Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
take ciki. Ganin haka yasa suka yi musu sallama suka fice cikin tausayin ta da na Jazlan da suka ƙara dubawa suna bin shi da Addu'a,sannan suka bada gaisuwar Dr Abida,da bakin zata zo anjima tana ɗan jiki ne... Godiya Mama Hafsatu take ta zabga musu har suka fice ganin irin kuɗin da suka kashe mata ga komai Baja ja.Mama Hasiya dai kai kawai ta girgiza tare bin Dr Abida da addu,AR samun lafiya,suma su Najiba shiru kawai suka yi babu wanda ya iya cewa komai,Ga shi suna Jin wani iri akan zancen da ta gama a ɗazu na arzikin jazlan da kuma wannan zubda kai da take shirin musu dan kam akwai nauyi godiya take musu kamar ta kai ƙasa. Nadiya kuwa da ke zaune shiru ne ta kalli Najiba ta ce " Me ye haɗin su da Dr Abida da zata basu saƙon zata zo anjima ". " Wallahi ban sani ba sai dai na fi tunanin ko yar uwar su ce dan ga kama nan ta bayyana har kan jazlan ". Najiba ta bata amsa. Mama Hasiya ce tace. " Eh itace mahaifiyar sa,wannan likitar jiya ya zo ai sai dai bai daɗe ba ma ya fita,bata faɗa mini ba amma ko makaho ya shafa ya sani,bare ma yan uwan sa sun nuna komai,saboda naji wata har cewa take yi Jazlan mai kama da Granul jiya.😂 ( Granny )ku ke cewa da turanci ko me na manta,na san dai kaka yake nufi,kuma ma daga baya sun faɗa mini danganta kar su" Ta kai ƙarshen zancen tana ɗan sakin murmushi. Idanu Nadiya ta zaro bakin ta sake ba ita kaɗai ba har Najiba sai da ta zaro nata wani irin mamaki yana kamata ta da al'ajabi sai yanzu ma ta Hango tsantsan kamar shi da ita.Haka ma Raliya itama ta hango. Dukkanin su mamaki ya kashe su musamman su da suke sun saba da ita saboda ɗan zuwa asibitin da Nadia ke yi tunda duk ta zo ita take tarar wa. Numfashi ta sauke tana rufe idanun ta da suka fara ɗan saki sai dai har yanzu mamaki ne danƙare da zuciyar ta ya za'ayi ace Dr Abida itace mahaifiyar Tanim ita tunda take bata taɓa jin yayi zancen umman sa ba,ko wani abu da ya dangan ce ta,To ko dai basa tare,Ko akwai wani abu tsakanin su,Ta tambayi zuciyar ta,ita ta bawa kan ta amsa da cewa ai da ba su zo nan tare ba a ɗazun.To me ma ya kawo shi asibiti mutumin da ya ce bai haɗa komai da Jazlan ba,lallai ko da ina kusa ko inuwar sa bazai gani ba amma zai dawo na sani Indai har ya cika mara kunya zai dawo.Ajiyar zuciya ta sauke tana jin wasu hawaye na silalo mata sai dai haaka kawai Tausayin Dr.Abida ya soke ta bata san dalili ba.Dan Babbar jarabawa ce irin wannan yanayi da ɗan ta yake ciki sai yanzu ta tuna tana yawan yin wasu maganganu da ke nuna damuwar da take ciki da kuma abinda ke zuciyar ta lallai tabbas akwai wata a ƙasa bayan halin da Tanim yake ciki,chan ta matse masa ko me ne ne ma yayi ajalinsa mugu azzalumi dabban mutun da bai san darajar mace ba Allah sai ya saka mini. Hawaye ne suka silalo mata inda tayi sauri ta goge gudun kar Mama Hasiya ta gani wadda take ta fama dasu su ukun Dan ita kan Mama Hafsatu ta koma gefe sai faman ciye ciyen ta take yi so take sai taji cikin ta babu ƙofa tun da Allah ya tsaga ma ɗiyar ta ƙashin arziki dan haka dole ta ci ta ƙoshi a cewar ta. Ita kan ta ta yi mamaki matuƙa dan basu taɓa haɗuwa da ita sai jiyan. Ƙamshin wani mahaukacin turare ne ya yi wa ɗakin sallama kafin murya ta cika ɗakin cikin izza da ya ƙunar fuska.Ko mafarki ta tashi zata iya gane fuskar ta tana cikin masu kawo kayan lefen Nadiya dan zata iya cewa itace mai hurar hanta a wajen ta gane ta tsafff dan haka ya sa ta miƙe tana washe baki tare da ajiye filet ɗin farfesun kaji da ta iba cikin kayan da yayyen Tamim suka kawo yanzu. " Maraba la le maraba lale da manyan baƙi". Ko kallon ta bata yi duk da taji ta ganin haka ya sa Mama Hafsatu ƙara furta Hajiya " Ga gurin zama ". Tayi zancen tana bata inda ta ɗaga. " Malama ba gurin ku na zo ba,nazo ganin suruka ta ne ". Tsitt haka ɗakin yayi shiru kamar an ce kowa ya kame bakin sa Dukkanin su basu ji daɗin abinda ta yiwa Mama Hafsatu ba saboda ita kaɗai ce ma ta kula ta da nuna alamar sanayyya,duk da itama Najiba sun gane ta. Komawa Mama Hafsatu tayi jiki a sanyaye ta cigaba da shan romon ta duk da ta ji haushi sai kawai ta share zancen. Zama tayi bakin gadon tana ƙare ma Nadiya kallo Wadda ta ke Binta da kallo itama daga kan kujerar da take zaune. Murmushi ta yi ta ce " Nadiya Barka da arziki ashe an sauke kayan nauyin nan,Allah ya bada lafiyar shayarwa ya kuma raya muna ".Ta kai ƙarshen zancen tana ɗan waigen Jazlan da ta hango hannun Raliya. Ameen Dukkanin su suka amsa har Nadiya ɗin sai dai fuskar ta ta kasa saki duk da ta matar a sake take. Fahimtar hakan ya sa Raliya ƙara ruƙe Jazlan a hannun ta dan taci Alwashin bazata taɓa bata shi ba.Sai dai ta gama zancen ta ta wuce dan taga babu alamar rashin mutunci a tattare da ita,kuma ma haka kawai bata yarda da ita ba. " Sunana Jamila,Suna kirana momy Nice mahaifiyar Tanim Na ga kamar kina mini kallon rashin sani Nice mahaifiyar sa". " matar uban sa ". No wonder Raliya ta gyaɗa kai, jin furucin ta na karshe, tana ƙara jin ƙudurin ta na ƙin bada shi,dan har sun fara tunanin to itafa Dr Abida ya zata zamo mahaifiyar sa bayan ga wata kuma sai da ta ƙara furta matar uban sanann suka samu dai daiton tunanin su. " Muga Jaririn " Ta ƙara yin furucin ganin Raliya ta masa riƙo na gammm Mama Hasiya na batun yin magana ta ce Raliya ta bata RALIYA tayi karaff ta ce " Bacci yake yi sai dai ki gan sa a hannu na ". Ta yi furucin ba tare da ta kalli kowa ba sai dai idanun ta na kan Jazlan ɗin dake sharar baccin sa hankali kwance cikin natsuwa. Ran Hajiya Jamila ya ɓace matuƙa sai dai bata nuna a fuska ba ji take kamar ta je ta shaƙi wuyan Raliya ta nuna mata ainahin ita Wacece,abun da take ji tayi ƙoƙarin haɗiyewa,A hakan dai ta shanye komai baƙincikin ta bai wuce ƙudurin da ta zo dashi ba zai tafi a banza. " Ok to bari na zo na duba shi nan " Tayi furucin zuciyar ta na kai wa wuya,da ƙoƙarin haɗiyewa. Miƙewa tayi cikin tafiyar ƙasai ta ta tsaya kan RALIYA tana ƙarewa Jazlan kallo.Murmushi ta saki bayan ƙare masa kallo sannan ta furta " masha Allah,Allah ya raya muna,Shin wane suna uban na sa ya ba shi ". "Uwar sa dai,Muhammad ne sunan sa,Jazlan muke kiran sa" RALIYA tayi saurin bata amsa tana jin kamar ta ce masa ta fita sun gode Dan haka kawai jikin ta da Zuciyar ta sunƙi bata natsuwa da ita. Shegen Murmushi Jamila ta saki sannan ta furta " Ashe sunan sa yaci Allah ya raya muna Jazlan suna mai daɗi ". A wannan karon Raliya dai bata tanka ta ba sai ma wayar ta sa ta Fiddo ta fara danne danne. Sallama ta musu ta fice tare da Ajiye musu ledar da ta shigo da ita,kuma sai ta kai ta gaban RALIYA ta ajiye tana bin Raliya da wani irin kallo tana sakin murmushi. Ko kallon ta Raliya bata yi ba har ta yi sallama da su ta wuce. Tana fita RALIYA ta ja mugun tsaki da ya garwaye ɗakin wanda duk sai da suka zuba mata ido karo na biyu.Kai Najiba da Nadiya suka girgiza suna sakin guntun murmushi kaɗan daga cikin Bad side na RALIYA kenan bata ɗaukar raini ko na mene sannan idan bata yarda da kai ba komai shige matan da zaka yi bazata ta ɓa yarda da kai ba ta fi su zafi matuƙa,yanzu da Allah bai taƙaita ba sai ta yaɓa mata maganar da sai ta tsaya mata a rai,amma sai Allah ya kawo ƙarshen abun ya kora musu ita da wuri dan ko su basu wani yarda da ita ba zaune kaɗai suke da ita sun matsu ta wuce haka kawai suke jin tsanar matar da kuma ƙyamar ta suke yi,suke kenan ma RALIYA wani irin warin ta ma take ji,haka take jin shi kamar ruɓaɓɓiyar gawa idan ta matso ta, dan da ƙyar take shaƙar numfashin ta tana ƙoƙarin haɗiyewa ne kawai take yi kuma tayi mamakin da su basa jin shi ko kaɗan Dan bata ga alamar wani abu akan fuskokin su ba. " RALIYA me ya sa zaki mata haka ". Mama Hasiya tayi furucin ba tare da Damuwar komai ba tun da ta san halin RALIYA ɗin. " Umma nifa kwata kwata ban yarda da wannan mata ba,wallahi,kinji qarni da warin da take yi kamar na ruɓaɓɓar gawa,wallahi umma da ƙyar nake shaƙar numfashi na da ta jima dana bar muku ɗakin,Shi ya sa ma na hana mata Jazlan sannan ban ma dai yar da ita ba zuciya ta bata aminta da zaman ta mutuwar kirki ba,da shigowar ta baki ga yadda ta shigo ba da wulaƙanci tayi sallama baki ga abinda ta yiwa Mama Hafsatu ba,Ai gwara a nuna mata ba ita kaɗai ce Ta iya ba ". RALIYA ta kai ƙarshen zancen tana ƙara jin Haushin ta. Mama Hasiya guntun murmushi kawai tayi tana furta " karki ƙara mata haka Raliya tana da iko kan Jazlan kinji ". Kai RALIYA ta gyaɗa mata badan ta ji zata iya ba dan ko yanzu ta dawo zata hana mata shi koda kuwa yana kan gadon sa ne. Mama Hafsatu kuwa Ɗan murmushi kawai ta saki bata ce komai ba. Su Najiba ma Murmushin suka ƙara saki. Najiba ce ta ce " Wallahi Nima da naji warin nan kawai shanye wa ne nayi " . Alama Nadiya ta mata da itama ta ji. " Ashe bani kaɗai bace,Har Umma take faɗin a bawa Wannan ƙazamar matar ɗan mu ". RALIYA tayi furucin tana ɓata fuskar ta da ta cika saboda tsufan da cikin na ta yayi tayi kyau ko ina ta cika ciff. " Sannu masu ɗaaa ohh ni Asiya,Allah ya shirya min ke Ralele ". Mama Hasiya tayi furucin tana sakin murmushi.. Kunya RALIYA ta ji hakan ya sa ta dariya tana rufe fuskar ta. Sukan su Nadiya Dariyar suka yi. Dan take sun manta da zancen Jamila inda suka fara taɓa fira a hankali a hankali Dan dama suna ta Allah,Allah kar ta yi zancen mutuwar Su Najiba ɗin dan har yanzu nasu sanar mata ba sun zata shiga tsoro sosai.Shi yasa dukkanin sun kasa maganar a gare ta,ko wani ya zo suna kaffa kaffa kar ya taɓo zancen. A ɓangaren Hajiya Jamila kuwa tana fita rai ɓace ta faɗa motar ta sai dai bata tayar ba sai dai ta busa hayaƙi tasha kusan kara biyar sannan ta tada motar wata unguwa ta nufa maimakon ta su. Unguwar sabon gari ta nufa dai dai wani tangamemen gida da gudu ta shiga gidan bayan yin horn aka buɗe mata gate. Cikin wani zafin Nama ta faɗa cikin gidan kasancewar bata da shamaki da komai na gidan.Ƙaton Falon ta faɗa babu sallama sai dai ganin hakan bai sanya ta jin ko ɗar ba sai ma wata hanya da ta bi cikin sauri Dan ta san tana nan,ta iya yuyuwa ana chan ana bajewa.Kamar yadda tayi tunani hakan ce ta kasance kuwa dan Jaruma ce da wata ƙatuwar mata da ganin ta irin shaggun karuwan nan ce a kan gado sai masha'ar su suke yi duk sun cika ɗakin da Nishin azaba. Zama tayi ba tare da ta ce musu ƙala ba dan bata cikin yanayin yanzu. Bayan sun gama ne sannan Matar da take mai suffar kilaki itama ta furta " Yanzu ake ganin ki Uwar harka,Allah ya sa dai lafiya naga kamar ranki a ɓace" ? Cikin ɓacin rai Ta furta " Ni Jamcy Uwar harka yarinyar chan ƙanwar Matar Tanimu zata wulaƙanta ban san yadda aka yi ba naji na kwaɗai da son yarinyar gata da gani yarinyar ce shakaf ɗin ta,da ina kusa da ita har ji nake kamar na rungumo ta amma shegiyar yarinyar nan ta kasa ko kallo na,ga shirina da ta ruguza, wallahi na so na kawar da jinjirin nan,Kinga da garin gubar nan a jaka ta sai na shafa wani a hannu na ina karɓar sa sai na shafa masa a fuska wanda kafin awa ya galabaita sai mutuwa ya koma hanyar da ya fito.Amma ko yanzu ba komai na ma fasa aiwatar da shirin Zan cigaba da Bibiyar har yaron ya dawo hannu yana tasawa sai mu ɗaura a harka mu a bawa ƙungiya shi ".Ta kai ƙarshen zancen tana sakin murmushi. " Kai Wallahi yarinyar nan na ke gani a ido na " Tayi furucin tana Lumshe ido. Kai Jaruma ta gyaɗa tana furta " ai dama sai da nace ki barshi haka kar ki yi komai yanzu kika matsa,Yanzu ai Gara mu raine sa shima kawai a bazashi a harka ".Tana zancen tana shafa wuyan Jamcy aiko take kamar jira take yi ta fara gantsare wa sai komai ya chanza musu nidai na fice daga ɗakin. A ɓangaren Tanim kuwa yau ya tashi da wata irin muguwar kasala a jikin sa,ga zazzaɓi yana neman rufe sa. Ga saƙon da yake ta shigo masa na ñumban America a wahtsapp wanda ko rantsuwa yayi matar nan ce da ya ajiye a chan waje Dan saƙo ne dake nuna kotu na neman sa daga nan da kwana biyu har suka ce idan bai zo zasu Turo jami'ai su tafi da shi dan haka yake cikin tashin hankali ya ma rasa wane irin tunani Zai yi . Dan haka ya yanke shawarar tafiya nan da kwana biyu ya ji dalilin neman sa, Dan ya san tabbas ita ce ta ta maka shi kotu to akan wane dalili Auren na su da dama na yarjejeniya ne tun asali ai mai take nema da wannan tunanin ya bar zancen a cikin zuciyar sa. Saƙon farko ya ƙara dubawa shine inda suka faɗa mishi abinda ake ƙarar shi " Yin zamba cikin aminci ".Mamaki ya kashe shi matuƙa sai dai shiru yayi bai san da zai yi maganar ba,ya san koda wasa bazai tun kari Shanty ba dan yau ma sai da suka yi rigima da ita akan yadda yake shasshare ta Dan yau ma haka taso su kasance kamar jiyan dan daren gaba ɗaya sun yi maƙalƙale da juna ne.Shi ko ƙarfin Hali yake yi shi ya sa yanzu ya kauce mata dan abun ya fita ransa kwara kwata yanzu ciwon da ke cin jikin sa shine abinda ke damun sa matuƙa. Wani gidan sa na hutawa ya nufa bayan fita daga gidan da shanty take. Ƙarar wayar shi ce ta sanya shi miƙewa daga kwance da yake ɗagawa yayi ganin mai kiran ɗai daga cikin yan ƙungiyar sune shi har ya manta da su tun qarin da ya shaƙo gurin su. " Lallai Tanim duk halin da muke ciki kai ka jefa mu a iya binciken mu matar ce ta haihu, Dan haka dole abun cikin nan zai zamo abun kwakwaran mu zamu bar shi ya tasa kafin mu ƙwato shi mu cigaba daga inda muka tsaya zuwa lokacin mun warke daga lalurar wari da ta same mu,da kuma rashin riƙe kashin da ya same mu lokaci ɗaya zamu dawo ta kan ka kaima baka isa ka fita daga wannan yanayi da muke ciki ba dole ka ɗan ɗana kaima, Dan haka sai mun buɗe ka buɗewa mafi muni wadda ko zama sai ya gagare ka ".Inda aka kai ƙarshen zancen ana gaɓɓatar Dariya kafin aka kashe kiran. Ƙirjin shi ne ya yi irin mugun bugawa kafin kan shi ya sara yana neman rabe masa gida biyu. Idanun da suke a rikiɗe suka ƙara rikiɗeewa waje ɗaya.Tashin hankali na bayyana ƙarara akan fuskar sa da ta mauje lokaci ɗaya. Sai yanzu ikon furta Inna lillahi wa Inna ilaiihi raji'un yake ta nanatawa bakin shi na rawa cike da wata irin razana,da nadama,Wace irin musiba ce wannan shi bai ma san lokacin da ya samu kan sa ciki ba,me ya ke shirin faruwa da ni.... Yayi furucin Wasu hawaye ba wanke masa fuska. Haƙƙin ta ne.ya ƙara furta wa Idanun jajjir. Muhammad Nake ji duk raba igigiyoyin da nayi nayi abanza,Nadiya rashin jin maganar ki zai jefa yaron da na fara ƙauna a jiyan nan cikin musiba me yasa baki bi umurni na ba me kika yi mini kika hana Ni zubar da cikin Nan.Tausayin yaron ne ya farmasa lokaci ɗaya hawaye ne suka ƙara silalo masa.Inda A hankali ya furta ta ya zan kare ka,taya zan kare ja daga sharrin su,Ni tawa ƙaddarar ce bana son ta shafe ka,bana son ta goge ka ban so zuwan ka duniya ba,amma qaddara ta a riga fata.Allah ya kare ka Jazlan.Ya kai ƙarshen zancen a sanyaye.Kasancewar yan uwan shi da suka yi masa Barka haka suka yi ta kiran Allah ya raya Jazlan yana karɓa musu jiki a sanyaye... A ɓangaren Shanty kuwa yau ta haɗa party na musamman murnan Sakin da Tanim yayi wa Nadiya domin kuwa tana da labarin komai a hannun ta.Dan haka murna kamar ta tada kan ɗan jariri sai ta haɗa party a cikin gidan ta tara ƙawayen ta da samarin su aka baje nan ana ta hura hayaƙi da baɗalaa ana raye raye.Duj da taji Haushin Zuwan Jazlan ɗin amma yanzu ita bata tashi take yi dama da uwar shi take kishi kuma an raba chan ta matse musu.... Hmmmmmmmm SHANTY kenan.a Kaa ce yaro bai san wuta ba sai ya taka...😒 Jamcy😭 Jaruma😭 Tanim😭 MUJE ZUWA...🚴🚴🚴✍️✍️ Yadda kuka ga update shiru haka online shi ru bansamu hawa online ba kwana biyu.Bana da lafiya...🙏🙏🙏 Yau ma page biyu na haɗa muku✌️ Ta yuyu daga wannan page sai bayan sallah in Allah ya haɗa mu.🙏🙏🙏🙏Allah ya sa muga Ramadan Lafiya,mu fara sa lafiya kuma mu kare sa lafiya.Ameen. Daga Alƙalamin✍️ Fa'eeh BG💋 Firstlady🙌 GIMBIYAR TASKIRA👑 Like,Share,Vote and react. Masu @Arewabooks Kuyi searching kuyi following ɗina a can. Fa'eehbg Masu @Wattpad Kuyi searching kuyi following ɗina a chan. Faiza murai. Whatsapp kuna iya tuntuɓa ta lambar waya ta kamar haka. 08069059746 Chat only pls 🙏 *YAR MUTAN ZAMFARAWA CE*✌️🤳 *_Typing_*📱 *TEAM TAURARI HUƊU* ⭐⭐⭐⭐ https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y _Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chan zaku samu cigaban update.Farkon labarin masu neman sai a mun magana a numban dana sauke ƙasan wannan page, Dan samun document.☝️_ *🌸RAYUWAR MU AYAU🌸* Ƙarya ko sakin Aure Gajeren labari Na Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim *✍️TEAM TAURARI HUƊU*✍️ ⭐⭐⭐⭐ _Fa'ee BG_ *RAYUWAR MU A YAU* _Matar Habibi_ *NIKEH DA IKO* _Haandy_ *NIKKAH ( MARRIAGE FOR RENT )* _Oum Amjad_ *RAYUWAR JANNAH* 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda Allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _*Daga marubuciyar littafin*_ _*A Mafarki Nasanta*_✍️ And now _*Rayuwar mu a yau*_ P.36 Haka suka watse partyn bayan an sha an busa hayaƙi anyi baɗala iri iri sannan kowa ya kama gaban sa,wanda har zuwa lokacin tanim bai dawo ba a taƙaice ma bai kwana gidan ba. *Nadiya kuwa Jiki nata samun sauƙi dan asibiti sun ƙara mata kwana ɗaya saboda bp ɗin ta da ya ƙara hawa.Domin abinda ya faru bayan dawowar su Hjy Jamila a asibitin tare da ƙawarta Jaruma da tace tana son ganin jaririn sai suka kwasa suka tafi bayan gama aikata ɓarnar su..Bayan gama ganin jaririn Da Raliya ta ƙara riƙewa ƙamm suka yi musu Addu,a da Jaje na Dawowar su Nadiya ɗin daga mutuwar da aka zata sunyi a farko wanda dukkanin su suke ɓoye mata sai gashi sun zo ita da ƙawar ta sun hargitsa komai dan ta samu labarin komai bayan Haihuwar Ɗan da sun san da cikin da tuni sun fitar dashi sai dai ya mamaye su.Duk da warin da ya sha musu kai a ɗakin basu nuna musu komai ba sai Rarrashin Nadiya da Najiba ta cigaba da yi cikin tausayin ta tana nuna mata abun farin ciki ne hakan, ba kowa Ubangiji yake bawa wannan damar ba da haka ta samu ta rarrashe ta,Su Mama Hasiya dai da Mama Hafsatu idanu kawai suka zuba musu,sai daga baya suka saka baki ganin taƙi samun natsuwa. Haka ma basu wa su Hajy Jamila komai ba na daga wani baƙar magana kamar yadda su suke ta ɗan jefa zance,haka su Jaruma suka wuce kamar iska kowace na rangwaɗa tana karairaiya sai dai duka hakan bai wani karɓar su saboda sun wuce irin wannan lokacin duk da yanayin na su ya bayyanar da barikin su ƙarara, Dan yadda suke tauna cingum a hanyar ma abun kallo ne. *** A ɓangaren Tanim kuwa ya yi tafiya ƙasar waje kamar yadda kotu ta aiko naiman sa gudun abun da kan iya zuwa ya dawo.Ba tare da yayi shawara da kowa ba ya tafiyar sa duk da ya so ya yi zancen da SHANTY sai dai taƙi bashi dama hakan ya sa ya tafiyar sa dan ya san koda ace ta saurare sa akwai rigima sai yayi nadamar faɗa mata.Haka ya tafi cikin ɗarr. Da zuwan shi kuwa aka yi zaman kotu inda kotu a ƙara gabatar da ƙoƙarafin da matar ta sa ta shigar a cikin kotun na zamba cikin aminci da ake zargin sa da aikawata. Tun da aka fara jero masa bayanin kamar yadda ta lissafa ma kotu ya sare ma lamarin turawa domin kuwa kai tsaye ta sanar wa da kotu cewa " Tun da Aka yi Auren su bai taɓa tarawa da ita ba,sannan kuma ya tafiyar sa ya barta duk da yardar da ta masa,yana neman wasu mata a ƙasar sa,da ma wata ƙasar saboda duk tana Bibiyar sa tana sane da abin da yake yi ta bashi dama ne taga ko zai gyara. Haka yayi shiru bai iya kare kan sa ba cikin mamaki domin bai shirya ma komai ba ko lauya nasa bai nema ba dan haka ya zuba ma sarautar Allah ido har aka yanke masa hukunci na zube mata maƙudan kuɗaɗe domin duk wani abu da ya tara anan ta kwashe komai kamar set up ne suka yi da kotun, cikin dukiyar sa kwata kawai ya tashi da ita duk an miƙa mata su,tare da saka shi Jail na wata ɗaya.Sai dai cikin kissa da ƙara son ƙwaƙwalar sa kiɗi ta nema masa rangwame mai haɗe da riba,inda aka janye zaman gidan kaso ɗin bayan ya zube miliyan goma da ta ce ya bada ta yafe masa,haka kuwa aka yi.Yanayin da yake ciki

Chapter 31 of 39