Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da dawowa ba yayo tafiyar bazata ga iyalin nasa.Domin tasan Hajiyar Dubai tace mata sai ya kusa wata biyar kafin ya dawo yanzu. Fatan ta kawai Allah yasa kar Asamu matsala Asirin ta ya tonu ba tare da ta samu ta mallakar Jamil ɗin ta ba. Mintuna ƙalilan sai gata ta fito ta sha wani uban ɗauri wanda ya zauna mata har a goshi kamar dai ture kaga tsiya.Sai uban ƙamshi take zubawa.ƙarar takalmin ta kuwa sai bada sauti suke yi kasancewar su masu tsini Mayafin ma nata a hannu yake . Hamdala tayi ganin Alhaji Ahmed baya nan da alama fita yayi domin babu motar sa a gurin wadda yake ɗan yawan fita da ita mai kyau ɗin sosai duk da suma sauran motocin masu kyau ne. Da sauri tsohon nan ya buɗe mata yar ƙaramar ƙofar yana furta " Allah ya taimaki Hajiya ƙarama Alkhairin Babu abinda kika yar na Alherin Iyayen ki,Allah ya yi Miki Albarka ya barki da yallaɓai Jamil ". Haka yake ta jera mata Addu,oin haɗi da kirari har sai da ta damƙa masa yan kuɗaɗe sannan ya juya kamar kullum bakin sa washe yana zabga godiya. Babu ɓata lokaci suka bar unguwar cikin wata danƙareriyar mota. Najiba ta kasa haƙuri ganin yau ya chan za mata har wani gyaran gashi aka yi masa na classy guys yayi wani irin kyau cikin suturar da Tanim ya bashi. Ga wata irin lafiyayyar mota da ya zo da ita ɗin yau wadda tana iya rantsewa sau uku kawai ta ganta kan titi sai kuma yau da ta gan ta ga Jamil. A hankali cikin wani irin farin ciki da ya dabaibaye ta wanda ke ƙara tabbatar mata da Jamil ɗin ta mai Arziki ne na ƙwarai. Ta furta " Ya Jamil motar nan ta mun kyau,Ni wai yaushe zaka siya mini motor Nima bai kama ta A ce matar mai Company guda ba na motoci tana tafiya ƙasa ko a kafi babur ". Wani irin burki Jamil ya taka har sai da kan Najiba ya daki gaban mota. Ɗagowa yayi da sauri yana bata haƙuri yana furta " Motar ce ta ƙwace mini My Naj I m sorry kinji,karki damu mota zan saya Miki idan munyi Aure Amma ba yanzu ba " . Kai Nadiya ta gyaɗa cikin farin ciki kafin ta fara bashi labarin ƙarya da gaskiya.Ai Hajiya tace kaza ta Dubai za'ayi kaza,America za,ayi kaza. Haka dai take ta jera masa surutun har suka isa Babban gurin shaƙatawa wanda ya amsa sunan sa domin kuwa ko kuɗin shiga cikin sa wani abu ne.Sai masu hannu da shuni da masu ƙarya ko yan ƙarfin hali. Kamar koda yaushe sai da ya kashe mata maƙudan kuɗaɗe wayen da yake jin su har cikin ransa sai dai baya da yadda zaiyi ta hakan ne kawai zai faranta mata kasancewar ta yar masu kuɗi,kuma ta hakan ne kawai zai saye zuciyar ta.. Hmmmm Jamilun Najiba kenan. Baka san kan garin ba ne.😆 Ina son Jamil Amma ƙaryar shi tayi yawa shi yasa na riƙe Dr Ammar ɗina muyi ta buga kishin da Halee (Nourah) ( A mafarki Nasanta ).🤗😇🤪💃😎 Har dare suna gurin idan anci wannan Aci wannan.Sannan bayan Sun gabatar da sallah isha'i wadda yau Allah dai ya nufa an yi sallah da wuri kan lokacin ta bayan Jamil ya matsa.Gida ya mai da ita sukayi sallama cikin ƙaunar junan su. Da sauri ta fito kamar yadda ta saba bayan ya ajiye ta.Napep ɗin ta ta haye sai ƙofar gida yana ajiye ta shige cikin gidan cikin sauri dan haka kawai yau take jin tsoron haɗuwa da wani cikin iyayen nasu bata san dalili ba wani tsoron su ne ke shigar ta har bata san haɗuwa da su. Malam Rabu'u kan sa kawai ya girgiza bayan duba ɗan agogon roba dake makale a hannun sa ganin har tara na dare tayi.Kuma ace ya mace wai yar sa ta cikin sa ta fita tare da wani sai yanzu ta dawo yawon ta biɗiɗi. Kansa ya ƙara girgizawa kasancewar yana da labarin ta, na shige da ficen ta daga nan zuwa gidan Hajiyar Dubai ɗin. Mai napep ɗin ta shine wanda ke kai masa duk wani rahoto. Haba mai okada ya zaka muna haka🧐🤨 Gaskiya idan Naj ta kama ka Babu ruwan mu 🌝😎 Alhamdulillah naji sauƙi sosai Nagode da kulawar ku yan uwa rabin jiki.Allah ya bar zumunci🤲🤲🤲 Ƙaunar ku daban take a gare ni wayen da na sani da wayen da ban sani ba. Heart ❤️ u oll guys Mutanen channel ina yin ku over 💞💞💕 Fa'eehbg ✍️ Ta kuce a kullum🤗🥰 mai neman ƙarin bayani sai ya tun tube ni ta wannan lambar. 08069059746. Like share,react,an vote pls 🙏🙏 GIMBIYA TASKIRA 👑👑 *🌸RAYUWAR MU AYAU🌸* Ƙarya ko sakin Aure Short story Labari da rubutawa Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* Daga marubucuyar littafin📚 _A mafarki nasan ta_ P.8 Da shigar ta cikin gidan direct ɗakin Mama Hafsatu ta nufa da manyan ledoji niƙi niƙi na sayayyayar da yayo mata Tarba ta samu mai kyau kamar ko da yaushe.Haka suka watse komai suka gyagije suka ci suka ƙoshi ko banza yau gidan ba,a ɗaura komai ba yana yi ya juyo yau da gobe dan wani lokaci sukan ɗan rasa abun taɓawa sai dai ke in kina da ki bawa ya yan ki.Sai dai Alhamdulillah kwanakkin nan basu rasa tuƙa tuwo sai kuma yau da lokaci ya juyo talaka bawan Allah. Allah ya ƙara rufa muna asiri duniya da lahira,kuma nufi ƙarfin buƙatun mu.Amin. Sun daɗe suna fira Har ta basu labarin motar da Jamil ya ce zai siya mata cikin farin ciki sai dai ta Bar baya da ƙura domin kuwa Nadiya da Mama Hafsatu basu ji daɗin zancen ba.Kowannen su da abun ya kwana acikin zuciyar sa. kwance yake shiru akan yar ya ƙusasshiyar katifar sa ya lula duniyar tunani ta ina zai samu kuɗin siyawa Najiba Mota shi da bai da ta kan sa ma ta shiga jama'a,gashi Najiba na so ga kuma maganar iphone 16 da yayi mata alƙawari wanda yanzu ya riga ya kai ƙarshen zancen zai yi duk yadda zai yi ya sa ya mata ita.Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yana sauke numfashi kafin ya kalli wayar sa dake gefen sa wadda ta farfashe,Sai Ringing take yi Numban Najiba ce da yayi saving da Baby Naj.Zubawa wayan idanu yayi kamar Najiba ce a gaban sa kafin a hankali ya sauke numfashi yana kallon wayar da kiran ya yanke wani na sake shigowa.Ɗaga kiran yayi sannan ya furta kamar mai alaman yana cikin bacci an tashe sa " Najiba ba ki yi bacci ba har yanzu,gashi kin ya da ni ina mafarki na mai daɗi tare da ke Beb "Yakai ƙarshen zancen yana buga wata ƙatuwar Hamma dake nuna baccin dai yake yi da gaske. Murmushi Najiba ta saki tana furta " Ya Jamil na kasa bacci ne farin ciki ya cika mini zuciya na zancen motar nan da kayi mini alƙawari shine na ce bari na kira ka muyi fira ashe har kayi bacci ".Ta kai ƙarshen zancen tana yin ƙasa da murya cikin farin ciki tare da kallon Nadiya da tayi bacci da waya maƙale a kunnen ta da alama tana cikin wayar bacci ya kwashe ta. " Haba My Naj sai kace wani babban abu ne ita motar Ni ko jirgi kike so zan iya saya Miki ƙaunar ki daban take a raina babu abun da bazan iya yi Miki ba a rayuwa ta har rayuwa ta zan iya badawa kan ki ".Ya kai ƙarshen maganar yana ɗan kauce fuskar sa daga kan Gariti da ya farka ya zuba masa idanu yana sauraren uwar ƙaryar da yake ta shirgawa ko kunya ba ya ji. Wani Farin ciki ne ya kama Najiba wanda ya bayyana a kan fuskar ta.Ji take kamar ta yi tsalle ta taka kan ɗan jariri.Kenan yanzu zai iya saya mini jirgi idan nace ina so ta furta a cikin zuciyar ta.Kai ta girgiza Sannan ta bawa kan ta amsa a hankali Ina Tausayin ka Beb ba yanzu zan yi zancen jirgin ba .Jamil dake sauraren ta ne yaji tayi shiru bayan yaji fitar kalmar sai ya furta A hankali " me kika ce Beb " Yayi furucin ƙirjin sa na wani irin bugu.Murmushi tayi tana girgiza kan ta kafin ta furta. " Nima ina ƙaunar ka Yaya Jamil,Allah ya mallaka mini kai ".Ta ajiye waccan maganar a gafe A jiyar zuciya Jamil ya sauke yana ɗan gyara kwanciyar sa dan baccin da ya kasa zuwan masa ya ji ya fara sauka jin Muryar ta da kuma kalmar da ta furta masa a ayanzu.Sai dai kuma zancen jirgin na ransa yana fatan karta ƙara ta da zancen dan ya fahimci ɗaukar wani mashahuri take masa duk da yake hakan ya ɗaura ta ne. Fira suka ƙara taɓawa kusan ta awa biyu wadda rabin ta duka ƙaryace ƙaryace ne ita dashi.Suna gab da yin Sallama ne ya sanar mata da maganar turo iyayen sa da yake son yi.Wani farin ciki ne ya ƙara mamaye zuciyar Najiba sai dai zuciyar ta cike take da tunanin kala kala ta yadda zata iya sanya mijin Hajiya Samira ya gana da Jamil.Sallama suka yi cikin farin ciki da ƙaunar juna.Har Asuba ta kusa babu wanda ya runtsa a cikin su kowa da tunanin yadda zai yi.Sai ana fara kirayen kirayen farko bacci ya ɗauke su dukannin su. A ɓangaren Su Malam Abdul basiɗ kuwa kamar yadda suka yi zama na biyu a jiya ɗin sun kai ƙarshen bawa Su Malan Adamu ragamar zama da ya yan na su kasancewar zukatan su suna musu wani iri suna ji kamar ba zasu iya fuskan tar lamarin ya yan na su ba.Hakan ya sa suka damƙa masa komai tare da dattijan da suke zama da su Agurin wayen da ke ƙoƙarin shiga cikin lamarin.Kamar yadda malam Abdul Basiɗ da Malan Rabu,u suka yi magana a jiya a yau ɗin zasu zauna da su Najiba a kan zancen Auren na su Dan suna son su haɗe su tare da na RALIYA .Hakan kuwa ta kasance ƙarfe tara na safe dai dai lokacin da suka san ba su isa fita ba Malam Adamu da wasu datiijai guda biyu Abokan nan su,suka buga sallama Cikin gidan.Tsaff ko ina yake cikin gidan kasancewar Mama Hasiya ta san da zancen, ta sanya RALIYA tun da safe ta kimtsa komai ta share gidan gaba ɗaya har ƙofar Mama Hafsatu ko ina tsaff sai gidan ya ƙara yin wani faɗi kin san yadda tsafta take guri ko babu siminti idan yaji shara sai kaga ya burge ka. Da farin ciki Malam Rabu,u da ya fito yanzu ya ke gaisawa da su tare da yi musu iso cikin Falon Mama Hasiya kasancewar sa gyare a koda yaushe kuma dama nan ne zasu yi zaman dan sun san halin Mama Hafsatu tsaff zata da gula masu lissafi.Ciki suka shiga tare zama suka yi akan yan kujerun dake a jiye guda biyu.Cikin minti biyu RALIYA ta ajiye musu abun tarba bayan ta gaidasu cikin ya bawa da tarbiyyar ta suka karɓa mata suna jinjina kai cikin burge su da tayi. " Ke tashi tawan Wallahi yau take sallah ".Nadiya ce ke ta bubbugar Najiba a cinya tana furucin cikin jin daɗi. Miƙewa Najiba tayi cikin magagin bacci ta tana murzar idanun ta da bacci bai ishe su ba. " Me ya faru " Ta furtawa Nadiya wadda ke tsaye a kusa da ita baki har haƙora " ke RALIYA ce ta zo tana neman mu,wai Su Malam Adamu Abokan su Baba suke son yin magana damu,da na tambaye ta sai take cemin kamar zancen Auren mu ne ''. Zumbur haka Najiba ta miƙe kamar wadda aka faɗawa wani abun tashin hankali haka kawai take jin zuciyar ta na bugawa kan zancen sai dai farin cikin ta ya bayyana saboda maganar da suka yi da Jamil a jiyan.. Da sauri ta saka hijabin ta akan kayan baccin na ta ficewa sukayi zuwa falon kasancewar Nadiya har ta shirya Mayafi kawai ta ɗaura a kan kayan jikin na ta. Mama Hafsatu suka tarar da ke ta Safa da Marwa tana jiran su dan ƙara tabbatar musu da suyi magana mai amfani kar su yadda su yi abinda zai janyo matsala a hana ɗayan su Auren Saurayin ta,kuma masoyin ta.Kasancewar Malam Abdul Basiɗ ya yi mata zancen wanda ya gama sa a tsorace dan jikin sa har wani rawa yake masa wanda yake jin sa cikin naman sa.Da ƙyar dai ya sanar da ita a taƙaice sai dai ta nuna farin cikin ta saboda sanin da tayi gaba tayi gare su dan dama abun da take jira kenan har zagaye tayi akan hakan.Shi yasa ta nuna farin cikin ta a fili da zuciya.Malan Abdul basiɗ dai bai bi takan ta ba ya ficewar sa inda shima ya shiga ɗakin na Mama Hasiya. Ficewa suka yi gaba ɗayan su inda ta bi su da kirari irin wanda ta saba. NADIYA ce a gaba cikin farin ciki tayi Sallama tana faɗawa cikin ɗakin.Najiba kuwa tsaye tayi kamar yar kazar da ƙwai ya fashe ma a ciki zuciyar ta na wani irin buagawa tana ji kamar kar ta shiga Dan haka kawa take jin tsoron haɗa idanu da mahaifin na ta malan rabu'u.Idanu ta rufe da ƙarfi tana sauke Numfashi kafin ta faɗa ɗakin cikin sallama ƙirjin ta na wani irin bugu.Ƙarewa falon kallo tayi tana ta zuba idanu taga inda zata hango mahaifiyar ta ko RALIYA sai dai babu ko ɗayan su a gurin.Mayar da hankalin ta tayi a kan su Malam Adamu sai dai idanun ta ba akan kowa suka faɗa ba sai a cikin idanun Malam Rabu'u mahaifin ta Wanda ya zuba mata idanu kamar yaga sabuwar halitta.Kan sa ya sauke daga kallon ta yana sauke Numfashi.Kai ƙasa ta gayar da su bayan ta ƙara buga wata sallmar cikin tsoro " Ina kwanan ku ".Ta furta jiki a a sanyaye Haɗa baki sukayi suna amsa gaisuwar kafin a hankali ya samu guri ta zauna kamar yadda Nadiya ta samu guri ta zauna a gurin.Buɗe taro malam Adamu yayi da Addu'a kafin a hankali ya fara da zancen sa " Najiba,Nadiya,Muna son jin idan kuna da mazajen da kuke so dan atsayar muku da su ".Eh muna da " Suka haɗa baki kai tsaye su duka biyun.Kai malan Adamu ya gyaɗa kafin ya bawa malam Amiru dama yayi magana cikin ɗai daga cikin dattijon da suka zo tare." Masha ALLAH Kuna Iya faɗa musu su Turo sai dai kuma ke Nadiya Mahaifan ki sun Miki Miji kasancewar shi wannan da kike so sunyi bincike a kan sa ba yaron kirki ba ne, Dan haka sun yanke shawarar Aura Miki Malam Sayyid na Islamiiyar ku,saboda ya zo ya nema kuma an ba shi kasancewar sa mutumin kirki,ina fatan zaki yiwa iyayen naki biyayya ki rabu da Tanimu Ni kaina sheda ne ba yaron kirki bane "Shiru yayi bayan ya kai ƙarshen zancen yana kallon Nadiya wadda ta zuba ma sa idanu kamar bata gane inda zancen na sa ya nufa ba.Sai kuma ya ɗan saki Murmushi yana furta " Najiba kuma zamu binci na ki idan iyayen sa sun zo shi kenan Allah ya tabbatar Da Alkhairii. " Wai me yake faruwa ne,me nake shirin ji " .Mama Hafstu dake laɓe bakin ƙofa tayi bururun ta faɗo cikin ɗakin Cikin tashin hankalin abun da kunnuwan ta suka jiye mata kan yar Tata.✍️ Ayi haƙuri ina fama da nauyin idanu ne shiya sa kuka ga wannan Page Babu yawa.🙏 Share fisabilillah 🙏🙏 🌸*RAYUWAR MU AYAU*🌸 Ƙarya ko sakin Aure Short story Labari da rubutawa Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _Daga marubuciyar littafin_ _A mafarki na santa_ *G.T.W*👑👑 P9. Dukkanin su zubawa mama Hafsatu idanu sukayi cikin mamakin ganin ta Dan ba su yi tsammanin ganin ta yanzu ba.Ƙara maimai ta zancen ta tayi tana harare2 tare da ɗaura wani zancen tana furta.. " Wallahi ba zata saɓu ba wai anyi wa uwar ɓarawo sata,wannan zancen dole a mayar dashi yadda yake domin,ya ta ba zata taɓa Auren talaka ba,yarin ya da zubin matan manya sannan a ce akaita,gidan ƙanana wallahi ba zata taɓa yuyuwa ba duk ma munafukin da ke wannan ƙulle ƙullen dole ya san abinyi Dan ba zan lamun ta ba yawwa ". Haka take fitar da zancen babu ko tsayawa hararen tujara da masifar da ke cin ta lokaci ɗaya cikin rashin shakkun mijin na ta da kuma ɗan uwan sa da kuma su Malam Adamu dake kallon ikon ALLAH sake da baki.Shirun da tayi ne ya sa malam Amiru sakin guntun murmushi yana sauke kan shi ƙasa jin da tsufan shi da gemun shi na sunnah an kira shi da munafuki duk da yasan tabbas ya san ta san Muryar shi ta ji zancen shi. A ɓangaren Malam Abdul Basiɗ kuwa wani irin rawa jikin shi ya ɗauka anan gurin ba zaka taɓa iya tantance abinda yake kan shi ba ganin haka ya sa malam Rabu'u da shi ma jikin shi ke rawa ya nemo ruwa yayi tofi ya bawa ɗan uwan na shi ya sha kafin a hankali ya fara sauke ajiyar zuciya sannan ya zuba mata idanun sa da suka rune sai dai bai iya furta komai ba sai ma jin kan shi na wani irin sarawa domin Hararar da take yi kamar idanun ta zasu zube haka tabi kowa da ita kafin ta yo kan shi. " Munafuki Algungunlmi kai da kai za,a haɗa baki a cuci yar ka kana kallo,to wallahi Ni bazan ɗauka gwara ma ku gyara wannan zancen ". Tana gama furucin taja hannun Nadiya fuuu ta fice da ita.Ita kuwa Nadiya sai a lokacin ne ta samu damar sauke wani irin kuka haka ta ja ta ƙi tana furta " Muje ɗiyar Albarka,Share tarin dolaye ". Haka ta sa ta gaba suka fice daga ɗakin tana jan mugun tsaki wanda ita kan ta Najiba dake gurin ta ji shi har ciki zuciyar ta ga zantukkan da suka tsaya mata arai wani iri take ji a cikin zuciyar ta take jikin ta yayi sanyi domin zantukkan na cin mutunci ga iyayen na ta abun ya taɓa.Musamman da ta kalli fuskar malam Abdul Basiɗ taga yadda idanun shi suka sauya da na mahaifin ta.Haka ma Raliya da Mama Hasiya da suke jin komai aɗaki rayukan su a jagule suke.Raliya kuka take haiƙan kamar zata shiɗe cin mutuncin da aka yi ma mahaifan su abun ya taɓa mata zuciya wani irin ɓacin rai ne ke taso mata sai dai bata da yadda zatayi ne da tsaff zata ciwa kowaye mutunci duk da bata da fitina. A haka ta sauke ajiyar zuciya tana fatan wannan lamari ya tsaya nan. " Toh Magana ta ƙare ko,sai wani zaman malam Abdul Basiɗ Ayi ta haƙuri ". Malam Adamu yayi furucin cikin Tausayin su ganin yadda suka zuba idanu basu iya yin komai wanda ya tabbatar musu da akwai lauje cikin naɗi dan babu yadda za,ayi suna kallo mace na musu irin wannan cin mutuncin sun zuba mata idanu suna kallon ta. Miƙewa sukayi suna yi musu sallama tare da ficewa daga ɗakin da barin zancen Anan a yanda suka yi shi.Dan su ba ayi macen da zata ɗaga masu hankali ba kamar yadda aka saka su jagoranci haka zasu kasa su tsare sai an samu yadda ake so shi ya sa basu nuna ma wata damuwa a kan fuskar su ba. A jiyar zuciya malam Abdul Basiɗ ya sauke da sai yanzu yaji nauyin da ke zuciyar shi ya rage.Wani irin zafi ne ke mamaye mashi zuciya na baƙin ciki sai yau ya ƙara tabbatar da ba lafiya ba,Ji bi yadda mama Hafsatu ke zuba Masifa a gaban shi ta faɗa masu mugayen kala mai. Idanun sa da sukayi jawur ya ɗan rufe jin kan shi ya wani irin sara mishi kafin a hankali ya zuba su kan ɗan uwan sa malam Rabu'u da shima na shi suke a rikiɗe ya kasa iya furta komai sai Ajiyar zuciya da yake ta sauke wa ta baƙin ciki domin rasa abunda zasu yi da Mama Hafsatu ɗin babban ciwo ne a gare su tun da suna ji suna gani tana ƙoƙarin hana su da ya ya'yan su kamar ita kaɗai ta haife su. Miƙewa suka yi suka fice gaba ɗayan su ba tare da sun kalli Najiba dake zaune gurin ba cikin ɗan shakku da tsoron da take ciki da kuma tausayin iyayen na su da ya dirar mata lokaci ɗaya.Har iyayen nasu suka fice tana zaune tana saƙawa da kwancewa bayan ta bisu da idanun ta da suka ɗan sauya itama.Babu abunda take tunani ta yadda Iyayen Jamil zasu haɗu da iyayen na ta da tana iya rantsuwa basu da wata yar shadda nan mai kyau wadda ta bata sha wanki sosai ba bare suje gidan su Jamil ɗin. Miƙewa tayi a hankali tana ƙarewa Falon na mahaifiyar ta kallo wanda ke gyare tsaff sannan ta kalli ƙofofin su da ta san cewa suna ciki ta sauke numfashi a ɓoye.Sannan itama ta fice daga ɗakin jikin ta a sanyaye.Sanin halin Raliya da mahaifiyar ta tayi hakan ya sa ta fito da sauri ta rarrashe ta,ta bata baki ko zata saki zuciyar ta dan tasan halin ta da riƙo. Bayan Najiba kawai ta gani kuma ta gane ta sai dai bata hana ta fita dan ita bata lura da ita ba.Ɗakin na su Raliya ta faɗa inda ta isko ta kamar yadda tayi zato idanun ta sunyi jazir taci kuka har ta gaji Hancin ta yayi jaa haka idanu wanda ke nuna alamar tayi kukan sosai.Zuba mata idanu tayi daga kwancen da take ta haɗe jiki guri ɗaya sannan ta Zauna a hankali kusa da ita tana ɓoye hawayen da ke ƙara silalo mata zuciyar ta na wani irin ɗagawa ga Tausayin Mijin ta da na yar ta da take ƙara ganin kuskuren ta na fitar da ita ɗakin ta wanda nadama ke ta ƙara dabaibaye ta. "Komai zai wuce kin ji dukkanin abinda yake faruwa cikin gidan nan idanu ya ke buƙatar sakawa da Addu,a,abinda zamu yi kawai mu dage da roƙon Allah,mu na

Chapter 6 of 39