Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
lokacin sa sun sani,kuma Allah baya barin wani dan ya faranta ran wani. Haƙuri ta ke ta basu ganin sun kasa furta komai kowa kan sa aƙasa. Miƙewa suka yi suka fice jiki a sanyaye. Zuwan su gurin ne ya sa mama Hafsatu fara jero tambayoyi hankalin ta tashe idanun ta har sun rikiɗa duk ta ruɗe mayafin na ta ma a hannu yake yana janjalinbo. Haƙuri malam Rabu'u ya fara da basu da yi musu ta fahimta kafin ya furta " Nadiya ta cika ta riga mu gidan gaskiya,da ita abun cikin na ta ".Ya kai ƙarshen zancen Muryar a karye. Mama Hafsatu kuwa kalmar farkon sa da yayi ce ta ratsa Kunnuwan ta sai ganin ta suka yi ƙasa wanwar kafin itama Nadiya ta ƙara sakin muguwar ƙara mai gigitarwa wadda ke nuna tabbacin rashi ne aka yi a gurin sai kuma naƙuda ta taso mata gadan gadan. Mama Hasiya da Nurses da sauri suka yi kan ta kafin suka ɗora ta kan gado suka yi ɗakin haihuwa da ita. Mama Hasiya kuwa idanun ta sunyi jazir itama babu abun da ke fita a kan fuskar ta face hawaye ba tausayin Nadiya..✍️✍️ ALLAH YA JIƘAN KI NADIYA😭😭😭😭😭 NAJI MUTUWAR BAIWAR ALLAH'n nan. Allah ya sa mudace.Tabbas mutuwa wa,azi ce a koda yaushe sai dai mai hankali ne kaɗai yake iya fahimtar hakan.Allah ya sa muyi kyakkyawan ƙarshe. Team Nadiya ya aka ji da haƙuri 😭😭😥 *DAGA ALƘALAMIN FA'EE BG*✍️ *FIRST LADY🙌* *GIMBIYAR TASKIRA👑* NI MAI ƘAUNAR KU CE HAR KULLUMM.💋🤩🤩🥰💔 REACT,SHARE,AND COMMENT PLS *_Typing_*📱 *TEAM TAURARI HUƊU* ⭐⭐⭐⭐ https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y _Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chan zaku samu cigaban update.Farkon labarin masu neman sai a mun magana a numban dana sauke ƙasan wannan page, Dan samun document.☝️_ *🌸RAYUWAR MU AYAU🌸* Ƙarya ko sakin Aure Gajeren labari Na Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _*Daga marubuciyar littafin*_ _*A Mafarki Nasanta*_✍️ And now _*Rayuwar mu a yau*_ P.33 Malam Rabu,U kuwa Duk yadda ya so ya danne ya kasa ya share hawaye, bayan an kwashi Najiba naƙuda gadan gadan,ga kuma Mama Hafsatu da ta farfaɗo cikin tashin hankalin da ya riske ta. Wanda tun bayan farfaɗowar ta take risgar kuka kamar wadda zata zubar da ruwan hawayen ta.Kukan ma,har wanda ba,a so take yi wanda da ƙyar malam Abdul Basiɗ dake jin kan sa kamar ya tarwatse ya tsawa ta mata l ganin yadda aka taru kan ta ana ta ba ta haƙuri ga kukan mai haɗe da kururuwa wanda ko musulunci bai ƙaunar sa yayi hanin sa. Ajiyar zuciya ya sauke ganin yadda Mama Hafsatu ta koma a bar tausayi lokaci ƙalilan babu abinda take faɗi sai ta shiga uku Nadiya ta ta tafi,kai ina bazai yuyu ba a dai sake dubawa. Haka take ta sabbatun ta ita kaɗai wanda dukkanin su sai dai suka zura mata idanu suna kallon ta ga tausayi ga haushi,tun da su kan su suna jin yadda take ji. A daidai lokacin ne kuma tanim ya samu kiran gaggawa ga Ɗai daga cikin members na ƙungiyar su wata matsala ta afku inda aka kira shi wurjanjan kasancewar allon tsafin su ya karye wanda dukkanin su babu wanda ya san dalilin faruwar wannan lamari sai dai baza su taɓa mantawa da sanadin ba dan an taɓa faɗa musu muddin aka samu jinin wani ya zo duniyar nan a tsakanin su kuma ya fito a wahalce to dole allon tsafin zai karye shine makarin shi. Haka ya figi mota daga inda yake zaune yana shaƙatawa bayan ya sauke Hajiya Jamila inda zai kai ta,daga gurin babu nisa,Ɗan haka cikin mintuna da basu wuce goma ba ya kai. Jikin sa na rawa ya faɗa gidan bayan gama parking sai dai tashin hankalin shi ne ya ƙaru ganin boka wanwar a ƙasa jikin shi kamar an babbaka masa wuta babu kyan gani wanda duk wani sashe da jini yake a jiye ya koma baƙi ƙirin sai wani irin wari dake tashi a gurin. Wanda wannan warin bana komai bane face jikin sauran Boka da na sauran Team ɗin na su da ke zagaye suna jimamin lamarin cikin tashin hankali da son gano bakin zaren matsalar wanda har yanzu babu wanda ya san ma ta ina matsalar take sai dai dukkanin su Bazasu manta da sharaɗin ba wanda kuma suke da tabbacin ya faru ne,sai dai A wane gefen a tsakanin su.Wannan shine basu sani ba. Sai dai kuma abun mamaki ya basu ganin yadda Tanim yake ta dadar hanci kamar wanda ya haɗu da kashi abinda ya basu mamaki kenan har suka kasa haƙura suka tambaye shi kasancewar su basa jin warin da suke yi kwata kwata amma shi yana jin shi yadda yake jin shi duk da ya rufe Hancin sa kamar wanda yayi wanka da kashi mai Shegen ɗoyi. Amsar da ya basu itace ta ƙara shigar da su cikin mamaki da tsoro wanda suka fara shinshinar junan su sai dai basa jin shi kwata kwata a jikin na su. Inda ya furta musu " Wani irin wari ke tashi a gurin na fitar hankali,kuma ina ga daga jikin ku ne ". Ganin yana neman shaƙewa saboda yadda kowa yake cewa a shinshina shi aji ko yana warin da gaske.Bayan jin furucin na sa.Hakam ya sa Tanim cikin tashin hankali ya baro ɗakin wanda yana fitowa ya fara kelaya amai kamar wanda zai amayar da yan hanjin cikin sa,sai da ya gama sannan ya faɗa mota da sauri gudun kar su same shi nan dan ya san muddin ya ƙara matsa su sai dai ya nemi Numfashin sa ya rasa.Ya ji tashin hankali matuƙa ba mutuwar boka yanzu ta ɗaga mishi hankali ba da karyewar abun tsafin su ba irin tsoron wannan warin da bai taɓa sanin Allah ya hallice sa ba sai yau muddin ta kasance shima yana irin wannan warin yagama yawo Dan babu inda zai ƙara fita har ƙarshen Rayuwar shi dan baya jin wannan warin turare kona na wa ne yayi maganin sa. Cikin tashin hankali ya isa gida ya ma manta da Matar gidan na asibiti da kuma zancen da yayi wanda sai da ya shiga cikin Falon dan ya ruɗe yana neman a shinshina shi ma kamar sauran Dan ya san halin da yake ciki Dan ya san wannan ba komai bane face izaya ce da Allah ya fara nuna musu. Kamar Zautaccce haka ya faɗa ɗakin Nadiya,Sai dai kansa ya dafe da sauri bayan ya leƙa ɗakin nata inda ya tarar wayaam hakan ya sa ya dawo da baya sannan ya kai kan kujera daɓasss zufa na karyo masa. Sai a lokacin ya ƙara fahimtar irin kuskuren da yayi duk da bada niyyar zaman Aure na rayuwa ta har Abada ya Auri Nadiya ba ya san tabbas ya cuta mata tun da ita kaɗai ya taɓa zaman ma da ita wanda dama niyyar shi sai ya gama moruwa da ita ya jefa ta gidan su sai dai kuma sai komai ya juye lokaci ɗaya kamar yadda ake juya waina a talle.Ga shi kuɗin ma bai bar ta ta wani ci su ba ta rage hasahi,wata zuciyar ce ta furta masa ai ka kashe mata a waje taci rabon ta sai dai ƙirjin sa ne yayi wata irin muguwar faɗuwa tuno da zancen cikin na ta da Najiba ta sanar masa ana son saka hannun sa.Haka kawai ya kwaɗaitu da son ganin jinjirin da yake tunanin ya isa fitowa duniya yanzu.Sai dai kuma wata zuciyarce ta kaɓe sa tana furta masa kar ka je ka riga ka gama mai wahala tura musu kuɗi kawai a kula da jinjirin,kai baka shirya zama uba ba.Ƙirjin shi ne ya ƙara ƙirewa ya faɗi fiye da ɗazu tuno da cewa dole team ɗin su zasu yi bincike su gano Musabbin faruwar lamarin inda take tsoro mai girma ya shige shi wanda bai san cewa yana da shi ba tsoron shi karsu illata yaro ko yarinyar da basu ji ba su gani ba. Shin me ya ke shirin faruwa dani.Ya tambayi kan sa.Da sauri zuciyar sa na halbawa,jini na zai zama abun haƙar su ina bazai yuyu ba.Ya yi furucin cikin ƙaraji,me ya sa bata cire cikin ba mai ya sa na kasa iya taɓuka komai akan cikin,me ya sa na zuba masa idanu. Sai kuma Tausayin jinjirin da bai san ya yake ba,ya kaama sa tare da na Mahaifiyar sa.Tuna yadda yayi ko oho da ita ne,da yadda ya sanar mata da sakin da yayi mata wanda ta kira shi cikin ɗan farin ciki ta sanar da shi abun da aka samu sai ta ji saɓanin abinda ya kusa illata rayuwar ta. Yadda yayi mata furucin ne ya tuno. " Ke lafiya wai " Ya furta hakan cikin hargowa bayan tayi sallama Muryar ta cike da farin ciki,zata bashi labari mai daɗi a tunanin ta zai ji farin ciki ko kaɗan ne,ko ta sanadin Muhammad komai ya sauya musu kafin ita. " Bani da alaƙa dake fa kinji ,Na riga na sake ki saki uku,sannan wannan jinjirin da zaki haifo na bar Miki,ki saka Aran ki baida Uba a duniya ". Tunowa da yadda ya zuba mata kalaman cikin rashin tausayi hakan ya sanya shi sauke ajiyar zuciya wasu abubuwan suna dawo mashi a kai me ya ke faruwa da ni ne ya ƙara furtawa da ƙarfi,kan sa ya dafe da ƙarfi jin yana neman rabe masa gida biyu.A hankali kuma kan ya daina juya masa sai kuma ya faɗi ƙasa sumamme. Few moment later.🔥🔥🔥 Idanun shi yake warewa a hankali yana kallon ƙaton falon kafin ya janyo wayar sa dake ajiye a gefe inda saƙonni kala kala suke kwance a notificafion bar ɗin sa. Ɗaya na Najiba ne,sai kuma wasu daga cikinsu yan ƙungiyar su, saura kuwa Daga mahaifiyar shi ne, wanda abun sai ya bashi mamaki yau shar bon shi da ita ya za,a yi ya samu kiran ta yanzu bayan ya san fushi take yi dashi an bata haƙuri inji Hajiya Jamila kuma tace masa karya ƙara ko shigowa sashen ta ta cire shi daga ya yanta,idan ya ƙara shigowa wajen ta sai ta tsine masa to mezata ce masa yan zu ko ta sauko daga fushin da shi bai san dalilin sa ba,bai san dalilin tsanar da tayi masa ba. Saƙon Najiba ya fara dubawa inda ƙirjin shi yayi wata irin girgiza wa da sai da ya fara gani buji buji saboda tashin hankalin da ya tsinci kan sa. Saƙo ne dai mai ɗauke da kalamai dake nuna an zalunce su kuma sun barwa Allah hukuncin sa.Inda ta ɗora wannan zancen bayan sanar da shi mutuwar Nadiya da abun cikin na ta wanda suka bawa Suna Muhammad bayan haihuwar sa... Kiran wayar ta Najiba yayi sai dai akashe take haka ma ta Nadiya ,Ɗan duk nan ta sake su kafin a shige labour room da ita.Ruwa ya fara korawaa da sauri jin zuciyar sa na wani irin ɗaukar zafi ga wata irin zufa da ta ƙara karyo masa a karo na biyu kenan dai wannan jinjiirin shine silar mutuwar Boka da karyewar allon tsafin su.Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un yake nanatawa wanda sai yanzu ya samu damar fitar da ita a bakin sa da zuciyar sa. Kan saƙon Mahaifiyar tashi ya koma cikin kiɗima inda take furta masa yayi sauri ya same ta hospital tana son yaga wani abu. Time da aka Turo saƙon ya duba wanda yake kamar dai dai dana Najiba ne dan lokacin dake tsakani bai da yawa,hakan ya sa wata zuciyar ta sanar mishi da suna a waje ɗaya tunda itace mafi kusa asibiti da ke nan,kuma ya san yadda ya bar ta dole asibiti mafi kusa take bukata,bai san abinda ya hana shi taimakon ta sai dai ya san hakan daga Cikin tsafin su ne, Domin bai ji wani mugun tausayin ta ba a lokacin sai dai kuma a zuciyar sa akwai raunin hakan, Babu tunanin komai ya sa kai zai fice sai dai har ya kai ƙofar barin Falon ya tuna da warin da ya ji sauran nayi hakan ya sa ya zo da sauri zuwa ɗakin sa ya ƙara bunbuɗa turare kamar zai zazzage kwalba. Sai da yaji ƙamshin yana hawar masa kai sannan ya fice daga daga gidan direct Asibitin ya nufa. Mu koma Asibiti. ^••^••^ Dr.Abida dake kai kawo bayan ta gama shan kukan ta na tausayin Nadiya da jinjirin bayan fitar su malam Rabu'u,wanda kuma har yanzu take ko kwanto akan sa inda ta yanke wa kan ta abun da zuciyar ta ta lissafa mata inda ta ɗauki wayar ta tayi typing saƙo ga lambar da har yanzu ta kasa yin savin g ɗin ta da kowane suna bata san dalili ba. Tana gama tura saƙon ta koma ta zauna. Tana sauke Ajiyar zuciya. Sai dai bata ko ɗauki mintuna goma ba sai ga Nurse ta shigo da sauri bakin ta washe da haƙora.Ganin ta hakan ya sa Dr Abida fitowa da sauri bata re da jiran jin abinda ya faru ba ta san dai komai ne ne good news ne tunda taga chanjawar fuskar Nurse Ɗin da suke taya ta damuwa ganin yadda ta damu da patient ɗin da take iƙirarin ta ta ce dan bata san dalili ba tana jin son yarinyar. Wani irin farin ciki ne ya ratsaata har zuciya lokaci ɗaya ganin yadda akaa jera na'urori a jikin Nadiya wanda ke nuna alamar da sauran ta sai dai tana cikin shan wahala wanda wayen nan na'urorin zasu taimaka mata sosai dan samun daidaituwar Numfashin ta Dan cikin kaso ɗari iyaka goma suka samu shiya sa aka manna mata su akai,fuska,Kan ƙirjin ta.Sai kuma hannun ta. Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana bin su da kallo tana sakin murmushi taka sa iya furta komai ita kaɗai ta san farin cikin da take ciki a yau wanda ya juye daga baƙin ciki zuwa farin ciki lokacin ɗaya a gare ta. Sannu a hankali take bin team ɗin da kallo tana furta. " congratulations ''. Suma murmushin dukannin su sukayi suna gyaɗa mata kai Suna cewa ur welcome tare da taya ta murna domin basu ta ɓa ganin ta cikin irin wannan farin ciki ba,basu san abinda ke damun ta ba dan mafi yawan lokutta tana shiga damuwa zata zauna ita kaɗai ko fuskar ta babu alamar farin ciki,amma akan Ganin Nadiya na da sauran numfashi sai hakan ya ƙara basu mamaki suka ƙara tabbatar wa da Cewa Nadiya nada wani ba gire na musamman a cikin zuciyar Dr.Abida. Har Likitotan da Nurses suka fice bayan gama duddubata bata iya ƙara furta komai ba sai zuba ma Nadiya idanu da tayi tana kallon ta. Jinjirin da aka saka a ƙaton zane ne bayan Umurtar ta su da aka yi suzo su rufe sa,kamar ko wane ɗan Adam Dan ya haɗu babu abinda ba a halitta masa ba ga shi gudan ƙato da shi da yanayin sa ya nuna cewa mahaifiyar sa ta sha Malta son ta ranta,kafin a ɗauki uwar itama da Ambulance da aka fita dasu za,a yi musu juye da dudduba su duk bayan ƙarshen wata. *** Ikon Allah suke kallo, dukkanin su sun zuba masa idanu tun bayan wankan da suka masa suke ji a jikin su akwai sauran numfashi a tattare da shi domin kuwa Malam Adamu shi ya fara hangen hakan inda ya ga kamar gashin idon jinjirin ya motsa abu kamar almara sai yayi musu nuni kafin suka zuba masa idanu suma ɗin dai hakan suka ƙara gani bayan yan shuɗewar seconni.Abu kamar wasa sai ga jinjirin nan ya fara wulla ƙafa kafin ya saki kuka mai sauti wanda ke nuna irin yanayin wahala da yake ciki hannyen sa dake a dunƙule malam Abdul Basiɗ ya riƙo wanda cikin farin, da wani irin yanayi na ƙaunar jinjirin ya kame hannyen sa yana sauke ajiyar zuciya cikin so da ƙaunar sa da Tausayin yaron da yake jin maraicin sa abun tausayi ya tashi Bai san mahaifiyar sa ba.Gashi yanzu daga buɗe idanun sa cikin iyawar Ubangiji itace abarda yake muradin kusanta Dan jin ɗumin jikin ta,da ƙosar da yunwar sa da ƙishin sa sai dai hakan bazai taɓa samuwa ba mai yanke wa ta riga ta yanke. Yana cikin wannan tunanin ne yaji wayar sa na ƙara daga gefe. Ajiye tunanin yayi yana furta Alhamdulillah kamar yadda su Malam Rabu'u suke yi da Malam Adamu cikin farin ciki suna furta Allah mai iko kai kake rayawa kuma kai kake kashewa wato tabbas idan lokacin ka bai yi ba,komai daɗewar lokaci zaka dawo cikin Numfashin ka,idan kuma yayi babu makawa babu wanda ya isa ya dakatar.Allah abun godiya.Allah ya jiƙan Mahaifiyar Sa Allah kasa chan ta fiye mata nan ka yafe mata kura kuran ta.Amin ya furta shima jiki a sanyaye,yana jin rashin Nadiya,yar sa tal har cikin zuciyar sa, Duk da yadda kulawa da su ya yan na su ya ja baya a gare su lokaci ɗaya wanda sukan su sun shaida a kwai wata ƙulalliya.A dai dai lokacin da ya da Kawar da tunanin na sa ne,kuma ya kasance dai dai da shigowar sabon kira a wayan sa. Ɗaga kiran yayi,Sai dai bayan ɗaga kiran abun da Kunnuwan sa suka jiye masa sai da ya ji sun daina aiki na kusan seconni. Miƙewa yayi bakin sa a washe yana furta Allahu Akbar.Allahu Akbar.Har sau uku Allhamdulillah ala ni'imati, Alhamdulillah ya Hayyu ya qayyum.Sai kuma hawaye suka wanke masa fuska kamar an buɗe famfo malam Rabu'u da suke kallon sa suma cikin mamaki suka zuba masa idanu suna son jin ƙarin bayani. Hawayen ya share yana sauke a jiyar zuciya sannan yace " Hasiya ce Take sanar dani Nadiya na da sauran Shan ruwa a duniya,ashe doguwar suma ce tayi irin mai wuyar ganewa dan wasu har sai an kai ga za,a rufe su suke farkawa,sai dai ita Allah ya ta ƙaita ba,a je ko ina ba ta dawo cikin rayuwar ta, wannan daga bayanin da Likitota suka musu ne,kuma sun tabbatar zuwa gobe zata iya farfaɗowa in sha ALLAH domin Numfashin ya dai dai ta,yanzu ta samu bacci wanda suka haɗa mata har da allurai dan ta samu natsuwa Ɗan tana da sauran Hawan Jini sai dai ya sauka sosai ". Allahu Akbar suka haɗa baki suna furtawa bakin su washe.Ikon Allah yafi gaban mamaki,Lallai Allah azimun ne shine mafi hikima,kuma shine ya san dalilin faruwar wannan lamari da ya juye muna daga baƙin ciki zuwa farin ciki.Allah mun gode maka.Allah ka basu lafiya shi da mahaifiyar ta sa. Ameen Malam Abdul basiɗ ya furta shida malam Adamu. Yanzu bari mu sallami Jama'ar da suke jiran zuwan gawar ta,dan sallace su ita da shi Jinjirin Muhammad. Allahu akbar bari a saka mishi suna kawai a yi masa huɗu ba. Duka wannan zance malam Rabu'u ne yayi sa cikin wani irin farin ciki. Inda ya karɓe sa yayi masa huɗuba Malam Adamu kuwa ficewa yayi ya sallaami mutane tare da sanar da su wannan labari mai shegen daɗi inda take jama'a kowa yake ta jinjina wannan al'amari tare da taya su murna domin kuwa rashi ne Babba ga wannan gida musamman da ya kasance wajen haihuwa ne ta rasa ranta,hakan kuma akwai tausayi sosai. wanda unguwar ta cika Tammm duk da yadda aka yi ta zagin su Nadiya akan hakan bai hana jama'a taruwa ba.cikin ƙanƙanin lokaci,bayan sanar da su kuwa sai gashi aana ta watsewa a hankali kowa na jinjina mu,ujiza ta Ubangiji duk da ba abun mamaki bane wanda kaɗan ne daga cikin Ikon Ubangiji. Daga nan dabino ya siyo da zam zam. Koda ya shigo malam Rabu'u na riƙe da shi bayan ya gama masa huɗuba tare da kiran salla a Kunnuwan sa inda yaron ya yi shiru sai kallon sama da Yake yi yana wuntsila ƙafafun sa alamar yana cikin ƙoshin lafiya. Ikon Allah Malam Adamu ya furta yana kallon sa tare da furta wa yana kallon malam Abdul Basiɗ " lallai Allah Abun godiya ne." " Allah ya raya muna,Ga dabinon sa da zam zam, ". Karɓa malam Rabu'u yayi shima cikin murmushi sannan ya buɗa bakin yaron Tare da furta " Bismillah karɓi Muhammadu". Karɓa kuwa jinjirin yayi kamar yaji abinda aka ce inda bayan an saka masa dabinon da aka tauna aka kafa masa ruwan ana ɗan matsa masa take ko ya hau sha kamar zai cinye leɓen sa dan har shi yake tsotsa wanda ya ƙara tabbatar musu da yunwa yake ji sai Tausayin sa ya kama su jikin su ya ƙara yin sanyi da suka tuna da yanzu haka zai cigaba da rayuwar shi daga ruwa sai madarar Bature.Shi ai ya ma ji daɗi idan ya samu ta Bature wani jinjirin babu wannan gaba ɗaya.Allah ne kawai yayi masa gata kuma shi yake rayar da bawan sa,sai kaga ya rayu cikin ikon ubangiji... Hakan ya taɓa faruwa da wani jinjirin kwanan sa biyu yana kwance a cikin wata gota ta gefen gari a cikin ɗan kwali haka,mahaifiyar shi ta yasar da shi.A hakan Kuma da aka same shi babu alamar yunwa tattare dashi,yadda aka gane shi ma motsin da aka hango ne inji wani bawan ALLAH da yaje wucewa.Sai kuwa ya ga yaron yana ta wuntsila ƙafa... Lallai Allah shi ne masani.Allah ne ya san yadda wannan jinjirin yayi rayuwa A wurin.Allah mai girma da ɗaukaka. *Tunatarwa* _Wallahi kuna zalintar su idan kin san bazaki iya ɗaukar wannan ƙaddarar ba mai zai kaiki faɗawa Tarayya da maza,kin san irin cutar da kike ɗibarwa kan ki,ga zunubi mai tarin ya wa,Kin san illar zina,Allah da sai da ya gargaɗe mu,ba cewa yayi kar muyi ba ma.Cewa yayi kar mu kusance ta mu gujewa duk wata hanya da zata sa damu da zina.Dan na san uwar dai da ta haifi ɗan ta na halak bazata yarda ta cillar dashi ba,koda akwai wani abu Bata da dalili mai girma kan hakan,ko ace tsananin rayuwa,wannan kuma Ubangiji shi ke da iko domin shi yake kawo kowane ɗan adam duniyar nan kuma yayi wa kowa iya tasa ibar kowa da arzikin sa yake zuwa,dai dai gwargwadon abinda Allah ya katsa masa.._ _Ku guji zina,mai tauye Ayyuka ce._ _Ku guji zina, mai karya Ƙarfin imani ce._ _Ku guji zina,Mai hana jin daɗi ce na duniya zata cigaba da saka rayuwar ki duhu,jin ɗaɗin mintuna ko awa sai ya kai ki wuta direct musamman idan baka/ki tuba ba har zuwa lokacin da,komai zai ƙure Maki/ka_. _Zina takan bi salsala.Ta faru tun kaka da kakanni sai ta garzayo ta dawo cikin jikoki ko yaya.Domin maganar Allah bata taɓa faɗuwa._ _Yadda kuka san jinin dake gudana a jikin mu haka take bin jinin ahalin mai yin ta sai wanda Allah ya tsallakar daga ciki._ _Muji tsoron Allah malammai da dama sun faɗi illolin zina kuma dukkanin su masu muni ne,bayyan mugun zunubin da zai samu matsuguni a cikin littafin ki._ _Allah gafururru rahimu ne.Kina da lokaci,ki/ka daina.Wayen nan ya'yan da kuke zubawar wa muguwar cuta ce kuke musu,ta yuyu wani Babban Malami ne wani mahaddaci ne,wani adili ne,wani waliyyi ne.Amma sai dai kun hana hakan kun toshe musu hanya saboda

Chapter 28 of 39