ba bata ga wani abun burgewa a ciki ba,Magana ma ta baki ta isa ba sai an cutar da mutun ba bare mutun mai daraja kamar ya Sayyadi mutun mai kamala.Haka kawai Tausayin shi ya kamata sai taji kamar ta zubar mashi da hawaye a ce ruwan da suke ajiye kusan sati biyu suna ɗoyi ga shi kowace irin najasa ta ruwa an zuba ciki ace an mishi haka mutun mai tsafta,kowa ya san ƙasƙanci ne babba wannan.
Numfashi ta sauke kawai ta juya ta koma cikin ɗakin tana jin zaman ɗakin ya gundure ta tana ji kamar ta koma ɗakin mahaifiyar ta yanzu wasu abubuwan da Nadiya ɗin ke yi suna sosa ran ta musamman yawan habaice habaice da take yi mata ita da Mama Hafsafu ɗin shiya gaba ɗaya taji ta gundura da ɗakin da mutanen dakin gaban mahaifiyar ta kawai take son ta samu kan ta sai dai yadda take da kafuwa da girman kan ta na tsiya da zuciya tana jin bata iya komawa sai an neme ta tunda ita ta Kore ta daga ɗakin,duk da ta san akwai ɓacin rai a tattare da mahaifiyar ta ta alokacin.Ita kan ta zuciyar ce ta ɗebe ta ta sanya ta fitowa ɗakin kai tsaye.Ajiyar zuciya ta sauke kafin tana ja numfashi jin wani irin sanyi da jikin ta yayi lokaci guda lamarin yar uwar Tata yanzu ya fara wuce kan ta dan har kwana ta fara yi a gidan Jamil sai dai bata tunanin akwai abinda ya shiga tsakaninsu Dan ta san irin taka tsantsan da Nadiya ɗin take yi kuma Mama Hafsatu na sane bata hana hakan ba.Sai ma murna da take yi tana rufe wa malam Abdul Basiɗ zancen tare da furta masa tana gidan ƙawar ta dake bayan Layin su.Duk da ta san cewa babu wani abun da zai yi.Dan sau biyu tana kwana a chan..
Wayar ta kalla wadda bata daɗe da sauke ta ba dan yanzu ta gama waya da Jamil ɗin ta.
A ɓangaren Jamil kuwa a jiyar zuciya ya sauke a hankali Yana sauke numfashi bayan gama wayar ta su da Najiba.
Wadda duka kan bikin na su ne suke magana akai sai kuma tunin da ta yi masa akan alƙawurran sa da yayi mata.Wanda ya tabbatar mata da yana sa ne da su kuma zai faranta mata sosai.Idanun sa ya buɗe a hankali yana kallon Gariti dake ta naɗe kayan sa da ya wanke da safe hankalin shi kwance.
" Yo to ba kai ka jawa kan ka ba,dole ne sai Najiba ba,Bama dole ka wahala ba,Na ce ka rabu da ita ka nemo yar talaka irin ka ka ƙi yanzu haka ke da daɗi mutun kullum cikin rashin kwanciyar hankali,kullum hannun ka a haɓa tunani kamar wanda ke ɗauke da ƙasa to ko tinubu baya irin wannan tunanin shi da ke ruƙe da ƙasar mu guda haba Ai wata rayuwar ta wahala ce kawai ".
Gariti yayi furucin yana cigaba da aikin gaban sa hankalin shi kwance sau ranshi kamar aɓace yake.
Wata irin Harara Jamil ya sauke masa yana bin shi da kallon baka da hankali.
Kafin ya sauke numfashi yana fara lissafin da ya ke neman saka shi hawan jini dan iya lissafin na sa yan miliyan biyun sa da wani abu ba su isa ayi hidimar bikin saboda yadda Najiba ke furta irin yadda bikin zai gudana wanda ta nuna luxury weeding take so irin na asalin wayen da suka jiƙe da naira..
Nadiya baki kyauta ba wallahi😥😥
Update ana samun shi duk bayan kwana ɗaya.🙏
Daga Alƙalamin.
Fa'eehbg✍️
👑GIMBIYAR TASKIRA👑
Firstlady 🙌🙌
A what's App channel ɗita nake update nasa.Ka ɗai.
Idan kina buƙata sai ki bibiya ki karanta.
Complete book na littafin A mafarki nasanta is available.
Masu buƙatar siya sai simini magana ta wannan lambar wayar kai tsaye.
Chat only.
*08069059746*
*🌸RAYUWAR MU AYAU🌸*
Ƙarya ko sakin Aure
Short story
Labari da rubutawa
Faiza Almustapha Murai
Daga Alƙalamin
Fa'eeh Bg ✍️✍️
Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨Amin.
Bismillahir rahmanir Rahim
💪📚📚
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_
*Aƙalaminmu ƴancinmu💪*
> >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>>
_*Daga marubuciyar littafin*_
_*A Mafarki Nasanta*_✍️
P.11
Numfashi ya sauke a hankali yana ƙara dawo da zancen da Gariti ya gama yi masa yana auna zancen.Tabbas ya san gaskiya yake faɗa masa aƙoda yaushe sai dai baya son ya rasa Najiba saboda kasancewar ta yar masu kuɗi daga lokacin da ta fahimci cewa talaka ne shi ko ƙarya yayi mata ta rabu dashi kenan kuma shi baya jin soyayyar da yake mata ta rabuwa ce ko nan gaba shi ya sa yake so a yi aɗaura Auren a wuce gurin idan aka yi Auren idan anje chan ayi duk yadda za,ayi duk da ba wani babban case bane sun riga sun zama ɗaya ne kuma sai yadda yayi domin wuƙa na hannun shi.
Miƙewa yayi a hankali yana sauke ajiyar zuciya tare da ajiye lissafin na sa da maganar zuci yana kama hanyar fita yin aikin sa dan akwai wasu Sababbin motocin da aka kawo zai wanke su duka kusan guda biyar haka.
Da idanu Gariti ya bishi yana girgiza kan sa lamarin na Jamilu na ba shi haushi sai dai kuma yana jin wani irin takaici da rayuwar da ya jefa kan shi akan wata yar mai kuɗi da shi bai da tabbacin ma ya kuɗin na su suke.
Yo dama Gariti ya za,ayi ka sani.🥱
A ɓangaren Malam Sayyid kuwa gida ya koma ya cire kayan jikin sa ya ɗauro wanka tare da alwallah
sai bayan ya fito ne ya ke bawa mahaifiyar sa labarin abinda ya faru wadda ke ta tambayar sa musamman jin yadda wari ya taso lokaci ɗaya bayan shigowar ta sa.Sai dai ya ce ta bari ya fito ya fara gusar da najasar sai ta ji komai .Kai ta jinjina tana furta..
" Allah ya tsare gaba Muhammad Sayyid ".
" Amin " Ya furta a hankali.
Domin kuwa ya ɓoye mata zancen na ainahi sai dai ya sanar mata kawai wata babbar mota ce ta yi masa wanka da ruwan kwata shine ya dawo gida ya chan za kayan da shima kan shi sun ishe shi da ɗoyi.
Sallah yayi mata ya fice fuskar shi a sake kamar babu wani abun da ya faru da shi.Ganin time na sallah la'asar yayi hakan ya sa ya faɗa masjid ya yi kiran Sallah kasancewar shine limamin masallacin na mahaifin su ko shi ko wani daga cikin yan uwan sa maza.
A ɓangaren su Mama Hasiya kuwa babu wani ɗarr sai hidimar gaban su suke yi itadah Raliya wanda duk abinda zasu tattauna sai sun sako zancen Najiba,a haɗe suke shirin,gwargwado kuma Ibrahim na Raliya akwai biɗa kamar yadda shima malam Sayyad yake da kula da neman halak na shi dan rufa wa kai a Siri ba su da wani girman kai karantarwar su a Islamiyya bai hana su neman na kai ba tare da samun abun dogaro suna buga kasuwancin su gwargwado irin na talaka wanda za'a samu na yau da gobe kasancewar dukkanin su ba wani jari ne da su ba haka ma ba su da wani ƙwaƙwaƙƙwaran aikin yi saboda yanzu karatun ma ya zama sai ɗan wane da wani ke samun aikin yi a ƙasar tamu da takardun ka sai dai ka jingine su idan baka da madafa,ka nemi sana,a idan baka da jari ka faɗa yawo tsakiyar titi ko zaman unguwa masu ɗan zuciyar nema su fita buga buga masu masu raunannan zuciya da matatta kuma a faɗa sana'ar banza wadda babu uwa babu riba,ko a koma zaman saka wa yan matan Unguwa idanu.Toh hakan ce ta kasance da su dan sunyi karatu makaranta ɗaya sun karanci business Administration ɗaya kuma ya karanci public Administration.Kuma dukkanin su sun fito da first class a kwalin su sai dai babu madogara face ta Allah.
Allah ka zamo gatan mu duniya da lahira.🤲🤲🤲
Suma su malam Rabu'u anan suka watsar da zancen na Nadiya sai dai abun na ransu,wanda yake saka musu mutuwar jiki suna gudun ayi Auren ta zo ta cutar dashi tun da sun san halin Nadiya kamar halin ta ɗaya da mahaifiyar ta bata shayi ko shakka ga rashin mutuncin ta idan ya motsa babu ruwan ta ko mai gemun sai ta iya zage shi shi tass.Ga wani irin ɗarr da zukatan su ke musu na tsoron wani zancen ya ɓullo daga malam Ahmad mahaifin Malam Sayyid.Dan idan yace ya fasa yarda da Auren lamarin na ya ƙara rikice musu.
A ɓangaren Tanim yana nan yana sheƙe ayar sa a ɗan ɓoye, kasancewar Nadiya yan kwanakkin nan tana ɗan leƙa shi su rage hasashi sai ta dawo gida wanda yanzu ta tsiro kwana chan .Sai dai babu abun da take bari ya shiga tsakanin su I yakar su shan minti kafin kuma ta kama gaban ta.
Rayuwa na tafiya yanda ya kama ta sai dai Kwanakki na ta ja, suna komawa sati,daga sati sai wata,Kuma hakan yana nuna muna kusantar ƙaburburan mu da muke yi ta hanyar kwananakkin mu dake tafiya.. Hakan yayi dai dai da cikar watannin da aka ɗiba na bikin su Nadiya.
Ta kowane gefe ana ta shirye shirye musamman Mama Hasiya da zata wanke yaya biyu farin cikin ta a koda yaushe yana tare da ita sai dai akwai giɓin Najiba dake susar ta na rashin kasancewar ta a kusa da ita.
Ta ɓangaren Ya Sayyid ma bai ƙara bi ta kan Nadiya ko wayar ta da yake ɗan takura ma ta da kira wanda bata san inda ya samu numban ba bai ƙara kira ba tun ranar da ya kira tayi mashi ɓacin ƙare dangi na cin mutunci. Kowa yana cigaba da harkan gaban sa.Haka ma tsakanin ta da Tanim Mama Hafsafu ta ce ya cigaba da hidimar bikin sa kamar yadda itama take hidimar bikin ta hankali kwance.
Sai dai dukannin su haka take kallon su kan ta tsaye da alama akwai abinda take shirya wa.
To mudai Mama Hafsatu A shirya Alkhairi.🤨🥴
Su malam Rabu'u ma hankalin su ya kwanta sosai ganin ta haƙura da zancen da tayi ba kamar yadda ta furta ba Sai Natsuwa ta shige su sosai hankalin su ya fara kwantawa.
A ɓangaren Najiba kuma har yanzu a gidan Hajiya Samira take gudanar da komai na ta gudun shan kunya.Haka ma suna shan soyayyar su wadda a koda yaushe ke ƙara ƙarfi itadah Jamil ɗin ta.
Haka ma ta ɓangaren Jamil Lamarin har ya fara taɓa shi saboda ya wan tunani ya fara rama sosai kamar shine Amaryar Najiba har dariya take masa tana tsokanar sa sai dai yayi murmushi kawai idan ya ji tana tsokanar shi da ramar, shi kan shi ya san yana wannan ramar wanda dama Dole ta bayyana a gare shi dama saboda yadda ya takura ƙwalwarsa musamman yanzu da yayi ƙundun bala ta sai mata wayar da take so ya saka a cikin lefen da zai kai a yan kwanakkin nan kamar yadda yayi mata alƙawari har da ƙarin lafiyayyar System ƙirar Company Apple yayi hakan ne domin ya ƙara faran ta ran Najiba wanda ke nuna irin zallar ƙaunar da yake mata har zuciya wadda bata da surki.
Yau ta kama Lahadi wanda ya kasance saura kwana biyar akai su ɗakunan su kuma a yau ne Jamil zai kai na sa lefen haka ma Tanim da yake ƙara jin matsuwa da ranar Auren na su dan tabbas idan har wani abu ya faru yayi mashi shamaki da Nadiya,duk da Mama Hafsatu ta tabbatar ma sa da ta sa ce,Wallahi sai dai ya bi ta yadda zuciyar shi a kullum take ƙawata masa yayi abun da ran shi ke so dan akoda yaushe wani irin ƙishin son ka san cewa da ita ke ta so masa kamar yadda zuciyar shi take ƙawace da lamarin a kullum da burin cimma iyakar sa ta hanya mai sauƙi dan kore sha'awar ta da yake ma duk wannan ya ƙin.
Hmm😥
Zazzaune suke a ƙaton Falon Hajiya Samira Hajiyar Dubai, suna jiran manyan baƙi kasancewar nan ne za,a tarbi manyan baƙin ma su kai lefe duk da maza ne ya ce shi zai kawo abun sa.Kuma hakan da yayi inaga shine dai dai domin tsegumi mata ba ƙarewa yake ba.Duk da dama koda a ce matan zasu kawo sai dai na aro kam kuma sai ya tushe maƙudden kudaɗe kasancewar classy ladies da manyan mata zai nemo kamar yadda yanzu suma ake hayar su dan cika guri da ƙarawa taro armashi.
Allah ya kyauta muna toh.🤔🧐Wai harda Dangi ana aro yanzu,yo ke fa'eeh tunda akayi hayar iyaye mene ne ba za,a iya hayar sa ba,Ai waton muna cikin wani lokaci ne mara kyau da komai ya ke ƙara tabarbarewa.Allah ya kawo muna mafita a koda yaushe.Amin Nikam nace duk da ban san wadda ta kira sunan na wa ba wadda ta bani amsar Dan maganar zuci bansan ta fito fili ba.Ashe ma ɗai daga cikin ƙawayen Hajiya Samira ne da ta gayyato.🥴😂🏃🤪
Mama Hafsatu ce zaune an chaɓa ado itama cikin wani haɗaɗɗen Less da Tanim yayi mata wanda take sakawa daga shekara sai shekara.Tayi kyau babu laifi.Haka ma duk wanda ke cikin ƙaton falon kasan ya amsa sunan sa domin ƙawayen Hajiya Samira sun mamaye ko ina duk inda ka motsa gwala gwala ne ke ta motsi.Ita kan ta Mama Hafsatu da ta yaɓa ta aro take ɗan jin kan ta sama tana yi tana shafo wuyan ta cikin dubara domin ta san idan har ta ɓata ta gama yawo dan Hajiya Samira tsaff zata ce sai ta biya ta.Dan akan kayan ta na gwal bata shayin kowa kasancewar sa kasuwancin ta na gida kamar yadda mijin ta yake da Babban kanti a Dubai.Dubai gidan Gwala-gwalai ba,a yi Miki ɓoyon kuɗi.😂
Jamil dake jin shi a wani irin yanayi tun dosowar su ƙaton gate ɗin gidan tare da wasu daga cikin Abokanai da yayo haya da manyan motocin da Ogan na sa ya sakar ma sa sabbi dal har A gama hidimar bikin.Kallon motocin yake da ke gaban su kusan biyar ta shi ce ta shida wadda yake ciki shida Gariti dukkanin su sun chaɓa a do sai dai Kowannen su fuskar sa babu annuri babu ma kamar Gariti da lamarin yake ƙara ƙuntata nashi zuciya musamman ganin yadda Jamil yake ta rama ga muƙaden kudaden da yake ta ajiya ya siye mata waya harda ƙarin system kuma kuɗin su kenan yake da su sai ya nemi wasu na hidimar bikin wanda ba su san inda zasu buga su samo rance ba tun da lokaci ya riga ya ƙure wanda shi da ta tashi ce babu uwar da za,a ƙara ba wa gidan su Najiba ɗin haka za,a rufe duk wata hanya da za,a same su har sai anɗaura Aure.Wazai ba Jamilu Rance na kusan miliyan biyu wanda kowa ya san wankin mota ne aikin shi sai ɗan tuƙin da yake wanda ba kullum yake fita yanzu ba ma saboda ta ka tsan tsan kasancewar a sirin shi ya kusa fita dan ya sha ne da ƙyar a ranar da Alhaji Ahmad ya haɗu dashi a traffic inda babu arziki ya yayi sama da glass ɗin sa fahimtar wanda ke kusa dashi.Wanda shi Alhaji Ahmed da ya juya lokacin ya dai ga an ɗaga madubin motar da duk ta kwamtse duk ta goge ta ci wuya har wani kukan tsohon ingin take fitarwa.
Sai abun ya ɗan bashi mamaki ganin yadda mai motar ya ja glass ha uban Nose mask akan fuskar sa kasancewar motoci sun samu cinkoso sai zafin da ake yi ya yawaita duk wanda ke gurin ji yake kamar ya kama da wuta saboda zafin da ake yi ga rana da ta buɗe sosai,wanda kuma ya san motar nan dai bata A.c bare ta zama akulle.
Kamar ya yi masa magana sai kuma ya share sa har aka ba su hannu suka wuce Alhaji Ahmed bai ƙara bi takan shi ba.Shi ko Jamil A jiyar zuciya yake ta saukewa zuciyar shi na wani irin bugu.Dole chan za hanya yayi saboda Tsoron sake haɗuwar sa da Alhaji Ahmed da yake yiwa Ɗaukar mahaifin Najiba...
Firgigit ya ɗan motsa bayan Ganin ya taɓa shi yana katse tunanin zucin na sa.Kafin a hankali ya sauke a jiyar zuciya.Ya fito daga motar kamar yadda Gariti ya nuna masa sauran Sun fito.Haka suka fara jidar akwatunan seti goma sha biyu tare da manya manyan Jakunkunan suma kamar set ɗaya irin manyan Ghana most go.Haka suka shigo da komai a ƙaton compound na gidan dake fitar da wani irin ƙamshi na turare da ya haɗe da ƙamshin flowers dake ƙarawa gidan armashi bayan jibga jibgan motocin dake a Parke a gefe cikin space na su.Haka suka shigo da komai inda take guɗa ta fara tashi Daga Nadiya da wasu daga ƙawayen su irin su yan ƙarya da ya'yan masu shuni da rayuwar su Najiba ke burgesu.Take ko, ko ina ya ƙara ɗauka manyan mata ana ta guɗa kun san mata akwai son ganin irin wannan kaya aƙasa.
Abun da ke cutar da wasun mu kenan,daga yan mata har iyayen na su.😥Allah ya sa mudace ya sa mu fi ƙarfin zukatan mu.🤲🤲
Kowa ka kalli fuskar sa farin ciki ne kwance sai saka ma Jamil albarka suke yi ganin irin ƙoƙarin da yayi Hakaa aka ba su tukwaici wanda suka ƙi karɓa domin dubu ɗari biyar Hajiya Samira ta fito da su gudun kar ayi kunya ganin irin kayan da aka zuba.Sai dai sun ƙi karɓa dagaske ganin yadda wata daga cikin Ƙawayen ta take musu magiya hakan ya sa Gariti da yake jin kamar ya karɓe kamar yadda shima Jamil yake jin kamar ya karɓe ɗin.Sai dai ya gargaɗe su tun kafin nan babu karɓar tukuici.Duk da yana jin yadda Jamil ke Hararar sa haka ya karɓi kuɗin ya zari Bandir uku ya mayar mata da biyu.Inda ya nuna jin daɗin sa ƙarara da nuna jin daɗin kararramar da akayi musu wanda ya shaida mata da badan ta matsa ba da babu abinda zai sa su karɓe su ana basu tukuici sai kace wasu mata.Haka dai suka yi sallama suka shissshiga motocin na su suka bar unguwar.Suna barin unguwar Jamil ya sauke ajiyar zuciya tare da saurin janyo kuɗin da ke miƙe sababbi dal da su miƙe sai wani irin haske suke fitarwa.Koda bai lissafa ba ya san Bandir ne na dubu ɗari ciff.Dariya Gariti ke ta sheƙawa ganin yadda yake ta da ƙular kuɗaɗen wanda fuskar sa ta nuna jin daɗin karɓo su da Gariti yayi.A zuciyar sa kuwa yau ya ƙara tabbatar da inda Jamilu ya kawo kan sa gida ne da bai dace dashi ba domin duk yadda yake tunanin yadda Jamil ke faɗin suna da kuɗi bai taɓa yarda ba sai yanzu da ya shiga gidan yaga yadda garage ɗin su ke cike tanƙam da manyan motoci na Alfarma ga manyan mata dake nuna abun na masu abu ne gwala gwalai to ina,ganin Wayen nan gwala-gwalai maƙale a wuyan su sai yaji kamar ya zare ɗaya ya samu na shi rabo.Sai dai hakan ba halin shi bane.Numfashi ya ɗan sauke yana sakin guntun murmushi kafin ya furta jiki a saɓule." Tabbas dole.kam ka tashi tsaye Dan bana tunanin su iya baka Aure idan bata wannan hanyar ba,Sai dai ba haka na na so ka zo ba tun da har tana son ka da a siffar ka kaje mata ta yuyu ta dalilin soyayyar ka mahaifin ta ya samar maka da abin da zai inganta taka rayuwar,Wasu masu kuɗin na hakan ga ya'yan su wayen da ba su ɗauki duniyar da zafi ba,Su ɗin ma su kuɗi ne kam na ƙwaran gaske Jamilu ,Addu,a ta dai kai kawai Allah ya baka ikon sauke nauyin da ka ɗaukar wa kan ka,nauyi ne babba Jamilu kuma wallahi akwai cutarwa ciki idan ya zamo baka bata rayuwar da ta saba da ita ba kuma ka san cewa baka da abun da zaka inganta rayuwar ta da ita ɗin kamar yadda ta taso cikin gata.."
Shiru Gariti yayi ganin yadda Jamil ya juyo Yana kallon sa da idanun sa da suka ɗan sauya na zancen sa sai yanzu ya tuno da tabbas akwai cutarwa sosai alamarin ko a addini haka ne idan bazaka iya kula da yar mutane gwargwado da kulawar gidan su ba ko ka bata wadda ya ɗan kusan shi, kar ka kai kan ka gare ta akwai cutarwa sosai.
Yoo kana ɗauko yar mutane tana cin basmatic 🤨🥱😂Rice da shayi, Different kind of meat na halal😋 da duk wani kayan gina jiki na armashi ka bata tuwon dawa ko masara,ko Taiba wanda may be tun da ta taso gidan su bata taɓa haɗuwa dashi ba.Kai ma kasan dole ya zama cutarwa maganin adaina kar a fara.Kowa yayi rayuwar da take dai dai shi shine dai dai, kar ka ari ta kowa kayi taka ka ingan ta ta ta zamo abin ado agare ka.Wadda zaka samu farin ciki mai yawa cikin ta.✍️
Idanun sa ya sauke ƙasa yana sauke nannauyan ajiyar zuciya kafin ya kalli kudaɗen yana Ajiye su anan.Tare da rufe idanun sa da yake jin sun ma sa nauyi saboda kan shi da yake sara mashi ga rashin barci tun da ya saka wayar nan kwana ya gagari idanun sa.
Kana talakan ka ka ɗaukar wa kan ka ina Dalili.Ai ƙarya bata yi ba kam🤔😒😥
A ɓangaren masu ganin lefe kuwa bayan buɗe lefen wata guɗa ce ta ƙara kaurewa ganin danƙararriyar waya ƙirar iphone 16 Fara sol. Da ita cikin kwalin ta sai kuma system da tambarin su ke nuna wa kowa a tare aka siyo su kasancewar su duka kamfanin Apple.
Babu abun da ke fita abakunan manyan matan da su ba baƙon su bane ganin hakan dan sun ga fiye da haka ma. Yarinyar ta yi goshi haka akeso yar ɗakin Hajiya tayi goshi haka ake ta sanbatun kayan ana jin jina ƙoƙarin sa musamman yana yin da ake ciki sai dai hakan ya ƙara tabbatar musu da tabbas yarinya ta tsinci dami a akala domin sun tabbatar da Jamil mai kuɗi ne tabbas.Nadiya dake ƙoƙarin haɗiye abinda ke taso mata haka take bin kayan da kallo tana sakin murmushin yake bata yi tunanin Jamil ya kai haka ba sai yanzu da ta ga yadda ake Fiddo da wasu irin tsadddun kaya babu ɗan ƙasa da ɗari sai sama ko mai yayi kyau ga waya ga system itama daga nin ta kasan tana da kuɗin ta masu zaman kan su.
Haka ƙawayen da ita kan ta Nadiya suke ta ɗaukar kayan hoto ana watsawa a duniya mutane na ta sambarka.Najiba da ta ga kayan suman zaune tayi ta rasa wane irin yanayi take jin kan ta ciki lamarin ya zo mata a ba zata.Hawaye ta share masu sanyi wani irin farin ciki na mamaye ta.Ka sa haƙura ta yi ta rasa wanda zatayi sharing farin cikin da take jin kan ta a ciki na ganin kayan da ko a mafarki akace mata nata ne zata ƙarya ta.
Cikin azama ta fice daga ɗakin zuwa ɗakin mahaifiyar ta fuskar ta na cike da wani irin farin ciki.
Da Raliya ta fara cin karo a falon da ta faɗa wanda ko sallama bata yi ba.
Rungume ta tayi ajikin ta tsamm.
A ba zata Raliya dake zaune akan kujera tana duba wasu kayan da Ibrahim ya tura mata daga cikin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 39