyayya,sannan daga ƙarshe ka koma kaine matar.🤔🤔to ina daɗi🤦 Wallahi tallahi kuɗi ba shine ƙarshen jin daɗin duniya ba,ki daiyi fatan Allah ya baki mijin da zai iya ɗaukar buƙatun ki ko nawa ne,wanda zai biya Miki su a take da abun da Allah ya hore masa,wanda zai iya ciyar dake ya tufatar dake,wanda zaki samu natsuwa a tattare dashi ba wanda zai saka ki cikin ƙunci ba fargaba da tashin hankali na yau da daban na gobe daban. Koda yaushe miji na ƙwarai shine komai a rayuwar "ya mace. Samun shi kuwa shine samun duniyar ki yar uwata.✍️ Ki roƙi Allah ya baki wanda zai zame Miki jigo a rayuwar ki. Masu buri irin na NAJIBA Allah ya ganar da ku. Allah ya sa mudace. ALLAH YA JIƘAN MAGABATAN MU😭😭😭🤲 *** Zama tayi tana furta "ki ƙara tunani a kan zancen nan Najiba bana son ki kafe yadda iyayen ki suke son ki koma ki koma shine maslaha a rayuwar ki ban san ki da gardama ba,kuma bana fatan ta zame Miki jiki domin gardama na kai ki ga dana sani,tana zama rigima,tana haɗa gaba,da ƙiyayya. Bana son wannan ɗabi'ar ta shiga jikin ki. Kinji.Allah yayi Miki Albarka, Sanann ki riƙa ɗaga kiran shi kinji ina ganin yadda yake kiran ki a kullum sai dai babu ɗagawa,tun da har ya iya takowa ƙofar gidan nan duk da ya fahimci kema hanya ɗaya ta kwaso ku bai ce ya rabu dake ba,sai ma ƙoƙarin dai dai ta tsakanin ku,Sannan ki sanar dashi Ajiyar shi da kike tare da ita. Kowa ya samu wani ɗan yankin farin ciki." Tana kai ƙarshen zancen ta sauke a jiyar zuciya duk da tana jin kunyar yar ta,kunyar yar fari dole ta yi magana ta fahimta ga yar ta, Dan mugun Tausayin Jamil take yi duk da bata taɓa ganin shi a fili ba sai a wayar RALIYA da ta taɓa nuna mata shi bayan Auren na su inda yake tare da Najiba sun yi kyau a hoton da ka gan su kasan cewa akwai soyayyar junan su a zukatan su. Kai Najeeba ta sauke cikin jin kunyar furucin mahaifiyar ta na ƙarshe. Kafin ta gyaɗa mata kan ta cikin sauke Ajiyar zuciya. Miƙewa Mama Hasiya tayi ta fice daga ɗakin. Numfashi Najiba ta sauke kafin ta miƙe ta faɗa toilet saboda magriba ta gabato anata kiraye kirayen Sallah. Bari mu leƙa sashen SHANTY da TANIM. A yau ɗin nan jirgin su ya sauka Nigeria daga tafiyar da suka yi a satin da ya wuce wanda ya kama iyakar su sati ɗaya da da yan kwanakki. Tun da aka kwaso su daga filin jirgi basu zame a ko ina ba sai A gidan da ya Ajiye ta wanda suke gudanar da rayuwar su a chan. Haka kawai yake son ganin NAJIBA dan tun da suka tafi bai neme ta ba. Shigowar su cikin Nigeria hankalin sa ya koma kan ta. Ana Ajiye su a mota wanka kawai yayi ya fice duk yadda shanty ta so hanawa abun ya gagara dan Dan share ta yayi ya bar ta tana ta faman mita. Yana dai dai ta parking ɗin sa bayan wangale masa gate da akayi ya fito yana takun sa ɗai ɗai kamar ba shi ba ya wani irin fayau dashi kamar wanda ya kwanta rashin lafiya. Hanyar Falon ya dosa yana bin gidan da kallo kamar wanda ya chan za masa. Babu Sallama ya faɗa babban falon Wanda yayi dai dai da fitowar Nadiya daga kitchen daga ita sai sai wata yar shimin riga wadda ta tsaya mata iya kar kusa da ƙwabrin ta,ta kuma bayyanar da ɗan jinjirin cikin ta da ya fara fitowa fili. Mutuwar tsaye Tanim yayi daga inda yake tsaye ya rasa wani irin Yanayi yake ciki har ta wuce bai motsa ba,shin abun da yake ɗan hangowa da gaske ne? Ya tambayi zuciyar sa.Ganin shuɗewar ta akan idanun sa hakan ya sa ya fara ɗan motsa ƙafar sa da ta riƙe masa mamaki da al'ajabi sun kama shi yaushe NAJIBA ta samu ciki ?me ya sa bai sani ba?,bare yayi maganin sa ,Yau she wannan fitinar ta kutso masa bai san da wanzuwar ta ba wannan wane irin kuskure ne ya akaita. Me ye mafitar sa ya zai yi....✍️ Allah ka yaye mini cutar rashin son typing 😥😩🥺😅 💋🔥Daga Alƙalamin fa'eeh bg🔥💋 Yau dai ina buƙatar comments.🤦🥱✍️ A gafarce ni. Kun san yadda typing wata rana sai a zare maka shi akai gaba ɗaya. Kaji ko shafi baka son kallo,bare kayi rubutu akan sa.🙏 Ƙarin bayani 08069059746 Chat only. *_Typing_* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *_Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chan zaku samu cigaban update.Farkon labarin masu neman sai a mun magana a numban dana sauke ƙasan wannan page,Dan samun document.☝️_* *🌸RAYUWAR MU AYAU🌸* Ƙarya ko sakin Aure Gajeren labari Na Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _*TAFIYAR TAURARI HUƊU*_ ⭐⭐⭐⭐ _*ZAZZZAFAN LABARI DAGA*_ _*TAURARIN MARUBUTA HUƊU*_ *Taurarin marubuta huɗu team* _*Daga marubuciyar littafin*_ _*A Mafarki Nasanta*_✍️ And now _*Rayuwar mu a yau*_ P.27 💫💫💫 *_#TAURARI HUƊU_* *_#NADIYA TANIM_* *_#DR.ABIDA_* ........ Yau she wannan fitinar ta kutso masa bai san da wanzuwar ta ba wannan wane irin kuskure ne ya akaita. Me ye mafitar sa ya zai yi..? Me ya kamata yayi da cikin ? Zufa ne ya ke to masa Ta ko ina sai dai sanyin AC dake zagaye da falon da iskan dake kaɗowa a bakin ƙofa ya hana zufan fara tsiyayayar masa. Jikin shi ya ja a hankali ya taka tsakiyar falon yana sauke Numfashi da Ajiyar zuciya. Zama yayi daɓas a kan yar ƙaramar sofa one sitter kan sa ya dafe da hannu biyu yana sauke huci mai zafi,shi kaɗai ya san dalilin shigar shi tashin hankali,shi ya san abun da zai faru ga gudan jinin sa idan ya shigo duniya a mace ko a namiji domin a ƙungiyar ta su babu haihuwa,suna da Abun tsafin da yake ƙara tara musu kuɗaɗe yana basu luck,Bayan homo da suke yi da neman Mata,suna da shugaban tsafin su wanda ya kasance kamar shine bangon su shi ke tare da bokan su,Kuma doka ce babu haihuwa a gare su idan har ka bari ka haihu to Ɗanɗan da zaka haifa ya zamo na ƙungiyar su wanda tun yana da ƙananan shekarun sa zasu mayar dashi a bun kwakwaran su a gaban ka.Mace ce,ko namiji su wannan ba Damuwar su ba ce,ga shi a bun na su kamar dabbobi haka suke yin shi idan suka samu ɗanyen jini,acewar Abin tsafin na su yafi kawo kuɗi. Wannan shine tashin hankalin sa ya san muddin Nadiya ta haihu suka samu labari abun cikin ya zama na ƙungiyar su.Dan haka duk yadda zai yi sai ya saka wannan cikin fita ta ƙarfi da ya ji,Dan bazai iya kallon gudan jinin shi a irin wannan rayuwa ba wadda sai yanzu da yaga zahiri yana da rabon samun yara jikin shi yayi sanyi soyayyar cikin na shigar sa a lokaci ɗaya.Numfashi ya sauke mai zafi yana sauke a jiyar zuciya yana goge idanun sa da suka ƙara yin wani jaaa. Me ya

Chapter 22 of 39