ce ta keto ma sa domin bai yi zaton yau ne ba a tunanin sa sai nan da kwana biyu haka saboda yau suke cike wata ɗaya da Auren na su.Idanun sa ne suka sauya lokaci ɗaya dan ya san sunyi maganar fahimta wanda yake tunanin komai zai lafa.Yana ajiye wayar tare da tuno yadda zancen '' kubar mini gida na na janye maganganun da mu kayi ina buƙatar sa a yanzu " ya shiga kunnen sa daga ta ɗayan ɓangaren da aka yi masa kiran.Tashin hankali ne ya ƙara tsintar kan sa jijiyoyin kan sa suka fito raɗam a goshin sa na tashi hankali sauƙin ta ma yayi yar dubara ya ƙara sa ginin gidan na sa wanda da bai san inda zai nufa ba dan yanzu bai da ko kuɗin zuwa kama Otel yan wayen da yake samowa ne idan yayi tuƙi sune yayi amfani dasu ya ɗaga ginin sa.Saboda yanzu yana fita da dubara sai ya je inda ake bada hayar Keke napep sai ya samu wani ɗan abu anan wanda dashi yake ɗan siya musu wani abun buƙata ba tare da sanin NAJIBA ba wadda take tunanin office yake zuwa tun da haka ta san zancen yake kuma ta san shi ke da Company guda.
Yana juyowa kuwa bayan gama wayar da NAJIBA dake bayan sa ya fara cin karo idanun ta jawur da su da alama ta yi kuka.
Hmmmmmmmm
Wata sabuwa an kace inji yan Cha Cha.🏃
Nidai bari inyi shiru kar inyi zagi nan kusa.🧐
Wai me yake shirin faruwa ne.
Ku bani amsa hiliss Jama'a Nadiya ta.😥
Yau dai bamu taɓo.Rale le ba matar Khalillullah ta gaban goshin mama Hasiya.🙃🙂😚
Mun kammala..
Book one
Sai mun haɗe a Book two.
Paid 💃💃💃💃🚶🚶
Daga alƙalamin ✍️
Fa'eeh big
GIMBIYAR TASKIRA 👑
Ƙarin bayani
08069059746.
*_Typing_*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chann zaku samu tun daga farko.☝️
*🌸RAYUWAR MU AYAU🌸*
Ƙarya ko sakin Aure
Gajeren labari
Na
Faiza Almustapha Murai
Daga Alƙalamin
Fa'eeh Bg ✍️✍️
Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin.
Bismillahir rahmanir Rahim
💪📚📚
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
> >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>>
_*Daga marubuciyar littafin*_
_*A Mafarki Nasanta*_✍️
And now
_*Rayuwar mu a yau*_
P.21
Idanun shi ya zuba mata cikin tashin hankali da tsoron da ya mamaye zuciyar sa.Cikin mutuwar jiki ga faɗuwar da ƙirjin shi ke yi ya furta " Me ya san ya ki zubar da hawaye,Akwai alamun kuka a idanun ki " ?
Kai ta girgiza masa kafin ta furta " NADIYA na ɗauke da Juna biyu sannan BP ɗin ta ya hau sosai,Sai kuma wata ƙwaya da take neman yi mata illa ta barci da take yawan sha.Abun ya bani mamaki yaza,ayi Nadiya ta riƙa shan irin wannan ƙwayan har ya so taɓa ta,Shin me yake damun ta da dole take shan maganin baccin a koda yaushe,sannan ga Bp Hawaye ta share masu zafi na tausayin yar uwar ta anan babu abinda yafi ɗaga mata hankali irin zancen cikin Nadiya wanda bata san dalili ba kwata kwata ba tayi murna da shi ba dan koda ta bawa Nadiya shawarar da ta bata ba wai dan ta zauna bane tana son ta bar gidan ne kawai kamar yadda shirin ta na farko yake Dan ta san yadda Tanim yayi Nisa zai yi wuya ya dawo hanya sannan tana zargin akwai wani abun da yake cutatama yar uwar ta bayan wanda ta faɗa mata.
A jiyar zuciya Jamil ya sauke fahimtar bata ji komai ba sannan ya ɗan ƙaƙalo murmushin dole yana furta.
" Na fi tunanin Cikin jikin ta ne yake saka ta shan ta,kuma yanzu zata daina sha kwata kwata in Sha ALLAH,Samun cikin ta Abun Farin ciki ne a gare mu NAJ Allah ya saukar da ita lafiya ".
" Amin "
NAJ ta furta duk da zuciyar ta acunkushe take da wani irin tashin hankali.Kuma tabbas duk abinda aka faɗa kan Nadiya Tanim yake zargi kai tsaye Dan zai yi fiye da haka ma.Shiyasa yayi saurin rufe zancen.Da wata maganar.
Game da maganin da aka samu na barci mai yawa acikin jinin ta abun da ba su sani ba da ita kan ta Nadiya. Tanim duka Kwalayen Hollandias ɗin da take sha ya saka musu wannan ƙwayar Dan wasu lokuttan yana shigowa a buƙace kuma kafin ya samu sai anyi dambe shine yake yin maganin ta yake saka mata a duk madarar bayan ya fahimci yanzu itace abinda tafi so bata iya shan komai na sha sai ita sai ya mai da harin sa chan,shi ya sa har yaci ya chanye kiɗin sa bata sani sai dai ta tashi ta gan ta a har gitse sai dai bata taɓa kawo shi ɗinne ba dan azaton ta mafarki ne tun da ɗakin na ta a rufe yake kafin ya fara Hauro mata ta window yana ɓoye kan sa a ɗakin ko kuma idan ta buɗe kofar sai ya shige ya ɓuya ba tare da sanin ta ba.Duk da wasu lokuttan tana mamakin yawan bacciin da take yi bata taɓa zargin komai ba sai ma hakan yayi mata daɗi dan tana samun natsuwa sosai domin koda zata tashi damuwar ta rabi da kwatar sa ya ɓace.Wannan kenan.
***
Ɗakin Da take kwance suka shiga inda suka same ta tana shan barcin ta hankali kwance an saka mata drip yana tafiya a hankali.
Cikin Tausayin ta haka Najiba ta ke kallon ta tana zama a kujerar da take kusa da gadon.Sai a sannnan ne ta dannawa Mama Hafsatu kira ta sanar mata da abun da ke faruwa.
Cikin tashin hankali ne ta bayyana ƙarara akan fuskar ta sai dai tana zuwa asibitin taji labarin juna biyu sai ta tsinci kan ta cikin farin ciki koba komai dai burin su na gabda cika zasu haifa wa Tamil ɗan sa da zai gaje sa.
Zuwan ta ne ya farkar da Nadiya da hayaniyar ta ta sanya ta buɗe idanun ta.Ɗakin ta fara bi da kallo kafin ta haɗa idanu da Najiba sai kuma mahaifiyar ta Dan Jamil ya fita amsa waya.
Numfashi ta sauke kafin ta ƙaƙalo murmushi ta a zawa fuskar ta,suma murmushin suka yi suna kallon ta ita Najiba na mata kallon tausayi ita kuwa Mama Hafsatu kallon kin biya Ni yar albarka take mata dan samun wannan cikin shine makamar su ita da yar ta ta.
Hmm
Miƙewa tayi tana zama dai dai akan gadon tana jin gina bayan ta akan filon da Najiba ta ɗaura mata. Dan tana da sauran ƙarfin ta shi ya sa bata nemi taimakon su ba ta miƙe da kan ta, kuma hakan yayi ma Najeeba daɗi.
Abinda take iya tunawa kawai shine faɗuwar ta da lokacin da kan ta ya sara mata sai juwa bata ƙara sanin ainahin yadda komai ya fara ba.Sai yanzu da ta buɗe idanun ta, ta tsinci kan ta cikin a sibiti.
" Sannu Kin ji ya jikin,Ashe rabo ya kama Nadiya,Allah ya fitar min dake lafiya,ya raya mini ɗan jika na,kai Masha ALLAH na san Tanimu yau sai yafi kowa murna wanga abun alkhairin ".
Mama Hafsatu tayi furucin inda ta kai ƙarshen zancen tana sakin yar ƙaramar guɗa mara sauti.
NAJIBA da NADIYA dai duka zuba mata idanu suka yi kafin suka kalli juna suka sauke Numfashi a tare,kowa da tunanin da yake a cikin zuciyar sa.
A jiyar zuciya Nadiya ta sauke wadda sai a yanzu ta fahimci dalilin zuwan ta asibitin.Hawaye ne ta ji suna son silalo mata sai dai ta ƙi basu dama sai ma Murmushin da ta janyo tana sauke numfashi tare da rufe idanun ta,ta rasa a wane irin mizani zata saka wannan zance,Shin kodai cikin nan na ta shine zai dai dai ta komai tsakanin ta da mijin ta,to Amma ita wannan ɗabi'ar da yake yi fa wadda ta ke zama a cikin jiki daram kana farawa sai buzun ka.Shin ya zatayi, ta fara shirin aiwatar da shawarar ta yar uwar ta ko kuma ta jiye makaman yaƙin ta ta bar masa gidan sa,to Amma cikin ta meye makomar sa fatan ta Allah ya sa ya karɓi cikin kar ya wofintar da shi dan ta tabbatar da Tanim ba ƙaramin ƙwaro bane.Ajiyar zuciya ta sauke bayan katse mata zancen zucin da Najiba tayi tana sanar da ita ta su SHANTY na gaida ita da jiki sai sun zo suka ce Anjima.
Kai ta gyaɗa mata tana sakin guntun murmushi tana furta " ina Amsawa " Asanyaye.
Raliya ma ta ce zata zo kuma tayi murna sosai Dan ita ma tana fama da ciwon kai bata sami zuwa ba a yau ɗin bayan sanar mata da Najiba tayi.Ta waya ta yi mata congratulations kafin suka yanke kiran.
Haka suka kasance a cikin asibitin har zuwan su SHANTY da wasu daga cikin ƙawayen su da mutanen arziki itama mama Hasiya ta zo ta duba ta da wasu daga maƙwaftan su.Kafin maraice na yi aka bata Sallama suka koma gida wanda har da Mama Hafsafu da ta nuna dole Nadiya ta koma gidan ta ya fi, Dan kai tsaye Nadiya ta nuna tana son a wuce da ita gidan iyayen na ta sai dai babu wanda ya ƙara furta komai cikin su tunda mama Hafsatu ta nuna ba haka ba.Najiba bata ji daɗin haka ba domin tayi kiran Tanim yaƙi ɗagawa da wayar ta har ta Nadiya ɗin wanda ya ƙara tabbatar mata tabbas yar uwar ta na zaune ne a cikin wani irin duhun yanayi mara fassaruwa sai tauye zuciya da kawar da Natsuwa.
Koda suka shiga ƙaton falon Mama Hafsatu santin gidan kawai take yi tana buɗe haƙora farin cikin ya kasa ɓoyuwa samun yar ta a cikin wannan fankacecen gida duk a an bata labari sai ta ga ashe yafi kyau ma afili gida kamar na Turai inji ta.Su dai sai Binta da idanun su suke yi babu wanda ya furta komai.Dan ko a wajen haka tayi ta santin gidan.
Bin ta ce da ke aiki a kitchen ta fito da sauri ta tarbe su tana yiwa Nadiya ya jiki cikin girmamawa.Sai hakan ya yi wa Mama Hafsatu daɗi matuƙa yar ta ta shiga gidan da ya amsa sunan sa na masu damshi wanda take da tabbacin su sun gama talauci da yarda Allah tunda wannan rabon ya biyo yanzu zasu fara ta tsar shi son ran su.Godiya Nadiya tayi wa Binta saboda NAJIBA ta sanar mata da itace ta kira ta kuma taji farin ciki sosai ko ba komai ta samu mataimaki da yanzu sai dai ta mace ita kaɗai a gida ƙila ma sai ta ruɓe a san da ita warin ta ya ishi mutanen unguwa sannan a zo bincike.Wani girman matar ta ƙara gani wadda zata yi sa,a da mama Hafsatu.Itama mama Hafsatu godiya tayi mata cikin sakin fuska abinci ta zubo masu dukkanin su sai dai babu wanda ya ta ɓa nashi a tsakanin Nadiya da NAJIBA,Mama Hafsatu kam zama tayi ta rushi abinta har naman da aka saka mata ko mai ƙashi ba ta rage komai ba.Shiru dukkanin su suka yi suna kallon ta ita kuwa ko ajikin ta Dan ko Tanim ya faɗo ba abinda zata bari anan sai ta ci tayi damm suko shine suke jin nauyin ya shigo ya ga wannan abun kunyar Dan har mayafi sai da ta cire ta ajiye gefe irin haka kuma a ɗakin Nadiya ya dace tayi haka daga ita sai yar ta.
Tana gamawa tayi Hamdala.Sannan ta bar gidan tana yin Hamdala murna ta cika mata ciki yar ta na cikin Alkhairi,yan kudaɗen da NADIYA ta bata da su ta shiga napep tana barin unguwar.Tana fita shiko Tanim yana kutso kan motar shi cikin gidan hankalin sa kwance.
Yana gama daidaita parking ɗin motar sa sai a lokacin idanun sa suka sauka akan shi yana zaune cikin mota ya kifa kan shi a kan steering abubuwa sun taru sun masa yawa.Shegen Murmushi ya sake sannan ba tare da ya bi ta kan shi ba ya shige cikin gidan sai dai yayi mamakin dalilin ganin shi cikin gidan yanzu abinda ya sani kawai NAJIBA na gidan shi ya sa ya raɓa shi ya shigewar sa.
Shiko Jamil dake cikin motar yayi zurfi a cikin tunanin sa bai ma san tafiyar Mama Hafsatu ba,Ya miƙe jin kamar takon tafiya sai dai bayan sa ne kawai ya hango yana shigewa cikin ƙaton falon.Duk da bai ga fuskar shi ba ya san ko wanene.Numfashi ya sauke a hankali yana mayar da kan sa akan steering ɗin motar kan sa na sara masa.
TANIM kuwa da shigar sa babu ko sallama ya fara yan waƙe waƙen sa yana yi yana ɗan yin tsalle irin na jin daɗi,duk da kuwa ya san NAJIBA na gidan hakan bai sa yayi behaving irin na mutumin kirki ba Har ya kawo tsakiyar falon.Yana tsintar kan sa tsakiyar falon ya fara ƙoƙarin zama a cikin falon yana sakin ɗan murmushi yana furta " A'ah Yau NAJ ce a gidan na mu ". Murmushi NAJIBA ta ɗan ƙaƙalo itama tana gyaɗa masa kai dan ita kam ayanzu ko magana bata jin tana son yi dashi haushi yake bata matuƙaa ga wata irin tsanar shi da take ji.Gaisawa suka yi lafiya kamar babu wani abu dan shi ma yaga kiran ta da gangan yaƙi ɗaga shi a lokacin yana tsaka da holewar sa da Da ƙaruwar sa,sai ya share kiran daga baya kuma maimakon ya kira sai ya share duka kiran duk da yayi mamakin ganin kiran nata ita da Najiba a lokaci ɗaya.Sai dai a ƙasan zuciyar shi dariya ce yake babbaka wa NAJIBA domin ya san abinda ke tun karo ta sai ya girgiza ta wanda ya san cewa ita taja wa kan ta ya so ace gaban shi za,ayi dambarwar ya sha kallo dan yana son irin wannan game ɗin tana da daɗin kallo a ranar da za,a buga final game,tunanin da ya ƙara shiga ne na abinda yake hangowa zai faru ya sa shi fara sakin wata irin dariya yanayi yana kallon NAJIBA kafin kuma ya shige bedroom ɗin sa ba tare da ya nemi sanin wani abu ba duk da ya ga hannun NADIYA da cannulation domin ba,a cire mata ba may be ta koma Asibitin,ko a same ta gida a ƙara ma ta drip dan samun Ingantaccen ƙarfin jikin ta.
Najiba kuwa da ke bin shi da ido kamar wadda ta ga sabuwar halitta ta sauke numfashi kafin ta juyo da kallon ta kan Nadiya da ke sakin wani irin Murmushi wanda zamu iya ayyana shi da murmushin da yafi kuka ciwo dan daga nin ta ka san ƙarfin hali take yi bana wasa ba.Miƙewa tayi bayan ta ƙara bata baki sannan ta fice da zummar zata dawo gobe.Haka Nadiya na kallo Najiba ta fice wanda take jin kamar ta dawo da ita.Tana wucewa ta miƙe cikin rashin ƙarfin da ke cin jikin Ta ta shige bedroom ɗin na ta.Tana shiga zama kaɗai tayi akan gadon nata kawai taji an Turo ƙofa da ƙar fi har sai da ta tsorata.Idanu ta zuba mishi ƙirjin ta na bugawa a hankali kafin ta samu bakin iya furta masa ido cikin ido " Lafiya ".?
Dariya ya ƙyalƙyale da ita kamar wani shaiɗani sannan ya dube ta da kyau yana haɗe ranshi yana furta " Haƙƙi na nazo karɓa ".Yayi furucin kai tsaye yana doso ta.Ko ɗar bata ji ba domin ta san shine abinda ke kawo shi guurin ta.
Daga inda take bata motsa ba sai hawaye da ke ƙoƙarin sauko mata ita kaɗai ta san halin da take ciki na rashin ƙarfi jiki sai kuma gashi wannan mara imanin zai ƙara sanya mata rauni wanda ya daɗe da zama a cikin zuciyar ta.Shanye hawayen tayi jin yana ƙara ke cewa da wata mahaukaciyar dariya kafin kuma ya janyo ta jikin sa da ƙarfi yana mannata akan fatar sa kasancewar towel ne kawai jikin sa da alama daga wanka a fito yanzu sai kuma yayi tushe nan,Dan da gani towel ɗin ne kawai jikin sa.
Ƙara Nadiya ta saki kaɗan kafin ta samu bakin ƙara furta " Kaji tsoron Allah Tanim " Dan yanzu babu wani boo babu wani sunan soyayya tanim ɗin shi take kiran shi dashi wata rana ma.Tanimun sa.
Yi yayi kamar bai jita ba kafin kuma ya sauke mata wani irin mugun mari akan furucin ta na ƙarshe " Abinda kake aikatawa Asara ce babba mai cike da wahala da ƙuncin azaba ribar masu aikata shi wuta ce idan babu tuba..." Shine abinda ta furta wanda ko gama furucin bata yi ba ya sauke mata marin da ya sanya yan hanjin cikin ta ya mutsawa kafin jini ya ɗan fara sauka daga gefe gefen bakin ta.
TANIM kuwa bai bi ta kan ta ba ya ɗaga ta Chak bai tsaya duba yanayin da take ciki ba,ya dire ta kan gadon kamar wata kayan wanki sannan ya bita jinin da ke ɗan ƙara fita ta bakin ta ta ya ke lakatowa da yatsan sa yana kaiwa bakin sa yana tsotsewa kafin kuma ya saka harshen sa ya lashe shi tsaff yana suɗar baki kamar wani tsohon maye.Sai da ya suɗe shi tass sannan ya haɗe da harshen ta da yayi jaa shima da haƙoran ta ya suɗe sannan ya fara ƙoƙarin ƙara kai mata wani marin janye fuskar ta ta yi da sauri cikin wani irin mahaukacin tsoro kafin ta ankara kuwa ya ƙara kifa mata wani marin da yafi na farko dan har jin ta ya ɗauke.Jinin da yake son ya ƙara fitowa ne ya fito ya kafa bakin sa da sauri yana lasa tare da zuƙowa yana sakin Ajiyar zuciya.A gare shi ba wani abun bane jinin yayi mashi daɗi domin a duk lokacin da ya bugu ya bugu idan yayi shaye shayen sa jinin shine abinda ke biyowa baya wasu lokuttan haka zai yanka hannun sa ya sanya a bakin sa ya zuƙe kamar wani mai tsafi sai dai ba haka bane zallar Chaji ne da yayi masa mugun ruƙo,jinin ma sabon Chaji yake ƙara masa na fitar hankali.Nadiya kuwa kuka kasa fito mata yayi sai sauraren ikon ALLAH da take yi domin ta kasa buɗe idanun ta tun da ya fara ƙoƙarin shige mata ta ƙarfi dan bayan mari harda bugu ta ko ina haka take jin shi yana juya ta ta ko ina har ya gama bidirin shi bata iya ko ɗaga yatsa sai yadda yayi da ita.
Numfashin sa da taji a kusa da kan fuskar ta ne ya sanya ta ɗan buɗe idanun ta dake zubar da hawaye wayenda suka yi wani irin jaa na baƙin ciki da wata irin mahaukaciyar ƙiyayya da Allah ya saka mata a a yanzu ta shi, a yanzu burin ta na farko ne yake shirin ya chan za burin shine barin gidan Tanim ta koma gaban iyayen ta lallai zata yi amfani da shawarar yar uwar ta har ila yau ta kai shi ƙasa ta bar gidan na sa.
Hmmmm Nadiya kenan Allah ya sa zaki iya.🤦Tanim hatsabibancin sa yafi shi yawa.
Team Nadiya aka wo agaji hiliss🧐
" Kin ƙara zaƙi Hajiya kwaɗayi ".
(Too ina daɗi,wanga kalar raini da cin mutunci kan abun duniya.🥺🥺)
Shine furucin da ya ya sauka a cikin kunnen ta kafin kuma.ta ƙara jin shi ya na furta " Me ye sirrin? Lashi money ".
Shiru ta masa kafin ta sauke Ajiyar zuciya ta na mayar da idanun ta ta rufe.
Rashin amsa masa ba damuwar shi bace hakan ya sa ya sauko ya nufi ɗakin na sa ba tare da tsoron wani ya gan shi a haka ba ko masu aiki ko baƙi.
Itako Nadiya kuka ne ya kubce mata mai taɓa zuciya sai da ta sha abun ta ta miƙe cikin tausayin kan ta ta faɗa toilet wanka ta ɗauro tare da yin brush sannan ta dawo ta yi Sallah sannan ta yi Addu,oin ta,ta haye gadon take kuwa bacci ya kwashe ta Dan shi kaɗai take bukata a yanzu.
MATAR KHALILLULLAH.
Raliya da Ibrahim kuwa wata irin shaƙuwa ce da fahimtar juna ce ta ƙara shiga tsakanin su tun daga wacchan ranar baka taɓa jin faɗan su sun haɗe kan su sun zama abu ɗaya kamar yadda ake faɗa kamar yadda kowacce budurwa ko uwa take fatan samun ingantaccen miji mai tausayi kamar sa ga yar ta to Ibrahim ya kai, Dan Ibrahim bai rage Raliya da komai ba ko tari ta yi sai ya bincika idan na lafiya ne,baya barin ta kuka gwargwado duk da baya da wani arzikin yana kashe mata ƙishin ta na duk wani abun da take buƙata a matsayin shi na adalin miji mai cike da ƙaunar matar sa abokiyar zaman sa.
A yanzu haka cikin yan kwanakkin nan ya nema maata gurbin karatu a wata college of health dake nan kusa da layin su.Wanda har ga fara zuwa ɗaukar karatu a dept ɗin community.Raliya tayi farin ciki sosai haka ma yan uwan ta mama Hasiya da ta san burin Nadiya ne ta yi murna sosai da Binta da fatan Alkhairi da addu,oin ƙara samun zaman lafiya ga ya'yan na su baki ɗaya da mazajen su.
Yau ma a gajiye ta dawo saboda wani irin ciwon ƙafafun da take fama dashi wanda bata san yaushe ya shige ta ba domin ta san cewa bata dashi.Har Ibrahim ya dawo ta tarbi abunta bata bari ya lura ba sai ƙarfin hali da take yi tana ɓoye yanayin da take ciki domin tabbas ita kaɗai ta san yadda take ji dan kamar ta ajiye su gefe haka take ji.Har ta gama sintirin ta ta zauna Ibrahim na lura da ita sai dai ya basar kawai ganin yadda take kame kame sai da ya gama cin abincin sa yayi Nak.sannan ya shiga bedroom ɗin nata yajanyo hijab kasancewar shiryen ta take kamar kullum tayi yar ƙibar ta ko'ina nata ya cike ciff bazaka taɓa cewa Raliyan Umma ce ta sauya ta koma matar Ibrahim ba yar Umma ba Dan a kallo ɗaya zaka san cewa ta na cikin kwanciyar hankalin ta da Natsuwar zuciya da mijin ta a cikin gidan na ta.Yoo gidan ta mana ai ya zama na ta.🙃
Kallon shi kawai tayi da hijab a tsaye kafin ta ankara har ya zura mata shi ganin ta kasa motsawa sai ido da take bin shi da shi da suka fara tara ruwa Dan ta kasa riƙe abun Dan ciwon na son yafi ƙarfin tunanin ta.Hakan ya ƙara tabbatar masa da ba lafiya take ba dan komai a bayyane yake ya san ciki da bai na Raliya tun shigowar sa ya san ba lafiya take ba.
Bai ce mata ƙala duk da yaga yadda hawayen ke neman fito mata sai ma hannun ta da ya kama.
Ficewa suka yi daga gidan bayan ya rufe ko ina mashin ɗin sa da ya fitar suka hau bai zame da su ko ina sai A sibitin Murtala dake kusa dasu anan ya kai ta Sauƙin ta ma babu jama,a anan sosai shiya sa suka samu aka karɓe su da wuri.Anyi mata Aune Aune bayan ganin likitan har result ya fito sannan suka koma gurin likitan.
Murmushi likitan yayi kafin ya kalli Raliya da duk ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 39