Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ɗan sama kaɗan haka ta cije da kuka da majina har ruwan nan suka huce tana ciki kafin zuwa lokacin kuwa ta ƙara galabaita tayi yaushi sosai jikin ta yayi jawur da shi ga wani irin zazzafan zazzaɓi da ke ratsa ƙasusuwan ta.✍️ Wayyo NADY😥😭 TEAM NADY A KAWO A GAJI HILISS 🥺 TANIM🧐🧐 Wata ta ce a mayar da labarin na kuɗi sai dai ni a bonus na baku shi FREE masoya na saboda ƙaunar da nake muku har zuciya na. Ina son duk wani mai mini kallo ƙauna na nesa da na kusa Allah ya haɗa mu a aljannar Firdausi maɗaukakiya.🤲🤲 Like share and comment,vote pls 🙏 Na roƙe ki taimaka ku tayani sharing Dan Allah.🙏🙏 Daga Alƙalamin Fa'eehbg✍️ GIMBIYAR TASKIRA 👑 Firstlady 🙌🤩 https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y _*Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chann zaku samu tun daga farko,harda sabon update ma.*_☝️ https://chat.whatsapp.com/H60CWiGISVFKEFT6NedEUw _*🌸RAYUWAR MU AYAU🌸*_ Ƙarya ko sakin Aure Gajeren labari Na Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _*Daga marubuciyar littafin*_ _*A Mafarki Nasanta*_✍️ Edited🖊️ P.16 Kukan da take ta riƙewa ne ya kubce mata lokaci ɗaya.Bwayan fitowar ta a cikin ruwan a galabaice inda ta haɗa tayi wani wankan da ƙyar na Tsarki da ruwan tap dake chan nesa kaɗan sannan ta fito daga toilet ɗin tana tafiya daƙyar domin ruwan sun taimaka mata sosai sai dai zazzaɓin da ke ƙara shiga jikin ta ƙara ruruwa yake yi. Cikin tafiyar ta da take yi a wahalce tana runtse idanun ta da wasu irin hawaye masu zafi dake zubo mata haka tayi ta share su sannan ta fice daga ɗakin da ƙaramin towel a jikin ta,rabin tafiyar ta Tata ana tsayawa ana hutawa har ta isa bedroom ɗin na ta Dan taji bazata iya zama anan ɗakin ba. Da shigar ta bakin sip ɗin ta ciro wata riga mara nauyi doguwa ta zuba sannan ta kabbara Sallah.Sallar Isha tayi tare da Asuba,sannan ta gabatar da sallah Azahar da lokacin ta ya kawo ana kiran sallah a wasu masallatai na kusa da su. Tana gama sallah ta haye kan gado babu wata Addu,a bare azhkar.Sai dai har yanzu idanun ta na zubar da ƙwalla azabar dake ƙara ratsa ta.Kwanciyar ta kan gadon ne ya ƙara fito da ainahin yunwar dake maƙale da cikin ta inda ya fara wani irin kuka sai kuma yunwar ta taso mata har wani amai ke taso mata saboda yadda take jin ta da alama ulcer ɗin ta ce ke shirin motsa mata. Cikin ta ta sha tana ƙoƙarin haɗiye wani kukan na baƙin ciki.Miƙewa tayi da ƙyar jin bazata iya jurewa ba hanyar kitchen ta nufa saboda ta san kan gidan abincin da ta tarar anci an rage ta ɗauka taci tana ta cusawa cikin ta hannu baka hannu akushi bakin ta har wani rawa yake yi da hannun ta.Haka ta cinye take away ɗin nan da an ci rabi an bar rabi wanda ke ɗauke da ketch up da Chips sai kayan ciki suma. A hankali ta ɗan fara jin rawar da jikin ta keyi ya fara ɗan saki.Sannan ta fara ƙoƙarin duba abinda zata iya girkawa shaf shaf.Indomie ta ɗauka guda biyu da ƙwai ta girka shaff shaff anan ta cinye ta cikin kitchen ɗin ta bar saura kasancewar ta saka wadda tafi cikin ta.. Ficewa tayi da lemu a hannun ta tana tana jan ajiyar zuciya ga wani zufa da yake to mata lokaci ɗaya falon take ƙoƙarin ratsawa sai dai me dariyar da taji daga gefen ta ce ta sanya ta ɗan juyawa tana kallon mai dariyar kafin kuma idanun ta su sauka akan shi yana zaune Da waya a kunnen sa hankalin sa kwance fuskar sa tass babu wata damuwa a ciki da alama ƙarshen wayar kenan saboda bai furta komai ba,kafin kuma ya ajiye wayar.Zuba masa idanu tayi kafin wasu hawaye suka silalo mata sai dai ta fara ƙoƙarin haɗiye su kar ya ga damar ta ma lokaci ɗaya. Yana nan zaune kawai taga an buɗo ƙofa an shigo.Bakowa bace kuwa face Lady.Cikin rausaya da kisina kamar wata ijabo ta zuba uwayen nails da attach akan ta ga wata irin make up da ta zuba a fuska sai hill ɗin ta da suke ta fitar da sauti. Da zuwan ta ta haye kan ƙafafuwan Tanim dake kallon ta yana sakin murmushi.Da alama da ita yake wayar. Shasshafa shi ta fara yi cikin Rashin damuwa ba tare da ta nuna ta ga wata halitta bayan su a gurin ba.. NADIYA kuwa wani irin rawa jikin ta ya fara idanun ta suna rufewa hakan ya sa da sauri ta kama hanyar bedroom ɗin ta sai dai ko Nisa bata yi ba ta tsinkayi Muryar sa da ta chan za wadda tayi zaton a kan kawai take chanzawa haka.Yana furta " ki girka muna wani abu ". Daga haka kuma ya miƙe da Lady ɗauke a kan jikin sa ya raɓa ta ya shige bedroom ɗin ta yana rufo ƙofar.juwa ce mai haɗe da wani irin bugun zuciya ya samu NADIYA lokaci ɗaya bango ta jingina da shi jin tana neman faɗuwa,kafin kuma tayi ƙasa tana sulalewa a gurin jin juwa na neman kada ita.Sai kuma Allah ya bata ikon Furta Kalmar Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un ta maimaita so uku hawaye na wanke mata fuska. Mamaki na kama ta da tsoron yadda rayuwar ta zata kasance agidan da take ganin yana neman zame mata duhu,duk da itama bata shigo gidan dan zama na amma taya zata samu abin da take so.Kenan ba ita kaɗai Tanim yake tare da ita ba sannan dama wannan itace ɗabi'ar sa,shine abinda iyayen ta suka guje mata kenan tun farko. Kuka ne mara sauti na baƙin ciki ya taso mata domin duk ba soyayya ce ta kawo ta gidan ba ta ji zafin abinda take gani da idanun ta domin kuwa babu macen da zata so aka wo mata wata a gidan ta,kuma alokacin da ya dace ace tana cin Amarcin ta,Kuma har cikin ɗakin da yake mallakin ta.Matuƙa abun ya taɓa ta.Sai da taci kukan ta sannan ta miƙe da ƙyar Dan jikin ta sai ƙara ɗumewa yake yi dan ta samu zazzaɓin farko ya sake t dan kan sa sai dai ba duka ba. Kitchen ta faɗa tana yi tana cije baki kafin ta fara ƙoƙarin haɗa musu abu mai sauƙi kasancewar a kwai komai na buƙata sai ta cigaba da aikin ta tana yi tana hawaye tare da cije baki ga rashin ƙarfin jiki da ta ke dashi dan yi take yi dagaske da ba haka ba zata iya tsintar kan ta ƙasa. Tabbas da badan wani irin tsoron Tanim da ya shige ta ba da bai ko gigin saka ta wannan aikin ta yi shi domin itama kan ta bala'in kan ta ce bata ɗaukar raini ko nawa sa ne. Har ta gama girkin tana zubar da hawaye da tunanin yadda rayuwar ta ta juya haka lokaci ɗaya duk ta fita hayyacin ta,shin me hakan ke nufi dama Tanim ba son ta yake ba,ko dai yana mata wulaƙaci ne saboda ya same ta gidan shi kamar yadda ta walaƙan ta shi a farkon haɗuwar su kafin ta tabbatar da asalin mai kuɗi ne na ƙwarai,ko dai bai samu yadda yake so ba duk wahalar da ta sha a daren jiya,to in haka ne ai takawo masa mutuncin ta ai.,Amma kuma,meyasa zai nuna mata rashin imani haka,sannan ya tsallake ta babu wani taimako har yanzu ko jin ya ta tashi,ko ta samu raunukka dan ba rauni ɗaya ba dan tana da tabbacin ta samu raunukka ayanda take ji.Shiru tayi tana sauke numfashi rasa mai bata amsar tambayoyin ta.Sai dai a ƙasan zuciyar ta kuma taci Alwashin sai ta rama cin mutun cin da yayi mata sai ta wawashe shi kafin ta bar gidan nan dan ita bada niyyar zama ta shigo ba dama tana biyewa mahaifiyar ta ne bata nuna mata bata son shi kaitsaye..Tabbas zata ɗan ɗana masa azaba mafi muni idan har ta gano yaudarar ta yayi da Auren kawai dan ya same ta. Ficewa tayi daga kitchen ɗin tare da tiren da ta ɗauro girkin akan shi wata irin zuciya na ta so mata wadda bata san cewa tana da ita ba. TANIM kuwa da suka gama ta,asar su akan gadon na NADIYA fitowa suka yi suna tiƙar dariya kamar wasu masoyan sabon Aure.Falon suka fito maƙale da juna suna cigaba da yin yan tsotsen su a gurin ba tare da sun nuna sun gan ta zaune gurin ba.Kai NADIYA ta sauke ƙasa ganin Tanim ya manna Lady a bango yana squieezing nata.Inda take nishin su ya karaɗe falon ganin haka ya sa Nadiya miƙewa cikin zafin nama da idanun ta da suka rufe ta shige kitchen da sauri bata ma san abinda ta ɗauko ba sai da ta buga wa lady ita akai ta san aika aikar da tayi bayan karar da Lady ta saki jin muciya ta ratsa kan ta da ke maƙale a wuyan Tanim.Tanim ma da yayi Nisa da kissing ɗin Lady ne ya sauke ta da sauri yana duba inda muciyar ta sauka akan ta ganin jini ya fara sauka a hankali hakan ya sa ya miƙe bayan zame wa ƙasa da yayi ita idanu rufe ganin abin da tayi ya zabga mata wani irin mugun mari wanda ya ɗauke ganin ta lokaci ɗaya a jin ta.Sai wasu taurari da suka wulga mata wutar zafin da ya shige ta. Dafe kuncin tayi kafin ta dawo hayyacin ta tana shaida abin da ya faru da ita ayanzu wai ita TANIM Ya saka wa hannu a fuska wannan abu ko a mafarki bata taɓa hango shi ba kenan ba son ta yake ba dagaske yana da wani dalilin Auren ta kamar ita ɗin dai.Maimakon ta samu hawaye sun zubo mata sai kawai ta samu kan ta da sauke guntun murmushi wanda yafi kuka ciwo da baƙin ciki kafin kuma ta shige bedroom ɗin na ta da suka fito tana sakin muciyar nan.Tanim kuwa da sauri ya taimaka wa lady ta miƙe da ita ya taimaka mata ta zauna sannan ya shige bedroom ɗin shi yan dube dube ya yayi sai dai idanun sa kan gadon suka sauka yadda gadon ya ke harmutse ga jini akan sa wanda bai da wani yawa,hakan ya sa tsikar jikin sa ɗan tashi kafin kuma ya doshi inda ya ajiye firsaidbox ɗin sa. Har ya kama ƙofar fita sannan ya dawo ya cire blanket ɗin ya tura shi toilet sannan ya rufe su dan ya san zasu iya shigowa a tare da Lady kowane irin lokaci. Treatment yayi mata inda ta ɗan bugu tare da bata pain relieve sannan ya janyo abincin da Najiba ta girka ya bata kaɗan taci sannan ta miƙe ta yi mashi sallama Dan ya tsorata da lamarin Nadiya bata yi zaton haka take ba,ya gano hakan ne a cikin idanun ta duk yadda yayi da ita shi yana son zaman na ta abun ya gagara ƙarshe ma dole ya zube mata maƙudan kuɗaɗen ta ta fice ta bar gidan gaba ɗaya inda ranshi yayi mugun ɓaci, cikin ɓacin rai ya miƙe ya shige ɗakin sa yana ajiye firstaidbox ɗin a ma'ajiyar sa,Sannan ya buɗe wata yar ƙaramar drower mai ɗauke da wasu irin kwalabe masu kyau da alama kuma alcohol drinks ne masu Shegen tsada Ɗaya ya zaro ya rufe ta sannan ya buɗe ta da iya ƙarfin sa ya fara tuttula ma cikin sa sai da ya sha fiye da rabi sannan ya ajiye,ya miƙe tare da zaro wata ƙwaya irin ta jiya ya samu madarar Hollandia da ciro yanzu a cikin fridge ya tsiyaya a cup ya haɗe su guri ɗaya bayan sun haɗe kuwa ya fice daga ɗakin yana layi alamar ya fara buguwa.Bedroom ɗin Nadiya ya nufa yana sakin wani Shegen murmushi. Allah ya fitar muna dake NADIYA.😥 Jamil kuwa da bansan abinda aka sanar dashi a waya ba ya dawo ɗakin fuskar shi na ƙara wanzar da damuwa.NAJIBA dake kallon shi kuwa kamar ta tambaye shi sai ta samu kan ta da kasa tambayar. Murmushi ya sakar mata kawai ganin tana binshi da kallo har ya ɗauki kayan ya fita dasu ya dawo.Toilet ya faɗa ya ɗauro alwallah ya wuce masallaci kasancewar an fara kiraye kirayen Sallah ta Azahar. Kai ta iya ɗaga masa kawai har ya fice bayan ya sanar mata da fitar ta sa.. Sai yanzu ta samu damar ƙarewa bedroom ɗin kallo bayan fitar sa inda wani irin farin ciki ke ƙara mamaye mata zuciya mai cike da samun kwanciyar hankali.Tunanin mahaifiyar ta ne da yar uwar ta ke ƙara taso mata lokaci ɗaya.Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta duba agogon ɗakin dake nuna ƙarfe ɗaya dai dai hakan ya sa ta miƙe domin yana ɗai daga cikin huɗubar mahaifiyar ta riƙe ibada yin Sallah a lokacin ta,wayen nan kalmomi sune na farko da suka fara ratsa Kunnuwan ta a cikin Nasihar mahaifiyar su hakan ya sa ta miƙe ta faɗa toilet ta ɗauro wanka tare da alwallah sannan ta kabbara Sallah.Tana gama Sallah kuwa ta shirya tsaff irin shirin da amare keyi jin jikin ta ya saki saboda ta ƙara gasa kan ta hakan ya sa ta dawo Falo ta zauna.Kallo ta fara sai dai ta saka ran ganin wani nashi ya zo sai dai babu,abu kamar almara babu wanda ya leƙo har aka kira sallah la,asar babu ko ɗayan dangin sa koda karen gidan su ne.Sama ta koma tayo sallah sannan ta sauko ta cigaba da kallon ta.Gajiya da kallon da tayi hakan ya sa ta kunna data inda ta tarar da sakonni rututu na ƙawayen su na jiya da kuma na yau da suke tambayar ta daren na jiya ya yakasance murmushi kawai tayi bata iya basu amsa ba,Tana sauke ajiyar zuciya,tuno da Nasihar da mahaifiyar ta, ta riƙe sirrin ta wanda ko ita bata yarda ta furta mata ba. Tana nan zaune ta fara jin hayaniya. Da sallama ɗauke abakunan su suka shigo cikin falon.Farin ciki ne ya mamaye zuciyar ta ganin dangin mahaifiyar ta na Jigawa wayen da zasu koma yau ɗin dan daga gidan na ta tasha zasu nufa saboda sun yi sallama Da Mama Hasiya ɗin sannan sunje ganin gidan Raliya. Cikin farin ciki ta tarbe su da murna sannan suka zagaya ɗakunan atare saboda basu samu damar zagayawa ɗin ba ajiya. Cikin farin ciki tayi sallama dasu tana Amsa addu'ar zaman lafiya da zuri,a mai albarka da suke bin ta da ita duk da ba afili take Amsawa ba saboda tana ɗan jin nauyin Ƙanwar mahaifiyar ta.Sai da ta musu kyautar Yan kudaɗen da take da su su ƙara kuɗin mota,duk da sun ƙi amsa amma haka ta matsa har da fara neman yin kuka dan su karɓa hakan ya sa yayar mahaifiyar ta wadda suke kira Adda Momy ta karɓa suka yi godiya suka wuce tare da yi mata bankwana. Suna ficewa Sama ta koma bayan ta musu rakiya fuskar ta na wanzar da murmushi,musamman da suka sanar mata da ga gidan Raliya suke sun same ta cikin kwanciyar hankali babu wata damuwa atattare da ita.Albarka tayi ta sakawa Ibrahim tana gode ma Allah da baiyi mata komai ba dan Tausayin ta take ji matuƙa kuma ta san shima hakan ne ya raga mata na wasu yan lokutta. Game ta Kunno da wayar ta,ta cigaba da yi sai dai ƙasan zuciyar ta tunanin Ina Jamil yaje haka ya daɗe abun na ran ta. Tana haka ne aka yi kiran sallah ta Magriba ta miƙe ta ɗauro alwallah ta tada Sallah sannan tayi addu,oi,karatun Qur'ani ta ɗan taɓa kafin ta naɗe sallayar sannan ta koma cikin toilet ta kara tsala wani wankan Sanann ta fito tayi shirin ta tsaff sai ƙamshi take zubawa cikin shigar ta ta ƙananan kaya riga da siket sai dai ba masu matse jiki ba. Jamil kuwa dake chan rigima ta kaure tsakanin sa da wanda ya bashi Aron kuɗi,Bayan ya baro gidan iyayen sa da ya shirgawa ƙarya na kayan jikin sa da kuma yadda suka ga ya ƙara yin wani irin kyau kamar wani mai kuɗi hakan ya sa suka rutsa sa da tambaya sai ya rufe zancen da ogan su ya ke sakar musu ganima a yan kwanakkin nan dan har abinci shi yake basu.wanda ya bashi aRon kuɗin kuwa Saboda ya nuna yana son abun shi yanzu wanda kuma ba yanzu sukayi da shi ba.Hakan ya sa suke ta raba zance tsakanin su Jamil na ta aikin rarrashin sa ya ƙara Mishi lokaci yanzu kudin da ke hannun sa na wayen da zai ɗan kula da Najiba ne kafin lokacin da komai zai bude masa.Jin ya ce yana da uzuri mai ƙarfi hakan ya sa mai kuɗin ya ɗibar masa lokaci nan da wata ɗaya hakan da ya furta kuwa ya ɗan sanyaya ran Jamil.Duk da haka kuwa haka ya shigo gidan zuciya babu daɗi ga wani irin nadama dake ta so masa lokaci ɗaya, dana sani ta lulluɓe shi. Ƙarewa Falon kallo yayi kafin ya kama step step ɗin ya Haye ɗakin ta ya fara dubawa ganin ta zaune a kan yar ƙaramar sofa dake a cikin bedroom ɗin mai cin mutun biyu hakan ya sa ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ƙara sa ciki yana sakin murmushi da shirya zancen da zai furta dan kare kansa dan ya san tsaff sai ta tambaye shi daɗewar da yayi. Ƙeya ce JAMIL mai sha ta sha sai dai a tara a rufe gaba.😔Sai da nace maka ka zamo mai gaskiya ka ƙi ji🤦 A ɓangaren RALIYA kuwa itama yau tana cike da kewar Mahaifiyarsa da ta yar uwar ta musamman da kowa ya watse aka bar ta ita kaɗai Dan Ibrahim ya fita bada daɗewa ba kuma ya ce yanzu zai dawo.Wayar ta ta janyo ta danna wa Numban Mama Hasiya da tayi Saving da Umma na.Kira ɗaya Mama Hasiya ta ɗaga tana sauke ajiyar zuciya.Murmushi ta saki tana furta " An Rale le na ɗiyar albarka ya gdn,ya ba ƙunta".Ta furta hakan bayan Raliya ta gama gaida ita. Murmushi tayi kafin a hankali ta furta " Gida ba daɗi " " Kull Raliya na hane ki,komai rashin daɗin sa kice Alhamdulillah shine a salin mumimi ya zama komai a gurin sa mai daɗ i ko mara daɗi ne idan aka tambaye shi ya furta Alhamdulillah,harshen shi ya riƙa furta Alhamdulillah,ya kasance yana godewa ubangijin sa a koda yaushe,Ubangiji kuma yana matuƙar ƙaunar masu gode masa a kowane irin yanayi na daɗi kona wuya hakan zai sa ya ƙara Miki ni'imar sa ki saba da hakan kin ji yar Albarka ". Murmushi Raliya tayi tana ƙara gode ma ubangiji da ya bata Mahaifiya irin Mama Hasiya wadda kullum take ƙoƙarin ɗaura su akan dai dai ta san cewa Allah ne ya jarabci mahaifiyar ta da rayuwar da yar uwar ta keyi sai dai ta san cewa tabbas mahaifiyar ta zata cinye wannan jarabawar saboda haƙurin ta da miƙa komai ga Ubangiji abu ɗaya ne ta sani wanda har yanzu yake ƙonawa mahaifiyar su rai shine yadda ta fitar da Najiba daga ɗakin wanda ita kuma ba haka take nufi ba guraɗau ne kawai take yi mata dan ta tsorata da ita,bata yi zaton Najiba zata iya tsallake ta ba sai gashi ta gani a aikace shine kawai abun da duk mahaifiyar su ta tuno da shi yake saka ta ɗan zubar da ƙwalla sai dai Alhamdulillah komai ya na kan hanyar komawa dai dai in sha ALLAH,ta san wata Rana sai labari. Muryar mama Hasiya ce ta katse mata tunanin ta. Tana furta. " Ina Ibrahim yana lafiya ". " Lafiya lau umma " " Ni kewar ku duk ta dabaibaye ni keda Adda NAJIBA,shi ya sa nace Miki gidan babu daɗi ". Ɗan murmushi Mama Hasiya ta saki kafin ta furta '' Zaki saba Raliya kinji,ki yi biyayya kinji Ibada ce wadda babu wasa acikin ta,kizamo daga cikin mataye na gari a gurin mazajen su,domin Aljannar ki na a tafin ƙafar sa,Sannan a ƙara riƙe ibada kinji na san halin ki babu wasa dan haka karki bari wani abu ya rinjaye ki kinji,ko ya shuumance ki, Karki bari shaiɗan yayi galaba akan ki,adage da Addu,a''. " To Umma in Sha ALLAH ". Raliya ta furta a sanyaye kafin wasu hawaye su silalo mata dan tabbas tayi kewar mahaifiyar ta.Mama Hasiya dake jin shesshekar kukan ta ƙasa ƙasa hakan yasa tayi mata sallama ta kashe wayar tana sauke numfashi domin ita kan ta tana haɗiye wa ne tun jiya,dan jiya ma bayan an watse taci kukan ta sosai sai da malam Rabu'u yayi ta aikin rarrashin ta. Tausayin yayan ta da rabuwa da su na sake narke zuciyar ta,tana jin babu daɗi ga wata irin kewar su da take ji.Dan ta kasa haƙuri tun wayewar safiyar yau take ta ƙoƙarin kiran Raliya da yar wayar ta itel ta kasa saboda tsoron jin yanayin da Raliya take ciki haka ma Najiba sai ta kasa kiran ko ɗayan su.Dole ta kashe wayar ma gaba ɗaya wanda sai lokacin ta kunna ta tana kunna wa kuwa kiran Raliya ya shigo inda ta ɗaga cikin farin ciki da kewar yar ta. Kuka ne ya ƙwace mata mara sauti inda ta sauke kan ta ƙasa ta tura shi acikin ƙafafun ta tana cigaba da sakin kuka kamar yarinya yar shekara goma. Ibrahim dake tsaye yana kallon ta tun ɗazu Dan ya kusa minti uku gurin ya saki guntun murmushi kafin ya ƙara so cikin bedroom ɗin yana zama kusa da ita.Raliya kuwa ɗagowa tayi idanun ta sharkaf da hawaye kafin ta sunne kan ta ƙasa ganin irin kallon da yake mata yana sakin murmushi kuma yaƙi rarrashin ta. Baki ta tura gaba cikin jin haushi,gashi shine sanadin kukan na ta ya rabo ta da umman ta. Murmushi ya ƙara saki sannan ya ce " Wai Umman mu me kika furtawa Raliyar mu haka,kuka take fa kamar yar Babyn da zata haifa muna nan da wata tara ". RALIYA dake sauraren shi kuwa shigewa ta ƙara yi cikin jikin shi,cikin jin kunya kasancewar ya janyo ta jikin shi bata iya musu ba duk da kunyar da take ji. Murmushi ta ƙara saki ganin yadda kunyar da ya bata na zancen sa ta ke bayyane.Shi mutun ne mai ƙaunar mace mai Alkunya mace duk yadda take Indai tana da matuƙar kunya a duk inda take burgeshi takeyi kuma yana ganin martabar ta.Zan iya cewa ba kai kaɗai bane Ibrahim domin kyawun mace mai mutunci ta zamo mai Alkunya domin itama kwalliya ce adon ta ce,kunyar mace hanya ce dake sarrafa tarbiyyar ta da hankalin ta tare da Natsuwar ta.Dan Haka.yar uwa karki yi wasa ki bawa Alkunyar da Ubangiji ya saka maki ta ya mace duk wuya ki zamo mai amfani da kunyar ki gurin sarrafa tarbiyyar da iyayen ki suka baki.Kunya maka mi ce Babba a gurin Ya mace.Duk wadda ta kasancewa bata da kunya zaka fahimci tarbiyyar ta ragaggga ce.✍️ Mu haɗe next page. Akwai yuyuwar naje hutu 🤦🚶🚶 Daga Alƙalamin✍️ Fa'eehbg✌️ Bazamfariya.🤩 Firstlady 🙌 GIMBIYAR TASKIRA 👑 Yawan react yawan Read more. https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chann zaku samu tun daga farko.👆 *🌸RAYUWAR MU

Chapter 12 of 39