Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na ta, cikin tausayin na ta da yake ƙara mamaye mata zuciya.Ji take kamar ta saka mata kuka itama sai dai bazata so ta ƙara samun rauni ba shi ya sa take ƙoƙarin shanye komai tunda har yanzu bata san abin da ke faruwa da yar Tata ba. Bayan ta tsagaita kukan na ta ne ta miƙe a hankali ta fice toilet ɗin su dake tsakar gidan.Alwallah ta ɗauro kafin ta tada Sallah. Bayan gama sallar ta ne malam Rabu'u ya shigo da sallama yana sauke ajiyar zuciya tare da zama a ɗai daga cikin yan madaidai tan kujerun dake falon. Gayar da shi Najiba tayi kafin ta miƙe ta shige ɗakin da yake mallakin su kafin su yi Aure wanda kuma yana nan yadda yake sai yar katifar da aka chanza masa wadda RALIYA ta bawa mahaifiyar ta,saboda Ibrahim ya sayo mata wata sai ta saka Tata a ɗakin na su. Kwanciya tayi akan gadon tana sauke numfashi kafin bacci yayi awon gaba da ita. Mama Hasiya da ta shige domin yin Sallah itama bayan ƙarasa sauran ayyukan da ta bari a tsakar gidan,inda Mama Hafsatu ke ta bugun cikin ta sai dai bata ce mata kala ba tunda itama bata san me yake faruwa ba har yanzu ta dai zuba ma saurautar Allah idanu,har Najiba'r ta ƙara samun natsuwa ta san lokacin zata iya yin magana yadda ya dace. Ganin idanun ta a Lumshe hakan ya sa ta jinjina kan ta ,ta juya zuwa cikin ɗan Falon na su. Malam Rabu'u da ke zaune yana ƙullawa da kuncewa ya ɗaga idanun sa ya kalli Mama Hasiya da ta zauna yanzu akusa da shi tana sauke ajiyar zuciya. Ɗan sauke idanun shi yayi kan ta kafin ya furta " Ta faɗa Miki abun ke faruwa ne ". Kai Mama Hasiya ta girgiza masa dan tabbatar masa tana zama a kusa dashi. Kai ya jinjina kafin ya furta " Lamarin Najiba sai dai muce Allah ya sauƙaƙa dan bazamu yi mata Allah ya ƙara ba jarabawa ce ta haɗu da ita,Mijin ta maƙaryaci ne kamar ta,yadda ta yaudare shi haka ya yaudare da ta har mu iyayen ta tunda har muka gama nema mata Auren sa muda su malam Amiru babu wanda ya san cewa ba asalin iyayen sa ne muka bawa Auren ta ba,Babu abinda yake na gaskiya a tarayyar su face soyayyar da Allah ya ceci zukatan su da ita,wannan shine makamin da zai daƙushe komai na gigin rabuwar su ba zan taɓa bari Najiba ta rasa wannan damar ba domin wata dama ce wannan Ubangiji ya bata bayan wasa da rayuwar ta da tayi,Ban san mai ya yan mu na talaka suka ɗauki rayuwa ba suna tunanin kamar rayuwar ya yan masu kuɗi itace rayuwar jin daɗi,Rayuwar masu kuɗin itace Duniya,shin me kuɗi na wa yake kwana cikin ƙunci,Mai kuɗi nawa yake zama da ƙunci harƙarshen rayuwar sa,mai kuɗi nawa kudin sa ya kasa amfana masa,mai kuɗi nawa yake kuka a rana,mai kuɗi nawa ke bara da arzikin sa,Mai kuɗi nawa kuɗin sa suka zame ma sa jarabawa,Masifa,bala'i,mai kuɗi nawa yayi kuka da dukiyar sa,wani babu lafiya da kuɗin na sa,ga kuɗin babu lafiyar ci,ga kuɗin rayuwa na neman tafiya,tana cike da wahala,sai dai bata yi amfani ba,wani babu zuciyar ci da kuɗin,wani da kuɗin amma matan sa da iyalan sa basa cin mai kyau su sha mai kyau,Waje da kyau ciki babu kyau,Sai kaga yarinya ta dage sai mai kuɗi kamar dai Najiba kuma wannan ba hanya ba ce,sai yanzu na ƙara fahimtar rashin kawo samarin nan nata gidan nan tana tsoron mu lalata mata komai saboda ta riga ta gina kan ta da karya ta ɗauki halin da ba nata ba ta ɗauki rayuwar da bata dace da ita ba,Ban san me ya,shiga idanun mu ba, Har muka iya zura musu idanu itadah Nadiya,sai dai Alhamdulillah muna kan gode ma ubangiji da ya sa basu zare mu a matsayin iyayen su ba saboda talaucin da suke gani a gare mu ". Ɗan numfasawa yayi yana sauke Ajiyar zuciya idanun shi na sauyawa kafin ya cigaba da magana yana furta. " Najiba ta yi abin da nake ji alabaran Da ke yawo a bakunan jama'a,Talaka baya da abun hange face mai kuɗi mai kuɗi kuwa babu wanda ya tsana kamar talaka mai neman na gobe,ba dukkanin su suke iya haɗa iri da mai neman na yau da na gobe ba,Idan duka yan matan da muke da su ya yan talakawa irin mu suka ce dole sai sun Auri mai kuɗi kamar dai NAJIBA,wa zai Auri Maza (yaran mu ) talakawa yayyen su da dangin su,inajin Haushin ganin masu irin wannan rayuwar sai dai ashe nima yata , ta ciki na a wannan turbar take kwance,Kai co na Ni Rabu'u,mai ya rufe muna idanu muka bar yar mu ta cigaba da rayuwa a wannan banzar rayuwar da bata ɓullewa bata da riba,yau gashi komai ya buɗe,idan an tashi bada misalin irin hakan sai An kira ya ta domin ya zamo izina ga wasu, NAJIBA dole zata koma gidan mijin ta yadda suka fara rayuwar su haka zasu ƙara Tata har ƙarshen Rayuwar su zan bata loka ci ne kafin na ga iya ruwa gudun ta,mun kitse magana da Yaya Abdul basiɗ komai zai wuce in Sha ALLAH,ki ƙara kwantar mata da hankali ta samu natsuwa,Shi yaron ya sanar damu komai ". Shiru yayi kafin ya bata labarin duk abinda Jamil ya faɗa masa saboda yayi ma ta a zantuka a dunƙule ya san tana buƙatar jin komai a buɗe. Shiru mama Hasiya tayi zuciyar ta cunkushe da wani irin zafi mai ɗaci ga wani irin Tausayin yar ta. miƙewa ya yi shige ɗaki ya bar Mama Hasiya zaune cikin wani irin yanayi da ke ƙara Kutsa jinin ta na tausayin yar ta, ta san lallai babban abune ya saka Najiba dawowa gida ga kukan da ta ke ta yi wanda daƙyar ta samo kan ta. Yar ƙwallar da ta sauko mata ta shafe cikin tausayi yar ta,Abun da ta guje mata tun farko kenan,lefen Najiba ma da aka kwashe lamarin ya tsaya mata a rai kuma tun na kawo shine,bata san dalili ba zuciyar ta,ta kasa natsuwa da komai na Auren yar ta shiya sa akoda yaushe take cikin yi mata Addu'a har ta ɗan fara samun natsuwa. Miƙewa tayi ta kama hanyar fita daga falon.Mama Hasiya da ta gama sauraren komai daga bakin ƙofar da take laɓe ne tayi Sauri ta cigaba da yin shanyar ta tana Yan kame kamen ta. Mama Hasiya dai bata kula ta ba sai ma Murmushi kawai da ta saki domin ta ga ne laɓe tayi musu.Shiya sa bata bi ta kan ta ba. Kayan da take ɗan wanke wa na wanke wanke ta karasa sannan ta dawo ɗakin sai dai tana yi tana sauke Ajiyar zuciya cikin tausayin yar ta.Zuciyar ta cunkushe da ɗaci ita tasan bata yiwa yar ta baki ba Amma ta san ɗabi'ar da Mama Hafsatu ta ƙara jefa ta ba mai ɓullowa ba ce,domin gaskiya bata taɓa zama akan ƙarya komai rintsi. Kiran sallar la,asar ne ya farkar da Najiba daga bacciin da ya kwashe ta kasancewar yanzu tana ɗan tashi da wuri ba kamar da ba,yanzu duk nauyin bacciin ta da lokacin Sallah yayi sai Allah ya farkar da ita. Ya mutsar fuskar ta ta fara yi Sannan ta miƙe tana sauke Numfashi jin idanun na ta na mata nauyi ga wani irin zazzafan zazzaɓi da ta tashi da shi kan ta har wani juyawa yake mata. Da ƙyar ta miƙe tana ambaton sunan Allah sannan ta fice ta ɗauro Alwallah adaddafe. Kasancewar bata tarar da kowa a falon ba a tsakar gidan ma,hakan ya sa ta yi Alwallah ta shige sannan ta tada sallah La,asar a nan. Mama Hasiya data fito da niyyar tada ita ce ta saki ɗan murmushi tana sauke Ajiyar zuciya. Saboda taji wani irin daɗi ya kamata na ganin yadda Najiba'r ta,tada, ta dawo Dan haka ta ɗau Alwashin bazata taɓa bari Mama Hasiya ta janye mata " yaa ba a wannan karon zata tsaya tsayin daka ta kula da yar ta. Abincin da Raliya ta saba Aiko ma iyayen nata ne ta zuba mata haɗaɗɗiyar jallof da ta ji wake,a gefen ta ta ajiye abincin tare da ruwa,sannan ta Nemi guri ta zauna,kasancewar ita ma ta riga ta yi Sallah. " UMMA ina wuni ". Najiba ta furtawa mahaifiyar ta cikin ɗan murmushi bayan tagama yin Addu,o,in ta. Mama Hasiya da ta lura da Najiba na yatsinar fuskar ta bayan Amsa mata gaisuwar ta ta,da murmushi itama kamar yadda Najiba tayi ɗin. " Kici abincin,sai Kisha magani,naga kamar akwai zazzaɓi kan ki ". Kai Najiba ta jinjina kafin tayi bismillah ta fara cin abincin hankalin ta kwance. Sai dai lomar farko kaɗai ta kai ta fahimci girkin yar uwar ta ne,taji daɗi sosai dan haka taƙara samun ƙwarin guiwar cika cikin ta dama wata irin yunwa ce ta ta so mata a lokaci ɗaya. Ringing ɗin wayar ta ne ya miƙar da ita,da sauri ta shige uwar ɗakin ta. Wayar ta ɗakko wanda har kiran ya yanke. Murmushi ne kwance akan fuskar ta ganin mai kiran nata. " Waslm RALIYA na kin wuni lafiya,ya makarantar,ya karatu ".? Mama Hasiya ta furta bayan jin sautin Sallamar Raliya da ta furta cikin farin ciki da murmushi. Amsar da ta bata ce ta sanya ta sakin murmushi tana ƙara furta. " Ai haka boko yake,ko nace neman ilmi RALIYA sai an kai zuciya nesa,Allah ya bada sa,a kinji an rale Le na ". " Ameen UMMA ". RALIYA ta furta zuciyar ta fess murmushi kuwa kwance akan fuskar ta.. " Wai Ni bana ce a daina dafa abincin nan da yawa haka ba,bamu cinye wanda kike aikowa RALIYA ". Mama Hasiya ta ƙara furtawa. " Umma na Yaya Ibrahim yace ariƙa saka muku da yawa ba sai kunyi girki ba,Naji yace ma Za,a kawo maku kayan abincin tunda kullum complain kike yi Umma ". RALIYA ta yi furucin tana ɓata kyakkyawar fuskar ta. Ibrahim dake da ya shigo,wanda ya dawo daga kasuwa yanzu ya sauke Ɗan murmushi yana kallon ta kafin ya buɗe hannayen sa ta faɗa yana sakar mata murmushi. Sallama sukayi da Mama Hasiya da tayi godiya tare da furta a gayar mata da Ibrahim. Sai dai bata faɗa mata wani magana game da yar uwar ta ba gudun ɓata mata yanayin da take ciki. Murmushi RALIYA ta ƙara saki tana shigewa jikin sa tana sauke Ajiyar zuciya saboda ƙafafun na ta sun fara sauƙi sosai laulayin ma ta daina sai abinda ba,a rasa ba. " Sannu da dawowa Hala lina ". RALIYA ta furta masa tana kallon fuskar sa mai cike da haiba da annuri hasken Amarci yana ta ƙara ratsa jikin sa yayi fresh dashi ya ƙara fitowa Ibrahim ɗin sa. " Yawwa my Halal,fatan kuna lafiya keda Babyn mu ".? Kai ta gyaɗa masa cikin jin yar kunyar sa sannan ta riƙa hannun sa bata zame da shi ko ina ba sai a bedroom na su. Da taimakon ta ya zame suturar sa Sannan ta haɗa masa ruwan wanka. Wanka ya ɗauro tare da alwallah duk da bayan la,asar ne. Tsaff ya shirya cikin riga da wando na captani masu kyau yan dai dai kuɗin sa. Abincin sa da kan ta,ta ciyar dashi da shayar dashi suna yi suna taɓa firar su ta soyayya wadda ke nuna irin shaƙuwar dake tsakanin su da ƙaunar junan su. Nan take sanar dashi rashin lafiyar Nadiya. Bai yi ƙasa aguiwa ba ya ɗauki ta ya kai ta gidan Nadiya. Tayi mata ya jiki suka taɓa yar fira sannan sukayi sallama. Sai dai dukkanin su suna kallon juna a kaikaice ne ita Nadiya na kallon mugun chanjin da ƙanwar ta su ta samu ne,ita kuma RALIYA na kallon yadda yar uwar ta ta sauya kamar ba ita ba,sai dai bazata iya tambayar ta dalili ba duk da yadda ta hango damuwar kwance akan fuskar ta ba .Ta ji babu daɗi aranta sai dai bata iya tambayar ta ba domin tana kunyar ta Sosai kuma tana son ta kamar yadda take son NAJIBA duk da banbancin mahaifa da suka zauna. Haka suka yi sallama da juna gudun kar ta sakawa ranta Damuwar ga ɗan ƙaramin cikin ta hakan ya sa ta bar lalacewar ta Nadiya a Matsayin shigar sabon ciki ne ke da mun ta. *** NAJIBA a jiyar zuciya ta sauke tana sauraren wayar da mahaifiyar ta ke yi wadda take a handsfree gaba ɗaya. Wata irin ƙaunar yar uwar ta ce ta ke ƙara Kutsa jinin ta na ragewa iyayen na su aiki,abinda ta so yi kenan sai dai Jamil bata ga fuskar hakan ba, Dan kaɗan yake ajiye musu abinci wanda in tace ta riƙa ɗibar sa zai ƙare musu da wuri,kuma ko bayan hakan mahaifiyar ta gargaɗe su da satar abincin miji kamar dai a ce ta fara ƙoƙarin aika ta hakan,sai ta ta kasa gudun abun da zai biyo duk da ta san shi mai kuɗin a chan baya sai bata aika ta hakan ba,kuma sai ta kasa neman izinin sa.Taji daɗi sosai da yar uwar ta ta yi dacen miji kamar Ibrahim da suke yi wa kallon talaka na ƙwarai ashe shine zaƙaƙurin miji duk da itama nata yana yi sai dai ƙaryar da ta surka su ce ita dashi ta hargitsa komai. Ajiyar zuciya ta sauke tana ajiye zancen zucin ta gefe tana baza Kunnuwan ta ga Mama Hasiya da ta fara magana a tsanake cikin Rarrashi. " Najeeba,bawa baya taɓa wuce ƙaddarar sa wannan ita ce ƙaddarar ki domin kin kasa tsallake mata duk guje gujen ki,Abinda kike gujewa ya riga ya auku,Auren Talaka ba mugun abu bane ba illa ce ba,Kinga shaida dan mahaifin ki talaka ne,kuma muna cikin farin ciki ke kan ki shaida ce,Najiba Auren talaka ba baƙar rayuwa bace,ba rashin jin daɗi bane,Amma kun kasa gane hakan kun biyewa zugar ƙawaye da suke kira muku, kuna da kyau sai ma su kuɗi da kuma Mamar ku Hafsatu domin na san tabbas har da zugar ta,sai dai ban ɗaura laifi kan ta ba domin ku ba ƙananan yara bane,kuna da hankalin ku,Na so ki gane wani abu tun kafin lokaci ya ƙure Miki Najiba,shi Auren talaka mai Rufin asiri wanda zai iya ci dake ya sha dake ya fi Auren wasu masu kuɗin sau tari ba adadi,Domin wani Auren mai kuɗin suna ya tara Najiba,Saboda babu kwanciyar hankali,babu natsuwar zuciya,kullum cikin zullumi da tashin hankali babu ci na kirki ba bu sutura,Shin Da irin wannan ba Gara Inda zaki zauna ki samu natsuwa ba,da yawa yan mata irin ku abun da basu gane ba kenan Auren mai kuɗi ba shine jin daɗin duniya ke dai kiyi fatan Allah ya bak mai iya ɗaukar dawainiyar ki,da kulawa da duk wata damuwa ta ki, wanda idan kika yi kuka zai share maki hawaye,yazamo idan kina cikin damuwa shima zai tsinci kan sa ciki,wanda zai san farin cikin ki da baƙin cikin ki,ba wanda zai Kalle ki ya watsar ba ko wanda bai da lokacin ki,bare ma har ya san da damuwar ki ya kawo Miki mafita.Wanda in kika lalle shi zai sakar miki murmushi ba wanda zai harare ki ba ya kira ki da mayya ba,Wanda ya san zafin ki da kishin ki,ba wanda zai ga ana cin mutuncin ki ba ya Miki Allah ya ƙara ko ya Miki dariya,ko ya ɗauke idanun sa ya wofintar da ke ,Ki samu mai tausayin ki ga ci ga sha ga sutura shine rayuwar jin daɗi, Wallahi Auren talaka natsuwa ce Babba idan kin samu mai son ki da tausayin ki,da kuma mai kulawa,Kiyi haƙuri Najiba haka Allah ya tsara komai zai zo ya wuce na san cewa wata rana in Allah ya yarda zaki samu yadda kike so a gidan ki, Wata rana Jamil zai yi arziki,kowa da yadda Ubangiji ya tsaro mishi rayuwar shi,Mafi yawancin masu kuɗin da kike gani a tare da matan su suka yi arzikin in ba waɗan da iyayen su suka tara musu ba irin masu mahaukatan kudaden nan,iyayen na su sukan tara musu ,sai kuma yanzu da kai ya waye matasa na nema sosai,kar ki saka damuwa kin ji komai zai wuce,bana son jin zancen sakin da naji daga bakin mahaifin ki domin ya sanar mishi da komai kuma yadda mahaifan ki suka lura yayi nadama sosai,Nasan cewa ko ba,a faɗa ba ke kin san da hakan, Ki yi haƙuri ki zauna da mijin ki lafiya ku gina rayuwar ki da ta iyalan ku da zaku tara anan gaba,ku riƙe soyayyar da kuke yiwa junan ku hakan zai sa ku ga cigaban ku,Allah yayi Muku Albarka,Ya saka ma rayuwar Auren ku albarka,Sannan ki rufe kunnen ki da zancen mutane,kamar yadda zan rufe nawa, haka Allah ya tsara wannan ba wani abun bane sauƙin ta ma Allah ya bayyanar da komai da wuri,ƙarya bata da kyau ko ta wasa ce karki ƙara kwatanta hakan a rayuwar Auren ki,sannan duk wata ƙawa da kika san tana ɗaura ki a hanya mara kyau ki rabu da ita kinji ". Mama Hasiya na gama zancen ta sauke numfashi tana sauke Ajiyar zuciya ganin Najiba Jikin ta yayi sanyi da alama zancen ya shiga kunnen ta Dan yadda ta natsu zaka san cewa zantukkan sunyi tasiri a gare ta. Hawaye ga share a hankali badan komai ba sai na tausayin yar uwar ta Nadiya da ke cikin ƙuncin rayuwar da bata taba hango kan ta a cikin ta ba,Rayuwar da ita kan ta Nadiya bata san inda ta jefa kan ta ba,kuma ba komai ya kai su ba face kwaɗayin Abun duniya dukkanin su,yar uwar su ce kaɗai ta bi hanyar da ta dace. Tabbas duk abinda mahaifiyar ta ta faɗa gaskiya ne,ba abinda zata iya cewa sai Allah yayi mata mafita Dan ita kam abu guda ne take jin zata iya bijirewa mahaifiyar ta shine rashin janye maganar saki dan bata jin zata iya komawa gidan Jamil kwata kwata dan taji zafin abun har cikin ran ta,matuƙa. Yoooo an rama kura haɗiyar ta Najiba ko wa ya jefa wani meye na ta da hankali a ci ki.🤦🤦🤔 Da wannan tunanin tayi wa mahaifiyar ta godiya sannan ta shige ɗakin na su tana share wasu hawaye da suka silalo mata na tausayin kan ta da na yar uwar ta. Kuka ne ya ci ƙarfin ta na tausayin yar uwar ta tare da na Tausayin kan ta da rayuwar su ta baya arzikin su ɗaya da komai ya buɗe musu da wuri. Tana fara kukan nan ko minti bakwai ba tayi ba bacci ya kwashe ta mai nauyi,zazzaɓin da ke jikin ta na ƙara haɓɓaka. Mama Hasiya da ta shigo yanzu bata maganin zazzaɓi ta sha ce ta sauke Nannauyan Ajiyar zuciya tana girgiza kan ta tare da sakin murmushi mara tsawo. Sannan ta fice daga ɗakin bayan ta ƙara taɓa jikin ta ba ta damu da bata maganin ba domin ta san zata iya yuyuwa ta tashi ciwon kan ya sake ta kuma shi ya sa bata matsa da sai ta, ta da ita daga baccin na ta ba. Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg✍️ Like,share,react.pls🙏 Ƙarin Bayani *08069059746* Chat only...... *_Typing_* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *_Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chan zaku samu cigaban update.Farkon labarin masu so sai a mun magana a numban dana sauke ƙasan wannan page, Dan samun document.☝️_* *🌸RAYUWAR MU AYAU🌸* Ƙarya ko sakin Aure Gajeren labari Na Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa Ga Mahaifiya ta Abar Ƙaunata Allah ya Ƙara Miki Tsawon Rai Mai Albarka Mama✨✨✨.Amin. Bismillahir Rahmanir Rahim 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _ *TAFIYAR TAURARI HUƊU ⭐⭐⭐⭐*_ _~~*Taurarin marubuta huɗu team*~~_ _*Daga marubuciyar littafin*_ _*A Mafarki Nasanta*_✍️ And now _*Rayuwar mu a yau*_ P.26 _# TAURARI HUƊU_ _# Fake life_ _# shame_ _# Najmil_ _# pregnancy_ _# Nadiya_ _#Tanim_ _#Khalillullah's wife💞_ *** Bata miƙe daga baccin na ta ba sai kusan sallar la,asar. A gajiye ta miƙe saboda bayan ta da ke ɗan yi mata ciwo da jiki ga kan na ta yana ɗan sarawa kaɗan sai dai ba kamar yadda ta kwan ta ba. Alwallah ta fita ta ɗauro sannan ta dawo ta tada sallah. Mama Hasiya data fito yanzu daga ɗakin ta bayan gama sallah ta saki Murmushi tana ƙara tsintar kan ta cikin farin ciki. Ɗakin ta koma tana cigaba da lazimin ta Dan dama fitowa tayi ta tada ita bacci sai ta tarar da ita tana Sallah. Á ɓangaren Jamil kuwa suna dawowa basu yi tsinke a ko ina ba sai ɗan ɗakin na su. Cikin farin ciki dan baiyi tunanin komai zai zo masa da sauƙi ba ta gefen mahaifin sa,sai gashi komai ya zo masa a sauƙaƙe. Gariti kuwa da shigar su ko hutawa basuyi ba ya dinga dariya harda riƙe ciki. Yana yi yana furta " Nifa Jamil abun na ku dariya yake bani yanzu,shin yanzu baka jin kunyar ƙara haɗa idanu da iyayen ta,da ita kan ta,ga kuma mutanen gari dan na san zance sai ya fita,ko da yake ita ma Najiba kan wa ɗaya ce da kai".. Yana kai ƙarshen zancen wata irin muguwar dariya ta ƙwace masa sai da yayi mai isar sa sannan ya yi shiru ya buge da tsokanar sa yana janyo masa abinda ya shuɗe yadda yake ta ƙoƙarin ganin ya burge Najiba a tunanin sa yar masu kuɗi ce. Jamil dai kai kawai yake girgiza wa dan ya fahimci lamarin na Gariti ba na hankali bane. Shi yasa yanzu ya koma yana bin shi da murmushi kawai ganin dariyar ta kasa tsaya masa duk da yasan dukannin maganganun sa gaskiya yake faɗa acikin su. Gashi har yanzu Mamaki bai sake shi ba Ace NAJIBA'r sa itama maƙaryaciya ce, ƙarya take yi masa duk tsawon lokacin da suka ɗauka,ace har wasu iyayen zasu iya goya ma ta baya,idan ba goyon baya ba mai zai sa Hajiya Samira ta yardar mata tana zuwa gidan ta ana cin amanar sa,Sannan Alhaji Ahmad mai zinari,har suyi miya suyi tuwo a Auren na su a matsayin Uban Amarya sai dangin ta da yake tunanin wasu dangin su ne na gefe a she iyayen NAJIBA'r ne. Ta yuyu bada son ran ta tayi ba,ta yi ne saboda taren ta da umman Nadiya Wata zuciya ta bashi Amsa. Numfashi ya sauke kafin ya miƙe yabi bayan Gariti da ya fice waje saboda lokacin sallar la,asar da ya gabato domin shima yanzu ya ƙara daidaita tsakanin sa da Ubangijin sa yana iya ƙoƙarin sa a wurin ibada,duk da dama baya wasa da ibada sosai haɗuwa da Najiba komai ya fara sauya masa. Á ɓangaren Tanim kuwa a gidan da su Najiba suka tashi nan ya ƙara gyarawa ya suka buɗe babin iskan cin su shida SHANTY Dan nan ta tare dashi kamar wasu mata da miji.Duk da hakan kuma tana zuwa wajen Najiba ɗin sai dai babu wata sakin fuska a tsakanin su ita Nadiya bata san dalilin da yasa take yawan fuske fuske ba idan ta zo,shi ya sa ma ta fita iskan ta ko ta zo zasu taɓa fira kaɗan,maganar Tanim kaɗai ce Shanty ke saka bakin ta a cikin idan zance ya haɗo dashi a firar ta su,kuma Nadiya bata taɓa zargin wani abu.. Sai dai duk wannan zagayen na Shanty bata taɓa lura da laulayin da

Chapter 21 of 39