ya sa bai iya ɗaga ƙara ba kamar yadda aka ce masa ya san ko haka aka tsaya haƙƙin Nadiya ya fita,Anan matar ta sake shi sannan ya suka rabu a kotun kowa ya kama gaban sa.Duk wannan abun da ya faru bai wani dame sa sosai ba irin Rayuwar da Jazlan kan iya shiga a yanzu tare da Nadiya,Bai yi zaton abun da yake aikawa zai iya dawowa gare shi cikin gaggawa ba ba tare da ya shiryu ba,yaso ya shiryu sai dai yayi jinkiri yau gashi yana girban abinda ya shuka da hannun sa.Koda ya koma masaukin sa da ƙyar ya iya bacci ga barazanar da ɗai daga cikin yan ƙungiyar su ke masa ga mugun ciwon kan dake damun sa da kasala sai da ya kora wasu kwayoyi sannan ya samu bacci ya kwashe sa da ƙyar cikin wata irin nadama da ke ta so masa ba tare da ya shirya ma zuwan ta ba a yanzu.
Kwanan shi uku ya ga alamar ciwon na son cin ƙarfin shi ya dawo gida Nigeria a hargitse domin duk ya fara fita hayyacin sa ya yi zaton ya samu Hutu sai dai ya gagara ga ciwo ga fargaba kwanan shida ya baro ƙasar.
Da saukar sa babu inda ya fara yin tsinke face a sibiti, sai dai bai same su chan ba saboda an sallami Nadiya ganin jikin ta yayi ƙarfi komai ya yi normal sai abun da ba,a rasa ba ta samu lafiya gwargwado hawan jinin ne ya sauka shima.wanda aka rubuta mata drugs nata da zata riƙa amfani dasu har ya sauka gaba ɗaya.Da wanda Jazlan zai riƙa sha shima na mura da ta kame sa.
Kwatsam Dr Abida dake ta aiki ta samu kira inda aka sanar mata da shi ɗin ne saboda kowa yan zu ya san yaron ta ne.
Da sauri ta iso kamar zata harɗe saboda yadda ta matsu ta samu ganin sa saboda yadda su kayi neman sa domin bata san yayi tafiya ba wanda ta lura da alama itama uwar ɗakin sa bata san inda yake ba itama,duk inda suka saka ran ganin sa basu gani ba,sunyi neman shi a lokacin da za,a sallami Nadiya ba su same shi ba wanda har hankalin su ya fara tashi abun ka ga jini sun tsorata matiƙa sai dai sun bar wa Allah ikon sa.Ganin shi zaune duk ya fita hayyacin sa ya sanya jikin ta ƙara yin sanyi wasu irin hawaye masu zafi na cika mata ido.
Zama tayi sannan ta furta " Ina ka shige "?
Bai tanka mata ba sai ma jefa mata tambaya kan sa a ƙasa " Ina Matata da ɗana"? Tausayin shine ya ƙara kamata tana ji kamar kukan da take riƙewa ya zubo mata na tausayin sa.
" Ina ɗan ka dai kaman ta babu komai tsakanin ka da Nadiya a yanzu ".Tayi furucin tana fara yin yan rubuce rubuce.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya furta " Na yi wata tafiya ne ta gaggawa ".
Kai ta jinjina masa.
Bayan ta gama yan rubuce rubucen da take yi ne ta juyo a hankali tace " Tun yaushe ka fara wannan rashin lafiyar ".?
" Tun Last three weeks ".
Ya bata amsa a tsanake yanayi yana satar kallon ta.Dan yayi zaton sai ta ƙure shi da wace irin tafiya ce haka.Sai kuma mamakin ya akayi ta fahimci bai da lafiya.
_Haba dai ai uwa likita ce mai zaman kan ta,ko wane yanayi zata iya fahimta ga ya yan ta idan har ta kasance mai kula.Koda yaushe ke uwa ki zamo mai kula da duk yanayin da ya'yan ki suke ciki,ki kasance mai gane damuwar su._
*ALLAH YA SAKA MA IYAYEN MU DA GIDAN ALJANNA.🤲*
Kai ta jinjina masa ta sake yin wani rubutu.Sannan ta ɗago ta ƙara yi masa wasu tambayoyin game da fever da yanayin da yake jin jikin sa.
Haka ya dinga bata amsa sai dai ita duk amsar da zai bata sai ƙirjin ta ya buga tana tsintar kan ta cikin fargaba da Tashin hankali haka kawai.
Tana gama jin sauran bayan nan na sa ta ta miƙe ta ɗebi jinin sa sannan ta fice daga office ɗin.Da fitar ta bata zame ko ina ba sai Lab, tana bada test ɗin ta samu guri ta zauna, bata damu da yadda suke ta kallon ba, kasancewar ba ko ina take shiga idan ba duba yanayin aikin su ba, yau ko gata har da samun guri ta zauna,tana zama ta rafka tagumi wanda daganin ta kasan tana cikin damuwa matuƙa dan hakan ya bayyana akan fuskar ta.
Ta ɗauki kusan mintuna goma domin general test ne ta saka a ka yi mishi dan bata son ta fitar da zargin ta fili yadda zuciyar ta ke bugawa ita kaɗai ta san yanayin da take jin ta.
Tana zaune aka kawo result ɗin kasancewar asibitin suna da wadatattun kayan aiki na na'ura shi yasa take ake bada result bare ma ita da take shugaba mai Asibiti kuma Babbar likita.
Jikin ta har tsuma yake yi wurin buɗe takardar musamman da ta ga suna miƙa mata suka fara shigewa a cikin ɗai ɗai kun offices nasu dake cikin gurin musamman wayen da suka yi awon duk sun ɓace ɓatt jikin ta ne yayi sanyi ƙalau tun kafin ta kai ga buɗe sakamakon.
" Dr da kin bari ki samu natsuwa sai ki zauna ki duba da kyau naga kamar bakya cikin natsuwar ki,babu wani abu komai normal ". Shugaban lab ɗin da ya zauna yanzu ɗan nesa da ita yayi furucin ganin kamar bata cikin natsuwar ta.
Murmushi ta ƙaƙalo tana ƙoƙarin ƙarasa buɗe ta kardar sai kuma ta cukuikuye ta ta gyaɗa masa kai ta fice daga office ɗin gaba ɗaya.
Tun shigowar ta ya zuba mata ido dama jiran Dawowar ta yake yi yana son zuwa gidan su Nadiya ya ga Jazlan amma bai san ta ina zai fara zuwa ba domin ya san ko ya je ba barin sa ganin ɗan sa Nadiya zata yi ba dan haka yake son neman alfarmar ta,ta masa jagora ya ga Jazlan ko hankalin sa zai kwanta,baya jin yau ɗin nan zai iya kwanciya bacci ba tare da ya ga fuskar sa ba.
Gurin zaman ta ta nufa ba tare da ta furta masa ƙala ba sai dai ta kasa yin zaman sai ma warware ta kardar da tayi tana zuba mata idanu kafin kuma ta haɗiye wani abu mai ɗaci da ƙuna a cikin zuciyar ta,tare da ƙoƙarin haɗiye hawayen ta da suke neman nuna abun da ke cikin zuciyar ta na zallar damuwa da tashin hankali cike da Tausayin Ɗan ta da take mugun so a duk cikin ya yan ta sai gashi kuma ƙaddara bata bar mata shi ba.
Zaune takai daɓaass kan kujerar tana sharce zufan da ya keto mata cikin wani sabon tashin hankali tsoron ta Ɗaya Nadiya Tana fatan Allah ya sa a gurin ta ba haka bane.
Kan ta ta ɗaga da ƙyar ta furta " Kayi haƙuri bawa bai wuce ƙadddarar sa,sannan wannan shine sakamakon ka na abun da ka aikata a baya ina fatan ya zamo maka izina ya zamo sanadin gyaruwar ka ko shiriyar ka,Abun da ya same ka Ba,a saka masa damuwa domin dubbanin mutane suna rayuwa a tattare dashi,idan har ka natsu zaka samu rayuwa mai kyau ''.Ta kai ƙarshen zancen tana sauke ajiyar zuciya.
Tun fara zancen nata ya ƙara zuba mata idanun sa ƙirjin sa na wani irin bugu ba gaira babu dalili ya rasa ta inda ta dosa.
" Kasan cewa kana ɗauke da Cuta mai karya garkuwar jiki kuma ta kusan wata bakwai a jikin ka,shine dalilin da ya sa kake ta ƙarewa haka,ga kuma rashin kuzari da fever,duk haka ya faru ne saboda rashin shan magani ba cutar ".
Yadda ya zuba mata idanu haka ya kasa ɗauke su miyan bakin sa sun ƙafe ƙaff duk wani sauran farin ciki na sa ya gushe kiɗima ta same shi,ya rasa sense ɗin sa na wucin gadi domin bai ma san yadda aka yi ya tsinci kan shi a tsaye ba idanun sa sunyi jajir kamar zasu yi aman wuta.Wannan wace irin Masifa ce daga wannan sai wannan me yake faruwa da rayuwar sa ko dai ta zo ƙarshe shi ya sa komai yake juya masa baya zuciyar sa ta raya masa haka a razane.
" Relax Son " ta furta cikin ƙarfin hali tana mai dashi zaune duk da bata iya ko ingiza sa sai dai yanayin da yake ciki hakan ya sa ta samu nasara ya koma.
Zama yayi yana yin ƙasa da kan sa hawayen da yake ta riƙo suka silalo masa masu zafi tabbas duk abinda mahaifiyar sa ta faɗa haka ne sakamakon sa kenan ba tun yau ba ya san masu aikata irin zunubansu a haka suke ƙarewa sakamakon su kenan na Duniya kafin ma aje gaban Ubangiji,yau gashi ya faru kan sa wai shi ke ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki bai sani,to a ina ya ɗauke ta ya san tabbas yana mu'amala da mata daban daban,haka mazan na ƙungiyar su duk da bai matse sosai a waccan harkar ba,Kuma ya san sai an yi kowane irin gwaje gwaje a tsakanin su wanann yana ɗai daga cikin ƙaidodin su ya san babu mai cutar a tsakanin su, Nadiya ce,ɗayar zuciyar sa ta basa amsa kan sa ya girgiza da sauri,yana ƙarya ta kan sa,Haka ma ta ƙara furta masa SHANTY kan sa ya girgiza anan ma kamar wani zautacce da baya hayyacin sa.Sai kuma tunanin Baturiyar nan Tsohuwar matar sa da ta yaudare sa.
Adai dai nan duk wani tunanin sa ya tsaya chakk inda jikin sa ya yi wani irin sanyi.
Sai kuma ya fashe da kuka domin ya san tabbas itace domin riƙaƙƙar yar bariki ce ta bugawa a jarida ya san tabbas itace ta san tana da cutar ta ɓoye masa dama akwai mugun nufi a ranta game dashi kudin sa take son ta wawu sa wanda ta kuma yi nasara Dan abun da yake dashi anan Nigeria bai da wani yawa sai kuma shagu nan su na Dubai Mallakin mahaifin sa wanda duk shi ya ke ɗan kula dasu.
Ita kan ta karfin hali take yi ji take kamar ta saka kukan kan tafukan hannayen ta da take share masa hawayen sa ya kifa fuskar sa yana ta dirzar kuka kamar wanda aka ce ma ga mutuwar sa nan.Ya tsinci kan sa a tashin hankali matuƙa ga wata irin nadama na mamaye illahirin jikin sa.
Sai da yayi mai isar sa bata dakatar dashi ba sannan ya saurara yana ta faman sauke Ajiyar zuciya kamar wanda ya rasa wani abu na sa mai mahimmanci,kukan zuci ya koma yi a raunane.
Nasiha ta ƙara yi masa tare da ƙara nusar da shi illar abun da ya aikata a baya wanda babu wanda bata sani ba,kuma ta san cewa tabbas akwai manaƙisar abokiyar zaman ta,cikin kaso goma tana da kaso biyar a ciki,itama kan ta ta san tana da nata domin zata iya ɗaukar kaso ɗaya ciki duk da ta san wani abu ba,a cikin hayyacin ta ta yi sa ba.
Drugs ta ɗaura sa a kai tare da sanar dashi ƙaidar da masu lalurar suke bi na ziyarar a sibiti duk bayan mako ɗaya tare da shan magani akan lokaci kuma akan ƙa'ida.
Ganin ya fara samun natsuwa ne sannan ta sanar masa da gobe ne ake yin sunan Jazlan dan tayi zuwa biyu gidan itama duk da kunyar da take ji wanda ta samu ta ɗan rage mata bayan ta bawa Nadiya haƙurin komai da ya faru tare da ƙara nusar da ita Mafi yawan halayen sa Hajy Jamila ce ta ta,az zara su ko ince itace sila a haka ta samu sassaucin Damuwar ta.Ga kuma uwa uba duk wani abu da suka san uba nayi Wa Ɗan sa Ita da yan uwan sa sun yi shi hatta ragon da za,a yanka guda biyu duk sun ajiye musu.Sai dai fargabatar itace har yanzu iyayen maza basu san abun da ke faruwa ba da mahaifiyar Nadiya ɗin dan komai a noƙe noƙe suke yin shi har su Najiba ɗin bata san dalili ba.Amma ko mene ne zata sanar musu da kan ta, Dan ko tafiyar da yayi ita ta ɓoye musu inda ta ce musu yayi tafiya ba tare da ta san da tafiyar ce yayi ba ko ko ba ita ba ce,kuma haka kawai yanzu ta ke jin zata iya fuskan tar su.
A tare suka fito daga asibitin bayan ta karɓo masa drugs ɗin sa.
Kasancewar magriba tayi hakan ya sa suka yi sallolin su shi ya wuce masallaci ita kuma tayi a office.Sannan suka fice a tare.
Ba su zame ko ina ba sai gidan Su Nadiya.
Shi ya tuƙa motar duk da bai da wani kuzari a jikin sa ga zuciyar sa dake a cunkushe da damuwa.
Da Sallama ta shiga gidan dai dai lokacin da Najiba ke sanar da iyayen na ta abun da ke faruwa a tsakanin ta da Tanim na mutuwar Auren su,saboda sun tsare ta ta kira sa maganar zanen sunan su ji inda yake son ayi shi, sai dai bata faɗa musu irin uƙubar da ta sha ba ta ɓoye komai dan mutun cin Dr Abida kawai.
Dukkanin su shiru suka yi cikin jimamin wannan lamari Mama Hafsatu kuwa Kamar ta ce yihuu saboda yadda zancen ya ratsa Kunnuwan ta ba haka ta so ba sai lokacin da zasu ci arziki sannan komai zai hargitse, ta ya aka yi Nadiya ta yarda hakan ya faru kenan duk shige da ficen ta ya tafi a banza.Tuno da saki uku ne ya ƙara dagula mata lissafi inda ta miƙe tsammmm ta bar tsakar gidan da suka shimfiɗa ƙatuwar tabarma saboda zafin da aka fara ga kuma sauƙaka ma Jama'a da ke zuwa Barka saboda ɗakin Mama Hafsatu dake Baya ɗaukar su.Sauƙin ta ma Nadiya tace bata taron suna wanda ba haka Mama Hafsatu ta so ba, ta so a tara jama'a kowa ya san yar ta ta haifi ɗan arziki dan duk da haka duk wanda ya zo Barka sai ta kai shi ya ga uban kayan da aka zuba ma Jazlan kamar shago da na ta Itama mai jegon.Haka ta so tayi ranar suna.Kuma tabbas take zancen ya karaɗe unguwa irin kayan da aka zuba ma Nadiya wayen da babu irin macen da aka zuba ma su gaba ɗaya a faɗin unguwar ta su saboda yadda unguwar take ta talakawa kafin kaga abun da yake an zuba kuɗi a cikin shi sai kaɗan.Take kuwa Mutanen unguwa suka yi ta shige da fice giye giye kamar masu ganin lefe.
Kukan da ta ɓarke da shi ne ya ƙara sanya jikin Dr Abida yin sanyi ga wani irin Tausayin Nadiya da kaunar ta musamman da ta ji ta ɓoye komai dake faruwa Dan tayi binciken zaman na su ta gano zaman ƙunci ne tayi a tare dashi tun bayan Kaita gidan.
Su Malam Rabu'u da Malam Abdulbasiɗ kuwa Jikin su yayi sanyi suma,domin yanzu kai tsaye ta nuna bata son ganin shi dan sun ce zasu neme sa suji dalilin saki irin wannan idan har laifin ta ne su san irin matakin da zasu ɗauka.Jazlan ne dake hannun Najiba dake ta nishi cikin ya tsufa yau ko gobe.Yana tsala kuka ta fito da shi tana ɗaura ma Nadiya shi a kan jikin ta tare da girgiza mata kai saboda akwai ɗan hasken Ya gaza (Joni) da ya haske gidan.
Ɗagowar da zata yi ce idanun ta suka sauka akan Dr Abida dake tsaye idanun ta sun sauya ba haka ta so ba ta so a ce ita ta sanar musu ta nemi gafarar su amma a yanzu ji take kamar ta juya bazata iya fuskan tar su ba,saboda yadda wata irin kunya ta mamaye ta.
" Barka da zuwa Momy ".
Najiba tayi furucin zuwa ga Dr Abida cikin girmama ta.
Firgigit Dr Abida ta motsa tana kallon Najiba da tayi furucin." Yawwa ta amsa mata, tare da ɗora mata " Ya tsufa Najiba,Allah ya fitar lafiya ".
" Amin " Najiba ta furta cikin jin nauyi tana kama ɗakin Mama Hasiya kasancewar ta dawo gida haihuwa saboda yanayin unguwar ta su dake da nisa sai ya maido da ita gida, Dan nan ta zaɓa ba gidan su ba.
Sai a lokacin duk suka lura da ita Takawa tayi izuwa gare su tana ƙaƙalo murmushi tare da gaisawa da su tana ƙara yi ma Nadiya ya jiki wadda tayi shiru yanzu sai nono da take bawa jazlan ta cikin hijab saboda kunyar su Baba da take ji shi ya sa take ajiye hijab kusa da ita dan irin haka.
Tana zama kuwa Bayan sun gama gaisawa ta basu haƙuri tare da nanata musu zancen Nadiya kasancewar ta ji komai yanzu.Kuma ta roƙi alfarmar kar su raba Tanim da yaron sa ta roƙe su.Babu wanda ya iya cewa komai dukkanin su har ta gama maganar ta.Anan ta sanar musu tare take da Tanim ɗin bari ta shigo tare da shi.
Tanim dake zaure shima fuska tayi masa jaa Dan yana jin duk abinda ya faru saboda ya biyo bayan Mahaifiyar sa da ta gama ƙare masa kallo ganin shi a cikin zauren alhali kuma a cikin mota ta bar shi da zummar zata kira shi daga baya.
Da sallama suka shiga sai dai ya kasa haɗa ido da kowa a cikin su sai satar kallon Nadiya da yake yi wadda tun kallon farko da tayi mishi ta ɗauke idanun ta kamar bata ga wata halitta mai kama da irin sa ba tamkar bata taɓa sanin sa ba.
Gaida su Malam Rabu'u yayi da mama Hafsatu dake zaune a wurin wadda ta dawo yanzu tana jin ta tamkar a ƙaya cike da haushin su, sai Auna ma Tanim harara take yi shida uwar sa mugun zafin sakin nan take ji dama ana bada wata fatawa akan saki uku da ta mayar da Nadiya ko ta ƙarfin sihiri ne sai dai babu hakan.Guiwoyin sa ya sanya ƙasa Dan yama kasa zama bare ya bawa kan sa mazauni.
Duk a tsantsance yake jin sauƙin ta ma Allah ya taimake shi NADIYA bata sanar dasu komai ba a yadda yaji komai kuma yaji daɗin hakan da yana da damar da zai gode mata kan hakan da ya gode mata matuƙa bai taɓa jin abinda aka yi masa wanda yayi masa daɗi kamar yau ba, Dan ya san tabbas da ace ta faɗi komai ko mahaifiyar sa sai ta tsane sa Bama iyayen na sa ba,mummunar ɗabi'ar da ya jefa kan sa bata re da ya sani ba yafi ƙyama ta tar sau dubu akan komai da ya aikata a baya,Kuma da ya tuna baiyi wani zurfi a ciki ba sai ya gode ma Allah.
Nasiha Malam Abdul basiɗ ya fara yi masa akan yadda Ubangiji ya tsani irin wannan sakin da rashin kyaun sa.Tare da ƙara nusar da shi haƙuri da juriya,da yarda da ƙaddara.Dan ganin yake yi kamar rashin haƙuri ne ya sanya sa yin sakin haka.Kuma abinda ɓacin rai zai iya kawo wa Hakuri shine maganin sa.Har ya kawo masa hadisai da dama masu magana akan masu haƙuri da rashin nuna ɓacin ran su akan komai,tare da ƙara lurarar dashi mata rabi muke ba mu cika ba,dole sai ana yi ana haƙuri damu da bamu kulawa domin da rabin awaza aka yi mu,sannan muna da ƙarar ƙwaƙwalwa,wadda bata iya tunani mai yawa, ba irin ta su ba.Da haka da yayi masa nasihohi masu shiga jiki wayen da suka ƙara sanya jikina yin sanyi.MATA MUNA DA RAUNI TABBAS ,ALLAH MUNA ROƘON KA KASA KAR RAUNIN MU YA ZAMO KASAWAR MU,KO ƁACEWAR MU🤲.Haka ma nadiya jikinta yayi mugun sanyi sai dai bata ji Tausayin sa ko ɗar ba a cikin zuciyar ta.
Haka ma Malam Rabu'u ya ɗora yi masa Nasiha mai shiga jiki.
Jiki a sanyaye bayan gama sauraren su Yayi godiya,tare da sanar musu shi bai san ya aikata hakan ba bai tunanin yana cikin hankalin sa,koda abubuwan sakin ya faru,kuma yanzu haka yayi nadama matuƙa dan da ace ba saki uku bane da bazai bar nan ba sai tare da matar sa.
Jin wannan furuci sai da Dr Abida ta zubaa masa ido saboda taga alamar yama manta cewa yana ɗauke da cutar da koda da sauran igigiyoyin zaman su ba zai yuyu ba,idan ma zargin Tanko hasashen ta gaskiya ne, bata tunanin Nadiya na da ita yadda take kallon ta garass kuma idan tana da ita da tuni ta nuna kamar dai shi yanzu.
Amma ko mene ne zata ɗauki jinin Nadiya ɗin kamar yadda ta zo da sample bottle Dan tantance wa.
Maganar sa daya fara ce murya na gargada cikin alamun kuka yake neman gafarar Nadiya yakai durƙushe a gaban ta ga jazlan ruƙunƙune ahannun ta yana ta buɗar ido ya sha ya ƙoshi ko kallon sa batayi ba dan wata irin tsanar sa ce ke ƙara mamaye illahirin zuciyar ta da gangar jikin ta ji take kamar ta cilla masa Jazlan ɗin ma su ɓace dukan su daga Rayuwar ta mutumen da ya tozarta rayuwar ta ya bar mata mugun dafi ya so halaka ta ya Kaita ga bala'i Bama na duniya ba Na lahira ta ya zata yafe masa.Yi tayi kamar bata da Kunnuwan sauraren sa dan shiru tayi ta haɗe rai tana jin sa yana roƙon ta gafara tare da son ta bashi Jazlan ɗin.Sai dai duk wani shesshekar kukan sa da zata ji wani irin sanyi take ji aranta babu alamar Tausayin sa ko ɗigo shi ko nadama ce zalla ke ɗawainiya dashi ga wata irin soyayyar su da take mamaye masa zuciya,ga Tausayin Nadiya ɗin na Abubuwan da yayi ta aikatawa a gare ta, ta re da cin fuska da su zalunci kuma haka ta haƙura ta zauna dashi sai gashi da kansa ya saka maciji mai mugun dafi ya cije sa ya halaka rayuwar da take saura a a gare sa yanzu dan tun jin cutar da yake ɗauke da ita ya san cewa rayuwar shi ta ƙare sai dai yana fatan ya ƙara sa sauran da aikata Alkhairii da komawa ga Ubangiji tare da yi masa biyayya kamar yadda Mahaifiyar da kuma Malam Rabu'u yayi masa Nasiha yanzu ta jin tsoron Allah da gyara hallayar sa da barin duk abun da Allah ya haramta.
Jikin kowa yayi sanyi ganin yadda ya fashe da kuka amma Nadiya sai ma miƙewa tayi da Ɗan ta tabar gurin hawayen ta sun ƙafe ƙaff bata jin zata bari yaga wani alama na tausayin sa a zuciyar ta.Wanda bata ma tunanin yanzu tana dashi na sa.
Da ido duk suka bita inda hakan ya ƙara tabbatar ma su Malam Rabu'u cewa akwai Babban abun da ya aikata mata ko kuma yayi mata wanda ta kasa mantawa kuma sun shaida ya faru ganin yadda yake kuka haka cike da nadama da ƙuncin zuciya.Sai dai basu matsa da son jin komai ba sai ma tuna cewa Mahaifiyar shi tace laifin shi ne amma komai ya wuce tun da Aure kam ya riga ya mutu babu kome, Dan bata san yadda zata fara ce wa iyayen na NADIYA ɗan ta har da mata yake kai mata cikin gida ba yake kwana da su har cikin ɗakin yar su ba.Ina abun bazai bada ma,ana ba ta san zasu tsane shi matuƙa,kuma suna iya yanke alaƙar dake tsakanin su da Jazlan wanda suka kallo ita dashi amatsayin sanyin idanun su.
Miƙewa yayi bayan wucewar ta ya bar gurin bata re da ya iya yiwa kowa magana ba.
Itama Dr. Abida miƙewa tayi shaff shaff tana ƙara basu haƙuri da roƙon su su shawo kan Nadiya ko zata bari ya ga ɗan sa domin ta san shine kawai ya rage masa abun farin ciki a yanzu,kuma bata ji komai ba akan abun da Nadiya tayi duk da ta ji babu daɗi a gaban ta ɗan ta na dar-zar kuka kamar mace wanda ta kan iya cewa inban da dazu bata ga kukan sa ba sai na yarinta irin haka dai.Ta san dalilin Nadiya mai karfi ne shi ya sa ta kasa iya furta komai har ta miƙe ta bar musu wurin.
Maganar Awon da zata yi ma Nadiya ta sanar musu inda suka amince ba tare da sun san abinda Zatayi da jinin ba ta dai ce musu Aune Aune ne zata yi mata na sabon haihuwa da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 39