Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na yi ƙundunbala da kuɗin da zan gyara muna gidan nan na siya Miki waya sannan a Auran mu na haɗa da rance ". Shiru yayi ya ɗan numfasa sannan ya cigaba da magana " Nayi nadama tun a farkon Auren mu,koda yaushe damuwa ta ɗaya ce ranar da zaki san gaskiya NAJIBA,ke da iyayen ki,ina tsoron ra saki,Wallahi Najiba son da nake miki da ace Ni mai arziki ne wallahi sai na Miki gatan da kowace mace zata so a duniyar ta,sai na zamo Miki irin mijin da kowace mace take burin samu,sai dai kash Hakan ba mai samuwa bane,saboda bana dashi,ta ɓoye ɓoye ta ƙare NAJIBA ina ƙara faɗa Miki Ni talaka ne ɗan talaka,amma duk da haka na Miki alƙawari zan baki kulawa ta musamman,zan ciyar dake gwargwadon iyawa ta da kuma a bun da nake dashi,zan nema kamar bazan samu ba Najiba dan na faranta miki na hanaki gani a gurin wasu na Miki wannan alƙwarin dan haka dan Allah ki yi haƙuri ki janye wata maganar rabuwa "Ya kai ƙarshen zancen yana sauke numfashi kafin Sannan ya cigaba da magana ya bata labarin yar jejeniyar su da Tanim da ya ce kar ya bada wata ƙofa da za,a gane shi ɗin wane ne domin ya san halin shi sarai kasancewar shi ogan su suna da labarin sa shida Gariti duk wani mugun aikin na sa atafin hannun su yake,saboda yana son rufe bakin shi sai ya bashi kyautar 1 million da kuma bashi aron gida da kuma lefe da motoci,da wasu daga kyaututtukan kasancewar ya fahimci yana mugun son Najiba,Yayi hakan ne kawai dan ya ƙara rufe masa baki duk da ya san cewa bazai taɓa faɗa ma koda NAJIBA ba ce dan shima yana tsoron rasa tashi a lokacin. Bai rufe mata komai ba sai da ya bayyanar mata da duk wani abun da bata sani ba. Duk wannan zancen da yayi mata bata motsa ba sai dai hawayen da take sharewa a hankali zuciyar ta na cigaba da ƙuna da tunanin irin sakarcin ta da kuma ɓakar rayuwar da ta jefa kan ta ciki,ita da yar uwar ta,Sai yanzu ta ke ƙara hango zancen yawan fitar ta da mahaifiyar ta ke hana ta,wanda kuma shine tushen komai domin yau kuɗin da zai kashe mata daban na gobe da ban ta mayar dashi ATM ba tare da ta san cewa Shi mai hantarar ta a bayan ta bane,kamar dai yar uwar ta da ta gina wa kan ta rame ta faɗa kamar ita.. Jikin ta ne ya yi wani irin sanyi nadama na saukar mata lokaci ɗaya. Zuciyar ta na mata zafi domin ta san cewa ita kan ta zata tsinci kan ta a kan wannan karagar ta kunya domin bata ga abun ɓoye ɓoye a ciki ba,sai dai tabbas ba zata zauna da Jamil ba yau ɗin nan sai ta kwana gidan su daga baya ya biyo ta da takardar ta. Cikin Ƙunar zuci ta furta masa a hankali " Ka bani takarda ta na wuce gidan mu " . Duban sa ya ƙara kaiwa akan ta yana rausayar da kan sa zuciyar sa na harbawa. Sannan cikin dakewa ya furta. " Babu wannan a cikin babin labarin soyayyar Jamilu ɗahiru da Najiba Ahmad ". Ajiyar zuciya NAJIBA ta sauke Domin ita kan ta bata wani ji zancen nata a jikin ta ba ta san cewa furucin yaudarar kan ta ne kawai tayi domin tabbas tana son Jamil so bana wasa ba kamar yadda yake son ta shima... Fuuu haka ta ja jakar ta da kuma mayafin ta da yasauka kasa tana jin zuciyar ta na cigaba da bugawa ta fice da ga ɗakin.Wanda Jamil kafin ya tara ta har ta fice. Da sauri ya biyo bayan ta sai dai kafin ya isa har ta kai zauren gidan ta fice. Sai hango ta yayi tana tafiya cikin sauri kamar harda kuka take yi ma. Faɗuwar gaba ce ta same shi sai dai bai hana ta tafiya ba domin ta san tabbas bata rasa kuɗaɗe a hannun ta na tafiya gida,ya san tafiyar itace maslaha a gare ta hakan ne kawai zai rage mata fushin da ta hau. Tuna yanayin yadda unguwar take shiru ne hakan ya sa ya fito d sauri ya bi bayan ta sai dai kafin ya isa har ta shiga keke napep koda ya iso har okada ɗin ta tashi. Shima ta rawa yayi ya shige ya bi bayan su Tafiya mai nisa suka yi kafin suka isa unguwar rijiyar lemu adai dai ƙofar gidan su NAJIBA. Jamil dake bin bayan ta cikin mamaki yake bin ta yana son yaga inda ta nufa domin ya ga ba gidan su ta nufa ba,to amma mai Zatayi anan ne,Bai gama zancen zucin na sa ba yaga napep ɗin ta ya tsaya a ɗan madaidaicin gidan su da suka mallaka,Wanda Kowannen su yake da kalar na shi burin a gurin iyayan nasu dan faranta musu musamman a yanzu da dukkanin su suka shige gidajen mazajen su.Sai dai abun da basu sani ba RALIYA ta fi su wannan burin na ganin ta tallafa ma Iyayen na su saboda a yan kwanakkin chan har girki tana aika musu dashi idan ta kwatanta, kuma ba wai Mama Hasiya kaɗai take Bawa ba har da Mama Hafsatu. Cikin mamaki haka Jamil yake bin gidan da kallo kafin ya biya masu napep ɗin har nata da ta bari bakin ƙofar gidan domin wani irin kuka na kunya ne da baƙin ciki ya taso mata bayan ganin shi a bayan nasu,wanda hakan ya tabbatar mata da komai nata itama ya buɗe kenan. Jamil kuwa ikon ALLAH yake ta kallo sai dai bai san wanda zai tambaya na abun da ke faruwa ba ganin NAJIBA a wannan ƙaramin gidan kuma a yadda ya lura da alama gidan sababbe ne a gare ta,yana son sanin meye haɗin ta da gidan. Kalle Kalle ya fara yi kafin idanun shi su sauka akan su malam Rabu'u da malam Abdul basiɗ dake zaune a gurin suna bin komai da idanu cikin mamakin meke faruwa domin a gaban idanun su komai ya wakana har ta shigewar ta gida idanun su na kan ta. Kowannen su fuskar shi ta nuna alamar tsorata sai dai basu bayyanar ba, dan tabbas muddin abinda zai saka NAJIBA kuka haka Babba ne,Sai kuma ga mijin ta shima a bayan ta wanda suka gani a yanzu shima hakan ya ƙara tabbatar musu da cewa akwai abun da ke faruwa. Kallon su yayi yana tuno da kamannnin Najiba ɗin da Nadiya,sai kuma tuna cewa suna cikin wayen da suka karɓi Auren su. Kuma tabbas ya tuna fuskokin su,May be yan uwan su ne dangin mahaifin ta,ƙila kuma ta shaƙu da su dan a irin wannan yanayin gun mahaifiyar ta ya kamata ta nufa da zancen itace kawai zata kwantar mata da hankali. Shiru yayi yana sauke a jiyar zuciya kafin ya matsa ya gayar da su cikin mutun ta juna shiru yayi bayan sun gama amsa masa yana sauke Ajiyar zuciya sai ya kasa magana saboda wani irin kwarjini da suka yi masa. Murmushi malam Abdul Basiɗ yayi kafin ya furta " Jamilu me ya faru kazo nan kayi tsaye kayi shiru " ? Cikin sauri Jamil ya ɗaga kan sa ya dube sa sai ya samu kan shi da ɗan sauke Ajiyar zuciya da sakin murmushi lokaci ɗaya dan wani irin kwanciyar hankali ne ya ji ya saukar masa lokaci ɗaya,tare da tsayuwar tunanin sa da zancen zucin sa. " Dama NAJIBA ce muka samu saɓani da ita ". Nan ya kwashe komai ya sanar musu domin haka kawai yaji natsuwa na saukar masa da su yana ji ajikin sa Bazasu taɓa goyon bayan NAJIBA ba.Daga ƙarshe ya rufe da basu haƙuri tare da furta yana neman Alfarmar Anema masa yafiya ga iyayen NAJIBA yana tsoron suce zasu raba Auren na su,saboda ya yaudari yar su da su kan su,Domin ya san masu kuɗi basa ƙaunar haɗa iri da talaka awannan zamanin. Har ya gama zancen babu wanda ya furta masa ƙala a cikin su sai dai bazaka iya tantance a bunda ke zaune a cikin zukatan su ba sai dai a zahiri zukatan su na cike da wani irin zafi na tausayin yar su,duk da hakan kuma basu ji ɗar kan Jamil ɗin ba domin kura ce ta ci kura saboda ita kan ta sun fahimci abinda ta tsunduma kan ta ne a ciki,ba tun yau ba sun san tana zuwa gidan Hajiya Samira,Wanda basu san dalili bama Mijin Hajiya Samira ya yi karan tsaye akan lamarin ashe wannan ne dalili. Sai yanzu suka ƙara fahimtar komai. Numfashi malam Rabu'u ya sauke da malam Abdul Basiɗ kafin suka kalli juna sannan malam Rabu'u ya gyaɗawa malam Abdul Basiɗ kai da alama akwai abun da yake son furtawa shine dalilin kallon ɗan uwan na sa yana neman izinin sa duk da ya san cewa ya isa da NAJIBA amma yana son jin ta bakin ɗan uwan sa. Ɗan gyaran murya Malam Abdul basiɗ yayi kafin a hankali ya furta.. " JAMILU ''! " Wannan shine mahaifin NAJIBA,Ni kuma nine mahaifin yar uwar ta NADIYA,wan mahaifin ta kenan "..Yakai karshen yana nuna malam Rabu'u dake zaune fuskar sa sai sa sai sa.Bazaka iya furta abinda ke zaune acikin zuciyar sa ba.Sai dai da alama hankalin sa kwance yake baya tare da wata damuwa sai ɗan Tausayin yar sa da ta tsunduma kan ta a rame mai zurfi. Abinda ta ke guje ma shine take tare dashi ba tare da ta sani ba.Talakan da ta guje ma yau shine mijin ta,mijin ta da take ma kallon wani shahararren mai kuɗi sai gashi rana tsaka ta fahimci bashi da komai talaka ne talak ashe sai ɗan kwangon da yake da shi. Wani irin rawa jikin Jamil ya ɗauka mamaki ya hana shi motsawa zuciyar shi ta shiga shawagi na tunanin lokuttan da suke da NAJIBA duk tsawon lokacin da suke tare tana bisa ƙarya ne itama.Shin me yake shirin faruwa ne...? Ya tambayi kan shi. Kafin ya rasa mai bashi amsa.So yake ya ɗaga idanun sa ya Kalle su sai dai ya kasa yana da tarin tambayoyi abakiin sa amma ya kasa iya furta musu. Numfashi ya sauke a hankali wnada ya fita da wani sanyi da zuciyar sa tayi masa nauyin da ke danƙare da zuciyar sa ya sauka. Ko me JAMIL zai furta oho🤦🥱 Yau dai KURA TA CI KURA NAJIBA.😂😂😂 ANKWASHI KUNYA KAMMM. Fa'eeh✍️ Chat me via WhatsApp or Telegram. No call... 08069059746 React,share,and comment pls 🙏 *_Typing_* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *_Masu son karanta labarin sai suyi following channel ɗita kai tsaye a chann zaku samu tun daga farko._*☝️ *🌸RAYUWAR MU AYAU🌸* Ƙarya ko sakin Aure Gajeren labari Na Faiza Almustapha Murai Daga Alƙalamin Fa'eeh Bg ✍️✍️ Sadaukarwa ga mahaifiyata Abar ƙaunata Allah ya ƙara miki tsawon rai Mai Albarka Mama✨✨✨. Amin. Bismillahir rahmanir Rahim 💪📚📚 *TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION* {T.W.A} https://www.facebook.com/profile.php?id=61565498797531 _Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda allah ya bawa ita da hikimar mu muke Alfahari_ *Aƙalaminmu ƴancinmu💪* > >>><<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>>>> _*Daga marubuciyar littafin*_ _*A Mafarki Nasanta*_✍️ And now _*Rayuwar mu a yau*_ P.23 Wani irin bugu ƙirjin nata ya ƙara yi wanda ya haddasa mata rawar jiki da sauyawar idanun ta da suke da haske izuwa jaaa,inda take hawaye suka fara saukar mata wayen da basu da lokacin daina tsayawa.Alamomin da ta gani na iyakar gaskiyar zancen sa ne ya ke faɗa mata yasanya ta fahimtar yadda tunanin ta ya juya mata da yake nuna mata abun kamar almara.A yanzu bugun zuciyar ta ya tsananta ta tsinci kan ta a cikin mawuyacin halin da bata taɓa tunanin zata haɗu da hakan a rayuwar ta ba. Shin me yake shirin faruwa da ni. Ta furtawa kan ta a cikin zuciyar ta. Idanun ta,ta sauke ƙasa daga na shi kafin ta share hawayen da ya silalo mata a kan fuskar ta.Da ƙyar ta iya buɗe bakin ta ta furta masa cikin ƙarfin hali da danasin halin da ta jefa kan ta da kan ta ta biye wa son zuciyar ta ta kai kan ta a inda bata taɓa tunanin ta samu kan ta ciki ba. Dan Gara ace tun farko haka ta Auri abun ta, kasancewar ita ɗin ma ba yar kowa ba ce kamar sa da ta sani a yanzu. " Na tabbata wannan zancen naka babu ƙarya a cikin sa,sai dai ka sani daga yau babu Auren mu yadda ka dabaibaye ni da ƙaryar ka,ka yaudare Ni to tabbas ka yaudari Auran ka,Ka bani mamaki Ya Jamil,ace duka tsawon wannan lokaci kana zaune a kan ƙarya ne,Me yasa baka zomin a yadda kake ba,me yasa ". Kuka ne ya ƙwace mata na baƙin ciki ba dan komai ba sai dan tuna itama nata a sirin na gab da tonuwa zata ji kunya kamar yadda ta san a yanzu Jamil yake jin ta,ina ma bata biyewa son zuciya ba., " Ni na jawa kaina,da na sani da ban yaudari kai na ba,me ya sa zan Ari rayuwar da bata dace dani ba,me yasa zan biye wa son zuciya da tarin ƙawaye,mai yasa na yi kitson wance banyi gashin ta ba ". " Kenan Yaya Jamil komai na mu na ƙarya ne,motar da na saka raina akan ta itama duka ƙarya ce,lefe na ma kenan ba satar shi aka yi ba ɗaukar shi akayi kamar yadda na ga an tsame kayana har da suke sababbi an kwashe ba companyn da aka haɗa lefen ". Najiba ta yi wayen kalaman cikin zubar da hawaye masu zafi. Jamil da bai san inda zancen ta na farko ya nufa ba ya Kalle ta da runannin idanun sa cikin tashin hankali,babu abun da ya ɗaga masa hankali irin zancen rabuwar Auren na su da take furtawa wanda har yanzu shi bai hango hakan ba,koda kowa zai taru akan sa,yana tare da ita mutu karaba sai dai ayi mai yi,Amma bazai taɓa sakin Najiba ba,Auren su babu saki a cikin sa. Ƙasa ya bi ta shima daga inda ta durƙushe yanzu ya furta " Najiba soyayyar ki ce sila,ba komai ya kai ni tsunduma a rayuwar karya ba sai ke, kasancewar ki yar masu kuɗi ya sanya dole na bi Miki ta hakan ke da iyayen ki,domin na san a talaka na ba bazaki taɓa bani dama ba,bare iyayen ki saboda na san yadda a wannan lokaci masu kuɗi suka tsani Aurawa yar su ɗan talaka ko Aurawa ɗan su yar talaka sai ma suka shafe hakan ta hanyar yin ƙwarya tabi ƙwarya atsakanin su inda Wannan haɗin ya zamo tarihi sai kaɗan daga cikin su. Ni kuma duk da ina taɓa ƙaryar sai dai ban kai sosai ba kamar yadda na jefa kaina a ciki yanzu,kuma duk saboda ke ne NAJIBA,Ni masoyin ki ne na gaskiya NAJIBA,tsoron rabuwa dake ya sa na ƙara bawa wannan rayuwar zama a littafin rayuwa ta ya zamo a cikin jerin fejika dake tsare a ciki,Najiba tun da ga iyayen da suka nemi Auren ki har companyn har motoci da duk wani abu da kika sani na kuɗi NAJIBA ba na wa bane,wayar hannun ki ce kawai na yi ƙundunbala da kuɗin da zan gyara muna gidan nan na siya Miki waya sannan a Auran mu na haɗa da rance ". Shiru yayi ya ɗan numfasa sannan ya cigaba da magana " Nayi nadama tun a farkon Auren mu,koda yaushe damuwa ta ɗaya ce ranar da zaki san gaskiya NAJIBA,ke da iyayen ki,ina tsoron ra saki,Wallahi Najiba son da nake miki da ace Ni mai arziki ne wallahi sai na Miki gatan da kowace mace zata so a duniyar ta,sai na zamo Miki irin mijin da kowace mace take burin samu,sai dai kash Hakan ba mai samuwa bane,saboda bana dashi,ta ɓoye ɓoye ta ƙare NAJIBA ina ƙara faɗa Miki Ni talaka ne ɗan talaka,amma duk da haka na Miki alƙawari zan baki kulawa ta musamman,zan ciyar dake gwargwadon iyawa ta da kuma a bun da nake dashi,zan nema kamar bazan samu ba Najiba dan na faranta miki na hanaki gani a gurin wasu na Miki wannan alƙwarin dan haka dan Allah ki yi haƙuri ki janye wata maganar rabuwa "Ya kai ƙarshen zancen yana sauke numfashi kafin Sannan ya cigaba da magana ya bata labarin yar jejeniyar su da Tanim da ya ce kar ya bada wata ƙofa da za,a gane shi ɗin wane ne domin ya san halin shi sarai kasancewar shi ogan su suna da labarin sa shida Gariti duk wani mugun aikin na sa atafin hannun su yake,saboda yana son rufe bakin shi sai ya bashi kyautar 1 million da kuma bashi aron gida da kuma lefe da motoci,da wasu daga kyaututtukan kasancewar ya fahimci yana mugun son Najiba,Yayi hakan ne kawai dan ya ƙara rufe masa baki duk da ya san cewa bazai taɓa faɗa ma koda NAJIBA ba ce dan shima yana tsoron rasa tashi a lokacin. Bai rufe mata komai ba sai da ya bayyanar mata da duk wani abun da bata sani ba. Duk wannan zancen da yayi mata bata motsa ba sai dai hawayen da take sharewa a hankali zuciyar ta na cigaba da ƙuna da tunanin irin sakarcin ta da kuma ɓakar rayuwar da ta jefa kan ta ciki,ita da yar uwar ta,Sai yanzu ta ke ƙara hango zancen yawan fitar ta da mahaifiyar ta ke hana ta,wanda kuma shine tushen komai domin yau kuɗin da zai kashe mata daban na gobe da ban ta mayar dashi ATM ba tare da ta san cewa Shi mai hantarar ta a bayan ta bane,kamar dai yar uwar ta da ta gina wa kan ta rame ta faɗa kamar ita.. Jikin ta ne ya yi wani irin sanyi nadama na saukar mata lokaci ɗaya. Zuciyar ta na mata zafi domin ta san cewa ita kan ta zata tsinci kan ta a kan wannan karagar ta kunya domin bata ga abun ɓoye ɓoye a ciki ba,sai dai tabbas ba zata zauna da Jamil ba yau ɗin nan sai ta kwana gidan su daga baya ya biyo ta da takardar ta. Cikin Ƙunar zuci ta furta masa a hankali " Ka bani takarda ta na wuce gidan mu " . Duban sa ya ƙara kaiwa akan ta yana rausayar da kan sa zuciyar sa na harbawa. Sannan cikin dakewa ya furta. " Babu wannan a cikin babin labarin soyayyar Jamilu ɗahiru da Najiba Ahmad ". Ajiyar zuciya NAJIBA ta sauke Domin ita kan ta bata wani ji zancen nata a jikin ta ba ta san cewa furucin yaudarar kan ta ne kawai tayi domin tabbas tana son Jamil so bana wasa ba kamar yadda yake son ta shima... Fuuu haka ta ja jakar ta da kuma mayafin ta da yasauka kasa tana jin zuciyar ta na cigaba da bugawa ta fice da ga ɗakin.Wanda Jamil kafin ya tara ta har ta fice. Da sauri ya biyo bayan ta sai dai kafin ya isa har ta kai zauren gidan ta fice. Sai hango ta yayi tana tafiya cikin sauri kamar harda kuka take yi ma. Faɗuwar gaba ce ta same shi sai dai bai hana ta tafiya ba domin ta san tabbas bata rasa kuɗaɗe a hannun ta na tafiya gida,ya san tafiyar itace maslaha a gare ta hakan ne kawai zai rage mata fushin da ta hau. Tuna yanayin yadda unguwar take shiru ne hakan ya sa ya fito d sauri ya bi bayan ta sai dai kafin ya isa har ta shiga keke napep koda ya iso har okada ɗin ta tashi. Shima ta rawa yayi ya shige ya bi bayan su Tafiya mai nisa suka yi kafin suka isa unguwar rijiyar lemu adai dai ƙofar gidan su NAJIBA. Jamil dake bin bayan ta cikin mamaki yake bin ta yana son yaga inda ta nufa domin ya ga ba gidan su ta nufa ba,to amma mai Zatayi anan ne,Bai gama zancen zucin na sa ba yaga napep ɗin ta ya tsaya a ɗan madaidaicin gidan su da suka mallaka,Wanda Kowannen su yake da kalar na shi burin a gurin iyayan nasu dan faranta musu musamman a yanzu da dukkanin su suka shige gidajen mazajen su.Sai dai abun da basu sani ba RALIYA ta fi su wannan burin na ganin ta tallafa ma Iyayen na su saboda a yan kwanakkin chan har girki tana aika musu dashi idan ta kwatanta, kuma ba wai Mama Hasiya kaɗai take Bawa ba har da Mama Hafsatu. Cikin mamaki haka Jamil yake bin gidan da kallo kafin ya biya masu napep ɗin har nata da ta bari bakin ƙofar gidan domin wani irin kuka na kunya ne da baƙin ciki ya taso mata bayan ganin shi a bayan nasu,wanda hakan ya tabbatar mata da komai nata itama ya buɗe kenan. Jamil kuwa ikon ALLAH yake ta kallo sai dai bai san wanda zai tambaya na abun da ke faruwa ba ganin NAJIBA a wannan ƙaramin gidan kuma a yadda ya lura da alama gidan sababbe ne a gare ta,yana son sanin meye haɗin ta da gidan. Kalle Kalle ya fara yi kafin idanun shi su sauka akan su malam Rabu'u da malam Abdul basiɗ dake zaune a gurin suna bin komai da idanu cikin mamakin meke faruwa domin a gaban idanun su komai ya wakana har ta shigewar ta gida idanun su na kan ta. Kowannen su fuskar shi ta nuna alamar tsorata sai dai basu bayyanar ba, dan tabbas muddin abinda zai saka NAJIBA kuka haka Babba ne,Sai kuma ga mijin ta shima a bayan ta wanda suka gani a yanzu shima hakan ya ƙara tabbatar musu da cewa akwai abun da ke faruwa. Kallon su yayi yana tuno da kamannnin Najiba ɗin da Nadiya,sai kuma tuna cewa suna cikin wayen da suka karɓi Auren su. Kuma tabbas ya tuna fuskokin su,May be yan uwan su ne dangin mahaifin ta,ƙila kuma ta shaƙu da su dan a irin wannan yanayin gun mahaifiyar ta ya kamata ta nufa da zancen itace kawai zata kwantar mata da hankali. Shiru yayi yana sauke a jiyar zuciya kafin ya matsa ya gayar da su cikin mutun ta juna shiru yayi bayan sun gama amsa masa yana sauke Ajiyar zuciya sai ya kasa magana saboda wani irin kwarjini da suka yi masa. Murmushi malam Abdul Basiɗ yayi kafin ya furta " Jamilu me ya faru kazo nan kayi tsaye kayi shiru " ? Cikin sauri Jamil ya ɗaga kan sa ya dube sa sai ya samu kan shi da ɗan sauke Ajiyar zuciya da sakin murmushi lokaci ɗaya dan wani irin kwanciyar hankali ne ya ji ya saukar masa lokaci ɗaya,tare da tsayuwar tunanin sa da zancen zucin sa. " Dama NAJIBA ce muka samu saɓani da ita ". Nan ya kwashe komai ya sanar musu domin haka kawai yaji natsuwa na saukar masa da su yana ji ajikin sa Bazasu taɓa goyon bayan NAJIBA ba.Daga ƙarshe ya rufe da basu haƙuri tare da furta yana neman Alfarmar Anema masa yafiya ga iyayen NAJIBA yana tsoron suce zasu raba Auren na su,saboda ya yaudari yar su da su kan su,Domin ya san masu kuɗi basa ƙaunar haɗa iri da talaka awannan zamanin. Har ya gama zancen babu wanda ya furta masa ƙala a cikin su sai dai bazaka iya tantance a bunda ke zaune a cikin zukatan su ba sai dai a zahiri zukatan su na cike da wani irin zafi na tausayin yar su,duk da hakan kuma basu ji ɗar kan Jamil ɗin ba domin kura ce ta ci kura saboda ita kan ta sun fahimci abinda ta tsunduma

Chapter 19 of 39