Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Bismillahir rahmanir Rahim 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _*Daga marubuciyar littafin*_ _*A Mafarki Nasanta*_ And Now *_Rayuwar mu a yau_*✍️ _Allah ya sa mun shiga 2025 a cikin sa,a.Allah ya tabbatar muna da alkhairin ta.Allah ya yafe muna kurakuran mu da muka aikata acikin sanin mu da wayen da muka aikata ba,a cikin sanin mu ba. Allah ya sanya ɗimbin Alkhairi a cikin ta.Allah kasa shekarar da zamu samu chanji ne mai albarka.Allah ya sauƙaƙa muna a bunda ya tsanan ta a gare mu.🤲🤲_ *Book 1.* *Free* P.20 *** _*#FA'EEHBG*_ _*#NAJMIL*_ _*# NADNIM*_ _*#FRIENDSHIP BETRAYAL*_ _*#WOMANISING*_ Tsaf ya Shirya cikin kayan da ta fito masa da su wayen da suke zube a cikin Siff ɗin sa,kuma rabi da kwatar kayan duka na Tanim ne dan duk sababbi ne kasancewar Tanim babu inda baya zama. Ficewa falon yayi inda ya same ta chan tana waya da Mahaifiyar ta sai dai babu wani sakin jiki a tattare da ita.Sallama suka yi tana yanke kiran dan dama wayar ta zo ƙarshe. Zama yayi kan ɗai daga cikin kujerun yana sakin guntun murmushin sa idanun sa akan ta.Itama haka. Zama yayi bayan ya ja kujerar sannan ta fara serving na sa. Abincin ta fara ci hankali kwance tana sakin Ajiyar zuciya domin ta kasa haƙura da zancen da ke yawo a zuciyar ta. A bazata haka Jamil ya ji saukar zantukkan na ta.Shiru yayi ya kasa haɗiye lomar da ke bakin shi zuciyar shi na wani irin rawa domin bai yi zaton tayi masa tambayar ba ya zata cewa bata shiga kunnen ta yadda ya dace ba ashe ya makaro,dole ya san abinda zai furta wanda zai rufe zancen,shi mai,ma zai ce mata ne? Tun da har ta iya kasa ya da zancen tabbas idan yayi wata magana mara saiti komai zai rikice masa lokaci ɗaya. " Ya Jamil abun da naji a cikin kunne na a daren jiya ina son ka tabbatar mini da rashin gaskiyar zancen bansan dalilin da ya sa na kasa cire abun a raina ba kalmomin suna mini kai kawo a cikin ƙwaƙwalwa tun wayewar safiyar yau ". Shiru yayi yana ƙara lissafo zancen na ta kafin ya ɗan saki guntun murmushi yana kallon ta tare da kanne mata ido ɗaya sannan ya furta. " Haba My Naj irin wannan fa ba,a sanin komai a ciki,saboda ba a hayyaci ake ba,yanzu tsaff zan yi yi Miki Alƙawarin saye Miki Duniya baki ɗaya,To kin ga babu wani abun kamawa anan,Bare ma Ke ɗince, ta daban kike My Qlbi My Naj,zumar ki da ban take ". Ya na kai ƙarshen zancen ya kanne mata ido ɗaya. Wani irin murmushi Najiba ta saki tana yin ƙasa da kan ta na jin yar kunya kafin ta sauke a jiyar zuciya jin da tayi ta ɗan samu natsuwa kaɗan a yanzu lallai haka ne zancen dan ta taɓa jin labarin wanda ya yi wa matar sa Alƙwarin Saye mata A merica.Da safe aka yi ta rigima har ta kai su ga rabuwar Aure domin shima ya haɗu da bahaguwar mace mai aiki da ƙwaƙwalwar yara. Yoo mai aiki da Ƙwaƙwalwar yara man😂 Waya ga kyautar America.🙈🏃😂 Murmushi ta ƙara saki kafin ta cigaba da cin abincin ta hankali kwance. Haka shima ajiyar zuciya ya sauke a ɓoye kafin ya cigaba da cin abincin na sa yana ƙara sauke ajiyar zuciya dan shi ya san yadda zancen ya shiga kunnen sa wanda ya nemi har gitsa zuciyar sa gaba ɗaya. Shiru ne ya ratsa su har suka gama yin breakfast ɗin suka miƙe inda shi ya fice Gidan gaba ɗaya ita kuma ta koma ɗakin ta Dan bacci take ji saboda bata samu damar yin na safen ba sai yanzu. Tana cikin tunanin zancen da tayi masa akan motar da yayi mata alƙawari wadda ya rufe mata baki da ta zaɓa daga cikin motocin da ke parkey a ƙaton garage na gidan domin ba,a samu wadda yayo mata order ba dan haka ya sanar da ita bata iso ba, a safiyar da aka kawo ta gidan,sai ya rufe bakin ta da cewa motar na cikin kwante na.Sai kuma yau da ta ƙara yin maganar ya bata umurnin zaɓar ɗaya daga cikin motocin gidan saboda ya manta ya faɗa mata Jirgin da ke ɗauke da motocin na companyn da yayi mata order ya nutse wanda aka kira shi a satin da ya wuce sai yau ya tuna ma da tayi zancen. Farin ciki ne ya kama NAJIBA farin ciki kamar ta taka kan ɗan jariri ta matsu ya dawo domin ta zaɓi motar sai ya dawo zai bata key ɗin ta.Tana cikin wannan tunanin bacci ya yi awon gaba da ita. A ɓangaren Tanim kuwa ko gida bai koma ba haka suka kasance cikin ɗakin Hotel ɗin nan suna cigaba da aikata ɓarnar su ba tare da sun tuna cewa Ubangijin da baya barci bare Hamma yana ganin su,ba tare da sun ji kunyar shi ba. Basu bar Hotel ɗin ba sai suka ɗauki kusan kwanakki biyar suna murzar juna.Sannan da safiyar kwana na biyar da zuwan su suka bar Hotel ɗin, wanda a hakan ma daƙyar suka rabu domin SHANTY ba ƙaramar yar hannu ba ce ta san kan ta,yar bariki ce ta ƙwarai,duk da wannan lokaci da suka ɗauka bata taɓa damuwa da ƙawar ta ta ba ko jin abinda take yi bai dace ba ga ƙawar ta. Kuma tun daga ranar sukan keɓe a mabanbantan gurare da dama suna cigaba da aikata ɓarna a bayan doron ƙasa,ɓarna wadda dubbanin mutane suka mai da ita abun Ado suke gudanar da ita bayan idanun jama'a,a tunanin su idan sun ɓoye ma mutane zasu ɓoye ma Ubangiji sai dai sun man ta idanun su sun rufe ƙwaƙwalwar su ta toshe,zunnubai sun shafe komai a cikin zukatan su,sun manta Allah yana ganin su a duk inda suke yana tare da mu a duk inda muke. Subhanallah Allah ka yi muna tsari daga aikata Zina,luwaɗi,maɗigo,gamsar da kai ( Masturbation ). Allah ka kare muna imanin mu a duk inda muke.Ya Allah kar ka kama mu da laifin da wasu daga cikin wawayen mu suke Aikatawa.🤲🤲 A ɓangaren Nadiya kuwa bata kawo komai ba na rashin Dawowar Tanim hasali ma bata ji wani rashin daɗi na rashin ganin wanzuwar sa cikin gidan ba kasancewar bata jin motsin sa ko ganin sa.Sai kuma zancen SHANTY itama bata kawo komai ba sai dai tayi mamakin abun da ya hana ta zuwa kwana biyu duk da ta sanar da ita ayyukka ne suka riƙe ta bata zo ba har yanzu wanda kuma bata saran zata zo yanzu gidan ba may be sai ranar da Allah ya kawo ta ko kuma ta zo ita da Tanim holewar su a cikin gidan idan nan suka yi ra'ayi domin ta sha Alwashin sai anyi komai gaban Nadiya har cikin bedroom ɗin ta Dan so take yanzu ta bar gidan ganin yadda take ta ɗora status na irin abubuwan more rayuwa da kuma yanayin yadda fatar ta tayi kyau sai take jin mugun kishin ta duk da ta san Tanim a yanzu bai da lokacin ta sai na ta,ita kaɗai ya riga ya kai NADIYA bola domin ya sanar mata babu abunda zai yi da ita a yanzu yana ma ƙoƙarin kora ta gida ne,wanda har yanzu a rasa dalilin da ya sa ya ƙi aiwatar da furucin na sa na bata saki a yanzu ɗin. Rashin zuwan SHANTY ya sanya mata yar damuwa kaɗan sai ta koma kamar lokacin da ta fara zuwa gidan,babu kwanciyar hankali da ta zuciya iyakar ta dai ta san zata ci mai kyau zata sha mai kyau haka ma sutura komai bai rage ta da shi ba sai dai babu natsuwa ga kuɗin bata da Natsuwar iya cin su domin kuwa Tanim kullum sai ya je mata ta ƙarfi da yaji wanda yanzu yake je mata ta inda Allah ya haramta a ranar da ya fara bi ta wannan hanyar ta yi kukan azaba ta ci kuka kamar zata mutu ga shi komai yake yi yana yi yana marin ta da ci mata zarafi da zagi har ya samu biyan buƙatar sa NADIYA ta yi kuka wanda bata taɓa yin shi ba ta roƙe saki kai tsaye ya nuna ba yanzu ba,babu wannan tsarin a tare dashi.Ta Aanusar da shi illar abun da yake yi sai dai bai bata amsa ba sai ma kai mata mugun mari tare da shuri wanda har da jimata yayi a gefen ƙugu dan ƙugun na ta sai da ya bugi gado wanda ta sume cikin zafin a zaba.Shiko ko a jikin sa sai ma ƙara shura ta gefe da yayi ya fice War sa yana gaggaɓar dariya.Yana shiga ɗakin sa kuwa ya baje kolin kalolin giyar sa ya shawu Sosai nan bacci ya kwashe shi. Haka tayi ta jinyar ƙugun ta har ta samu ya warke mata tsaff sai dai har yanzu bata sanar Wa da kowa halin da ta ke ciki ba.Sai dai a yanzu da take jin duniyar ta yi mata zafi ta yanke wa kan ta hukuncin sanar da yar uwar ta.Haka kawai taji zuciyar ta ta Amin ta da sanar mata dan ta na ji a zuciyar ta zata samu mafita ko kaɗan ce,koda kuma ba,a samu ba, zuciyar ta zata rage nauyin da take ma ta. A hankali ta fito daga cikin bedroom ɗin na ta da wayar ta a hannun ta cikin doguwar riga mara nauyi tayi kyau sai dai tayi yar rama sai dai ba mai yawa ba,hasken fatar ta na nan ko ramar sai ka zuba mata ido da ya wa zaka hango hakan domin tana ƙoƙarin ɓoye damuwar ta ta. Ɗan ɗin gishi take yi a hankali tana bin falon da kallo dan yanzu ta daina tsoron Haɗuwar ta da Tanim ɗin dan ta rasa yadda ake yi ya ke shigar ma ta ɗaki duk da a rufe yake shi ya sa ta daina wahalar da kan ta da rufe shi domin ta fahimci Tanim Shu'umi ne duk yadda zata yi bai hana shi isa gare ta ba. Zama tayi a kan kujerar tana sauke A jiyar zuciya.Kiran Binta mai aikin gidan na su tayi.Da sauri ta zo umurnin uwar gidan tabi inda ta koma kitchen da sauri ta kawo mata kwallin Hollandia ɗin da cups guda biyu tsiyaya mata ta tayi tana miƙa mata sannan ta juya ta koma kan aikin ta cikin tausayin Uwar gidan ta ta.Domin matsayin "Yaa ta ɗauke ta tana jin ta kamar yar cikin ta wadda ta haifa dan tana da ya mai irin shekarun Nadiya wanda ko rantsuwa tayi bazata yi kaffara ba zasu yi sa,a da juna,tana jin Tausayin ta sosai domin tana karantar rayuwar gidan,kuma ta na ganin komai da idanun ta wanda take karantar komai a fakaice shi ya sa take cike da Tausayin NADIYA kuma bata son shige mata hanci bata son ta zamo tsohuwar banza shi ya sa ta share bata taɓa yi mata maganar ta san abunda ke gudana ba game da zaman na ta da mijin ta da wasu halayen da yake yi domin har yanzu yana shigowa da yan mata wata rana ma maza.Kuma ba su barin gidan sai wata safiya suke ficewa wanda tana lura sosai dan tana yawan yin laɓe dan an ba ta ɗaki a cikin gidan.Ada da yar ta suke gudanar da aikin amma ganin yanayin mai gidan sai ta mayar da yar ta gida ta ce karatu ta koma gudun kar yar ta ta shiga tarkon Tanim ɗin.. Madarar ta zuba kasancewar a ayan zu bata iya shan komai sai ita yadda Tanim ya sabar mata da ita, Sannan itama ta rasa dalilin da ya sa take yawan jin son shan ta, bata da abun sha sai ita.A yanzu. Idanun ta,ta Lumshe jin zuciyar ta tayi wani irin sanyi tana jan ajiyar zuciya yadda madarar ta ratsa mata zuciya. Kafin a hankali ta juyar da kan ta tana ɗaukar wayar ta dake a jiye a gefen ta.Dialing numban da tayi Saving da tawan ce ta danna wa kira.NAJIBA dake kitchen tana ta aikace aikace ce ta ji ƙarar wayar ta ta a Falo hannun ta ta wanke tare da goge shi tana kashe gas dake ɗauke da stew akan sa sannan ta koma falon tana ɗaga wayar tare da yin Murmushi ganin mai kiran ta ta dan sun kwana biyu ba su haɗu da juna ba ko magana da juna a wayar dan ta rage hawa online Nadiya ɗin wanda bata san dalilin ba,sai dai sanin cewa lafiya take bata damu ba. Gaisawa sukayi cikin kewar juna kafin Nadiya ta yi shiru. Jin hakan ya tabbatar ma NAJIBA akwai matsala hakan ya sa a hankali ta furta. " Tawan Allah ya sa dai komai yana tafiya lafiya ta gurin ki ". Numfashi ta sauke mai nauyi kafin ta furta NAJIBA ina cikin matsala. " Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un subhanallah tawan Allah ya sa ba matsala ba ce Babba kamar yadda ki ka alaƙanta kan ki da ita kasancewar matsala ko ƙanƙani ce bata da daɗin ji ko ambato ". " Me ya ke faruwa ". NAJIBA ta furta zuciyar ta babu daɗi tana jin wata irin faɗuwar gaba. Numfashi Nadiya ta sauke kafin ta furta. " NAJ Tanim neman mata yake yi abun bai tsaya akai na ba har cikin gida na har cikin bedroom ɗina ya kwanta da mace akan gado na,Najiba Abin baƙin ciki kullum fyaɗe yake yi mini da tozarci ". Tana kai ƙarshen zancen wani irin kuka ya taso mata mai tsuma zuciya wanda bata taɓa yin irin shi ba a rayuwar ta ta duniya ba.Duk yadda take son bata sauran zancen ta kasa. NAJ ma kukan ta ke yi a ɓangaren ta tana furta inna lillahi wa Inna ilaiihi raji'un wani irin rawa zuciyar ta ke yi mata tashin hankalin da ta tsinci kan ta ya fi na yar uwar ta zuciyar ta zafi take mata.Ta daɗe tana hasashen hakan akan Tanim sai dai babu bakin magana domin ta taɓa ganin shi da wata a cikin mota a lokacin tana tare da Jamil suma zasu wuce lokacin da hanya ta haɗa su tun da ga lokacin ta kafa mishi ayar tambaya domin daga yanayin shigar budurwar zaka san bata ƙwarai ba ce akwai wani abu a ƙasa dan yarin yar ta ɗage glass ɗin ta wanda ka ke iya hango har hannun Tanim ɗin akan jikin yarinyar da nata akan na sa jikin. Hawaye ta share masu zafi tana tuno wa da yadda ta ganshi a cikin idanun ta wanda ta kasa yarda sai dai ta dasa zargi mai tsanani musamman yadda ta ga yake mu,amala da yar uwar ta, ta san bazai yuyu a ce ita kaɗai ce ba rashin riƙe abun a zuciyar ta ya sa ta furta mata kalmar da ta daɗe tana cin zuciyar Nadiya.Tana cikin wannan tunanin ne ta ƙara tsinkayo Muryar NADIYA na furtawa cikin gunjinn kuka. " Ashe gaskiya kike faɗa mini NAJIBA,Ashe Tanim ba sona yake yi ba,soyayyar da ya nuna mini akan abu ɗaya ce, NAJIBA Auren Sha'awa da nake gani a labarai novel,da wasu labaran a social media shi Tanim yayi mini,Najiba ya tozarta mini rayuwa ya illata ni,tun zuwa na gidan nan daren da aka kawo Ni bai shuɗe ba sai da na ɗanɗani a zaba mai raɗaɗi wadda bazata taɓa ɓacewa a cikin ƙwaƙwalwa ta ba,nayi kuka nayi kuka babu mai Rarrashi duk wata hanya da nake tunanin zan iya cin kuɗin sa na wawushi na wa kamar yadda na zo da burin hakan abun ya gagara ya rufe ko ina ,na rasa farin ciki na sanadin son zuciya ta na ci zarafin masoyi na na gaskiya NAJIBA na san haƙƙin sa ne ke Bibiya ta,Nakai rayuwa ta a cikin kurkukun ƙaddara na bi yewa son zuciya ta,na biyewa abun duniya,Ina jin tsanar komai da komai a yanzu ba zan iya kisa ba da tuni na kawar da Tanim kafin baƙin cikin shi ya kawar dani,Ina tuna yadda su Baba suka so ganar da Ni na ka sa gane hanyar ashe kaina nake rurawa wuta kuma na jefa kaina a ciki,ashe Tanim azzalumi ne mai aikata babbar ɓarna ne a doron ƙasa,Haƙƙin Baba nake tsoro da na ya Sayyid ya cigaba da Bibiyar rayuwa ta,kai cona,Ni NADIYA na faɗawa ƙaddara mai ido ".Ta na kai ƙarshen zancen ta ƙara fashewa da wani mahaukacin kuka domin dama duka zancen tana yin sa cikin gunjinn kuka ne mai sauti wani baya ko fita sai dai Dan ta waya ne shi ya sa NAJIBA dake ta risgar kuka itama take jin ta. Sai da suka ci kuka sannan NAJIBA ta fara Rarrashin NADIYA da bata baki kafin ta fara harhaɗo abinda zata furta mata domin ta rasa abun faɗa zuciyar ta ta cunkushe mata. Shirin da taji ne da saukar ajiyar zuciya na Nadiya hakan ya sa ta fara magana. " Kiyi haƙuri,kowa da tashi kallar ƙaddarar sai dai kuma tabbas taki mai ido ce kamar yadda kika faɗa,Kiyi haƙuri ki miƙa lamurran ki ga Ubangiji shine zai Miki mafita kuka ba shine Magani ba,Face ƙarin damuwa da raunana zuciya mai ƙarfi ". Numfasa wa tayi sannan ta cigaba da da magana. " Tabbas na yarda da zancen ki domin kuwa Ni shaida ce na gani da ido na domin na ta ɓa ganin shi da wata a mota shine dalilin da ya sa na ke miki zancen da na taɓa yi Miki a baya ". Labarin yadda ta gansu ta bata hannun shi akan cinyar yarinyar ita ma kuma tana jan gemun sa a lokacin motar su ta gangar a kan titi wanda bata san abun da zasu yi ba a gurin duk da tare da jamil suke sai dai ta lura kamar shi bai gan shi ba. Sai dai abun da bata sani ba Shine wanda ya fara gani sai yayi pretending saboda bai son ta ɗago wani abu,ko tayi mishi tambaya. Numfashi NAJIBA ta sauke haka ma NADIYA sai dai bata iya furta komai ba sai dai tsagwaron wautar ta da ta hango da kuma biyewa son zuciyar ta da kuma zugar mahafiyar ta da take ƙara ɗaura ta akan hanya wanda ko yanzu idan zasu yi waya sai ta mata zancen shirin na su na son wawasar kuɗin na sa kamar yadda suka tsara,duk da hakan kuwa ta kasa ɗaura laifin akan mahaifiyar ta. Cigaba da magana tayi tana furta. " A bu ɗaya ne ina ga zaki yi a yanzu wanda zai Sauya Miki shi,idan har kina son cigaba da zama dashi,karki ji babu daɗi a zancen da zanyi na san cewa ba dan zama kika Auri Tanim ba dukiyar sa ce ta ja ki kamar yadda shima jikin ki ya ja shi,ban sani ba ko abun da nake hasashe a yanzu gaskiya ne sai dai zan Miki tambaya Dan samun makamar zancen na wa.Kina son Ya Tanim da gaske ne a yanzu ko har yanzu kamar farko ne da kike kan wannan turbar ?". Shiru ne ya ratsa su kafin NADIYA ta sauke numfashi.Sai dai bata iya furta komai ba dan bata san abinda zata ce ma yar uwar ta ta ba dan ita kan ta bata san abinda ke cikin zuciyar ta ta ba.. " Dalilin tambayar da na maki shine banji kin kawo maganar kina son rabuwa da shi ba,duk da naji yadda kike lissafo iya adadin yaudarar da yayi Miki da yadda komai ya taɓa zuciyar ki,Na san cewa a chan baya baki san cewa kina son Tanim ba,sai dai na san cewa kina son shi tabbas sai dai zan iya cewa ba wata soyayya ce mai ƙarfi ba,A yanzu kuwa duk wani mataki da zamu ɗauka yana tafiya dai dai da yadda kike jin shi a cikin zuciyar ki ". " Kina son cigaba da zama da shi ne ko,a'a ".? NAJIBA ta furta mata. " A'ah ". NADIYA ta furta a sanyaye domin tabbas ta san zama da tanim cutarwa ce a gare ta domin mai irin aikata barñar da yake aikatawa zama dashi Masifa ne,zai iya illata mata rayuwa ta zamo a bar kwatance domin kuwa zama cikin mutane ma zai mata wuya idan ba pampers ta mayar abin sakawar ta ba saboda ta taɓa jin labarin yadda wayen da suke aikata haka kamar dai yan homo yadda suke ƙarewa ba sa iya riƙe kashi bare zawo tana tsoron ranar da zata haɗu da irin wannan ƙadddarar da mai ido da sanin ta.Numfashi ta sauke tana jan ajiyar zuciya.Tana fatan Allah ya shirye shi. Numfashi Najiba ta sauke sannan ta cigaba da magana. " Kina son fita gidan kenan,? ''. Shiru tayi mata bata amsa ba duk da taji tambayar da ta yi mata.. Murmushi NAJIBA tayi wanda yafi kuka ciwo kafin ta fara magana jikin ta a sanyaye.. Kashe wayar su kayi bayan ta yi mata wasu yan zantukkan da suka ratsa zuciyar ta kuma ta ji ta gamsu da shawarar ta yar uwar ta. Suna gama wayar ta saki Murmushi tana jin yanzu ne zata aiwatar da shirin ta na ta tsar sa zata aiwatar da shirin ne kamar yadda najiba ta tsara mata,tana ji yanzu ne zata shimfiɗa ta ta izzar,zata koma asalin Nadiya'r ta,zata nuna masa ita ba kanwar lasa ba ce,zata nuna masa mene ne shu'umancin mace. Miƙewa tayi daga zaunen da take tana sakin murmushi wanda ta daɗe bata yi irin sa ba.Sai dai me tako ɗaya biyu tayi sai ta fara ganin juwa kafin ta iya yin komai sai gata ƙasa tun tana gani buji buji har ta koma bata gani idanun ta na rufewa ta sume a gurin. Binta mai aikin ta dake laɓe tana jin ta ce ta fito a guje tana yin kan ta sai dai kafin ta isa gare ta ta sume a gurin. Ruwa ta nemo ta yayyafa mata sai dai bata motsa ba bata da yadda zata yi sai dan bata iya ɗaukar ta ta fita da ita,dubara ce ta faɗo mata ta kiran wayar wani nata.Cikin sa,a kuwa tana ɗaukar wayar ta dake ya she a ƙasa ta ga tana kan call log a recents calls ta danna wa numban dake farko kira ringing biyu aka ɗaga. Cikin tashin hankali Najiba dake jimamin lamarin yar uwar ta wanda yanayin yadda kalaman ta ke fitowa zai nuna maka akwai wani abun da ta ɓoye mata bayan wanda ta sanar mata sai dai bata san dalilin ta na ɓoye mata ba.Tana cikin wannan tunanin da Addu,ar Allah ya shirya ma Nadiya Tanim ɗin kamar yadda suke fata sai ga kiran ta sabo ya shigo wayar tana cikin mamakin me zata ce mata kuma kiran yayanke sai dai ana kira na biyu ta ɗaga. Cikin tashin hankali ta kira Jamil wanda ya zo a hargitse shima Dan kuka take ta yi itama tun da Binta ta sanar mata da bata numfashi ta tsinci kan ta cikin tashin hankali. Har suka isa gidan suka ɗauko ta NAJIBA kuka take yi inda da gudu suka isa asibitin saboda Driving ɗin da Jamil yake a high speed yadda zasu isa da wuri.Wata private hospital da ke ɗan kusa da su suka isa inda aka karɓe su cikin gaggawa. Taimakon gaggawa Likitotan suka bata kafin sukayi nasarar samo ta. Suna fitowa kuwa suka nemi ganawa da yan uwan ta.A bunda ya shiga kunnen Najiba ne ya sanya ta sumar zaune ƙirjin ta na wani irin bugawa ta rasa farin ciki zata yi ko baƙin ciki ƙirjin ta kuwa cigaba da wani irin mahaukacin bugu yayi lokaci ɗaya wanda bata san dalili ba. JAMIL kuwa da yake a hargitse yana amsa wayar da ake masa daga chan ɗayan ɓangaren kamar abun da ake sanar masa har an gama aiwatar dashi,wanda dama shine tashin hankalin da yake neman zuwa dashi gida sai ga kiran NAJIBA ɗin itama hankali tashe. Kuma dai dai lokacin ne aka shiga gidan na su aka kwashe kayan lefen Najiba baki ɗaya babu abinda aka bari da yake na lefen na companyn da aka yi mata sayayyar. JAMIL zufa

Chapter 16 of 39