" Hasiya ai shi yaro ta lalama ake binsa ba haka ya kamata ki mata ba,kuma naga dai yan kayan maƙwalashen nan ana rage zafi dasu yanzu duba kiga Ni har na mance yadda ake cin tuwon dawa da ace kina ɗan rage wannan kayan da yar su holondiya da yaghurt dasu yar shabarman nan ai da kin rage kya rabu da tuwo ,Nikam dai Lafiya lau ne dama Najiba ta ɗaki nace ai ɗana kowa ne kwaso kayan muje ciki Naj ɗita yan mata masu Aji".
Turo baki gaba Najiba tayi sai kuma taja jakar kamar irin tana hasale ɗin nan maganganun mahaifiyar ta kuwa babu wanda ya shiga kunnen ta sai ma ɓata mata rai da sukayi inda ta fi gwammace ta bar ɗakin domin tagane mahaifiyar ta ta fi son Raliya ƙanwarta tafi bata kulawa anata hangen ko muce zato.
Kuskure na farko da mahaifiyar Najiba tayi (Hasiya)ba,a yiwa yara haka haƙuri ake yi dasu Aduk yanayin da suke har Allah ya kawo ƙarshen ijaba.
Sannan mukan yi irin wayen Nan kuskuren ga ya yan mu sai mu riƙa banbanta wa afili ga wanda muke so duk da gaskiya ita zuciya tana son mai kyautata mata da mai jinƙanta.Amma iyaye mata akula da hakan komai yadda kike son wani daga cikin ya yanki koda yafi kyautata miki da miki biyayya ariƙa ɗan ɓoye soyayyar nan domin ta kan zamo illa awasu lokuttan sauran sukan saka idanu kuma.Hakan yana saka musu waswasi azuciya,kamar dai Najiba Ayanzu✍️
***
Wanke motar yake yana sauke nishi na gajiyar da ya kwaso duka yau tun ta safe na wankin motocin da yayi da kuma jigila, cikin galabaita duk da kasancewar sa na miji mai ƙarfin hali, a hankali Gayen da ke kallon sa wanda ya fito daga wani ɗan ɗaki daga cikin ƙaton parking lot na motoci wanda duka rabin su na siyarwa ne wasu kuwa na masu ajiya ne anan.Ya furta " Jamilu kayi ka gama kazo muyi lissafi ".
Kai ya ɗaga masa.Yana cigaba da wankin motar.bai janye daga kanta ba sai da yayi mata ta tass sannan ya kai komai inda yake kafin ya shigo ɗakin yana faɗawa kan yar yaƙusasshiyar katifar dake ɗakin wadda duk ta cinye har ta fara gashi irin mai riƙe jiki.
" Yau dubu ɗari biyu ka kashe inda shi ya zama miliyan ciff ,Kaga saura miliyan biyu cikin abinda ka tara na kuɗin aikin nan naka da derebancin ka ".
Idanu Gayen ya zaro inda wannan Gayen bakowa bane face jamil na Nadiya.Cikin jimanin ya furta chab wai har miliyan ɗaya ya shige cikin wata shida,yau ma fa sai da nayi ƙaryar kira da na ta tsu fiye da haka''.
" Hmmm kana wasa ai wanann yarinyar indai bazaka rabu da ita ba ko ka nemi auren ta da wuri to sai ka koma baka da komai wallahi tunda ka ɗaukarwa kanka wahala Ni ina zan iya inzaki soni yadda kike ki so Ni in Baki so kowa ya kama gabansa sai inje in nemi yar malam Shehu iri na,Amma wannan rayuwa ai batayi ba kabiyewa yar masu kuɗi kana ta wahala ita fa ko ajikin ta"..yakai ƙarshen zancen nasa yana jan tsaki tare da ƙara furta nadai faɗa maka saura miliyan biyu ga bashin gwaska kan ka na kaya jiya baka bada ba ɗazu Zubair yake faɗa mini da naje shagon fira".
Jin ya furta gwaska hakan ya sanya shi miƙewa da sauri yana ɗaukar kayan da ya cire tare da mai dasu yadda suke ya ƙara fesa musu turaren kaya mai ƙamshin sabon ta sannan ya fice daga ɗakin cikin sauri inda bai tsaya Ako ina ba sai wani ƙaton boutique wanda ke kusa da parking lot ɗin nasu na wankin motoci da sai da motoci wanda shi aikin nasa wanki ne sai kuma jan mota da yake yi zuwa ƙauyukka mafi kusa da Kano irin local government nata naɗan nesa.
Da shigarsa ya furta" afwan Zubair wallahi na dawo agajiye ne shiyasa gasu nan Nagode ga cikon kuɗin ka".
"Kayi arziki Jamilu gwaska bai nan da wallahi yau ya kama mu duka sai mun ci ubanmu nida kai dan ya gargaɗe Ni kar in ƙara bawa masu zuwa aro kayan mu saboda shi bai m yarda da wannan shirmen ba".
Gayen da aka ita Zubair ya furta.
Murmushi Jamilu yayi kafin ya furta " Allah dai ya kau da rana kam".
kuɗin Zubair ya amsa tare da mayar da wandon inda yake a mazaunin sa Sannann sukayi sallama yana komawa cikin ɗakin nasu.
Inda yake tariyo komai tun haɗuwar sa da Najiba yan kuɗin sa da yan sana,oin sa suka taɓarɓare gashi yanzu yan ƙudin da yake adana na Aure sun fara wagarewa dole yayi wani abu tabbas da badan yana son Najiba da Aure ba Wallahi da babu abinda zai hana ya rabu da ita.Amma shi tsakani da Allah ya ke son ta.
Haka yake ta yin tunanin ka barkatai sai dai tuna da yayi bai yi magrib ba bare isha hakan yasa ya miƙe da sauri yana ɗauro Alwalla tare da jera sallolin cikin gajiyar da ke cin jikinsa.
Domin yaso su tsaya suyi sallar Najiba ta hana tace yabari suje gida kawai ita tagaji.
Wal iyazubillah 😢😢🙏
Wannna rayuwa Allah yayi maganin ta.Allah ka rabamu da abunda zai shagaltar damu da ibada🤲🤲
Me kuke tunani da rayuwar Najiba zata gyaru ko zata cigaba daga inda ta tsaya bayan komawar fa ɗakin uwar ɗakin Tata (mama Hafsatu )
Waye Jamil.
Su waye Najiba,Nadiya,Raliya.
Mu haɗe next page
Kuyi sharing pls 🙏🙏
*🌸RAYUWAR MU AYAU🌸*
Ƙarya ko sakin Aure
Short story
labari da rubutawa faiza Almustapha
Daga Alƙalamin fa'eeh Bg ✍️✍️
Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin.
Bismillahir rahmanir Rahim
💪📚📚
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
P.3
Kayan nata takai cikin ɗan ɗakin na Nadiya sannan cikin Rashin damuwa da kukan da ta ga mahaifiyar Tata nayi ta jawo kayan da ta shigo dasu na siyayyar da Jamil yayi mata na ci maka.Haka suke cin komai cikin nishaɗi bakin Mama Hafsatu har kunne saboda farin ciki haka take yagar naman kaza kamar wata kura sai da sukayi nak dukkanin su sannan suka sanya saura acikin ɗan ƙaramin fridge da suka haɗa suka siya itada Nadiya saboda ajiyar irin Wayen nan kayan da basa son zafi saboda sun zama kamar sune ci ma.kar su. Haka suka watse bayan taɓa fira kafin kowa yaje ya kwanta itada najiba ɗin.
" My Boo kasan kasan fa wallahi nayi missing ɗin ka nidai abar maganar wasa shin dagaske goben zaka dawo ne"?.Takai ƙarshen zancen cikin ƙara yin ƙasa da murya kamar mai rarrashi.
Ban san Abinda aka furta achan ɓangaren ba kawai naga ta miƙe tana sakin yar ƙaramar dariya mai haɗe da kuwwa sai kuma ta daɗe bakin ta tare da ɓata fuska jin uban dukan da Najiba ta kai mata tana furta " Shegiya tawan wallahi har Naji tsoro ko Beb dake cikin wayar nan yaji ƙarar da kika yi nasan ma kin razana sa ".
Takai ƙarshen zancen tana nuna wayar ta da ta ɗan janye daga kan kunnen ta.
Nadiya kuwa murmushi ta saki tare da hararar Najiba sannan ta furta " My Boo dagaske Aiko gwanda da ka shaida mini da wuri domin awannan karon nida kaina nake son nazo tarbar ka ".
Murmushi ta ƙara saki na amsar da aka bata chan ɓangaren kafin A hankali kuma ta ƙara yin ƙasa da murya tana furta " Ai kasan kai nawa ne Ni kaɗai karka damu my Boo Babu wani sai kai Azuciyar Nadiya Wannan gonar kace babu wani da ya isa ya iya kaiwa kan ta ".Rufe fuskar ta tayi tana sakin murmushi bayan gama zancen da kuma Amsar da aka bata aɗayan ɓangaren haka suka cigaba da fitar su cikin nishaɗi har bacci ya kwashe ta ba tare da kowaccen su ta damu da yin sallolin da ke gaban ta ba Gara ma Najiba in ALLAH ya farkar da ita tana tashi ta yi su a daren Amma itakam Nadiya babu wannan zancen wadda aka samu yi anyi kam babu abinda aka sani sai dai aɗau wanka afita yawon gari biki kala kala kuwa na masu kuɗi duk sai ka gansu achan kai ba ɗan wani ba.Haka suke gudanar da rayuwar su yadda suke so babu mafaɗi sai dai ma ma ƙarin zaƙi.Domin kuwa mama Hafsatu mukan iya cewa itace tushen zamowar su hakan ita ke ɗaura su akan wannan hanyar tun bayan fara yawon fitar tasu ganin suna bata ɗan abun taɓawa ita mai bakin wahala da kwaɗayi shine ayanzu ta ɗaure musu gindin agidan tana cin arzikin da suke kawo wa,acewar ta wannan arzikin shi ke nuna maka kayi haihuwar ya ya mata masu daraja.
ALLAH ya kyau ta,ya ganar da Mama hafsatu.🙏✍️
WACE CE NADIYA,NAJIBA, RALIYAH.
***
Nadiya Abdulbasiɗ shine cikakken sunan ta ya ce tilo ɗaya ga Malam Abdul basiɗ da Hafsatu wadda suke kira mama hafsatu.Nadiya mace ce mai shegen son kuɗi kamar yadda mahaifiyar ta ta koyar da ita tun farko sai hakan ya zame mata jiki saboda babu kwaɓa har ila yanzu kuwa haka rayuwar ta take.
Najiba da Raliya dukkanin su ya ne ga Malam Rabu'u da Hansatu Wadda suke kira (Umma)Najiba itace ta farko kafin Raliya ahaihuwa duk da ba wata tserewa gare su ba dan idan kaga Raliya da najiba ba zaka ce akwai wani banban ci mai yawa atare da su ba.Dukkkanin su tsatso ɗaya ne domin Malam Abdul basiɗ da Malan Rabu,u uwa ɗaya uba ɗaya ya haife su an haife su a garin Jigawa,dutse acikin wani ɗan ƙaramin ƙauye da ke acikin dutse ɗin.Almajiranci shine abinda ya kawo iyayen nasu cikin garin Kano daga nan har suka fara gudanar da rayuwar su kamar kowa suka ɗan fara riƙa ayyuka irin su noma da dako ana basu kwabo har Allah ya saka wa abin Albarka suka gina ɗan madaidaicin gidan su bayan sayen fili wanda suka saye shi da ƙyar suka gina sa. karatun firamare da da secondry kuwa su Nadiya dukkanin su sunyi shi wanda aka gama shi daƙyar su sun gama tun shekara uku da suka wuce sai dai har yanzu basu wuce makaranta ba kasancewar babu kudin sponsoring kuma babu mai taimako. ita kuwa Raliya yanzu ta gama Tata jarabawar inda tayi ta da ƙyar domin kona zana jarabawar da ƙyar aka neme su dan har ta cire rai sai ga mahaifin ta da kuɗin thumprint ɗin da komai yayi rance .Dukkanin su sunyi karatun Arabia gwargwado kafin su Najiba su yaye kansu.Suka daina zuwa tun bayan kan su da ya fara fashewa,suna ganin sun zama big girls sai suka aske zuwa islamiyyar duk da complain da malam masu ke kawo wa iyayen nasu. Inda Mama Hasiya tayi iya ƙoƙarin ta abu ya faskara.Najiba da Nadiya halayen su iri ɗaya ne fara ɗaya suke rabawa shiyasa ta su ta zo iri ɗaya.Raliya itace kawai baiwar ALLAH Wadda ya tsamo ta daga cikin su babu ruwan ta akoda yaushe tana kan hanyar makarantar ta ta islamiya wadda ta yi nisa sosai da littafai bayan haddar qur,ani da take yi.Raliya mace ce mai kula da kuma kamun kai dan idan ka gansu atare bazaka ce tarbiyya ɗaya ke aiki akansu ba.Ta banbanta da su ƙwarai da gaske.
Wannan kenan,Tana jin zafi sosai akan rayuwar da yan uwanta ke yi sai dai babu yadda zata yi dasu ko ita yar uwar ta ko maganar Mahaifiyar su ba taji bare Tata su kuma iyayen maza sun kasa yin komai kamar Wayen da akayiwa da baibayi..
" Beb gamu nan muna jiran ka har da Nadiya kasan yau Boo ɗin ta zai dawo,kuma ita zata je tarbon sa" .
Bansan abinda aka furta mata ta ɗayan ɓangaren ba naga tayi murmushi tare da yiwa Nadiya alama da idanun ta.
Tashi kuwa Nadiya tayi ta ɗan ƙara dudduba kanta akan a madubin tana sakin murmushi.
Inda itama Najiba ta katse kiran ta tashi tsaye tana duba kanta ɗan madaidaicin madubin na ɗakin.
Fitowa sukayi cikin shiri kowaccen su ta matse babu ma kamar Nadiya abun nata komai Abayyane saboda yanayin jikin ta yafi na na Najiba tafi ta cika ta ko ina.
Fitowar su Falon ne ta bawa Mama hafsatu dake kan tabarma tana shan rediyo ta washe baki tare da rangaɗa uwar guɗa kamar za,a kai Amarya sannan ta miƙe tana bin su da kirari wanda ke fasa musu kai suna ƙara jin sun isa.
"Kai Ma sha ALLAH, ALLAH dai ya nuna mini Auren yan gata ranar akwai shagali" ta ƙara rangaɗa guɗa bayan kai ƙarshen zancen nata.
Dukkanin su murmushi suke saki kamar wayenda aka biya wa hajji kafin Nadiya ta ɗan jujjuya gaban mahaifiyar ta tana furta ya kika ganni Umma na kin gane wannan yarinyar kuwa " tana zancen ta na ƙara juya wa mahaifiyar ta mazaunan ta tare da ƙara jujjuyawa ta ko ina.
Mama hafsatu ƙara washe baki tayi sannan ta ƙara rangaɗa guɗa tana furta " Ai duk faɗin Kano babu kamar yan mata na,Najiba juya mini ingani kema ".
Aiko juyawar tayi kamar wata mai yin modelling haka ta fara rangwaɗa kafin ta ɗan jujjuya tana sakarwa mama hafsatu murmushi.
Dukkanin dariya suka yi wadda ke nuna abun ya musu daɗi musamman samun yabon mama hafsatu ayanzu.
"Najiba kuyi maza ku wuce kar ya tafi bai same ku asamu matsala gwara kuje chan ku ƙara shiryawa,Ku gayar mini da Hajiya Samira ku faɗa mata in nasamu sarari zan kawo mata ziyara.".
Shiru tayi bayan ƙara sa zancen ganin wani irin kallo da Malam Abdul basiɗ ke Binta da shi wanda zata iya cewa bata gane ma kansa ba,suma su Najiba ɗin idanun sa ya bisu da su kafin yafice batare da ya furta komai agare su ba.Dan dama yana cikin uwar ɗakin nata yana bacci surutun mama hafsatu da guɗar ta ta ya tashe sa da hayaniyar su.
Ajiyar zuciya mama hafsatu ta sauke kafin ta furta "Allah ya tsare mini ku muna nan muna jiran tsaraba dan nasan yau sai mun ture ta kam" .
Ficewa sukayi cikin shewa suna furta Karki damu Umma har sai kin ture kin bawa maƙota.
Haka suka fice kowace figai figai kamar wasu ɗiyan shegun.Kallon ƙofar ma na banza Najiba ba tayi wa ɗakin mahaifiyar tata ba ta saka kai suka fice suna ɗan taɓa fira kai idan kagan su bazaka taɓa cewa awannan gidan na talakawa suka fito ba dan shigar su ko kaɗan ba ta nan bace irin ta manyan manyan big ladies ce na Abuja saboda sun san ta kan wanka kam su Najiba kuma yana karɓar su kasancewar kowaccen su ba baya ba tana da kyanta gwargwado.
Napep ɗin ta dake jiran ta kuwa da sauri ya taso bayan hango su inda har sun shiga ciki gaisawa kawai sukayi kafin ya ja su sai ƙofar gidan Hajiyar Dubai domin dama chan yake kaita akullum shiyasa bai tambaya ba ma.
***
"Raliya yar uwar ki kashe Ni take son yi yaya hafsatu ta ɓata mini yaa ga shi na ƙara ɓata komai maimakon na jawo ta jiki na na rarrashe ta nasaka ta ajiki nan wanda hakan zai iya saka ta ta daina Amma ga abun da zuciya ta kai ni,kuma nasan yanzu ko nace Najiba ta dawo bazata ta taɓa dawowa ba sai lokacin da ta ji ra,ayi."shiru tayi tana sauke numfashi kafin ta ƙara furta" Raliya mu dage da Addu,a Abun su Najiba yana bani tsoro iyayen su maza fa sun kasa yin komai akai kamar Wayen da aka yiwa asiri abun yana ɗaure mini kai akoda yaushe idan suka zo da kuɗi suka bawa yaya Abdul basiɗ karɓa yake yi nasha ganin shi Nadiya na bashi kuɗi ya karɓe tsoro na in ba wannan kuɗin da suke bashi yasa yaka sa iya hana su ya bar tarbiyyar su ta har gitse duk da nasan yaya Mai tsantseni akan al amuuran iyalan sa ke shaida ce akan yadda yake iya ƙoƙarin sa akan ku amma lokaci ɗaya komai ya chanza".
Shiru tayi tana jin raɗaɗi har cikin zuciyar ta.
"Mama kiyi haƙuri in Sha ALLAH ko mai zai wuce Aunty Naj zata dawo nan itama Aunty Nadi zata daina da sunyi Aure ai shikenan,Umma dan ALLAH kar ki saka damuwa da yawa aranki".
Murmushi umma tayi kafin ta furta " Raliya kenan kina tunanin Wayen da suke wanka ɗin su Aure su ne bakowane na miji ke iya Auren masu rayuwar su Najiba da Nadiya ba,koda ace anyi Toh ta iya yuyuwa sun samu dai dai sune Amma ina Amfanin ƙarya mahaifinka yana neman na gobe na yau ka ɗaura wa kan ka wahala kai sai kazama ɗan masu gishiri shine abunda ke taɓa mini zuciya kan Najiba saboda na karanci halin ta tsaf,sai nake ganin kamar Azuciyar ta takan iya furta bamu kyau ta mata da muka haife ta anan ba yadda naga idanun ta sun washe hankalina yana tashi".
"Haka ne kam Umma Addu,ar kawai zamu cigaba da yi musu yanzu haka na ɗan leƙa ta bule naga fitar su ita da Aunty Nadi bansan inda sukayi ba ".
Kai mama hasiya ga girgiza kawai sannan ta miƙe tana furta" bari naje na ɗan yi bacci ko na minti talatin ne jiya ban samu yin Bacci ba,ki kula da komai in ba baccin zaki je kiyi ba dan kema da alama baki wani baccin kirki ba ga idanun ki nan ya nuna".
Murmushi Raliya tayi tana ɗan share zancen mahaifiyar ta ta hanyar furta " Tau Umma".
Shigewa tayi ɗakin nata bayan jin amsar ta Raliya.
Raliya kuwa wasu littafan Addini ne ta cigaba da dubawa a atsanake.
******
Malam Abdul basiɗ da malam Rabu,U kuwa dake zaune akan rumfar da ke maƙale da gidan nasu sun ga fitowar ƴaƴan nasu sai dai basu ce musu ƙala ba sai ma yin ƙasa da kai da kowanne su yayi kamar Wayen da aka saka yin haka har su Nadiya da basu ma lura dasu ba Agurin suka fice.
Bayan mai napep ɗin ya ajiye su sun shiga sun ƙara kimtsawa sannan suka ƙara fitowa inda suka tarar da wata irin mota mai numfashi fake aƙofar gidan Najiba cikin farin ciki Dan yana ɗai daga cikin abinda ke burgeta da masoyin nata ga iya ɗaukar wanka ga wankan motoci kamar wani ɗan mai kamfanin su.
Glass ya zuge cikin murmushi fuskar Nan tasa fess ya furta " Agafarce ni ayyuka ne suka mini yawa a office Beb ".
Murmushi Najiba ta ƙara saki tana furta "
Ƙorafi ya karɓu Ya Jamil my Bebe".Tayi furucin tana ɗan jujjuya masa wayar sa ya fiddo da ita yayi mata hotuna tare da ko ɗa wankan nata.
Sannan ya gaisa da Nadiya cikin mutunci har dasu yayar mu yake kira inda ita kuwa murmushi kaɗai tayi masa.
Da sauri suka shiga mota inda suka bar unguwar kasancewar Nadiya tace lokacin saukar Boo ɗin nata yayi,Basu zame a ko ina ba kuwa sai filin jirgi da isar su kuwa aka fara sanarwar jirgi zai sauƙo bakin Nadiya har kunne farin cikin ta ya kasa ɓoyuwa ta kasa iya ɗauke murmushi akan fuskar ta.
Haka suke tsaye har shi Jamil ɗin inda yake kusa da Najiba suna ɗan taɓa fira sama suna kallon jama,ar da ke fitowa da ga cikin jirgin gwanin burgewa musamman shi Jamil Dan yakan iya cewa bai taɓa kawo wa nan ba saboda bai da business da gurin yana ɗan talakan sa mai zai zo yi afilin jirgi Gara itama Najiba sun taɓa rakiyar Boo ɗin na Nadiya wanda a ranar sun buga ƙauyenci dan kalle kalle suka dinga yi har sai da Boo ɗin yayi gyaran murya.
Wata irin ƙara ta sanya ta farinciki hango sa da tayi yana tun karo gefen da take tsaye jaye da trolley da wata bag abayan sa Dan bata lura da ya sauko ba duk zuba idanun da take yi.Aiko cikin wani irin sauri ta faɗa jikin sa tare da ƙanƙame sa shima haka yadda kasan wasu new couples haka suka rungume juna kamar sun shekara basu ga juna ba.Mutane kuwa sai kallon su sukeyi cikin burgewa domin zakayi tunanin mata da miji ne a bayyane.
A hankali ta janye jikin ta jin yana mata wani salo akan wuyan nata kuma tasan halin sa ba kunya gare shi ba yanzu sai ya barta cikin kunya shi ko ajikinsa.
Ɓata fuska yayi bayan ta janye jikin nata da nasa.
Ɗan murmushi tayi ta karo fuskar ta tayi masa zance ƙasa ƙasa.
Murmushi ya saki jin zancen nata kafin ya furta Wallahi kinsan nayi missing naki ke ɗin ce Big Girl babu dama ".yakai ƙarshen zancen yana shafa kansa.
Haka Nadiya take satar kallon sa tana taɓe baki duk da shigar tasa ta burgeta sai dai in aka ce maka babu so arai kai ma kasan ko ƙawar duniya mutun zai saka bazai taɓa burge ka ba ta fannin soyayya.
***
Sunan sa ta Tanim Abdulkarim mahaifin sa mai kuɗi ne domin yana sana,ar sai da motoci daga kwatano zuwa Nigeria zuwa sauran ƙasashen.Shiya sa duk abun da yake so shi mahaifin sa ke masa kasancewar tilo ɗaya acikin yan uwansa mata su shida ayanzu haka shi yake cigaba da ruling Company na mahaifin nasa.Shi haifaffen garin Kano ne ta ko ina.Shiyasa yake yin yadda yake so ya maida womanizing ( Neman mata ) sana'a ya zamo Babban womanizer na bugawa a jarida yau da wacce zaka Gansa daban gobe ma haka. Inda shine abinda yasan ya shi maƙalewa Nadiya tun farkon haɗuwar sa da ita,sai dai itace kawai wadda ya ke biyewa har yanzu da sunan soyayya dan yasamu abinda yake so. Dan tun Ganin sa da ita ya ji sha,awar ta ta kama sa har yaji bazai iya haƙura ba sai ya lashi zumar ta,Sai dai taƙi bashi haɗin kai tun farko shi yasa yake bin ta ta lalama har ya cimma burin sa batare da tasan manufar sa akan ta ba.
Kamar ko yaushe shigar sa ta wasu irin haɗaɗun jeans da T shirt ne masu kyau da suka ji Naira sai kuma wata shirgegiyar sarƙa kamar ta gold a wuyan sa da wasu irin zobuna akan hannayen sa da yan kunne akunnen sa,sai uban az dawun nasa da wasu haɗaɗɗun boat masu kyau da wata P cap da ya ɗaura akan sa, yasha kitso irin na maza ɗin nan da ake saka zare aciki.Shigar tasa kam ko kaɗan batayi kama da Musulmi ba sak kamar ta turawa da arna. Tanim dai shima kyakkyawa ne sai dai Jamil ya fishi kyau kam dan shi baida wata halitta irin ta maza je masu ƙarfi ajiki.
Jakar ta sa ta karɓa trolley bag tana riƙewa cikin murmushi bayan gama ƙare masa kallo.
Cikin tashin hankali Jamil dake zantawa da Najiba yaga Fitowar Tanim akan jirgin yayi mutuwar tsaye kafin a hankali ganin ya kusa isowa kusa dasu ya faɗa mota da sauri yana furta "Beb bari na Duba wani abu".
Kai ta ɗaga masa kafin ta fara gaisawa da Tanim da ya iso gurin cikin bashi girman sa.Haka suka shiga motar bayan an saka kayan nasa abayan motar.
Jamil kuwa tada motar yayi batare da ya furta komai ba inda ya ɗaura p cap akansa wadda ta rufe masa rabin fuskar sa tare da facemask sannan a hankali bayan Nadiya ta furta Yaya Jamil baku gaisa da Boo ba.
Ya cire facemask ɗin fuskar sa daƙyar yana haɗa zufa ya furta "Barka da dawowa Tanin ya hanya".
Shiru yayi jin bai tanka masa inda kuma cikin mamakin sa yaji sautin sa yana furta lafiya lau jamilu
Gaban sa ne yayi wata irin faɗuwa har sai da motar ta ɗan so kubce masa sai kuma ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 39