Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta wasu alamomin suna nuna kamar ta daina son ta kamar chan baya. Hawayen ta, ta share tana jin nauyin da ke kan zuciyar ta ya ɗan ragu ba dan komai b sai maganganun da mahaifiyar ta ta furta mata wayen da bata yi tsammanin ta same su ba a gare ta. Murya a shaƙe ta furta " ki bani maganin ciwon kai ina jin zazzaɓi ". Baki Mama Hafsatu ta washe kafin ta furta " Nadiya har yanzu kina nan da sakarcin ki,dama zazzaɓi kike yi wa kuka haka,a'a to bari na nema Miki magani ba,a rasa shi anan ba ". Tana kai ƙarshen zancen ta miƙe ta shige uwar ɗakin ta.Tana Murmushi domin ta san cewa cikin ne mai sakar mata wannan zazzaɓin. NADIYA kuwa hawaye ta share masu zafi tana bin mahaifiyar ta da idanun ta da suka rikiɗe zuwa jaaaa. Maganin ta kawo mata sannan ta ɗebo mata ruwa ta bata ta sha tana gama sha da kusan minti talatin bacci ya kwashe ta nan take bacci mai ƙarfi,inda take ta faman sauke Ajiyar zuciya. Mama Hafsatu filo kaɗai ta aza mata sannan ta cigaba da ayyukan gaban ta da zata yi. Nadiya Bata farka ba sai da aka fara kiraye kirayen Sallar Azahar sannan ta miƙe tana ɗan jin jikin ta sakayau. Alwallah ta fita yi sai lokacin ne Mama Hasiya ta gan ta.Baki sake ta zuba mata idanu sai dai bata bayyanar da alamun mamakin ta ba duk da yadda tayi mamakin ganin ta Dan ta daɗe bata zo gidan ba wanda tun tana farkon kaiwa ne bai wuce zuwa biyu ba. NADIYA cikin ɗan sakin fuska ta gayar da Mama Hasiya tana ƙaƙalo murmushi. Mama Hasiya ma cikin murmushi ta amsa mata tana furta. " Yau Manya ne a gidan na mu,maraba,Saukar yaushe ". " Tun ɗazu da safe na shigo bacci ya kwashe ni ban ta shi ba sai yanzu shiya sa ban shiga gurin ki ba ". Najiba ta furta. " Fatan komai lafiya,gidan naki da mai gidan ".? Mama Hasiya ta furta cikin kulawa ganin yanayin Nadiya'r da yanayin ta ya nuna kamar tana cikin damuwa. Duk da kuwa tayi bacci wani abun ya rage. Kai Najiba ta sauke ƙasa sannan cikin haɗe miyan da ya maƙale mata a maƙoshi ta furta. " Lafiya Lau Umma ". Kai Mama Hasiya ta gyaɗa Bada n ta yarda da zancen na ta ba.Hanyar ɗaki ta kama wanda dama ta gama alwallar da ta fita yi. Numfashi Nadiya ta sauke sannan ta fara gabatar da Alwallah. Tana gamawa ta shige ɗakin Mama Hasiya ɗin da sallama ɗauke a bakin ta. Najiba dake zaune tana ɗan tsakurar kwaɗon da Mama Hafsatu tayi mata na rama wadda taji ƙuli ƙuli da yaji dai dai gwargwadon masu ciki. Baki sake Najiba ke kallon ta kafin ta washe baki bayan ta furta " To rufe bakin,Hangama ". Zama tayi a kusa da ita itama cikin murmushi ta furta. " Tawan Wannan kallon mamaki fa,kamar na chan za Miki ". Ɗan murmushi Nadiya tayi kafin ta furta " Ba wani Mamaki fa,Amma fa kin mini bazata, yaushe ki ka shigo ban sani ba,da alama har bacci sai da kika yi a nan,an ya ba nan kika kwana ba ma ". Ƙaramar Dariya Najiba tayi tana furta " Taya Mama zata barni bacci nan,ai sai in taga wuta za'a jefe Ni,ko shi ɗin ma tana iya ƙyale Ni ta ce Ƙanƙara ce aka jefa ni,Tun ɗazu na zo,Ai mun gaisa da Umma yanzu a waje bata faɗa Miki ba ". Najiba da ta ta watsar da farkon zancen na ta wanda tayi kamar ba ta ji ba ta furta " Bata faɗa mini ba ". " Kin zo lafiya,Ya unborn babyn mu "?. Ɗan numfashi Nadiya ta sauke kafin furta. " Alhamdulillah yana lafiya ". Ta kai ƙarshen zancen tana shafa cikin ta kafin kuma murmushin da ke kan fuskar ta ya ɗauke ƙaf sai kuma hawaye su biyo baya. Jikin Najiba ne yayi sanyi ƙalau itama murya a karye cikin Rarrashi ta furta " Kiyi haƙuri kinji tawan dan Allah karki yi kuka har Umma ta ji ". Tayi furucin ganin Nadiya na neman ɓare baki tayi kukan da yake kuka bana zallar hawaye ba. Hawaye ta share mata tana kallon ta cikin tausayawa kafin ta furta " Najiba Cikin yake son na zubar ". Zaro idanu NAJIBA tayi cikin tashin hankali sannan ta riƙo hannayen ta tana furta. " Saboda me ".?? Tsaff ta kwashe komai ta sanar da Najiba cikin zubar hawaye da ƙuncin da ke mamaye da zuciyar ta wanda take jin ya ragu lokaci ɗaya saboda ta faɗi damuwar ta, Dan hakan ta ji sanyi a cikin ranta ta samu wanda zasu sharing baƙin cikin a tare. Najiba dake sauraren ta wani irin ɓacin rai ne ya taso mata sai dai ta san babu a binda zata iya yi sai Rarrashin ta da bata haƙuri da taya ta da Addu,a domin ita take buƙata a yanzu,kamar yadda itama take cikin buƙatar Addu,ar. Nadiya kuwa tana kai ƙarshen zancen wanda ta bata labarin har zuwan ta asibiti kuka ne ya ƙwace mata mai tsuma zuciya Najiba nata aikin rarrashi har ta samu ta yi shiru. Kafin a hankali jiki A sanyaye cikin tausayi yar uwar ta ta ta furta " NADIYA kiyi haƙuri ki maida komai gurin Ubangiji shi zai Miki mafita,mu jarabawar mu ce,mun kutsa kai cikin ƙaddara mai ido musamman ma tawa da na ɗaurawa raina son kaina,Sai dai a yanzu nafi jin taki Damuwar itace a raina,Kuma Dukkanin mu muna da laifi akan abin da ya faru,bamu yi aiki da tunanin mu ba,bamu hango gaban mu ba,bamu tuna bayan mu ba,Sai dai ba,a je ko ina ba saboda Allah ya na son mu hasken sa ya nuna muna kuskuren mu muke girbar Abinda muka shuka,Dan haka karki je cire cikin nan ,ki bari mu samu wata mafita kafin,Yanzu karki bari ya riƙa ganin cikin koda na kwana biyu ne haka kafin A samu mafita,Mu haɗu da jarabawa Kuma muna fatan Allah ya bamu ikon canye ta ". " Ameen ". Nadiya ta furta jiki a mace zuciyar ta na mata wani irin zafi sai dai kamar yadda yar uwar ta,ta faɗa haka take a gurin ta ita yanzu ta damƙawa Ubangiji lamurran ta wanda dama a hannun sa suke kuma shi zai mata mafita.Zata dage da Addu,a in sha ALLAH ba dare ba rana zata kai kukan ta ga mai share hawayen bawan sa. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta haɗiye hawayen na ta ganin yadda fuskar Najiba dake kallon ta ke ji kamar ta saki kuka wanda idanun ta har sun tara hawaye baƙincikin ta ɗaya ta ya za,a ce yaron da baiji bai gani ba za,a cire shi ana murna kuma a koma kuka ta san yadda Mama Hafsatu ta ƙwallafa rai a cikin a she shi ubangayya ɗan cuna rai ne dama sai da ta yi hasashen haka a farko dan ta san bakowa ne mai irin halin sa ke son haihuwa ba gudun abinda zai shafi na su ya'yan. ' Da sauri ta bar bakin tagar da take tsaye tana sauraren dukkanin wani zance na su,wanda ta zo da niyyar fito da Nadiya ɗakin Dan ta san bata wuce chan tunda bata gan ta ba.Tana kawowa kuma yayi daidai da fara zancen NADIYA ɗin sai ta tsaya saurara domin ta san tana shiga zancen zai datse,shi ya sa ta dawo bakin window saboda bata ji ta ƙofar.. Ɗaki ta shige da sauri kamar ta kife cikin tashin hankalin abinda Kunnuwan ta suka jiye mata.Wanda take jin dole ta ɗau mataki tun wuri. *** Najiba hawaye ta share a hankali ba tare da ta bari Nadiya ta gani ba sannan ta ɗaura mata ramar dake kusa da ita. Tana furta. " Mu ci kwaɗon ramar ". Kai Nadiya ta gyaɗa tana furta. " Zanyi sallah,nayo Alwallah ne ". Hijab Najiba ta miƙa mata tana shimfiɗa mata sallaya a nan inda ta tashi bayan tayi Sallah. Hawa kan sallayar tayi bayan ta saka hijab ɗin. A tsanake ta yi Sallar ta sannan ta sallame bayan tayi raka'at huɗu.Addu,oi tayi sannan ta naɗe sallayar tana cire hijab ɗin tare da naɗe shi. Zama tayi ƙasa kusa da Najiba wadda ke ta bin ta da Idanu cikin tausayin ta Tunanikka kala kala. Kwaɗon ramar suke ci a hankali suna taɓa fira kowa rai babu daɗi kuma ba su son Aji komai daga firar su wadda ko wannan aka yi ta cikin rage murya gudun kar wani ya ji sai dai sun makaro domin kuwa Mama Hasiya babu abinda ba ta ji ba itama.Sai dai ta kasa fitowa gudun kar ta katse musu fira,kuma su ji babu daɗi idan suka gane ta ji komai,su kasa sakewa. Mamaki ne kwance akan ƙirjin ta na abinda taji wai bai son Ɗan na sa wanda yake haihuwar fari ma bai taɓa ganin gudan jinin sa ba. Sai da ta tabbatar har sun fara cin kwaɗon sannan ta fito tana yin yar Hamma tare da furta '' Nadiya an shigo ". '' Eh Umma ". Nadiya ya bata amsa kai tsaye tana cigaba da cin kwaɗon ramar da ya mata daɗi sosai. " Ni bacci ya kwashe ni daga gama sallah,Addu,a kawai na yi sai gyangyaɗi kafin bacci ya ci ƙarfin na wa ". Tana gama zancen ta sake yin yar Hamma. Murmushi NAJIBA tayi Haka ma NADIYA sannan ta furta " Umma tsufa ne ". Yar hararar Wasa Mama Hafsatu ta sakarwa Nadiya tana furta. " Da sauran mu tun da muna kafe ɗauri har yanzu ". Ta kai ƙarshen zancen tana sakin ɗan guntun Murmushi na manyan akai kaice cikin tausayin halin da Nadiya'r take ciki.Dama Mama Hasiya tana da ɗan barkwanci ga ya yan ta da kowa ma haka take mai faran faran. Dariya Nadiya tayi wadda ta ɗan daɗe bata yi duk da ba wata mai tsawo ba ce. Itama haka Najiba dariyar tayi ta nuna jin daɗi ganin yar uwar ta na dariyar da ta kan ce tun shigar ta damuwa bata ƙara yin ta ba. " Bari na ƙara muku ta Raliya sai ku ƙara inada wadda na ajiye zanci Anjima,sai na kwaɗa mata idan ta zo ". Mama Hasiya ta furta ganin alamar kwaɗon yayi musu daɗi dan sai suɗar hannu su ke yi. Washe haƙora Nadiya tayi tana jin sanyi a ran ta.Yau ta samu farin ciki wanda zai ishe ta har zuwa lokacin da zata samu mafita ta cire cikin,ko barin sa.. Haka kuwa aka yi ta ɗakko musu ita wadda aka Ajiye ma Raliya suka saka ta gaba suna ci,hankali kwance,Suna taɓa fira sama sama. *** Zagaye take tayi cikin uwar ɗakin ta ta dake harmutse gadon ko gyara bai samu ba. Numfashi ta sauke mai zafi sannan ta furta. " Ba zai saɓu ba dole cikin nan ya rayu,Bazai yuyu naga samu naga rashi ba,dole nayi wani abu tun wuri ". Haka take ta irin wannan surutan ita kaɗai tun bayan shigowar ta ɗakin cikin tashin hankali. Sai da ta gaji dan kan ta sannan ta zari hijabin ta, ta fice gidan gaba ɗaya. Tana fita gidan Rahane ƙawar ta wadda take maƙwabciyar su ce. Da sallama ta shiga gidan amsa mata da akayi ne ya san ya ta shigewa cikin gidan direct cikin ɗakin da Muryar ta fito ta faɗa . " Hassi nifa na gaji da baki rance yanzu kusan fa dubu ishirin nake bin ki,Tun wanchan aikin da na saka a kayi Miki na saka kuɗɗi na kuma kin sani gashi nayi ta Miki aike har yanzu sai dai ki bani haƙuri ". Rahane tayi furucin bayan Mama Hafsatu ta gama furta mata tana son ta je wurin Bokan su ya ƙara yi mata aiki akan rufe idon Tanimu har ta haife cikin babu ruwan sa da shi. " Haba Rahane ai nida ke ne Kinga yanzu Nadiya'r ta zo zan ɗan tsakuri wani abu gurin ta yanzu dai ki taimaka harda ƙari zan Miki, Zan fitar da katifa ta ma idan har ban samu wani abu a gun ta ba,na san zan mayar da komai har sauran hasarar da nayi zan ci riba nida ke na Miki alƙawarin tare zamu ci komai dake " Hmmm Rahane ta yi sannan ta kyaɓe baki tare da furta. " Haka kike cewa kullum tun kafin ayi Auren nan yanzu anyi shiru babu uwar kowa haka ma yanzu zaki tsara ni da zancen ki,Ni ban ma yi niyyar komawa ƙauyen nan ba,saboda ban daɗe da komawa aka yi mini aiki ba ". " To naji karɓi wannan yanzu ". Mama Hafsatu tayi furucin tana kwanto ƙulli a gefen zanen ta. Kuɗi ne ta ciro wayen nada suka murɗe waje ɗaya ta miƙa mata. Washe baki Rahane tayi tana kallon kuɗin da ta lissafa kusan dubu talatin ne da yan kai. " Ki e bashin da kike bi na saura kuma kije da shi sai ki Ara mini wani abu nan a hannun ki idan kika dawo zan mayar Miki in sha ALLAH ". Mama Hafsatu tayi furucin tana miƙewa tare da ƙara furta. " Karki mance ayi komai da kyau,Idan kuma na samu lokaci nima zan je da kaina bayan kin dawo ". Baki washe Rahane ta furta " Toh An gama surukar masu kuɗi,kakar Mai kuɗi,ciki an gama haife shi,Tare da ƙashin arzikin sa ". Washe baki Mama Hafsatu tayi saboda jin daɗin kirarin. Sallama tayi mata tana ficewa daga gidan gaba ɗaya. A ɓangaren su NADIYA kuwa suna tsaka da cin abincin ne sai ga sallamar RALIYA. Cikin farin ciki suka tarbe ta sannan aka fara firar duniya.Duk da Raliya taga yanayin Nadiya bata nuna komai akan hakan ba,saboda ba hurumin da zata iya tambaya ba bane basu saba haka da Adda Nadiya ba.Kwaɗon ramar Mama Hasiya ta yi mata ta ci itama sannan suka koma ɗaki suka dasa sabuwar fira suka bar Mama Hasiya da Malan Rabu'u da ya shigo gidan bada daɗe wa ba. Mama Hafsatu kuwa kamar wadda tayi Ƙarya haka ta shige gidan bata ma lura da babu su Malan Abdul basiɗ a gurin. Da shigar ta ta shige ɗakin na ta. Malam Abdul basiɗ dake zaune Akan yar ta barmar dake zagaye da falon ne ya ɗaga idon sa ya kalle ta sannan ya girgiza kan sa.. Ɗan kame kame ta fara sannan ta furta. " Malan Ashe ka shigo,Ni ban ma lura da babu ku a gurin ba ashe kun tashi ". Bai ce mata ƙala ba sai furta mata da yayi " Bani abinci na ". kulolin da ta gani ne na RALIYA hakan ya san ya ta washe baki tana jan ta sar tuwon da ta tuƙa a ɗazu gefe. " Yar Albarka ashe ta kawo abincin ". Ta sake furtawa bayan ta buɗe abincin da ya ji kifi sai ƙamshi ke tashi na jallof ce da ta ji haɗi na musamman ko daga kallon ta zaka ji miyan ka ya tsinke. Zuba mishi tayi ta ta aje mishi gaban shi tare da aje mashi ruwa. Ɗibar ma kan ta tayi itama saboda dama yunwa take ji kuma shi take ta jira, sai dai ganin ba,a kawo da wuri ba hakan ya sa ta cire rai ta saka niyyar ƙara cin tuwon. Tana fara ci ta fara zuba santi tana sakawa RALIYA albarka tana mitar rashin yin irin haka ga su Nadiya. Shi dai Malam Abdul basiɗ bai ce mata ƙala ba sai cin abincin ya ke anatse. *** " ADDA NADIYA ki bawa Adda NAJIBA baki ta haƙura ta koma gidan mijin ta su Baba sun bata kwanakki kuma kamar gobe suke cikewa ma,naga har yanzu baki ce komai ba Adda kan maganar,sannan ya kama ta ta sanar Da yaya Jamil kan cikin nan tunda har yanzu bai san da shi ba,umma ma ta mata maganar amma naga ta share ". RALIYA tayi furucin suna tsaka da yin fira. Fuskar ta cike da damuwa. Numfashi NADIYA ta sauke kafin ta dubi NAJIBA da bata ko kalle su ba sai ma ɗauke kan ta da tayi alamar bata son maganar. Murmushi Nadiya tayi sanann ta furta " Ƙyale ta Zata koma in sha ALLAH RALIYA,ki kwantar da hankalin ki ". Kai RALIYA ta jinjina cikin jin daɗi. Wayar Najiba Nadiya ta yiwa RALIYA signal alamar ta miƙo mata kasancewar tana akusa da ita.Murmushi RALIYA tayi sannan ta miƙa mata wayar. Komawa tayi gefe ba tare da ta bari Najiba ta gani ba ta buɗe wayar kasancewar ta san password ɗin ta. Numban Jamil tayi searching Wadda tayi saving da Bae tayi taping ta ƙaitaccen saƙo sannan ta tura masa sannan ta saka shi a trash bin.Ta goge minimizing ɗin sannan ta sulale tayi ƙasa alamar kwanciya.Haka ma RALIYA sulalewa tayi ta kwanta ƙasa fuskar ta cike da murmushi duk da bata san me Nadiya ta furta ba ta ji dadi sosai dan ta san Jamil tayi wa wannan saƙon. Najiba kuwa bata kula su ba sai ma fadawa duniyar tunani da tayi tunani wanda yake bai wuce wanda ta saba yi a kullum na mijin ta da tayi kewa,wanda take cikin ƙuncin rashin sa a kusa da ita sai dai tana iya ƙoƙarin ɓoye wa,ga kuma komawar da ake son tayi da wuri haka, Dan ta riga ta aje maganar saki tun da Mahaifiyar ta ta bata baki ta ɗaura ta a hanya. A ɓangaren Jamil zugumm yake zaune ya rungume kafaɗu ya zurma cikin tunani,Gariti ya hana shi irin zaman nan da ya ke yi kar ya janyo ma kan sa ciwo a bun ya gagara sai dai ina ya kasa abinda ma ya rage Damuwar shine yadda mahaifinsa ya tabbatar masa da yayi zancen fahimta da su malam Abdul Basiɗ. Ƙarar shigowar saƙo ne ya sanya shi sauke numfashi yana ajiye wani sabon tunani da ke son ƙara kutso masa. Duba wayar ta shi yayi ganin daga inda saƙon ya fito Hakan ya san ya shi ɗan razana yana waro idanu da karfi zuciyar shi na wani irin lugude.✍️ Allah ka iya muna. Allah ka kawo muna sauƙi da sauyi acikin wannan ƙasa tamu.🤲 Ƙarin bayani. 08069059746 *_Typing_* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y _Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chan zaku samu cigaban update.Farkon labarin masu neman sai a mun magana a numban dana sauke ƙasan wannan page, Dan samun document.☝️_ *🌸RAYUWAR MU AYAU🌸* Ƙarya ko sakin Aure Gajeren labari Na Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _*TAFIYAR TAURARI HUƊU*_ ⭐⭐⭐⭐ _*ZAZZZAFAN LABARI DAGA*_ _*TAURARIN MARUBUTA HUƊU*_ *Taurarin marubuta huɗu masu aiki da hazaƙa da zallar ilmin Adabi* _*Daga marubuciyar littafin*_ _*A Mafarki Nasanta*_✍️ And now _*Rayuwar mu a yau*_ P.29 _"Hi Bae Ina baka haƙuri akan abun da ya faru,sannan ina rokon ka yafiya,ka yafe mini,sai kuma albishiri mai daɗi da nake son faɗa maka shine ina ɗauke da juna biyu ɗan sati Uku.Baby na cike da kewar mahaifin sa nagode,ka kula da kan ka."_ Wani irin farin ciki ne ya mamaye masa zuciya bayan ƙara karanta saƙon da ya shigo wayar sa.Hawaye ne suka silalo masa ya sanya hannun sa ya goge da sauri. Yau shi Jamil shine ke shirin zama mahaifi . Allah abun godiya ya furta A hankali yana jin zuciyar shi fess duk wani baƙin cikin da ke ciki ya gushe masa take sai zallar farin ciki da ya samu kan sa a ciki. Hannun sa har rawa yake yi wajen dialing numban ta ta da yayi saving da Qalbi. Yana saka wa Najiba Albarka a bayyane da zuciya.Farin cikin sa ya kasa ɓoyuwa. Ringing ɗin wayar ta ne ya sanya ta juyowa tana furta. " RALIYA Bani wayar ". Miƙa mata wayar tayi wadda Nadiya ta bata ta mayar inda ta ajiye a sace.Raliya kuwa ɓoye murmushin ta tayi ganin mai kiran na ta wanda dama tayi tsammanin haka,kamar yadda ta san ta san Nadiya haka take tsammani. Ɗan ƙaramin tsaki ta ja tana kallon kiran na shi da ta kan iya cewa kwana biyu ta yi kewar shi ita tama yi zaton Yayi fushi ne. Kamar ba zata ɗaga ba sai kuma ta ɗaga bayan ta dubi gefen da Nadiya take taga tana bacci haka ma Raliya itama kamar bacci take yi saboda kamar abun haɗin baki sun rufe idanun su kamar dagaske Bacciin suke yi. Jikin ta ne yayi sanyi bayan ɗaga kiran da yayi wanda yake na kusan uku ne sannan ta ɗaga. Muryar shi da ta ji ce cikin wani irin rauni ya sa jikin ta mugun yin sanyi.Ta ma kasa amsa mishi sallamar shi sai Ajiyar zuciya da take ta saukewa. " Najiba dagaske komai ya wuce,Najiba ashe burin mu ya cika,mun kusa haihuwar mai sunan Umma ". Waɗannan maganganun sun ƙara saka ta jin ta wata duniyar da ban. Ƙara tsintar Muryar sa da ta yi yana furta. "Allah Miki Albarka Najiba,Nagode,Nagode,Nagode,Allah saka Miki da Alkhairi da wannan kyauta da kika mini,Zan cigaba da sanya ki farin ciki Najiba dai dai gwargwadon hali na ki yafe mini kema na san na cutar dake duk da komai yana da tushe,Amma mu watsar da komai mu fuskanci gaskiya,zan zo anjima in sha ALLAH tare da goron Albishirin ki Naji daɗi sosai Qalb Allah ya bani ikon kulawa dake da Babyn mu". Har ya gama magana bata iya furta komai ba sai sauraren sa.Sai dai zuciyar ta ta wanke fess abu ɗaya take mamaki wane irin Albishir ne ita tayi Albishirin ne ko wani daban. Jin ya yanke kiran ne hakan ya sa ta ajiye wayar gefe tana sauke Ajiyar zuciya. Kafin ta kalli gefen RALIYA ta san bata taɓa tura masa saƙo ba,to wane irin saƙo ne Ya zaama Albishir, cikin jikin ki zuciyar ta ta bata amsa. Idanu ta waro da ƙarfi tana kallon gefen Nadiya kafin ta kai mata dundu a bayan ta sai yanzu ta fahimci komai kenan har zancen da ya furta komai ya wuce, wanda da farko ta ji yana furta hakan kan ta ya ɗan ɗaure mata. NADIYA kuwa da ƙarfi ta miƙe wadda har bacci ya fara kwasar ta abun ka ga mai ciki. Gefen da ta kai ma bugu take sosawa tana hararar ta tare da furta " Lafiya wannan duka haka,ko wane sabon mugun ta ne wannan kika fara ban sani ba,duba fa ki ga gurin har ya so yin jaa" Ta kai ƙarshen zancen tana ɓata fuskar ta.Tare da hararar Najiba ɗin. Najiba kuwa cikin Murmushi ta furta "Wallahi na san aikin ki ne,Tawan,ke kika yiwa Ya Jamil saƙo haka zuciya ta ke faɗa mini ". Kallon baki da hankali Nadiya ta bita da shi kafin ta furta " Shi ya ce Miki haka,ke idan ma haka ne Ai nayi gyaran Aure ". Tayi furucin ta na komawar ta ta kwanta saboda dariyar da ta taso mata ganin ta na neman buɗe kan ta duk da ta san ba wani abu bane. Najiba kuwa Dariya tayi tana furta " Dama na sani ai sai ke Dan RALIYA bazata iya wannan aikin ba,Ni yaushe ma kika ɗauki wayan ban sani ba ". " Ai fa sai kiyi tun da ni na masa saƙon ". Tayi furucin tana sakin murmushi tana rufe idanun ta saboda Bacciin da ya fara kama su. Najiba kuwa itama murmushin tayi tana sauke Ajiyar zuciya ta ji daɗi sosai tun da ga kan fuskar ta zaka gane hakan. Ba abinda

Chapter 24 of 39