Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da tayi shiru ne ta ɗan ɗago idanun ta ta saci kallon Dr Abida wadda ke.kallon ta da karantar ta tsaff. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta furta. " Mijin ta ne ta kama da ƙawar ta,ƙawar ta wadda ta san sirrin ta,kuma a cikin ɗakin ta, Dan nasan Nady bata ɓoye mata komai tsakanin ta da mijin na ta ". Tayi furucin hawaye na kwararo mata. " Subhanallahi shi Sayyid ɗin ne ya aikata haka,gashi da suna mai kyau,wasu mazan babu tausayi bare adalci a zukatan su ". Da sauri Najiba ta ɗaga ido ta kalle ta kafin ta mayar ƙasa tana sauke Ajiyar zuciya da tunani kala.kala. A ina ta san ya sayyid,Matsayin mijin Nadiya,sai dai idan itace ta furta shi amatsayin mijin na ta.Lallai ita ce to amma meye ma,anar hakan. Tayi wa kan ta tambayar. " Najiba,lallai dole Ya samu shock irin wannan case babba haka,ya kamata Ku Kai zancen gurin iyaye yafi,a zauna da iyayen sa da na ku,amma kam ya cutar da ita sosai,Allah zai saka mata in sha ALLAH,ai Allah ya baya barin haƙƙin wani kan wani ". Kai Najiba ta gyaɗa zuciyar ta babu daɗi sai dai ta kasa gane ma,anar shigar sunan ya Sayyid a matsayin mijin Nadiya ɗin,sai dai bata matsa ma kan ta da son sanin dalili ba ta bar shi akan sai yar uwar ta ta samu lafiya ta samu labari a wajen ta. " Na so ace cikin ya zube Dr.,mu Raba Auren nan,Saboda ba kan ƙawar ta kaɗai abun yake ba har na waje ma,kuma har gida yake shiga dasu,Ga wulaƙanci iri iri " . Najiba tayi furucin zuciyar ta babu daɗi. ",Kwanan baya ta zo mini da zancen ɓoye cikin na nuna mata babu hanya,sai zubarwa kuma mu baama yi anan,sannan karta ma fara irin wannan tunanin ta bar cikin ta ta haife abun ta.Bazan so ace cikin ya fita ba,ta bar shi zata ji daɗin abun ta nan gaba,koda uban shi baya son sa.Sannan maganar ki da kike son cikin ya zube,Najiba.Ai ko cikin ya zube bashi ne ke bata tabbacin rabuwar Auren ba,saboda shi Aure Allah ke haɗa shi da raba shi,kawai ku dage da Addu,a,idan Allah ya shiryar mata dashi shikenan,tun da Allah ke shiryarwa,A duk lokacin da ya so,kamar yadda nake kwana Addu,a haka zaku tashi tsaye ku kai kukan ku wurin ubangiji idan da rabon shiriya zaku ga an samu sauyi" Dr.Abida tayi furucin wani irin ƙololo na taso mata zuciyar ta babu daɗi,ga zafi na taso mata daga ƙasan zuciya wanda ta daɗe tare dashi.Ga wani irin bugu da zuciyar ta ke yi a duk lokacin da yi zancen Mijin Nadiya ɗin wanda tun waccan ranar take jin haka,Yau ma gashi yana maimaita kan sa. Kai Najiba ta gyaɗa tana Amsa Addu,ar samun lafiya da Dr. Abida ta ke yi ma Nadiya. Ɗakin Najiba ta koma inda ta same ta tana shan barcin ta a natse Nurse ɗin kuma ta fita bada daɗewa ba saboda aiki da ya taso musu. Zama tayi tana sauke numfashi.Ta kasa kiran kowa cikin iyayen na su sai da ƙyar ta yanke shawarar kiran RALIYA dan ta kawo musu abinda zasu saka ma cikin su da kuma ɗan abun buƙata kasancewar da jinin ya shige za,a sallame su. Raliya da Najiba ta kira cikin tashin hankali itama ta shirya ta yo nan dama a shirye take Dan yanzu ne ta shigo gidan saboda sun fasa practical ɗin sai gobe. Dukkanin abun buƙata ta je musu dashi cikin tausayin Nadiya.Duk da bata san asalin abun da ya faru ba.Ga mamakin abinda ya same ta haka har da kwanciya asibiti cikin abun da bai fi awa ɗaya ba. Shiru tayi tana sauraren Najiba dake kora mata bayani bayan shigowar ta asibitin inda da kwatance ta samu ɗakin. Cikin tausayi take kallon fuskar Nadiya ɗin idanun ta sun kaɗa sunyi jazir ita ta san cewa akwai abinda ke damun Addar ta Nadiya sai dai bata matsa ma kan ta da son sani ba.Ashe kuwa zaman haƙuri take mai wuya zama da manemin mata ai shine asalin zaman haƙurin dan mace na ƙunsar baƙin ciki ba ƙarami ba. Allah ka.muna tsari daga faɗawa hannun Azzaluman mazaje. Allah kayi muna tsari daga sharrin zina. Ka hana muna kusan tar ta.🤲 Kukan ne ya kubce mata bayan gama jin halin da Nadiya take ciki da ƙuncin da take fuskanta. Kukan na ta ƙarfi yayi ganin haka yasa Najiba fara Rarrashin ta kar abun ya taɓa abun cikin ta. Bayan ta tsagaita kukan ne ta ce a hankali murya a karye " Adda NAJIBA karmu bari wannan zance yaje gurin iyayen mu,mu binne komai anan gurin bana son su shiga tashin hankali musamman Su Baba". Hawaye ta share wayen da suka ƙara silalo mata. " Adda NAJIBA ki bani dama naci uban Shanty wallahi na koya mata hankali,na nuna mata bata iya bariki ba,yar iska Azzaluma,muguwa mai butulci kawai,kuma.Allah sai ya saka ma.Adda Nadiya an zalunce ta ƙwarai dagaske ". Kuka ne ya ƙara ƙwace mata sai dai bai yi ƙara sosai ba kamar na ɗazu. Najiba bata iya Rarrashin ta ba sai shiru da tayi tana kallon ta zuciyar ta babu daɗi. Ita kan ta da zata iya samun shanty da sai ta nuna mata zallar hauka Amma ta san yanzu shanty baza ta iya bari su ƙara haɗuwa ba zata ɓoye kan ta. Kuma muddin ta bawa RALIYA go a head zata bibiye ta ta ci zarafin ta ta san RALIYA ta fi su zafi a wasu lokutan sai dai tafi su sanyi kuma.Amma ta fannin faɗa idan aka taɓa ta ana rasa gane kan ta saboda zuciyar bala'i da take da ita shi ya sa bata cika shiga harkar mutane ba kamar su tun chan da. Sai wuraren ƙarfe bakwai na dare RALIYA ta koma gida bayan mijin ta ya zo ya ɗauke ta ya duba jikin Nadiya ɗin. Mama Hasiya da ta ji shiru ta kira Najiba inda ta sanar mata da an basu gado amma kar afaɗa ma Mama Hafsatu inji Nadiya wadda tayi furucin bayan farfaɗowar ta daga bacci na awa kusan biyu. Haka kuwa akayi mama Hasiya bata sanar da ita komai ba duk da ta shiga jin bahasin neman abinda ke faruwa Bayan ganin fitar ta Najiba tana rusar kuka. Addu'ar samun lafiya ta bita da ita. " Ki yi haƙuri ki barwa Allah,komai zai wuce,Nady Ni shikaɗai ne abinda zan iya furta Miki domin na san tabbas an cutar da ke kuma Shanty sai ta ga abun ta tun anan duniya,Wallahi dukkanin su zasu girbi abun da suka shuka,Ai zalunci baya taɓa dawwama,mu cigaba da Addu,a kawai shine mafita,Allah ya baki lafiya,kuma ya bamu ikon cinye jarabawar mu ". Najiba da ta gama zancen ajiyar zuciya ta sauke tana kallon Nadiya da ke zaune idanun ta rufe bayan ta gama cin abincin da aka zuba mata. Numfashi ya sauke kafin ta buɗe idanun ta da suka sauya izuwa jaaa.Sai yanzu ta ji kuka na neman ta so mata.Duk yadda take son dakatar da shi abun ya gagara.Dan wani irin kuka ne ya kubce mata mai tsuma zuciya bakin ta har rawa ya ke yi zuciyar ta na mata wani irin mugun zafi da ciwo. Najiba bata hana ta kuka ba sai ma gefe da ta koma tayi shiru domin ta san wannan shine zai rage mata zafin da take ji acikin zuciyar ta,Rahama ne a gare ta kukan. Sai da tayi mai isar ta sannan ta yi shiru kafin bacci ya kwashe ta. Najiba dake kallon ta cikin tausayi ta ta sauke Ajiyar zuciya tana kallon ta sannan ta rufe mata jiki tare da gyara mata kwanciyar ta. Itama tana gyara ma kan ta saboda dukkanin su sunyi sallolin su. Bacciin ta kwanta itama bayan tayi musu Addu'a saboda jinin har yanzu bai ƙare ba sai zuwa gobe. A ɓangaren su Tanim kuwa basu wani damu ba sai yar kunyar da suka tsinci kan su a ciki.Nadiya da Najiba na barin gidan suka koma kan network hankalin su kwance a cikin ɗakin na Nadiya. Jamil ne tsaye ƙofar gidan na su Najiba ya sha kyau kamar wani sabon ango fuskar shi sai ƙyalli take yi na farin ciki da murna.Sai ƙamshi yake bazawa. " Ance bata nan,amma ka shigo daga ciki ". Yaron da ya aika gidan ya sanar masa da hakan. Numfashi ya sauke sannan ya sallami yaron ya shige gidan anatse.Ɗakuna biyu ne ya gani a jere sai dai bai san wanda zai shiga ba hakan ya sa ya yanke shawarar shiga wanda ya hango haske a cikin sa. Da sallama ɗauke a bakin sa ya shige ciki yana sauke Ajiyar. Mama Hasiya ce zaune da Azkar a hannun ta tana karatu. Ta amsa masa sallama. Ƙasa ya kai yana gayar da ita cikin jin kunya dan tun daga kallo ɗaya ya fahimci itace maman su Najiba,Ga kama nan ta bayyana ƙara ra. Murmushi Mama Hasiya ta saki tana ɗan satar kallon sa sannan ta furta " Jamilu ne yau a gidan namu,shine ka tsaya waje ". " Eh Umma Ai munyi magana da ita zan zo a ɗazu ". Jamil yayi furucin. Wani irin murmushi mama Hasiya ta saki tana sauke Ajiyar zuciya wani irin farin ciki na mamaye zuciyar ta. Tunda har Najiba ta amsa kiran shi ta san ta sauko kenan ta a jiye makaman ta. Ya gida tayi masa da aiki. Ya amsa da ALHAMDULILLAH yana jin kansa cikin farin ciki. Nasiha ta masa sosai mai ratsa zuciya wanda dama itace dalilin cewa ya shigo. Sannan ta sanar masa da Najiba a asibiti zata kwana ya kira ta ya ji a ina ne,sai ya same ta. Nadiya ce babu lafiya taje kula,ta sanar masa. Godiya yayi ma ta sannan ya fice yana sauke.Ajiyar zuciya.Yana mamakin yadda akayi Naj ɗin sa ta samu halin da ta aro wanda ba na ta ba dan kwata kwata bai ga wani abu atattare da iyayen na ta ba tun daga maza har mata. Nace hmmm ai da ka haɗe da uwar gayya mama Hafsatu da ka shaida itace uwar ƙulle.😅 Mama Hafsatu TEAM kuyi haƙuri. Ba Ni na faɗa ba fa gaban ku akayi komai kuma kun gani akwai ƙulle ƙulle ga Mama Hafsatu.Yo mutun na zuwa wajen boka ba dole na kira shi da mai ƙulle ƙulle ba ƙullin na sharri. Allah ya sa mudace. Ya sa mufi ƙarfin zukatan mu. Yana fitowa anan yayi kiciɓus da su malam Abdul Basiɗ sun dawo daga wani masallaci wajen wa,azi suna zaune har su Malam Adamu. Gayar dasu yayi har ƙasa. Yana neman musu sallama malam Adamu ya fara magana. " Ban da gobe Asabar ya kama ko,ka zo ka tafi da matar ka,Allah ya bada zaman lafiya,Sannan a kula banda ƙarya ko yar ƙarama ce duk abinda Allah ya hore maka ka ciyar da ita dashi kar ka koyawa kan ka abun da bazaka iya ba,Karka saba mata da abun da baka iya cigaba da yi ka riƙe gidan ka da abun da Allah ya hore maka." Jamil dake sauraren su har da malam Abdul Basiɗ murmushi yake ta saki shi kaɗai yana ƙara ganin girman su da ƙimar su. Amin yake ta Amsawa bayan malam Abdul Basiɗ ya ƙara masa Nasiha mai ratsa zuciya tare da ƙara damƙa mishi amanar Najiba ɗin.Sannan ya bi Da Addua sai da suka yi Addu,oi masu yawa sannan yayi musu sallama cikin farin ciki ya wuce kamar ya taka tsalle.Yau ya ƙara ganin daraja da ƙimar iyayen Najiba. Mama Hasiya da bata lura da ledojin da ya bar mata ba ta zo saya ɗakin ta kenan ta ci karo dasu da mamaki take kallon su.jin ƙamshin Turaren da Jamil ya shigo dashi ne ya sa ta sakin ɗan guntun Murmushi tana girgiza kan ta. Tun da ya san bazata karɓa ba shine ya bar mata kayan nan bai ce mata ya ajiye ba. Ɗaukar kayan tayi ta saaya ɗakin na ta sannan ta shige ɗakin ta tana bin shi da Addu,a tare da Najiba. Wayar Najiba ya kira sai dai samun ta akashe ya sanya shi wucewa labarta ma Gariti abun farin ciki.✍️ 💋💞Daga Alƙalamin✍️fa'eeh💋💞 Like share,and react. Ƙarin bayani. *08069059746* *TEAM TAURARI HUƊU* ⭐⭐⭐⭐ _*ZAZZZAFAN LABARI DAGA*_ _*TAURARIN MARUBUTA HUƊU*_ *_Typing_* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y _Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chan zaku samu cigaban update.Farkon labarin masu neman sai a mun magana a numban dana sauke ƙasan wannan page, Dan samun document.☝️_ *🌸RAYUWAR MU AYAU🌸* Ƙarya ko sakin Aure Gajeren labari Na Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _*Daga marubuciyar littafin*_ _*A Mafarki Nasanta*_✍️ And now _*Rayuwar mu a yau*_ P.31 An Share kusan sati ɗaya Nadiya tana jinyar jikin ta sai dai a gidan ta Dan tun wan sahake aka ba su sallama bayan jinin ya ƙare,wanda Najiba take taimaka mata,saboda an bawa Nadiya bedrest saboda cikin na ta da yake rawa tun zubar jinin da ta samu sai asibiti suka bata hutun saboda cikin ya ƙara yin ƙwari da lafiya saboda raunin da ya samu..Najiba kuwa ta koma gidan ta Wanda Jamil yayi wa yar kwaskwari ma ya ɗan yi haske sai dai har yanzu babu silin bare fenti.Ta karɓi Tata ƙaddarar shi ya sa bata yi jayayya ba bayan zaman da iyayen ta suka yi da ita na biyu ta amince Jamil ya kwashi Abar sa suka koma gidan suka cigaba da gudanar da rayuwar su.Dama tana ƙaunar shi tun chan asali kwaɗayi ne kawai da karya suka so suyi mata cikas. A ɓangaren Tanim kuwa tun ranar da suka ci zarafin Nadiya a gidan bai ƙara bi takan ta ba sai ma shafe babin ta a cikin gidan na sa da yayi,wasu lokuttan ya manta da ita ma a gidan na sa bare cikin na ta.Sia dai hakan yana da nasaba da aikin Mama Hafsatu akan cikin Na Nadiya. Haka ma Shanty tana nan na naƙe da Tanim Kamar cingum duk inda zashi tare suke zuwa kamar wasu ma'aurata sannan yanzu yakan kai ziyara ga baturiyar da ya Aura wanda itama basu raba auren ba har yanzu sai dai bada sanin Shanty ba. A ɓangaren RALIYA ma Alhamdulillah tana cigaba da rainon cikin ta kamar sauran yan uwanta, ta ɗayan ɓangaren kuma tana cigaba da yin karatun ta hankali kwance taimakon da take bawa iyayen su kuwa sai abun da yayi gaba yanzu har abincin yake kai musu su girka da kan su shi ya sa Alhamdulillah yanzu komai suna samu dai dai gwargwado albarka kuwa kullum cikin shanta suke ga su Malam Rabu'u da Malam Abdul basiɗ har ma da su Mama Hafsatu. Lokaci na shuɗewa akwana a tashi ba wuya yau a wata bakwai da Auren su Nadiya da yan kwanakki ma sai dai duk wayen nan kwanakkin suna tafiya ne cike da baƙinciki mai tarin yawa a cikin zuciyar Nadiya dan ma Allah ya taimake ta ta duƙufa wajen yin Addu'a da ibada inda hakan ya taimaka mata ya rage mata damuwa har hawan jinin da ya same ta ya sauka sai abun da ba,a ra sa ba,ta ɓangare ɗaya cikin ta yana cikin ƙoshin lafiya.Sai kuma abu ɗaya da yake bata mamaki har yanzu shine rashin furta komai a kan cikin na ta da Tanim bai yi ba,zai zuba mata ido har cikin sai dai bai iya furta komai sai kallon ta hatta zuwa wajen ta kamar an yi ruwa an ɗauke sannan ya daina shigo mata da mata a cikin gidan na sa,sai ma wasu lokuttan tana jin muryan shi da maza a cikin falon kuma bata taɓa matsawa kan ta da son sanin ko me yake kawo su gidan ba tun da ta san komai. Iyakar ta da shi kallo ne babu musguna wa babu hantara bare kallon banza. Hakan ya ƙara mata kwanciyar hankali koba komai cikin ta da ita zasu samu kwanciyar hankali hakan kuwa ta kasance domin kuwa har da yar ƙiba Nadiya ta yi ta yi fresh cikin ya ƙara mata kyau tayi fess kamar yadda ya karɓi Najiba da Raliya haka itama ya zauna ɗass a jikin ta gwanin burgewa fatan ta kawai Allah ya sauke ta lafiya ta samu ko zata iya dai dai ta mijin ta su zauna su rufawa juna asiri Dan yanzu Tausayin shi take ji matuƙa ya koma salaff baya yin hayaniya ko kaɗan,sai take jin ta janye ƙudurin ta zata dage da roƙa masa shiriya wajen Ubangiji tun da har rabo ya haɗa su.Dan haka ta sanar ma Najiba ta haƙura da zancen rabuwa.Wannan kenan. Yau ta kasance weekend kowa na gida na yana hutawa.Tsaye take cikin kitchen ɗin da uban cikin ta yau ko gobe,Waƙa ce take sha a wayar ta ta Hausa wadda mace tayi cover ɗin ta,waƙa mai suna "Wazata soni" inda take fitar da sauti mai daɗi na waƙar da take bi saboda yadda take son waƙar. " ..Ni ba kuɗi nake nema ba Miji na gari nake so... da so samu ya zam mai tsafta sannan mai yawan zikiri na samu wanda ko dan da "ya'ya na gaba na fahari dan miji na gari shine natsuwar dukkan al'amari,wanda ya soni zan so shi ba babu ban ban zana kula dashi da karfi na babu banban..... Jikin ta ne yayi mugun sanyi bayan gama bin wannan baiti da take jin shi har cikin jikin ta a duk lokacin da ta kawo dai dai nan gurin sai ta tuno da iyayen ta maza da ta watsawa ƙasa a ido saboda kwaɗayi da ya rufe mata idanu da son abun duniya,ga kuma masoyin ta na gaskiya da har yanzu take kallo zallar hasarar da tayi ta masoyi na gaskiya, Dan ta san tabbas da Sayyid ta Aura da yanzu tana cikin kwanciyar hankali,amma kwaɗayi da son abun duniya da rayuwar flexing sun rufe mata Idanu ta zaɓi kuɗi fiye da soyayya.Wasu irin hawaye ne suka silalo mata masu zafi da ta tuno yadda ta bijire musu da irin wulaƙanci da tayi wa Ya Sayyid yau gashi ta faɗa a rame mai zurfi wanda bata san ranar fitar shi ba,kuma ta san cewa harda haƙƙin sa da na mahaifiyar shi a ciki.. Bata taɓa yadda samun miji nagari rahama ce da natsuwa ba sai yanzu da taga yadda yar uwar su RALIYA take cikin kwanciyar hankali tayi ƙiba wadda yanzu dukkanin su babu mai haɗa ƙwarin jikin sa da nata ta samu lafiya.Haka ma Najiba itaama tayi ƙibar ta gwargwado dan tana iya ƙoƙarin ta wurin kawar da komai da ya wuce ta fuskanci rayuwar da suka faɗa a yanzu ta maleji kuma gwargwado tana samun kulawa dai dai ta talaka mai Rufin a siri ga mijin nata domin baya barin ta ta gani ga yan uwan ta kullum yana ƙoƙarin faran ta mata da sai mata duk abin da take so wanda bai fi kuɗin sa ba.Haka ma abinci yana aje mata komai na buƙata sai dai gidan na su har yanzu yana nan yadda yake ɗan gyara kaɗan ne. Ajiyar zuciya ta yi bayan ta sauke nonstick da take amfani da ita wurin toya wainar fulawa da take kwaɗayi yau kasancewar yanzu ta fara aiki da kan ta cikin yayi ƙarfi ya zaunu. Fitowa tayi tana jan ƙafa saboda yadda cikin yayi mata wani irin nauyi kamar cikin yan biyu kasancewar an sanar mata da ɗaya ne a wurin a wo inji Likitota da hasashen su. _Ahtoo hasashe mana Allah ne kaɗai ya san abun da ya ajiye kuma yana basu dama ne kawai sai ayi sa,a abun da suka faɗa ne ya kasance wasu lokuttan kuma sai kaga yadda suka faɗa bashi ne ya kasance ba.✍️_ Zama tayi tana cin wainar fulawar ta da ta ji kayan haɗi ci take a hankali tana haɗawa da yajin da yaji haɗi wanda Mama Hasiya ta haɗa Musu duk su ukun ta bawa Kowa na shi saboda taga yadda suke son haɗin yaji. Tana tsaka da cin wainar ta ce ta ji motsi daga bayan ta.Ko ba,a faɗa mata ta san shine.Juyawar da tayi ce ta bayyanar da wanzuwar sa a gurin kan idanun ta saboda ta bawa ƙofar falon baya sai dai ta ji motsi sai in ta juya kuma. Kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kan sa kamar wani soko ya cigaba da tafiyar sa izuwa ɗakin sa.Nadiya da yanayin ta yake nuna ko ajikin ta ne ta kyaɓe baki ta harari bayan sa dan ita wannan yanayi da suke ciki burge ta yake yi zaman babu ruwan kowa da kowa, zafin ta ɗaya shine taren sa da ƙawar ta da ta ci amanar ta Dan bata cikin ko wace hayaniya ita dai burin ta ta samu ta haife cikin ta lafiya,Ta raine abun ta kamar yadda ake rainon kowane ɗai mai galihu.Wannan cikin shine farin cikin ta.Haka take yawan furtaa yar uwar ta. Tanim kuwa da yake jin shi wani iri ya sauke numfashi ya na wuce wa toilet ɗin ɗakin na sa inda ya watso ruwa kawai sannan ya fito yana fitowa ya gabatar da sallar Azahar da ya baro a nayi a waje Dan yanzu yana ɗan yin sallolin na sa kan lokaci sai dai ba complete ba wata rana biyu kawai yake yi a rana da abun da ya sawwwaƙa,wasu lokuttan sai abun yayi gaba sai yayi baya. *** " Wai ni Yaushe zaka bar Ni na je ganin matar Muhammadu tanim ina son zuwa amma ka na hana ni,me ya sa ba zaka barni da baƙin cikin da nake ƙunsa shekara da shekaru ba,me ya sa da zaran na ce zanje ganin matar ɗana da kuka hana ma ta zuwa gani na sai ka hana,ko har yanzu bani da iko da shi,da girman na sa ma kun raba Ni dashi ".. Wani irin kuka ne ya ƙwace mata mai sauti wanda yake fitowa daga ƙoƙwon zuciyar ta ita kaɗai ta san zafin da take ji a cikin zuciyar ta na abun da ke ji kan ɗan ta.Shin yaushe zata samu Shiriyar ɗan ta yaushe farin cikin ta zai dawo duk cikin yayan ta shine Namiji kuma shine take mugun so sai dai an mata shamaki da shi kan son zuciya wanda har ta mutu bazata ta ɓa mantawa da wannan zalunci ba bazata ce kai tsaye bata yafe ma Alhaji ba Amma tabbas matuƙa gaya ya cutar da ita. Kuka ta ƙara rushewa dashi jin komai ya dawo mata sabo tana katse maganar zucin ta akan case na kusan shekara goma sha biyar. Jikin shi ne yayi sanyi ganin yadda take ta rusar kuka har jikin ta na motsawa saboda yadda kukan ke sauka da ga zuciyar ta wanda shike nuna yadda take jin raɗaɗin a bun a zuciyar ta. Dafa ta yayi yace " Ki yi haƙuri Maman Sabira ,Na san na cuta Miki amma ina so n ki fahimci wani abu tun farko ke kika cuci kan ki ya zaki dinga hantarar yaro na sha faɗa Miki ki daina masa faɗa a duk abinda yake yi kin kasa haƙuri kullum cikin hantara,Shiriya ta Allah ce,yau gashi Tun yana zuwa gaida ke a matsayin ki na mahaifiyar sa har ya daina zuwa gaba ɗaya,Ita Jamila da ta iya taraiyar sa ba

Chapter 26 of 39