AYAU🌸*
Ƙarya ko sakin Aure
Gajeren labari
Na
Faiza Almustapha Murai
Daga Alƙalamin
Fa'eeh Bg ✍️✍️
Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin.
Bismillahir rahmanir Rahim
💪📚📚
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
> >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>>
_*Daga marubuciyar littafin*_
_*A Mafarki Nasanta*_✍️
* _OUM AMJAD DATA SERVICES_*
_We offer you the best affordable cheapest of Price_🔥
*_NETWORK'S_*
*MTN*
500MB- 200
1GB-300
2GB-600
3GB-850
5GB-1400
10GB-2850
*AIRTEL*
500MB-200
1GB-350
2GB-650
3GB-870
5GB-1450
10GB-2870
*9MOBILE*
500MB-250
1GB-350
3GB-950
5GB-1470
10GB-2850
*GLO*
500MB-250
1GB-350
3GB-950
5GB-1470
10GB-2850
Ga masu bukata zaku iya tuntuban ta ta wannan layi kamar haka+2349025859622
OUM AMJAD..
FREE BOOK.
BONUS TO MY FANS💞
P.17
Tsaye ya miƙe da ita a jikin sa yana furta " Na bar zancen tunda kunya kike ji ".
Murmushi Raliya ta ƙara saki tana sunne kai ƙasa jin furucin na sa.Shima murmushin yayi yana riƙo hannun ta ɗaya sannan ya wuce da ita bedroom ɗin ta da ke tsaff sai tashin ƙamshi yake yi.Kasancewar lokacin Sallah Isha ya gabato hakan ya sa ya fice daga gidan bayan ya ɗaura Alwallah.Itama RALIYA sallah ta gabatar saboda tana da alwallah ta Magriba da tayi.Tana gama sallah kuwa ta yi Addu,oin ta sannan ta ƙara gyara kwalliyar ta tare da ƙara fesa turarukan ta masu ƙamshi,
Ibrahim kuwa Yana dawowa gidan ya rufe kai tsaye.Ledojin da ke hannun sa ya koma ya Ajiye akan wani ɗan table dake a Anan falon kafin ya shige cikin uwar ɗakin na ta.Zaune ya tarar da ita tana taɓa yar madaidaiciyar wayar ta ta da alama kamar game ne take bugawa.Sallamar da yayi ta amsa tana Sakin murmushi tana sauke kan ta ƙasa bayan haɗa idanun da sukayi inda ta ci karo da murmushin na sa.
Hannun ta ya riƙo a hankali bayan ɗan takawa da yayi gurin ta.Kan kunnen ta ya furta a hankali bayan ya ɗan durkusa.
" Kinyi kyau my Halal ".
Murmushi ta saki cikin jin daɗin yabon kwalliyar ta ta da yayi da kuma kunyar halal ɗin da ya kira.
Falon suka nufa a tare ledojin ya buɗe musu wayen da ke ɗauke da Lafiyayyun Gasassun kaji suya mai kyau sai ta shin ƙamshi suke yi da turirin ƙamshi.Sai kuma manyan gorunan five alive guda biyu.
"Bismillah".
Ya furta yana tura mata kazar gaban ta sannan ya kai ta bakin shi yana fara tattaunawa.Kasa ci tayi sai ɗan sunne kai da tayi ƙasa tana Jan Ajiyar zuciya ƙirjin ta na bugawa A hankali.
Sai da ya ci ya ƙoshi sannan ya sha five alive ɗin sa tare da ruwan da ya ajiye na gora suma.Ganin ta kasa ci hakan ya sa yayi murmushi tare da zarar naman yana kaiwa bakin ta tare da furta mata.
" Haaa ".
Bakin kuwa ta buɗe sai dai jiki a sanyaye.A hankali yake bata tana karɓa bai sauke hannun sa ba har sai da ta nuna ta ƙoshi sannan ya rufe sauran Naman ya mayar dashi a cikin ɗan ƙaramin fridge da ya saka mata anan cikin ɗakin a wani ɗaki dake gefe da alama kitchen ne ɗan madaidaici.
Five a live ɗin ta sha sannan ta yi Hamdala tare da miƙewa ta biyo bayan sa da ɗan ƙaramin cup na glass da suke da kauri kamar dai na glass wanda ya zuba mata five a live ɗin wanda ya san zata iya sha.
Hanya ya bata yana sakin murmushi.Itama murmushin ta saki kafin ta saki a jiyar zuciya tana a jiye filet ɗin a inda ya dace ta dawo tsakiyar Falon.
Koda ta dawo Ibrahim baya falon ya shige uwar ɗakin na ta.kasancewar shi ne kawai suke dashi sai wani ɗan ƙaramin ɗaki da ke a jiye a gefe kamar ɗan ƙaramin store sai kitchen ɗin shima ɗan madaidaici.
Tana shigowa yana fitowa daga toilet ɗin da alama Alwallah ya ɗauro saboda hannyen sa da fuskar shi dake jiƙe da ruwa da wasu gurare a jikin nasa ga hannun rigar sa da ya tankwankwahe waje ɗaya yana warware su.
" Kije Kiyi Alwallah ".
Ya furta mata kai tsaye yana jan hannun rigar ta sa tare da shimfiɗa sallaya.Ɗan shiru tayi kafin a hankali cikin sanyin jiki ta furta.
" ina da Alwallah ".
Kai ya jinjina mata yana sakin ɗan guntun murmushi.Ta gefen ido ya bita da kallo ganin ta kama hanyar toilet wanda ya san bazai wuce baki zata kuskure ba.
Kamar yadda yayi zato hakan ce ta kasance domin kuwa fitowa tayi tana nufar inda hijab ɗin ta na sallah yake wanda bata daɗe da ajiye shi ba.
Bayan shi ta bi Inda suka gabatar da sallah raka'a biyu wadda ya ja ta da tsawo tare da yin Addu'oi kamar daren jiyan sannan suka shafe.Kasancewar ya san bata daɗe da yin wanka ba sai bai matsa mata ba kawai ya shige ya watso ruwan sa ya shirya.
Kayan da ya Fiddo mata da su ne ta sanya masu laushi cikin set na barci da ya saka mata.Duk da kayan ba su wani bayyanar da jiki amma haka take ɗan sunne kan ta ƙasa tana wasa da yan ya tsun ta.
Ibrahim kuwa shirin sa yayi tsaff sannan ya haye kan gadon tare da ƙyafato ta yana sauke ajiyar zuciya da sakin murmushi yana kallon kyakkyawar fuskar ta.
Takawa tayi a hankali tana sauke A jiyar zuciya bakin gadon ta tsaya ciki ya matsa yana sakin murmushi.Alama yayi mata da hawa kan gadon cikin bin umurnin sa kuwa ta haye gadon tana sakin ɓoyayyiyar ajiyar zuciya.
Miƙewa yayi ya yi Addu,a sannan ya shafe a jikin sa.Itama Addu,ar tayi tana sauke a jiyar zuciya tana gamawa itama ta haye kan gadon tana rufe jikin ta da bargon dake ke edge na bed ɗin.
A hankali kuwa idanun ta suka fara rufewa inda bacci ɓarawo ya kwashe ta sai dai zumu mut ta miƙe cike da tsoro jin kamar ana ta ɓa jikin ta." Shiii" Yayi da hannun sa akan bakin ta ganin tana batun saka kuka.Tsit kuwa RALIYA tayi tana sauke numfashi da wani irin tsoro da ya shige ta lokaci ɗaya.Duk da ta fahimci gogan na ta ne amma taji tsoro sosai musamman abinda take gani a cikin idanun sa duk da duhun da ke a cikin ɗakin dan ya kashe haske.
Numfashi ya sauke mata mai zafi sannan ya furta Cikin natsuwa da wata rikitac ciyar muryar da ta ƙara saka ƙirjin RALIYA dukan tara,da kuma furucin na sa.
" Haƙƙi na nake so RALIYA my Halal ".
Shiru tayi masa kamar bata ji ba sai dai kunya tana dabaibaye da ita ƙirjin ta na bugun tara tara.Ga wani irin tsoro da ke sake shigar ta.
Jikin ta ne ya mutu mururus bayan ya dakata da sumbatar da yake sauke mata a baki.Hakan ya sa ta kasa iya furta komai sai jan numfashi cikin baƙon lamarin da ke shigar dukkanin gaɓɓan jikin ta.
Ibrahim kuwa ganin ta kasa iya furta komai hakan ya sa ya cigaba da bata darasin sa wanda take ɗauka harafi harafi kalma kalma shafi shafi.Sai dai komai chanza mata yayi lokaci ɗaya a lokacin da ta tsinci kan ta a wata irin sabuwar duniya mai cike da radaɗin azaba,anan ne ta fara neman agaji tayi kiran sunan umma har ta gaji haka ma sunan Adda NAJIBA da NADIYA har su malam Rabu'u sai da aka kira sai dai Da alama Ibrahim baya jin sautin komai yayi nisan kiwo kamar yadda su Nadiya basa jin ta haka shima ya koma ɗuff rayuwar da ya samu kan sa a ciki mai wuyar fassarawa ke shawagi a ƙwaƙwalwar sa da tunanin sa.Duk yaƙushin da yake samu babu wadda ta shiga jikin sa.
A wannan dare ne Ibrahim ya kafawa Raliya tarihi na mai da ita cikakkiyar Babbar mace mai daraja a idon mijin ta da ƙima kasancewar ta kawo Mishi babbar kyautar da mata da yawa suka kasa kaiwa a gidajen mazajen su awannan lokaci da muke ciki wanda hakan ya sa mafi yawan maza suke ɗaukar mata rabi da kwata a watsatsi.
Zaka ji ma suna faɗin akwai budur bazar.
Akwai Bazar budur,Akwai Budurdur.Sannan a kwai budurwa itace cikakkiyar budurwa saura kuwa kowa yana da na shi ma,anar.
Allah ya sa mudace.
Kuma ya bamu ikon riƙe mutuncin mu a duk inda muke.🤲
A ɓangaren Tanim kuwa ta ƙarfi da ya ji haka ya ɗura ma Nadiya madarar nan duk yadda ta so ta ƙwaci kan ta ta kasa dan tana zargin wani abu yake saka mata acikin madarar saboda Baccin da ta sha har yanzu yana bata Mamaki da tsayawa a Ran ta dan tun da take gida bata taɓa yin irin wannan Baccin ba kaf a rayuwar ta ma bata taɓa yin sa ba.
Cikin a bun da bai fi yan sakanni ba bacci ya fara cin ƙarfin ta sai dai tana jin komai dake faruwa da ita sama sama amma bata iya komai saboda yadda Baccin yaci ƙarfin ta domin kuwa maganin bacci ne ya saka mata mai ƙarfi domin guda ɗaya ya saka ba kamar jiya da yayi mix ba da desire tablet.
Tun tana jin shi yana bidirin sa har ya gama bata ƙara sanin inda take ba sai da bayan sallar Isha sannan ta farka a matuƙar galabaice Dan raunin da take da shi ya ƙara samun fami.Idanun ta ta buɗe Wayen da suka ƙanƙance lokaci ɗaya sannan ta fara bin ɗakin da kallo kafin ta sauke Ajiyar zuciya hawaye na sauko mata na tausayin kan ta domin kuwa ta ƙara tabbatar da Tanim Akwai abun da yake bata bai barta hakan ba bayan ta ƙarewa agogon bangon dake ta aiki a cikin bedroom ɗin na ta kallo.
Miƙewa tayi a hankali wasu hawaye masu zafi na ƙara silalo mata ba komai ya faɗo mata a arai ba face hasashen Yar uwar ta NAJIBA da ta taɓa furta mata tana ganin kamar ba son gaskiya Ya Tanim yake mata ba,wanda kan wannan zance har sai da ta Share ta na kwana biyu.Shin dagaske ne Tanim ba sona yake yi? Wannan shine silar Auren nawa me ya sa?,to Amma me ya sa bai bani takarda ta ba tun a daren jiyan ko safiyar yau kamar yadda maza irin su keyi ?.Shiru tayi jin Babu Amsar tambayar ta kafin ta sauke Ajiyar zuciya ta miƙe a wahalce tana jan ƙafafu da Gwale Gwale ta shige toilet domin yau ɗin ma ta ji jiki sai dai ba kamar jiya ba yau da sauƙi.
Har ta fito wankan da ta tayi guda biyu tunanin yadda ta farka ne ɗazu da yadda da yanzu wanda yanayin suka yi mata kama in da ta ƙara tabbatar da wani abu Yake bata wanda yake bashi damar yin amfani da ita yadda ya so.
Tana fitowa ta gabatar da Sallah la'asar Magriba da Isha sannan ta sanya kayan barci Bayan ta yi yan addu,oin ta.
Rufe bedroom ɗin ta yi da makullin sa kasancewar wani irin tsoro da ya ƙara shigar ta na Tanim ɗin tana tsoron ƙara shigowar tashi a yanzu.Bata cire makullin ba dan ta san ba,a rasa extra key a hannun sa.
Gadon ta haye tana sauke Ajiyar zuciya.
Wayar ta ta janyo wadda ke yashe a gefe Dan tana tsaka da duba saƙonni a wahtsapp ya shigo mata sagadam babu ko sallama.
Saƙonni kuwa ta tararr da yawa wanda duka rabi da kwata na ƙawayen su ne yan fafa,da ɗiyan masu Naira, yan tambayar ya an ka kwashe yan son jin ƙwaƙwaf.
Bata bada amsa ba sai da ta gama karance saƙonnin wayen da wasu ta saki Murmushi wasu tayi dariya Sannan ta fara bada amsa tana tsintar kan ta cikin farin ciki domin ta rage damuwa sosai a yanzu.
Ƙawar su mai son jin ƙwaƙwaf kuwa ganin NADIYA ta ƙi furta komai a kan daren na su hakan ya sa ta bi ta private dan ta same ta online ita kaɗai.
NADIYA kuwa cikin Rashin damuwa ta kwashe komai na daren na su na jiya sai dai ta ɓoye mata ƙetar da take tunanin yana haɗa mata da ita na saka mata wani magani a abun sha.Shanty kuwa cikin jin daɗi take ƙara bugun cikin Nadiya ita kuwa kamar sakar ya haka tayi ta sakar mata bayani dalla kamar mai bata karatu domin babu kunya atsakanin su.Wannan chat ɗin da suka yi ne ya rage mata zafin da take ji zuciyar ta nayi na baƙin cikin lady da shi kan shi Tanim ɗin wanda bata sanar wa Shanty komai ba da ya faru akan Lady ɗin wanda ita kan ta bata san dalilin yin hakan ba.
A hankali bacci ya fara rufe idanun ta hakan ya sa ta kashe data ɗin tana yin Addu,a wadda bata wani yita yadda ya dace ba sannan bacci ya ɗauke ta.
Nadiya ta ƙara yin wani kuskuren.
Yanzu fa kai ya waye ba,a sakin baki ana bada sirri irin wannan ga ƙawaye,amma tun da na ga Abinda Nadiya tayi na san Har Yanzu ana nan ana irin wannan shirmen.Yan mata ku hankaltu kuyi wayo,ku gane illar fallasa wannan sirrin,ku gane amfanin ruƙe sa.
Yadda Allah subhanahu wata'ala ya ɓoye shi to bar shi a ɓoye shine alkhairi.Dan Allah karki sakarwa ƙawaye baki idan sunje gurin ki ko ta waya kar ki bari fira tayi daɗi ki bada labarin sirrin mijin ki,ki zamo mai iya riƙe harshen ki da sarrafa shi akan sirrin mijin ki da gidan ki.Duk bugun cikin su da son jin ƙwaƙwaf zuba musu ido Kiyi kamar baki fahimce su.✍️
A ɓangaren Tanim kuwa yana gama biyan buƙatar sa ya bar ɗakin ya ƙara tsallake ta hankalin sa kwance, yana fita kuwa wanka kaɗai yayi ya fice gidan gaba ɗaya babu inda ya nufa kuwa face wurin ƙawayen na sa a chan suka taɓa fira suma dai kan daren ne nasa, ya zumar ta take shine abinda suke ta tambayar sa sai dai kawai abun da ya iya furta musu She's sweet wanda su ba haka suka so ba ya basu labarin kwatta hilla,Wanda zasu ji kamar a gaban su aka yi dan hakan Kowannen su keyi Dan cikin su akwai wanda yayi Aure fiye da biyar akwai wanda ya yi uku Tanim ne kawai ke da ɗaya wanda yayi da wata baturiya sai dai ana ɗaura Auren bai samu abinda yake so ba ya dawo Nigeria saboda wani uzuri wanda da ya sa har yanzu bai san yadda take ba abinda ya sani kawai ya na sakar mata kuɗi masu yawa.
Kuma dukkanin su bada sanin iyayen na su ba suke yi Auren Ɗabi'ar su ce da sun fahimci ba yar hannu ba ce ke zasu bi ta wannan hanyar dan samun cikar burin su na kwana ɗaya kona sati,A wasu lokuttan ma har ɗan ɗana mini sukanyi sai dai atsakanin su suna yin hakan ne ga wanda ka yarda dashi a cikin ƙungiyar ta su wani ya jewa matar wani sai dai bada sanin ta ba dan suna amfani da ƙwayar bacci ne dukkanin su da desire tablet mai ƙarfi.
Basu ɗaga gurin ba sai da aka kira sallah Magriba wanda la,asar ɗin ma ba kowa ya gabatar da ita a cikin su ba dan Tanin yana cikin su.
Suna gama sallah kuwa suka wuce club.Ƙaton club ne wanda yake shaƙe taff da mata da maza kowa yana sha'anin gaban shi,Kowannen su rabin jikin shi a sake babu ƙyan gani bare burgewa.
Su Tanin na shiga wuri ya ɗauki ihu na murnan zuwan big boys Dan haka ake kiran ƙungiyar ta su wanda zasu kai aƙalla su goma sha kowannnen su ɗan ɗan wani Shege ne sai dai mafi yawan su ya yan manyan yan siya sa ne masu ji da Naira da tantiran ci wayen da suka feɗarekke a ƙasashen Turai da sunan karatu,sun dawo gida suka cigaba da baƙar ɗabi'ar su a ɓoye ba tare da sanin iyayen na su ba wasu kuwa iyayen na su sun sani sai dai basu da ikon hana su saboda tsoron su da ya mamaye su domin gatan da suka basu har yayi illar da ta saka suke yiwa iyayen yadda ransu ke so har hakan ya da sa musu tsoron su wanda yake cike da ƙaunar su.
Kwalaben Alcohol aka jere musu akan table na su na musamman inda take mata suka zagaye su kowacce ta samu ɗaya ta haye.ƙafafun sa,da kan su ke shayar da su Alcoholic drinks ɗin suna yi suna taɓa jikin su.Sai da duk sukayi tatil sannan kowacce ta ja ɗaya suka rabu kowa ya shige ɗaki da taimakon yan matan dan ba su da wani ƙarfi ajikin su, ɗakin na bisu sai dai ganin abun da ke shirin wakana a gaban idona ya sa na fice domin suma Matan fitsarru ne babu wata alamar kunya tattare dasu daga yanayin yadda ɗayar su ke gudanar da komai ma wa Tanim zaka shaida hakan.
Wal iya zubillah😭
Rayuwar nan kamar ba,a mutuwa jama'a kowa yanayin don ranshi,mutane suna manta haɗuwar mu da Ubangiji.😥
Allah ka ƙetarar damu da Zuri'ar mu faɗawa hanyar Zina.🤲
Allah ka bamu ikon nisan ta da ita ya Ubangiji.🤲
***
Murmushi tayi tana kallon shi kafin ta Mishi sannu da zuwa tana bin fuskar shi da kallo ganin yadda yake ta ɗan yatsinar fuskaa a yanzu da alama lamarin da ya baro duk da ya ji daɗin sa yana ransa.Murmushin ya ɗan ƙara ƙaƙalowa kamar dai yadda ya shigo dashi.
Zama yayi a gefen gadon na ta kafin ya Amsa mata Barka da zuwan da tayi masa Cikin jin daɗi.
Miƙewa tayi a hankali cikin rashin jin ƙwarin jikin ta.Abincin da aka kawo mata bayan sallar la'asar ta zubo masa wanda kuma shine ya bada akawo mata shi dan a Restaurant yayo ordern sa,wanda ita take tunanin duka daga gidan su Hajiyar sa ne tana jin daɗi, Sai dai bata taɓa komai ba kasancewar bata jin wata yunwa.
A bincin ta zubo masa bayan miƙewar ta, komai ta ajiye masa a gaban sa na buƙata sannan ta zauna kusa dashi kaɗan tana kallon sa da furta masa " Bismillah ". Bayan tayi Serving ɗin sa da kan ta.
A bincin ya fara ci yana yi yana sauke ajiyar zuciya, zuciya a cunkushe ga wani irin zafi da ta ke masa ya rasa mai ya kamata yayi yanzu,Ya sanar Da ita gaskiya ko ya ƙyale ta ko kodai ya bari sai nan gaba idan taji da kan ta lokacin da komai zai buɗe da kan sa komai zai zo ya sauya mata.Baya da mai taɓuka Mishi zancen hakan ya sa ya yi murmushi kawai wanda ya fi kuka ciwo, zuciyar shi na cike da Tausayin ta.Har ya gama cin abincin ita bata ci komai ba ta sage hannu tana kallon sa ganin yadda yake tsakurar abincin ga kuma yawan tunanin da ta lura yana shiga a wayewar safiyar ta yau farin da take gani atattare dashi ragagge ne,kuma ba haka tayi tunanin komai ya kasance ba.
" Beb " !
Ta kira sunan da take kiran shi da shi a wasu lokuttan a tsanake.
Ɗagowa yayi yana kallon ta kafin ta ɗan sakin murmushi yana furta.
" Na'am.Qlbi "
Murmushi ta ƙara saki kafin ta sauke Ajiyar zuciya tayi furucin ta kai tsaye.
JAMIL kuwa idanu ya zuba mata kamar yaga sabuwar halitta jin furucin na ta.✍️
Yawan react,yawan Read more,Vote pls and comment 🙏
KU TAYA NI SHARING PLS
Daga Alƙalamin ✍️
Fa'eehbg
Firstlady 🙌🙌
Kuma
GIMBIYAR TASKIRA 👑👑
Idan kina buƙatar mu ruƙa viewing status na juna zaki iya yi mun magana idan kinyi saving numba ta da na saka muku a ƙasa sannna ki mun sallam ki faɗi sunan ki.🙏
Domin neman Ƙarin bayani.
08069059746
Chat kawai pls 🙏
Banda kira.
Zaku update ya zama shirme mun fara hidima ne.Amma zanyi ƙoƙarin baku ko kaɗan ne in sha ALLAH kamar yadda aka saba.
_*Typing*_
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
_*Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chann zaku samu tun daga farko.☝️*_
*🌸RAYUWAR MU AYAU🌸*
Ƙarya ko sakin Aure
Gajeren labari
Na
Faiza Almustapha Murai
Daga Alƙalamin
Fa'eeh Bg ✍️✍️
Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin.
Bismillahir rahmanir Rahim
💪📚📚
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
> >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>>
_*Daga marubuciyar littafin*_
_*A Mafarki Nasanta*_✍️
_Masu buƙatar talla hajar su ƙofa a buɗe take._
*08069059746*
P.18
_*# Taurari huɗu⭐⭐⭐⭐*_
_*# Fa'eehbg*_
_*# Najmil*_
_*# Himral*_
_*# Nadnim*_
_*# Shanty.*_
***
" Kamar baka farin ciki da Auren nan namu ya Jamil ".
Ta ƙara maimaita zancen.
Numfashi ya sauke yana sauke idanun sa kan ta.Ta ya zai mata bayanin ba Auren ne bai yi farin ciki dashi ba,Halin da zai shiga idan ya rasa ta shine abun tsoron sa da damuwar sa domin ya san tabbas ta samu labari komai ya buɗe ita da iyayen ta ba zasu barshi da ita ba sai sun raba Auren wanda shi bai taɓa hango hakan ba ya fi son ayi ta rigima babu saki a tsarin sa.
A jiyar zuciya ya sauke yana ɗan ƙaƙalo murmushi sannan ya ce.
" Ina tunanin nafi ki farin ciki Qlbi,kawai dai gajiya ce ke ɗan ɗibata shiyasa kika ganni some how. "
Murmushi Najiba tayi tana sauke numfashi sannan ta ƙara furta.
" Wai ina ka je ne Ɗazu? nayi ta jiran ka ga tsoro gidan shiru,Ni kaɗai ".
Cikin Waskewa da son Basar da zancen Jamil ya furta.
" Naje ganin su Hajiya ne tace a gaishe ki,Yawwa baki ci abincin ba fa ".
" Bari na ciyar da Amarya ta da kaina kar ta chanza ace ban iya kiwo ba ".
Inda ya kai ƙarshen maganar yana ɗaukar spoon ɗin dake gaban ta ya fara bata haɗaɗɗiyar Fried Rice wadda taji haɗi na musamman.
Murmushin jin daɗi mai cike da ƙaunar Sa ta saki tana buɗe bakin ta inda ya fara saka mata Abincin.
Fira suka cigaba da taɓawa A hankali mai cike da wata irin soyayyar junansu har ya gama ciyar da ita.
Kiran da akayi ne na sallah Isha hakan ya sa suka miƙe atare suka yi sallah inda ya ja su jam'i sannan suka yi nafila suka yi addu'a,oin su kafin kuma Najiba ta faɗa toilet ta ɗauro wanka da yin brush ta fito ɗaure ƙaramin towel a jikin ta.Cikin jin kunya Musamman da take jin idanun Jamil akan ta kafin ya shige toilet ɗin.
Tsaff ta shirya cikin wasu yan madaidaitan kayan barci masu taushi sannan ta haye gadon bayan ta tuttula turaruka masu ƙamshi da sanyi.
Shiko Jamil da ƙyar ya iya shiga toilet ya kasa ɗauke idanun sa a kan ta har ya shige toilet
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 39