Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
basu lura dashi ba har ya gama tsayin sa ya wuce. Dr Abida kuwa tana shiga a lokacin Alhaji Abdulkarim shima ya gama shirin sa tsaf na fita ta fashe masa da kuka.Cikin tashin hankali ya tambaye ta abun da ke faruwa bata yi ƙasa a gwuiwa ba ta zayyane masa komai da hukuncin da ta yanke. Shi kan shi jikin shi yayi sanyi a hankali ya furta " Allah duk abinda ka yi akan bawan ka Dai dai ne,muna godiya,Allah ka bamu ikon riƙo da ƙaddara mai kyau ko mara kyau ka bamu ikon cinye jarabawar mu ". "Amin". Dr. Abida ta amsa masa hawaye na cigaba da kwaranya akan fuskar ta. " Hakan da kika yi shine dai dai Tun da kince kin hango natsuwa a tattare da yarinyar da nadama, haɗin shi yafi dacewa Gara su zauna su riƙi ɗan su,Idan har wanchan Mahaifiyar shi ta bada shi in case ko bamu ba yana da mai riƙa masa dan bana tunanin su cigaba da riƙe Jazlan saboda itama dole zata yi wani Aure,kuma ba kowane namiji yake son a je masa da ya yan wani a gida ba sai yan kaɗan Dan haka Allah ya san ya Alkhairi ya saukar da ita lafiya,in sha ALLAH zamu je ga iyayen ta idan na samu lokaci ''. Murmushi Dr Abida ta yi sai yanzu ta ji sanyi a ranta tare da wani irin zafi a lokaci ɗaya na zancen hasken rayuwar su Jazlan da yayi wanda shima ta san sai yaji babu daɗi saboda yadda Allah ya ɗaura musu son yaron ganin da yayi masa bai wuce uku ba amma ya shiga ran sa sosai,kuma ya so su Malam Rabu'u su basu shi su cigaba da bashi madara kasancewar ance yafi shan madarar amma suka nuna masa kai tsaye Bazasu raba ta da ɗan ta ba wanda ya san shima son kai ne kawai zai yi inya yi hakan.Sai dai a hakan suke kula dashi ana ta jibge masa komai na buƙata babu abinda ya rasa shida mahaifiyar sa da take cin albarkacin sa domin ita kan ta siyayya ake mata bata wasa ba. Haka ma Najiba Zehra babu abinda ta take nema saboda shima Jamil arziki ya buɗe sai fankama akeyi sai dai kasancewar yana da hankali bai bari kuɗin da aka bashi sun tarwatse Aban za ba sai ya buɗe ƙaton provision store da wani store ɗin na kayan sakawa na mata da yara.Cikin ikon ALLAH kuma komai yana tafiyar masa yadda ya dace.Harda mota sai da ya siya yar miliyoya ta hawa da kuma wayen da za,a riƙa yi masa haya a direban ci. Alhaji Abdulkarim ficewa yayi bayan ya gaisa da Shanty Dake Zaune zugumm bayan ta gama karyawa suna ɗan taɓa fira ita da Sahiba dake jan ta da firar cikin tausayi ta Itakuwa tana amsa mata kamar ta bata so saboda yanzu ta kasa sakewa ga kunya ga raɗaɗin da ke zuciyar ta domin sai yanzu ta tuna yadda ta shigo falon ta tashi zube ma Sahiba kwandon rigimar ta. Dan haka take ɗan jin kunyar ta tare da duka mutanen gidan.Har Alhaji Abdulkarim ya zo ya gaisa da ita bata wani sake ba dan bata yi zaton ta samu tarba mai kyau ba a gare su ba. Itama Dr.Abida wadda ta fito yanzu dan zuwa da Shanty a sibiti Murmushi tayi ganin ta kasa sakewa.Sannan ta ce su tashi suje asibiti kowa motar sa ya hau itace baya sannan suka fice. Bayan Auna ta da ƙara tabbatar wa aka bata magani mai kyau tare da wanda zai bawa abun cikin ta kariya da kuma ƙara masa lafiya sannan suka yi sallama da Dr Abida ɗin tana ƙara rarrashin ta Dan ji take kamar Sahiba ce tun da zata yi same age da Sahiba tana kwatanta idan ta ta ce ta kasance hakan. *** Ina labarin ya Sayyid.??? *Tun bayan Auren Nadiya,da aka ɗaura masa Auren sa yake saka ran dawowar Nadiya a gare sa,Saboda yadda jikin shi ke bashi ba daɗewa zata yi gidan ba saboda sun san waye mijin na ta,bai da halaye masu kyau,shi ya sa akullum cikin yi mata Addu,a yake ta fatan Alkhairi, sai dai shiru har ta share watannin da ya ɗibar mata dan alissafe yake duk da wulaƙanci da tayi masa amma bai ji son ta ya ragu a ran sa ba,duk da itama matar sa yana son ta ayanzu gwargwado amma ya rasa dalilin da ya sa ya kasa cire Nadiya aransa,Ga wani irin Tausayin ta da ke nanaƙe dashi domin yana da labarin komai da ke faruwa a gidan na ta a farko a gurin mai aikin da yake kai mata a gidan,Sai kuma gashi kwatsam ya ji ta fito a gidan su ma yaji zancen yaje gaida mahaifiyar sa suna maganar ana Faɗar haƙƙin sa ne ya farmata tare da na mahaifiyar sa da mazan da ta yaudara gashi nan kwaɗayin ta yakai ta domin sun san shi ya ja mahaifiyar ta gashi an sakar mata ya tana gadon asibiti gadon ma na naƙuda gado mafi haɗari da tsoro. A lokacin da yaji zancen ya shiga farin ciki matuƙa wanda bai san yadda zai kwatanta ta shi ba,wanda har matar shi da ke jego itama sai da ta fahimci haka har take tambayar shi bai ji ɗar ba ya sanar mata ta taya shi farin ciki itama saboda ta san yadda yake zancen Nadiya ɗin kuma sai da ya roƙe ta yafiya a duk abinda zata ga yana yi,kuma ta fahimce sa sai take ƙoƙarin ganin yayi farin ciki bata taɓa nuna masa taji zafi ba idan yana zancen Nadiya akusa da ita,idan yana waya da mai kawo masa rahoto.Hakan kuma sai ya ƙara mataa daraja da ƙima a idon sa dan ta fahimce sa sosai. Ya yanke hukuncin komawa gare ta ko Allah zai sa ya dace. *** Zaune take shiru ta saka waya agaban ta tana kallo bayan ta gama bawa Jazlan Nono yayi bacci da ƙyar saboda yau rigima yake ji ko madarar yaƙi sha ga Zehra ma Tana taya sa sai duk suke cikin rashin natsuwa kafin komai ya dai dai ta yaran suyi bacci. Kallon ñumban ta ƙara yi tana sakin Numfashi tare da ajiyar zuciya bin umurnin zuciyar ta tayi bayan tuno da zancen sa a lokacin da yake cewa ta ajiye ñumban zata mata amfani wata rana a duk lokacin da take neman sa zata same sa,kuma zai taimaka mata. Shiru tayi tana ƙara tunanin rayuwa ashe zata ga wannan rana a rayuwar ta bata taɓa hangowa ko hasashen haka ba Amma yau gata gaban iyayen ta da jinjirin ɗan da ta ke mugun so kuma take mugun tsanar mahaifin sa,bata jin a yanzu tana da babban maƙiyi kamar sa duk ta tuno da illar da yayi wa rayuwar ta sai ta koka,kuka marar iyaka. A jiyar numfashi ta ƙara yi kafin hannun ta ya danna call.Kiran har ya fara ringing ta yanke da sauri ƙirjin ta na dukan tara tara,tambayar kan ta take idan ya ɗauka me zata ce masa kuma.Shiru tayi Dan ita kan ta bata san abun ce masa ba dan kunyar sa take ji matuƙa. Zaune yake yana ƙara shigewa a cikin sabon tunanin da ya Kunno masa kai akan yadda zai t in Kari Nadiya ɗin sai ga kira ya shigo wayar sa.Kafin yayi yunƙurin ɗaga kiran sai ya yanke.Har ya so basarwa sai kumaya sanya hannu ya janyo wayar ta sa ƙirar iphone latest one yar yayi wadda take dai dai da zamanin yau.Duba ñumban yayi da kyau kamar yadda yake saka ran samun kiran ta akullum sai abun ya bashi mamaki da ɗar sa ma sa ko dai idon sa ne ba ita bace bai gani dai dai ba may be hakan ya sa ya ƙara tale idanun sa zuciyar sa na mugun bugun tara tara.Wani irin murmushi ya saki wanda ya daɗe bai yi ba,sannan ya baro kan kujerar da yake wadda ke ɗauke da su ƙaton tebur dake ɗauke da tulin takardu a cikin office ɗin kasancewar shine manager a gurin,ya samu aiki bayan kasuwan cin sa,a wani Babban gidan man fetur inda ganin yana da ƙwazon aiki suka bashi Manager a sabon companyn ASAD PETROLEUM LTD. Haka yayi ta samun cigaba har Allah ya ƙara kimtsa masa Babbar rumfar sa wadda suke da haɗa ka da Ibrahim kafin ya cire nasa shima ya buɗe ya ƙara nasa kayan ya zama kowa yana riƙe da nasa ne zallah arziki Alhamdulillah yana ta buɗe musu ta ko ina.Dan ko Ibrahim Alhamdulillah Raliya na cikin kwanciyar hankali farin cikin ta take yi tana rainin yan uku ɗin ta da suka yi ɓulɓul da su. Zama yayi akan Manyan kujerun Alfarma Dake a cikin office ɗin na shi kafin ya dannawa ñumban kira. Nadiya da har ta cire rai tun da ta san kiran ya riga ya shiga hakan ya sa ta razana ganin wayar ta na fitar da haske kafin ta fara tsuwwa alamar neman agajin ɗauka. Cikin faɗuwar gaba take duban wayar har kiran ya tsinke kafin wani ya sake shigowa. Ɗagawa Najiba tayi da sauri wadda ke shirin barin gidan zata koma gidan ta asabon gidan da Jamil ya siya musu.Gida na alfarma. Tana ta haɗa kayan su cikin Tausayin yar uwar ta da zata bari yin zaman zawarci,zawarcin da baya da daɗi ko kaɗan face tarin ƙalubalen rayuwa da zata riƙa cin karo dasu. Ajiyar zuciya ta sauke ganin Najiba gaban ta tana sakin murmushi tana gyaɗa mata kai.Hakan ya sa tana jin sallamar sa ta sauke ɓoyayyiyar Ajiyar zuciya. Tana amsa Sallamar jin yadda ta ratsa mata Kunnuwa cikin natsuwar sa da ta ƙara shigar sa da kuma yanayin hutun da ya fara shigar sa. Shiru dukkanin su suka yi bayan amsa Sallamar. Sai itace tayi ƙoƙarin amsa masa da. " Barka da yini ". Bai amsa ba har sai dai ta ƙara maimaita wa sannan yace " Lafiya lau Diyah ". Wani irin murmushi ne ya suɓuce mata jin sunan da ya kira ta dashi dama shine kaɗai yake kiran ta da sunan tun lokacin da ya fara nuna mata so. Shima murmushin ya samu kan sa da yi yana jin zuciyar sa fes jin murmushin na ta da ya saukar masa har tsakiyar zuciyar sa. " Ina Jazlan ɗina ".? Samun kan ta tayi da fashe masa da kuka zillau jin wannan tambaya ta sa,Ashe Jazlan yana da wani uban bayan Azzalumin mahaifin sa,Ashe akwai wanda zai kalli jazlan a matsayin nasa,Haka ta ke ta nanatawa a cikin zuciyar ta cikan Tausayin jazlan ɗin wanda ta zuba ma ido yanzu,Yana bacciin sa hanakali kwance yayi ɓul ɓul abun sa yayi wayau,Ta gefe ɗaya kuwa kuka sai da tayi mai isar ta sannan ta share hawayen ta tana sauke ajiyar zuciya.Wani farin ciki na ƙara mamaye ta.Kenan yana bibiye da ita bai yi fushi da ita ba duk wulaƙancin da tayi masa wanda take kunyar kan ta da kan ta,da kuma Haushin biyewa Mahaifiyar ta har yanzu take ƙauye malam Abdul Basiɗ ya kai ta akwatin mantuwa yanzu kusan watan ta biyu a gida. " Bana son ki ƙara bawa wasu hawaye damar zuba shi yasa na barki kiyi mai isar ki,Zan share dukkanin hawayen da suka zuba a yanzu da kuma wayen da suka zuba a lokacin da bana kusa,kiyi haƙuri ki karɓi ƙaddara Allah dai dai yake akan duk abinda ya nufi bawan sa dashi,So Dan Allah karki ƙara mini asarar hawayen nan,kiji Tausayin bawan Allah kinji Oum Jazlan ". Tsikar jikin ta ce ta fara zuba a hankali ta Lumshe idanun ta da suke da sauran ruwan hawaye a cikin su jin yadda yake maganar sa a tsanake cikin so da bege da ke addabar rayuwar sa.Sai yanzu ta ƙara sanin cewa ta tafka babban kuskure a rayuwar ta domin kuwa barin ya Sayyid shine asara mafi muni da tayi a zaman rayuwar ta.Bata san yadda lokaci ɗaya ta masa mugun tsana ba ita kan ta tana mamakin tsanar da tayi masa wanda take tunanin kwaɗayin su ne ya rufe musu ido a lokacin ita da najiba wanda ya jefa su a tashin hankali musanman ita.Tabbas a wannan karon ba zata ta taɓa yarda tayi wasa da damar ta ba , yadda yanzu take jin mugun son sa a ranta bazata bari ya kubce mata ba kamar yadda Najiba ke bata shawara zata riƙe sa da hannu bibbiyu zata zaɓarwa Ya yan ta uba na gari bazata duba komai na rayuwa ba zata zaɓi farin cikin ta da kuma soyayya. Tunanin ta ne ya katse jin yana furta " Kin amince na turo,cos bana son aja komai da sauri Nadiya,na fi son ki ƙarasa samun kwanciyar hankalin ki a gidana". Ajiyar zuciya ta sauke wani farin ciki na mamaye ta kafin Ta furta " na amince "Sai hawaye shar suka ƙara silalo mata masu zafi wanda ta rasa na farin ciki ne ko na meye " Ka yafe mini na san na cuce ka kuma na yaudare ka,nasan wannan duka daga cikin abinda na shuka ne,baka min komai ba sai bi na da Alkhairi amma na watsa maka ƙasa saboda kwaɗayin abun duniya na biye wa zugar ƙawaye na shiga cikin sahun masu gujewa Hukuncin uban giji,Ka yafe mini na roƙe ka,kuma ka roƙa mini Hajiya ta yafe mini ". Ta kai zancen ƙarshe tana fashewa da wani sabon kuka mai ratsa zuciya da gangar jiki. Rarrashin ta yayke yi yana jin kamar ya fasa kukan zuciyar sa babu daɗi,ya furta " Ni dama ban riƙe ki ba Nady Kawai dai kin san ba,a rasa ɓacin rai,kuma ma,ma Diyah Soyayyar ki bata barin ɓacin ran Allah wannan Bawan Allah tasiri a zuciya ta, wallahi Allah Nadiya har mamakin kai na nake yi,ko lokacin da na sha ruwan wari a jiki na babu abun da ya ragu a zuciya ta,da Auren ki na sa ake bibiyar mini lafiyar ki,kafin nadaina jin yadda kike,Ina ƙaunar ki Nadiya kuma zan saka ki a farin ciki mara iyaka in sha ALLAH Nadiya,na Miki tanadi mai kyau,kuma karki ji wani abu akan matata mace ce mai saurin fahimta ta san komai,Ni dai kawai yardar ki nake nema,kuma Hajiya ma ta yafe Miki ai tuni tun da kin ƙwamushe zuciyar ɗan ta "Ya kai ƙarshen zancen yana sakin murmushi mai cike da shauƙi da bege. Murmushi kawai ta saki itama,Wani sanyi na ƙara ratsa ta.Duk da ta san zancen Hajiya ya dai faɗa ne kawai Amma tayi farin ciki sosai,Dan har ya kasa ɓoyuwa,Wai ita ake yiwa irin wannan soyayya lallai da ta tafka muguwar asara a rayuwar ta,Kuma ta shaida Allah na son ta da rahamar sa tun da har ya dawo mata da Ya sayyid.. Dan haka ji take kamar yau ta sauko duniya,ashe duk chan shirme take yi wa rayuwar ta ta hana ma kan ta jin daɗin ka kwaɗayin abun duniya Mai ƙarewa,Ya Sayyid shine firstlove nata kuma koda akayi Auren ta da Tanim yana ran ta kawai dai ta rasa dalilin tsanar ta sa,sai kuma kwaɗayin abun duniya da ya rinjaye ta har ya so jefa ta a mahalakar duniya ba jin daɗi ba.haka suka cigaba da taɓa firar sama sama cikin wani irin yanayi mai haɗe da shauƙi.Kafin Jazlan ya tashida rigima hakan ya sa suka yi sallama dama shine mai magana ita kam shiru har yanzu ta kasa sakewa dashi.. A gurguje dai a haka rayuwa ta cigaba ta gudana ta kowa ne sashe masu farin ciki nayi masu baƙin ciki nayi. Mama Hafsatu na cikin masu farin ciki domin kuwa Malam Rabu'u da kan sa yaje ya yo bikon ta da saka bakin ɗan uwan sa ganin yadda ya matsa masa dan tana gab da cika iddar ta.A hakan ya dawo da ita gidan sai dai kuma ta shiga taitayin ta matuƙa ta fahimci komai talaucin su gidan ta ya fi mata mutunci dan haka ta dawo tare da niyyar gyara tarayyar ta da kowa domin ta san ta aikata wa mutane babu daɗi,tayi ta neman gafara wurin Ubangiji na zagayen wajen malamman tsibbo.Ta zamo shiru shiru ga ta kaɗan ya rage ciwon yunwa ya kan mata tuwon da take rainawa ko irin shi bata samu a inda ta ya ajiye ta a chan rigar su garin iyayen ta,daga furaa sai fura wadda itama ba kullum take samun ta ba,sai ta ci baƙar wahala ta samu saboda yadda ƙauyen suke ɓoye hatsin su har sai lokacin damuna a lokacin rani suyi ta wahala da nema gashi ba,a samu sosai. A cikin masu baƙin ciki kuwa Gidan su Ya Sayyid suna ciki domin kuwa samun labarin yadda Ya koma ma Nadiya ya matuƙar basu haushi da ɓata masu rai musamman yayyen sa,domin a ganin su bai san ciwon kan sa ba nan har mahaifiyar su aka isko har gida aka cima ta mutuncin kan ta aka kuma zage su tsafff sannan aka kira musu matsiya ta amma shine zai koma mata dan yana da sallatattar zuciya. Ganin dagaske yake zancen dan ya kawo shi gida ga yayyen na sa cikin ɗar ɗar hakan ya sa duk suka rufe masa ƙofar ganin fuska bare a tada maganar da ya riga ya shan mace su da ita,Ga kuma wani gefe mahaifiyar sa da ta ce babu shi babu ita idan ya koma ma matsiyata,ta yafe shi, sai yanzu da suka ga yayi kuɗi ya samu jin daɗin da suke so zasu bashi ragin wani to Dan haka ba zai yuyu ba sai dai ya zaɓa ko ita ko ita.Hakan ya sa ya shiga tashin hankali matuƙa sannan ya cigaba da Rarrashin Nadiya dake cikin tsoro mai yawa jin abinda ke faruwa Dan ta saka rai ga Ya Sayyid a yanzu, haka ma mama Hafsatu ta ji tsoro matiƙa tare da tausayin yar ta da ta gane itace mabuɗi na farko da ta illata tarbiyyar Ya'yan nasu.Tayi Nadama matuƙa tare da tausayin yar ta wadda duk ta tuna rayuwar da tayi sai ta zubda ƙwalla akai akaice. Haka komai yayi ta tafiya yau kusan wata uku ana abu ɗaya a gidan su ya Sayyid da Nadiya. Ya'yan su mai muguwar zuciya ya ce basu san wannan Magana ba duk da sauran sun sauko amma mahaifiyar sa da ya'yan nasu sun rufe ido.Haka aka yi ta taƙaddama familyn suna ta zagin Nadiya ita da mahaifiyar ta da suke ganin kuɗin Ya Sayyid yanzu shine ake son ƙaƙa ba masa ita,saboda Shegen kwaɗayin su.Yau wata kusan shidda ana magana ɗaya,dan su malam Rabu'u har sun fara gajiya saboda masoya nata ɓullowa Nadiya ta ko ina amma Sayyid shiru,komai ya cunkushe masa yayan ya sa ya kafe.Da ƙyar aka samu komai ya lafa bayan saukowar wannan ya yan na su amma Badan suna son Nadiya ɗin ba abinda aka yiwa na su ya taɓa su dan ya daɗe bai dawo normal ba koda aka yi Auren sa da yar uwar ta sa.Allah ya sa matar sa mai haƙuri ce ma,duk da yar dangi ce da tuni an riƙa zama dasu,amma ita kan bata damu ba Allah ya bata haƙuri bata taɓa ko kai ƙarar shi gida ba,duk da akwai zumunci babba a tsakanin su.A haka dai aka fara shirye shiryen bikin da kowane gefe ba,a cewa komai Gara su,su Nadiya gidan su ana mugun son Sayyid kowa na farin ciki dashi.Amma.gidan su ya Sayyid maɗunɗun basa son Najiba ko kaɗan. Yau bikin ya kama saura wata ɗaya da sati Uku. *** A ɓangaren Sauran yan Qungiyar su Tanim kuwa tun samun labarin abinda ya faru ga Su Jamcy sai kowa ya ƙara shiga taitayin sa suka ƙara fara nemawa kan su magani cikin wata irin nadama da suke dabai baye da ita da natsuwar da ta shige su.Suka aje duk wata ramuwa a gefe suka fara fuskan tar mahaliccin su dan neman gafarar sa,tare da neman sauƙin lalurar da suke ciki. A ɓangaren Shanty ma tun da ta nemi gafarar Nadiya ta yafe mata ta samu sauƙin rayuwar ta haka ma Tanim,sai suka cigaba da gudanar da rayuwar su a tsanake sai dai ta ƙasa kuwa kowa na ɗauke da jin zafin kasancewar sa da cuta mai karya garkuwar jiki.Yau cikin SHANTY wata takwas da yan satuka biyu akai,Wanda yayi dai da ɗaurin Auren Nadiya tare da Angon ta Sayyid wanda aka ɗaura a ƙofar gidan su Nadiya ɗin wanda ya tara jama'a da dama tako ina,ana ta yi ma Ango da amarya fatan Alkhairi bakin ya Sayyid har kunne ya sha kyau matuƙa kamar Auren fari. Tun da aka gama ɗaura Auren ya fito yana jin jiri na ɗibar sa,Da ƙyar ya kai kan sa gida har jiri na neman kai sa ƙasa,Yana zuwa ya kulle kan sa ɗaki.Kuka ya zauna ya sharƙa kamar ƙaramin yaro yadda mai sanarwar ɗaurin Auren ke furta An ɗaura Auren Nadiya Abdul basiɗ da Angon ta Sayyid Abdul Rahman liman.Ji yake ina ma shi aka saka ina ma sunan shi ne bana Wani ba,Wani irin Tausayin kan shi ne ya kama sa wanda take yanayin da ya shiga ya saukar masa da mugun zazzaɓi wanda yakai shi ga kwanciya asibiti haka suka yi ta jinyar sa a sibitin har aka sallamo sa. Nadama tun yana gadon asibiti yayi ta tafi dubu ji yake ina ma akwai agogon da ke saita rayuwa ta dawo baya ko yayi gaba da ya gyara kurakuransa sai dai kash Allah ya riga ya tsara komai.Allah ya bashi ikon cinye jarabawar sa.Har suka isa gida ajiyar zuciya yake yi.Sai dai farin ciki ya samu kan sa samun JAZLAN A gidan wanda aka karɓo yau ɗin, saboda yanzu tana bada shi a zo dashi gidan kuma duk lokacin da ya so ganin sa tana bada shi har yawo yake fita dashi yayo masa sayayyya.Hakan kuma duk umurnin ya Sayyid ne da ya ce ta ji Tausayin Tanim ta bar shi ya riƙa ganin ɗan sa dan yaga yadda duk ya lalace kamar ba Tanim ɗan gayu ba sai ya koma tanimu ɗin sa.Haka ya wuni cikin farin ciki tare da ɗan sa yana jin rabin Damuwar sa ta kau ganin gudan jinin sa da yake mugun ƙauna arayuwar sa da tausayi.Duk ya tuna da kan sa ya bada kuɗin cire cikin sai ya koka da hawayen sa kuka na baƙin ciki da dana sani,ina ma lokacin yayi ma Nadiya gata wanda ba,a taɓa yiwa wata ya mace ba.Zuwan Jazlan yau kuwa Dr Abida ce ta roƙa masa domin ta san zai kasance cikin farin ciki ganin ɗan na sa zai rage mata wata yar Damuwar sa,ta san zata gushe masa sanadiyyar ganin sa,koda ta ɗan lokaci ne.Sai ta saka sahiba ta karɓo shi,Ita kuwa Nadiya bata yi musu ba ta bada shi dan ba wannan ne zuwan sa na farko gidan ba.ana yawan ɗaukar sa dan ya rage rigima yanzu. Anyi shagalin biki tare da saka tarewar amarya a wani sati mai zuwa. Ta ɓangare ɗaya kuwa Soyayyar su suke sha babu kama hannun yaro.Duk da Nadiya har yanzu ɗar ɗar take yi da Dangin mijin nata.Lefen ta ma sun hana akai mata shi sun ce sai taje chan ta gani ai ba budurwa bace dan haka ba zasu lamun ta yi mata kwatankwacin abun da aka yi wa budurwa ba ga Haushin su na kayan ɗakin da ya yi da kan sa dan cewa yayi ba sai an je da komai ba.,hakan ya sa suka rage kusan kala goma na lefen da ya haɗa mata na kaya masu Shegen tsada dan babu ƙaramin abu ciki ya san Nadiya na son wanka dan haka ya taƙarƙare ya haɗo musu kaya masu kyau ita da Matar sa mai suna Saudah.Bai ce musu komai ba har ita Sauda ɗin da suka zube ma kusan kala biyar sannan aka rabawa wasu daga cikin dangi kala biyar ɗin.Sai dai abinda basu sani ba mata da miji sai Allah Sauda bata ko haɗe kayan nan da suka bata ba Amatsayin ta ta tasu ta ajiye su gefe yana dawowa ta damƙa masa su,Tace bata so amayarwar ƙanwar ta da kayan ta. Murmushi kawai yayi yace ta ƙara zai saka mata wasu daga baya.Ta yi masa godiya itama cikin murmushi jin yana saka mata albarka,tare da kira mata yar aljanna kamar yadda ya saba tsokanar ta da sunan da yayi mata ɗin. A yau Sati ya zagayo kuma ayau ne Nadiya

Chapter 38 of 39