gashi yana zaune lafiya a gurin ta ba,duk da yake naki ne gashi nan tana riƙo kamar ɗan cikin ta tana zaune lafiya da shi,Ni ban ga abun tada hankali a ciki ba da har kike yawan ambatar cuta,Na sha faɗa Miki bana lamuntar cin zarafin ɗana kibar shi yayi yadda yake so kin ka sa haƙura shi ya sa na ga ya dace na yi maganin matsalar tun wuri,sai kuma Ga Jamila ta karɓe shi ba gashi yana cikin kwanciyar hankali ba yanzu tun da koda girman na shi na san zaki iya bin shi da faɗa."
Kallon shi ta yi da idanun ta da suka ƙara rikiɗewa,tana jin kalaman sa kamar ana yayyafa mata ruwan zafi saboda yadda suke ƙonar mata zuciya sannan cikin wata Muryar kuka ta sauke ajiyar tace " Alhaji Ba zaka taɓa ganewa ba,cuta ce an riga an cuce Ni,Amma tabbas wata rana gaskiya zata yi halin ta idan har Muhammad yana da rabon shiriya ina masa fatan Allah ya shirye shi duk wani abu da yake yi a tafin hannu na yake matar shi kawai bana saka wa ido,Na bar wa Allah shine wanda zai mun mafita kuma shine wanda yake shiryar da bawan sa.Allah Dan Sunayen ka tsarkaka Allah ka shiryi Tanim ka sa yana da rabon samun rahamar ka,Allah ka sassauta mini ka shirya mini shi Ka sassauta mini damuwa ta kayi mini maganin ta.".
Tana gama zancen haɗi da Addu,a ta ce Amin jiki a sanyaye.
Numfashi Alhaji ya sauke ba tare da ya masa da Amin ba dan shi bai ga wani abun tashin hankali a ciki,shi na zai iya takura yaro ba he's matured Dan haka ya san abin da yake yi shi ba zai ta kura sa ba kuma duk abin da ke nan ita ta nema saboda yawan hantarar sa da take yi lokacin da ya fara rashin ji.Shiru yayi yana tsayar da zancen zucin sa sannan ya ce
" Ke har yanzu baki ajiye musulunci ba su yaran yanzu a sannu ake bin su sannan kuma yanzu ɗabi'ar boko a ke yayi bata al'ada ba ko Addini,abun da ki ke gani Muhammad yana yi ba wani abu bane face hutawa tun da ba Neman mata yake yi ba,Baya sata bare homo ai Alhamdulillah iyakar shi kwasar yan mata titi Dan haka Ni ban ga abun takura anan ba da har kike je ro masa Addu'o,i kamar kamar mai aikata babban Laifi,Kuma ita Jamila tayi iya yin ta ta bashi tarbiyya ke kina amsa ke kika haife shi kawai dan Haka kar kiyiwa Allah butulci sannan ki daina saka masa idanu domin ɗana adai dai yake,Matar shi kuwa kina iya saka su shukrah ta kai ki,Kuma idan baki godewa Jamila ba zaki zage ta ba ta riƙa Miki ɗaaa da zuciya ɗaya. ".
Rai ɓace ya gama furucin yayi ficewar sa daga gidan saboda yadda ya ji Haushin yadda take furta an cuce ta,wata rana gaskiya zata yi halin ta duk ƙoƙarin da Jamila ke yi bata gani ba,shine take zargin ta da ta yi wa yaron da take iƙirarin na ta ne wanda ta haifa sai dai ba ita ce ta raine shi ba Jamila ce a hannun ta ya tashi saboda ita ALLAH bai bata haihuwa ba har yanzu da shekaru suka jaaa kaɗan..
Hawaye ta share masu zafi tana bin shi da idanun ta da suka rikiɗe izuwa jaaa sannan ta sauke a jiyar zuciya kukan da tayi tana jin yana rage mata Damuwar da take damun ta.
Sabira ce Wadda take Autaar mata.Dan ita kaɗai ce bata yi Aure ba saboda bata da isasshiyar lafiya tana fama da iska kuma itama yayar Muhammad ce,amma zaka yi tunanin itace ƙamwa idan ba faɗa maka akayi ba, Dan duka mata ne Allah ya bata su biyar sai Muhammad na shidda wanda yake Auta. Da sauri ta shigo tana cewa " Mamaa Ga Hajiya chan tare da Muhammad ban san yaushe ya shigo gidan ba yanzu Nima na hango shi,da alama fita za suyi tare ".
Ta kai ƙarshen furucin jikin ta sanyaye ganin yadda ta zuba mata idanu alamar ƙarin bayani take nema ga kuma idanun ta alamar sun sauya izuwa jaaa wanda ke nuna kuka ta sha kamar koda yaushe dan babu ranar da zata shuɗe bata mahaifiyar su bata yi kuka ba.Sai jikin ta yayi sanyi duk da ba yau ta saba ganin hakan ba gare ta,Kuma hakan bai da rasa nasaba da yanayin da Muhammad Yake ciki da kuma nata ciwon,juyawa tayi ba tare da ta iya furta komai ba zuciyar ta cunkushe ta bar mahaifiyar ya su ita kaɗai kasancewar ta san bata son hayaniya a irin wannan yanayin da take ciki.
Kiran wayar ta da akayi ne ya sanya ta miƙewa da sauri bayan amsa kiran da tayi.Mayafin ta ta shige ɗaki ta janyo da car key ɗin ta sannan ta fice compound. Motar ta ta faɗa da sauri ta shige ta tayar direct private hospital ɗin ta ta faɗa.
Emergency ta faɗa wanda yake Sashen maternity a chan ta tarar da Nurses sun duƙufa kan Nadiya da aka kawo yanzu naƙuda ta taso mata gadan gadan.
Abinda ya faru da Nadiya tana tsaka da cin wainar fulawar ta ta ji cikin ta ya fara mata wani irin ciwo ga bayan ta ya riƙe lokaci ɗaya,Cikin zafin azaba ta saki filet ɗin ta ƙasa tana durƙushewa ƙasa wani irin ciwo na taso mata, Tanim da ya gama shirin sa ya fito kuwa kallo ɗaya yayi mata ba tare da ya ji Tausayin ta ba ya tsallake ta ya fice duk da yadda ya ga take haɗa uban zufa da alama naƙuda ce ta tasar mata tsakiyar rana tun da cikin bai ma haura kwanakkin haihuwar sa ba.
A haka ta rarrahwa ta kira Najiba cikin zafin azaba saboda yadda take jin gaɓɓan ta na rabewa suna haɗe kan su ga rashin sabo.Duk da ita haihuwa ba,a taɓa sabo da ita.
Allah ya saukar da duk wata mai ciki lafiya ka rayar da ita da abun cikin ta.🤲🤲
A haka har ta isa bedroom ɗin ta cikin wahala da azaba ta kira Najiba,Najiba itama dake fama sai dai ta kira Mama Hasiya ta sanar da ita halin da Nadiya take ciki haka suka isa gidan a tare suka yi asibiti da ita.Sai dai tun da suka je da ita ta kasa iya haihuwa sai yan dabaru Unguwar zoma suke yi jin jirin yaƙi fita.
Babu yadda suka iya dole suka kira likita.
Dr Abida kuwa da tashin hankali ta faɗa ɗakin da Najiba take ciki musamman jin sunan patient ɗin ta ta da Aka kira aka sanar mata tana buƙatar C.S na gaggawa saboda cikin na ta da suka ji ya daina motsi a yanzu kamar baya da rai saboda wahalar da ya sha gashi bai cika sauran watannin shi ba.
Sahannun dangin aka nema sai dai Najiba ta ce bari ta kira Tanim ta sanar da shi ya zo ya saka saboda yanzu ya fi su dama da ita.
Kiran farko da aka fara yi masa da wayar Nadiya ƙin ɗagawa yayi sai ana biyu ya ɗaga wayar yana ɗagawa kuwa kamar wanda aka yiwa bushara bayan gama sauraren Abun da Najiba ke faɗa ya sauke Ajiyar zuciya kafin yayi furucin da ya kusan zautar da Najiba.
Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un shine abun da Najiba take iya furtawa kafin wayar ta suɓuce hannun ta tsoron ta na bayyana ƙara ƙara jin furucin na sa da har yanzu yake amsa kuwwa acikin kunnen ta wanda ya furta ba tare da tausayin Halin da Nadiya take ciki ba.
Daga Alƙalamin Fa'eeh bg✍️
Firstlady 🙌
GIMBIYAR TASKIRA 👑👑
Zamu yi paka paka in sha ALLAH saboda Azumi da ke gabatowa mu gama shi...
Idan mai kowa da komai ya nuna muna.
Allah ka gwada muna Ramadan lafiya.
Ameen.
Ku tura zuwa wasu group saboda Allah.
Like and react. Pls 🙏
*TEAM TAURARI HUƊU*
⭐⭐⭐⭐
_*ZAZZZAFAN LABARI DAGA*_
_*TAURARIN MARUBUTA HUƊU*_
*_Typing_*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
_Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chan zaku samu cigaban update.Farkon labarin masu neman sai a mun magana a numban dana sauke ƙasan wannan page, Dan samun document.☝️_
*🌸RAYUWAR MU AYAU🌸*
Ƙarya ko sakin Aure
Gajeren labari
Na
Faiza Almustapha Murai
Daga Alƙalamin
Fa'eeh Bg ✍️✍️
Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin.
Bismillahir rahmanir Rahim
💪📚📚
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
> >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>>
_*Daga marubuciyar littafin*_
_*A Mafarki Nasanta*_✍️
And now
_*Rayuwar mu a yau*_
P.32
" Na sake ta Saki Uku,Sannan kar ku ƙara danganta Ni da cikin nan ban haɗa komai da shi ba ".
Kuka ne ya ƙwace mata mai ƙarfi bayan jin kalaman na sa sun ƙara kutsawa cikin Kunnuwan ta kamar yanzu yake furta mata su.
Wayar ta ke kallo tana faman tsine masa a cikin zuciyar ta tare da bin shi da jafa'i kala kala sai dai ta kasa bayyanar da ko ɗaya a fili.
Mama Hasiya da take kallon ta kuwa sai baza ido take ta yi cikin mamakin abun da Najiba take yiwa kuka haka kamar ran ta zai fita kuma ta san da mijin Nadiya ne,tayi waya yanzu, to me yake faruwa ta tambayi kan ta sai dai babu amsa.
Ajiyar zuciya ta sauke dai dai Dr.Abida ta iso gurin dan ganin ko an saka hannun ba tare da ta bar Nurses su kula da hakan ba saboda yadda take ji akan Nadiya ɗin da bata san dalilin da ya sa ta ke jin son ta ba.
Kallon Najiba ta yi wadda idanun ta suka yi jazir sannan ta ce " Lafiya kuwa kuka haka Najiba,ai zata sauke in Sha ALLAH aikin kawai shine mafita in Sha Allah da anyi shi an gama,Duk da taci wuya zamu yi iya ƙoƙarin mu in sha ALLAH."
" Mijin ya saka hannun ne ?".
Ta kai ƙarshen zancen tana kallon Najiba da ta ƙara fashewa da kuka kafin ta karɓi biro hannun wasu Nurses da suka iso gurin yanzu wayen da ke kula da sashen.
Hannu ta saka sannan ta miƙa ma Dr Abida ba tare da ta iya furta komai ba.Dr Abida da jikin ta yayi sanyi bata ce mata ƙala ba ta karɓa ta duba sannan suka saka a file ɗin ta suka wuce sai dai cikin tunani take na dalilin kukan Najiba gashi kuma taga ita ta saka hannun kan ta,bayan mijin ta ne ya chan chan ta ya saka ta so ta hana sai dai bata da kuzarin yin hakan saboda yadda ta ga Nadiya na jin jiki dole tana buƙatar aiki na gaggawa wanda baya jiran dogon zance fatan ta dai Allah ya sa su wanye lafiya.
Haka suka faɗa Theatre ɗin nan da ita inda suka fara ƙoƙarin ceto ran ta da na abun cikin na ta da har yanzu baya motsi wanda suka fi saka ran ya mutu a ciki saboda wahalar da ya sha.
A ɓangaren NaJiba kuwa Dr Abida na wucewa ta ƙara fashewa da kuka mai tsuma zuciya ba kowa take tausayi ba face yar uwar ta shin ya zata ji idan ta farfaɗo ta ji wannan mummunan labari mai cike da rashin imani da rashin tausayi,Burin ta na son dai dai ta shi ya tafi a banza gashi cikin da ta ƙwallafa rai akan sa shima Likitota sun fara raɗe raɗen baya motsi alamar ya mutu kenan.Innalillhi wa Inna ilaiihi raji'un kawai take nanata wa cikin wani baƙincikin da yake ƙara ta so mata mai cike da Tausayin yar uwar ta,ita a gare ta hakan maslaha ce saboda yadda ta san Nadiya na kuka da Damuwar gidan Tanim,amma ta san yadda ta ƙudiri aniyar gyaran sa bayan ta haife cikin jikin ta sai ta koka matuƙa,sai dai ƙaddara ta riga fata abun da ta so a farko bashi ya kasance ba sakin da suke nema ido rufe yau gashi ya zo sai dai a lokacin da ba su so hakan ba musamman Ita Nadiya'r ta san tabbas abun zai iya ma taɓa ta har dai idan ya kasance hasashen likitota ya tabbata, ya zata sanar mata da labarin mara daɗi mai ƙona zuciya ?Ya zata iya furta shi ga mahaifiyar su.Shiru tayi tana tsayar da hawayen ta tare da fyace majina jin Mama Hasiya ta dafa ta tana ambatar sunan ta cikin son sanin abun da yake faruwa da ya saka ta kuka har haka ga cikin ta ya tokare kar abun ya shafe shi yana cikin ƙoshin lafiyar sa.
" Najibatullallahi! Me ya ke faruwa ne kuma,kike ta kuka tun ɗazu kin kasa furta komai ,Da likitar bata zo nan ba sai na yi zaton ko Nadiya'r ce muka ra sa,abu ga mai ciki zuciya da kwashe kwashe na rashin natsuwa,ki faɗa mini abun da ke faruwa na sa n akwai abun da kike ɓoyewa Najiba ".
Mama Hasiya ta yi furucin Jikin ta a mace dan tun da ta ga yadda Nadiya take wahala da yadda suka zo da ita jikin ta ya mutu mutu tus,Ga wata faɗuwar ƙirji da take ta so mata haka kawai babu dalili tun shigowar su asibitin amma ta san bata da nasaba da Yanayin da Nadiya take tun da kowa yake da mai haihuwa a cikin asibiti ko gida baya da kwanciyar hankali sai ya ji kukan jinjiri da fitowar uwar lafiya.
Kallon mahaifiyar ta tayi da idanun ta da suka ƙara cika da hawaye sannan ta tace " Ya sake ta Umma ".
" Kamar yaaaa ya sake ta " .?
Mama Hasiya ta yi furucin cikin son tabbatar wa da tsoro.Tayi furucin ne jin zancen wani iri kamar abun Almara.
Najiba ta gyaɗa mata ba tare da ta iya furta komai ba sai dai idanun ta hawaye yake zubarwa.
" Saki na wa ".?
" Ukku ''
Najiba ta furta murya a karye.
Mama Hasiya tayi furucin jikin ta da yanayin ta na sauyawa wanda take jin wata irin faɗuwar gaba da tashin hankalin wannan labari da ya riske ta rashin imanin yayi yawa ko a Film bata ta ɓa gani ba,ko a novel cewa an saki mace da irin wannan saki ba na tozarci,da rashin tausayi,da rashin imani an sake ta tana naƙuda,Bata ma san wanda ke tare da ita ba tana cikin halin rai ko mutuwa a ce an sake ta wannan wane irin miji ne suka Aurawa yar su,wane irin Mutum ne Tanim da bashi da tausayi ko ɗigon imani.Duk Ƙarfin Halin Mama Hasiya sai da ta zubar da ƙwalla Hawaye ta shafe a kaikaice saboda abun ya girgiza ta bata taɓa jin hakan ya faru ba sai yau, Zancen zuci ta fara...da ya sani ai sai ya sake ta tun farko,ko ya bari sai ta haihu sai ya yi sakin amma wannan wane irin zalunci ne,zaluncin da yake a bayyane.
Tunanni Kala da alajabi ne suka ƙara mamaye mata zuciya tare da tsoron mazan yanzu duk da ta wuce wannan level ɗin ta Aurar da duka ya yan ta amma ta na hango sauran yan mata masu ta sowa domin ta fahimci mazan yanzu yan ƙalilan ne masu adalci kuma na ƙwarai saura ba,a cewa komai ana haka ma ina ga shekarun gaba.Yau wai Nadiya ce aka yiwa saki uku na wulaƙan ci macen da take labour rai hannun Allah.Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un shi ne ta ke ta ƙara nanata tawa a bayyane da zuciya bayan dakatar da zancen zucin ta da tsoron da ya mamaye ta yayi mata shigar sauri.Lallai Nadiya da taga jarabawa domin zawar ci Masifa ce shi ya sa ta ke gode ma Allah da ya sa Najiba ta haƙura ta koma ma mijin ta ta rungumi abun ta domin ko kashe Auren ta yi bata san inda zata faɗaba wala Allah na ƙwarai ne ko akasin sa,shi ya sa aduk inda kake ka yi haƙuri shine zaman,ita rayuwa tana tafiya ne tare da haƙuri da juriya.Idan dai da ci dasha Na Rufin asiri duk yadda kike son kashe Auren ki ki haƙura shine maslaha a gare ki,baka san inda zaka faɗa ba idan ka fito musamman masu Ya ya A yi haƙuri a daina barin yaya a gidan uban su bai da amfani face ma ya kan zamo makami mai illata tarbiyyar yaran ka,Gidan mijin ki shine Rufin asirin ki kai duk wata mace ma.
Numfashi ta sauke tana kara zancen zucin ta tare da turawa a fili a sanyaye " Allah ya sauƙaka,ya sa hakan shine mafi Alkhairii a gare ta ".
" Ameen ".
Nadiya ta ce tana yin ƙasa da kan ta cikin jimami aka rasa mai iya ƙara furta komai ita da mahaifiyar ta sai zancen zuci da Kowannen su yake yi.
Suna nan a zaune har su Dr.Abida suka fito daga Theatre ɗin bayan ɗaukar yan awanni.
Da murmushi Dr Abida ta iso gare su,wadda take cikin wani irin shock tun ganin jinjiirin da suka yi nasarar ciro wa a jikin ta wanda kamar sa da Uban sa take bayyane ko makaho ya shafa ya san jinin muhammad ɗin ta ne,Sai dai ta kasa gasgata zancen sai ta ji cikakken sunan mijin na Nadiya kafin ta tabbatar da abun da idanun ta suke gane mata ƙara ƙara sai dai tana cike da mamaki sai dai kuma.ba,a bun mamaki bane tun data san da Auren matar ce bata sani ba.Haka ta isa gare su cikin farin cikin da ya mamaye ta. duk da yanayin da ta ga fuskokin nasu sai dai suma ganin nata yanayin ya sa suka saki jikin su tare da sakin fuskokin su sun san cewa akwai alamun na sara a fuskar ta.
" Congratulations an samu nasarar ciro mata santalele...."
" Docrrrrrrrrrrtorr "!
Furucin da ya ratsa kunnen ta kenan kafin ƙara sa zancen da take son ƙara sawa a gare su.Yanayin yadda Nurse ɗin ta ambaci sunan ta ta san akwai matsala kafin ma ƙarasowar ta kusa da ita.
Nurse ɗin da ta ƙara so yanzu tana haki ce ta furta yanayin ta a razane.
" Babyn ya koma Dr.,mahaifiyar kuma ta samu severe Bleeding wanda ya haddasa mata girgiza yanzu haka fama muke yi numfashin ta ma ya na neman ɗauke wa kamar dai yanayin ta itama zata bi yaron at any time,Dan komai nata yayi collapsed her pulse is not active sunyi collapse,tun da kika fita da ta ce a bata waya zata yi magana da mijin ta sai kawai muka ga komai ya sauya lokaci ɗaya ".
Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un Dr.Abida take furtawa Bayan jin bayanin wannan Nurse da tayi mata da turanci.
Najiba da take ɗan gane wani abu a cikin turancin ta ratsa wata irin mahaukaciyar ƙara kafin suka neme ta suka tsinta ƙasa kafin a riƙo ta har ta kai ƙasa inda alamu suka tabbatar ta suma.Cikin ta shin hankali Dr Abida ta yi kan ta tare da yayyafa mata ruwa baiwar ALLAH duk ta ruɗe ta rasa ta inda zata kama Ganin Najiba haka ga mutane sun taru kan ta hakan ya sa ta sheƙa da ɗan gudun ta sai ɗakin da Nadiya take kwance an ɗaure ta da wasu ƙarafuna ƙafa gefe hannu gefe sai dai kuma gata nan kwance cikin jini wanda sauran Likitotan suka yi nasarar tsayar wa da ƙyar, Numfashin ta kuwa Asama yake kamar zai bar jikin ta haka take ɗagowa tana komawa abun gwanin tausayi Sauƙin ta ma fisge fisgen ya tsaya.Dr Abida dake jin kamar ta fasa ƙara ce ta kalli yaron da har an rufe sa ta sauke ajiyar zuciya cikin tausayin Nadiya da na Jaririn ta da ta ga yadda take ta wasar haƙora bayan Fiddo dashi da aka ɗora mata shi a jikin kanta duk da baya da isassshiyar lafiya bai da kuzari,sun ma yi zaton ya mutu a ciki cikin Ikon Allah sai gashi lafiyar shi lau,sai dai babu lafiya Ɗan ko kuka bai yi ba har yanzu da ya komawar sa.Bayanin da sauran Likitotan suka ƙara yi mata ne ya ɗaga mata hankali jin cewa har da jinin ta yayi wata irin muguwar hawa dan su kan su sun tsorata da yadda jinin ya hau lokaci ɗaya,Kamar bayan zu take.lafiya ba,Ko ita da take tsohuwa take da matsaloli,take cikin alhini na shekara da shekaru ai jinin ta bai taɓa hawa haka ba duk kuwa da baƙin cikin da take kunsa.Kuma sun tabbatar mata dalilin zuwan wannan matsalar hakan bai rasa ba saba da Wayar da tayi yanzu mintinan biyar da suka wuce sudai sunga yanayin ta ya sauya kafin kuma ta saki ƙara sai ɓallewar jini da tsinkau tsinkau,sai kuma janyewar numfashi.Tsoron ta shine numfashin da ake ta ƙoƙarin dai dai tawa ya ƙi tsayuwar waje ɗaya ya ƙi dawowa..
Tana cikin wannan alhini da tashin hankali kawai suka ji Nadiya na wani irin kakari kafin komai na ta ya tsaya Chak babu Numfashi a tattare da ita.
Tashin hankalin da Dr.Abida da sauran team ɗin suka tsinci kan su ba ƙarami bane a wannan lokaci dan ita ta ma kasa taɓa ta sai zufa da yake keto mata da wani irin tsoro da tausayin Nadiya ɗin har da su Najiba ma sai dai gefe guda kuma Rashin ganin mijin na Nadiya na tayar mata da hankali kuma ta san ya san cewa Tana asibiti tunda babu yadda za,ayi matar ka na labour baka sani ba.
Haka suka duƙufa kan ta ganin ko akwai sauran numfashi da shan ruwa a gare ta sai dai kamar suna yin komai a banza.
Nadiya ta tafiyar ta Dan duk dubarun da ake yi babu abun da ya motsa na jikin ta.
Hawaye ne suka silalo ma Dr Abida cikin wani irin rauni kafin ta ɓarke da kuka wanda bai ra sa na saba da tausayin Nadiya ganin yadda suka gama binciken su suka rufe ta da farin ƙyalle wanda ke nuna alamar ta bar duniya kenan ta shiga layin gawa.
Wani irin Tausayin ta ne da na Jaririn da har yanzu take kallon hoton fuskar sa acikin idanun ta sak lokacin da ta haifi ɗan ta Muhammad.
Ajiyar zuciya tayi tana Addu,ar Allah ya jiƙan Nadiya da Rahama ya yafe mata kura kuran ta.Fitowa tayi da ga ɗakin adai dai lokacin da Mama Hafsatu ta iso tare da su Malam Abdul basiɗ da rabu,u da aka kira yanzu inji Najiba wadda ta farfaɗo cikin ruɗewa.
Shiru tayi ganin yadda duk suka Zuba mata idanu kafin a hankali murya na rawa cikin son riƙe yanayin ta ta furta " Malam muje Office ɗina " Tayi furucin tana kallon fuskokin su malam Rabu'u da Abdul basiɗ da suke cike da tashin hankali.
Bayanta suka bi da sauri.
Sai da ta ɗau minti uku haka sannan ta sanar da su rashin da suka yi har na yaron da a koma kafin mahaifiyarsa sai dai bata ko kai ƙarshe ba tayi shiru zuciyar ta babu daɗi Tausayin A halin na kama ta badan komai ba sai dan ganin yadda lokaci ɗaya idanun su suka yi wani irin mugun jaaa dake nuna tsantsan tashin hankalin da suke ciki da yadda lamarin ya kiɗima su duk da kowa baya wuce
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 39