ya bashi Amsa.
" Akwai abun da nagani da idanu na kuma yaron gida na ya shaida mini gaskiyar lamarin.Yaron da na taɓa ganin yar wajen ka dashi a ranar mai suna Tanim, Ma nemin mata ne na ƙwarai yaro na ya shaida mini ya taɓa ganin sa da yan mata,yan matan kuma an tabbatar riƙaƙƙun ƙaruwai ne a cikin motar sa, kuma a majalisar su yana jin ana yawan zancen sa kasancewar sananne ne ɗan masu kuɗi,Ance yaron yana ɓata ya yan mutane ne ya gudu ya barsu ".
Numfashi malam Abdul Basiɗ ya sauke kafin ya furta Cikin sanyin da jikin sa yayi ƙalau yana yin sa kuwa bazaka taɓa iya gane sa ba.
" Hmm Naji daɗin jin wannan bayani Malam Abdul basiɗ "......
Shiru yayi yana kallon ɗan uwan sa malam Rabu'u da ya zauna gurin ayanzu.Sannan ya cigaba da magana yana furta " Ban san abun da zan iya cewa cikin wannan lamari ba Malan Nasiru komai yana shige mun akai na nakan rasa madafa akan lamurran ya yan mu na kan ji zafi ganin su suna tagayyara haka a layi zuciyar mu akoda yaushe cikin rauni take nida ɗan uwa na duk da bai taɓa faɗa mun ba nasan yana jin zafin rayuwar da ya yan mu suke yi wata irin rayuwa ce wadda zamu iya kiran ta da Rayuwar mu a yau kasancewar wani irin zamani da muka ciki yanzu,Amma ayanzu ina jin Bazan yi ƙasa a gwiwa ba zan saka hannu alamarin duk abinda nake ji zan daure kuma zamu cigaba da dagewa da Addu,a kamar yadda muke yi a kullum, kuma muna roƙon ku kuma ku taya mu da Addu,a ''.Yakai ƙarshen maganar yana sauke numfashi wasu hawaye Masu zafi na silalo masa yana tuno yadda komai ya fara na taɓarɓarewar rayuwar ya yan su wadda yanzu basu da wani iko dasu wanda lamarin ya same su ne a lokacin da suka fara tsawatar wa yaran sai suka nemi duk wani baki nasu suka rasa kuma aka hana musu damar kasa cin abun yaran.
Shi kan shi Malam Rabu'u Shiru yayi sai dai bai furta komai ba sai ma wata irin ta farfasa da zuciyar sa ke yi na zafin abun da rayuwar da ya yan su ke ciki da suka kasa taɓuka komai cikin ta.
" Thoh Allah ya kyauta,kuma in sha ALLAH zamu saka ku cikin Addu,a malan Abdul basiɗ Allah yasa mudace kuma yasa nufi ƙarfin zukatan mu lamarin ya ya ne sai Addu,a musamman idan Allah ya baka ya ya mata Dole ka kasance cikin Addu'a ako da yaushe domin Allah ne kaɗai ke bada kariya ".Malan Nasiru yayi zancen cikin Tausayin su domin kowa yana sane da lamarin.
" Amin ya Rabbi muna godiya Malan Nasiru ".
Malan Rabu'u ya furta jiki A sanyaye.
Sallama yayi musu ya wuce cikin tausayin su da wannan jarabawar da suke fuskanta.
•••
Bayan wucewar malam Nasiru kuwa.
Malan Abdul Basiɗ ya dube ɗan uwan sa ya sauke kan sa ƙasa sannan ya zayyane masa komai dake faruwa na bayanin da malan Nasiru yayi masa yanzu yana.Yakai ƙarshen labarin zuciyar sa na wata irin suya sai dai ko yanzu bai jin acikin zuciyar sa zai iya yin wani abu mai kyau akan lamarin yana jin guiwowin sa sun sage bakin sa na masa nauyi.
Kai Malan Rabu'u Ya girgiza cikin wani irin baƙin ciki tuna tsawon lokacin da Nadiya take tare dashi.
" Yaya me ne ne mafita lamarin nan abun yana bani tsoro ina tsoron Kar ya ran nan su jawo muna abun kunya muna zaune ƙalau cikin mutun cin mu da rufin Asirin Ubangiji ".
Shiru yayi jin Malan Abdul basiɗ bai tanka masa ba sannan ya ƙara furta " na fahim ce ka ya ya Nasan abun da ke zuciyar ka abinda kake ji shi nake ji amma a wannan karon zamu daure ne mu cije muyi wadda ke yuyuwa mu ceto rayuwar ya yan mu Ni kaina ina jin bakin a yana ƙara yin nauyi yaya,Karka damu Addu,a itace kaɗai abun da zai magance muna damuwar mu Ubangiji baya bacci bare Hamma yana kallon mu kuma zai taimake mu Dan haka mu dage da Addu,a ".
Yakai ƙarshen zancen yana sauke numfashi.
Ajiyar zuciya malam Abdul Basiɗ ya sauke kafin ya furta " haka ne Rabu'u Allah ya dafa muna a wannan karon mu ceto rayuwar su da mutun cin mu da ke neman zubewa wanda ko nace Mutun ci su ".
Shiru sukayi dukkanin su kowa da abun da yake tuannin azuciyar sa.
Bayan kamar minti biyu haka Malam Rabu'u ya fara magana Cikin ƙwarin guwiwar da ya samu " Yaya mai zai hana mu yi musu Aure ace kowaccen su ya fito da wanda take so ta hakan ne itama Nadiya zata rabu da wannan yaron nasan bazata kawo shi a matsayin uban ya yan ta ba,kagaa dukkanin su suna da Samarin,nida ma muna da yadda zamuyi da wannan malamin na islammiyar su yana da mutunci,wannan Wanda yake ta fafutukar neman soyayyar ta a yanzu da shi muka Aura mata tun da tun farko Naji Ance sun fara soyayya dashi daga baya ta barshi kuma har yanzu yana zuwa gidan nan,sai dai ta raka shi da wulƙan ci kamar yadda naji bakin Raliya tana faɗawa Hasiya kaga sai mu ga yadda za,ayi hankali na yafi kwanciya da shi da ita".
Numfashi malan Abdul basiɗ ya sauke yana kallon Ɗan uwan sa kafin ya sauke murmushi yana furta " Shawara mai kyau daɗi na da kai Rabu'u akwai dogon tunani Ni nazo kawai amatsayin wa '' yakai ƙarshen zancen yana ɗan ƙawata fuskar sa da Murmushi wanda Ni kaina na daɗe ban gan shi akan fuskar sa ba.Tun bayan faɗa War yaran su wannan mummunan dabi'a ta gararan ba akan titi da gardawa wayen da babu tabbas idan Akwai Aure atsakanin su wasu ma ba dan Allah suke tare dasu ba.
Shima malam Rabu'u murmushi ya saki jin Zancen ɗan uwan nasa da ganin ɗan yanayin farin ciki kwance akan fuskar ya'yan nasa..
A hankali ya furta " Haba yaya Ai kaine dai uban gida Ai shi tuwo tuwo ne ba,a taɓa chanza masa suna sai dai ayi masa kwalliya ko kwaskwarima ".
Kai malam Abdul Basiɗ ya girgiza.
Kafin ya ƙara furta " Haka zancen ka yanzu muyi magana da su kawo Malam Adamu muji yadda za,ayi domin har yanzu Ni bana jin zan iya wannan maganar sai dai gaba yanzu haka harshe na wani irin zugi yake Mani Rabu'u yanayin da nake ciki bazaka taɓa gane sa ba,ina tuannin ko me ne koda ace sihiri aka yi muna na wa yafi kaifi domin yadda nake ji akan yaran nan in nayi zancen su Allah ne kaɗai yasani kuma shi zai yaye muna,Maganar malamin su na Islammiya malam Sayyid Nasu zamu duba muga,wannan zance naka shi ne zai Haska mana komai kuma in sha ALLAH shine sanadiyyar shiryuwar su Nadiya,Allah ya shiryar muna dasu ''.
" Amin " Malam Rabu'u ya furta jiki sanyaye domin shima dai ba laifi yana jin yadda ya yan nasa ke ji kasancewar ya yan nasa yafi shi tsauri shiyasa lamarin ke bashi mamaki har yasanya shi ya fara alaƙan lamarin da sihiri.
Fira suka cigaba da taɓawa Sama sama.
***
" Yau Beb yana cikin farin ciki daga wayar da mukayi dashi na fahim ci haka,Yau ma babu inda zamu je ya ce mu huta kawai zuwa gobe ".
Najiba ke wannan bayanin wa Nadiya dake zaune kusa da ita tana chat cikin haɗaɗɗiyar wayar ta ƙirar iphone 15 pro max da Tanim ya sawo mata kwanan baya .
Nadiya dake sauraren ta kuwa Murmushi tayi tana furta " furta ina jin Muryar sa sama sama ai Tawan.
' Wata irin ƙara ta sanya cikin farin ciki tana miƙewa daga kshingiɗen da suke kan ya ƙusasshiyar katifar tasu.Aikin Nadiya ne.Domin kuwa abinda ta gani a cikin message box nata na Whatsapp ya sanya ta farnciki matuƙa.
" Ke lafiya ".
Najiba ta furta tana ɗan ajiye wayar ta agefe itama tana subawa yar uwar ta idanu.
" Ba na faɗa Miki sabuwar wayar nan Iphone 16 my boo ya siya ba kwanan baya,to ranar Ni ma na saka Mishi rigima sai ya saya mini yace bazai saya ba sai na bashi abun daɗi,Wanda shima ranar daƙyar dai na sha Dan har sai da mukayi rashin magana na kwana biyu saboda Ni zalamar sa ce tayi yawa mutun Bama zai bari ayi Auren ba,Ni wallahi da badan kuɗin nan nasa ba ban ga abunda zanyi dashi b, kuma dana gama cin su zan kwashe komai nasa na barshi,domin in nace Miki inason shi yanzu na Miki ƙarya Naji ".
Shiru tayi kafin ta cigaba da magana tana yatsinar fuska kamar taga Tanim ɗin a kusa da ita.
Hmmm Nadiya manya aci kuɗi lafiya,har yanzu da alama ita lamarin mazan nan bai buɗe idanun ta ba,bata gama karantawa da lamarin su ba.😒😠😅
Cigaba da magana tayi jin Najiba na furta " kin bar Ni a gantale baki ƙarasa mini farkon zancen ba "...
" Eh shine fa yanzu ya ke sanar Dani wani sati za,a kawo wayata Iphone 16 d'in da yake na ƙara yi masa magana a satin da ya gaba ta tun yana America ".
Kai Najiba ke gyaɗawa cikin farin ciki tana furta kice mun ƙara zama manyan babies.Sai kuma tayi shiru sannan kuma a hankali ta buda bakin ta ta ƙara furta " Niko nace Nady bazaki bar wannan ɗabi'ar ba duk da ba kuyi nisa ciki ba ku hakura har ayi bikin ku kin sa yadda mazan nan suke ina tsoron wata rana yaci galaaba kan ki,na taɓa ganin wani labari irin haka wanda suka san juna tun waje daga baya ana gabda Daurin Aure Saurayin yace ya fasa.Da ga ƙarshe yarinyar nan har da asibiti ta kwanta kuma har yanzu ita akeyi yace shi bazai Auri yar iska ba wadda ta ke bin maza,kuma an ce maza masu yiwa mata haka mafi yawan cin su bason Allah sukeyi wa mace ba jikin ta suke so kuma da sun samu shi kenan zasu yada ke,Nima sirrin ya mace na mai Jidda Bello nake jin irin wayen nan labaran .''
Shiru Nadiya tayi bayan gama sauraren ta kafin ta sauke numfashi tana furta " kar ki damu Naji ina da wayau Najiba babu abun da zai iya yi mini a yanzu nasan shi sarai kuma.Munyi deal idan ya matsa zan rabu dashi kin san yana mugun sona shi yasa ya haƙura kawai har mu zama intimate,Kuma fa lamarin nan naga kamar Kema kina son ki ɗan taɓa ko,shan minti Ai ba wani abu bane ba yanzu kowace budurwa nayi ya zama ruwan dare.Amma Please kar ki ƙara sako irin wannan zancen idan muna magana karki manta munyi alƙawari wa junan mu kowa zaiyi minning business nashi " Tana kai aya kuwa ta tashi ta fice zuwa Falo domin haka kawai take jin tsoro ya ɗan shige ta na zancen Najiba.
Ita kuwa Najiba shiru tayi sai kuma ta Mere baki tana furtawa A hankali " Allah ya baki haƙuri Nady Ni haka kawai yanzu nake tsoron Tarayyarki da Na Tanim Abun da kuke yi kuskure ne,sai yanzu na ƙara fahimtar irin son da Ya Jamil yake mini shiyasa yake ƙoƙarin kare mutun cina da nasa.Murmushi tayi bayan gama zancen nata ita kaɗai tana ƙara duba wani post dake gaban screen ɗin ta wanda ya shafi yadda zaka gane na miji na yi maka so na gaskiya wanda akayi posting a facebook group sirrin ya mace na mai jidda Bello.
Ina bibiyar group na ( Sirrin kwalliyar ya mace ).
(Mai Jidda Bello ) da na ( Nusaiba tasi'u Abdul Rahman ) Suna ƙoƙari sosai A kan kawo mahimman cigaba ga mata da bada topic mai kyau da zai sanya mata da dama ɗaukar darasin rayuwa . Allah ya saka musu da Alkhairii.🤲🤲
Cigaba da Bibiyar post take yi wani tayi murmushi wani tayi dariya..Har ta manta da zancen Nady.
A ɓangaren Nadiya kuwa ta samu mahaifiyar ta a ɗaki inda ta je mata rai ɓace kamar zata saka mata kuka domin farin cikin da take ciki ya gushe akan zancen da Najiba tayi mata yanzu.
" Ya mace ikon ALLAH,Ya mace jari,Ashe kuwa ba Haushe yayi gaskiya domin kuwa Ni shaida ce gani ƙalau Allah ya bani nawa jarin,ya bani tsaleliyar budurwa wadda kowa ke alfaharin mallaka,Ko mace sai ta Sara ma Nady Baby ta kyakkyawa babu kamar ta duk garin Kano sauran mata duk rakiya suka zo ".
Wani irin murmushi ne ya suɓuce mata wanda bata shirya ma zuwan sa ba kasancewar kirarin na mahaifiyar ta ya shige ta da kyau.Har wani girma take jin kanta yana ƙarawa wani irin daɗi take ji mai daɗi a zuciyar ta.Ire iren wayen Nan kalaman sune mahaifiyar ta ke yawan furta mata suna kara mata jin kan ta wata shegiya ko acikin su ita da Najiba ɗin musamman da suka fahimci Tanim yafi Jamil kuɗi.
Dariya Mama hafsatu tayi tana riƙo hannun ta tana furta "......
Ba yawa 🙏🙏
Next page loading ✍️
Daga Alƙalamin ✍️
~*Fa'eeh bg*~
*GIMBIYAR TASKIRA*👑
*FA'IZA ALMUSTAPHA MURAI CE*.🤙
Ku nemi naku a channel ɗita domin anan nake update nasa mai buƙata sai yayi following kai tsaye.✍️✍️
Vote,Like,react,share,and comment ✍️🙏
🌸*RAYUWAR MU AYAU*🌸
Ƙarya ko sakin Aure
Short story
Labari da rubutawa
Faiza Almustapha Murai
Daga Alƙalamin✍️
Fa'eeh Bg
Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin.
Bismillahir rahmanir Rahim
💪📚📚
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
> >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*💤A MAFARKI NASANTA WRITER💤*✍️
*_Rayuwar mu a yau ba complete book bane,yanzu nake typing nasa,sannan kuma ba sauran novels bane taƙaitaccen labari ne.Ki bi ki karanta zaki Amfana sosai trust me.Tataccen labari ne mai cike da ilmantar wa da faɗakarwa harda nishaɗantarwa bana rubutu haka kawai sai na nazarce sa da kyau ta yadda zai amfani Al'umma domin samun cigaba ga Al'umma_*✍️
P.7
" Me yake faruwa ya ta ".
" Najiba tace wai Tanim ba sona yake yi ba jiki na yake so ".
Ta bawa Mama hafsatu Amsa cikin jin haushin zancen.
" Ke dallah ƙyaleta baƙin ciki ne ke cin ta ita da uwar ta,kuma yadda basu so haka zasu gani yawwa,in banda abunta wanda yake son jikin ka ai masoyin ka ne,shima wannan soyayya ce ".
Mama Hafsatu ta furta cikin son kwantar wa da yar ta hankali...
Murmushi tayi kafin ta ƙara furta Umma " Waya Tanim zai chanja mini Babba,kin san kuɗin ta fa yana sayen buhun shin kafa fiye da goma har da wani abu,ga baki ɗaya bata da daɗe da shigowa Nigeria ba manyan ya yan masu kuɗi ke riƙe ta sai matan manya irin mu ".
Takai ƙarshen zancen tana wani juya idanu.
Mama Hafsatu kuwa guɗa ta rangaɗa sannan ta furta cikin jin daɗi..
" Ni dama nasan ban haifi yar tsiya ba sai yar arziki,kice Kin ƙara zama Hajiya Nadiya wata rana zamu jiki ana zancen arzikin Nigeria dake " Ta kai ƙarshen zancen suna kwashewa da dariya kamar wasu taɓaɓɓu ita da yar ta ta.
Albarka ta cigaba da sakawa Tanim tana ƙara zuzuta Nadiya da koɗa ta.Suna cigaba da firar tasu.
***
"Beb ki shirya Zamu fita an jima bayan la,asar hope dai Dady baya nan ko? ".
Jamil yayi furucin bakin shi washe yana zaune daga cikin ɗakin nasu kan yar ya ƙusassshiyar katifar sa.
"Eh Beb Yana Dubai Amma ya kusa dawowa Sunyi waya da Hajiya tace ya kusa zuwa Nima kuma da muka yi waya yace zai dawo amma bai faɗa mini ba time ba ".
Kai ya jinjina kafin ya ƙara furta " Ki zama ready kawai Beb yau akwai shagali zamu yi outing mai kyau ".Jamil yayi furucin.
Fira suka cigaba da yi chan suna gab da yin sallama Najiba ta ƙara yin ƙasa da murya ta furta " Beb wai Ni yaushe zaka sauya mini wayar nan da ake ta yayi ".??
" Waya kuma Najiba " ?
" Ehh " Ta bashi Amsa.
" Ban daɗe da saya Miki waya ba Najiba ita ai Ta yayi ce ko baki gani ba iphone 14 ai Babba ce Najiba ".
" Uhmm ai akwai manyan ta Beb ni sabuwar yayi nake so,Iphone 16 "
Wani irin shaƙewa Tanim yayi har sai da Numfashin sa ya kusa ɗauke wa jin zancen ta ƙwaƙwalwar sa sai da ta daina aiki na wuccin gadi.
Jin shirun sa bayan gama tarin nasa yasa Ta ambaci sunan sa tana furta "Ya Jamil lafiya kuwa"??
" Uhm "Ya furta mata a sanyaye jikin sa yayi wani irin sanyi.
Sannu ta ke ta jera masa Cikin Tausayin sa Jin har Muryar sa tayi ƙasa "Baka ce komai ba Yaya Jamil ".Ta ƙara furtawa a hankali.
" Zance Naj " Ɗan shiru yayi kafin ya ƙara furta" zan yi magana ayo maki order ɗin ta in Sha ALLAH tun da ita kike so,Amma mai zai hana ki bari asaka Miki ita alefen ki Yadda abun zai yi armashi Dan dama ina da burin Saya Miki ita naga ita ake yayi musammam yan mata,sai dai nace na bari har muyi Aure domin na kusa zuwa gida na tura iyaye na su zauna da naki ".
Wani irin farin ciki Najiba ta tsinci kanta mai yawa jin zance Aure da ya shigo ciki wanda burin ta kenan ta bar wannan gida nasu da babu abinda ke cikin sa sai kayan wahala babu komai na more rayuwa.Kullum tuwo da kunu.
Cikin farin ciki ta amince masa tace ta yarda domin tasan zasu bada kala ace harda Babbar waya aka sako mata a lefe zasu zama topic of the day a cikin unguwa yan baƙin ciki su ji su gani su ji Haushi.
Fira suka cigaba da yi wadda rabi da kwata duka Najiba ce mai yi kafin sukayi sallama.
" Zufar da ke ƙara saukar masa tun jin zancen nata ne ke ƙara tsiyayar masa ajiki,zuciyar sa na wani irin bugu bana wasa ba, Zancen ya tayar masa da hankali ".Tunani yake yi yadda zai ɓullowa lamarin ina zai samu wayen nan kuɗaɗe na sayen wannan waya.Shi ta lakan sa ina ya ga kuɗin sayen irin wannan waya mai Shegen tsada shi kan shi ko a mafarki bai taɓa hangowa kan sa ya ganshi akusa da wayar ba sai dai yau gashi Najiba na son ta.Kuma Baya da kuɗin sayen ta.
Wani tunani ne ya faɗo masa inda yasauke ajiyar zuciya yana ƙara godewa uban gidan nasa.Duk yadda ya yi tsarin ajiye wayen nan ku daɗe da ya bashi dole ya haƙura ya cire su ya ƙara wasu na ajiyar da yake yi ya saya mata wayar domin farin cikin ta.
***
Miƙewa tayi harda taka tsalle na murna bayan gama wayar tasu.Nadiya ce ta shigo wadda ke Falo zaune suna taɓa fira da mahaifiyar ta wanda harda ita kira ne ya taso ta daga cikin su.
" Ke lafiya kike kuwa ".
Nadiya ta furta cikin mamakin yar uwar Tata da ta samu tana ta faman juyi aɗaki.
" Mind your business "
Najiba ta bata amsa kai tsaye tana sakin murmushi tana cigaba da juyin ta.
Nadiya kuwa ɗan kallon ta tayi kafin ta mere bakin ta sannan ta samu guri ta zauna tana furta in tayi wari maji.
Najiba bata ce mata ƙala ba har sai da ta gaji da rawar da yanzu ta kunna mata waƙa sannan ta koma ta zauna.
***
" Raliya shekaran jiya munyi magana da mahaifin ki akan Ibrahim wai iyayen sa sun zo ".
Mama Hasiya tayi furucin tana kallon fuskar ta yar ta dake wanze da murmushi.
Shiru tayiwa umma ɗin sai murmushi.
Ganin haka yasa Mama Hasiya sakin murmushi sannan ta furta cikin ƙaunar yar ta ta.
" Ba zaki ce komai ba Raliya ".
" Ni Mai zance Umma ".Ta furta a sanyaye
Tana yin ƙasa da kan ta.
Kai mama Hafsatu ta girgiza kafin ta ƙara furta " Maganar Auren ku ce sun zo nema kuma an basu ni ma bai faɗa mun ba sai baya bayan nan a she sun daɗe ma da zuwa ".
Ɗan shiru tayi kafin ta ƙara furta " kuma an bashi an saka bikin ki nan da wata huɗu kuma ya sanar mini akwai yiyuwar a haɗe da na yan uwan ki Ajiya ".
Jin wannan zance na farin ciki yasan ya da sauri ta ɗago ta na kallon mahaifiyar ta ta.
Kai ta gyaɗa mata dan tabbatar mata.
Murmushi ne ya suɓucewa Raliya har sai da haƙoran ta suka bayyana wanda ke ƙara bayyanar da asalin yarin tar ta da kyawun ta.
" Allah ya tabbatar muku da Alkhairi Raliya yasa wannan hanya ta zamo sanadiyyar shiryywar yan uwanki,Allah ya baku mazaje na gari ".
" Amin ya hayyu ya qayyum Umma Mungode da Addu,ar ki"
Murmushi mama Hasiya tayi tana kallon Raliya ɗin.Sannan ta ƙara furta " Allah ya ƙwato mini yata ki ta yani da Addu,a Raliya Ina son Najiba ta dawo guri na " .
Hawaye ne suka silalo mata ta sanya hannu da sauri ta share.
Kai Raliya ta girgiza cikin Tausayin Mahaifiyar ta tana jin wani irin Tausayin yar uwar ta da kuma na Mahaifiyar ta.
Wani zancen Mama Hasiya ta janyo suka cigaba da firar su ta ya da uwa cikin kewar Najiba duk da bata wani cika zama ɗakin ba yanzu.
***
Wani irin sauti ne ke fitowa daga ɗakin wanda bazaka iya tantance wa ba tsaye.
Bayan yan mintuna naji shiru hakan ya sa na kutsa kaina cikin ɗakin.
Ƙaton bedroom ne mai ɗauke da kayan armashi komai na ɗakin Daga nin sa babu karami komai ka duba kuɗi ne a dakin kamar yadda wajen gidan yake da tsari haka shima cikin yake tsare gidan masu kuɗi wayen da suka amsa sunan su masu kuɗin.
Fuskar sa kake hangowa sai kuma mace kan ƙafafun nasa ta juya baya ta sha uban attach kamar wata arniyya.
Sai zuba karuwan ci take yi tana yi tana shafa ƙirjin sa.Da wasu sassan jikin sa.
" Lady pls is ok kije ki buɗa wacchan lockern ik ɗauki abun da kike so ".
Tamin ya faɗa fuskar sa sai sai.Miƙewa yayi bayan gama maganar yana ɗan tura ta kaɗan gefe.Toilet ya faɗa ya bar ta zaune kan gadon tana yatsine ya tsine.
Miƙewa tayi ta sanya suturar ta ta shirya tsaf sannann ta buɗe lockern da ya faɗa mata ta zari iya abinda zata iya sannan ta fice daga gidan ba tare da tabi ta kansa ba.
***
" Kai Masha ALLAH Kinyi kyau Najiba,Mu dai kar amanta a yo muna tika way". ( Take a way ).
Turanci koda bala'i 🤪😅
Mama Hafsatu ce ke zancen ga Najiba bayan gama koɗa ta.
Ita kuwa sai Washe haƙora take yi kamar wata sakarya.
Hijab ɗin da ke hannun ta ta sanya kan matsatsin kayan jikin ta Sannan ta gyaggyara shi tare da ɗaukar wata leda wadda ke ɗauke da mayafi da takalmi.
" Ki gayar mini da Hajiya Samira ".
Mama Hafsatu ta ɗaga murya tana furta mata.
" Toh" kawai ta amsa cikin murmushi.
Ficewa tayi daga gidan gaba ɗaya bayan ɗan ƙarewa ƙofar Ɗakin Mama hasiya dake tsaftace Kallo haka tayi kallon sa daga tsayen da take Sai da tayi kamar ta shiga sai ta kasa kawai ta sa kai ta fice.
Kamar kullum napep ɗin da tayi haya ne ya kwashe ta sai ƙofar gidan da sauri ta faɗa gidan bayan yin yar magana da tayi da Shi.
Sum sum haka ta shige gidan bayan gaisawa da tayi da Alhaji Ahmed mai gidan kenan wanda bai daɗe
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 39