Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
taya iyayen ku Addu,a da yar uwar ki dama ita kan ta Yaya Hafsatu da Nadiyar, Nikaina banji daɗin abun da tayi ba,kwata kwata babu mutunci a cikin lamarin idan har zata musu ta bari sai sun zama su kaɗai a gidan namu Amma ace gaban su malam Adamu ta nuna basu da wata power a gidan nasu ". wasu hawaye ne masu zafi suka silalowa mata ta share a hankali kafin ta share ma Raliya na ta dake ta kwaranya a kan fuskar ta. "In Sha ALLAH,Umma zan yi". Rakiya ta furta a sanyaye tana son kawar da komai ganin yadda itama mahaifiyar ta ta idanun ta suke a rikiɗe da alama itama ta koka ko kaɗan ne. Ajiyar zuciya mama Hasiya ta sauke sannan ta yiwa Raliya sallama tana furta " Ki fito ki gyara maana sauran ganyen letus mu kwaɗa yunwa nake ji na san suma malam haka ce a gurin su ".Kai Raliya ta gyaɗa tana haɗiye ɓacin ran dake zuciyar ta akan mama Hafsatu ɗin. Ita kuwa Mama Hasiya tana gama zancen ta fice daga ɗakin Raliya jikin ta itama a sanyaye.. Haka kuwa akayi ta fito ta faɗa wani ɗan ɗaki ta fito da komai na buƙata tare anan ta zauna falon na su ta yayyanka komai ta cire na cirewa babu hayaniya.Tana cikin yin aikin ne akayi kiran sallar Azahar kasancewar ta gama haka ga wanke shi ta zube a wani ɓararren kwando da ya ji jiki sannna ta wuce gurin sallah.Mama Hasiya da ta fito ta ga komai na kimtse ta zauna ta haɗa musu Lafiyayyen kwaɗo gwargwado na talaka.Haka ta kasa wa kowa har su Najiba da Nadiya da Mama Hasiya duk da ta san ba lallai su iya cin shi ba tun da sun saka ma kan su rayuwar ƙarya. A ɓangaren Mama Hasiya kuwa tana fita da Nadiya bata zame da ita ko ina ba sai falon na ta da har yanzu bai samu gyara ba duk da an daɗe da tashi dan yanzu kusan Sha biyu saura.Haka take rarrashin ta kamar ta mayar da ita ciki Dan wani irin kuka ne take yi wanda ke ƙara tunxura zancen su malam Adamu da ta san cewa su Malam Rabu'u ne suka Hassala shiryar da hakan kasancewar ta san babu abinda zasu iya shine suka saka mugayen waklilla ƙwafa tayi tana furta. '' Kuma zan bi ta kan ku, Azzaluman mutane kawai ". Sannan ta cigaba da magana tana bawa Nadiya ƙwarin gwiwa tana ɗorawa da furta " Wallahi idan kin ga kin Auri wani banza malamin islamiyya chan wai shi Sayyid,to sai dai in bana raye amma babu ɗan iskan da ya isa ya Miki Auren dole,shi kenan dan anga yarin ya yar Hutu da gayu kyakkyawa duk unguwar nan shine ake son ayi mana ikon da ba zamu ɗauka,,an ga zaki Auri mai kuɗi duk unguwar nan shine ake neman yi maki sabau to,to wallahi ba zata saɓu ba kima daina zubar da hawayen ki,Aure kamar an ɗaura shi ke da Tanimu ".Ta kai ƙarshen zancen tana sakin murmushi da guɗa lokaci ɗaya tana ƙara furta " Kamo ta nan kamo ta nan ".Tana zancen tana dariya tare da jan kumatun Nadiya da ke Turo baki gaba alamar ta fara sauka kenan.Dan sai yanzu ta samu damar yin motsi kalaman mahaifiyar ta sun mata wankin tsantsa take taji damuwar ta ɓace mata.Najiba dake zaune a gefen ta takure guri ɗaya suka zubawa idanu dan yanzu ganin suke kamar harda ita akayi wannan munafuncin kasancewar ta ta ɓa furta mata Tanim ba son Allah ya ke mata ba. Wanda sai yanzu suke haɗa rashin Auren da aka ce na su aminta ba da kuma na ta zancen..Wanda har saboda ita yanzu mama Hafstu ta yaɓo wasu kalaman. Ɗauke kai suka yi a tare sannan suka cigaba da taɓa firar su ta ya da uwa dake nuna shaƙuwar su sai dai har yanzu Najiba ba ta saka bakin ta ba dan zantukkan sun mata wani iri sosai kwata kwata bata son abinda ya taɓa iyayen nan na su musamman Malam Abdul basiɗ saboda Allah ya saka musu ƙauna mai tsanani a tsakanin su a chan baya idan ba faɗa maka a kayi ba ka gan su a waje zaka yi tunanin shi ya haifi Najiba da cikin sa.Sallamar Raliya ce ta katse musu maganar su inda ta shigo a sanyaye bayan tayi sallama da kuma haɗa idanun da tayi da yar uwar ta Najiba... "Aah Tsiren Talaka yau muka samu a gidan,ai da yake ma bamu da yunwa,ko dai ki tafi dashi kawai ". Mama Hafsatu ta furta tana murmushi.Raliya kuwa bata nuna komai ba akan fuskar ta sai kawai ta fara ƙoƙarin juyawa Hawayen ta na son silalo mata na tausayin Najiba dake rakuɓe gefe idanun ta sun ɗan sauya na damuwa da alama akwai abun da ke damun ta wanda da ace a gaban mahaifiyar su ne da tuni ta sanar mata ko menene dan neman mafita. " Ki dawo dashi an jima zamu ci ".Ta tsinkayi Muryar Najiba na zancen saboda haka kawai taji bayan cin fuskar ba zata yarda a mayar dashi ba,zata karɓa ta ci ta ajiye sauran ko banza ganye ne tana son shi.Musamman haɗin mahaifiyar ta. Haka kuwa Raliya ta juyo fuskar ta na wanzar da murmushi wanda bata shigo da shi ba sannan ta a jiye ma Najiba robar tana sakin murmushi haka ma Najiba ɗin murmushi ta saki tana kallon lafiyyar robar ta Mahaifiyar ta wadda take tsaff sai dai akwai alamar tsufa a tattare da ita. Ficewa tayi tana sakin murmushi ganin Najiba ta ɗan fara tsakura bayan ta nemi ƙaramin pork gudun saka masa hannu ya lalace. Haka ta fice tana komawa ɗakin su sai dai bata sanar da mahaifiyar ta komai ba.Wanda ta hango farin ciki kwance akan fuskar ta ta.Bayan ganin bata dawo da robar ba.Na su malam Adamu ta ɗauka ta kai musu anan rumfar ƙofa gidan na su dake Manne da yar takangar ƙasa ta gidan wadda ke zagaye da kara darnin kara. Su malam Abdul basiɗ da suke zaune bayan an watse daga sallah ta Azahar da suka gudanar akan lokacin karɓa su kayi suna saka mata albarka kafin suka fara cin abinsu hankalin su kwance kasancewar sun watsar da komai duk da abun na zaune a ƙasan zukatan su.. Najiba kuwa sai da ta ji cikin ta ya ɗauka sannan ta ajiye kwaɗon ba wai dan basu da abinci ba fridge na su shaƙe yake da snacks ɗin su da namomi.Sannan ta saka shi cikin fridge ɗin ta bar falon izuwa waje arwallah kawai ta ɗauro ta dawo ta wuce ɗakin na su ta raɓa Nadiya da ta buɗe fridge ɗin ta fiddo da kwaɗon tana ci Dan ganin yadda Najiba ke cin shi hankali kwance ya san cewa yayi daɗi sai ta kwaɗaitu da son cin shi.Sai dai bata ce mata komai ba dan ta san dama za,aYi haka shi ya sa ta saka shi cikin fridge ɗin ma.Ita kuwa Mama Hafsatu ta so hana Nadiya ɗin sai dai ganin ta na so ya sa ya ƙyale kafin itama ta zura hannu suka haɗu suka cinye shi suna lasar kufan roba.Suna ƙara yarda da garɗin hannun Mama Hasiya domin duk wani abu da ta yi da hannun ta sai ka ji test ɗin sa ya maka daɗi.Suna gama cinye wa suka sha ruwa suka yi Hamdala kafin kowaccen su ta miƙe dan gabatar da sallah. *** Haka rayuwa ta ke tafiya duk bayan seconnni,mintina,Awanni Kwanakki kuma duka kwanan mu ne ke raguwa a cikin duniyar lillahi da wuya da babu daɗi kowa yana rayuwar shi yadda ALLAH ya tsaro mashi da yadda zata kasance.Yau Sati Uku kenan.Inda su Malam Adamu sunyi bincike akan Jamil sun yaba da tarbiyyar iyayen shi da ta shi domin a binciken na su sun gabatar da shi ne tare da mijin hajiya Samira hajiyar Dubai da Najiba da kan ta ta saka mama Hafsatu gaba da zancen suka shigar dashi cikin lamarin a matsayin uban Najiba wanda da ƙyar Alhaji Ahmad ɗin ya yarda wanda sai da matar shi ta tilas ma shi sannan kasancewar yana ƙasar sai ya shige ciki ake ta zancen da shi cikin Dattako Wanda har an tsaida zancen Auren na su kamar yadda aka tsaida na Raliya rana ɗaya nan da wata uku masu zuwa. Najiba daɗi kamar ya kashe ta samun wannan labari.Haka ma ta ɓangaren Jamil burin shi dake da dab da cika lamarin yayi masjid daɗi. Ta ɓangaren soyayyar su suna nan suna gudanar da ita yan da suke so abu ɗaya ne Jamil baya yarda shine ke ɓantar su duk yadda zuciya da kuma wasu halaye da Najiba ke nunawa ya kame kan sa bai bawa wata ƙofa damar karya mishi tsarin shi ba yana tare da ita kamar yadda yake son ta da kaunar ta saboda Allah, Dan ita kam abun burge ta yake yi yadda su Najiba ke gudanar da tarayyar su suna yan tsotsem su na shan minti. A ɓangaren Nadiya kuma da Mama Hafsatu suna nan tsaye kan bakar su haka ba su san da wanchan zancen ba.Dan ma wani babin soyayya Nadiya ta buɗe ita da Tanim ɗin wanda shi ma ya zage yana nuna na ƙwarai yake a fili saboda samun abinda ya ke so anan gaba yana ƙara nuna mata ƙauna tare da kashe mata maƙudan kuɗaɗe dake ƙara nuna mata irin soyayyar da yake mata wanda take ɗauka a matsayin pure love domin har iphone 16 ɗin ta an kawo mata wanda harda dan ƙaramin party ta haɗa awani gurin shaƙatawa ita da kawayen su. Yau ma zaune take bayan tafiyar Tanim ɗin da ya kawo ta gida bayan sun gama sheƙe ayar su ya dawo da ita har ƙofar gida kamar koda yaushe anan ma dai da sai da suka daɗe ƙofan gidan sannan suka yi sallama da juna.Sallamar yaro ce da ke furta ana sallama da Nadiya ya saka ta ƙunduma Ashar daga cikin ɗakin da take kasancewar yan kwana biyun nan Ya Sayyid ɗin yana zuwa ƙofar gidan sai dai bata taɓa fita ba.Ranta a ɓace ta furta " Gani Nan zuwa Dan kutumar ubanku kai dashi,idan baka ɓace mun daga nan ba sai na jeme ka ". Sum sum haka yaron ya juya yana tsoron ta zane shi ganin yadda take harare bakin ƙofar da ta ɗan ɗaga ya ƙusasshen labulan ga zagin da suka ƙarba shi da wanda ya aiko shi. Hijabi kawai ta ɗaura kan jikin ta. Wanda sallah kaɗai ke saka ta saka shi amma yau saboda masifar da ke cin ta haka ta kwashi hijabin ta fice duk yadda mama Hafsatu ke ƙwala mata kira bata saurare ta ba sai ma ficewa da tayi daga gidan wata irin zuciya na ƙara cin ta.Har ta fita ta dawo da sauri tana yin ƙyafci tare da yin ƙwafa tana ɗaukar wasu ruwa dake ajiye kamar na ƙazan ta haka Dan har wari suke yi,ita kan ta sai da ta daɗe hanci domin ruwa ne da mahaifiyar ta ke tarawa a ƙaramin bokitin kamar na wankin kaya haka ko wani abu sannan a je a fitar waje saboda inda ruwan su ke wuce wa ya toshe. Haka ta fice tana surutai ita kaɗai bakin ta har kumar Masifa yake yi Mama Hafsatu dake kallon ta kuwa murmushi tayi ba tare da ta dakatar da ita ba sannan ta saki labulen tana juyawa ranta fess Dan dama tunanin a bunda zasu masa take yi kafin ta kai ga cin galaba akan aikin ta. Ikon ALLAH Nadiya me kike shirin yi wai 🤔🤔 Mu hadu next page.✍️ GIMBIYAR TASKIRA👑 Daga alƙalamin✍️ Fa'eehbg ✌️ Firstlady🙌🙌 *🌸RAYUWAR MU AYAU🌸* Ƙarya ko sakin Aure Short story Labari da rubutawa Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa ga Mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _Daga marubuciyar littafin_ _*A mafarki Nasanta.*_ P.10 *_Ongoing_* A what's App channel ɗita nake update nasa.Kaɗai. Idan kina buƙata sai ki bibiya ki karanta. *** Ya sayyid dake tsaye yana jiran ta a hankali yana ɗan duba Agogon hannun sa ganin lokaci na tafiya duk da ba wannan ce rana ta farko da yake zuwa ƙofar gidan ba,tun da aka bashi ita,bai samun ganin ta hakan ne ya sa ya ke ɗan duba a gogon sa idan lokacin da ya ɗiba bata fito ba ya tafiyar sa.Sai dai me yana cikin wannan tunanin na fitowar ta ta kawai ya ji saukar ruwa masu ɗumi da wari a jikin sa wanda suka ɓata masa farar shaddar sa dake saye a jikin sa wadda ta ƙara fito da kamalar sa da annurin malanta kar sa na cikakken a haluss Sunnah.Idanu ya zaro cikin tashin hankalin abun da yake ji a jikin sa kafin ya sauke idanun sa kan Nadiya dake riƙe da botiki a hannun ta tana huci hannun ta daɗe da Hancin ta saboda wani irin mugun wari da ya taso na ruwan lokaci ɗaya.Dariyar da ta ke ce da ita ce tana nuna sa ganin yadda ya zaro idanun sa kan ta.Idanun sa ne suka yi wani irin jaa na wannan cin mutun cin da tayi ma sa sai dai kuma a hakan bai ji wani abu daga son da yake mata ya ragu ba duk da ya san bata son shi yanzu dai dai rana ɗaya bai taɓa damuwa ba kasancewar ya san an riga ansaka ranar su ko tana so ko bata so sai an kai ta gidan sa an bashi sadaki kaɗai ya rage.Shi ya sa a kullum idan ya zo baya damuwa da rashin fitowar ta da yagama tsayuwar sa na lokacin da ya ɗiba sai ya tafiyar sa hankalin sa kwance. " Ai Indai baka da zuciya a ƙirjin ka,wallahi yanzu ka fara gani,ba dai kai naci ba ka nace sai Nadiya wallahi yanzu ka fara gani da irin wannan zan riƙa yi maka illa har ka janye da kan ka ba tare da ka wahalar da ni ba,Ka kalle kan ka da wata hula taka kamar ta sa wai kai ustaz kai daga nin kala ta ka san ba kalar a jin ka nake ba,na fi ƙarfin ka ko wanda yafi ka na fi ƙarfin shi,duka dangin ku babu aji na ,nace ma ka bana son ka,bana kaunar ka Ana dole ne mtsww ". Tana gama wannan furucin ta tofa ma sa miyau a fuska ta wuce tana harare harare ba tare da ta kalli su malan Abdul Basiɗ dake zaune a cikin yar ƙaramar rumfar tasu ta kara ba. Idanun sa sun rikiɗe sun ƙara yin wani irin jaa baƙin ciki kamar ya Fiddo da zuciyar Malam Sayyid.Sai dai shi tashi jarabawar kenan duk da ya ji zafin abinda tayi masa kuma ya tsinci kan shi a wani irin yana yi mara kyau hakan bai sa ya ji son ta ya ragu a zuciyar sa ba sai dai zantukan ta sun taɓa shi sosai sun zafafa zuciyar shi ta yanda yake jin kamar zata faso ƙirjin shi.Bai taɓa sanin ƙiyayyar da Nadiya ke masa ta kai haka ba.A she rashin fitowar ta ta maslaha ne a gare shi.Ashe zuciyar shi bata mashi adalci ba a chan baya ya saka wa zuciyar shi haƙuri sai dai a wannan karon da iyaye suka shiga ciki ya ji ba zai iya haƙura ba saboda Allah ya ke son ta wanda ita ta koya mishi soyayyar ta, itace wacce ta fara nuna masa alamar so tun bata da wayau har Allah ya sanya mishi ta ta, ta karɓe shi ashe haka so zai masa,ya zame ma sa ƙiyayya rana tsaka saboda yana talaka kuma malamin islamiyya,da ya sani da bai nemi Auren ta ba,ya haƙura kamar farko da ya sani da bai dawo ba.Wani Irin numfashi ya sauke yana bin ta da idanun sa da suka sauya yana ƙara mamakin abinda ya sa me shi lokaci ƙalilan wanda ya ɗauke shi a matsayin ƙasƙanci wanda bai taɓa haɗuwa da shi ba. A hankali ya shinshina rigar shi da ƙudaje suka fara bi sannan ya sauke numfashi yana girgiza kan shi rasa abinda zai yi hakan ya sa ya yi tsaye gurin.Malan Rabi'u ne ya taso da sauri bayan wucewar Nadiya ya riƙo hannun sa yana furta.. " Subhanah Sayyid,Ayi haƙuri kaji komai mai wucewa ne,kar ka damu in sha ALLAH zaka dara a nan gaba Allah yana kallon ka da zuciyar ka,kuma ya san irin taimakon da kake kokarin yi zai dafa maka ".Ajiyar zuciya Sayyid ya sauke wanda suke kira ya sayyadi sannan ya ɗan ƙaƙalo guntun murmushi yana furta. " Babu komai Baba,in Sha ALLAH haƙuri kam ya zama dole". " To yanzu ya za'ayi ko muje kan murtsatse ka wanke tufar ka a samo maka omo cikin gida ". malam Rabu'u ya faɗa cikin Tausayin sa da ƙara ganin ƙimar shi. " Aah Baba bari kawai na wuce gida dole kayan na buƙatar cirewa saboda ruwan najasa ne ba su da tsarki kuma an kusa sallah la'asar ". Sayyid ya furta fuskar shi na fitar da wani ɗan siririn murmushi wanda ke ƙara fitar da kamalar shi. Kamar yadda kuka sani dai Sayyid malamin su Najiba ne a islamiyya kuma tun tana yar ƙaramar Matashiyar ta ya nuna mata so suka fara soyayya daga baya ta guje shi da idanun ta suka buɗe. Sayyid Ahmad shine cikakken sunan sa shi shima ɗan gidan malammai ne iyayen sa cikakkun yan ahlussuna ne mahaifin sa shi ke da Islamiiyar ta su Nadiya haka ma rabi duka ya yan sa ne ke karantarwar a makarantar kamar Sayyid ɗin.Sannan iyayen sa ba wasu masu kuɗi ba ne sai dai suna da Rufin a sirin.Sayyid mutun ne mai kau da kai bashi da saurin fushi sai dai baya iya daukar wulaƙanci ko Najiba ma saboda son da yake mata ya sa yake ɗaga mata ƙafa.Malan Sayyid Cikakken baka no ne sai dai shima ba farar fata ba ce chocolate irin mai kyau ɗin nan,sannan kuma cikakken Namiji yana da tashi ƙirar gwargwado kamar ta Ibrahim na Raliya wanda kuma ƙawaye ne dama su biyun sai dai banbancin su Ibrahim baya ɗaukar raini kuma baya wani ɗaga ƙafa idan ya ga za,a raina ma sa da wayau shi ya sa Raliya ta ƙara samun mazauni a cikin zuciyar shi saboda babu ruwan ta hayaniya bata sha mata kai ba kamar ta su Najiba. Sallama suka yi da malam Rabu'u da Malam Abdul basiɗ wanda ke zaune kamar skeleton ya kasa motsawa sai ma zuba musu idanun shi da yayi yana jin zuciyar shi na wani irin harbawa babu babban baƙin cikin shi yar shi ta cikin shi take zuba irin wannan rashin mutuncin a gaban sa.A hankali zuciyar shi take masa wani irin zafi sai dai bai da wani kataɓus wanda yanzu lamarin na bashi tsoro shi kan shi ya fara fahimtar akwai wani lamari wanda Allah ne kaɗai ya bar wa kan sa sani.Kan shi ya saukar ƙasa bayan sunyi sallama da Sayyid ɗin wanda ya ƙara jin Tausayin shi da kaunar shi sun mamaye shi lokaci ɗaya. Numfasa wa malam Rabu'u yayi shima yana zama gurin tare da kallon yaran da suka yi cirko cirko da wasu daga jama'a yan gani da ido kafin ya ga sun fara wucewa daya bayan ɗaya ganin wanda aka yiwa ya nuna rashin damuwa har ya kama gaban shi.Wanda sun zata sai ya zabga mata mari a gurin. " Yaya Ya zamu yi lamarin nan yana ta ƙaratowa komai yana lalacewa,ka duba Nadiya yadda take zuba rashin mutunci a gaban mu,bata ko shakkar faɗan mu wai me yake faruwa ne,me muka aikata haka,wa yake ɓata tarbiyyar yaran nan ".? Malam Rabu'u ne yayi furucin zuciyar shi na suka.Duk da ya san cewa Akwai hannun Hafsatu a cikin lamarin amma ba su saurin yanke hukunci kai tsaye saboda rashin shaidar hakan. Numfashi malam Abdul Basiɗ ya sauke bayan gama sauraren ɗan uwan nasa inda a hankali ya furta " Ina son wannan haɗin da Sayyid mutumin kirki ne zai iya tanƙwara Nadiya,shi ya sa na yi murna sosai da zuwan sa a lokacin da muke tsananin buƙatar sa,ina ganin tabbacin zata shiryu,Duk da bani da wani ƙarfin zuciyar da zan tunkari Hafsatu da zancen kai tsaye amma tabbas,zan tsaya tsayin daka Nadiya ta same shi dan Ni shi kaɗai nake tunanin zai iya riƙe Nadiya da rawar kan ta shi ne mai mata son gaskiya,ina baƙin cikin wannan yanayi da muka samu kan mu,amma In sha ALLAH komai zai wuce koma me nene zai buɗe wata rana,kuma tabbas Hafsatu zata yi nadama domin tana da kashi saba'in a cikin lalacewar ya yan mu ".. " Allah ya sa mu dace yanzu bari muyi magana da malam Adamu a cigaba da abinda ake yi,kaga malam Ahmad ma nata ƙoƙari ". Malan Rabu'u ya furta a hankali. " Amin ". Malam Abdul basiɗ ya furta yana sauke ajiyar zuciya. Fira suka fara taɓawa a hankali ta yaran nasu da basu iya yin wata magana mai nauyi ko basu kariya.Har rumfar ta fara cika da mutane irin su. A chan cikin gida kuwa Nadiya haka ta faɗa tana jan mugun tsaki tana zagin Sayyid wanda ta kasa zagin shi gaban sa duk da yadda ta tafi da kwandon zagin na ta ta sauke masa sai ta samu kan ta da kasawa Dan ko zantukkan cin fuska da take da su kasa sauke masa su tayi duka. Da sauri ta faɗa ɗakin tana gunguni bayan wanke hannun na ta da tayi tana cigaba da zagin Sayyid ɗin zuciyar ta na tafarfasa kafin kuma a hankali ta ɓarke da dariya tuno yanayin fuskar sa da yadda mutane suke kallon sa suna doɗar hanci saboda yadda ruwan yake da mugun wari kamar kwata. " Aiki yayi kyau kenan Nadiya,wannan irin dariya haka kamar an daura Auren ku da Tanimu ". Ta kai ƙarshen zancen tana sakin guntuwar dariya. Mama Hafsatu ce ke zancen tana kallon yar ta ta dake ta wasar baki dariya harda tintsirewa tana kai wa ƙasa. Nadiya kuwa wani irin farin ciki ne ke ratsa ta kafin a hankali ta furta. " Wallahi ko Umma na aiki ya cika,kin gan shi kuwa yadda ruwan nan ya shige sa take ya baɗe guri da wari,na san zuwa anjima zaki ji an fa sa zancen Auren,An tsayar da Tanim dole ". Mama Hafsafu murmushi kawai tayi tana bin Nadiya da kallo tana furta " ƙwarai ko yi dariyar ki son ranki babu ke ba Auren talaka sai dai idan ana yi a lahira,dan ni kam ban haifi matar talaka ba Auren ki da Tanim kamar an riga an gama,Dole ki Aure shi tun da shine zaɓin ki,ke koda bakya son shi haka zamu karɓe shi mu yagi Naira son ran mu ." Kai Nadiya ta gyaɗa kafin a hankali suka taɓe da mahaifiyar ta ta tana sakin murmushi tare da juya idanun ta na zancen mahaifiyar ta da ta ce bata haifi matar talaka ba. Hmm Nadiya tamu 😒🧐 ke da maman nan taki zaku kunce mini notikan Kai 🧐 Najiba da ta fito yanzu bayan ta gama waya da Jamil ɗin ta fuskar ta na fitar da kyakkyawan murmushin ta sai dai abinda taji ne ya tsaya mata arai abinda Nadiya ta yi bata ji daɗin shi

Chapter 7 of 39